Showing 36001 words to 39000 words out of 307403 words

Chapter 13 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

ka fahimce ni,bakasan cewa niba musulma bace!ko daddynku bai ta6a faɗa maka bane,Ni bana sallah,I don't even know how to do it,"
  Jin haka yasa junaid sake fashewa da wani sabon kukan mai sautin gaske yana cewa"Mommy ki tashi muyi sallah,ki tashi mommy!wlh idan baki tashi munyi sallah kinmun addu'a ba mutuwa zanyi,"
  Tashin hankali,gaba daya junaid yabi ya rikice mata ya hanata sakat,duk yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita ba musulma bace,bata sallah amma abun ya faskara,junaid ya kurmance mata,
  Babu arziƙi ta amince zatayi sallar,tasata gaba yayi ta shiga toilet ta dauro alwala,ko alwalar bata wani iyaba,ruwa kawai ta watsa a fuskarta,ta wanko hannayenta da kafafuwanta tafito,shi ma ya shiga cikin toilet ɗin,wucewa tayi wurin wurin closet ɗinsu,ta buɗe kayan Abbansu ne a jere sai kayan sawar ta,wanda tazo dasu,gaba daya babu hijabin da zata sanya,dakyar ta samu wani mayafin doguwar rigarta mai ɗan tsayi,ta ɗauko shi tare da sanyashi ajikinta,sae yayi mata tamkar hijabi,
  tsayawa tayi tana jiran junaid ya fito suyi sallar,lamarin nashi ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ƙiri ƙiri junaid yasata za tayi sallah,ya rufe idonshi ya nuna tamkar baisan cewa ita ba musulma bace,aranta tace"Anya junaid bai samu ta6in hankali ba?in ba haka ma meyasa zai yi forcing ɗina akan inyi salla bayan yasan cewa ni ba musulma bace,Omg!ni bansan ma ya akeyin sallar ba,ko time ɗin baya dana ta6a musulunta ba don Allah nayi ba,ko sallah banyi a lokacin,"
tana cikin zancen zucin nata sai ga junaid ya fito daga cikin toilet yana faman yarfa hannunshi,ruwan alwalar da yayi yana ɗiɗɗigowa ƙasa,
   Carpet ɗin salla ya dauko masu na abbansu sannan ya dawo ya shimfiɗa masu shi,
  Juyawa yayi tare da kallon Mommyn tasu wanda tayi sototo tana binshi da kallo,
  "Ni zan shiga gaba saiki tsaya abaya,"
   Dawowa bayanshi tayi ta tsaya,shi kuma ya tsaya agaba,tare da daidaita natsuwarshi,ya kabbara sallar,anatse suka shiga yin sallar atare,tunda suka kai raka'a dayan farko,bacci ya kwashe Alexandra,junaid bai sani ba yaci gaba da yin sallarshi,sai da yayi kusan raka'a takwas sannan ya sallame,
  cikin bacci taji an ambaci sunanta da ƙarfi"Mommy"!!a firgice ta farka tare da buɗe idanunta tana kallonshi,muryarta adisashe irin ta mai bacci tace"junaid har mun kammala sallar,"zum6ura mata baki yayi rai a6ace yace"nadai kammala sallar mommy,kin barni ni kaɗae,kina ta bacci,"
  cikin lallashi tace"kayi haƙuri romeo ɗina,saida na faɗa maka cewa banyin sallah,nifa ban iya ba,nadai samu nayi ɗaya,dakyar itama na samu nayi ta,don bacci nake ji,"
  "Shikenan kiyimun addu'a yanxu,sai muje mu kwanta"
  Yadda yayi maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,nan take taji kamar bata kyauta mashi ba,jiki asanyaye ta sanya hannunta tare da ruƙo hannunshi,ta shiga karanta mashi addu'oin,cikin harshen Faransanci,bai damu da yaren da takeyi mashi addu'ar ba,saboda yasan cewa Allah yana ji da kowani irin yare aka roƙesa,"
  Ta jima tanayi mashi addu'a tana tottofa masa asaman sumar kanshi,kafin daga bisani suka koma saman gadon suka kwanta,ba ƙaramin kwanciyar hankali junaid ya samu ba,tunda ta tofa mashi addu'ar nan take yaji wani sanyi aranshi,tamkar an bashi ƙwarin guiwa,kuma tunda ya kwanta bacci ya ɗaukeshi bai ƙara jin an zungure shi ba,

DARE YAYI GARI YA WAYE,

Tun bayan Kammala Sallar asuba,Azmee da Saude,Suka fara ɗaura girke girken da zasuyi anan cikin gida,Uban aiki ne a gabansu,saboda Abinci ne kala kala zasuyi,na kasashe daban daban,saukin su ma Naman da za'a yanka basu zasuyi aikinshi ba,An riga da an bada aikin naman already,sai dai kawai in an kammala akawo masu shi Hada snacks sukayi order wanda za'a ci,akwai kuma Naman da Azmee zatayi masu farfesu dashi,da kuma tsiren nama,don ta kware a wannan 6angaren,Sunyi nisa acikin aikin sai ga Hajiya azeema ta shigo,bayan sun gaisa da junansu,itama tace tazo ayi aikin da ita,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,nan suka haɗu su uku,suka tasar ma girkin nan,Cikin ƙanƙanin Lokaci,Wani irin daddaɗan ƙamshi ya gauraye ko'ina na kitchen ɗin,

Hatta main palour ɗin kamshi ya karaɗe cikinsa,gwaggon katsina dake kwance,saman gado,tun bayan sallar asuba ya ɗauketa,tana cikin bacci ta dinga jin ƙamshin abinci nashiga Hancinta,ba arziƙi ta farka tana faɗin"wannan wani irin ƙamshi ne mai tashin mutun daga bacci"?tana maganar tana shinshinar kamshin,saukowa tayi daga saman gadon,jikinta sanye da kayan baccin nan nata na gado,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nata tana tunkarar inda kamshin ke fitowa,

Kamar daga sama suka ji muryar gwaggo tana cewa"Ikon Allah,ƙamshi ya tashe ni daga bacci,ya kawo ni cikin kitchen,don inci daɗi,"
  Murmushi suka saki gaba ɗayansu,kafin suka shiga gaishe da ita,
  ƙarasawa tayi cikin kitchen ɗin suna haɗa ido da saude ta watsa mata harara tare da cewa"ya akai kuka bar wannan tana girki?bafa ta iya girki ba,Rannan ta zuba mana Gishirin lalle amatsayin gishiri cikin farfesun nama,gaba ɗaya girkin nan bai ciyu ba,ƙarshe saboda tsoran kar asirinta ya tonu inyi mata faɗa,ta dauki farfesun ba tare da sanin kowa ba taje ta zuba ma karnukan layinmu,kunsan kare da nama nan fa suka lashe farfesun nan tasss suka cinyi shi,aikuwa cikinsu ya kumbura sumtum,sukayi mussai,gaba ɗaya suka mace aka zubdo su,mai karnukan nan yace bazai yarda ba,sai yayi shari'a da Saude,ranar saude har gudawa saida tayi don jin za'a kaita ƙara kotu,yarinya tabi ta burkice mana,daƙyar Harrisu ya biya diyarsu,daba don haka ba,da tuni saude an jima da yanke mata hukuncin kisa....'
  Tunkan gwaggo takai karshen Labarin da take basu gaba ɗaya suka fashe da dariya,banda saude wadda ta tur6une fuska,rai a6ace tace"Kai gwaggo,"
  gwaggo tace"ƙarya nayi?ko ba haka akayi ba,ki faɗi tsakaninki da Allah in ba ayi hakan ba,ranar fa har gudawa kikayi,kika dinga kuka kina cewa gwaggo ki maishe ni rugarmu,saboda kawai na kashe karnuka shine za'a kai ƙarata kotu,wlh ko shanun baffa na kashe ba za'ayi mani wannan hukuncin ba,sai ku ƴan gayu da kuka ɗauki ran kare da mahimmanci karen da ko hisabi baza'ayi dashi ba,"
  Sake fashewa da dariya sukayi,yadda gwaggo take kwaikwayon muryar Saude,ba ƙaramin dariya ta basu ba,saboda hausar irin ta fulanin da basu kware bace,"
fuskar saude tamkar zatayi kuka,batasan meyasa gwaggo keyi mata haka ba,duk in suka shiga cikin mutane saita kunyata ta,wannan labarin da take bayarwa ya jima da faruwa,tun lokacin da Dr harris ya ɗaukota daga rugarsu ya kawota gidansu,lokacin batasan komai ba,ita arayuwarta ba abunda ta bama mahimmanci inba Kiwon shanu ba shi kadae tafi sani,gwaggo kuma bata koyar da ita komai ba,kwana uku da zuwanta gidan ne,ta shiga kitchen ta ɗaura masu girki,tana cikin girkin ta fara neman gishiri zata zuba acikin,gafa gishirin acikin farar roba an zubashi,amma saboda ta saba ganin gishiri kulle acikin leda yasa tayi zaton koba gishiri bane,hakan yasa ta fito ta wuce ɗakin gwaggo don ta sanar da ita cewa babu gishiri a gidan,tana shiga ɗakin gwaggon katsina,ta same ta tana bacci,harta juya zata fita shine taga wasu kullun kaya da aka kawoma gwaggo acikin leda,nan fa ta shiga laluban kayan,ta zaƙulo ledar gishirin lalle ta fuce dashi,duk a tunaninta gishiri ne,dayake kanta a toshe yake,kwata kwata bata lura da lallen dake acikin ledar ba,ita dae kawai gishirin lallan ta ɗauko,taje ta zuba masu acikin girkin,ba don Allah yasa gwaggo ta tashi tana neman gishirin lallanta ba,har saude taji,daba ƙaramin illa zata yi masu ba,karshe dai abun kan karnukan layinsu ya ƙare,tun daga wannan lokacin ne harris ya sanyata a makaranta,da kuma makarantar koyon girki,har ta samu ta kammala secondary,daga nan ne akasamu kanta ya waye,
  "Gwaggo me kikeso a zuba maki ne?nasan yunwa ce ta koro ku,"azmee ce tayi maganar,
  Gwaggo tace"komi ma da kuka girka,a zuba mun in ɗanɗana inji yaya ɗanɗanon girkin naku yake,don tunda kuka sanya saude acikin girkin nan naku nasan cewa dole a samu matsalar rashin gishiri kodae ta zuqa shi,ko kuma yayi kaɗan,"
murguɗa mata baki saude tayi tare da juyawa ta shige cikin store,tana faɗin"nashiga uku da wannan matar,a haka Haris yakeso in zama surukarta,bansan ya zan ƙare da ita ba,lafiya lou nake yin girkina acan gida,har santi takeyi amma yanzu tazo sai sharri takeyi mun agaban mutane,Zamu koma gida ne,nasan me zanyi mata,ae mun saba dama,"
  Saude bata fito daga cikin store ɗin ba,sai da taji fitar gwaggo daga kitchen din,bayan sun zuzzuba mata abincin da suka girka,komai sai da tasa suka zuba mata,a ƙaton tray ta fuce dashi tana cewa"idan na cinye wannan zan dawo a ƙara mun,"
  dawowa tayi cikinsu suka cigaba da aiki,azeema tace"sai kin dinga haƙuri da ita,bayin kanta bane,ku tayata da addu'a,Allah ya yaye mata wannan haukan da aka ɗaura mata,"
  Saude tace"insha Allah,zamu cigaba da tayata da addu'a,ae yaya harris ya sanar dani komai,na tausaya mata sosai,Allah dai ya tonu asirin waɗanda ke shirya masu wannan maƙarƙashiyar,Allah ya kawo ƙarshensu,"
  Azmee tace"ae bazasu kai labari ba,a sannu asannu zasu gane kurensu,"
  Suna aiki suna tattaunawa game da irin rayuwar da su sehrish sukayi a baya,

Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin tamkar ba'a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziƙin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buƙaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za'a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar ƙasa da naira dubu ɗari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuɗaɗen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin ɗaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu ɗari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haɗa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai ƙaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan ɗaya,Jahad miliyan ɗaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu ɗan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka'aba ɗakin Allah,harma in roƙe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,

Sehrish na cikin toilet tana wanka,amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi akan Sgr,kalamanshi na jiya ne suka shiga dawo mata acikin kanta,dole tayi aiki a ƙarkashin shi batasan meyasa yake son ganinta a matsayin ƴar aikinsa ba,
Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo muryar jahad,daga waje tana cewa"Sehrish dan Allah kiyi sauri ki fito,inaso nima nayi wankan,kafin asake kiran mu,"
jin haka yasa tayi saurin kammala wankan ta fito,ɗaure da towel a waist ɗinta,shiga ciki jahad tayi,don tayi wankan itama,duk hosana na zaune gefen gadonsu hannunta ruƙe da biro da memo din Sehrish sae faman lissafin kyaututtukan da suka samu takeyi,"
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"Aiki ya same ki hosana,kowa na ɗokin zuwa yayi wanka amma ke hankalinki na akan kuɗin da muka samu,abunda baki sani ba,idan mukayi wanka mu kayi kwalliya,sae mun samu ninkin abunda muka samu a yanzu,"
Juyowa hosana tayi tare da waro ido jin an ambaci kuɗi tace"dagaske kike sehrish idan mukayi wanka mukayi kwalliya zamu samu fiye da wannan kuɗin da muka samu"?
Jinjina kai sehrish tayi tace"kwarai kuwa,ke dai kawai ki tashi ki fara yin wanka,jahad na fitowa,ki shige ciki,"
Cike da zumuɗi ta miƙe ta koma ta tsaya a kopar shiga toilet ɗin tana kwankwasa ma jahad,
"Ki fito nima in shiga,"
Murmushi sehrish ta saki,dama wayau tayi mata,don taji ɗazu suna magana da jahad tana cewa ita ba yanzu zatayi wanka ba,sae da marece,bayan tun yanzu akeso su shirya,don agansu da kyau,
Gaban dressing mirror ta zauna,tana shafa mai ajikinta,sae faman sauri takeyi saboda taje part ɗin Sgr,kamar yadda ya umarce ta akan taje da safe ta kai mashi breakfast ɗinshi,kuma ta gyara mashi bedroom ɗinsa,light makeup tayi a fuskarta,saboda wannan wankan safe ne zata ɗauka,da anjima Azmee tace za'ayi masu makeover,tamkar brides haka zasu fito,

Bayan ta kammala yin kwalliyar,komawa tayi wurin wardrobe din kayansu ta buɗe tana ƙare masu kallo,dama kullum zata zura kaya ajikinta sai ta tsaya yin ruwan ido wurin za6en kayan da zata sanya,
"Da rana zan sanya shadda lace ɗita,da marece kuma zan ɗauki wankan Swiss lace,yanzu dae bari na sanya wannan Arab gown ɗin,naga sai faman ƙyalli takeyi,in na sanyata ajikina,ba ƙaramin kyau zanyi ba,"ta ƙarasa maganar tare da janyo rigar,golden colour ce,gaba ɗaya jikinta adon stones ne masu ƙyalli da ɗaukar ido,batare da 6ata lokaci ba ta shiga kiciniyar zura rigar ajikinta,daƙyar ta shigeta saboda ta matse ta,gaba ɗaya tabi shape ɗin jikinta,kirjinta ya fito sosai,ga wani uban hips daya bayyana ajikin kayan,dama akwaita da diri sosai,don dai bata cika sanya kayan da zasu bayyana surar jikinta bane,hannun rigar na net ne,dogo ne ya kawo har wrist ɗinta,kana hangen fatar hannunta ta ciki,
siririn mayafin ta ɗauko,ta sanyashi asaman kafaɗarta,wa'iyazubillah,ba ƙaramin wankuwa sehrish tayi ba,juyowa tayi tare da kallon Hosana wadda ta saki baki tana kallonta,tace"Nayi kyau,"
Yadda hosana ta saki baki,tana kallonta ko kyaftawa batayi ba ƙaramin dariya ya bata ba,har saida ta ambaci sunanta,sannan hosana ta iya buɗe baki tace"Wlh kinyi kyau Sehrish sosai,kamar ƴar matan aljanna,"
Dariya Sehrish tayi yayin da ta koma gaban mirror tana kallon kanta,hannu tasa tare da daukar kwalbar turarenta,tabi jikinta ta feshe,sannan ta fuce daga ɗakin,tun da tafito idon kowa ya dawo kanta,abokanan matasan gidan da suka hallara a babban falon,duk saita tsargu,kitchen ta wuce anan ta samu Azmee tana zuzzuba ma saude abinci acikin warmers tana fitarwa waje,wurin baƙi tana kai masu,
Ae tunda azmee tayi arba da ita tashiga zuzuta kyanta,
"Aunty Azmee ni nasan ban kai haka ba,kawai kina hura mun kaine,".

Azmee tace"ae kin zarce duk yadda nake faɗi maki,dama shi mai kyau bai gane yana da kyau,sai in ana faɗi,"
murmushi kawai ta saki tare da cewa"Aunty azmee ina kayan breakfast ɗin babban yaya inaso nakai mashi,"
"Oh kin manta cewa abusufyan ya hanaki"?
"Nasani Aunty azmee,bansan ya zanyi bane,babban yaya jiya yace,baison ki ƙara aiki part ɗinsa,ni kawai yakeso in dinga zuwa inayi mashi aiki,kuma har faɗa mashi nayi akan cewa daddy ya hanani amma yace shi babu ruwanshi,kawai nayi mashi aiki,
Jinjina Kai azmee tayi tare da cewa"Tabɗijancan,aikuwa akwai matsala!don wlh Abusufyan yaji wannan maganar bazai yadda ba,kuma ke in banda abunki kin manta wanene abusufyan a wurinki,mahaifinki fa ne,taya zaki tsallake umarninsa kibi na babban yayanku?hakan na nufin cewa yafi iko dake akan mahaifinki?kina ganin cewa abusufyan zaiji daɗi idan yaji cewa kin cigaba da yi mashi aiki"?
Jin wannan maganar ta azmee yasa jikinta yin sanyi,sunnar da kanta ƙasa tayi,tuni idonta sun ciko da kwalla,
Gyaɗa kai azmee tayi tare da cewa"Nasan don baki da yadda zakiyi ne sehrish,zan shirya maki breakfast ɗin ki kai mashi,amma karki kuskura ki bari Uncle abusufyan ya gani,kuma koda ya kamaki,kada ki sanya sunana aciki,"
Amsa mata tayi da toh,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta shirya mata warmers da sauran tarkacen abincin acikin kayataccen tray ta bata takai mashi,'
Tunda sehrish ta fito daga kitchen ɗin gabanta ke faduwa sai faman waige waige takeyi,tsoranta kar daddynsu ya ganta,cikin sa'a ta haye upstairs batare da taci karo dashi ba,
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin data ƙarasa cikin falonshi,babu kowa aciki,hakan yasa ta tunanin ko bai tashi daga bacci bane,tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinshi,taji muryar namiji a bayanta,
"Ji mana,"a firgice ta juyo don taga wanene,ɗan zaro ido tayi tana kallon matashin daya biyota,acan falo ta ganshi tare dasu kanal yousouf da alama abokinsu ne,
Murmushi ya sakar mata tare da cewa"Am sorry na biyo bayanki batare da saninki ba,nagaza jurewa ne shiyasa na yanke shawarar yin hakan,'
muryar sehrish na kerma tace"Am...um..dan Allah ka jira ni awaje,yanzu zan fito,
"Okey,zan tsaya awaje,but pls don't stay long,"
Ya faɗi hakan tare da juyawa zai fita,har ya sakai zai fita daga falon,ya kuma juyowa tare da kallonta har lokacin tana a tsaye yace"Kin tafi da imanina sosai,zan iyayin komai don na mallake ki,"ya ƙarasa maganar tare da fucewa,
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke aranta tace"Kowanene wannan jarababben,baisan nan part ɗin wanene ba,so yake yaja mun masifa,ya wani kwaso kafafunshi ya biyo ni,'
kamar ance ta juya,idanunta suka sauka kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,fuskar nan kwata kwata babu annuri,daga shi sai short fari ajikinsa,

Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,ƙiris ya rage ta saki tray ɗin hannunta,tuni jikinta ya soma rawa,

  "Zoki wuce ciki,"yayi maganar babu alamun wasa a fuskarshi,jiki na rawa ta nufi bedroom ɗin nasa,matsa mata hanya yayi ta wuce,sannan ya kama hanya azafafe ya fito daga falonsa,anan waje ya samu saurayin nan,tsaye yana jiran fitowar sehrish bawan Allah,ya ɗauki wankan suits,sae faman zabga murmushi yake yi,
..jin an ta6a kafadarshi yasa shi juyowa don yaga wanene,gabansa ne ya faɗi Rasss lokacin da yayi arba da sgr tsaye agabanshi ya ruƙe qugu,tamkar zaki haka ya koma mashi,mugun tsoranshi suke ji,saboda ko magana bata ta6a haɗashi da abokanan ƙannenshi ba,labarinshi kawai suke ji a wurin su Irfan,babu wanda baisan Sgr ba,wato babban yaya,
  Fuskarshi a tamke yace"Wani ganganci ne yasa ka biyota har cikin part ɗina!"?
   Muryarshi na kerma yace"wlh ni ba ita na biyo ba,zuwa nayi kawai don in gaishe ka,dama Jabeer ne yace yakamata muzo mu miƙo gaisuwa wurin babban yayansu,kaji dalilin dayasa na kwaso ƙafata nazo,"
  Wani irin kallo sgr ya wurga mashi,jin ya sharara mashi ƙarya bayan yaji duk abunda yake faɗa ma sehrish,
  Sunnar dakai saurayin yayi yana faman mazurai,tsoranshi karya kai mashi naushi,
   Hannu Sgr yasa tare da ruƙo neck tie ɗinsa yace"menene sunanka"
   Cikin sauri yace"Jazz,"
Sgr yace"Jazz ko?let me warn u,ka tsaya a iya matsayinka,in ba so kake ka kwana a gadon asibiti ba,ka rufe idanunka daga kallon matan mutane,hakan zaisa ka zauna lafiya,'yana kai ƙarshen maganarshi yace"just u can leave....."ae tunkan sgr ya ƙarasa maganar,Sir Jazz ya watsa da gudu jiki na rawa ya sauka downstairs,
  Ajiyar zuciya sgr ya sauke tare da juyawa ya koma ciki,

a ƙopar shiga bedroom ɗin ya tsaya,yana kallon sehrish dake ƙoƙarin gyara mashi gadonshi,har ta ajiye mashi kayan breakfast dinsa,yadda ta rankwafa shape ɗin hips ɗinta ya fito sosai,ba ƙaramin kyau tayi masa ba,sai yanzu ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login