Showing 93001 words to 96000 words out of 307403 words
Chapter 32 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
ba,gaban dressing mirror taje wurin da ta ajiye ribbom ɗinta before ta shiga wanka ɗaukarsa tayi tare da zura shi acikin hannunta,sai da tafara tattara gashin kafin ta sanya ribbom ɗin ta ɗaure shi tamau,
"Ko dai in tashi hosana,tayi wanka itama?kin ga ko sallah batayi ba,"acewar jahad,
Sehrish tace"ko baki tasheta ba,Yunwa zata tayar da ita,kibarta kawai,kada ki tado mana jangwamgwam,"
"Baiwar Allah ni tausayi take bani,duk in na tuna yadda ta samu ciwon haukanta,sai inji idanuna sun cika tab da kwalla,"acewar jahad,
Sehrish tace"Ni kaina ina tausaya mata sosai,Amma inaji araina cewa,Wata rana hosana zata dawo cikin hankalinta ne,sannu a hankali,Haka muke fata in sha Allah,
Suna cikin magana,Jiniyar motocin dake shigowa cikin gidan ta karaɗe kunnuwansu,da ƙarar gaske har cikin dodon kunnuwansu,
"Su babban yaya ne suka dawo daga sallar juma'a,bari in leƙa inga wankan daya ɗauka yau,!"
Cike da farin ciki sehrish tayi maganar tare da juyawa ta nufi window,jahad ma tabi bayanta,janye labulan sukayi sannan ta zuge masu glass ɗin,Baza idanunsu sukayi suna kallon abunda ke wakana a farfajiyar gidan,
Da gudun gaske motocinsu ke shararowa saman titin da zai kawo ka har wurin parking space na gidan,tun daga bakin gate titin ya fara,
"Wlh abun kamar a shirin film" jahad ce tayi maganar,abun ba ƙaramin burgesu yayi ba,
Lokacin da motocin suka ƙaraso ciki,a wani slow suka tsaya a jere,
"Ko wanene zai fara fitowa,bari mu zuba ido muga wankan su babban yaya,"acewar sehrish,
Jahad tace"Ni har na ƙosa,in ga wankan da daddynmu ya dauka yau da kuma wankan Baby junaid,"
Suna cikin magana,wani gabjejen soja mai ƙirar samudawa,ya buɗe motar farko,Abbansu junaid ne ya fito,other side ɗin kuma Uncle Abusufyan ne,fuskokinsu ɗauke da murmushi,yadda kasan Gonar auduga,
Bayansu kuma sae motar da ke bin bayan tasu,Abokin Abbansu ne Tafeeda tare da abokin Omar,Adams da kuma shattima,daga motarsu sae motar Marshal Omar,zuba ido su Sehrish su kayi suna kallon Ya Omar dinsu,ganin ya fito daga cikin motar ya kuma zura hannayenshi acikin motar,jimm kaɗan sae gashi ya kinkimo junaid tare da aza shi asaman kafaɗarshi,
Waro ido waje su sehrish sukayi Jahad tace"Mun shiga uku!meya faru da baby junaid ɗinmu?kodai bashi da lafiya ne?kalli fa yadda ya Omar ya ɗaukoshi asaman kafaɗarshi,"
"Yanzu haka rigimarshi ce,nasan junaid sarai,har goyashi zai iya cewa ayi,yadda yake jin kanshi kamar jinjiri,"Sehrish ce tayi maganar fuskarta ɗauke da dariya,
Jahad tace"wannan fa ba abun dariya bane,tunda kika ga an ɗaukoshi asaman kafaɗa to tabbas akwai abunda ya faru dashi,nidai Allah yasa kafiyarshi ƙalau,
Sehrish na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,ta hango Amstrong ya fito daga cikin motar Sgr,da sauri ya zagaya tare da buɗe mashi motar,zuba ido tayi tana jiran fitowarshi,
A hankali ya zuro ƙafarsa ɗaya waje,almost 5 mins,tukunna ya ƙarasa fitowa daga cikin motar gaba ɗaya,
Gabanta ne taji ya faɗi rass!ba ita kaɗae ba hatta jahad ya tafi da imaninta,a rude sehrish ta shiga yarfa hannu tama rasa abunda zata ce,just speechless,
Jahad ce tayi ƙoƙarin cewa"Tabarakallahu Ahsanul khaliqin!gaskiya babban yayanmu duniya ne!Irin wannan ɗaukar wanka haka!Ni tunda nake a rayuwata ban ta6a ganin mutumin da shadda tayima kyau sosai irin Babban yayanmu sae kuma Ya Omar,Wankan shadda ba ƙaramin kyau yake yi masu ba,ko don suna da ƙirar jiki mai kyau ne,!koda yake shima fa Ya yusouf ba ƙaramin kyau shadda takeyi mashi ba,kinsan shi wani irin sanyin kyau ne dashi na miskilai,hatta su twins da fawan kowa ma yana yin kyau idan suka sanya shadda amma ba kamar yaya Rafayet ba,da ya Omar,junaid kuwa na dabanne shi,"
Jahad sae faman zuzuta su takeyi,duk a tunaninta Sehrish na sauraronta,batasan cewa sehrish ta lula wata duniyar ba,gaba ɗaya Sgr ya tafi da Imaninta,ya janye hankalinta,babban farin cikinta shaddar daya sanya ajikinsa,saboda tana kwaɗayin son tagan shi sanye cikin kayan hausawa,kuma ta gane cewa shaddar nan ce wadda ta ta6a dauko mashi a kwanakin baya,Ya ƙi sanyawa saboda baya sanya kayan hausawa sai nasu na turawa,
Yadda kasan tauraro acikin taurari haka ya bayyana,fuskar nan babu annuri,ya tamketa tamau,kamar wanda aka ɗaura ma aure da Mutuwa,hannunshi na ruƙe da hular da abbansu ya sanya mashi kafin su shiga masallaci,don a ganshi da mutunci,amma ɗan tahalikin nan kamar jira yakeyi a kammala sallar,suna fitowa daga masallacin bayan ɗaurin auren ya tumbuƙe hular,don shi arayuwarshi ya tsani duk wani abu da zai rufe mashi sumar kanshi,ba ƙaramin ji yake da ita ba,zaiyi wuya kaga Sgr da hula akanshi,sai dai Facing cap ko kuma in ya sanya jacket mai hula ajikinta shine zakaga ya sanya hula,hatta shaddar dake ajikinshi atakure yake da ita duk da shi kanshi ya shaida irin kyan da yayi acikinta,ya saba da kayansu marasa nauyi shiyasa yake jinshi duk atakure,Ƴan uwanshi kowa farin ciki yake yi gashi ya hana kowa ya furta kalmar nan Wato ango kasha kamshi,ya tsani yaji an ambaci hakan,ko kuma a kirashi da sunan Ango,kowa so yake ya ɗanyi mashi wasa da dariyar nan da ƴar zolayar nan da akeyi ma angwaye amma rafayet ya hana hakan!yaƙi jinin akirashi da sunan ango,
Gaba ɗaya suka tunkari ƙopar da zata sadaka da babban palourn gidan,"
Jiki asanyaye sehrish ta zuge glass ɗin windown,ta gyara labulen,
Zuba mata ido jahad tayi tana kallonta,ganin yadda ta sauya lokaci guda kamar wadda aka zarewa lakar jikinta,
Gefen gadon ta koma ta zauna,sam tagaza samun natsuwa acikin zuciyarta,ganin rafayet da tayi ya fama mata ciwon dake acikin zuciyarta,
"Sehrish wai meya faru ne?Yanzun nan fa muke raha dake,amma lokaci guda kin canza,ko baki lafiya ne"? Ta ƙarasa maganar,tare da samun wuri gefen sehrish ɗin ta zauna,
Muryarta tamkar zata yi kuka tace"bakomai,kawai zuciyata ce har yanzu bana jin daɗinta,"
"Dan Allah ki kwantar da hankalinki rishi,Ki saki jikinki,ko zaki kwanta ne?ki ɗan samu bacci may be Ki samu natsuwa acikin zuciyarki,"cike da kulawa jahad keyi mata maganar,
..Sehrish na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,suka ji an kwankwaso ƙopar ɗakin nasu,
Da sauri Jahad ta miƙe tare da tunkarar ƙopar tana tambayar wanene,
Daga waje taji ance"Daddynku ne"
Jin haka yasa jahad yin saurin buɗe mashi ƙopar,
Shigowa ciki Abusufyan yayi fuskarshi ɗauke da ƙayataccen murmushi,zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi baki asake,from head to toe,irin kallon ƙurullar nan,
A ruɗe tace"daddy!kaine!"
Dariya ya ɗan saki tare da cewa"Ni ne mana,me kika gani"
A susuce tace"Wow daddy kayi kyau Over,kamar matashin saurayi ɗan shekara ashirin da biyar,"
Wannan maganar ta jahad,ba ƙaramin dariya ta bashi ba,ta wani 6angaren yaji daɗin yabon da tayi mashi,
Miƙewa Sehrish tayi jin maganar daddynsu nufo wurinsu tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Masha Allah,daddy kayi kyau sosai Allah,kamar irin sabbin ƴan dubu dubu ɗin nan,kasan yadda suke da ɗaukar ido,ga kyau,gasu da burgewa,"
Fashewa da dariya Abusufyan ya kuma yi bakin shi yaƙi rufuwa sai faman hura mashi kai sukeyi,
daƙyar ya samu ya tsagaita da dariyar yace"har kun tuna mun da mommyn ku,duk in naje ɗaukarta daga islamiyya in aka tashe su,Ƙawayenta suyi ta santin wankan da na ɗauka,Har leƙena akeyi ta cikin mota ana nuna ni ga mijin abu nan yazo,Ya iya ɗaukar wanka,ya haɗu sosai,Mommynku ta tsani taji suna yabona,abun haushi yake bata,idan na kuskura na fito daga mota ina jiranta,haka zasu zagaye ni suna kallona,harma suyi mun magana mu gaisa,da zarar abu tazo fuskarta a ɗaure,a fusace take ruƙo hannuna ta tura ni cikin mota,mu tafi,hakan ba ƙaramin dariya yake bani ba Inajin daɗin kishina da takeyi sosai,amma kishin da takeyi mun yajawo rabuwarmu da ita ba don naso ba......"kasa ƙarasa maganar yayi,saboda wani abu da yaji ya taso mashi mara daɗin ji acikin zuciyarshi,tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,
tsananin tausayin Abbansu ne ya kamasu duk jikinsu yayi sanyi,daƙyar jahad ta iya buɗe baki tace"daddy,dan Allah kayi haƙuri da duk abunda ya faru tsakaninka da Oumman mu,nasan cewa abun yana yi maka ciwo acikin zuciyarka,Oumman mu bata kyauta maka ba,gashi sanadin hakan ta jefa rayuwarta cikin haɗari da kuma rayuwarmu,sau dayawa takan zauna tayi ta kuka,musamman da daddare ko runtsawa bata iya yi,kullum cikin ambaton sunanka takeyi tana cewa haƙƙin Abusufyan ne yake bibiyar rayuwarta,na cutar dashi sosai,Mijina yana so na amma na butulce mashi,saboda baƙin kishi na,nayi danasanin rabuwa dashi sosai,Ya Allah ka yafemun,mu lokacin duk bamu san abunda take nufi ba...."tuni hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,itama sehrish hawayen ne suka soma shararowa daga cikin idanunta,Hannu Abusufyan ya sanya tare da janyo su ya rungumesu sosai ajikinshi,sae lokacin ƙwallar dake cike taf cikin idanunshi ta shiga wanke mashi fuskarshi,muryarshi a kasalance ya soma magana"Oummanku yarinya ce sosai,Ko a lokacin ban ruƙe ta a raina ba,saboda akwai ƙuruciya sosai atattare da ita,Nasha wahala sosai akanta,saboda Allah ya jarabce ni da tsananin sonta,ina sonta sosai,har yanzu soyayyar da nake yi mata na nan yadda take,babu abunda ya canza,Nayi kukan zuciya a lokacin dana rasa ta,kamar in zauce,lokacin dana ji zancen aurenta da sayyadi,Allah kaɗae yasan ƙuncin dana ji acikin zuciyata,bakomai nake tunawa ba,fa ce Amanarta da mahaifinta ya damƙa mun,ya yarda dani sosai baba buzu,yasan cewa banajin magana,ga ƙuruciya dake ɗibana amma a haka ya toshe kunnuwansa Ya aura mun ƴarsa,Naji daɗi sosai,A lokacin kamar kamar me,Allah ya jiƙanshi,
Atare suka amsa mashi da Ameen,ɗagowa dasu yayi daga jikinshi yana ƙoƙarin kai hannu ya share hawayen dake zuba akan fuskarshi,da sauri suka riga shi sanya tafukan hannyensu suna goge mashi hawayenshi,
Murmushi ya saki,don ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba,
"Dama nasani wata rana zaku share mun hawaye na,gashi Allah ya nuna mun ranar da raina kuma da lafiyata,"
Yayi maganar tare da sanya hannayenshi duka biyu,asaman fuskokinsu yana share masu hawayensu,bayan ya kammala goge masu hawayen,yace"oh namanta,ban baku tsarabar masallaci ba,"da sauri ya zura hannunshi cikin aljihun wandon jikinshi,
Farar leda ce ya curo mai ɗauke da dabino da goro,
Miƙa masu yayi tare da cewa"hada aya da kwakwa nasiyo maku amma ta hosana ce ita kaɗae zan bamawa,wannan dai gashi ku raba a tsakaninku,"
Kar6ar ladar jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi,sehrish tace"dama na lura kafi ji da hosana,"
Abusufyan yace"eh mana,saboda itace autarku a yanzu,nafi sonta,kuma nafi ji da ita,"
Zumbura baki sehrish tayi tare da cewa"yanzu duk irin cizon da tayi mana a jikinmu baka gani ba?
"Nagani mana,ae gwaggo ta tabbatar mun da cewar ba yin kanta bane,Ya sayyadi ne yazo da suffar kura yayi maku wannan aika aikar....."karasa maganar yayi tare da fashewa da dariya,suma dariyarce ta kufce masu,
Wucewa cikin ɗakin nasu,yayi tare da zama daga gefen gadon yana kallon hosana dake kwance tana bacci,baki a buɗe,
Da sauri ya sanya hannunshi,a cikin aljihun ya curo ledar dake ɗauke da yankakkar kwakwa da ƙullin aya acikinta,
Kwakwar ya ciro,cike da tsokana ya zurata cikin bakin hosana,cikin bacci hosana ta kama kwakwar ta shiga taunarta abakinta,
Dariya sosai sukayi abun ba ƙaramin nishaɗi ya basu ba,
Wuri suka samu suka zauna,suna kallon tsokanar da Daddynsu ke yi ma Hosana,
gaba ɗaya ta cinye kwakwar daya sanya mata abakinta,wata kwakwar ya kuma curowa,tare da zura mata abakinta,kamar wata kura haka ta kama kwakwar tana gartsa,tana taunewa acikin bakinta,
"Daddy,ɗan janye kwakwar mu gani ya zatayi,"acewar jahad,
A hankali ya shiga ƙoƙarin janye kwakwar daga cikin bakinta,ta cije ta da haƙoranta,yana ja tana rurruƙeta,dariya sosai Abusufyan yake yi abun ba ƙaramin nishaɗi yake sanyashi ba,
Da ƙarfi ya janye kwakwar aikuwa a firgice hosana ta farka,fuskarta a yamutse,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,muryarta a kasalance ta ambaci sunanshi"daddy!"
"Na'am,hosana,"ya amsa mata,yunƙurawa tayi dakyar ta miƙe daga zaune tana ƙare mashi kallo kafin ta kwantar da kanta asaman kafaɗarshi,tana faman lumshe ido saboda baccin da tasha,
"Kin tashi lafiya?ko baccin bai isheki bane?
A shagwa6e tace"Ya isheni,yunwa ma nake ji,Cikina babu komai,gashi ko wanka banyi ba,Su jahad duk sunyi wanka basu tashe ni ba,balle inyi nima,"ta ƙarasa maganar tana kallonsu sehrish dake a bakin gadon,murguɗa masu baki tayi tare da harararsu,
"Shikenan,bari in na fita yanzu zanyi ma azmee magana,sae ta shirya maki lunch ko"?
..ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Miƙa mata ledar kwakwar yayi"kar6i nan,tsarabarki ce,ta masallaci kada ki ɗanma kowa kinji ko"?
Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i ledar daga hannunshi
"Nagode sosai daddyna,kuma bazan ɗan masu ba,"
Wurga mata harara jahad tayi tare da cewa"Sannu ko?daddynmu zakice ba daddyna ba,ae bake kaɗae bace a wurinshi ba,"
Gatsina mata hanci hosana tayi tare da ƙara rungumo Abusufyan ajikinta don suji haushi,hakan ba ƙaramin dariya ya bashi ba,
"Daddy,ƙamshin turaren jikinka akwai daɗi sosai Allah,"tayi maganar tare da sanya hancinta ajikin rigar shaddar jikinshi tana shaƙar ƙamshin turaren kamar wata mayya,
"Idan kinaso ma,zan ɗauko maki kwalbar turaren gaba ɗaya,sae ki dinga shafawa kema hakan yayi maki"?
Girgiza kai tayi"a'a daddy,kabarshi kawai,Ya Omar ya hanani shafa turare,idan na shafa wannan turaren zaiyi ƙamshi sosai,kuma idan Yaji bazaiji daɗi ba,zaice hosana bakijin maganata ko?to daga yau babu ni babu ke,ni bazan zauna da mai kunnan 6era ba,'
Fashewa da dariya su jahad sukayi,tuni hosana ta ɗaure fuskarta tana harararsu,Abusufyan yace"yayi kyau babyn Omar,yana da kyau ki dinga jin maganarshi,kina yi mashi biyayya,kada ranshi ya 6aci,"
Cike da jin kunya hosana ta janye jikinta daga na Daddynsu,ta janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,
Wayar Abusufyan ce ta shiga yin ringing,har lokacin fuskarshi ɗauke da murmushi,yace"Bari na shiga ciki,zansa azmee ta shirya maku launch,"
"To daddy,"suka amsa mashi da sauri ya fuce,
*JUNAID ROMEO*
Tashin hankalin da ba'a sama shi date,Tun wurin ɗaurin aure da junaid yaji sanarwar ɗaurin auren Babban yayansu,tare da Rishi ɗinsa,acikin masallacin ya yanke jiki ya faɗi a sume,saboda baisan da zancen ɗaurin auren ba,kwatsam yaji ana sanarwar,
A bedroom ɗinsa Omar ya kwantar dashi,bayan sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,koda ya buɗe idanunshi yaga Abbansu ga kuma yayyansu Isha da Abbas,ga Marshal Omar da sauran matasan duk suna tsaye akanshi,Fashewa yayi da matsanancin kuka mai cin rai,Cikin shesshekar kuka yace"Wayyo Allah na!Wlh an cuce ni,Abba kana sane da cewar ni ke son sehrish amma ka aura ma babban yayan mu ita,wlh bazan yarda ba,Ae ni na fara sonta,don me za'a aura mashi ita!ashe baku sona,hakanan kuke nuna mun soyayya,Wlh nidai bazan yarda ba,abba ka cuce ni sau nawa ina faɗa maka cewar inasonta,Ita nake da burin in aura amma....." bai ƙarasa maganar ba,Omar ya daka mashi tsawa wadda ta gigitar dashi,
"Rufe ma mutane baki junaid!shashasha kawai!Abban ne kaka cewa ya cuce ka?kai ko kunyar yin zancen aure agaban mu baka ji?ubanwa zaiyi maka aure da ƙananun shekarunka?kai da ita waye zai raini wani in anyi maku auren"?
Tafin hannayensa ya sanya tare da rufe fuskarshi,yana cigaba da kukan kuma hakan baisa ya daina sambatun da yake yi ba,
"Ya omar ba zaka gane bane,Abun da ciwo,wlh ina sonta sosai,ina son rishi,kuma itama tana sona,wlh ba babban yayanmu take so ba,Ni take so,don me za'a aura mata shi..."
A zafafe Omar ya zabura zai kai mashi mari a kan fuskarshi,da sauri Abba ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Kuyi mashi uziri,wlh nasan yana sonta sosai,banta6a tunanin cewa junaid ya san so ba,ni duk a tunani na wasa yake yi mun,ashe dagaske yakeyi,dole yaji ciwo acikin zuciyarshi saboda ya saba da ita sosai," muryarshi a sanyaye yayi maganar,Abun ya ta6a mashi zuciyarshi,tsananin tausayin junaid ne ya kamashi,
Shi kanshi marshal Omar jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,kowa yasan da irin shakuwar dake atsakaninshi da sehrish amma ba suyi tsammanin cewar dagaske sonta yakeyi ba,
Hatta su ishaq dake tsaitsaiye cirko cirko agaban gadon nashi ba ƙaramin tausayi ya basu ba,duk yabi ya burkice,fuskar nan tayi jawur da ita,jijiyoyin jikinshi duk sun bayyana,
Adai dai lokacin da Abusufyan ya ƙaraso kopar ɗakin junaid ɗin,kasa shiga ciki yayi saboda jin maganganun da sukeyi aciki,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin cewar junaid sehrish yake so,kuma adalilinta ne ya suma a masallaci,
Duk yadda suka so su shawo kan junaid da lallashi don yayi shiru abun ya faskara,hancinsa har ya fara bleeding,hankalinsu yayi mugun tashi,
Matsawa sukayi kusa dashi suna lallashinsa,Ja da baya ya dinga yi asaman gadon har ya ƙure ma head board ɗin gadon,sautin muryarshi ashake saboda tsabar kukan daya sha,
"Ku rabu dani,bana son ganin kowa!ba kunfi so na mutu ba!to zan mutu ne yanzun nan sae hankalinku ya kwanta,"
Hawaye ne suka cicciko tab a idanuwan kowannansu,
"Junaid dan Allah kayi haƙuri,Allah ya riga daya ƙaddara faruwan hakan,dama can ita ba matarka bace," Acewar Abbas,
Girgiza kai ya shiga yi yana cewa"yaya abbas,bazaku gane bane,bakusan yadda nake ji acikin zuciyata bane,tafarfasa take yi mun,wlh bazan iya jurewa ba,inason rishi sosai,idan har kuna so kuga farin ciki na,to akwance ɗaurin aurenta da babban yayanmu a aura mun ita shine kawai,in ba haka ba mutuwa zanyi,Wayyo Allah rishi ɗina,"yana magana yana shessheƙar kuka,
Abbas yace"Calm down ur mind junaid,akwai mata da yawa agari suna yawo kyawawan gaske,ga ƙanwar matata nan Amal,baka ganta ba ƴar ƙarama dai dai kai,idan kayi hakuri zaka samu wadda tafi ta ma,"
Bubbuga kafafunshi yayi asaman gadon tare da cewa"Ya Abbas wlh banson kowace mace in ba ita ba,Sehrish itace juliet ɗina ita kawai nakeso,kodai aban rishi ko kuma in haɗiyi zuciya in mutu,"to fa,!junaid ya tashi hankalin kowa,yaƙi saurarar kowa,yau an ta6a romeo shugaban ƴan soyayya,
Cikin lallashi Abbansu ya ambaci sunanshi"Babyn Abbanshi,"
Wani irin kallo ya wurga ma abban nasu idanuwan nan sunyi luhu luhu saboda tsabar kukan daya sha,
"Ni ba babynka bane,Romeo ɗin mommynsa ne,saboda baka sona Abba,"ya karasa maganar yana faman matse kwallar dake sharara daga cikin idanuwanshi,
Shiru Abbansu yayi bai ƙarasa maganar tashi ba,junaid yafi jin haushinshi akan kowa,saboda yasan da cewar yana sonta amma ya ɗaura mata aure,duk da shi bai ɗauki maganar tashi serious ba,sae yau daya haukace masu,
Turo ƙopar Abusufyan yayi jikinshi duk ya mutu,tsabar tausayin junaid ne ya kamashi,
Juyowa suka yi suna kallonshi,matsa mashi hanya sukayi ya wuce,har izuwa gaban gadon junaid din,
Zuba mashi ido yayi yana kallonshi,duk ya fita cikin hayyacinshi ya zama abun ban tausayi,wannan ya tabbatar mashi da cewar ba ƙaramin son sehrish yake yi ba,
ɗagowa junaid yayi tare da kallon Uncle ɗin nasu,Cikin shessheƙar kuka yace"Un..cle!hada kai aka ɗaura ma rishi ɗina aure da babban yayan mu,bayan kunsan cewa ina sonta sosai,"
Hawa saman gadon abusufyan yayi tare da janyo junaid ya rungumoshi ajikinshi yana ɗan bubbuga bayanshi da hannunshi,cikin lallashi yace"Junaid,Ni bansan cewa kana sonta ba,da