Showing 285001 words to 288000 words out of 307403 words
Chapter 96 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
kanta da hannunshi,
"Nayi maka alƙawari,"jinjina kanshi ya ɗanyi,Okey,zan zuba ido naga zuwanki,idan ma baki zo ba,Ni zanzo,don na baki maganinki"ba don yaso ba,ya saketa,ta mike tare da kai hannu ta ɗauki tray ɗin kayan abincin da suka kammala ci,a hankali take tafiya,yayin da ranta ke bata cewa yana kallonta,
Sai da takai bakin ƙopar,ta ɗan dakata dayin tafiyar,juyawa tayi don ta saci kallonshi,karaf suka haɗa ido dashi,murmushi ta sakar mashi,shima ya mayar mata da martanin murmushi na gefen fuska,dimple ɗinshi ya lotsa,juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin,
Tana tafiya tana tunaninshi sai kace ba yansu suka rabu dashi ba,tsananin ƙaunarshi take ji acikin zuciyarta,kitchen ta fara zuwa ta ajiye tray ɗin hannunta,kafin ta koma besdroom ɗinsu,kaitsaye ta faɗa saman gadon,yayin da idanuwanta ke kallon sama,A hankali ta furta"I luv u so much Ya rafayet,Mijina nakaina"
A 6angaren hosana kuwa,Lokacin da taje Kai ma Omar abinci,Cike da zumuɗi ta zabga sallama hannunta ruƙe da tray,sae faman zabga murmushi take yi,kamar wata zautacciya,kamar yadda ta saba shiga ɗakin shi ko sallama babu,a haka ta faɗa ciki sai da tashiga tukunna tayi sallamar daga baya"Assalamu Alaikum"a lokacin yana kwance saman gadonshi,hannunshi ruƙe da wayarshi,ɗagowa yayi tare da kallonta,wani irin kyau yaga tayi mashi,miƙewa yayi daga zaune yana kallonta batare da ƙyaftawar ido ba,gaba ɗaya ta tafi da imaninshi,ganin ya ƙura mata yasa ta ɗan turo baki tare da cewa"Ya omar,wai lafiya kake kallona,"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da cewa"hosana,wa yayi maki kwalliya?
"Ni nayi abunda,"
"Amma dai,ni akayiwa kwalliyar ko"?
Murmushi ta ɗan saki tare da ɗaga mashi gira alamar Eh,
Ba ƙaramin daɗi yaji ba"Ki kaimun abincin falo,Yanzu zo muci tare ,
Da sauri ta juya,tana shiga ta sauke tray ɗin a saman table,jiki na rawa ta zura hannunta cikin bra,ta zaro paper din da jahad ta rubuta mata kalaman soyayya,
Karantawa ta farayi don ta samu ta haddace wasu kafin ya fito,
"Ya Omar,inasonka so irin wanda uwa keyi ma jaririnta,kaine mutun na farko dana ji ya kwanta mun araina,nakeson kasancewa dashi na har abada,A matsayin mijina uban ya'yana,"tana cikin karantawa Tajiyo mutsu mutsun fitowarshi,A ruɗe ta nannaɗe takardar ta turata acikin bra ɗinta,
Ƙarasowa cikin falon yayi,hannu yasa ya ɗauki tray ɗin data ajiye saman table ɗin,Ya sauke shi saman carpet don suji daɗin cin abincin atare,
"Bismillah,"yayi maganar yana nuna mata wuri,da sauri ta zauna tare da lanƙwashe ƙafafunta,kamar yarda shima yayi,da kanshi ya zuba masu abincin Yace mata"mu fara ko'maƙe mashi kafaɗa tayi"Ae ni naci ya omar,kaidai kaci,"gyaɗa kai yayi batare da yayi mata musu ba,Ya soma cin abincin,
Yana kokarin cin abincin karaf suka hada ido da ita,dakatawa ya ɗanyi"Wannan kallon fa"?
Ƙayataccen murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Kai dai kawai kaci gaba da cin abincin ka,"jinjina kanshi ya ɗanyi kafin ya mayar da hankalinshi kan abincin dayake ci,
Tunani ta shiga yi,Ta manta kalaman data haddace,ganin hankalinshi baya akanta,yasa tayi sauri tura hannu ta ɗauko takardar duk ta cukuikuye,jikinta har kerma yake yi wurin karantawa,bayan ta kammala ta ninke ta mayar,
Murmushi ta ɗan saki kafin tace"Ya Omar"ɗagowa yayi tare da kallonta yana jiran jin me zatace
"Kasan yadda nakeson kuwa"?tayi tambayar fuskarta babu alamun wasa,
Girgiza kai Omar yayi"a'a saikin faɗa,"
"Inasonka sosai ya omar,irin son da uwa keyi ma ɗanta,banajin zan iya rayuwa da wani ɗa namiji in bakai ba......'
Saboda tsabar mamaki baisan lokacin daya saki cokalin hannunshi ba,ya fada cikin plate ɗin gabanshi,zuba mata ido yayi yana kallonta,
"Kaine tauraron dake haska zuciyata,dakai nake kwana dakai nake tashi Ya omar,bani da burin daya wuce in mallake ka a matsayin mijina......."
A sukwane marshal ke kallonta,abun ya ɗaure mashi kai,kamar an sanya mata radio sai zuba take yi,abu kamar na hankali,ganin ta kakare yasa ta ɗan dakata tare dacewa"masoyina meyasa kake kallona?kaci gaba da cin abincinka mana,ni kuma zan cigaba da faranta maka rai"
Shiru yayi yana tunanin taya akai hosana ta iya kalamai masu daɗi na hankali,Sam bai yarda da ita ba,
"Hosana miƙe tsaye,"yayi maganar yana yi mata nuni da hannunshi,miƙewa hosana tayi,tsaf ya shiga kallonta daga saman har kasa,don yana zargin kamar karantowa take yi,ganin baiga komai ba yasa shi cewa tayi tsalle,
Ranta ya 6aci sosai,a kule tace"Ni bazanyi ba,"
Murmushin gefen fuska omar ya saki,
"Shikenan,koma ki zauna,sannan kuma ki cigaba da fadamun daɗaɗan kalaman nan,inajin daɗinsu,"
Murmushi ta saki,cike da zumuɗi ta koma ta zauna,tana kokarin kai hannu ta zaro takardar ya kafe ta da idanuwanshi,duk tabi ta susuce,
Ashagwa6e tace"Ya omar wai menene haka?ka ƙuramun ido,kaci gaba da cin abincinka mana,"
Girgiza kai yayi"a'a,nafi jin daɗin kallonki,yayin da kike faɗamunsu,"da biyu Omar yayi mata haka,
Shuri tayi tana ta faman mazurai,domin kuwa bata iya komai ba,
"Am listening to u,My baby "yayi maganar yana kallonta,
Haushi ya isheta,daƙyar ta cigaba da cewa"yakai bunsurun dake cin ciyawar zuciyata,"
Waro ido waje Omar yayi"Hosana!ni ne bunsurun"?da sauri ta sanya tafin hannu ta toshe bakinta,tana girgiza mashi kanta"wlh Ya Omar su6ul dabaka nayi,ba haka nakeso nace ba,kaine ka tsare ni da idanuwanka,"
Harara ya ɗan jefa mata,Hannu yakai tare da ɗaukar lemu ya tsiyayashi Acikin cup,kafin ya ɗago tayi saurin Zura hannu ta ciro paper ɗin,hannunta nata kerma ta shiga dubata,da sauri ta mayar cikin bra ɗin ta ajiye,tana faman mayar da numfashi kamar wadda tasha gudu,
Ɗagowar da zaiyi A furgice Yace"hosana!kyankyaso....."tana jin haka ta miƙe a ruɗe tana kakka6e jikinta,hada kuka nan take takardar da take ta faman 6oyo ta faɗo ƙasa a cukuikuye,tuntsirewa Omar yayi da dariya,hada dafe cikinshi,ya hasala ta sosai,Ta bubbuga ƙafarta,tare da fashewa da wani sabon kukan da gudu ta nufi hanyar fita daga falon tana kuka,miƙewa yayi da sauri yabi bayanta,har ya samu ya ruƙota tare da jangota jikinshi ya rungumeta,Yana ɗan bubbuga bayanta"Am sorry,banso na 6ata maki rai ba,nasan kinyi ne donki faranta mun raina,"
*Boss Bature*
A 6angaren Amrish kuwa,Har kusan one hour tana zaman jiran Kanal Yousouf,tuni ta jima da kammala Cin abincin,ta mayar da plate ɗin kitchen,A saman doguwar sofa ta kwanta tana jiran zuwanshi,har bacci ya ɗauketa,wuraren ƙarfe ɗaya da rabi,Motar shi ta ƙaraso bakin gate ɗin gidan,Yana yin horn baba mai gadi ya buɗe mashi,A mutunce suka gaisa da junansu,saboda ya ganeshi sosai,kuma yousouf yayi mashi bayanin zuwanshi,Bayan ya buɗe mashi gate ɗin ya wuce da motar cikin gidan,parking ɗinta yayi,kafin Ya fito ya nufi cikin gidan,A ƙopar shiga falon Ya tsaya yana zabga sallama shiru ba'a amsa mashi ba,kusan sau biyar,A karshe ya yanke shawarar shiga ciki,Da sallama abakinshi ya shiga falon,Tunkafin ya ƙarasa ciki ya hango Amrish,kwance tana bacci,gaba daya mayafinta ya zame ƙasa,tsayawa yayi yana kallon kitson kalabar dake akanta,manya manya,tayi mata kyau,baisan ta yarda zai tashe ta,Tunawa da makullin motar hannunshi Yasa shi yin dabarar girgiza key din saitin kunnanta,Sautinne Ya farkar da amrish daga bacci,mutsu mutsu ta fara tana kokarin buɗe idanuwanta,duk bata Lura dashi ba,har ta miƙe tsaye ta Sauko da ƙafafuwanta ƙasa,Ta ɗaga hannayenta tana yin miƙa,Da sauri Yousouf Ya kawar da idanuwanshi,ganin yadda ƙirjinta ya fito sosai,
Sai daga baya ta lura dashi,da sauri Ta ɗauko mayafinta,ta rufe kanta dashi,
"Yaya yousouf,ka dawo,"
Batare daya kalleta ba yace"Am sorry,na barki kina ta jirana,wani uzirine ya ruƙe.ni"
"Babu komai,"ta ambaci hakan tare da mikewa ta ruƙo trolley ɗin kayanta,Gaba yayi tabi bayanshi har suka isa motar,kowa ya shiga ya zauna kafin ya tashi motar,ya nufi hanyar gida dasu,yana driving suna fira da ita,
*Boss Bature*
*Amani*
Tana cikin gyara kitchen tajiyo muryar Jahan daga falo yana kwaɗa sallama,fuskarta ɗauke da murmushi ta tunkari falon,A zaune ta same su saman Sofa,su biyu sun ɗauki wankan suits,ba ƙaramin kyau su kayi ba,dama duk in jahan zai zo zance,Atare da Ayaan suke zuwa,kamar yadda suke twins komai atare suke yinshi,
"Yau kune a gidan namu,"tayi tambayar tare da samun wuri ta zauna tana fuskantarsu,
Haɗa baki su kayi wurin gaisar da ita"Ina yini aunty,mun same ku lafiya"?
"lafiyalou,Ya kuke?ya mutanan gidan naku?Ya jikin junaid da fawan"?
Ayaan yace"Kowa yana cikin ƙoshin lafiya,marasa lafiya kuma jiki yayi kyau,".
"Masha Allah abu yayi kyau,"acewar amani,
"Bari nakawo maku abunsha"da sauri suka haɗa baki wurin cewa"a'a,bama bukatar komai,"
Dariya ta ɗanyi,ba ƙaramin burgeta suke yi ba,har magana ma wani lokacin in zasu yi atare suke yinta,
Ta lura da jahan sai faman waige waige yakeyi,
"Amal ko"?tayi tambayar fuskarta ɗauke da murmushi,
Murmushin gefen fuska Jahan ya saki tare da cewa"eh,tana ina ne?naga banganta ba"
"Bari nakira maka ita,"miƙewa tayi tare da juyawa ta nufi upstairs,
"am so eager to see her,nayi kewarta sosai,"jahan ne yayi maganar yayin da yake zaro wayarshi daga cikin aljihunshi,
Ayaan yace"In ka kwantar da hankalinka,Cikin ƴan kwanakin nan za'a shafa fatihar auranku,idan yaso saika mayar da ita madubi kayi ta kallonta,"
Harararshi jahan yayi "oh kana nufin zan aureta ne,kawai don na ajiyeta,na zuba mata ido ina kallonta?kaima ka sani wlh,"
Dariya ayaan yayi,kafin ya ƙara cewa wani abu,Amal ta sauko jikinta sanye da riga da skirt na material maroon colour,tasha uban makeup,
Da sauri jahan ya sanya tafin hannunshi Ya rufe ma Ayaan fuska,wai don kada ya kalle mashi matarshi,
Buge hannun Ayaan yayi yana fadin"Me yayi zafi?Bari na tashi na baku wuri,idan kun kammala Zancen ka kirani in dawo in ɗaukeka,"yana kai ƙarshen maganar ya miƙe tare da nufar ƙopar fita falon yana dariya,
Ƙarasowa Amal tayi,Tana ƙokarin zama ya nuna mata laps ɗinshi wai tazo ta zauna asama,waro ido waje tayi tana girgiza mashi kai"a'a kunya nake ji idan aunty amani ta gani fa,"
Zare mata ido yayi"Ina wasa dake?zaki zo ki zauna ko sai ranki ya 6aci,"sam babu wasa a fuskarshi,dama haka take fama dashi,baida kunya ko kaɗan,ita kuma kunya gareta sosai,kuma sam bai iya soyayya ba,yafi ƙwarewa a harkar romance,ta ko'ina jahan yafi ƙarfinta,lalla6awa kawai take yi dashi don tana sonshi,
"Ni bazan zauna asaman cinyarka ba,Amma zan zauna a gefenka,in kuma hakan baiyi maka ba,ni zan koma ciki"idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
Sassauta muryashi yayi"its ok,don't cry nima wasa nake maki,zoki zauna,"gefenshi ta zauna ya tsareta da idanuwanshi,sae faman gyara mayafinta take yi,saboda kallon ƙurullan da yake yi mata,.
"Baki yi farin ciki da zuwana bane"cikin sanyin murya yayi mata maganar,
"Yakamata ki saki jiki dani,nan bada jimawa ba,za'a ɗaura mana aure,ko baki sona ne"?
Ƙasa kasa da murya tace"inasonka mana,"
"To meyasa ko kallona bakya yi"?
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta,matsawa yayi tamkar zai shige mata,ruƙo hannayenta yayi cikin nashi,
"Amal,"ta amsa mashi da na'am,
"Yakama ki koyi zama dani,tun yanzu in ba haka ba,zakisha wahalata,Kin cika kunya,ni kuma banason mace me kunya,its better ki cire kunyarki wurin nuna mun soyayya,kinji ko"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Shafa gefen fuskarta yayi"faɗamun idan munyi aure,a first night ɗinmu,me zaki yi mun,"shiru amal tayi tana tunanin amsar da zata bashi,hasalima bata gane me yake nufi ba,
"Kinyi Shiru bakice komai ba"?
Cike da jin kunyarshi tace"Ni bansan me kake nufi ba,"
Dai dai satin kunnanta yakai bakinsa tare da cewa"I mean...idan zamuyi sunnah,"
Still bata gane me yake nufi ba,
"Ya jahan ni ban fahimce kaba,"
Takaicine ya isheshi,a ƙule yace"oh,kina nufin bakisan Komai ba?a haka zamuyi aure?that's impossible,"
Ganin yadda ya 6ata ranshi yasa tace"Am sorry,wlh bansan kan me kake magana ba,"
"Gaskiya idan har kinason mu zauna lafiya dake,to ki koyi yadda zaki farantamun kinji ni ko"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
"Idan na tafi,kice ma Auntynki ta koya maki yadda zaki kwanta da mijinki,ina fata kinji ni"?
Gaba ɗaya ta dabarbace,Amma tabbas bata gane me yake nufi ba,
"Zan faɗa mata,"jinjina kanshi yayi yanzu naji magana......'ya jima a wurin Amal,kafin yayi masu sallama,ya kira ayaan ya ɗaukeshi suka koma gida,
[3/19, 2:58 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags
Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃
Remain few pages 😢
Bayan tafiyar Jahan,Amal ta sanarwa Amani abunda yace ta koya mata,tasha ruwan mamaki,amma ta wani 6angaren ba ƙaramin taimakonta yayi ba,tunda gashi Ya tuna mata abunda ta manta bata koyar da Amal din ba don tasan tana bukatar hakan,
A taƙaice cikin ƴan kwanakin nan,wata irin shaƙuwace a tsakanin Sgr da Sehrish,Soyayyarsu gwanin ban sha'awa,wani irin so suke yiwa junansu,a koda yaushe yana manne da ita idan har ba lokacin sallah bane tunda aikinshi na Nigeria Ya qare,jikinta yayi sauƙi sosai,tana samun kyakkyawar kulawa a wurinshi,komai atare suke yinshi,Cin abinci,bacci,da sauransu,Yanzu kowa na gidan hatta su Ammi sun gane cewa Sehrish da Sgr sun sasanta tsakaninsu,wannan yasa ammi bata ƙara neman Sehrish da su zauna akan maganar kar6ar takardarta ba,dama abunda suke fata kenan,
A 6angaren Omar da Hosana,abun sai son barka,hajiya azeema ta gyara mashi ita sosai,yanzu ta rage wannan soki burutsun nata,duk da akwai sauranta,Amma an samu cigaba,
Idan muka dawo 6angaren Romeo da Juliet,ko ban faɗa ba kunsani,Masoyane na gaske,duk da rashin jin Junaid haka Jahad ke son abunta,kamar yadda shima yake sonta,basu gajiya da bama furannin soyayyarsu ruwa,wata irin shaƙuwace a tsakaninsu,hakan yasa koda yaushe suke manne da juna,
A 6angaren Kanal Yusuf da Amrish kuwa,tuni ya bayyana mata soyayyarshi,kuma da Maganar aure ya fara zuwan mata,don baya buƙatar su 6ata lokaci wurin yin soyayya a waje tunda sun aminta da juna,abu ne kana so ana sonka,no need to waste time,hatta Abbansu yasan da maganarsu,
Saboda tafiyar Sgr da Omar U.s,Yasa aka shirya yin bikinsu a cikin ƙurarren Lokaci,gagarumin bikine aka shirya yinshi cikin sati guda,Wanda tuni an fara sanarwar ɗaurin Auransu wanda za'ayi ranar Juma'a,gaba ɗaya Social media ta ɗauka,gidajen talabijin dana radio,Ko'ina zancen auran Ƴa'ƴan Abban sojoji ake yi,Labarin ya karaɗe Duniya,wato bikine na zaratan samarin gidan wanda sukayi shura a duniyar nan tamu,daga cikin waɗanda za'a daura auransu,Akwai Omar da Hosana,Junaid da Jahad,Jahan da Amal,Yusuf da Amrish,Osman da Khadija,Adam da Nafeesat,Fawan da Yusra ɗiyar abokin Abbansu Tafeeda,dama sun jima atare tun lokacin da yake tashen rashin jinshi atare suke da ita,kafin Allah ya shiryi kowannansu,Ayaan da Yuhana ƴar wurin ƙawar Mommynsu Dr Harriet,wanda Mommynsu ta haɗa shi da ita,Don ayi auransu atare da Jahan,saboda ya nuna cewa in dai baza'a ɗaura Auransu da Ayaan ba sai dai shima a fasa nashi,wannan dalilinne yasa Mommynsu ta haɗa Ayaan da Yuhana kuma cikin sa'a,A rana ta farko da Ayaan ya haɗu da ita yaji ta kwanta mashi aranshi,ita ma kuma haka,sun amince da junansu batare da sunsha wahala ba,bayansu kuma sai Uban gayya,Babban ɗa a wurin Abban sojoji,General Ishaq tare da Amaryarshi Hajjaju,Sai daga baya Abbansu yaji labarin rabuwarshi da Laila,Yasha faɗa a wurinshi duk da yayi mashi bayanin dalilin rabuwar aurannasu,daƙyar ya samu Abba Ya haƙura da maganar,
Abusufyan ma yana ɗaya daga cikin wanda zasu Angwance,Shida Uwar ya'yanshi Zainabu Abu,
Waɗanda aka sanyama biki kuma,Hafsat da Ya mu'allim,bayan dagar da suka sha dashi,da farko taƙi amincewa da auranshi saboda malamine,Amma daga baya ta amince da auran nashi,gaba ɗaya sauran matasan gidan,tun daga kan Captain Najeeb,Jabeer,khaleed,da Talal,kowannansu An sanya ranar auranshi,
Murna awurin Family dinsu ba'a magana,musamman Abbansu yafi kowa farin ciki,burinshi na qarshe da ya rage mashi a duniyar nan shine yaga auran ƴa'ƴanshi,kodan yaga ƴan jikokinshi
Ba ƙaramin ƙoƙari Hajiya azeema tayi ba,tare da Mommy da Oummansu Sehrish,domin kuwa sune suka yi tattaki har zuwa Dubai wurin haɗa masu lefensu,jigunannun kaya haɗaɗɗun gaske,An kashe kuɗi kamar ba'asan wahalar nemansu ba,musamman a lefen Sehrish da Hosana da Jahad,shi Junaid ko sisi bai kashe ba,Komai da aka kashe ma Jahad Sgr ne ya ɗauki nauyin komai,hatta sadakin Junaid,Sgr ne ya biya shi gaba da baya auran gata za'ai mashi,Daga Hosana har Jahad sadakinsu da Gold aka biyashi irin na Sehrish,sauranne aka biya sadakinsu kowacce dubu ɗari uku uku,Amrish ta samu kyauta sosai a wurin Sgr da Abbansu,saboda sune suka biya kuɗin komai na kayan daki,da duk wani abu da zata buƙata,
Special Gift Sgr ya shirya ma Sehrish,Amma yace Sai sun koma California zai bata kyautarta ta musamman,Saboda ta bashi abu mafi daraja the most greatest gift,wanda kowani miji yake burin ya samu a wurin matarshi a rana ta farko daya kusanceta,tunkafin ma wannan kyautar acikin akwatinan lefenta hada na kayan adon mata,zallar Diamond ne acikinshi,
Ba ƙaramin gyaran jiki Amaren suke sha ba,masu gyaransu har daga kasashen ketare,koda yaushe cikin gyarasu akeyi,tun cikin satin da za'a ɗaura Auren,gaba daya amaren suka hallara a gidan,saboda programes da aka shirya,gidan yasha gyara sosai,An ƙawata shi,idan ka shiga cikinshi kamar ka bar Nigeria ne saboda tsabar haɗuwar da yayi,Naira tasha kashi,an ɗaukko masu aikin cikin gida,manya manya chefs waɗanda zasu gudanar da abincin bikin,da kuma Event planners wanda zasu tsara shagulgulan da za'ayi na bikin,
Anyi shagulgulan biki na kece raini,An yi shiga ta alfarma,Anci ansha An godema Allah,kuma kowa ya nishaɗantu,
A ranar Juma'a,dubban Jama'a suka shaida ɗaurin Auran zaratan Samarin gidan Abban Sojoji A Abuja central Mosque,Masallacin ya cika maƙil da Mutane,ba masaka tsinke duk wani wanda ya amsa sunansa a Nigeria ya hallaci daurin auren,Bayan kammaluwar ɗaurin auran,A daren Ranar aka kawo duka amaren wanda acikin gidan Abba zasu zauna,don tuni an fara gine gine na wasu 6angarori da za'a ƙara,Amma kafin nan,kowaccensu zata tare a ɗakin Mijinta ne na wani lokaci,dama burin Abbane kowannansu in yayi Aure yafi son ya zauna a gidan tare da matarshi,saboda baison suyi nesa dashi,
Shirye shiryen tafiya U.s Ya kankama,tun ana saura kwana ukku ya rage jirginsu ya ɗaga,Sehrish ta lalla6a Sgr don ya kaita Gidan Yari taga Aunty azmee,Dayake yanzu farin cikinta yakeso,Baiyi mata musu ba,da kanshi yakaita prison,Lokacin da taga Azmee tasha kuka sosai kamar ranta zai fita,Azmee ta rame ta ƙanjame,idanuwanta daƙyar take buɗesu,Sun rungume juna sosai,koda Sehrish ta sanar da ita cewa zata sanya a sassauta hukuncin da aka yanke masu,sai cewa tayi ita batason fita daga gidan yarin saboda gudun ta ƙara faɗawa halaka,tafi son zama anan saboda tafi samun natsuwa wurin yin ibadarta da neman yafiya wurin Ubangiji,kuma ta nemi yafiyar Sehrish akan Laifin da tayi mata,tun daga kan juya mata da tunaninta da tayi,lokacin da ta manta dasu Hosana,tace ita tayi hakanne saboda halin da tashiga na yawan damuwa shiyasa ta mantar mata dasu,da kuma lalurar da ta ɗaura mata na yin gane gane,duk sai da ta nemi yafiyarta,ta kuma sanar da ita