Showing 225001 words to 228000 words out of 307403 words

Chapter 76 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

ambaci hakan lokacin daya ƙarasa wurinsu,
  "Yau naga abun al'ajabin da banta6a gani ba,Dan Allah ku wayarmun da kaina!wanda ya mutu ne ya dawo ko kuwa ghost dinsa ce"?Yayi tambayar yana kallonsu,a lokacin Sgr ya ɗan buɗe idanuwanshi,Sun canza launi sosai,
  "Nikaina Abun Yayi mugun ɗaure mun kai wlh,Still ina doubting,Am confused Allah,ni dai idan ma mafarki nake yi kada ku tashe ni,Ku barni inta yin shi,"cike da tsantsar farin ciki Omar yayi maganar,hannunshi na dafe da saitin Zuciyarshi,No more tension
  Dafa kafaɗar Sgr Dr emran Yayi da hannunshi yana kallon fuskarshi,
  "Sgr fa kamar suman tsaye yayi,Ku tayani dubawa,"Dariya Sehrish tayi,Da alama farin cikine Ya hanashi yin magana,Ko ƙyafta idanuwanshi baiyi,Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi ya shiga zurfin tunani sosai,hankalinshi Ya tafi wani wurin daban,

Wayarshi daya jefar ƙasa sai dai Sehrish ta ɗauketa,komawa Sehrish Tayi wurin Oummansu,wuri ta samu ta zauna tana kallon Jahad da ta kifa kanta saman laps ɗin Oummansu,
  Cikin sanyin murya ta Ambaci sunanta"Jahad"
"Na'am"ta amsa mata,batare da ta ɗago da kanta ba,'
  "Inason magana dake,"jin haka yasa ta ɗago da kanta,fuskarta duk a yamutse,idanuwanta sunyi jawur,
  "Sehrish amma dai ba gaskiya bane ko!nasan hakan bazai ta6a zama gaskiya ba,Junaid Ya mutu akan idona,Ni naji kukan shi acikin mota Lokacin da yake ƙonewa,Yau kuma sai gashi ya dawo da ranshi"?tayi tambayar a ruɗe,
  "Just believe it!Junaid bai mutu ba,Yana araye,ba lalle ne ki fahimce ni ba a yanzu,Amma tabbas Junaid muka shigo dashi,"_
  "Bazan ta6a yarda ba Sehrish,Sa dai ko me kama dashi ne kuka ɗauko,Amma Junaid dana sani baya acikin duniyar nan"tana kai ƙarshen maganar ta fashe da kuka tare da mayar da kanta saman laps ɗin Oummansu ta kwanta,Tsananin tausayinta ne Ya kamasu,
  "A yanzu ba lalle ne ta fahimce ki ba,Kada ki wahalar da kanki wurin yi mata bayani,"A cewar abu,da ta raba tsakaninsu,
  Gyaɗa kai Sehrish tayi tare da jingina bayanta jikin seat ɗin da suke,

Har time ɗin sallar Magrib ya shige basu ankara ba,Sae da Abusufyan ya tunasar dasu,daƙyar Ya tattarasu gaba ɗaya suka tafi masallaci,

Ya rage daga Alex dake tsaye a bakin ƙopar ɗakin,Sae Su Sehrish da Oummansu dake zaune saman waiting seat,Hosana dae tuni ta jima da yin nisa a baccinta,Duk wannan budurin da ake ita bata sani ba,anan Cikin asibitin ke akwai masallaci,Na mata dana maza,lokacin da suka tashi Yin sallar suna neman inda zasuyi wata Nurse ce ta yi masu jagora zuwa masallacin mata,Kowa sai da Yayi sallah banda Mommy da Hosana,Basu jima da yin magrib ba aka fara kiraye kirayen Sallar Isha'e,basu Baro masallacin ba sae da suka kammala Sallar Isha'en Sannan suka dawo,Ba ƙaramin natsuwa suka samu ba,

Dawowar su Sehrish da ƴan mintuna,ɗaya daga cikin likitocin dake dubasu Ya fito tare da basu izinin Shiga ciki,Alex ce ta fara Shiga,Oumma tare da su sehrish suka bi bayanta,gefen gadon ta zauna yayin da idanuwanta ke akan Junaid,sun canza mashi kayan jikinshi,Riga suka sanya mashi kamar uniform blue colour iya guiwarshi ta tsaya,hannunshi na sanye da kanula ana yi mashi ƙarin jini,Hancinshi na sanye da robar Oxygen,Sai jan numfashi Yake Yi da ƙarfi da ƙarfi,siraran hawaye ne suka sauko akan fuskarta,ruƙo yatsun hannunshi tayi acikin nata,

Jahad dai ta toge a bakin ƙopar ɗakin tana lekenshi,A tsorace take dashi gani take kamar fatalwarsa ce aka kawo masu,taƙi yarda cewa Shi ne Ya dawo,
  Matsawa Abu tayi zuwa gaban gadon ta samu wuri saman kujerar dake fuskantar gadon ta zauna,Addu'o'i ta soma karantowa tana tottofa mashi akan fuskarshi,hakan baƙaramin daɗi yayi ma Alexandra ba,
  Amrish dae na tsaye ta lullu6e kanta da kallabin lace dinta,hannunta na ruke dana Sehrish,gabanta sae faɗuwa yake yi,tana cikin mawuyacin hali,Duk ta tsani kanta,Gani take yi kamar in suka ji cewa Mahaifiyarta ce tayi ma Junaid haka zasu koreta ne,ko su fara ɗaukar fansa akanta,
  "Ki kwantar da hankalinki,ba abunda zai faru,nasan kina jin tsoro ne shiyasa kika tashi hankalinki,"Sehrish ce tayi maganar cikin sigar lallashi,don ta lura da yanayin da Amrish ɗin ke ciki,
  Ƙasa ƙasa suke magana,a tsakaninsu,
"Ji nake kamar in gudu,kafin kowa yaji labarin ainihin abunda Ya faru da Junaid,ni nasan cewa tawa ta ƙare,Ga kuma Mommy tana can tana nemana ta kashe ni"ta shiga damuwa sosai,batasan yanzu ina zata dosa ba,
'Kina tunanin cewa zamu barki ki tafi ne?duk irin ƙoƙarin da kikayi mana,indai kina fargaba ne akan Family ɗinmu,to ki kwantar da hankalinki,Suna da kyakkyawar Zuciya zasu fahimceki su kuma kar6eki hannu bubbiyu,In ma basu amshe ki ba,ni bazan bari Ki tafi ke kaɗai ba zan bi ki ne,"on a serious note,Sehrish tayi maganar,
Har cikin zuciyarta taji daɗin kalaman Sehrish kuma hankalinta ya kwanta,duk da akwai sauran fargaba,

"Assalamu Alaikum"Abusufyan Ne ya shigo fuskarshi ɗauke da Murmushi Hannunshi ruƙe dana Sgr,Omar na abayansu tare da Ya mu'allim,yayin dasu Fawan ke biye dasu,Kowa ka kalla tsantsan farin cikine bayyane akan fuskarshi,tsayawa su kayi agaban gadon cirko cirko suna kallon Junaid,Har lokacin Abbansu na kwance gefen Junaid,tunda akayi mashi allurar bacci bai farka ba,

Sai faman sauke ajiyar zuciya Omar da Sgr suke yi,sun jinjinawa lamarin,ƙaryar da suka shirya ta zama gaskiya,Ga ƙannensu sae murna Suke yi Junaid ya dawo,kidnappers sun sake shi,basu san dawan garin ba,
Da zarar Sgr ya haɗa ido da Omar saisu sakarwa juna murmushi,abun ba'a magana,shigowa ciki doctor Emran Yayi fuskar nan ɗauke da ƙayataccen murmushi,jerawa yayi tare dasu,yadda kasan sun Samu talabijin haka suka ƙurawa Junaid ido suna kallonshi,
Dr emran ne ya soma magana a tsanake,
  "In sha Allah,Zasu samu sauƙi,dama damuwarshi rashin Junaid ne,Yanzu gashi Allah ya dawo mana dashi"yana kai ƙarshen maganar,
  Ya mu'allim ya ɗaura da cewa"Yakamata mu nuna godiyarmu ga Allah subhanahu wata'ala,daya bayyanar mana shi,sannan muyi masu addu'a"
Atare suka ɗaga hannayensu sama,Ya mu'allim ya shiga yi masu addu'a suna amsa mashi da Ameen,sun ɗauki tsawon Lokaci kafin suka shafa Addu'ar,
  Suna zame hannayensu daga saman fuskokinsu,yatsun hannun Junaid suka fara motsi,Da ƙarfi Mommy ta ambaci sunan"Junaid"fuskarta ɗauke da murmushi,hankalin sauran ya dawo kanshi,
  Mutsu mutsu yaci gaba da yi,Jahad sai leƙenshi take yi daga tsayen da take abakin ƙopar,ita dai har yanzu bata yarda ba,
  Mutsu mutsun yaci gaba da yi,duk sun zuba ido suna kallonshi,la66ansa sae kerma suke yi,Slowly ya soma sambatu tun yanayi ƙasa ƙasa harya fara yi da ƙarfi Sunan Abbansu yake ambato,"Abba!Abba!"cikin fitar hayyaci ya soma kokarin ɗaga hannunshi zai cire Oxygen ɗin da aka sanya mashi,Da sauri Dr emran da Omar suka ƙarasa ta gefenshi tare da rurruƙe hannayenshi,hankalinsu gaba ɗaya ya tashi ganin yadda Junaid ke ta firgita,
  "Abba!Abba"daƙyar sautin ke fitowa daga bakinshi,tunda Ya Mu'allim yaji hakan,Sae ya basu shawarar Su matso da Junaid kusa da Abbansu,tunda akwai interval a tsakaninsu,da alama yana ji aranshi cewa mahaifinshi na a kusa dashi,Shiyasa yake ambaton sunanshi,
  Dubara su kayi a hankali suka janye Junaid zuwa gefen Abbanshi,Abun mamaki suna gyara mashi kwanciyarshi sae gashi yana kokarin lalubar jikin Abbansu,Abun yayi mugun ɗaure masu kai,Sam fa baya acikin hayyacinshi amma yaji aranshi Abbanshi na kusa dashi,daƙyar ya iya ɗaga hannunshi ya ɗaurashi akan fuskar Abbansu yana shafata,kuma wani abun mamaki idanuwanshi arufe suke gam,jikin ne kawai ke motsi,

Har saman wuyanshi Junaid yakai hannunshi zuwa saman ƙirjinshi,har lokacin bai daina ambaton sunanshi ba,ga la66anshi sae kerma  su ke yi,
  Murmushi kawai suke saki suna kallonshi,
"Gaskiya tunda nake banta6a ganin ƙauna tsakanin mahaifi da ɗansa ba,irinta mahaifinku da wannan ƙanin naku,"Dr emran ne yayi maganar,da mamaki akan fuskarshi,
  Sai lokacin Alex ta samu damar yin magana
  "Nikaina da nake mahaifiyarshi bana tunanin yanayi mun irin son da yake yiwa mahaifinshi,Koda yake dole yaso mahaifinshi akaina,shaƙuwarsu ta wuce tunaninmu,"
  Suna cikin yin maganar,Abbansu ya fara ƙoƙarin buɗe idanuwanshi,Wani irin nauyin bacci ne ya hanashi tun ɗazu ya farka,amma yana jin muryar Junaid acikin kanshi,sake ambaton sunanshi Junaid yayi da wata irin kasalalliyar murya,
  "Abba,"tunkafin Ya buɗe idanuwanshi ya soma kiran sunanshi"Junaid"gaba ɗaya suka matso kewaye da gadon suna murmushi,Yayin da idanuwansu ke akan Abbansu,
  Ruƙo hannun Junaid yayi acikin nashi,sosai har cikin ranshi Yaji dagaske Shi ɗinne,kokawa ya shiga yi da baccin dake ƙoƙarin hanashi buɗe idanuwanshi,
  Daƙyar ya ɗaure ya ware idanuwanshi,a wani slow ya wurga eye balls ɗinshi kan Junaid dake kwance agefenshi,Tunda ya ɗaura eyes ɗinshi akan fuskar Junaid ko ƙyaftawa baiyi kamar an dasa mashi aya,wani irin farin ciki ne ya lullu6eshi lokaci guda hawaye suka shiga wanke mashi fuskarshi,Muryarshi na kerma Ya ambaci sunanshi"Junaid!dagaske kaine a kusa dani,Junaid ɗina ne atare dani"?
  "Yaya hossein dagaske ne abunda kake gani,ga Junaid ɗinka nan,an dawo maka dashi"Abusufyan ne yayi maganar,
  Lumshe idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu a hankali yana cigaba da kallon fuskarshi,Lokacin daya ankara da Jini da ake ƙara mashi aruɗe yace"Me ya same shi?Sun cutar mun dashi ko?duk sun canza mun Junaid ɗina kamar bashi ba,"
  "Abba,ka kwantar da hankalinka,Junaid yana samun sauƙi,"Omar ne yayi maganar cikin sigar lallashi,
   "Alhamdulillah Ya Allah daka dawo da farin cikana"ya ƙarasa maganar tare da dago da hannunshi zuwa cikin sumar kanshi,
  "Allah Ya baka lafiya Junaid ɗina,ka yafe mun duk laifina ne halin daka shiga,Bazan ƙara yin kuskuren da zan rasaka a kusa dani ba"yana magana hawaye naci gaba da sauka akan fuskarshi,

Jikinsu duk yayi sanyi,tsananin tausayinsu ne ya kamasu,

Wuraren ƙarfe 10 na dare,Abusufyan ya kwashe su Sehrish zuwa gida,Su biyar ya ɗauko hada Amrish da Oummansu,Ba don sun so ba ya ɗaukosu,lokacin da ya ƙaraso cikin gidan bayan yayi parking ɗin motar,Buɗe motar Oummansu sehrish tayi tare da fitowa waje,Bayan Abusufyan Ya fito ya zagaya ya buɗema su Sehrish,saukowa tayi daga cikin motar,Amrish ma ta sauko bayan ita sai Jahad,duk suka fito banda Hosana,ruƙo hannunta Yayi tare da ambaton sunanta,Daƙyar ta iya buɗe idanuwanta,
  "Ki fito ku wuce gida,Sae ki kwanta ki ƙarasa baccin naki,"A yamutse ta fito daga cikin motar,ruƙe hannunta Sehrish tayi ganin tana tangal tangal zata faɗi ƙasa,
  Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da kallonsu yace"Ku wuce ciki mana,Ni zan koma ne,zuwa gobe zamu dawo gida sai acigaba da jinyar tasu a gida,"
  Gyaɗa kai abu tayi tare da cewa"shikenan,Allah ya basu Allah,Amma Mommy fa?zata dawo itama"?
  "Sai zuwa gobe zamu dawo tare da ita,"ya ƙarasa maganar tare da kallon Jahad,
  "Banga kina farin ciki ba,ko bakiyi murna da ganin Masoyin naki bane"? Zuba mashi ido kawai tayi batare da tace komai ba,itafa har yanzu bata yarda Junaid bane,zaiyi wuya ta yarda inba an sanar da ita Yarda akai Ya tsira daga cikin motar nan ba,
  Sehrish na ƙoƙarin buɗe baki tayi mata magana,muryar AZMEE ta katsesu,
  "Sannunku da dawowa,"gaba ɗaya suka kai idanuwansu kanta,
  Jikinta na sanye da dogon hijabi,fuskarta da alamun damuwa,
  Ɗaure fuska Abu tayi,sam ta tsani ganin Azmee arayuwarta,
  Ƙarasowa tayi gaban motar da suke a tsaye,
  "Abusufyan Ya mai jikin?ɗazu naso na biyoku asibitin amma bansamu hali ba,Da yake tunda safe ina kwance ba lafiya,"tunda ta soma magana,Amrish ta ƙura mata ido tana yi mata kallon sani,kamar yarda amrish ke kallonta,itama haka take kallon Amrish ɗin,
  "Jikinshi da sauƙi,zuwa gobe zamu dawo gida,Ya jikin naki?naji kince bakya lafiya,"
  "Alhamdulillah,Naji sauƙi,Idan zaka koma asibitin akwai dinner dana kammala Yanzu,bari na shirya maka kayan abinci saika kai masu,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta wuce ciki,
  Abu ji take kamar ta hana Abusufyan ya kar6i abincin nan don bata yarda da ita ba,tsoranta kada ta sanya masu guba aciki,"
   Ganin sunƙi shiga gidan Yasa Abusufyan yi masu magana"Tsayuwar me kuke yi ne?ku wuce ciki mana,wanda zaiyi wanka yayi wanka,ku kwanta ku huta,"
   Sallama su kayi mashi,kafin suka nufi cikin gidan,Sehrish sae faman waiwayon Abusufyan take yi har sai da ya lura da kallon da take yi mashi,tsoro take ji Ya tafi ya barsu tare da Aunty Azmee cikin gidan,gashi babu kowa Su kaɗaine mata,
Bayan shigarsu da ƴan mintuna,Azmee ta fito hannunta ɗauke da food basket mai faɗi,A bayan boot ɗin motar ya shigar dashi,komawa ciki tayi jim kaɗan ta dawo da wasu kayan abincin ya lodasu bayan motarshi,Sallama sukayi dashi ta juya ta koma cikin gidan,

*Boss Bature*

Bayan Shigarsu gidan kaitsaye ɗakinsu suka wuce,bayan sun shiga Amrish ta buƙaci shiga toilet don tayi wanka jikinta yayi mata nauyi,bayan ta shiga wankan Sehrish ta ɗauko mata kayan da zata sanya idan ta fito daga wankan,asaman gadonsu ta ajiye mata kayan,
  "Oumma Yunwa nake ji,"Hosana ce tayi maganar tun lokacin da suka shiga dakin ta baje saman gado,Jahad na zaune gefen gadon tayi zugudum,
  Tunanin zuwa kitchen tayi don ta Shirya masu abinci,tana ƙoƙarin ruke handle ɗin ƙopar,Sai ga Azmee ta turo ƙopar ɗakin,
  "Na shirya maku abinci,nasan kuna jin yunwa,"
  Bata jira amsar da abu zata bata ba ta juya ta fuce daga dakin,Saukowa saman gadon hosana tayi jiki na rawa ta kama hanyar fita ɗakin,da sauri Abu ta ruko hannunta"Ina zaki je,"
  "Abinci zanci,"
  "Ba zaki ci shi ba,Ki bari in girka maku,"
  Kamar zata fashe da kuka tace"Nidai ki barni inje inci na Aunty Azmee tunda ta gama,"
  "Koma ki zauna,yanzu nima zan kammala girka maku,"
   "Kina tunanin cewa zan cutar daku ne?"Kwatsam taji muryar Azmee,turo ƙopar ɗakin tayi"Don me zaki hanata cin abinci na"?ranta a6ace tayi maganar,
  "Saboda ban yarda dake ba,bazan bari ƴa'ƴana suci abincinki ba,"
  "Hosana,koma ki zauna,"tayi maganar tare da nuna mata cikin dakin,
  Idanuwanta cike tab da kwalla ta juya zata koma,
   Miƙewa Jahad tayi tare da takawa zuwa bakin ƙopar ɗakin,
  "Oumma!Meya haɗaki da Aunty Azmee"?
  "Jahad babu komai,kawai banason Hosana taci abincinta ne,"
  "Amma meyasa oumma?kullum ita ke girka mana abinci muna ci,sai yau kuma Oumma"?tayi tambayar da damuwa akan fuskarta,
  Sehrish dae tana cikin ɗakin tana sauraronsu,
  "Bansan laifin da nayi ma Oummanku ba da har ta hanaku cin abinci na,Babu komai,Nidai ga abinci can wanda yaga dama yaje yaci,"takai ƙarshen maganar tare da juyawa tabar ɗakin,

  Guntun tsoki abu taja,kafin ta fuce daga ɗakin ta nufi kitchen,Don ta girka masu abincin da zasu ci,

Komawa Jahad tayi jiki asanyaye ta samu wuri gefen gadon ta zauna,yayin da zuciyarta ke ci gaba da tariyo mata fuskar Junaid,
  Hosana sae faman shessheƙar kuka take yi saboda an hanata cin abinci ga yunwa tana ji,

Fitowa Amrish tayi daga cikin toilet jikinta ɗaure da towel,
"Idan kin kammala shafa mai,ga kayanan na ɗauko maki,wanda zaki sanya"ta ƙarasa maganar tana nuna mata,kayan da ta ajiye mata saman gadon,
  Murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Nagode sosai,"sai lokacin ta lura dasu Jahad,tun suna asibiti take taso tayi mata maganarsu amma tashin hankali ya hanata,Tayi mamakin kamaninsu koda yake wannan ya wuce kama,
  "Ƴan uwana ne su naga kina kallonsu,ƴan ukune mu,Ga Jahad can wadda ke zaune gefen gadon,Wannan mai kukan banzan kuma Sunanta Hosana,Sha takwas sha tara ce,ina fata kin gane,"ta ƙarasa maganar tana dariya,Wurgo mata harara Hosana tayi ba don tana jin yunwa ba da ba abunda zai hana takai mata bugu,

Murmushi Jahad tayi tare da cewa"kiyi haƙuri,tun a asibiti naso mu gaisa,bansamu dama ba saboda halin da muka shiga,Amma yanzu inayi maki barka da zuwa,"ta ƙarasa maganar tare da ƙokarin yin murmushin dole,
  "Nagode sosai da irin karramawar da kukayi mun,"hankalinta ya ƙara kwanciya,gaban dressing mirror ta zauna,ta dauki man shafawarsu ta soma shafama jikinta,bayan ta kammala,Sehrish ta miƙa mata Kayan baccin da ta dauko mata,hannu biyu tasa ta kar6a tana yi mata godiya,

Juya baya Sehrish tayi don tasamu damar sanya kayan,Ganin hosana na kallonta yasa Sehrish wurga mata harara tace"Lafiya kike kallonta?baki ga tana sanya kaya bane,"
Murguɗa baki Hosana tayi'Yo me zan kalla,Tana mace ina mace,Dama Namiji ne"
  Gaba ɗaya suka fashe da dariya,hatta Amrish ɗin,ba ƙaramin nishaɗi ta basu ba,
  Shaf shaf amrish ta zura kayan ajikinta ba ƙaramin kyau su kayi mata ba,white colour ne,
  "Nasan kina jin yunwa,Kiɗan ƙara haƙuri,ga Oummanmu can tana girka mana abinci,bari naje na tayata ma,"kama hanyar fita ɗakin tayi da sauri,
  Gefen gadonsu Amrish ta zauna,
"Yaushe zaki tafi gidanku"?
Baki asake Jahad ke kallon Hosana,
Shiru Amrish tayi bata tanka mata ba,saboda bata da amsar da zata bata,
"Nan zaki kwana ne"?ta kuma tambayarta,
  Rai a6ace Jahad tace"Ba'a sani ba dan uban mutun,Ina ruwanki da ita?ko saman kanki zata kwana ne?sai shegen ɗumi kamar aku,"
  Tsuke baki hosana tayi"nidai ba ubana ba,daga tambaya sai cibi ya zama ƙari?ƙari kuma ya zama ƙwababa"
Cike da takaici Jahad ta kalli Amrish"Am sorry pls,Wlh bata da hankali,Sai addu'a,Kuma hada ƙarin tana jin yunwa shiyasa take ta soki burutsun nan,"
Murmushi amrish ta ɗan saki tare da cewa"Bakomai,na fahimce ta,"

Lokacin da Sehrish ta shiga kitchen,Oumma ta samu tana ta faman zarya,Abincin da ta ɗaura masu take jira ya kammala dafuwa,
  "Oumma"jin muryar Sehrish yasa ta dakata da yin zaryar,Ta juya tare da kallonta,
  "Me kike dafa mana ne"?
Murmushi abu ta ɗan saki tare da cewa"jallof ɗin taliya na ɗaura tama kusa dafuwa,"
  Wucewa cikin kitchen ɗin Sehrish tayi,agaban gas ɗin ta tsaya,hannu tasa ta buɗe tukunyar ta leƙa ciki,
  Cike da mamaki tace"Oumma!amma dai yanzu kika zuba taliyar nan ko?naji kince ta kusa dafuwa amma kuma naga kamar yanzu kika zubata,"
  Jin haka yasa abu ta nufi wurin gas ɗin"kusan minti 15 fa da daurata,Ya isa ace ta kammala dafuwa yanzu"
  Leƙa tukunyar tayi,abun mamaki Taliyar tana nan yarda ta zubata,tamkar ba acikin ruwan zafi take ba,"
  Kallon juna su kayi at same time,abun ya ɗaure masu kai,
   "Oumma,ni a tunanina kawai mu haƙura muci abincin Aunty azmeen,
  Girgiza kai abu tayi"bazaiyiwu ba,Zanyi ƙoƙari naga taliyar nan ta dafu,"
  Wasa wasa taliya fa tayi kusan awa ɗaya bata dafu ba,
  Kodai gas ya qare ne,tayi tambayar tana leƙa ƙasan tukunyar wuta saici takeyi alamar akwai shi,
Jinjina kai tayi"wannan aikin Azmee ne,Wato don na hana ku ci abincinta,shine tayi mun haka,"
"Nima raina ya bani cewa itace,Kawai ki hakura Oumma,Dare yana kara yi ga Amrish tana jin yunwa sosai,"ba don taso ba,dole ta kashe gas cooker ɗin ta sauke girkin,

Komawa ɗakinsu Sehrish tayi,tana shiga ta sanar dasu cewa su fito suci abinci,

Jiki na rawa Hosana ta sauko daga saman gadon,Amrish ma ta mike tare da Jahad suka fito,Atare suka shiga dining area ɗin kowa ya zauna,Sehrish ce tayi serving ɗinsu,kowa ta zuba mashi a cikin plate ta tura masu agabansu,Sosai suka ci abincin,Ita dae bata ci ba Lemu kawai ta dinga sha,saboda gudun kada taga wani abu da zai tayar mata da hankali,don bazata manta da irin wahalar da tasha ba a jiya,

Wuraren ƙarfe goma sha biyu suka shirya kwanciya,A Bedroom ɗinsu Sehrish,Jahad da Oummansu tare dasu hosana suka kwanta,Amrish da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login