Showing 165001 words to 168000 words out of 307403 words

Chapter 56 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

abunda ya faru,Ina nufin irin mutuwar da Junaid yayi,kawai asanar dashi cewa Ya rasu ne ta hanyar rashin lafiya na rana ɗaya..."tun kan yakai ƙarshen maganar Omar yace"idan ya nemi ganin gawarsa fa?Ya zamuyi kenan"?
  Shiru Armstrong yayi can yace"sai ace anyi burying dinta tunda dama ku baku taking time kafin ku rufe deceased" wani kallo Omar yayi mashi yace"kana ganin in ance masa hakan zan yarda ne,alhalin yana araye,sam hakan ma ba mai yuwuwa bane" shiru Armstrong yayi don kuwa bai yi nazari ba kafin ya bada shawarar,
  "To yalla6ai mezai hana kawai a 6oye mashi komai game da mutuwar Junaid ɗin!in yaso koda ya tambayeshi sai asanar dashi cewa,Sgr ya tura shi U.s ne,wurin yin training ɗin aikin soja,"Major ne yayi maganar,
  Murmushin takaici Omar yayi tare da kallonshi yace"Ita kuma jahad ɗin fa?ko itama mun turata U.s ɗinne training?
  Duƙar da kai ƙasa major yayi,Sgr dai bai tanka masu ba shi kaɗai yasan irin tafarfasar da zuciyarshi keyi mashi,
  "Gaskiya akwai gagarumar matasala!yanzu idan muka ce an tura Junaid U.s zai kar6i training ɗin soja,Jahad kuma ya zamuyi da ita?Zata tona mana asiri ne,ta hanyar sambatun da takeyi in har bata dawo hayyacinta ba,koba wannan bama Shi Abban zai iya buƙatar yin waya da jubaid!Dole fa ya nemi layin waɗanda ke a u.s don yaji ya lafiyar ɗanshi,duk kuma in hakan bata samu ba zai ce zaije can ne don ya ganshi"Marshal Omar ne yayi wannan jawabin
  Armstrong yace"Inaso naji abunda Sgr zaice,Saboda nasan baza a rasa mafita a wurinshi ba,"
  Mayar da hankalinsu su kayi akan Sgr wada ya ɗan lumshe idanuwanshi,
  Cikin sanyin murya Omar yace"muna sauraronka ya zamuyi yanzu?Daddy yakusa dawowa,kuma da alama bashi kaɗai zai dawo ba,dukkansu zasu dawo",saboda tsabar tashin hankalin da suke ciki,Ko tunanin abinci ma basuyi,bawai don basu jin yunwa ba,
Slowly ya buɗe idanuwanshi sai lokacin ya soma magana atsanake
   "Duk shawarwarin da kuka bayar ba masu 6ullewa bane,a karshe dai dole mahaifinmu yasan cewa ɗanshi ya mutu,Ba don naso ba,Amma ba yadda zanyi ne,ya zama dole muyi wa mahaifinmu ƙarya a karo na farko don mu ceto rayuwarshi...."dakatawa ya ɗanyi da yin maganar,yana sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗaura da cewa"Shawarata shi ne,Za'a sanar dashi cewa,Anyi kidnapping ɗinsu su duka biyun!saboda babu junaid jahad kuma ta zauce,muddin muka mayar da ita gida asirinmu zai tonu ne,kuma mahaifin yarinyar yanzu yana cikin farin cikin ganin mahaifiyarsu,idan har ya dawo ya samu ƴarshi a cikin wannan yanayin yaya kuke tunanin zaiji aranshi?ga kuma babban rashin da mukayi na Junaid!that's the reason why ya zama dole a killace Jahad acikin asibitin nan na tsawon wasu kwanaki har asamu ta dawo cikin hayyacinta,hikimar yin hakan shi ne na farko idan daddy yaji cewa anyi kidnapping ɗinsu,tabbas hankalinshi zai tashi sosai,Amma zai sa ran bayyanar junaid a koda yaushe,kuma zamu sanar dashi cewa Junaid zai dawo Zamuyi ƙoƙari wurin ganin mun ku6utar dashi hakan zaisa Ya ɗan ji sauƙi aranshi duk da zai shiga matsananciyar damuwa,mu kuma zamuyi ƙoƙari wurin ganin mun shawo kanshi,Abu na biyu shi ne bayan wasu ƴan kwanaki idan Allah yasa Jahad ta dawo cikin hayyacinta,Zamu lallasheta ne nasan zata fahimce mu,Zamu fara sakinta ta koma gida a matsayin su kidnappers ɗin suka saketa,Wannan zai ƙara kwantarwa Abbanmu hankali saboda zaisa Ma ranshi cewa shima junaid zasu sako shi,Ta wani 6angaren Abusufyan ma zaiji sauƙi aranshi in yaga dawowar Jahad,may be ma kafin ya dawo daga kano zata koma,so daganan a hankali a hankali zamu cigaba da ƙoƙarin fahimtar da Daddy,koda zaisan cewa junaid ya mutu sai daga baya lokacin komai ya wuce kamar next 1 to 2 month haka,Sae asamu babban malami ya zaunar dashi yayi mashi nasiha sannan ya sanar dashi ainihin abunda ya faru,radaɗin da zaiji aranshi bazai kai raɗaɗin da zaiji ba a yanzu idan aka sanar dashi..."yana kai ƙarshen maganar shi,ya rufe idanuwanshi yayin da zuciyarshi keta harbawa,
  "Good Idea"!acewar Armstrong,
Major ya ɗaura da cewa"Yanzu yakamata a fara kawar da duk wani abu wanda zaisa Labarin hatsarin daya faru yaje masu,dama an kori ƴan jarida daga wurin,yanzu haka akwai sojojin dake kewaye da wurin an rufe shi,basu bari kowa ya ɗauki video ko hoton abunda ya faru ba,Zamusa su tsananta bincike akan mutanen dake a wurin dama kuma ba wasu mutane da yawa ne su kai witnessing incident din ba,ko masu wuce wa a mota babu sosae,dakuma mai siyar da ice cream ɗin nan,Hatta wayarshi za'a canza mashi saboda gudun kar ace ya dauki rahoto in ma ta kama asa ya canza wuri ne sai ayi hakan,Zamu toshe duk wata hanya da zaisa labarin mutuwar Junaid yaje kunnan mutanen gidan in sha Allah,"
Jinjina kai Omar yayi tare da cewa"hakan yayi,Yanzu yakamata a hanzarta zuwa yi mashi jana'iza,Yamu yamu zamu halarta wurin yi mashi sallah,mu binne tokarsa awurin,bayan an kammala sai a kawar da ƙarahunan Motar,A shafe duk wani abu da zai nuna cewa Anyi hatsarin mota a wurin,"cikin karyayyar murya ya yi maganar.

Sun jima suna tattaunawa akan yadda zasu tafiyar da komai,daga bisani wuraren karfe 2,Suka ɗunguma gaba dayansu zuwa wurin da incident ɗin ya afku,Sgr kamar yayi hauka lokacin daya yi arba da motar Junaid,Yaji mutuwar nan har cikin ranshi,daƙyar suka samu kowa ya dan daidaita natsuwarshi,Alwala su kayi gaba ɗayansu banda Armstrong da wasu da suka kasance ba musulmai ba,Anan sukayi mashi Sallah tare da burying ɗin tokarsa A gefen wata bishiya,bayan sun gama jana'izar,sojoji suka kawar da motarshi daga wurin,jikin kowa fa yayi mugun sanyi,Don suna kammala sallar jana'ixar Sgr ya zukunna gefen ƙabarin Junaid,tare da kwantar da kanshi asaman ƙabarin,Addu'o'e ya shiga jerowa abakinshi yana tottofa mashi,a ƙarshe yace"Allah ya jikanka Junaid,bazan ta6a yafewa kaina ba,idan har ban ɗauki fansa akan irin kisan wulakancin da akayi maka ba,Na ɗaurawa kaina alhakin mutuwarka,Saboda laifina ne Junaid da ban baka kariya ba,na tabka babban kuskuren da har duniya ta naɗe bazan ta6a mantawa dashi ba,"
   Kasa ɗagowa yayi daga kan ƙabarinsa,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*



   Kasa ɗagowa yayi daga kan ƙabarinsa,
  Marshal Omar ne ya ɗaura da cewa"In sha Allah junaid na aljanna,muna yi mashi kyakkyawan fata,Allah yasa ƙarshen wahalarshi kenan,"gaba daya basu ji daɗin irin yadda mutuwar junaid ta kasance ba,kamar wani mara gata,babu mahaifinshi akusa babu ƴan uwanshi,
  Ruƙo hannun Sgr major yayi,tare da janyoshi,jikinshi duk ya saki,daƙyar ya iya mikewa ya tsayar da kanshi akan ƙafafunshi,
  Sojojin dake kewaye da wurin sunyi su 50,Layi sukayi wani na bin wani,kowa yazo wurin ƙabarinsa sai ya tsaya ya tottafa mashi addu'a kafin ya wuce,Na bayan shi yazo shima yayi mashi addu'a a haka har suka kammala,ba tare da mutane sun samu damar tsayawa ganin abunda ke faruwa ba,dama kuma hanyar sam ba mutane sosae.
   Basu bar ƙabarin junaid a fili ba,saboda gudun kada mutane su dinga tattake wurin batare da saninsu ba,ko su zauna abakin bishiyar,waya suka sa suka kewaye bishiyar,

Sun jima a awurin cike da jimamin mutuwar junaid,kafin wani lokaci suka shige motocinsu suka tafi ba don sunso ba,Kuma duk da haka sai da Sgr ya sanya sojoji guda biyu suka tsaya a wurin,batare da uniform ajikinsu ba,

    *RIJF BABY JUNAID*

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 5:30 na marece,
Slowly motocinsu suka shiga cikin gidan,Bayan sunyi parking ɗinsu Major ya buɗe masu mota,don atare suka zauna shi da Sgr a motar Omar,kowa jiki babu ƙwari haka suka fito daga cikin Motar,kaitsaye suka nufi ƙopar shiga falon,

A lokacin hosana na zaune saman Sofa,duk ta takure kanta,tun da tafarka daga bacci take ta faman yin sintiri acikin gidan tana jiran dawowar Omar don ta faɗa mashi abunda haroon yayi mata,

Jin motsin shigowarsu yasa tayi saurin miƙewa jiki na rawa ta tunkareshi zata rungumeshi,
Da hannu yayi mata alamar karta matso kusa dashi,fuskarshi babu annuri,har cikin ranta bata ji daɗin abunda yayi mata ba,har gaishe dasu tayi amma babu wanda ya kulata,acikinsu,
  Upstairs suka wuce atare,kowa ya nufi part ɗinsa,komawa hosana tayi saman sofa ɗin tana kuka,abun ya ƙona mata rai,Yadda Omar ya dakatar da ita don karta ta6a shi,
  Faɗawa yayi saman gadonshi yayin da idanuwanshi ke fuskantar Ceiling,Fuskar Junaid ya dinga ganin tana yi mashi gizau,ji yake tamkar abunda ya faru mafarkine ba gaskiya ba,saboda wani sashe na zuciyarshi na raya mashi cewa Junaid yana raye bai mutu ba,Yayin da wani sashen na zuciyar tashi ke gasgata mashi mutuwar junaid,runtse idanuwanshi yayi Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi daurewa kawai yake yi,ya jima a haka idonshi na kallon sama,kafin daga bisani ya miƙe tare da faɗawa toilet bayan ya rage kayan jikinshi,

Kwance yayi tsulundum acikin jacuzzi (kwamin wanka)wanda ke kewaye da glass,da niyyar yin wanka ya shiga toilet ɗin,Amma sai kasala ta baibayeshi ko yatsan shi ya gaza ɗagawa,abubuwa sunyi mashi yawa,tunda yake a rayuwarshi bai ta6a fuskantar mummunar rana irin wannan ba,da ace mutuwa hutu ce agareshi da ba abunda zai hana ya roƙi Allah akan ya ɗauki ranshi ya huta,Yaci alwashin saiya ga bayan waɗanda suka kashe junaid,Alƙawari ne ya ɗaukarwa kanshi,Ko bacci bazai ƙara yi ba,in har bai ɗaukarwa junaid FANSA ba,kamar yadda Sgr yaci Alwashin ɗaukar fansa haka shima Omar ya ɗauka,

Kasa jurewa yayi saboda kukan da hosana ke raira mashi ta la6e a ƙopar dakinshi batasan halin da yake ciki ba,
  "Hosana,"ya ambaci sunanta,muryarshi a kasalance,
  Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"
  "Zonan,"
Hannu tasa ta tura ƙopar tare da shigewa ciki,Kwance ta same shi saman gadonshi,Ya baje daga shi sai short,kallo guda zakayiwa fuskarshi ka gane cewa yana acikin matsanancin tashin hankali,
  har Saman gadon hosana ta hau ta zauna tana kallonshi,lokaci guda ta dakata da yin kukan nata,Ganin dry tears asaman fuskarshi,nan fa hankalinta ya tashi sosai,
  "Ya omar,hawaye akan fuskarka?meke damunka ya Omar,Ban ta6a ganin hawayenka ba,Sae yau,"
  A hankali ya bude idanuwanshi da sukayi jawur dasu yana kallonta yace"Hosana,ki taimaka mun kaina kamar zai fashe,Ina cikin matsananciyar damuwa,Zuciyata raɗaɗi take yi mun,pray for me hosana kona samu sauƙi acikin zuciyata,
  Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,hannayenta ta sanya tana kokarin janyo shi hakan yasa ya dan matso daura kanshi tayi saman laps ɗinta,Addu'o'i ta shiga karantowa tana tottafa mashi asaman fuskarshi,shafa sumar kanshi ta shiga yi,tana cewa"Ya Allah ga bawanka nan,kai kaɗai kasan meke damunshi,Ya Allah ka yaye mashi damuwarshi,Ka sanyaya mashi zuciyarshi,Alfarmar Annabi Muhammadu (S.A.W),
  Ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai ya gyara kwanciyarshi sama sama bacci ya fara ƙoƙarin daukarshi,
Yana jiyo muryarta tana tambayarshi Ko zaici abinci ta kawo mashi,
   Daƙyar ya iya amsa mata da cewa"A'a hosana,bana iya cin komai yanzu,"
  "Shikenan ya Omar ɗina,kayi baccinka kawai,zanci gaba da yi maka addu'a,har ka farka,"
   Shafa sumar kanshi taci gaba da yi,tamkar jinjiri haka ta dinga treating ɗinsa har bacci yayi awon gaba dashi,Yau hosana tayi mashi abunda bai ta6a tsammani ba,Ta bashi kyakkyawar kulawa kamar ba wannan mai ta6in hankalin ba,wani iko na Allah ta so sanar dashi damuwarta,amma tunda ta gane cewa baya a hayyacinshi,Sae kawai ta fasa sanar dashi.

*Tashin Hankali!"

Jin dirar motoci acikin gidan yasa shi yin firgit ya farka,tare da yunƙurawa ya miƙe zaune,Hosana ya gani kwance tana bacci,asaman gadon ya ɗauketa,
  Jiki na rawa ya saukko daga saman gadon ya samu jallabiya ya zura ma jikinshi ya bude ƙopar dakinshi da sauri ya nufi downstairs,Tunkan ya ƙarasa ya jiyo Muryar Abbansu yana ƙwalama Junaid kira,ko sallama baiyi ba,Burinshi kawai yayi tozali da junaid,
  "Hasbunallahu wani'e mal wakil"ya furta hakan tamkar zai fashe da kuka,
  Yana cikin wannan yanayin sai ga Sgr shima ya fito daga part ɗinsa,jikinshi sanye da jallabiya shima,kallon juna suka yi kowa fuskarshi ayamutse take,
   "Daga shigowarshi ko sallama baiyi ba sunan junaid kawai ya ambata,yanzu yaya zamuyi dashi'?omar ne yayi maganar tare da kallon Sgr dake tsaye a gefenshi,
   "Yanzu ya dawo yana buƙatar ya huta,yakamata muyi ƙoƙari wurin ganin mun daidaita natsuwarmu,if not za'a samu matsala ne,"

Shigowa cikin falon suka karasa yi,Abbansu ne sai Mommynsu,tare dasu twins,fawan gaba ɗaya matasan gidan sun dawo,hada kanal yousouf su irfan da sauransu,Banda gwaggon katsina suma sun shirya dawowa tare dasu Ammi,zasu zo daga baya,

Agajiye suke kowa ya samu wuri saman Sofa ya zauna,Abba kuwa jiki na rawa ya wuce upstairs,su Sgr najin takun takalminshi hankalinsu ya ƙara tashi,Yana tafiya yana ƙwalawa junaid kira,
  "Junaid!Junaid!where are you?Ur dad is back,Nayi missing ɗinka sosai...."
  
Bai ƙarasa maganar ba,ganinsu Omar atsaye,cirko cirko,ƙaƙaro murmushi suka yi gaba dayansu suka tunkareshi,Sgr ne ya fara yin hugging ɗinshi,Daddy I really missed you,Ya gajiyar tafiya?ya ƙarasa maganar tare da ɗagowa daga jikinshi,Bai amsa mashi gaisuwar tashi ba,yace"Yaushe ka dawo Abuja?ko kun dawo ne'?
   "A'a daddy,Wani uziri ne ya kawo ni,Amma zan koma kano ɗinne,"wani kallo da yaga Abbansu na binshi dashi yasa ya ɗan sha jinin jikinshi,
  "Abba sannu da dawowa,"Omar ne yayi maganar,wurga idanuwanshi yayi akan fuskar Omar,aɗan ruɗe yace"kunyi rashin lafiya ne?meke faruwa ne?naga fuskokinku duk sun kumbura,fuskar Rafayet tayi jawur da ita,kaima haka...."
  Da sauri Omar yace"Am...Abba..I know u are tired,kana buƙatar hutu,yakamata muje bedroom ɗin ka Inyi maka tausa,"
  Harara Abban ya ɗan watsa mashi tare da cewa"a ƙule nake dakai Omar,ina ta nemanka jiya,ka tashi ka kashe mun waya hmmmm..."yana kai ƙarshen maganar ya soma ƙoƙarin wuce wa ciki,Saboda tsabar ruɗu Sgr baisan sa'adda ya tarboshi da hannunshi,Zuba ma hannun nashi ido Abbansu yayi,fuskarshi ɗauke da mamaki yace"Rafayet,lafiyarka kuwa?cikina fa ka tarbe,"
  Zame hannunshi yayi tare da ɗan sosa ƙeyarshi yace"Am sorry Daddy,pls u need a rest,mu sauka down ka huta mana,ka kwaso gajiya,inaso na baka abinci kaci ka huta,Omar zaiyi maka massage ka ɗan ji daɗin jikinka,
  Cike da mamaki Abbansu ke kallonshi,"Rafayet!yau kaine da kanka kake zancen zaka bani abinci a baki na naci?Omar kuma zai yi mun tausa,sae kace wani ƙaramin yaro,"gyaɗa kanshi yayi tare da cewa"Naji toh,Amma saina fara zuwa ɗakin Junaid,idan nadawo sai mu je ɗakin nawa,"yana kai ƙarshen maganar ya wuce tare da nufar ɗakin Junaid yana ƙwala masa kira,
  Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,A hankali Abba ya tura ƙopar ɗakin junaid ya shiga daga ciki,Wayaam yaga babu kowa aciki,Bai kawo komai aransa ba,saboda ƙarar saukar ruwa dayaji a toilet,hakan yasa shi tunanin ko ya shiga wanka ne,ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya fito daga ɗakin,da niyar idan ya huta zai dawo wurinshi,don yau atare yake son su kwana dashi,

Koda suka yi arba da Abbansu yana nufosu sai kowannansu ya shiga ƴan kame kame,fargabarsu kada ace zai tambayesu ina Junaid ya ke,. 
   Tunkan ya ƙaraso wurinsu suka ji yace"Ashe ya shiga wanka ne,idan ya fito daga wankan pls ku sanar dashi cewa nadawo kuma inason ganinshi,a bedroom ɗina,"
  Atare suka haɗa baki wurin cewa"Toh Abba"

Saukowa down sukayi atare da abban yana gaba suna a bayanshi,Sae faman sauke ajiyar zuciya suke yi,

Lokacin da suka sauko down,Su kanal Yousouf na ganinsu kowa ya miƙe fuskar nan ɗauke da farin ciki,Yayin da su kuma kowannansu ya dabarbarce,
Daƙyar suke gaisawa da ƴan uwan nasu,kowa ya lura da yanayinsu shiru kawai su kayi,Su fawan sai tambayar Junaid suke yi,Yana ina?basu ganshi ba,amsa daya suke basu ta yana a cikin toilet yana wanka,Duk wanda yaje ɗakin Junaid yaji sautin saukar ruwa daga cikin toilet,sai yayi tunanin cewa wanka yake yi,Ashe fanfo ne Aka bari a kunne ba'a kashe ba,
   Daƙyar suka samu kowa ya haƙura da ganin junaid,Omar yace su wuce ɗakunansu kowa yaje ya huta,an kwaso gajiya,
  "Nifa ban yarda dasu babban yaya ba,Shi da ya Omar akwai wani abu da suke 6oye mana Allah,"Acewar Jahan,
A yayin da suke shiga bedroom ɗinsu,
  Ayaan yace"nikaina na lura da hakan,musamman faces ɗinsu,kamar sunsha kuka Allah,Gaskiya hankalina bazai kwanta ba,sai naga junaid,ni ban yarda wanka yake yi acikin toilet ba,"
  Jahan yace"mu bari mu huta,Zuwa dare sai muje ɗakin nashi,nasan lokacin idan ma wankan ne ya gama,"
  Ƙarasa shiga cikin ɗakin sukayi,kowa ya shiga rage kayan jikinshi,Jahan ne ya fara shiga waka,Ayaan ya zauna gefen gadon yana jiranshi ya fito shima ya shiga wankan,
   A can falo kuwa,Mommynsu ta tsare Sgr da Omar,Tasa su gaba tayi tana binsu da kallo one by one,dama bakowa Sgr yafi ji ba fa ce Mommynsu,tana da wuyar sha'ani,
  "Mommy,"Sgr ne ya ambaci sunanta,
bata amsa mashi sunan nata daya kira ba,sai cewa tayi"you didn't answer my question,It seems like you are hidding something for us!Rafayet where is junaid!kada kuyi mun ƙarya nasan ba halinku ba ne,just ku faɗamun Gaskiyar abunda ya faru,"
  Murya na rawa Omar yace“Am..mommy,Junaid fa yana a toilet yana wanka zai fito ne...m"daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da take yi mashi,kallon tuhuma,kallon ban yarda dakai ba
"Wai taya za ku ce mun junaid yana wanka?Nifa ba ƙaramar yarinya bace,balle kuce zakuyi mun wayau,tun daga kan fuskarku na gane cewa akwai wani abu daya faru dashi...."
  Saussauta muryarta tayi,sannan taci gaba da magana"pls idan wani abu ne ya faru da Romeo ɗina ku sanar dani,i will accept it,"yadda tayi maganar yasa su kaji jikinsu ya ƙara mutuwa,
  "Am listening to u guys,ku faɗamun meya faru dashi ya mutu ko"?
  Gabansu ne ya faɗi rass!da sauri Sgr ya ruƙo hannunta muryarshi na kerma yace"Mommy dan Allah kiyi haƙuri,ki rufa mana asiri,I will explain to u mu shiga daga cikin bedroom ɗin..."
  "Rafayet,meyasa zaka sanar da ita"?Omar ne yayi maganar fuskarshi a yamutse,
  "To ya kakeso nayi Omar,Mommy bazata ta6a yarda ba,kwara kawai mu faɗa mata gaskiyar abunda ya faru,Ka wuce wurin Daddy,ni zanji da Mommy,'
  Ya ƙarasa maganar tare da jan hannunta,Suka wuce upstairs bedroom ɗinshi,
  Ajiyar zuciya Omar ya sauke,Ya jima atsaye yana tunanin Yadda zasu ƙare da Abbansu,tsoranshi kada farat ɗaya zuciyarshi ta buga idan yaji cewa Anyi garkuwa da junaid kamar yadda suka tsara,
  "Omar,lafiya kuwa,"firgit ya ɗanyi tare da kai idanuwanshi wurinta,Azmee ta nufo shi,Ganinshi a tsaye kamar akwai damuwa atattare dashi,
  Dakyar ya ƙaƙaro murmushin yaƙe yace"bakomai,"
    "Omar,dama inaso na tambayeka ne,Wai ina junaid ne?tun jiya da suka fita shi da jahad shiru har yau basu dawo ba,nashiga damuwa sosai akan rashin ganinsu,har cewa yayi idan suka je shan ice cream zaiyi min tsaraba," ta ƙarasa maganar tana kallonshi,
  "Aunty Azmee,bazan iya 6oye maki ba,Junaid da jahad anyi kidnapping ɗinsu...."jin wannan maganar yasa Azmee ta dafe ƙirjinta da ƙarfi,idanuwanta suka firfito waje,hankalinta yayi mugun tashi,
  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"kusan sau biyar tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login