Showing 252001 words to 255000 words out of 307403 words

Chapter 85 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

ta shiga,ko sallama babu,Amrish ta samu agaban wardrobe tana lalubo abayar da zatayi sallah,jin an turo ƙopar ɗakin yasa ta juyo don taga wanene,duk a tunaninta Sehrish ce,
   "Kin dawo kenan"
Turo baki hosana tayi"Ina rishi ɗinmu take?ita nake son gani,"sai da tayi magana sannan ta gane wacece
"Nima bansan inda taje ba,tun da na farka ban sanyata a idanuwana ba,"
  Guntun tsoki hosana taja,duk a tunnaninta,Amrish ƙarya take yi mata,
  Toilet Ta buɗe ta shiga tana neman Sehrish,Jim kaɗan ta fito daga toilet ɗin,Duk amrish na kallonta,Har ƙarƙashin gado ta leƙa bata ganta ba,a ƙarshe Tayi ƙwafa tare da bude ɗakin ta fuce,bedroom ɗinsu ta koma,A lokacin har Abu da Jahad sun kammala Sallah,toilet ta shiga shaf shaf ta ɗauro alwala,
Ta fito ta ɗauko hijabi a wardrobe ta jera dasu,


Bayan an kammala Sallar Asuban,suna dawowa gidan,Abusufyan bai nufi ko ina ba sai upstairs,tsabar sauri kamar zaiyi tuntu6e ya faɗi,Abba na biye da bayanshi,Omar ma yabi bayansu,kowannansu na sanye cikin jallabiya,

Yana shiga bedroom ɗinshi,Yaga wayaam babu kowa,yayi tunanin yana acikin toilet,wuri Ya samu gefen gadonshi Ya zauna yana jiran fitowarshi daga cikin toilet ɗin,Don ayita ta ƙare kowa ma ya huta,
A tsaye Abba ya tsaya Omar na agefenshi,Gabanshi sai faɗuwa yake yi,Sgr ya tafi ya barshi da zullumi,duk yabi yasha jinin jikinshi,
  "Omar me ya hana Rafayet zuwa masallaci"?Abusufyan ne ya jefo mashi tambayar,
  A ruɗe ya soma ƙoƙarin yin magana,En ena ta hana shi"am...um...'
  Cike da mamaki Abusufyan ke kallonshi don a iya saninshi Omar baya en inar magana,Amma sai gashi yau daga ƴar tambaya duk yabi ya dabarbace,
  Wurga idanuwanshi yayi kan Abbansu dake a gefenshi,Suna haɗa ido Omar yayi saurin sunnar da kanshi kasa,Dama ance Labarin zuciya a tambayi fuska,Tuni Abbansu Yayi hasashen wani abu acikin ranshi,kuma ga dukkan alamu Sgr baya acikin toilet ɗinshi,
  "Abusufyan"!ya ambaci sunanshi,
"Na'am yaya,"
"Ina tunanin bayan fitarmu masallaci Rafayet ya fita yin sallah shima,mu ƙara haƙuri mujira dawowarshi,"
  Girgiza kai Abusufyan yayi"ba inda zanje,ina nan ina jiran dawowarshi "
  "shikenan,Omar inason magana dakai," ya ƙarasa maganar tare da ruƙo hannun Omar,Suka fito falonshi,

  "Omar ka faɗa mun gaskiyar abunda ya faru,Ina SGR ya tafi"?cike da tuhuma yake kallonshi,
  A ruɗe Omar yace"Bansan Komai ba Abba,bani da masaniya akanshi,"
  "Hmmmm Omar kenan,Nifa mahaifinka ne,Har akwai abunda zaka iya 6oye mun?fuskarka kawai na kalla raina ya bani cewa wani abu ya faru kuma kana da masaniya akanshi,Shiyasa har kake in ina,"shuru Omar yayi batare daya ce komai ba,
  "Zuciyata har ta karaya,Dan Allah Omar ka faɗamun meya faru?Ina Sgr ya tafi tunda Asuba,"?ganin yadda Ya shiga damuwa sosai,Yasa Omar Ya soma bayyana mashi abunda Ya faru,tun daga kan zuwan da Sgr yayi bedroom ɗinshi,bai 6oye mashi komai ba kaf ya sanar dashi,
  "Innalillahi'wa' Inna ilahirraji'un!"

jiri ne ya soma ɗibarshi,Yayi tangal tangal zai faɗi,da sauri Omar ya ruƙoshi tare da taimaka mashi Ya zauna saman Sofa,Hankalinshi yayi mugun tashi,
  "Nashiga uku Omar,Ashe rafayet bai da hankali!Dama saboda ya aikata mata hakan Ya nemi da mu ƙara mashi lokaci....wlh in har ya kuskure yarinyar nan ta rasa ranta,shima sai na kashe shi,
  "Abba pls,ka rage muryarka,bansan ya zanyi ba,idan Uncle yaji wannan maganar,shiyasa tun jiya nayi ƙoƙarin in dakatar daku akan kubi komai asannu amma kuka ƙi saurarena...."tun kafin yakai ƙarshen maganarshi Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa"Amma Omar rafayet bai kyauta ma kanshi ba,Yayi tunanin idan yayi mata hakan zai zame mashi mafita,Gashi yanzu ya ƙara jefa kanshi cikin tashin hankali,Bansan wani irin bauɗaɗɗen mutun bane shi,Nikaina da nake mahaifinshi Yafi ƙarfina...."Idanuwanshi cike tab da kwalla yayi maganar,
  "Abba,kayi haƙuri da abunda zance,bai kamata kuna ganin laifin Rafayet ba,Irin rayuwar da aka saba mashi da itane,komai yake so shi yake samu,tunfarko kuskuren da aka tabka shine barinshi da kayi Uncle donald ya tafi dashi U.s,tun kafin ya mallaki hankalinshi,Kasan wanene Donald,Yayan Mommy ne,tarbiyar ɗan uwana kwata kwata ba irin tanan bace,ya taso ba a musulmi ba,kuma an damƙashi hannun wanda ba musulmi ba kuma bature,taya rayuwarshi bazata kasance haka ba?Abba kayi tunani,da ace kai da kanka kaba shi tarbiya ya taso a wurinka,Ya kake tunanin zai kasance? ......'ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon Abbansu,wanda tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,tsananin tausayinshi ne ya kamashi,
"Omar ka faɗi gaskiya,Laifina ne wlh,nayi danasani yafi a ƙirga,duk in na tuna cewa Sgr ba a hannuna ya taso ba,Na cutar da rayuwarshi banyi mashi adalci ba,banbari Ya taso a hannuna ba,a lokacin so ya rufe mun idanuna bani da burin daya wuce in faranta ma Alex rai,komai tace tana so gudun kada ranta ya 6aci yi mata shi nake yi,inaji ina gani Sgr ya taso ba'a musulmi ba,kullum in zaku tafi masallaci batare dashi ba,Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata,Donald yazo ya ƙwallafa rai akanshi,Alex tace in bar mashi shi ya tafi dashi can,wlh Omar bada son raina ba,Allah na gani inason Rafayet sosai,na amince ne don tayi mun alƙawarin zata ƙara haihuwa dani,kuma hada ƙarin don bana son ina ganinshi a matsayin wanda ba musulmi ba,shiyasa kawai na yanke shawarar Ƙwara yayi nesa dani,in banda ma rashin hankali irin nawa na ɗauki ƙaramin yaro naba wanda ban haɗa komai dashi ba,ƙanwarshi kawai nake aure,shi ba musulmi ba,Yanayin rayuwarsu da al'adarsu ba irin tamu ba,yanzu da ace rafayet ya mutu a wannan yanayin me zance ma Allah?Akan amanar daya bani!,ya makomarshi zata kasance Ya mutu a matsayin wanda ba musulmi ba,wlh na cuci rayuwarshi........'kasa ƙarasa maganar yayi saboda kukan daya ciyoshi,Tafin hannunshi yasa Ya rufe fuskarshi,shi kanshi Omar hawayen ne sharkaf akan fuskarshi,gefen Abba ya koma Ya zauna,tare da janyoshi jikinshi,Yana lallashinshi,
  "Ba don Allah yasa a wannan lokacin nayi tunanin haɗaka dashi ba,Har ka bisu U.s,kuma cikin sa'a ata dalilinka Ya musulunta,da bansan Ya rayuwarshi zata kasance ba,duk cikin ƴa'ƴana Rafayet ne ban yiwa adalci ba,Ya Allah ka yafe mun...."
  Lallashinshi Omar ya soma yi"Abba kayi haƙuri dan Allah,kadaina zubar da hawayenka,Yakamata muyi ƙoƙari wurin ganin mun nemo inda ya tafi da ita,bamusan a wani Hali suke ciki ba,naji takaici da ban taimaka mashi ba a lokacin da yazo wurina cikin mawuyacin hali,na rufe ido na kore shi da duk hakan bata faru ba,yasan cewa ni kaɗai zan iya fahimtarshi shiyasa yazo wurina,Sam baya acikin hayyacinshi amma haka yazo,Ni kuma maimakon in jashi ajikina in taimakeshin saina yi mashi tsawa nace ya fita ya bani wuri,

Duk wannan maganganun da suke yi akan kunnan Abusufyan dake tsaye abayan sofa ɗin da suke zaune,Kaf yaji abunda suke tattaunawa tun daga farko har ƙarshe,jikinshi yayi mugun sanyi,Hankalinshi Yayi matuƙar tashi,Har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi,

Ba zato ba tsammani suka ji muryarshi ta bayansu,
  "Rafayet ya kashe mun ƴata,"firgigit sukayi gaba ɗaya suka miƙe atare suna kallonshi,Fuskarshi sharkaf da hawaye,
  Aruɗe Abba yace"Abusufyan tun yaushe kake tsaye awurin nan"?
  Muryarshi adisashe ya basu Amsa"tun lokacin da kuka fara magana nake tsaye ina sauraronku....."dakatawa ya ɗan yi da yin maganar,cikin sanyin murya ta wanda ya karaya yaci gaba da magana
"Dan Allah ku faɗamun gaskiya,Sehrish tana raye kota mutu?Ina Rafayet yakai mun ita?Ni ko gawarta ce dan Allah ya maido mun,"
  Wannan maganar da yayi ta ƙarshe ba ƙaramin Kashe masu jiki tayi ba....
  "In sha Allah,Sehrish tana raye Uncle,a duk inda suke yanzu nasan Sgr yana akan gyara 6arnar da yayi mata ne,dan Allah ina ba kowa hakuri amadadin ɗan uwana,wlh duk wani hali da zamu shiga ayanzu bamu kama ƙafarshi ba,Ya tsorata sosai,tunda nake a rayuwata ban ta6a ganin Sgr cikin matsanancin tashin hankali ba irin na yau,nasan ya cutar da ita,Amma duk yayi wannan ne saboda son da yake yi mata,Yana tsoran ku rabashi da ita ne........
  "Omar,Kana goyon bayanshi ne?Ni ƴata ba mutun bace!Allah kaɗai yasan irin muguntar da yayi mata,Rafayet baida Imani baida tausayi,Wlh nayi danasanin aura mashi Sehrish!Kuma duk inda ya shiga acikin garin nan saina nemoshi,Ya dawo mun da ƴata,koda gawarta ce" duk yadda Omar yaso ya fahimtar dashi,Amma yaƙi sauraronshi,a zafafe ya nufi hanyar fita daga falon,Da sauri Abba yabi bayanshi tare da ruƙo hannunshi,idanuwanshi sun rufe rai a6ace yake magana"Ya Hossein ka sake ni,Wlh bazan ƙyale rafayet ba,har ni zai wulaƙanta ma ƴa?Allah hukuma ce zata rabani dashi,"ranshi a matuƙar 6ace yake magana,
  "Kada ka yanke hukunci cikin fushi,muzo muna danasani....."tunkan Abba yakai ƙarshen maganarshi,Abusufyan ya fusge hannunshi,A fusace Ya fuce daga part ɗin,
  Bai ta6a tunanin Abusufyan zaiyi mashi haka ba,ya 6ata mashi rai sosai,
"Abba,ni ina ganin me zai hana A sanarwa Ammi halin da ake ciki,wata'ƙila ta dakatar dashi,
  Girgiza kai Abba yayi"kabarshi kawai,Yadda zuciya ta ɗebeshi ɗin nan bazai saurari kowa ba,Sam baya cikin hayyacinshi,Ni tsorona ma kada yace zai yi driving a irin wannan yanayin da yake ciki,"

Hannu Omar ya tura cikin trouser pocket dinsa Ya zaro wayarshi,Layin Abusufyan ya dinga kira,Wayar nata ringing amma yaƙi ɗagawa,
  "Dama kadaina wahalar kiranshi,don bazai saurareka ba,Ni yanzu babban tashin hankalina bansan a wani hali suke ciki ba,Omar ba yadda za'ae asan Location dinshi"?
  "Abba wayarfa tana a bedroom ɗinshi ya barta,Sannan nayi kokarin kiran Armstrong yaƙi picking,kuma ya toshe duk wata hanya da za'a yin tracking layinsa,'
  "Ina kake tunanin ya tafi da ita"?
  Shuru Omar ya ɗanyi yana kokarin yin tunani akan inda Sgr zai tafi da ita,
  "Da farko nayi tunanin asibitinshi ya tafi da ita don ya dubata,Amma munje har can nida Major bamu same shi ba,nidai inaji araina cewa Suna acikin garin nan,Sgr bai gudu da ita ba,nafi tunanin ya 6oyeta a wani wurine saboda gudun kada Abusufyan yaga 6arnar da yayi mata,Amma Ina da tabbacin cewa zaiyi ƙoƙarin Yi mata aikine da kanshi,"
  Jinjina kai Abba ya ɗan yi,tare da cewa"Dan Allah Omar,kuyi ƙoƙari wurin ganin kun gano mana inda yake,Zan cigaba da kiran Layin Abusufyan,har Allah yasa ya ɗaga,"

Amsa mashi yayi da toh Abba,A hanzarce Ya fuce daga part ɗin,Abba yajima zaune asaman sofa yana ta faman kiran Abusufyan Amma yaƙi ɗaga kiran,A ƙarshe ma sai ya kashe wayar gaba ɗaya,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,jiki asanyaye ya fito daga part ɗinshi,Ya sauko downstairs,bedroom ɗinshi Ya shiga,Mommy ya samu zaune gefen gadon,hannunta ruƙe da Cup,Tana ba Junaid magungunanshi yana sha,jin motsinshi yasa suka kai idanuwansu wurinshi,
  "Abba,"Junaid ne ya ambaci sunanshi,
Mommy tace"Ina ka shiga ne?Tunda kuka tafi masallaci ban ganka ba"
  Daƙyar ya iya buɗe baki yace"wani abune ya tsayar dani,"tunkafin ta ƙara tambayarshi,yayi saurin cewa"Junaid ya jikin naka"?
  "Alhamdulillah Abba,Am feeling better,Nayi missing dinka sosai,jiya kace zaka tashe ni mu tafi masallaci sallar Asuba atare,"
  "Am Sorry,Na manta ne,Amma gobe in sha Allah,Zamu fara zuwa masallaci dakai,tunda naga jikin naka ya murmure,"Ya ƙarasa maganar,yana kakaro murmushin dole,Mommy dai ta kafe shi da ido,Don ta lura akwai damuwa atattare dashi,Ga hawaye nan bushe kan fuskarshi,toilet ya shige yaja ƙopa ya rufe,a Gaban sink ya tsaya fuskarshi duk ta yamutse,Ya damu sosai akan son sanin Halin Da Sehrish take ciki,Allah yasa tana raye bata mutu ba,baisan ina zai tsoma ranshi ba,

"Abban Junaid"!mommy ce ta kira shi,daga cikin ɗakin,Da sauri Ya kunna fanfo ya wanke fuskarshi sosai,Kafin Ya nufi ƙopar ya fito daga cikin toilet ɗin,

A tsaye ya sameta,tana jiranshi,
"Inason magana dakai,"tayi maganar batare data jira amsarshi ba,Ta ruƙo hannunshi suka ja gefe guda,
"Wani abu ya faru ne?naga canji akan fuskarka,"
"Babu komai,bana jin daɗi ne kawai,ki tayani da Addu'a,"
"Ni banyarda ba,inaji araina wani abu ya faru,kawai ka sanar dani,"
Shiru yayi yana wasi wasi acikin ranshi,kodai ya faɗa mata gaskiyar abunda ya faru,wata'kil ta taimaka mashi,ta wani 6angaren kuma yana jin fargabar ya sanar da ita cewa,SGR yana da Aure,baisan ya zata ɗauki abun ba,
"Ka tsareni da ido,Ka faɗamun mana,meke faruwa ne"
Juyawa ya ɗan yi tare da kallon Junaid,Sam hankalinshi baya a wurinsu,Ya lullu6e kanshi cikin bargo,
Mayar da idanuwanshi yayi kanta"Zan faɗa maki,Amma ba yanzu ba,"
Ruƙo rigarshi tayi"kodai ka faɗamun abunda ke damunka ko kuma wlh duk inda zaka je saina bika,"
Gyaɗa kai yayi"shikenan zan faɗa maki,Amma dan Allah inaso ki fahimce ni........."natsuwa tayi tana sauraronshi,gaba ɗaya ya kwashe duk abunda ya faru tun daga kan auren Sgr da Sehrish da sukayi a 6oye har izuwa aika aikan da yayi mata yau,Don ance za'a rabashi da ita,Yayi tsammanin Mommy zata Balbaleshi da masifa,musamman da yaga ta kafe shi da blue eyes ɗinta,batare data ƙyafta ba,

"kiyi haƙuri dan Allah,nasan nayi maki laifi da ban sanar dake ba,na damune sosai akan halinshi,Shiyasa na ɗauki shawarar abokina akan inyi mashi aure ko zai canza,wannan dalilin ne yasa mukayi amfani da wannan damar muka shirya hakan tsakanina da Abusufyan"muryarshi asanyaye ya ƙarasa maganar,yana kallonta,

Jinjina kai ta ɗan yi kafin tace"banji zafin auren da kayi mashi batare da sanina ba,Amma naji haushin Tursasa mashi da kuka yi akan ya saketa,Meyasa?Gashi yanzu kun jefa rayuwar yarinyar cikin hatsari,U made a mistake ku dukanku,U know him better than any other person, tunda ya nuna yana son tafiya da ita dat means yana sonta ne,tunda kasan yana da masu yi mashi aiki,,"ranta a6ace tayi maganar,

"Wlh nayi danasani sosai,laifin da rafayet yayi shine dabai miƙa wuya ba,Ya nuna cewa yana son ya tafi da ita don taci gaba da yi mashi aiki,maimakon Ya amince zai tafi da ita amatsayin matarshi,wannan maganar tashi ce ta harzuƙa Abusufyan harya tursasa mashi,Ni na goyi bayan Abusufyan ne,Saboda kafiyar da rafayet ya nuna,babu yarda banyi dashi ba akan Ya soke yarjejeniyar,amma yaƙiya,duk da dama bamu aura mashi ita da sunan yarjejiniya ba,tun tana yarinya Abusufyan ya bashi ita,........."dakatawa yayi da yin maganar yana sauke ajiyar zuciya,
Jinjina kai Mommy tayi kafin ta soma magana"Yanzu menene solution?Gashi babu wanda yasan inda ya tafi da ita,balle asan wani hali suke ciki,Babban tashin hankalinma idan Mahaifiyar yarinyar nan tasan cewa bata acikin gidan nan,Dole ta damu sosai,"_
"Ke zaki taimaka mun,kafin Allah yasa mu gano inda suke,kisan yarda zakiyi wurin kawar mata da tunaninta akanta,"
"Shikenan,Zanyi hakan,Amma pls kuyi kokari kafin rana ta faɗi asan inda suke,Sannan yakamata a bincika ɗaya daga cikin guest house ɗinmu,Zai iya zuwa can"_
Hugging ɗinta yayi don ba ƙaramin kwantar mashi da hankali tayi ba,
"Nagode sosai da shawarar da kika bani"ya ƙarasa maganar,tare da kama hanyar fita daga dakin,
"Allah yasa aje asa'a,"_
Ya amsa mata da Ameen kafin ya fuce,

Ta jima atsaye cike da zullumin abunda zai biyo baya,bata ji daɗin abunda Sgr yayi ba,tashiga damuwa sosai akan halin da Sehrish take ciki,fatanta Allah yasa yarinyar bata mutu ba,

Fucewa tayi daga cikin ɗakin,Ta nufi kitchen,Oumma tasamu tare da Hajiya azeema da Saude suna shirya abincin karin kumallonsu,kamar yadda suka yi jiya,Suna aiki suna fira,tunda tashiga kitchen ɗin,idanuwanta na akan Abu dake tsaye agaban Gas cooker tana motsa Farfesun da ta ɗaura,
Hajiya azeema ce ta lura da ita"Ina kwana Aunty,kin tashi lafiya,"daƙyar Mommy ta ƙaƙaro murmushin dole,
"Lafiya lou,sassanunku da aiki,Tun ɗazu naso na shigo kitchen ɗin,na tsaya wurin Junaid ne,"
Juyowa abu tayi suka haɗa ido da Mommy,murmushi tasakar mata,cikin girmamawa abu ta gaisar da ita,mayar mata da martanin murmushin tayi tare da amsa mata gaisuwar,Saude ma ta gaishe da ita,
Cike da zolaya,Mommy tace"Amaryar harrisun gwaggo,yau naga hada make up akan fuskarki,Shi kikayi ma kwalliya,"Cike da jin kunya,Saude ta ajiye wuƙar da take yanka kayan lambu da ita,Ta sanya tafin hannunta akan fuskarta,dariya su kayi gaba ɗayansu,
"Kamar wata me kunya,Ae gwaggo ta sanar dani komai,abar kaza cikin gashinta dai kar a fige,"ta ƙarasa maganar da zolaya,
A shagwa6e Saude tace"dan Allah Aunty azeema kidaina yarda da maganar Gwaggo....."bata ƙarasa maganar nan ba,Gwaggon katsina ta faɗo cikin kitchen ɗin,Jikinta sanye da waɗannan kayan baccin nata na gado ƴan ƙasar turƙiya,Duk sunyi squeezing sun cukuikuye,kanta ko kallabi babu duk hurhura,ta ƙwama glass baƙi kato akan fuskarta,
Tsayawa tayi tare da ruƙe qugu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,kafin tace"Waye ke kiran sunana?Wato ina can ina bacci ana nan ana yi mun munshari,"
Ƙumshe dariya sukayi gaba ɗayansu,dabsauri hajiya Azeema ta nuna Saude"Kin ganta nan itace ke kiranki,"
Uwar harara gwaggo ta watsa ma saude"Munafuki dai baiji daɗin rayuwarshi ba,Ae naji abunda tace,Wato adaina yarda da maganata,Ni ga mahaukaciya ko?Wlh saude kiji tsoran Allah,A haka kikeso In bari Harrisu ya aureki?kina yi mun rashin kunya?Allah ya kiyaye,Ae sai dai ki koma rigarku ki samu irinsu jauro ki aura badai harrisuna ba,"tayi maganar tana murguɗa mata baki,
"Gwaggo nifa ba haka nake nufi ba,dan Allah kiyi haƙuri idan na 6ata maki rai,
Guntun tsoki taja,kafin ta mayar da idanuwanta kan Abu,Lokaci guda ta soma washe baki"Ina ƴa'ƴan Abusufyan ɗina suke?yau har mafarkinsu nayi,"
Murmushi abu tayi"Gwaggo suna nan cikin ƙoshin lafiya,"
"Madallah,bari naje na dubosu,dan Allah ashirya masu lafiyayyen abinci,suci su ƙoshi,"
Hankalin Mommy ne ya tashi,Gudun kada gwaggo taje ta taras babu ɗaya daga cikinsu,Da sauri ta dakatar da ita,
"Gwaggo,ki tsaya mana,ga farfesu ya sauka,Yakamata ki ɗanɗana girkin Amaryar Abusufyan ɗinki,"
A sukwane ta juyo fuskar nan ɗauke da murmushi"dagaske abusufyan zaiyi aure"?
"Eh mana,Za'a maida aurenshi da zainabu abu,kinga nan bada jimawa ba zaki samu wasu ƴa'ƴan na Abusufyan,"
Wani irin farin cikine ya lullu6e gwaggo,Hada sanya hannu ta dafe saitin zuciyarta,
"Wlh bakiji daɗin da naji ba,Wayyo Allahna,Ranar dana daɗe ina jira gashi zata zo,Zainabu abu zata koma ɗakin Abusufyan,Ga harrisu shima zai angwance,dole inyi rawa," ta ƙarasa maganar tana kwaso shoki da hannuwanta,Gaba ɗaya suka fashe da dariya,

A 6angarensu Hayaam,Sun fuskanci matsanancin tashin hankali A gidan malam liman,Duk sun rame sun kode saboda yunwa,Ga tsangwamarsu da akeyi,aikin gidan gaba ɗaya ya dawo kansu,sune wanke wanke,Sune shara hatta dabbobin gidan suke wanke garkensu,duk yawan mutanan gidan Suke girka masu abinci,a ƙalla yana da ƴa'ƴa kusan talatin,Ga matanshi huɗu,Sun tsanesu sun addabi rayuwarsu,Wata rana kwatsam sai ga mahaifinsu Ya dawo Abie,Ya zama cikakken mutun,Yanzu babu asirin mammy ajikinshi,tun lokacin da Amal ta bashi waɗannan kuɗin ta gudu wurin Amani,Shima Ya gudu zuwa kano wurin wani Abokinshi,Acan ya fara ta6a kasuwanci,Labarin mutuwar mammy ne ya riskeshi acan ta hanyar wani ɗan uwanshi da suka haɗu dashi a nan kano ya sanar dashi komai daya faru ya kuma bashi shawarar ya dawo ya rungumi ƴa'ƴanshi,tunvkafin ya rasasu,

Wannan dalilin ne yasa Abie yayi tattaki zuwa Maiduguri,Lokacin da yayi arba dasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login