Showing 99001 words to 102000 words out of 307403 words

Chapter 34 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

dae ba wani abu ya faru ba,"sehrish tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,
  "Kodai naje najiyo mana abunda ke faruwa cikin gidan"?Hosanar tayi tambayar tana kallonsu,
  Jahad tace"A'a,babu ruwanki,tunda ba kiran mu akayi ba,"

Cigaba da ɗaukar hotuna sukayi acikin ɗakin,Shigowa junaid yayi fuskar nan tashi ɗauke da murmushi,Suna ganinshi suka haɗa baki wurin cewa"Baby Junaid!"
  Ɗaure fuskarshi yayi tare da ɗan turo bakinshi ashagwa6e yace"Ni ku daina Kirana da sunan baby,In ba haka ba,ran kowa zai 6aci a wurin nan,"ya ƙarasa maganar tare da aza idanunshi kan Sehrish dake tsaye tasha Kwalliya abunta,sakin baki yayi galala yana kallonta,a ruɗe ya ambaci sunanta"Reesh,"
  Murmushi Sehrish ta sakar mashi,tare da yi mashi fari da ido,sannan tace"Na'am,Junaid ya kaga wankan nawa,"?
   daƙyar ya iya cewa"reesh,yanzu kina sane aka ɗaura maki aure da babban yayan mu bayan kinsan da cewar Ina sonki"?
  Gabanta ne ya faɗi rassss!!Ba ita ba hatta su Jahad da hosana a ruɗe suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma,da Babban yayan mu!"
  Shi kanshi junaid ɗin sae da gabanshi ya faɗi,tunani ya shiga yi anya Sehrish tasan da auren kuwa?Yanayin yadda ya ga ta razana ya tabbatar mashi da cewar batasan da zancen auren ba!acikin ranshi yace"meke faruwa ne?Mommy batasan da auren babban yaya ba,kuma itama rishi dasu jahad basu san da auren ba!Abba ya 6oye masu kenan!aikuwa saina tona masu asiri kowa yaji,dama ya 6ata mun raina yau,duk irin amanar dake tsakanina da Abba ya rasa dame zai sakamun sai da wannan,"
  "Junaid dan Allah kayi mana bayani dalla dalla yadda zamu fahimta!"acewar jahad,
   Kallon fuskar sehrish yayi ganin ta zuba mashi ido tana kallonshi,kalmar daya furta masu ce take ta maimaitawa acikin zuciyarta
   "nidai baza aji mutuwar sarki abakina ba,Abba yace kar na faɗama kowa cewa an ɗaura aurensu,"yayi maganar tare da sanya hannu ya toshe bakinshi,
  Hankali atashe suka shiga kallon juna atsakaninsu,
  "Don Allah junaid ka faɗamun auren wa aka ɗaura"? muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,
   "Sehrish kiyi haƙuri bazan iya sanar dake ba,Amma idan kina son samun ƙarin bayani,kije wurin Uncle ki tambayeshi,

  Jiki na rawa sehrish ta kama hanyar fita da sauri Hosana tabi bayanta,suka fita atare,
    Matsawa yayi kusa da jahad,tare da ruƙo hannayenta yace"Jahad!Albishirinki"?
"Goro,"ta bashi amsa fuskarta ɗauke da murmushi,
"Fari ko Ja"? Wurga ido ta ɗan yi sama kafin tace"Fari,"
    "Uncle ya bani aurenki,"jin wannan maganar yasa hankalin jahad ya tashi,lokaci guda ta ɗaure fuskarta,tare da fisge hannunta daga cikin nashi,
   Gabansa ne ya faɗi,ganin yadda ta canza mashi lokaci guda tsoranshi kada ace jahad ba son shi take yi ba,
  "Jahad baki sona?bakison ki aure ni ko"?
  Shiru jahad tayi tana ƙare mashi kallo daga ƙasa har sama,
   Tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,fargabarshi wata amsa jahad zata bashi,in har bata amince ba shikenan zai rasa damar da yake da ita,na mayar da gurbin rishi ɗinsa daya rasa,
   Motsi ta soma yi da la66anta daƙyar ta iya cewa"Junaid!dagaske kake mun ko wasa?tell me the truth pls,i know u are just teasing me,'
    Girgiza kai yayi tare da cewa"Am serious jahad,Bazan 6oye maki ba,da farko sehrish nake so sosai,in har ba zaki manta ba,lokacin dana ɗauko ki a school matsayin sehrish,idan zaki iya tunawa sunanta nake ambata a matsayin ke,nayi tunanin itace shiya sanya na sanar dake abunda ke acikin zuciyata,Amma yau batare da sani na ba,A masallaci naji sanarwar ɗaurin Auren Sehrish da babban yayan mu,har sai da na kusa zaucewa ƙarshe a masallacin na yanke jiki na fa....."
  A razane jahad ta katse shi da cewa"Wai dagaske an ɗaura auren Sehrish!kuma da babban yayan mu!?
   ɗaga mata kai yayi alamar eh,kafin ya ɗaura da cewa"Ni kaina bansan da zancen auren nasu ba sae a masallaci dana ji ana sanarwar,abun ba ƙaramin ta6a zuciyata yayi ba,na shaqu sosai da sehrish,
  Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,jin zancen auren Sehrish da Sgr,ta rasa gane a wane yanayi take ciki,farin ciki ko kuwa akasin hakan!babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda aka 6oye masu ba'a sanar dasu ba,Ko meyasa?Yanzu shikenan an ɗaura auren rishi ɗinsu?ta zama married woman?
   Runtse idanuwanta tayi tare da sanya hannu ɗaya ta dafe gefen goshinta,a hankali ta furta"Ya salaam,"
   "Jahad,inason naji amsar tambayar da nayi maki"?muryarshi a kasalance yayi maganar,don ya qagara yaji amsar da zata bashi,
   A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar junaid,tana kallonshi tace"junaid Daddy da kanshi ya baka aure na?kuma ya tabbatar maka da cewar bada wasa yake maka ba"?
   Bubbuga ƙafafunshi yayi saboda hasalar da yayi,a ƙule yace"eh mana,shi da kanshi ya mallaka mun ke agaban kowa da kowa,yaji tausayina ne saboda halin dana shiga,"
.....fuskarta aɗaure tace"Meyasa daddy zai yi mun haka?nace mashi ina sonka ne?kuma ya rasa ma wazai ba aure na sai kai?junaid kayi mun ƙanƙanta!Ni bazan iya zaman aure dakai ba,nafison namijin daya mallaki hankalinshi ba shagwa6a66e ba sangartacce irinka...."tun kafin takai ƙarshen maganarta,hawaye suka fara wanke mashi fuskarshi,cikin shessheƙar kuka yace"au haka ma zaki ce jahad?shikenan babu komai,"da sauri junaid ya juya tare da nufar kopar ɗakin nasu gwanin ban tausayi,
  Yana ƙoƙarin kai hannu ya buɗe ƙopar,da gudu jahad ta faɗa bayanshi tare da rungumoshi sosai tana dariya,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya junaid ya sauke,kwantar da kanta tayi asaman bayanshi,magana ta soma yi mashi anatse"junaid,ko da yake yanzu na canza maka suna,Ka tashi daga junaid ka koma Babyn jahad,Ina fata hakan yayi maka,"
  Tafin hannayenshi ya sanya tare da share hawayenshi,wani irin sanyi ne ya ratsa cikin zuciyarshi,Calmly ya ambaci sunanta"Jahad,Kin amince da aure na?a yadda nake?zaki iya haƙuri dani?ki zauna dani amatsayin Mijin ki uban ƴa'ƴanki kuma"?
  Lumshe idanunta tayi yayin da hancinta ke shinshinar ƙamshin turaren jikinshi,
   "I accept ur love junaid,I love u so much,nayi farin ciki sosai da daddy ya baka aurena,a ashirye nake dana baka kulawar daya dace junaid,"
  Saboda tsabar farin ciki bakin junaid yaƙi rufuwa,hannunta ya ruƙo tare da zagayo da ita,ta dawo gabanshi suna facing ɗin junansu,zuba ma juna ido sukayi na wani lokaci,batare da sun sha Wahala ba,Sun amince ma junansu kowa ya samu abunda zuciyarshi ke muradi,janyota yayi ta faɗa asaman ƙirjinshi,zagayo da hannayenshi yayi ta bayanta,sosai ya rungumeta,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,lokaci guda suka kamu da tsananin son kasancewa da junansu,
 

*Boss Bature*

  ❤🤍❤
 

"Rafayet!Ka 6ata mun rai!ka ƙuntatamun!Amma kai ko ajikin ka?meyasa zakayi mun haka"?Abbansu ne yayi maganar a yayin da yake tsaye acikin bedroom ɗin Sgr,Idanuwanshi sun cika tab da hawaye,
  "Abba,don me zaka tashi hankalin ka akan auren nan!You know the reason why I married her,Saboda inaso taci gaba dayin aiki a ƙarƙashina,ni ban shirya yin rayuwar aure ba,Babu wannan a tsari na," yana magana huci na fita a bakinshi,saboda tsabar 6acin ran da ya ke ciki,ji yake gaba ɗaya sun takura rayuwarshi,ba don komai ba sai don saboda sun nemi Alfarmar ya taimaka yayi koda hoto ɗaya ne shi da Sehrish don su ajiye na tarihi,
  Gyaɗa kai Abbansu yayi tare da cewa"A haka kakeso kai ayi maka biyayya,bayan Ni ban isa na sanya ka abu kayi mun ba,narasa gane kai wani irin mutunne!ka ce yarinya bazata zauna a part ɗinka ba!kuma ba zaka ɗauki hoto ba atare da ita,nasan meyasa kayi hakan!saboda kada hotonku ya shiga duniya a dinga nunata a matsayin matarka!saboda kai a wurinka wannan ƙasƙancine aganta a matsayin matarka,saboda ka fi ƙarfin ta ko"?
  Yayi maganar ranshi a 6ace,Sgr kuwa ko ajikinshi,yana daga tsaye agaban dressing mirror ɗinshi ya juya ma Abbansu baya,har lokacin bai canza kayan jikinshi ba,babu wanda baizo yayi mashi magana ba akan ya amince da buƙatar mahaifinsu amma yaƙi yarda,hatta Ishaq da Abbas sunyi sunyi har sun gaji sun ƙyale shi,haka Marshal Omar sunyi barambaram dashi,saboda ya 6ata masu rai,
  "Zan tafi na bar maka ɗakin ka,Amma inaso na ƙara tunasar dakai cewa Abusufyan ya baka tsawon wata ɗaya kacal akan ka canza ra'ayinka game da auren yarjejeniyar nan,Zaka iya soke shi in har kana so acikin ƴan kwanakin nan,Amma idan har ka bari wata ɗaya ya wuce baka canza ra'ayin ka ba,duk abunda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa ka kuka da kanka!kuma babu ruwana Na zame hannu na aciki,
  A fusace Sgr ya juyo tare da kallon Abban nasu yace"bazan ta6a canza ra'ayi na ba akan hakan!Idan ma yana tunanin hakan to ya daina!Bana buƙatar wani time nayin tunani!wata uku na cika zan sallame ta ne!
  Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,ta wutsiyar idonshi ya hango mutun atsaye,a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,
  Sehrish ce atsaye tana kallonsu,gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa,domin kuwa taji duk abunda suka ce kaf acikin kunnanta,Jikinta har kerma yakeyi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa akan fuskarta,
  Jin shessheƙar kukanta yasa Sgr Juyawa tare dakai idanunshi wurin da take tsaye a ƙopar ɗakin nashi,tun daga ƙasa har sama yabita da kallo,
  A hankali Abbansu ya ambaci sunanta"Sehrish!"
  Juyawa tayi da gudun gaske tabar ƙopar ɗakin nashi,gaba ɗaya tabar part ɗin nashi,saukkowa tayi downstairs,Su fawan ne tsaitsaye acikin babban falon,koda suka ji shessheƙar kukanta sae hankalinsu ya koma akanta,kowa ya shiga tambayarta lafiya,
  Bata tsaya sauraronsu ba,da gudu ta wuce bedroom ɗinsu,tana shiga ciki ta samu junaid da jahad azaune gefen gadonsu suna shan soyayya,jin shigowarta yasa suka mike tsaye hankali atashe suka shiga tambayarta Lafiya,
  Bata basu amsa ba,kai tsaye ta nufi toilet ta buɗe ƙopar ta shige ciki,da ƙarfi ta datse ƙopar,sannan ta tsugunna ƙasa tana kuka tamkar ranta zai fita,

Gaba ɗaya Jahad da Junaid suka nufi ƙopar,Suna kwankwasawa suna kiran sunanta"Sehrish!Sehrish!dan Allah Rishi ki buɗe mana kopa!
  Turo kopar ɗakin nasu akayi,Abusufyan ne tare da hajiya azeema suka shigo ciki hankalinsu atashe,basu jima da shigowa ba,sai ga Abbansu junaid,dama tunda yaga ta watsa aguje tana kuka ya biyo bayanta,
  A bakin kopar shiga toilet ɗin suka tsaitsaya cirko cirko
   "Dama nasan abunda zai biyo baya kenan!"acewar hajiya azeema,
  Abusufyan yace"Ni bansan waya faɗa mata ba,Naso ace ni na fara sanar da ita,"
  Fuskar Abba a yamutse yace"wlh bansan da ita ba!Yanzun nan fa naganta a ɗakin Rafayet,muna cikin magana dashi akan zancen auren nasu,kawai naji shessheƙar kukanta,ashe duk taji abunda muka ce,"
   Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,musamman Abusufyan har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata,
   Ƙoƙarin lallashinta suka shiga yi amma ina,Sehrish taƙi sauraron kowa kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita,tana jin muryoyinsu a waje sai faman yi mata magiya sukeyi akan ta buɗe masu ƙopar,
   Junaid duk yabi ya ruɗe sam baisan cewa abun zai ta6a zuciyarta ba har haka,Ita kanta jahad ba ƙaramin tausayin Sehrish taji ba,kowa sai da yasha jinin jikinshi,babban abunda suke ji ma tsoro kada ta illata kanta,

Bakomai ne ya ƙona mata rai ba,Fa ce abunda kunnuwanta suka jiyo mata,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,komai ya fita aranta,tabbas tana son Sgr sosai har cikin ranta,kuma babu abunda ya canza acikin zuciyarta,tayi farin ciki mara misaltuwa na kasancewarta matarshi,wannan babbar kyauta ce agareta,sae dai kash bataso ya aureta batare da yana sonta ba!Sam bata ta6a ra'ayin hakan ba,tafi son ta auri wanda take so kuma yake sonta,bawai wanda takeso ba,Shi baya sonta,bugu da ƙari kuma ya aureta ne don taci gaba da aiki a ƙarkashinshi na wata uku kacal!
    "Idan ba damuwa inaso ku ɗan bani wuri in shawo kanta,"hajiya azeema ce tayi maganar,
   Abusufyan yace"kina ganin zaki iya shawo kanta kuwa?
  "Ku je kawai,Ni nasan yadda zanyi da ita,ku ɗan bamu wuri,"
  Kama hanya sukayi gaba ɗayansu hadasu jahad suka bata wuri,kamar yadda ta bukaci su fita daga dakin,
  Zuƙunnawa hajiya azeema tayi abakin ƙopar toilet ɗin,Saboda ranta ya bata cewar sehrish tana zuƙunne a ƙasa,ta gane hakan ne ta hanyar sautin kukan nata,
  Cikin lallami ta ambaci sunanta"Sehrish,"
  Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"
  "Inason magana dake!dan Allah ki bani haɗin kai,kada ki bani kunya,inaso kizo ki buɗe mun ƙopar nan!,"
   Miƙewa sehrish tayi,jikinta sai faman kerma yake yi,daƙyar ta iya sanya hannu ta buɗe kopar toilet ɗin,
  Sauke ajiyar zuciya hajiya azeema tayi tare da mikewa tsaye tana kallonta,fuskar nan tayi suntum da ita,gaja gaja da hawaye,idanun sun kumbura,janbakin da ta shafa duk ya 6ata mata fuskarta,mascara ɗin da aka shafa mata asaman eye lashes ɗinta,duk ya jike sharkaf da hawayenta ya 6ata fuskar da baƙin,kayan jikinta ne kawai basu 6aci ba,
  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita daga gefen gadon nasu,itama ta zauna suna fuskantar juna,
"Haba amaryar babban yaya,kuka bana ki bane,Farin ciki ya kamata na gani akan fuskarki,"cike da zolaya hajiya azeema tayi mata maganar hada jan kumatunta,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shesshekar kuka tace"Am...amma..Aunty azeema..meyasa za'ayi mun haka?saboda me za'a ɗaura mun aure tare da babban yayanmu batare da an sanar dani ba?Nasan cewa sun isa dani!Amma yakamata ayi mun adalci,Auren wata uku fa?kawai saboda buƙatar kanshi"?
  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi cikin sanyin murya tace"Inaso na tambayeki wani abu,amsa ɗaya kawai nakeso ki bani,kuma ki faɗamun gaskiya,'
Dakatawa sehrish tayi da yin kukan tare da mayar da hankalinta kan Aunty azeema tana sauraronta,
   "Inaso ki faɗamun gaskiya,Shin kina son Sgr ko bakya son shi ne"?
  Shiru sehrish tayi yayin da idanunta ke akan yatsun hannunta da ta harɗesu wuri guda tana murzasu,
  "Kinyi shiru baki ban amsa ba"?
ƙasa kasa tayi da muryarta tare da cewa"bazan 6oye maki ba Aunty azeema,ina son Yaya rafayet sosai,fiye da yadda nake son kaina,"
   Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi,dama saida ranta ya bata cewar tana sonshi,
  "In har dagaske kina son shi bai kamata kiyi kuka ba don an ɗaura maki aure dashi,"
  "Aunty azeema ba baƙin ciki nake yi ba,bakomai ne ya 6ata mun rai ba fa ce irin auren da akayi mun dashi,Saboda kawai nayi  aiki a ƙarƙashinshi,na tsawon wata uku?meyasa za'ayi mun haka?idan aka barni ma zan iya yin aiki a ƙarkashinshi ba sai ansa ya aure ni ba,ba bisa son ranshi ba,tunda ba sona yake yi ba,ni kaɗaice nake ɗawainiya da son shi tun kafin nasan wanene shi,Wahala kawai zansha a hannunshi,Ni ban ta6a son na aureshi ba batare da yana Sona ba,"
  Jinjina kai hajiya azeema tayi tare da cewa"hakane kin faɗi gaskiya,ba'ayi maki adalci ba,Ni kaina bansan dalilin yin auren ba sai daga baya nake ji a wurin Abbanku,Amma kiyi haƙuri dan Allah kada hakan yasa ki bijire ma iyayenki,kiyi masu biyayya in sha Allah zaki ci ribar yin hakan,"
  Batare da musu ba Sehrish tace'Shikenan,in sha Allah zanyi masu biyayya,kamar yadda kika ce,kuma koda baki faɗamun haka ba,Ni bazan yi kuskuren bijire masu ba,"
  Murmushi hajiya azeema tayi tare da sanya hannunta ta shafa gefen fuskar sehrish,
"Good girl,Naji daɗi sosai da kika amince zakiyi masu biyayya,Ni kuma nayi maki alƙwarin cewa atare zamu yaƙi sgr,acikin waɗannan watannin guda uku kacal,Zamu canza mashi ra'ayinshi,don ya gane kuskurenshi,kinsan ance DUK ƘYAN TAKALMI ƘAFA CE KE TAKASHI,So nake ki take mun wannan tsadaddan takalmin da ƙafafun nan naki ya taku sosae,"
Sae lokacin Sehrish ta fashe da dariya,har hakoranta suka bayyana,maganar da hajiya azeema tayi mata ta ƙarshen nan ba ƙaramin dariya ta bata ba,

Cigaba da magana hajiya azeema tayi"domin aikin mu yayi kyau muna buƙatar mu shirya plan A da kuma plan b zuwa c,zamu fara jaraba plan A,idan har akaci nasara akan shi kinga basai mun buƙaci plan B ba,Abunda nakeso dake yanzu shine muna buƙatar satar amsa,kuma ke kaɗae ce zaki iya samo mana wannan satar amsar da muke buƙata a wurinshi,
A tsorace sehrish tace"Ni kuma!"hajiya azeema tace"kwarai kuwa,ba wani abun tashin hankali bane,just akwai bukatar musan me yake so da kuma abunda baya so don mu kiyayesu,Ni dae a iya sanina Sgr mutunne maison abi umarninshi ba'ayi mashi musu,yafi so ayi mashi biyayya abishi sau da ƙafa,sannan mutunne shi mai tsaftar gaske,ya tsani ƙazanta,bayan haka kuma Yana son abinci mai daɗi,shiyasa yake cin girkin azmee saboda tana da tsafta kuma ta iya girki,yakama ki koyi kalar girke girkenta,"
"Ae na fara koyo a wurinta,Kuma na iya waɗansu,amma zanyi mata magana akan ta ƙara koyamun wanda ban iyaba,"
"Yawwa haka nakeson ji,ki dage sosai,Nidae ta 6angarena zan baki gudummuwa sosai,""
Sun jima suna fira atsakinsu tamkar ba uwa da ƴa ba,har sae da aka fara kiran sallar Magrib,sannan aunty azeema tayi mata sallama,
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta samu ƙwarin guiwa sosai a wurin Hajiya azeema kuma taci alwashin zata ɗaura ɗamarar zama da sgr,har na tsawon wata ukun

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 12 na dare,tana a tsaye cikin ɗakinsu,sae faman zagaye zagaye takeyi,tana jiran dawowar Sgr,tun bayan sallar isha'e bai dawo cikin gidan ba,har lokacin wedding gown ɗince a jikinta,ta gyara kwalliyar fuskarta,sannan ta daure gashin kanta da ribbom,
Jahad da hosana sun jima da yin bacci ita kaɗae ta rage batayi bacci ba,zuciyarta cike take da damuwa,sam tagaza samun natsuwa babban abunda takeyi ma fargaba shine taya zata fara tunkarar SGR a matsayin Mijinta?shin zata iya jure zama dashi?tasan cewa dole ta fuskanci ƙalubale dayawa a wurinshi,
Tana cikin wannan zancen zucin taji shigowar motocinsu,ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa gefen gadonsu ta zauna tana jiran su ƙarasa shigowa cikin gidan,
Almost 30 mins,sannan ta miƙe tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito waje,babu kowa kai tsaye ta nufi kitchen,batare da 6ata lokaci ba,ta shirya mashi dinner ɗinshi a saman ƙayataccen tray ta ruƙo shi da hannayenta,a hankali take tafiya saboda tsinin takalman dake a ƙafafunta,bata saba tafiya da irinshi ba,babu kowa a main palour ɗin hakan yasa ta wuce upstairs part ɗinsa,
Da sallama abakinta tashiga falon,babu kowa aciki sae dae kamshin turaren nan nashi,kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi tayi,a bakin ƙopar ta tsaya tare da yin sallama"Assalamu alaikum"
"Who's there"abunda taji yace kenan,
daƙyar ta iya cewa"Ni ce"
"Okey,Come in"
A hankali ta zura ƙafarta cikin ɗakin nashi,samun shi tayin kwance asaman katafaren gadon nan nashi na mulki,ko takalman ƙafarshi bai cire ba,still shaddar ce ajikinshi,
Ƙarasa shiga ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table,kamar wata mara gaskiya ta juya zata kama hanyar fita daga ɗakin muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Baki iya gaisuwa bane?"
dakatawa tayi tare da ɗan juyo ta saci kallon fuskarshi,A lumshe ta samu idanunshi tamkar maijin bacci,
Muryarta na rawa tace"Ina yini"
Ta6e la66ansa yayi tare da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login