Showing 42001 words to 45000 words out of 307403 words

Chapter 15 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

alama dae wannan ba ƙaramin masifaffe bane,
"Wuce ki shiga,"ya faɗi hakan tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,shi kuma ya fuce daga ɗakin,
jikinta sai kerma yakeyi saboda tsoran mutumin da tayi arba dashi,hakanan taji tsanarshi aranta,kuma sam baiyi mata kama da mutanen kirki ba,
Lokacin da ta ƙarasa shiga ɗakin a kwance ta samu junaid,daga shi sai farar shirt da short fari a jikinshi,ya kwantar da kanshi asaman pillow,idanunshi na arufe,ajiye mashi tray ɗin tayi asaman front table ɗin gadon nasa,sannan ta samu wuri daga gefen gadon ta zauna tare da ambaton sunanshi"junaid,"
A hankali ya buɗe idanunshi tare da azasu akan fuskar jahad,yanayin shi ya nuna tamkar baijin daɗin jikinshi,idanunshi kansu sun marairaice,
Bai tanka mata ba sae da ya gama ƙare mata kallo sosai,saboda ya tantance wacece acikinsu,tashi yayi daga zaune sannan yace"Jahad ko"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan ta ƙara da cewa"duk yau ban ganka ba,shiyasa nace bari nazo na duba ka,hada abinci ma nazo maka dashi,duk da bansan ko kana jin yunwa ba,"
"Thanks for your caring,duk yau babu wanda ya damu dani,sai ke kawai,naji daɗi sosai,"yayi maganar tare da sauko da ƙafafunshi ƙasa,hannu yakai zai ɗauki jug,ta riga shi ɗaukar jug ɗin tare da cewa"bari na zuba maka,"dakatawa yayi ta tsiyaya mashi lemu mai sanyi acikin cup,sannan ta miƙa mashi,yasa hannu ya kar6a,tare da kai cup ɗin saitin bakinshi yana kur6a,
binshi tayi da kallo,yayi wani irin haske fari fat,kamar mara jini a jiki,hakanan ta dinga jin wani irin tausayinshi na shigarta,ga tsananin ƙaunarshi da takeyi kamar kamar me,
Har ya kammala shan lemun bata sani ba,juyawar da zaiyi suka haɗa ido dashi,kawar da idonta tayi gefe guda tare da yin saurin cewa"Kamar baka lafiya ko"?
"Me kika gani"?
"Kawai yanayinka na gani,kamar na wanda bashi da ƙoshin lafiya,"
"Lafiyata ƙalou,don inajin yunwa ne shiyasa kika ganni haka,amma da zarar naci na ƙoshi,zan dawo dai dai,"
"Kasan kana jin yunwa amma meyasa baka tashi ka nemi abinci ba"?tayi maganar a yayin da take janyo plate ta shiga zuba mashi fried rice aciki,
"Tun safe fa naketa yin bacci,ni kaina bansan ya akai nayi bacci mai tsayi ba,kuma dana tashi jikina duk ba ƙwari,shiyasa bansamu na sauko downstairs ba,saboda kasalar data baibaye ni,
"Kuma baka sha wani abu ba?kamar maganin bacci"?
Shiru junaid ya ɗanyi yana tunani kafin yace"a'a bansha komai ba,amma ya haroon ya kawo mun wani tea a cup wuraren ƙarfe takwas yace mun insha,kuma saida na tambayeshi maganin menene yace mun maganin ƙara kuzari ne,shine nasha,tun daga lokacin nidai ban ƙara sanin meke wakana ba,yanzu ma da kika ganni a kwance tashi na kenan,kuma shi ya tashe ni,yace mun in tashi inyi wanka in shirya,lokacin walima ya kusa,"
ɗagowa jahad tayi tare da kallon fuskarshi tace"Wannan mutumin daya fita yanzu shine Ya haroon"!?
ɗaga mata kai yayi alamar eh,
ta kuma cewa"Wanene shi?don ban ta6a ganinshi ba a gidan,"
Junaid yace"Shima yayan mu ne,bai cika zama gida bane shiyasa baki ta6a ganinshi ba,"
"Kada na cika ka da surutu,ka fara cin abincin,"
Maƙe hannayensa yayi tare da cewa"Hannu na ciwo yakeyi mun,"murmushi ta saki tare da kai hannu ta ɗauki cokali tana faɗin"bari na baka abaki to,"
ɗebowa ta dinga yi tana tura mashi abakinshi yana Ci suna fira,gwanin ban sha'awa,a haka harta samu yaci abincin sosai,sannan ya tashi ya shiga toilet wanka,zama tayi tana jiran fitowarshi saboda yace ta jira shi,su fita atare,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,a sannu a sannu dai junaid ya fara sakewa da ita,Allah sarki

*Boss Bature*

Bayan Sallar la'asar,kowa ya ɗauki wani sabon wankan,Amani da kanta tayi masu Jahad makeup ita da Hosana da Sehrish,gaba ɗayansu suka sanya Swiss lace ajikinsu,wanda aka ɗinka masu shi domin su sanya a aranar walimar,riga da skirt ne ba ƙaramin kyau kayan sukayi masu ba,sun wanku iya wankuwa,yadda kasan dollar wurin kyau haka suka koma,Suna acikin ɗakin nasu Su huɗu hada Amal,in aka haɗa da Amani sun zama su biyar kenan,zama tayi tana ƙarasa gyara masu ɗaurin ɗan kwalin da tayi masu,

A Can ciki kuwa Matasan gidan duk sun hallara,Azmee da Saude ne suke ta ɗawainiyar bin kowani table dake a wurin suna Jejjera abinci kala kala,daga bayane hayaam ta samu damar fitowa daƙyar,tun tana ƴan kame kame kamar mara gaskiya har dae ta fara sakewa,tashiga tayasu Azmee kai ma baƙi lemu,

A hankali Motarsu Aunty Babba,ta shararo izuwa cikin gidan,a dai dai parking space,hafsat ta tsayar da motar,tare da juyawa ta kalli fuskar Mommyn nata dake ta faman jan minshari,tunda suka taho ta kama bacci acikin motar,hannu hafsat tasa tare da bubbuga kafadarta,a firgice Aunty babba ta farka tana fadin"Har mun ƙaraso ne,"
  Hafsat tace"eh mana,gamu acikin gidan ma,kin barni da driving kina ta sharar bacci,'
Yamutsa fuska Aunty babba tayi tare da buɗe motar tana faɗin,wlh agajiye nake,ga baccin ma bai isheni ba,kuma yunwa ma nake ji,'
   Bayan motar ta tsaya tare da buɗe Boot ɗin motar,ta curo trolley ɗin kayansu,tare da saukko dashi ƙasa,
   Sai da hafsat ta sanya niqabin da ta siya a hanya sannan ta buɗe motar ta fito,hannunta ruƙe da ƴar purse ɗinta,ganinta da niqabi yasa Aunty babba jan guntun tsoki tare da fadin"Yau naga ikon Allah,kamar wata Munafuka,kin nace dae yau sai kin sanya wannan baƙin abun a fuskarki,kamar wata ƴar shi'a"
   "Mommy ba zaki gane bane,"
Tayi maganar tare da kama hanyar shiga cikin gidan,bin bayanta aunty baba tayi tana fadin"ba zaki zo ki kar6i trolley ɗin ba"
  "Haba Mommy,Duk aikin driving ɗin da nayi,kuma sai na wani ɗauki trolley,ae ke yakamata ki janyoshi,tun fa da muka kamo hanya kike ta bacci,kika barni da aiki,nima agajiye nake bazan iya ɗaukar shi ba,"
   "Kar Allah yasa ki ɗauka toh,"suna tafe suna magana har suka shiga cikin Main palour ɗin,Hayaam najin sallamar Aunty babba,ta wani saki ihu har saida hankalin kowa ya dawo kanta,da gudu taje ta rungumota tana faɗin"Wayyo Allah aunty laila,tun dazu nake ta baza ido inga zuwanku amma shiru,har na fara fidda rai da zuwanku ashe kuna hanya,"tayi maganar tare da raba jikinta daga na aunty babba,fuskar nan awashe Aunty babba tace"Mezai hana mu zuwa,naso na sanar maki wlh mantawa nayi,koda yake bacci fa nayi a mota,hada ƙarin haka yasa ban samu na kira ki awaya ba,'
  "Gaskiya nayi kewar ku sosai,"acewar hayaam tayi maganar a yayin da take mayar da idanunta akan Hafsat dake sanye da niqabi,a ruɗe tace"Kai!wai hafsat ce sanye da niqabi,"
  Hannu hafsat ta sanya tare da ɗan ɗage niqabin tace"Nice mana,gaba ɗaya hankalinki na akan mommy dayake kinfi damuwa da ita,"
  Washe baki hayaam ta kuma yi tare da rungumo hafsat ajikinta tana faɗin"Sorry bangane ki bane wlh,kema ce kin sanya niqabi kamar wata mara gaskiya,"
  Suna cikin magana muryar Azmee ta katse su da cewa"maraba da manyan baƙi,Yau su hajiya laila ne a gidan namu,wata sabon gani,yau za'ayi ruwa da ƙanƙara,"
  Dariya sukayi gaba ɗayansu,kafin daga bisani Aunty babba tace"Ae wannan zuwan na musamman ne,Har sai kun gaji damu Allah,"tana magana hafsat na zungurinta alamar ta daina faɗin zasu jima,amma zafin ɗumi yasa ko lura batayi ba balle ta ankare,
  "Ae tunda na ganku da trolley ɗin kayan nan nasan cewa zaku jima mana anan,wataƙil ma har sai an aurar da ƴa'ƴan namu tukunna,kunga sai ayi agabanku,'
  Gaban aunty babba ne ya faɗi rass,a razane tace"Auren wasu ƴa'ƴa kenan"?
  dariya azmee tayi tare da cewa"Ƴa'ƴanku mana na wurin Abusufyan,"
  ɗaure fuska Aunty babba tayi tana fadin"haba dae,wani aure kuma ana zaman lafiya,daga ganin yaran kuma sai ki fara yi masu fatan yin aure,duka nawa suke,bana ji ance ƴan shekara sha bane,'
  kafin azmee ta kuma cewa wani abu hafsat tace"Dan Allah mu shiga ciki mu zauna,wlh agajiye nake,gashi ko salla ma ba muyi ba,"
 Atare suka ƙarasa shiga ciki,bayan sun kammala gaisawa da mutanen dake zaune a babban falon,daga bisani hayaam takaisu bedroom ɗinta,suna shiga ciki hafsat ta cire niqabin data sanya,tai wurgi dashi saman gadon,tashige toilet don ta ɗauro alwala,a ƙagare take da tayi arba dasu jahad,duk da tsoran karsu canza mata,musamman in suka tuna abubuwan da sukayi masu a gidansu,tana cikin toilet tajiyo muryar hayaam tana fadin"Tun jiya fa na tura maki hotunan nasu,baki gani bane,kuma har hafsat saida na kira a waya na sanar da ita don ta tunasar dake,'
  Aunty babba tace"Gaskiya ni banga wani hoto ba da kika turamun a whatsapp ɗina,mu barma zancen tunda dae gani acikin gidan zan gansu da ido,batare da nasha wata wahala ba,'
  Hayaam tace"Ae yanzu haka suna can cikin ɗakinsu tare da Amani...'
  Cike da mamaki Aunty babba tace"Amani kuma?Ubanme ya haɗata dasu da har take shiga ɗakinsu?Oh ni yau naji ikon Allah,wannan shisshigi da kutsu irin na Amani,"
  "Nima azmee ce ke sanar dani cewa tana a ɗakinsu wai tanayi masu kwalliya,ni duk bama wannan bane damuwata ba,Akwai wata kyakkyawar yarinya fara da Amani tazo da ita,na rasa gane wacece yarinyar nan,kuma fuskar yarinyar sak irinta amanin ce,"
  Aunty babba tace"To fa,ko ina tasamu yarinya,zai iya yuwuwa fa daga gidan marayu Abbas ya ɗaukko masu ita don su raina,kinfa son cewa basu ta6a haihuwa ba,'
   "Bari naje ciki,kada azmee taji ni shiru,ina ɗan tayata aiki ne,'acewar hayaam
  Harara Aunty babba ta watsa mata tare da cewa"dama aiki na turoki kiyi acikin gidan?shiyasa naga duk kin zabge,nida zanzo inga ko'ina na jikinki ya cicciko,amma sai uban ƙasusuwan wuya,kamar wadda tayi jinya,'
  Tsuke fuska hayaam tayi tana faɗin"Bakisan halin dana shiga bane,shiyasa zaki ce haka,tunfa da Sgr ya kore ni daga gidan nan,ban ƙara samun kwanciyar hankali ba,kullum ina ƙumshe acikin ɗaki saboda tsoran kar muyi arba dashi,ga ciwon yunwa dake damuna,ba don azmee ba ae da tuni na jima da sheƙawa,itafa ce take kawomun abinci har ɗakina,wani lokacin in ta manta bata kawo mun ba,sae dai fa in dare yayi kowa yayi bacci in saci hanya inje kitchen in ɗebo abinci,gaskiya nasha wahala sosai,
  "Laifinki ne hayaam,kina zaman zaman lafiyarki acikin gidan nan,Amma kika toƙano masifa,kirasa wa zaki kaima hari sai Sgr,ae wlh ki godema Allah dabai kakkaryaki ba,nikaina nayi mamaki da kikace iya korarki yayi kawai,'
  Tur6une fuska hayaam tayi tare da juyawa tana fadin"Ni dae mu bar maganar ae yariga da ya wuce,kuma ma ae ya yafe mun,bakiga yanzu ina yawo na hankali kwance acikin gidan ba,"
  Aunty babba tace"Allah yasa dagaske ne cewar ya yafe maki ɗin,sai kiyi taka tsantsan kafin mu samu Allah ya cika mana burin mu,don wannan karon da shirina nazo,Bazan bar gidan nan ba,har sai naga an shafa fatihar aurenki,keda Sgr,"
Cike da farin ciki hayaam ta sanya tafin hannunta tare da rufe fuskarta tana sakin dariyar farin ciki,
   "Aunty laila kina ganin hakan zai yiwu kuwa?ga Yaran nan ƴa'ƴan abusufyan,wlh ba ƙananu bane balle ace basu isa aure ba,Sun kaifa sha Takwas inaji,kuma wlh bakiga surar jikinsu ba,matane sosai,ni tunda nagansu ma duk sai naji na tsani kaina,kuma kinga su ƴan gidane za'a iya tunanin haɗasu auren Zumunci...'
  Tunkan ta ƙarasa maganar aunty babba tace"Impossible!wlh bazai ta6a yiwuwa ba!Muddin ina numfashi ɗaya daga cikinsu bazata ta6a auren Sgr ba,kwara ma Omar abra saita haƙura amma Allah sgr ya Haramta agaresu na haramta masu shi,da bala'e sai ya aureki,ko anaso ko ba'aso,babu wani shege daya isa ya hana wlh,babu shi,"yadda Aunty babba ke cika baki tana magana ba ƙaramin dariya ya so yaba hafsat ba dake acikin toilet tana sauraronsu,ita batasan halin da suke ciki ba,sae faman kuri take tana cika baki,
   Ita kuwa hayaam sae faman washe baki takeyi,gaba daya ta miƙa yardar ta ga Aunty babba,ae gani takeyi zata iya aikata komai don ta mallaka mata Sgr,
     Bayan fitar hayaam daga ɗakin Hafsat ta fito daga cikin toilet din,idonta na akan Aunty babba data ɗan kishingiɗa asaman gadon,
  "Mommy yakamata kije kiyi sallah,kinsan fa yanzu za'a hallara gaba ɗaya wurin waleemar yakamata ki hanzarta yin sallar,"
   yatsina fuska tayi tare da cewa"Anya zan iya yin sallar nan kuwa,nagaji sosai,zuwa anjima dai nayi sai in haɗa da magriba duka inyi,"
  girgiza kai kawai hafsat tayi batare da ta ƙara cewa komai ba,don ba yau ta saba yin haka ba,ita kanta hafsat ɗin zamanta dasu jahad ne ta fara yin sallah cikin lokacinta,
 
Zaune yake agefen gadonshi ya zabga uban tagumi,tun bayan da suka dawo daga sallar la'asar,yadawo ɗakinshi atakure,turo kopar ɗakin nashi Abba yayi tare da shigowa ciki,ba ƙaramin tausayi abusufyan ya bashi ba,wuri ya samu tare da zama daga gefenshi sannan yace"Bana faɗa maka cewa ka kwantar da hankalinka ba?jibi yadda duk kabi ka tukura kanka,"
  ɗagowa yayi tare da kai idanunshi kan abba,muryarshi asanyaye yace"bansan ya zanyi bane,hankalina yaƙi kwanciya wlh,bansan wane hukunci Ammi zata yanke mun ba,ni tsorona kada tace bata yarda cewar da aure na samu su jahad ba,kasan halinta yaya hossein,tana da wuyar sha'ani,"
Abba yace"hakane,amma insha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na fahimtar da ita,kaima kasan cewa bazan ta6a bari yaran nan su tozarta ba akan idon kowa,Ammi tana buƙatar hujjoji masu ƙarfi kafin ta gasgata abu,zamuyi kokari wurin ganin cewa munyi amfani da hujjojin da muke dasu a hannu wurin fahimtar da ita,abunda nakeso dakai yanzu ka saki jikinka,nasan cewa da anjima kaɗan idan ta farka daga bacci zata fito nan babban falon,so nake kazo da ƙwarin guiwarka ka gaishe da ita,kasan kun jima baku haɗu ba,kuma dama can kai mai laifi ne a wurinta,'
  fuskar Abusufyan cike da damuwa yace"Hada ƙarin hakan yasa nake fargabar haɗuwa da ita,Ni kullum mai laifi ne a wurinta,ko kirana ma bata ɗagawa,tunda nabar nigeria shekara goma sha,amma mommy bata ta6a ɗaukar waya da sunan zata kira ni ba,kuma ko na kirata bata ɗagawa,ni ina ganin kamar bata so na ne,shiyasa takeyi mun haka,'
   ruƙe hannunshi abba yayi acikin nashi"abunda kake tunani ba haka bane,zanma iya cewa tafi sonka fiye da kowa,kuma ta damu da kai sosai,babban laifin da kayi mata shine naƙin sanar da ita dalilin da yasa kabar Nigeria,ammi batasan komai game da tafiyarka ba,tayi kewarka sosai,don akwai lokacin da ta kirani a waya,kuka ne kawai batayi ba a lokacin,saboda ka tafi batare da saninta ba,wannan dalilin ne yasa take fushi dakai,amma yanzu ina da tabbacin cewar in har muka sanar da ita dalilin tafiyarka,zata fahimce mu,kuma zata kar6i yaran nan hannu bibbiyu,kuma zata yafe maka"
  Jiki asanyaye abusufyan yace"Allah yasa,dana fi kowa farin ciki,"
  Murmushi abba yayi tare da miƙewa tsaye ruke da hannun abusufyan yana cewa"Tashi muje ciki,nasan yanzu haka triplet ɗinka suna nan,sun ɗau wanka suna jiran daddynsu don suyi hoto tare dashi,"
  Jin haka yasa Abusufyan sakin fara'a a fuskarshi nan take yaji damuwarshi ta ragu saboda an ambaci ƴan ukunshi,
   atare da abba suka fito daga cikin ɗakin,adai dai lokacin Hajiya Azeema da gwaggon katsina da saude suma duk sun fito,kowa yasha kwalliya a fuskarshi,ga harris shima tare da Marshal Omar duk sun hallara anan falon,A jere su Sehrish suka fito su uku Ita dasu jahad hosana,sae Amal dake abayansu tare da Amani,
  Ae tunda suka shigo cikin falon hankalin kowa ya dawo kansu,yadda kasan wasu taurari haka suka bayyana,kai tsaye wurin abusufyan suka nufa,haɗasu yayi su duka ya rungumesu sosai,bayan ya sakesu,suka gaishe da Abba tare dasu Marshal Omar dake tsaitsaye a wurin,Hannu abba yasa tare da jan kumatun hosana yace"Amaryar Omar,irin wannan kyau haka,"da sauri tasa hannu tare da rufe fuskarta,tana dariya,kawar da kai gefe Omar yayi yana ɗan sakin Murmushi,da zasu bashi dama da ba abunda zai hana ya rungumota don ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,matsowa kanal yousouf yayi kusa dasu yana fadin"Uncle ni wacce za'a bani acikinsu tunda ya Omar yayi kamun tashi,kada su ƙare ni in rasa,"dariya sukayi gaba dayan su,Uncle abusufyan yace"Layi zaka bi,don mutun ko da kuɗinshi saida rabonshi," Abba ya kar6e da cewa"kwarai kuwa,sae wanda ya dage da sallar dare zamu bamawa,"
daga bayansu suka jiyo muryar junaid yana cewa"Kamar ni kenan,duk gidan nan babu wanda yakai ni tashi yin sallar dare,"ya ƙarasa maganar tare da ruƙe qugunshi,fuskar nan ɗauke da wannan kyakkyawan murmushin nashi,yayin da idanunshi ke akan jahad,
fashewa suka kumayi da dariya,kanal yousouf yace"haba junaid,cewa zakayi duk gidan nan babu wanda yakai ka,sharar bacci idan dare yayi,mutumin da daƙyar ake tashin shi sallar asuba shine yake cika baki yana faɗin yafi kowa sallar dare,"
bubbuga ƙafa junaid yayi cike da shagwa6a yace"Kai yaya yousouf dan Allah ka daina faɗin haka,kada kasa araina ni,"
"Raini kuma na yaushe junaid!agabansu fa kake bubbuga ƙafa kamar ƙaramin yaro kana shagwa6a,a haka kake cewa kar araina ka,wace mace ce zata so ta auri shagwa6a66an namiji irinka?acewar kanal yousouf,
Tur6une fuska junaid yayi yana faman zumbura baki,juyawa yayi tare da kai idanunshi kan abusufyan yace"Uncle,ae dai zaka bani kyautar ɗaya ko"?
Abusufyan yace"mezai hana junaid?ko sisi bana buƙata,duk wacce kakeso acikinsu,zan baka ita kyauta,basai ka biya sadaki ba," gwalo yayi ma kanal yousouf yana fadin"ae dae Uncle yace zai bani,kuma a kyauta ma,"
Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba,duk wannan rashin wayon da Junaid ke yi akan idon jahad,zubama sarautar Allah ido tayi,aranta tace wai dama haka yake?saboda ita bata ta6a ganin junaid na shagwa6a agabanta ba,hada su gwalo ɗabi'unsa kamar na yaron goye,kaɗan kika gani

Cike da nishaɗi sukeyin firar tasu,adai dai lokacin General ishaq da Abbas suka shigo cikin main palour ɗin,sae faman sakin fara'a suke yi,ƙarasa shigowa sukayi kai tsaye suka nufi inda su Abba ke tsaye,gaishe da abba sukayi,kafin su jahad suka haɗa baki wurin gaisar dasu,

Fuskar ishaq ɗauke da murmushi yace"Masha Allah,nama rasa abunda zance,yanzu wannan duk namu ne"?yayi maganar yana nuna su hosana,Abba ne ya bashi amsar cewa"Naku ne ishaq,halak malak Allah ya mallaka maku,gasu nan harsu uku,"
Abbas yace"kamar yadda Allah ya nuna mana wannan ranar da ranmu kuma da lafiyarmu,ina fata Allah ya ƙara haɗamu a ranar auransu kamar haka dae........' haɗa baki su Abba suka yi wurin cewa"Ameen,"banda abusufyan wanda ya sunnar da kanshi ƙasa yana murmushi,Sehrish da jahad kuwa duk kunya ta gama rufesu,
Abba yace"ko baku son auren ne"? Shiru su kayi suna faman ƙumshe dariya,

"Sun ma isa suce basa so?ga yayyansu nan duk tazurai,ae dole su bada hadin Kai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login