Showing 213001 words to 216000 words out of 307403 words

Chapter 72 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

da mayar da fuskarta jikin pillow ɗin ta rufe,

Suna cikin wannan Yanayin na shauƙi Hosana ta kwala Sallama da ƙarfi,da sauri Sehrish taja bargon ta lullu6e kanta gaba ɗaya,Wucewa can cikin ɗakin yayi wurin closet ɗinshi,Jallabiya Ya zura ajikinshi kafin ya dawo ya zauna daga gefen gadon,

Jin Anyi shiru ba'a bata izinin shiga ba yasa tace"In shigo"?tayi tambayar tana leƙa kanta cikin ɗakin
  "Come in"ya bata permission din shiga,a tare da Jahad suka zo ɗakin tana la6e abayan Hosana,dama tun kafin su Shigo taja kunnan Hosana akan karta kuskura ta faɗa masu ɗaki batare da an basu izinin shiga ba,don tasan halinta,ɗan kaine da ita,

A tsanake suka shigo cikin ɗakin hannunsu ruƙe dana juna,
  "Yaya Rafayet ina kwana,kun tashi lafiya?Ya mai jiki"?
  "Alhamdulillah"bayan ya amsa masu ya miƙe tare da kallon Jahad a lokacin Hosana ta koma bakin gadon tana kallon Sehrish dake kudundune cikin bargo kamar mai bacci,
  "Ki ɗauko mata kayan da zata sanya ajikinta,"
  "Toh"ta ambaci hakan tare da juyawa ta nufi kopar fita daga ɗakin,fitowa palour yayi tare da samun wuri saman Sofa ya zauna,

"Rishi ya jiki?kinji sauƙi"?a hankali Sehrish ta ɗan zame bargon data lullu6e fuskarta dashi,kamar wadda ta tashi daga bacci haka tashiga mutsustsuka idanuwanta,kallon Hosana tayi daƙyar ta iya buɗe baki tace"da sauki,"
"Allah ya baki lafiya rishi,jiya fa ko bacci banyi ba saboda tunaninki...."murmushi kawai Sehrish tayi mata don tasan cewa ƙaryane,ba ƙaramin abu bane zai hana hosana yin bacci ba,
  Cigaba da magana Hosana tayi"nasha kuka Allah,Oumma tayi tayi dani akan in kwanta inyi bacci,Naƙiya nace nidai bazan iya bacci ba,har sai kin samu sauƙi,"ta ƙarasa maganar,hada ɗan kwa6e fuska,
  Murmushi Sehrish taci gaba da yi tana kallonta,
  Dawowa Jahad tayi hannunta ruƙe da rigar da ta ɗauko ma Sehrish,turkey gown mara nauyi red colour mai maɗaurin igiya daga tsakiyarta,atare da mayafinta ta ɗaurosu asaman hannunta,Shigowa palourn ta yi da sallama abakinta,Amsa mata sallamar yayi kafin ta wuce bedroom ɗin,

Anan ta samu Hosana tana ta shirga mata ƙarya,da alama ba ƙaramin nishaɗi take sanyata ba,agaban gadon ta tsaya tare da kallon hosana"ki sauka down Oumma na kiranki zaku ci abinci ne An kammala shirya breakfast,"jin haka yasa Hosana ta juya da gudu ta fita daga bedroom ɗin,dama wayau Jahad tayi mata don tabar ɗakin ko Sehrish ta samu ta shirya,ta lura babu kaya ajikinta,

"Ya jikin naki My own sis,"fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa mata da ƙyar"Am feeling better now,"
"Allah ya ƙaro lafiya,Ga wannan Ya rafayet ne yace in kawo maki,"tayi maganar tana miƙa mata kayan,yunkurawa tayi tare da miƙewa daga zaune takai hannu ta kar6i kayan,kafin ta sauko daga saman gadon,ɗaure da ɗan towel ɗinta,
"Bari na jiraki a palour,"da sauri Sehrish ta dakatar da ita"A'a,zan shiga daga cikin ɗakin na sanya kayan,Idan na kammala sai mu fita tare,"ba ƙaramar wahala take shaba idan zatayi magana,kamar ana tsaga bakinta haka take jin raɗaɗin,juya baya jahad tayi tana ƙarewa Bedroom ɗin kallo,a can ƙasan zuciyar kuwa tsabar farin ciki ne,Saboda ta gano wani abu game da Babban Yayansu,Da alama Ya fara faɗawa tarkon rishi ɗinsu,ashe da Rabon mafarkinta ya zama gaskiya,Wato na ganin Sehrish da ƙaton ciki ga kuma kwaɗayin Son Ganin Ƴa'ƴansu da take yi,lokaci guda kuma Yanayinta Ya canza,matsananciyar damuwa ta bayyana akan fuskarta,Bakomai Yasa ta shiga wannan Halin ba,Fa ce Masoyinta da ta tuna,tayi babban rashi wanda har ƙarshen rayuwarta bazata ta6a manta raɗaɗin rasa shi da tayi ba,a duk lokacin da suke waya dashi haka zai addabeta da tambaya wai Idan sunyi Aure A daren farko me zasuyi,duk in ta tuna wannan tambayar ta Junaid sai Murmushi Ya bayyana akan fuskarta,wasu siraran Hawayene suka soma saukowa saman cheeks ɗinta,

"Jahad,na shirya zamu iya tafiya,"jin muryar Sehrish yasa tayi saurin goge hawayenta,sannan ta juya tana kallonta,Ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,kamar wanda zata gasar kyau,Hannunta na a ruqe da wayarta da ta ɗauko,
  "Masha Allah"tayi maganar tare da ruƙo hannun Sehrish tana murmushin dole,

Atare suka shigo cikin palourn,har zasu fita ta ɗan dakata tare da juyawa ta kalli Sgr dake zaune saman sofa,ya jinginar da bayanshi,yayin da ya lumshe idanuwanshi tamkar wanda Bacci bai ishe shi ba,
  Sakin hannun Jahad tayi"ina zuwa,"
Fita daga wajen palourn Jahad tayi tana jiran dawowarta,

   A hankali ta ƙarasa wurin sofan dayake zaune ta tsaya,Cikin sanyin murya ta soma magana"bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu ba wurin yi maka godiya,saboda irin kyakkyawar kulawar daka bani,Thank You So much Ya Rafayet"tunda ta soma magana,Ya natsu yana sauraronta,daɗin voice ɗinta yake ji kamar kamar me ba kaman da take maganar a hankali,
  "Never mind,"yayi maganar batare da ya buɗe idanuwanshi ba,Juyawa Sehrish tayi da sauri ta nufi hanyar fita falon,Sai da ya tabbatar tabar wurin tukunna ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da waigawa yana kallon bayanta,har sai da ta fuce daga falon,

A 6angarensu Hayaam da Abra waɗanda tun jiya suka bar Abuja,Abun da ya faru lokacin da suka isa unguwarsu,wuraren marece tunkafin Su shiga gidansu suka lura da yadda mutane ke kallonsu,tun daga nan suka sha jinin jikinsu,Har nunasu akeyi da hannu ana cewa gasu can sune ƴa'ƴanta,Sun dawo daga yawon biɗiɗin nasu,Wlh anyi asarar Rayuwa,wasu kuma na cewa,Ae laifin uwar tasu ne da bata basu tarbiya ba ita ta lalatasu,Lokacin da suka ƙarasa ƙopar gidansu,A buɗe suka samu gidan,Da sallama suka shiga sunyi tunanin za'a amsa masu amma sai suka ji shiru,gidan babu kowa,komai na gidan babu,An kwashe komai,hatta butoci da bokatai babu,Har kan fanfonsu an 6alleshi,

Nan fa hankalinsu yayi mugun tashi,Tun a tsakar gidan Abra ta saki trolley ɗin hannunta,da gudun gaske suka shiga cikin ɗakunan suna kwalawa Mammynsu kira,Mammy! Mammy!!gabansu ne ya faɗi ganin ɗakin mammynsu babu komai wayam hatta katifarta,yanke shawarar zuwa makwabtansu Suka yi donsu tambayi Ina mammynsu taje ne,

Suna zuwa zauren gidan suka fara jiyo hayaniyar mutane,kasa kunne suka yi suna sauraran Surutun mutanen da sukayi masu dandazo a ƙopar gidan,
"Kuna ina la'anannu!waɗanda basu son ciwon kansu ba,Ku fito muci ubanku inba haka ba Mu ƙona gidan da fetur,kun tafi kun barmu da bala'e acikin unguwa,Yau sai mun fanshe haushinmu akanku,Jinin ku ya halatta"
  Jin wannan yasa tsoro ya kamasu,da gudu suka Koma cikin gidan,A ɗaki suka datse ƙopa,Hankalinsu Yayi mugun tashi,Sun rasa gane zunubin da suka aikata har mutane ke neman bugunsu,Suna Cikin wannan halin ne suka ji anyi masu Sallama,muryar Limamin Unguwarsu ce,ƙin fitowa su kayi har saida suka ji yace"Kada kuji tsoron komai,ku fito inason magana daku ne,Naba mutanen anguwar haƙuri Sun tafi,"jin wannan maganar yasa suka buɗe ƙopar ɗakin suka fito,Bayin Allah kowacce jikinta sai kerma Yakeyi,hawaye sharkaf akan fuskarsu,

Nasiha yayi masu sosai,A ƙarshe ya sanar dasu laifin da suka aikata wanda yasa mutanan unguwar ke neman kashe su,Abunda Ya faru Bayan tafiyar Abra,tabar Mammynsu ita kaɗai kwance tana jinya ta kwana ta yini cikin mawuyacin hali a lokacinne makwabciyarta tsigai wadda suke zuwa yin gulma a kuma gidanta ne ake kulle Amal,ta shigo ta sameta a wannan halin da kyar ta taimaka mata alokacin tana ta sababi tana fadin ina ma amfanin haihuwar yara irin nata,uwarsu ba lpy sun haura kafa sun tafi gantali,a washe gari tsigai tafiya ta kamata dama bata cika zama ba,ta ba yaranta umarnin su rinka leka Mammy suna kai mata abinci ai tun ranar farko da suka taras da ita acikin kazanta basu sake komawa ba sai ma wayarta da suka sace don rashin tsoron Allah,sauran mutanen unguwar babu wanda yasan da mara Lafiya acikin gidan,kowa yazo gidan nasu Yayi sallama ba'a amsa mashi ba,Sai yayi tunanin cewa babu mutun a gidan,Basu tashi sanin abunda ke faruwa ba,Sai da azababben wari ya ishi mutanan unguwar kamar gunyar ƙwai ta fashe,aka rasa daga ina wannan warin ke fitowa,Mutane suka kasa samun natsuwa a ƙarshe da aka tsananta bincike Aka gano cewa wannan warin a gidansu ne,Matasan unguwar suka shiga cikin gidan suna bincikawa har suka samu gawar Mammy ta ru6e naman jikinta ya zagwanye,tsutsotsi duk sun mamaye jikinta suna ci,Wa'iyazubillah,lokacin da su hayaam suka ji wannan Mummunan labarin a wurin limamin nan,Anan take Abra ta sume,Hayaam kuwa har kusan Zaucewa Tayi,sunyi danasanin rayuwarsu fiye da tunanin mai tunani,Sun tsani kansu,sun muzanta a idon jama'a,A ranar basu kwana acikin gidansu ba,Saboda mutanan dake dakonsu,Malam Liman ya tafi dasu gidanshi,kafin komai Ya lafa😭
 
A lokacin daƙyar aka samu wasu bayin Allah da taimakon limamin nan suka kawar da gawarta,An yi mata jana'iza kenan da Sati guda,Wannan makwabciyar tasu Tsigai,Ta sanya matasa suka kwashe mata kayan gidan kaf saboda tana bin Mammy bashin kuɗi kafin ta mutu,dama kuma a wurinta suke cin bashi in zasu wurin boka.

Gani Ga wane Ya ishi wane jin tsoron Allah,ya Allah ka kare mu daga aikata aikin danasani,

A 6angaren Ishaq kuwa,Aunty babba ta addabe shi da kira da numbobin mutane,bata gajiya da aron waya tana yi mashi magiya akan Ya taimaki Rayuwarta,Abunda yasa Ishaq bai mayar da hankali akanta ba shine tasaba yi mashi ƙarya ba kamar in tana son ta samu kuɗi,wannan dalilinne yasa bai ɗauki maganarta Serious ba,a ƙarshe ma data isheshi da kira sai ya cire Sim ɗin wayar gaba ɗaya ya ajiye shi,Ya musanya da wani sabo,ɗaya daga cikin illar yin ƙarya kenan Gashi tajama kanta,Gaba ɗaya yanzu hankalinshi na akan Hajjaju,domin kuwa ta amince zata aureshi,Soyayyarsu Tayi ƙarfi har sun fara zancen Yin aure,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 12 da rabi na rana,Amrish tana ta faman zarya acikin babban falon gidan,ranta a matuƙar 6ace,Ta cika tamkar zata fashe,tun safe ta ƙwallafa rai akan zasu fita a siya mata waya,Amma Mommy ta sa6a mata alƙawarinta,daga shiga ɗaki ta shirya ta fito bata ganta ba,ashe tabar gidan cikin motarta,Sae da ta bari ta ɗauki wankan lace ta sha uban make up tukunna tayi mata tsiya,Ta sha kuka harta gaji,fuskarta duk tayi jaga jaga da hawaye,tayi kukan harta gaji,a ƙarshe ta yanke shawarar zata nemo wayarta,Yau saita bincika ko'ina na gidan har sai Allah yasa ta gano wayarta,Upstairs ta fara hawa a buɗe ta samu ƙopar ɗakin Mommynta,Shiga ciki tayi tana ƙarewa ɗakin kallo,tunani ta shiga kota ina zata fara neman wayarta,bedroom ɗin ya haɗu sosai,Katafaren gado ne side by side ɗinshi kuma drawer ce,akwae faskekiyar wardrobe,ga tanƙameman Dressing mirror,da sauransu,hannu tasa ta cire kallabinta ta ɗaure shi a qugunta,drawer chest ta fara bubbuɗewa tana neman wayarta,sai da ta duba ko'ina duk ta hargitsa kayan bata ga wayarta ba,tuni ta haɗa gumi sai zufa ke tsastsafowa akan fuskarta,tsayawa tayi ruke da qugu tana faɗin"Wlh bazan haƙura ba,Duk inda kika 6oye mun wayata yau saina gano abuna,Ae ba ita ta siyamun wayar ba,Ya haroon ne ya siyamun,don haka dole a fiddo mun wayata,indai ana son Zaman lafiya"ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki ta nufi hanyar fita daga ɗakin,tana ƙoƙarin ruke handle ɗin ƙopar ta ɗan dakata yayin da kwalwarta ke tariyo mata wani abu kamar taso taga waya a saman gadon Mommynsu,
A waske ta juya tare da wurga idanuwanta kan Wayar dake ajiye asaman pillow,da farko tayi tunanin wayarta ce saboda iphone ce,Amma lokacin da ta ƙarasa gaban gadon ta ɗauki wayar sai taga ba wayarta bace,
  Cike da mamaki tace kodai Mommy ce ta siyamun sabuwar waya don tayi suprising ɗina'?
Jujjuya wayar ta shiga yi a hannunta,a kashe wayar take,
  Wuri ta samu gefen gadon ta zauna,ranta ne ya bata cewar ta kunna wayar ta gani,
  Danna power ɗin tayi nan take screen ɗin wayar ya kawo haske,Zama Amrish tayi tana jiran wayar ta kammala buɗewa,runtse idanuwanta ta ɗan yi kafin wayar ta buɗe,
  A hankali Amrish ta buɗe idanuwanta kan screen ɗin wayar,ƙura ido tayi tana kallon hoton wallpaper ɗin
Abun yayi mugun ɗaure mata kai!cike da mamaki tace"kai!Wannan ae hoton Yayan Sehrish ne,JUNAID ROMEO,wanda ke kawota makaranta!ya akai wayarshi tazo hannun Mommynmu,"miƙewa tsaye tayi tana ƙarewa hoton kallo,Fuskar nan ɗauke da wannan kyakkyawan murmushin nashi,tama rasa ina zata dosa,wani tunani zata yi,kwakwalwarta ta cunkushe,ita dai a iya saninta basu da alaƙa dasu Sehrish,Amma kuma ga wayar Yayan sehrish ɗin a gidansu,MEYA KAWO TA? tayi takaicin ganin wayar da face security dole sai da fuskar mamallakin wayar sannan za'a Iya buɗe ita,

Fitowa Amrish tayi daga cikin ɗakin Mommynsu hannunta ruke da wayar Junaid,Saukowa downstairs tayi a tsanake take taka staircases ɗin zuciyarta cike fal da mamaki,Zurfin tunani ta shiga bakomai ya faɗo mata aranta ba,fa ce Kalmar nan da Mommynta ke faɗi lokacin da tayi mata la6e a ƙopar ɗakinta,Wato akashe akashe shi kawai ko kuma a ƙwaƙule mashi idanuwanshi,tabbas kuwa ta fara zargin wani abu dangane da Mommynta,Akwai alamar Tambaya akanta babba ma kuwa,
  Gabanta ne ya faɗi lokacin da ta tuna da agogon Diamond ɗin da ta tsinta a tsakiyar falonsu,nan ta gane cewa iri ɗaya ce da agogon hannun Junaid da ta gani a hoton fuskar wayarshi,In har kuwa hakane kenan dole abu biyu zai kasance!

Ruƙe qugunta tayi da hannu ɗaya,tana ci gaba da zurfafa tunaninta
  "Kodai su mommy sunyi kidnapping ɗinshi ne shiyasa suka shigo da agogonshi da wayarshi acikin gidan nan,ko kuma Sun shigo da Yayan Sehrish acikin gidanmu daren Jiya,dama kuma tajiyo dirar motoci agidan,Daga baya kuma taji shigowar mutane a falonsu,duk da bata samu damar ganin meke wakana ba,'

Kasa samun natsuwa Amrish tayi,gudu gudu sauri sauri ta fito daga cikin gidan ta nufi Baba mai gadin gidansu dake zaune saman benci,yana sauraran radio,tsohon har saida ya firgita da ganin Amrish kamar yar daba haka ta faɗo mashi,Ɗankwali ɗaure da qugunta,kitson shuku ne akanta,

"Lafiyar kuwa Amrishi?ko sallama babu"?baba mai gadi yayi tambayar yana kallonta,
  "Ina fa lafiya,dan Allah so nake na tambayeka!a daren jiya wasu baki sun shigo cikin gidan nan,Ka lura dasu"?
  Shiru tsohon yayi yana tunano abunda ya wakana a wannan lokacin,Hajiya taja kunnanshi akan cewa ya rufe idonshi Ya zama tamkar makaho,Sannan ya rufe kunnuwanshi Tamkar kurma,
  Tuna wannan yasa shi yin saurin cewa"Bansan komai ba,lokacin da suka shigo cikin gidan nan bacci ya ɗauke ni...."tunkan yakai ƙarshen maganar Amrish tace"mai ƙarya ɗan wuta,wlh kaji tsoron Allah baba mai gadi,Tsofe tsofe dakai zakayi mun ƙarya,in har dagaske bacci kakeyi to waye ya buɗe masu gate?dole kaji horn ɗin mota kuma dole ka farka,

A ruɗe baba mai gadi yace"kinga dan Allah ki rufa mun asiri ki bar wurin nan,Hajiya ta kusa dawowa idan ta ganki a bakin gate ɗinnan zata tuhumeni ne"
  "Wlh bazan bar wurin nan ba,ko ka faɗamun amsar tambayata,Ko kuma wlh in ƙala maka sharri wurin Mommy ince kana nemana,"
  A firgice Baba mai gadi Ya miƙe tsaye yana ambaton"Subhanallahi!Amrishi kina da hankali kuwa?kinsan me kike faɗa"?duk ya tsorata saboda yasan cewa jarababbiya ce,kamar uwarta,tsaf zata iya ƙala mashi sharri
  "Zan tafi baba mai gadi amma inaso ka sani,Wlh saina ƙala maka sharri,Kasan police station?kasan Gidan Yari"?tayi tambayar tana kallonshi
  Jin haka yasa shi ƙara firgita,Cikin lalama ya soma magana"zan faɗa maki gaskiya amma dan Allah Amrishi karki faɗama kowa,kada ki bari kowa yaji,"

"Naji bazan faɗa ma kowa ba,Nayi maka alkawari,"

  "Yawwa,wlh wasu danƙara danƙaran motoci ne suka shigo cikin gidan nan,Ina zaune ina sauraron radiyo ɗina naji hon dinsu,da azama na buɗe masu gate ɗin suka shigo a jere,bayan motocin nan sun tsaya,Hajiya ta fito daga motarta,ɗayar motar kuma wani gabjejen mutun ƙirar samudawa ya fito daga cikinta,Ya zagaya ya buɗe gidan bayan Motar,ina baki labari wani gabjejen ƙaton ƙirar adawa ne ya fito daga cikin Motar ashe su biyu ne,kwatsam!ingaya maki Sai naga ya sanya hannu ya ɗauko wani matashin yaro duk yaci wahalar rayuwa amma wlh baki ganshi ba,Kyakkyawan gaske fari tasss mai kwantacciyar Suma,kamar irin waɗannan indiyawan da nake gani a talabijin,Basamudan nan ya cuccuboshi saman kafadarshi Yaron kamar matacce baya motsi,ko'ina na jikinshi Ya raunata Amma fa yana numfashi don naga yatsun hannunshi na kerma........."
  Tashin hankali!,tunda baba mai gadi ya soma bata Labarin ta kasa kunne tana sauraronshi abun kamar a mafarki take jinshi,
  Sauke ajiyar zuciya baba mai gadi yayi kafin yaci gaba da cewa"kinsan Allah har ƙwalla saida na zubar saboda yaron nan,gwanin ban tausayi,Don Allah ko kin san Meyake damun Yaron nasan kin ganshi......"
  Hannun Amrish na kerma ta miƙa ma baba mai gadi wayar Junaid"duba ka gani shi ne wannan yaron"?
  Kar6ar wayar baba mai gadi yayi yana ƙarewa hoton Junaid kallo,
  "Gaskiya kamar shi wlh," cike da kokwanto Yayi maganar,Can kuma yace"tabbas ma shi ne,Ae daga ganin wannan hoton kafin ya fara shan wahala ne,jiya kuma dana ganshi Ya jigata sosai bawan Allah,dan Allah Amrish in kin shiga ciki,Kice ina yi mashi ya jiki,"
  A ruɗe tace"Baba mai gadi ae baya acikin gidan mu,jiya baka ga sun tafi dashi ba"?
   Girgiza kai Baba mai gadi yayi"basu fita dashi ba,Yana acikin gidan nan!bayan da suka shiga da yaron,ina zaune cike da jimami naga waɗannan Samudawan sun dawo batare dashi ba,kuma akan idona suka ja motarsu da gudu suka bar gidan nan......"yana kai ƙarshen Maganar Amrish ta kar6i wayar daga hannunshi,juyawa tayi da gudu ta nufi cikin gidan
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋





𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠 paid book

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*





Not edited👌



Lokacin da suka sauko downstairs,gaba ɗaya kowa Ya hallara akan dining suna Yin break fast,ƙarasawa Su kayi Bayan sun gaishe da kowannansu,Kowa saiyi Mata Ya jiki Yake yi,Taji daɗin yarda Suka nuna damuwa akanta,kusa da oummansu ta xauna,Jahad ma ta zauna a gefenta,a dai dai Lokacin Azmee ta dawo hannun ɗauke da wasu kayan abincin data ɗauko a kitchen,A saman table ɗin Ta ajiye tray ɗin,Atare Sehrish da Abu suka ɗago ido suna kallonta,fuskarta ta kumbura idanuwanta sunyi jawur kamar wadda tasha kuka,a gefen fuskarta hada gurjewa,fatar wurin ta tattare,Abu batayi mamaki ba,don kuwa ta gane cewa Itace ɗin tazo mata da suffar mage a daren jiya,Ga alamu nan Sun nuna,

Zagayawa tayi wurinsu Sehrish,plate biyu ta ɗauko ta zuzzuba masu abinci,tare da tura masu agabansu,Jahad ta hauci,Sehrish kuwa ƙin cin abincin tayi,Miƙewa Tayi daga saman chair ɗin,

  "Ina zaki je"?omamnsu ce tayi magana ganin ta miƙe,
  Daƙyar ta iya cewa"Kitchen zanje,"ta ƙarasa maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen don ta shirya mashi breakfast ɗinshi,tun da ta fara jin sauƙin jikin nata,

Shaf shaf Ta shirya mashi asaman ƙayataccen tray,Ta wurinsu ta gifta cikin main palour,Upstairs Ta haye lokacin data ƙarasa part ɗin nashi tana ƙoƙarin Shiga,tajiyo muryoyinsu suna magana Shi da Omar,
  "The same fa irin message ɗin da aka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login