Showing 306001 words to 307403 words out of 307403 words
Chapter 103 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
idanuwanshi,Yayi mamaki Ganin babu Sehrish asaman gadon,Ga kuma shessheƙar kukan da yake ji acikin kunnanshi,saukowa yayi daga saman gadon,kaitsaye ƙwayar idonshi ta sauka akan ɗigon jinin dake a ƙasan tiles ɗin ɗakin,A jere jinin yake har zuwa toilet ɗinsu,Lokaci guda Hankalinshi Ya ƙara ɗunguma,A gigice Ya miƙe ya nufi toilet ɗin Yana faman ƙwala mata kira"Reesh!reesh!where are u"?Hannu yasa ya tura ƙopar toilet ɗin,Sai dai kash adatse take,ƙwaƙƙwaran naushi yakai ma ƙopar,ta buɗe Ya afka ciki a haukace,tuni idanuwanshi sun ciko tab da ƙwalla,Kwance ya hangota acikin bathtub ruwan dake acikin kwamin wankan ya gauraya da jinin dake ajikinta,Alamu sun nuna cewa ta jima Da mutuwa,hawayene suka wanke mashi fuskarshi,Sam Ya kasa ƙarasawa cikin toilet ɗin,Zubewa Yayi asaman guiwowinshi,sosai ya fashe da kuka,fuskarshi tayi jaga jaga da hawaye,sam bazai iya jure rashinta ba,Zuciyarshi barazanar harbawa take yi,Jiya jiyan nan suka sha soyayya da daddare gashi yau Ya wayi gari batare da ita ba,ashe dama na bankwanane sukayi"?
Runtse idanuwanshi Yayi sosai,Kafin Ya buɗesu a hankali,zurfin tunani ya shiga,Ƙura ido yayi yana kallon ɗagon jikin dake a gabanshi,Yatsanshi yakai tare da dangwalo jinin Yana kallonshi,Kokwanto ya shiga Yi Kamar ba Jini ba,Sam babu ƙarnin jini Ajikinshi,Azafafe Ya miƙe ya ƙarasa shiga Toilet ɗin,Ya tsaya gaban Bathtub ɗin yana kallonta,cike da saran abunda yake zargi,
Muryarshi na kerma Ya ambaci sunanta"Reesh...."shiru bata motsa ba,Almost 3 times Yana Calling Name ɗinta bata amsa mashi ba,jikinshi yayi sanyi sosai,dagasken dai ta mutu,Ya rasa reesh ɗinsa
Girgiza kanshi ya shiga yi la66ansa na kerma Ya shiga faɗin"Reesh why kika barni,Meyasa mutuwa zatayi mun yankan ƙaunane,wlh bazan Iya rayuwa batare dake ba,Zan kashe kainane,"A hanzarce Ya juya Ya fito daga toilet ɗin,jikinshi Na kerma Ya nufi bedside drawer ya ɗauko bindiga,cikin kunnanshi Ya saita bingidar Tare da rufe idanuwanshi,yana karanto kalmatusshahada,Sam batayi tunanin Sgr zai Iya aikata abunda Ya faɗa ba,da gudun gaske Ta fito daga cikin ƙwamin wankan daga ita sai undy data ja har zuwa saman ƙirjinta,tana ƙoƙarin buɗe ƙopar toilet ɗin Tajiyo ƙarar fitar bullet,Wata irin gigitacciya ƙara Sehrish tasaki,tana fitowa Ta same shi baje a ƙasa,jini duk ya wanke fuskarshi,Fashewa tayi da matsanancin kuka,A sukwane ta zube saman guiwowinta
"Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya rafayet!ka tashi!Nifa wasa nake maka Wlh ban mutu ba Wayyo Allah nashiga uku,Na bani Na lalace,gaba ɗaya tabi ta rikice Ta ruɗe,hannunta duk ya 6aci da jininsa,jijjiga shi tadingayi tana kuka kamar ranta zai fita,a ƙarshe ta rungumeshi tana kuka,ta tsorata sosai,daga wasa tayi silar mutuwar masoyinta,sai da ta jigata sosai,duk ta fita cikin hayyacinta,Sautin dariyarshi data dinga jine yasa ta yin saurin ɗagowa Tana kallon fuskarshi,Zazzare idanuwanta tayi akan fuskarshi,Ganin Yana ta faman tiƙar dariya,ya buɗe idanuwanshi sosai,
Daƙyar ya samu ya tsagaita da yin. Dariyar yace"Reesh ke kika iya tsara drama irin wannan balle ni da nake soja?I can do better than u,'
Fashewa ta kumayi da matsanancin kuka Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Meyasa kayi mun haka Ya rafayet!Nifa wasa nake maka,"
Jifa mata harara yayi"haka ake wasa a gidanku?waya gaya maki ana wasan mutuwa?ko shima duk cikin Soyayyarne?da ace tunfarko ban gane so6o bane kika sanya me kike tunanin zai biyo baya,Zuciyata har kusan bugawa tayi lokacin da naganki kwance cikin jini,
Kowannansu Yaji jiki,
Sosai take kuka"Wlh bazan Yarda ba,Ya rafayet Ka tsoratar dani"tayi maganar muryarta na kerma,
"So6on da kikayi amfani dashi kika ajiye bottle ɗin Saman fridge dashi nayi using na kwararama Kaina," Still hawaye basu daina zuba akan fuskarta ba,har wani zazza6i take ji ajikinta,
Kafeta da ido yayi yana kallonta,Kamar wata ƙaramar yarinya,kowa ya bata shawarar tayi mashi irin wannan wasan,
"Naji tsoran na rasaka,"tayi maganar ashagwa6e,
"In har zaki cigaba dayi mun irin wannan wasan to kuwa tabbas wata rana zaki rasa nine,"
Fashewa ta kuma yi da wani kukan Sosai ta sanya mashi rigima,tana faɗin Wlh bazan yarda ba,Ae ni ba haka nayi maka ba,ka tayarmun da hankalina......"
Cikin sanyin murya Ya bata hakuri"Am really sorry,"
Girgiza kai tayi"a'a Bazanyi haƙurin ba,"miƙewa Yayi daga zaune"Yanzu me kikeso nayi maki?wanda zaisa ki yafe mun,"
"Frog jump"ashagwa6e ta bashi Amsa,
Zaro Eyes ɗinshi Yayi "Frong Jump"?Ya maimaita abunda tace,
Ɗaga mashi kai tayi"Eh shi nakeso kayi mun,"
"Zanyi kneeling agabanki,In baki haƙuri"
Bubbuga ƙafafunta Tayi"idan ba zakayi Tsallen kwaɗi ba,ni bazan haƙura ba......."
Ganin Ya tsareta da ido Yasa ta Fashe da wani sabon kuka Hawaye duk suka wanke fuskarta,A ruɗe Sgr ya Zuƙunna tare da kama kunnuwanshi,
"Can zaka tafi,idan kakai saika dawo nan,"da hannu take nuna mashi inda zaije,Bakinta ƙumshe da dariya,Sam bai kawo komai aranshi ba,Ya soma Yin tsallen kwaɗi ya nufi inda ta nuna mashi Ya juyo Ya nufo inda take,
Tuntsirewa Sehrish tayi da dariya Tare da buga tsalle Tana faɗin"Na rama !Na rama!"
Abun ya ɗaure mashi kai,Sakin kunnuwanshi Yayi tare da miƙewa tsaye yana kallonta,Tsantsar farin ciki Ya gani akan fuskarta,Kamar wadda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,A ruɗe yace"Reesh are u ok"?
"bakaine kake sanyani Yin tsallen kwaɗi ba,lokacin da muna a gida?Yau nima Na rama,Na sanya Surgeon General Rafayet Tsallan kwaɗi,",tana kai ƙarshen Maganar,Ta watsa da gudu Ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi Tana dariya,
"Ke ko"?ya faɗi hakan fuskarshi ɗauke da ƙayataccen Murmushi,Abun ma dariya ya bashi,Wai ta rama,Ashe abun ya tsaya mata aranta,kamar zautacciya Haka taci gaba da dariya tana faɗin "I luv u Ya rafayet!Mijina nakaina"
"I luv u too,matata takaina,"ya amsa mata cikin so da ƙauna..............."
💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃*HAPPY ENDING*
*💋Boss Bature💋
*Alhamdulillah!* *Alhamdulillah!!* *Alhamdulillah!!!💃💃💃💃💃💃💃*
*A nan na kawo karshen littafin Abban sojoji wanda na dau tsawon lokaci ina rubutawa😍*
_Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala,the most compassionate and the most omniscient,da ya bani ikon kammalawa cikin ƙoshin lpy kaman yadda na fara,to him be all the glory🙏,tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi muhammad(S.A.W)😍Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da yan'uwana da malamai na da dukkan masoyana a duk inda suke a faɗin duniya🥰kura kuren ciki Allah ubangiji ya yafe man🙏_
_Gaisuwar ban girma ga mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya,she is my first luv and my everything💘,Allah ya ja da rai ya kara maki lafiya my sweetheart😘,My beloved Siblings💞waɗanda littafin nan Sadaukarwa ne a garesu,Nafisat,Aisha,Zainab,Khadija,maimunatu,Abdul'azeez,Fatima,Maryam,Ameenatu,I luv you so,so much,kune ni,in baku bani,I really appreaciate ur Encouragement💪,prayers and all-round support👍,Allah ya kara haɗa kawunanmu ya jiƙan mahaifinmu,Ameen_
_Special thanks to,Fadeela Lamiɗo,sadeeq Abubakar Ceo Lafazi writers,Abubakar Sadeeq AlQuramy,Maisalati,Kamala Kabeer,My Editor Aunty Zainab Laluh,whose contribution in no small measure serve as spices to this work,ina matukar godiya a gareki🙏da ƙarfafa man guiwa da kika rinka yi har zuwa kammaluwar wannan littafi ina rokon Allah kema ya baki ikon kammala littafinki lafiya Asanadin Maƙwabtaka😍and My P.A Munah Bature,ansha gwagwarmaya dae😂,ina matukar godiya agareki my other half😘_
To My Novel's Fans
Ba zan manta da yadda kuka rinƙa karfafa man gwiwa tsawon lokaci ta hanyar daɗaɗan Comment ɗinku,Summayer khutubi,Princess Bahilot,Meenarly Al'ameen,Oummi Sudeis,Asma'u Sani,Amjad (Mrs Rafayet),Maman shureim,ummu khaleel,maman aminu,Aunty hadiza,Xahra haroun,Hamida Yahaya ghandy,Asmieybash,Sadeeya attahuru kaoje,Zahra da sauran waɗanda bansamu na lissafo sunayensu ba,ina sane daku,ina matukar godiya a gareku ur comments means a lot to me,
Members of Comment Section 1&2,bansan da wane kalmomi zanyi amfani wurin gode maku ba,sai dae ince Allah ya barmu tare don ku din kun wuce fans kun zama yan'uwana agareni,
*JINJINA Ta musamman Ga dukkan Masoyan Littafin Abban Sojoji waɗanda suka Cire ƙyashi suka Biya kudin littafin Donsu karanta,ina magana akan Members Na paid group ɗina💃*
(1) Abban Sojoji
(2)Abban Sojoji Vip
(3)Junaid Romeo(Takun ƙarshe)
(4)Father Of Soldiars
*Allah Ya bar zumunci daga nan har Gidan Aljanna,Allah Yabiya maku dukkan bukatunku,Allah ya baku ikon Yin amfani da darussan dake acikin Labarin nan,Ina matuƙar godiya,Da irin haƙurin da kukayi,da kuma uzirin da kukayi mun har Allah ya bani Ikon Kammala Littafin nan,Yanzu gashi komai Ya wuce,Sai in Allah Yasa ina da rabon yin wani littafin kuma Ina fata zaku kasance A biye dani😰Zanyi missing dinku sosai*
*Littafin nan Ya ƙunshi darussa daban daban Na rayuwa,Ya ilmantar,Ya faɗakar,Ya kuma nishaɗantar damu💃💃💃*
*Wai ina mutanan dake cewa idan littafi yayi yawa ƙarshen shi baiyin daɗi😂da waɗanda kecewa Yayi tsawo yen yen yen Suka ishi mutane da surutu😂mahakurci mawadaci Yau dai Surutu akan Littafin Abban Sojoji Ya ƙare,No more Tsegumi No more Complain,No More typing No more Tension Boss Zatayi bacci hada minshari🥱🥱🥱*
*Hafsat Bature Muh'd*
*Boss Bature*✍️
*Ga masu Buƙatar Karanta Book na Abban Sojoji daga Book One zuwa 3 Complte Suyi mun magana ta whatsapp dina 0810388440*