Showing 264001 words to 267000 words out of 307403 words

Chapter 89 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

Mara tausayi mara Imani,sanna kuma ba sonta yake yi ba, Jikinta yake so,shiyasa yake yi mata komai da mugunta don yaga yaƙarar da ita,kafin Ya koma U.s,tunda yasan rabasu Za'ayi,

Yinin ranar tana kwance samn gadon,Anan Abba ya same ta,Yayi mata ya jiki,da kuma ban haƙurin abunda Sgr yayi mata,taji daɗin yadda Abba Ya nuna 6acin ranshi,kuma yace duk abunda takeso Yanzu shi za'ayi,bayan fitar Abba,Su jahad da Amrish suka dawo cikin ɗakin,Yanzu kowa Ya Zuba Ido Yana jira dawowar SGR,

Wuraren Ƙarfe shida na mare ce,Omar Ya fito daga cikin toilet,Jikin shi sanye da Jallabiya,Yana ƙoƙarin Zama gefen Gadon,Wayar shi dake ajiye gaban mirror ta soma ringing,miƙewa Yayi izuwa gaban madubin ya tsaya,Hannu yasa ya ɗauki wayar,Ya duba me kiran nash,A hankali Ya furta Sunanshi"Rafayet,"kafin ya ɗaga kiran tare da manna wayar a kunnashi,
Tunkafin yayi magana,Sgr ya ambaci sunanshi"Omar,"cikin sanyin murya,tamkar bata shi ba,
  Ajiyar zuciya Omar ya sauke"Rafayet,Meyasa ka tafi ka barni?Nasan ban kyauta maka ba,dana barka a wannan yanayin,Amma banji daɗin tafiyar da kayi ba,"
  "Bani da za6ine Omar,bansan ya zanyi ba,banyi tunanin zaka ɗaga kira na ba,Saboda kowa fushi yake yi dani,"
  "Dole suyi fushi dakai,abunda kayi sam bai dace ba rafayet,duk in na tuna cewa ɗan uwanane ya aikata hakan sai inji ɗaci araina,why Rafayet?
  "Omar,I ave regretted,i hate my self,ban kyautawa kowa ba,Zan ba kowa hakuri,In yi nesa da kowa,"
  Waɗannan kalaman na Sgr ba ƙaramin ta6a mashi zuciya su kayi ba,tuni Ya karaya,
  "Am Sorry Nayi maka laifi na ɗauko Sehrish batare da saninka ba,"
  "Don't worry about that,Nima nayi niyar na dawo da ita gida,just ina fargabar abunda zai biyo bayane,"
  "Rafayet,ka dawo gida kawai,Ka nemi afwar Abba da uncle,nasan zasu sauko ne,".  .
  "Its Okey,Zan dawo,amma sai zuwa sha biyu na dare".  .
  "Shikenan,i will be waiting for u,Ko bacci bazan bari ya ɗaukeni ba,har sai naga ɗan uwana,Nayi hugging ɗinsa ajikina,"
  Sun jima suna waya da juna,Kafin daga bisani su kayi sallama,yana ajiye wayar gaban mirror,Hosana ta bango ƙopar ɗakin nashi,cak ya tsaya yana kallonta ta cikin madubi,doguwar rigace ajikinta mai baza daga ƙasa,babu mayafi akanta,da alama gayu akayi mashi,ta sauko da Curly hair ɗinta,An shafa jan baki ja,

A tsiyace ta toge tare da ruƙe qugunta"Ya Omar,"
  A sukwane Ya juyo yana kallonta,from head to toe,Ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,cikin sanyin Murya ya ambaci sunanta"Hosana,"
  Murguɗa mashi baki tayi,Yace"To fa!Halan wani laifin nayi,"
  Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
  Ashagwa6e tace"Ya Omar wai dagaske idan aka ɗaura mana aure bada ni zaka tafi U.s ba,Wai a gida zaka barni,"?
  "Wurin wa kika ji hakan"?
Bubbuga ƙafarta tayi"Nidai ka amsa mun tambayata,"
Jinjina kanshi yayi tare dacewa"Eh,Anan zan barki,amma zan dinga zuwa duk ƙarshen.....  ..'
Bai ƙarasa maganar ba saboda wani kallo da yaga tana jifarshi dashi,kallon baka isa ba,
  "Ya omar ae wlh baka isa ba,Ko kana so ko ba kaso,Dole ne duk in da zaka tafi mu tafi tare,Ƙafata ƙafarka,Nida kai mutu karaba takalmin kaza,"ta ƙarasa maganar tana jefarshi da harara,
"Oh,a haka zan tafi dake can?Kina murguɗa mun baki,Sai kace wani tsaranki,Nifa in kika takuramin Allah,Zan fasa auren ne,"
Turo baki tayi"Yo he me?Ka fasa,Kai kasani wlh ya omar,Maza rubibina suke yi saboda kyau na,Don ma dai kawai ina sonka yasa nake kulaka,"
  Ƙumshe dariya yayi acikin bakinsa,don baisan tayi tunanin ko wasa yake yi mata,juya mata baya yayi batare daya ƙara tanka mata ba,

Yayi tunanin zata fita daga ɗakinne Amma sai yaga ta tattare bazar rigarta,ta haye saman gadonshi can tsakiyarshi ta baje tana kallon ceilling,
  Girgiza kai yayi"Oh ni Omar na ɗebo ruwan dafa kaina,"Yayi maganar acikin zuciyarshi,

"Ya Omar"ta ambaci sunanshi yayin da idanuwanta ke kallon ceilling kamar me nazarin wani abu,
  "Na'am,"ya amsa mata,

"Ya Omar,idan aka ɗaura auren kai kana America,Ni ina a nigeria,To wai taya za'ae in samu Ciki,"
  Rass Yaji gabanshi Ya faɗi,A firgice ya juyo yana kallonta,Hankalinta kwance tayi mashi tambayar,Abun ya ɗaure mashi kai,mamaki ne ya kamashi,
  "Ke!Waya faɗa maki cewa dole sai muna atare zaki samu ciki,"?
  "Yo oho,Nidai nasani ae,Ko kaza sai da zakara take samun cici,Kaga kenan,Nima sai kana tare dani zan....."bata ƙarasa maganar ba,da gudun gaske ta turo daga saman gadon ta nufi hanyar fita,A hanzarce ya damƙo hannunta,Ya juyo da ita,a jikin bangon yayi mata rumfa,sai faman zazzare mashi manyan idanuwanta takeyi,
  "Saboda rashin gaskiya,daga ganin na nufoki,kika watsa da gudu ko"?
   Runtse idanuwanta tayi"Ya omar,wai menene haka,kalli yadda ka takure,"
  "So nake ki faɗamun,Wayake koya maki waɗannan maganganun da kike gaya min,ko kunyata bakya ji"
Turo baki tayi"Babu kowa,"
  Sam bai yarda da ita ba,A matsayinta name ta6in hankali baya tunanin zata Iya sanin wannan,Sai dai ko gaya mata akeyi ko kuma tana kallon a wayarta,
  "Kiji tsoron Allah,ki faɗamun gaskiya,taya akai kikasan cewa dole sai muna atare da juna zaki samu ciki"
  A ƙule tace"Nifa babu kowa,"
Jinjina kanshi yayi"where's ur phone"?
  "Tana a ɗakinmu,"
"Ok,je ki ɗaukomin ita"

"Toh,"ta amsa mashi tare da juyawa da gudu taje ɗakinsu ta dauko wayar ta dawo bedroom ɗinshi Ta miƙa mashi"Gata,"
  "Cire pass word din"
Ashagwa6e tace"Sunanka ne,"
Ta6e baki ya ɗanyi,Acikin Zuciyarshi kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,
  Yana rubuta sunanshi Omar,Nan take pass word ɗin Ya cire,
   Bincike yashiga yi mata acikin wayar,Gallery ya fara shiga kaf ya duba videos ɗin dake a wurin,baiga abunda yake zargi ba,ita kuwa sai faman sakin murmushi takeyi,
  ɗagowa yayi suka haɗa ido da ita"Kin gogesu ko"?
 "`Wai me kake magana akai Ya omar,"
Moving yayi kusa da ita,lalla6ata ya shiga yi"Pls My hosana,Ki fadamun gaskiya,Bazan maki komai ba,A ina kike sanin abubuwan da kike faɗamun,"?
    Kafin ta bashi amsa,aka kwankwaso ƙopar ɗakin,
  "Omar,zoka buɗe mun ƙopa,"muryar abbansu ce,da sauri ya saki hosana,ya ƙarasa bakin ƙopar ya bude mashi,
  "Abba,"omar ya kira sunanshi,
"Kunyi waya da rafayet"?fuskarshi da alamun damuwa yayi maganar,
Omar yace"eh,munyi magana dashi,"
  "Dan Allah omar,kasan yadda za'ae ya dawo gida,"
  Murmushi Omar ya ɗan saki kafin yace"Abba,kana missing dinshi ne ko,"
"Omar bazaka gane ba,inaso ya dawo ne,"tun da ya shigo bai lura da hosana ba,don tuni ta la6e bayan labule,kamar wata mara gaskiya,
  "In sha Allah zai dawo abba,Yace mun around 12 na dare zai shigo gidan,"
Ajiyar zuciya abba ya sauke tare da cewa"Allah ya kawoshi lafiya,Naga an fara kiran Magrib,Ka hanzarta shiryawa mu tafi masallaci,"
  Amsa mashi yayi da toh,Bayan fitar abba,Shaf shaf Ya shiga toilet Ya ɗauro alwala,Kafin Ya fito tuni hosana ta bar ɗakin,Dama haushinshi take ji ya tsareta da tambayoyi kamar wata ƙaramar yarinya,acewarta

Wuraren ƙarfe 10 na dare,Wayar jahad ta soma ringing,a lokacin har Bacci Ya fara ɗaukarta,Tana kwance gefen Sehrish,Hosana dake bayanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,Oummansu kuwa na zaune saman darduma tana karatun qur'ani,

A saman mattress ɗin ta ajiye wayar,Bayan ta ɗauketa ta duba mai kiranta Sunan Fawan ne ya bayyana akan screen ɗin wayar tayi matuƙar yin mamakin ganin kiranshi,

Picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta,
  "Assalamu Alaikum"
On the other hand,Fawan ya amsa mata"Wa'alaikum Salam,Ya kike"?
  "Lafiyalou,"
"Sorry fa,bansani ba ko na tashe ki daga bacci,naji muryarki kamar kin fara ko"?
Murmushi ta ɗanyi kamar tana agabanshi"Hakane na fara amma banyi nisa ba,"
  "Dama junaid ne,ke son magana dake,ya bi ya ishe ni ya hanani sakat,Kinsan yanzu babu waya a hannunshi,Ina fa bacci sai gashi har bedroom ɗina,wai in kira mashi juliet dinshi,Sai kace baisan hanyar zuciya ɗakinku ba"
Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Jahad,a hanzarce ta miƙe daga zaune,
   "Gashi ku gaisa"jim kaɗan taji muryar junaid,
  "My juliet,"batasan lokacin da ta saki murmushi ba,
  "Na'am My romeo,Dama kana tunawa dani,"?
   "Yeah,ae bakison zuwa duba jikina,shiyasa nake fushi dake,"
  "Kaine ka juyamun baya,tun rana ta farko da nazo wurinka,Ka nuna tamkar baka sanni ba,abun ya tsayamun araina,rana ta biyu dana zo,kaƙi kallona,rana ta uku dana zo,Kana yin tozali ka rufe idanuwanka,kamar kaga wani mugun abu,"
   Sai da takai ƙarshen maganarta,Sannan yace"Am sorry,just forget about it,I really missed u,In ba damuwa inason ganinki yanzu,"
  Da sauri ta kalli agogon bangon dakin
  "Ƙarfe goma fa?Kuma oumma na kallona bansan ko zata barni in fito ba,"
  "Idan ta tambayeki,Ki sanar da ita cewa,Mijinki ne ke kira,Ae an biya sadaki,"
Jin wannan maganar yasa jahad ta fashe da dariya,Har oummansu dake karatun qur'ani saman darduma sai da ta ɗago ta kalleta,
  "still baka canza ba,kana nan a romeo ɗin dana sanka,"
  "Of course,I will be waiting for u pls,"yana kai ƙarshen maganarshi yayi rejecting ɗin kiran,
  Ajiye wayar tayi,A hankali ta sauko da ƙafafunta ƙasa,Jikinta na sanye cikin night gown pink colour,ta ɗaure gashin kanta da ribbom,
  Sai da ta miƙe tsaye sannan ta soma tunanin abunda zata ce ma Oumma,
  Gaban wadrobe taje ta bude ta lalubo hijab Ash colour ta zura ajikinta,saɗaf saɗaf Ta nufi hanyar fita,jin Oummansu Ta janyo doguwar aya,tasan bazata katse taba,balle tayi mata magana,da sauri ta buɗe ƙopar ɗakin ta fuce, babban falon ta nufa tana ta ƴan waige waige,duk ta ƙosa tayi tozali dashi,

A hankali Yake saukowa downstairs,Jikinshi na sanye cikin sleeping dress dinshi,riga da wando,Yayi haske sosai,Ga wani irin kyau daya ƙara,kwantacciyar sumar kanshi tayi tsayi sosai,Saboda bata samu aski ba,Gashin ya fara taruwa,

Hannayenshi duka biyun na acikin trouser pocket dinsa,A hankali ya ƙarasa saukowa cikin palourn,Kaitsaye ya nufe ba,kasa janye idanuwanta tayi daga kallonshi,Sai da ya ƙaraso kusa da ita,Suna fuskantar Juna,tun daga ƙasa har sama yake kallonta,lokaci guda suka sakarwa juna ƙayataccen murmushi,dimples din kowannansu Ya lotsa,zunzurutun kyau abun ba'a magana,
  Miƙa mata hannunshi yayi,ta zura nata asaman nashi,Ya ruƙe hannun sosai acikin nashi,wani irin daddaɗan ƙamshi ke fita daga jikinshi,
  "Mommy tace mun zaka zo wurina muyi shawara ko"?
  "Eh hakane,tace daga yanzu in zanyi shawara dake yakamata nayi,"
  Ba ƙaramin daɗin maganar nan taji ba,
  "Tunani me kyau,Banaso wani ya ganmu anan,Kunya nake ji,"
  "Zan jiraki a bakin swimming pool,Ki kawo mana Coffee,Yadda zamu ji daɗin tattaunawa,"
  Zaro ido ta ɗanyi"Dare fa yayi har 10,ko baka duba agogo bane,"
  "I know,ae ba jimawa zamuyi ba,Just 30 mins,"
"Shikenan yanzu xan zo,"takai ƙarashen maganar tare da juyawa da sauri ta nufi kitchen,
  Fitowa daga falon yayi kaitsaye Ya wuce bakin pool din,A ɗaya daga cikin ƙayatatun kujerun dake a wurin Ya xauma yana jiran zuwanta,wata irin iske ce mai daɗin gaske take kaɗawa a wurin,

Badajimawa ba,Jahad ta dawo hannunta ɗauke da Cup guda biyu ta ajiyesu saman table din gabanshi,Kafin ta zauna itama,sunji daɗin yanayin sosai suna shan Coffee dinsu suna fira,Tsawon 30 minutse kafin Suka bar wurin Kowa ya koma ɗakinshi,

Wuraren ƙarfe Goma Sha biyu na dare,Motar Sgr ta shararo da gudun gaske izuwa cikin gidan,Bayan Amstrong yayi parking ɗinta Ya fito tare da zagayawa Ya buɗe mashi mota,A hankali Ya zuro ƙafarshi ɗaya kafin Ya ƙarasa fitowa waje,

Jikinshi na sanye da jallabiyar nan daya fita da ita a lokacin da ya ɗauki Sehrish,hannunshi na ruƙe da leda fara mai ɗauke da sunan asibitin Dr harriet,Sallama yayi ma Amstrong kafin Ya nufi cikin gidan,Baisamu kowa a palourn ba,kaitsaye ya nufi upstairs,A hanzarce Ya fada part ɗinshi,A rufe ya samu ƙopar palourn,Hannu yasa ya turata,Sannan ya shiga daga ciki,ko'ina fess an gyara mashi,Sa6anin yadda ya tafi tabarshi,Bedroom ɗinshi ya shiga nan ma ya tarass An gyarashi,yayi mamaki sosai,bai ta6a tunanin za'a samu wanda zai kawar da ƙazantar da ya bari saman gadon ba,Ajiyar zuciya ya sauke,Kafin ya ƙarasa ciki,toilet Ya shiga,After Some minutes Ya fito daga wanka,Jikinshi sanye cikin bathrobe,A gaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi,Bakomai yake fargababa,face haɗuwarshi da Abbansu,Da kuma Uncle abusufyan,yayi danasani sosai,Baisan da wani ido zasu kalleshi ba,zama yayi saman front chair din madubin,Ya zabga tagumi da hannu ɗaya,ya damu sosai akan son sanin wani hali Sehrish take ciki,taci abinci ko bata ci ba,ga allurorinta da bai kammala yi mata ba,hada medicine dinta,Duk yau batasha ba,

Yana cikin wannan zancen zucin,Omar ya faɗo ɗakin nashi,ta cikin mirror ya hangoshi,farin cikine Ya lullu6eshi,Da sauri ya miƙe tare da juyawa ya nufeshi,Hankalin Omar ya ɗan tashi ganin yadda Sgr ya canza,Yayi rama,ya kuma yi haske sosai,kamar ka ta6a jini ya fito,yana ƙarasowa suka rungume juna sosai,kamar zasu haɗiye kawunansu,
  "Nayi missing dinka sosai,ɗan uwana nakaina,"Omar ne yayi maganar,Yayin da hannunshi ke abayan rafayet yana dan bubbugashi,
   Tun da ya kwantar da kanshi a kafadar Omar,Jikinshi yayi sanyi sosai,Hawaye suka cicciko tab a idanuwanshi,sam ya kasa buɗe baki yayi magana,Shi kaɗai yasan halin da yake ciki,
  Ɗago dashi Omar yayi"Rafayet"ya ambaci sunanshi tare da kai hannunshi saman fuskarshi,
  "Ka rame sosai,Duk ka canza,Kodai atare kukayi jinyar,"?
  "I don't ave peace of mind,ina cikin matsanancin tashin hankali Omar,na damu sosai,bansan ya zanyi ba,"
Lallashinshi Omar yayi tare da janyo shi suka zauna gefen gadonshi,Sosai ya shiga yi mashi nasiha akan abunda ya aikata,a ƙarshe yace"Tun wuri Rafayet,Kaje ka samu abba da uncle abusufyan,ka nemi yafiyarsu,Sannan ka sanar dasu cewa Kana son matarka,Kuma zaka tafi da ita u.s ba amatsayin mai aiki ba,idan har kayi wannan shikenan zaka zauna Lafiya,Nima kuma zan samu kwanciyar hankali,"
  Muryarshi asanyaye yace"Shikenan,zanyi hakan amma nasan zaiyi wuya uncle ya yafe mun,"
  "Zai yafe maka,ka jaraba yin hakan,Yanzu ka tashi ka shirya ka fara zuwa wurin Abba,Nasan baiyi bacci ba,"
  Amsa mashi yayi da toh,duk tausayinshi ya kama Omar,Miƙewa Omar yayi tare da kallonshi"Ka kulamun da kanka,Duk yarda ku kayi dasu saika sanarmun "
   Har yakai bakin ƙopar Sgr ya dakatar dashi"Na manta,Akwai injection din Sehrish tare da medicine ɗinta,Dana zo dasu,"

"Tana kwance a ɗakin oummansu,"ya ƙarasa maganar tare da fucewa daga ɗakin,

Shaf shaf Ya kammala shiryawa cikin Sleeping dress dinshi,White colour masu ɗigon baƙi,Bayan ya feshe jikinshi da turare Ya sauko down stairs,Direct Ya nufi ɗakin abbansu,A ƙopar ɗakin ya tsaya cike da zullumi,almost 5 mins yana a tsaye bai motsa ba,Ya kasa sanya hannunshi balle ya kwankwasa ƙopar,

Ji yayi bazai iya haɗa ido da abbansu ba,jiki asanyaye ya juya zai bar ƙopar ɗakin,Ba zato ba tsammi sai ga abbansu,A tsaye Ashe Yaji ma a bayanshi yana kallonshi,bai jima da shigowa ciki ba,gabanshi ne Ya faɗi rass,Da sauri ya duƙar da kanshi kasa,duk yabi ya dabarbarce,
  "Ka dawo kenan"?daƙyar ya iya buɗe baki yace"Eh,"
   "Banyi tunanin zaka ji kunyar haɗa ido dani ba,"yayi maganar yana kallon fuskarshi,shiru Sgr baice komai ba
"Munga takardar saki mun gode,"yana kai ƙarshen maganar,Ya soma ƙoƙarin bi ta gefen Shi zai wuce ya shiga ciki,Da sauri Sgr ya ruƙo hannunshi,Rai a6ace abba yace"Ka sakarmun hannuna tunkafin ranka ya 6aci,Mara mutunci kawai,wlh rafayet ka bani kunya,ban ta6a tunanin zaka yi mun haka na,Kana ɗaya daga cikin ƴa'ƴana waɗanda nake alfahari dasu,Amma sai gashi Ka watsa mun ƙasa a ido,"tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,hankalin Sgr ba ƙaramin tashi yayi ba,
  Muryashi na kerma Ya ambaci sunanshi'Abba,"
  "Ni ba abbanka bane,ban haifi ɗa irinka ba,Tunda ban isa na sanyaka abu kayi mun ba,"jin wannan maganar yasa hawayen dake kwance cikin idanuwanshi suka soma gangarowa saman fuskarshi,Gaba ɗaya Ya tafi Zai zube saman guiwowinshi,da sauri Abba ya ruƙoshi"kada ka kuskura ka zukunnamun,Saboda bakayi a lokacin daya dace ba,"
  "Am sorry abba,Nasan nayi kuskure,kuma nayi danasani,pls abba,kada kayi fushi dani,"

Zuciyar abba ta karaya sosai,daurewa kawai yake yi,ba don son ranshi yake furta mashi kalaman bakinshi ba,
   "Idan har kanaso,In shirya dakai,Kaje ka fara neman Yafiyar abusufyan,Sannan ka dawo wurina,"Yana kai ƙarshen maganar,Ya buɗe ɗakin Ya shige,

Ya jima a tsaye batare da ya motsa ba,Daƙyar ya iya jan ƙafarshi Ya doshi ɗakin abusufyan,A ƙopar ɗakin ya tsaya cike da zullumi,yafi jin shakkar tunkararshi akan kowa,hannu yasa yayi knocking ɗin ƙopar,Kusan sau uku yana kwankwasawa amma ba'a buɗe mashi ba,tunanin tura ƙopar yayi sai gashi ta buɗe,Da sallama abakinshi ya shiga ɗakin,Hasken bedside lamp ne ya haskaka mashi gadon abusufyan,Yana akwance yayi nisa acikin baccinshi,Was wasi ya tsaya yi acikin zuciyarshi Ya tafi koya tsaya,in har abusufyan bai yafe mashi ba,Abba ma bazai yafe mashi ba,Taya zai samu kwanciyar hankali?mahaifinshi na fushi dashi,

Kasa tafiya yayi,wuri ya samu gefen gadon uncle ya zauna,batare daya tayar dashi ba,Don yaci alwashin bazai ta6a tafiya ba,koda kuwa zai kwana a dakinne har sai Uncle ya yafe mashi,har wuraren ƙarfe 1:30 na dare yana zaune babu alamun bacci atattare dashi,Yayin da abusufyan keta sharar baccinshi,

Daya gaji da zamanne ya kwantar da kanshi gefen saman gadon,har bacci yayi awon gaba dashi,Lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar asuba,Wayar abusufyan dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,da ƙarfi kiran ya shigo,har cikin kunnanshi yajiyo sautin,A hankali ya ɗan buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci don bai ishe shi ba,daga kwancen da yake ya wurga idanuwanshi kan Agogon bangon ɗakin,Lokacin sallar asuba yayi,dama sai da ya kawo hakan aranshi,don kuwa bamai kiranshi a wannan lokacin in ba abba ba,domin ya tashe shi sallar asuba,sam bai lura da mutun a gefenshi ba,daƙyar ya samu ya miƙe yana yin hamma,tare da yin miƙa,kafin ya sauke hannunshi ne karaf idanuwanshi suka sauka akan Sgr dake kwance yana ta sharar bacci,Gabanshi ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,don baiyi tsammanin ganin mutun adakinsa ba,kuma farat ɗaya bai waye shi ba,don har sai daya ɗan raza,Cike da mamaki yake binshi da kallo,Abun yayi mugu mugun ɗaure mashi kai.
"Rafayet"!ya ambaci sunanshi da ƙarfi,hannu yasa ya ɗan bubbugi kafadarshi,nan fa ya fara sambatu yana faɗin"Am sorry uncle,ka yafe mun,bazan ƙara ba,Nasan nayi kuskure amma ba'a son raina ba uncle i ave realized my mistake,a shirye nake dana kar6i koma wani irin hukuncine daga gare ka........"duk cikin bacci Sgr yake wannan sambatun batare daya sani ba,hada hawaye akan fuskarshi,tsananin tausayinshi ne ya kama abusufyan,ya lura da irin ramar da yayi,sam babu natsuwa atattare dashi,dama sai da ammi ta sanar dasu cewa duk irin raɗaɗin da zasuji na abunda ya aikata,Basu kaishi ba,don saiya fi su jin jiki,tuni idanuwan abusufyan sun cicciko tab da kwalla,

Slowly yakai hannunshi saman sumar kanshi,bai ta6a tunanin Sgr zai iya sauke girman kanshi ba,Yazo neman yafiya a wurinshi,sai gashi da kanshi ya bashi mamaki,Allah kadai yasan tun lokacin dayazo ɗakin yana jiranshi ya farka,

Bubbuga kafaɗarshi yayi tare da ambaton sunanshi"Rafayet!Rafayet"!a firgice Sgr ya farka,yana faman zare blue eyes ɗinshi,Koda su kayi ido biyu da Uncle abusufyan da sauri ya sunnar da kanshi ƙansa,cike da jin kunyarshi,
"Tun yaushe kazo ne"?
Cikin sanyin murya yace"Tun wuraren ƙarfe sha biyu da rabi,nazo na same ka kana bacci,".
"Meyasa baka tashe ni ba"?
"Saboda Banaso na takura maka ne,"daƙyar yake magana,saboda nauyinshi da yake ji,
Yaƙi yarda su hada ido,Baisan yaushe Sgr ya fara jin kunya ba,Tabbas


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login