Showing 192001 words to 195000 words out of 307403 words
Chapter 65 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita,
_Sae da suka kammala hoton sannan ta lura da zoben diamond ɗin dake hannunshi,sae faman ƙyalli yake yi_
_Waro ido waje tayi alamar mamaki tace"wow junaid wannan fa,waya siya maka shi_
_Mommy azeema ce ta bani shi,dama ɗazu na sanar dake cewa zan nuna maki gift din da takawo mun,to itace wannan_
_Ya ƙarasa maganar yana nuna mata zoben da Wrist watch din_
_Junaid sunyi kyau wlh,musamman daya kasance kaine ka sanyasu_
_Thank u reesh,sunyi mun kyau amman idan ke kika sanyasu sae sun fi yi maki kyau,bari na ciro maki su ki sanya,nafison su kasance a hannunki_
_cikin sauri tace mashi"no junaid that's impossible,Auntynku azeema ce ta baka shi,muddin ta neme shi a hannunka bata ganshi ba zata nemi jin ba'asin inda ka kai su,kuma ma in banda abun ka junaid wannan ae irin naku ne!kamar diamond ne fa,nida ko zoben azurfa ban ta6a sanyawa a hannu ba,balle diamond_
A firgice Sehrish ta farka daga baccin da ya dauketa,mafarkin da tayi yayi matukar ɗaure mata kai,Zurfin tunani ta shiga lokacin guda ta gane wannan zoben da Junaid ya ta6a nuna mata Shi ne tagani a ɗakin Aunty azmee kamanninsu ɗaya Sak!tabbas kuwa shi ne na Diamond wanda Aunty azeema ta siya mashi mai harafin *j*
Wata irin zufa ce ta shiga gangaro mata agafe da gefen fuskarta,tunani ta soma yi mai yakai zoben Junaid a dakin Aunty azmee?Yakai mata ajiya ne,?sam bata kawo komai aranta ba,Amma tunawa da tayi cewa junaid duk inda zaije zoben nan na ahannunshi wannan yasa ta fara kokonton wani abu,Zumbur ta miƙe daga saman sallayar ta nufi saman gadonsu,
Lalla6awa tayi ta haye saman gadon,saitin wurin da Jahad take a kwance,hannu tasa tana ɗan bubbugata yayin da take ambaton sunanta a Hankali don kada ta tashi Oummansu,
"Jahad!jahad!"can cikin bacci jahad tajiyo muryarta,dakyar ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,ganin Sehrish yasa ta dan mike daga zaune"lafiya rishi?dama baki yi bacci ba?"
"Jahad duk ba wannan ba,wata tambayace nakeso nayi maki,A ranar da kuka fita tare da Junaid shan ice cream shin kin kula akwai agogon diamond da ring a hannunshi ko babu"?
'Meyasa kikayi mun wannan tambayar Sehrish!So kike ki tayarmun da hankalina?Kinsan fa banaso ana tunamun mutuwar Junaid,"tayi maganar hawaye na zuba akan fuskarta
Arude Sehrish tace"dan Allah ki sassauta muryarki Jahad,bana so kowa yaji,nasan baki so amma dan Allah ki yi hakuri ki amsa mun tambayata,"
Shiru Jahad ta ɗan yi da alama ta shiga zurfin tunani,kusan minti 5 kafin tace"Kamar naso naga zoben a hannunshi,Amma bazan iya tunawa ba gaskiya"
"Ko hoto baku ɗauka tare dashi ba"?
Rai aɗan 6ace Jahad tace"haba Sehrish sai kace wata ƴar jarida,irin waɗannan tambayoyi haka?
"Nidai ki amsa mun tambayata,"a kule tayi maganar,
Ganin ranta ya 6aci yasa Jahad cewa"Am Sorry,munyi hoto da junaid,hada ma videos muka ɗauka,Amma wayar bata a hannuna,Tana a wurin Ya Omar....."tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta fuce daga cikin ɗakin a fujajen.
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Abun ya ɗaurewa Jahad kai,irin wannan tambayoyi haka,Anya ba aljanu bane suka shige ta ba,
Babu kowa a babban falon,ko tsoro bata ji haka ta nufi Upstairs,gudu gudu sauri sauri take tattaka staircases ɗin,kaitsaye ta wuce bedroom ɗin Marshal Omar,sallama tayi jin anyi shiru ba'a amsa mata ba,Yasa ta fada cikin falon nashi,babu kowa a falon,da sauri ta nufi bedroom ɗinshi,a bakin kopar ta tsaya tare da Leƙawa cikin ɗakin nashi,A kwance ta same shi yana ta bacci,Ajiyar zuciya ta sauke,Cikin sanɗa ta shiga cikin ɗakin nashi,saɗaf saɗaf ta nufi side drawer dinshi dake a righ hand na gadon,Zuƙunnawa tayi agaban drawer chest din,Ta sanya hannu tana bubbuɗesu a hankali,tare da bincikawa ko zata ga wayar jahad,babu ita aciki,a hasale ta miƙe ta nufi wardrobe din kayan shi,gaba daya duk ta hargitsa kayan amma bata ga wayar ba,tsayawa tayi a tsanake ta shirya mashi kayanshi yadda suke,Bayan ta kammala jiki asanyaye ta nufi hanyar fita daga ɗakin dakatawa ta yi da yin tafiyar,Waiwayowa tayi tana kallon cikon ɗakin,tunani take yi kamar akwai wurin da bata duba ba,can ta tuna da Drawer ɗin dake ɗauke da mirror,da sauri ta juya izuwa gaban mirror ɗin,Janyo gida na farko tayi lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya,ganin Wayar Jahad ajiye aciki,
Saukowa downstairs tayi,a main palour ɗin ta zauna saman Sofa tare da kunna wayar don akashe take,Allah yaso babu password a wayar,
Direct ta shiga Gallery ɗin wayar,videos ta gani tare da hotunan dasu Jahad sukayi tare da juna,A hanzarce ta shiga kunna videos ɗin ta ƙura ido tana kallonsu,
Cikin motar Junaid shi da Jahad suka ɗauki video ɗin da take kallo,da hannu ɗaya yake ɗaukarsu video,yayin da dayan hannu ya rungumo jahad ajikinshi yana dariya,yana fadin"With My Juliet,My wife to be in sha Allah"
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rass!rass!a zabure ta miƙe tsaye tana kallon yatsun hannun Junaid dake sanye da diamond ring ɗinsa,ya Aza hannu saman sumar kan jahad Sosai Zoben ya fito mai ɗauke da harafin *J* sai ƙyalli yake yi
Abun yayi matukar ɗaure mata kai,a rude tace"Kai!junaid ya fita da zoben shi aranar!Ya akai zoben kuma ya koma ɗakin Aunty azmee?Taya akai hakan ta faru?Ta yaya zoben shi ya koma ɗakin Aunty azmee..?" tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Still bata kawo komai aranta ba,
Jiki na rawa ta nufi bedroom ɗinsu,asaman side drawer ta ɗauki wayarta da ta ajiye,kafin ta ajiye wayar Jahad asaman drawer ɗin,
Gaban mirror ta koma ta zauna saman kujera,Layin Aunty Azeema ta kira,Cikin sa'a wayar ta soma Ringing,'natsuwa tayi tana jiran ta amsa kiran nata,jikinta sae kerma yakeyi,Allah Allah take yi acikin ranta ta samu Aunty azeema ta ɗaga kiran,
Almost 15 missed Calls hajiya Azeema bata ɗaga kiran ba,A ƙarshe dole ta haƙura da kiran nata,ba don taso ba,saboda akwai wani muhimman abu da take so ta tambayeta kuma a wurinta ne kaɗai zata iya samun amsoshin tambayoyin da take dasu,
Ajiye wayar tayi gaban mirror ɗin,Kafin ta miƙe tsaye tare da kai idanuwanta ta kalli wall clock ƙarfe 2 na dare,
Dafe kanta tayi saboda matsanancin ciwon kan da ya farmata lokaci guda,a sakamakon tunanin da take ta yi,Zuciyarta tayi nauyi sosai,ga kokwanton da take yi,ga fargabar da take ji,Abubuwa dak sun tarar mata,
Don bala'e a zaune ta kwana,batare da ta runtsa ba,sai wuraren sallar asuba bacci ya ɗauketa can cikin kunnanta taji ana ambaton Sunanta sehrish sehrish,a firgice ta farka,idanuwanta a zare,
Oummansu ta gani atsaye tana kallonta"Sehrish A zaune kika kwana?meyasa baki tafi ɗakin Auntyn taku ba"?
Muryarta da alamun bacci bai isheta ba tace"Oumma,bansan bacci ya ɗauke ni ba,"
"Ki tashi kiyi sallah,Anata kira"ta ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin toilet,
Miƙewa tayi dakyar take iya ɗaga ƙafarta saboda baccin da take ji,zuwa ta fara yi ta hau saman gadonsu ta tayar dasu Hosana suka farka tukunna ta sauko,bayan kowa yayi al'wala,Abu ta shimfiɗa masu Sallaya suka kabbara Sallah,a tsanake suke yin sallar,Bayan sun kammala sallar ne sun zauna kowa ya ɗaga hannunshi suna addu'a,Sehrish ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa"Oumma,Jahad Hosana,dan Allah ku tayani da addu'a,Akan abunda nake yi,"
"Kada ki damu indai addu'a ce kin samu rishi,"acewar Oummansu,hosana tace"A nawa"?
Harara Sehrish ta wurga mata batare da ta tanka mata ba,
Suna cikin yin addu'ar nan,Wayar Sehrish dake ajiye gaban mirror ta soma ruri,A zabure ta miƙe tare da nufar wayarta,
"Kira kuma tunda Asuba?Wanene ke kiranki"?tsayawa tayi cak jin abunda oummansu tace,juyawa ta ɗan yi tare da kallonta,ɗan murmushi ta sakar mata"ummm dama Ina tunani ko Aunty Azeema ce ke kira ne"
"Okey,ki amsa kiran"da sauri Sehrish ta ƙarasa gaban dressing mirror ta dauki wayar tare da duba screen ɗin,Wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ganin kiran Aunty Azeema,
Juyawa ta ɗan yi kamar mara gaskiya ta saci kallon Oummansu dake zaune saman darduma,Hosana harta fara hammar bacci sai cewa takeyi"Wai Oumma addu'ar bata isa haka ba?Dan allah mu koma mu kwanta,murmushi abu tayi tare da kallonta,
"kije ki kwanta mana,Wani ya ruƙe maki ƙafafunki,ibadarma baki iya yi da abinci ne duk mun yawanshi sai kin tada shi....."jahad ce tayi maganar tana harararta,
Ganin hankalinsu ya koma kan Hosana yasa ta lalla6a ta fuce daga cikin ɗakin,Gudu gudu sauri sauri take tafiya,kaitsaye ta nufi hanyar nan da zata sadaka da wajen gidan,fitowa tayi ta nufi garden don batason kowa yaji ta,
A gefen wata bishiya ta tsaya,tare da duba Screen ɗin wayar missed call har 3 Aunty azeema tayi mata,Danna mata kira Sehrish tayi cikin sa'a Auny Azeema ta ɗaga kiran,
A hanzarce Sehrish ta kara wayar a kunnanta,tun kafin tayi magana Aunty Azeema tace"Sehrish lafiya kuwa?kin tashi hankalina,kawai ina farkawa yin sallar asuba sai naga missed calls ɗinki"
Muryar ta har shaƙewa takeyi saboda tsabar saurin tayi magana"Aunty azeema,babu abunda ke faruwa,lafiya lou nake,Dan Allah wasu tambayoyi ne nakeso nayi maki,Wani Assignment ne aka bamu a school,"
"Okey,Allah yasa nasani"
"Aunty azeema,Malamar da ta bamu assignment ɗin tana buƙatar muyi bincike akan wani accident daya faru ne,Sai mu sanar da ita amsar da muka samo,"
Natsuwa hajiya Azeema tayi tana sauraronta,
"Saurayi ne da budurwa,suka shirya zuwa shan ice cream,to akan hanyar zuwansu,sai suka dakata agefen titi,ita budurwar ta tsallaka titin zata siya musu ice cream,ta bar saurayinta acikin motar,kwatsam sai ga wata truck ƙatuwa tabi ta kan motarsu,nan take kuma sai wuta ta kama ci da motar,kafin ƴan kwana kwana su ƙaraso wurin,Wutar taci ta cinye,ba'a samu komai ba daga sassan jikin saurayin,
Katseta Aunty azeema tayi"ita malamar taku me takeso ku gano mata ne,"
"Bari na kai maki ƙarshen labarin,shi saurayin ya zama toka,sai ƙarahunan motar aka samu,to abun mamaki kawai sai kuma ga Zobenshi na Diamond an tsince shi a hannun wani dattijo,zoben bai yi komai ba,sai ƙyalli yake yi kamar sabo,to shine take son kowa yayi nazarin labarin ya fada mata abunda yake hasashe"
Abun mamaki tana kai ƙarshen labarin sai taji Aunty azeema na dariya,bubbuga ƙafa Sehrish tayi kamar tana agabanta"Wayyo Allah mommy azeema,meyasa kike dariya,dan Allah ki taimaka ki bani amsar tambayata,"
Tsagaitawa tayi da yin dariyar,sannan tace"Abun mamaki abun Al'ajabi,kawai sai aka tsinci zoben diamond ɗin saurayin a hannun wani,bayan shi mamallakin Zoben ya ƙone ƙurmus,Gaskiya Sehrish ta baku Assignment me wuya,Amma fa ni abunda nake tunani,in har babban Diamond ne kamar irin wanda na ta6a siya ma Junaid,nasan kin ta6a ganinshi a hannunshi mai harafin J,"
Muryarta har kerma takeyi wurin amsa mata"eh naganshi ahannunshi"
"Yawwa,so kin ga kalar wannan Diamond ɗin,In har wuta ta ta6a shi baiyin komai,Sai dai akwai wani abunda yake yi idan wutar ta haura mintuna tana ci ajikinshi,Stone ɗin jikinshi zaiyi duhu sosai,kuma ba hakan yana nufin ya mutu bane,Lafiyarshi ƙalau Amma fa wannan duhun da dutsen jikinshi yayi,A nigeria basu da chemical ɗin da zasu gogeshi,Sae dai anan dubai Companyn da nake siyayyar Diamonds ɗin a wurinsu ne kaɗai zasu iya goge wannan baƙin ya dawo yana ƙyalli"
"Amma Aunty Azeema me kike tunani game da Zoben da aka tsinta hannun wani dattijon?Wanda kuma ba'a gabanshi hatsarin ya faru ba,kuma shi saurayin da zoben ya shiga cikin motar Har ya haɗu da hatsarin"ta ƙarasa maganar tana jiran amsarta,don a ƙagare take,
Shiru Aunty azeema ta ɗanyi na wani lokaci da alama nazarin wani abu takeyi,
"Naji kinyi shiru mommy,"
Sai lokacin ta ɗaura da maganarta"Gaskiya abu biyu ne nake tunani,Shi wannan dattijon suspect ne,Amma kuma in har dagaske shi matashin da zoben ya shiga cikin motar,dole abu biyu ne zai kasance!Kodai Shi saurayin ne yayi wurgi da zoben ya faɗo daga cikin motar ko kuma mamallakin Zoben Yana raye!!Yayi escape daga cikin motar shiyasa har aka samu Zobenshi kuma lafiyarshi ƙalau zoben babu alamun wuta ta ta6a shi,kinga kuwa Shima mai zoben bai mutu ba a hasashe na kenan,
Gaban sehrish ne yayi wani irin mugun bugu,Hankalinta yayi matuƙar tashi,idanuwanta azazzare,jikinta har kerma yakeyi,
.."amma Aunty azeema,meyasa kike tunanin cewa mamallakin Zoben yana raye,"
"Wlh sehrish ni ko a school ban ta6a cin karo da question mai sarƙaƙiya ba irin wannan tambayar da kikayi mun,Gaskiya nidai nafi kyautata Zaton Shi Mamallakin Zoben ya ku6uta daga cikin motar,Ai kince ita budurwar ta tsallaka titi ne,taje siya masu ice cream.
Katse mata hanzarinta sehrish tayi"Amma fa Aunty,ita budurwar koda ta tsallaka titi,Shi saurayin sai da ya kira sunanta,ta juya har yana ɗaga mata hannu ta cikin motar,"
"Kinsan tazarar minti nawa ita budurwar ta ɗauka lokacin da mai ice cream ɗin yake zuba mata ice cream ɗin?
Girgiza kai sehrish tayi kamar tana agabanta haka take gani"A'a bansani ba gaskiya,"
"Idan har aka samu tazara koda na minti biyar ne,ita budurwar ta kawar da idonta daga kanshi,ta mayar da hankalinta wurin mai siyar da ice cream din,A wannan interval ɗin zai iya yiyuwa Ya ku6uta daga cikin motar,ko kuma an ɗaukeshi,Ni daga jin wannan labarin ma wlh duk shiri ne aka tsara don a caza maku brain ɗinku,kin sani sai surutu nakeyi ko breakfast banyi ba,"ta ƙarasa maganar da zolaya,
Dariya Sehrish tayi tare da cewa"Am sorry Auntyna,thank u so much Aunty Azeemana,Kin taimake ni sosai,Yanzu na samu amsar da nakeso,"
"Kada ki damu Daughter,duk lokacin da wani abu ya shige maki,ki sanar dani kawai a shirye nake dana baki shawara"
Murmushi sehrish ta saki,har sunyi sallama zata kashe wayar da sauri hajiya azeema ta dakatar da ita "Wait!kince saurayin ya zama toka ko"?
"Hakane,"ta amsa mata,
"Taya za'ace ko ƙashin jikinshi ba'a samu ba?wutar tayi more than one hour ne tana ci?ba kince an kira motar kwana kwana ba,"
"A'a banda masaniya akan wannan amma zan tambaya,"
"Okey,akwai wani incident daya ta6a faruwa, makamancin labarin da kika bani,almost 30 mins wutar naci A motarsu,ba'a kashe wutar ba,saboda babu wasu a kusa,Ko daga baya da mutane suka zo aka kashe wutar an samu wasu konannun 6angarori na jikinsu,duk da zai iya faruwa dagaske ae yasha faruwa ma,mutun ya ƙone ƙurmus sai tokarshi,ko indiyawa ma ai suke ƙona gawarsu su kuma ƙulle tokar in zasuyi jana'iza Amman kinga ai wutan tana daukar lokaci tana kona gawar,Amma nidai gaskiya a labarinki Ban yadda cewa Wannan mamallakin Zoben ya mutu ba!!Amsar da zaki ba malamar ku kenan!Ki sanar da ita duk wani bayani da nayi maki,Nasan zata baki mark sosai,"
Jiki asanyaye sehrish tace"in sha Allah Aunty azeema,Zan rubuta duk wani bayani da kika yi mun nagode sosai,"
Daga haka su kayi sallama,kamar jira takeyi ta katse kiran,jiki a mace ta zauna gefen bishir,Ta gaza yadda da abubuwan da kunnuwanta suka jiye mata,Dama kuma it will be very hard farat ɗaya ta fara suspecting ɗin Azmee,Bakomai yafi tsaya mata arai ba,fa ce waɗannan tambayoyin masu matuƙar wuyar amsuwa Junaid yana raye ko ya mutu?taya akai zoben Junaid yaje ɗakin Aunty Azmee?kodai zoben aljani ne yana da fiffike harya tashi sama ya fito daga cikin motar da fika fikinshi yazo ɗakin Aunty azmee?Sai lokacin ta soma tunanin wai ma wacece Aunty azmeen nan?tunda suke atare da ita,bata ta6a bata labarin danginta ba,kwata kwata bataso a tambayeta dangane da danginta,Sannan kuma tunda take da Aunty Azmee bata ta6a cewa zata je gano gida ba,Uwa uba kuma Aunty azmee bata ta6a gajiyawa dayi masu aiki ba,A ƙalla idan zata lissafa shekarun Junaid da akace ta shayar dashi tun yana jinjiri,Azmee tayi more than 20 years a gidan,
Zurfin tunani ta shiga yi,maganganun ya sayyadi ne suka shiga dawo mata acikin kanta,inda yake cewa kaf family dinsu a tafin hannunsu suke,Duk wani motsi nasu akan idanuwansu suke,Kenan Suna da ɗan leƙen asiri acikin gidan?Dolen doliya akwai wanda ke shirya wata maƙarƙashiya acikin gidan,Tunawa tayi da wannan malamin makarantar nasu Ya Mu'allim da ya ta6a bata ruwan addu'a ta sha saboda yawan bacci da take a aji,lokacinne kuma ta Manta dasu Hosana kwata kwata,Tabbas Akwai abunda akayi mata,still Sehrish bata fara zargin kowa ba kuma har lokacin bata sanyawa ranta cewa Aunty Azmee tana da sa hannu a Mutuwar Junaid ba,Tama fi zargin Haroon don yasha sanar da ita cewa Zai kashe farin cikin gidan,Duk da tana doubting akan kalamanshi,Saboda shi ɗan giya ne yawancin kalamansu suna faɗi ne ba don su aiwatar ba,koba don haka ba,tana ji aranta cewa Haroon bazai iya kashe junaid ba,
Sehrish bata bar wurin bishiyar nan ba,Har sai da ƙarfe 10 ta buga,kamar wadda tasha ƙwaya haka take tafiya,Ga wani matsanancin ciwon kai da ya rufar mata,Ta caza ƙwaƙwalwarta sosai,
Lokacin da ta shigo cikin gidan,ta ƙopar da ta fita,kaitsaye bedroom ɗinsu ta wuce,Tura ƙopar ɗakin tayi ta shiga,Oummansu ta samu zaune gefen gado tana shan Coffee,
Jin motsin shigowar sehrish ne yasa ta ɗago da idonta tana kallonta,
"Ina kika je ne?har muka kammala yin breakfast baki dawo gida ba,"
Daƙyar ta iya buɗe baki tace"na shiga garden ne shan iska,"gudun karta ƙara tambayarta yasa tayi saurin cewa"Oumma,Coffee kike sha"
"Azmee ce ta kawo mun shi yanzun nan,"
Murmushin yaƙe sehrish ta dan saki tare da samun wuri gefen oummansu ta zauna,
"Ba zaki ci abinci bane"?cike da kulawa tayi mata maganar,
"A'a,na ƙoshi bana jin yunwa sai zuwa anjima zanci,"
Miƙa mata cup ɗin hannunta tayi"kar6i kisha,"batayi mata musu ba tasa hannu ta kar6i Cup din takai bakinta tana sha,kur6a uku tayi ta dakata da shan Coffee ɗin tare da kallon Oummansu,
Ganin tana kallonta yasa tace"Lafiya,kike kallona?"
Murmushi sehrish ta dan yi "babu komai oumma,kawai inaso na tambayeki wani abu ne,"
"Ina sauraronki"
"Amm oumma,jiya naga kin ɗan razana da kika ga Azmee,kinsanta ne?
"Kamar nasanta amma bazan iya tunawa ba,"
"Dan Allah Oumma kiyi ƙoƙari ki tuna,"
"Shikenan,idan na tuna zan sanar dake,"
Ba ƙaramin daɗi taji ba,Miƙewa tayi da sauri ta nufi toilet,Shaf shaf tayi wanka,lokacin da ta fito bata samu Oumman tasu da ta batari a azaune ba,babu kowa a ɗakin,
Tunani ta shiga yi ko Sgr Yana acikin gidan?tanaso taje ta duba lafiyarshi amma tana fargabar a wani hali zata same shi,dan kwanakin nan sam baya buƙatar kowa atare dashi,
Wani haɗaɗɗen lace ta ɗauko Ash colour sai ƙyalli yakeyi,riga da skirt ne,Sanya kayan tayi a jikinta,sunyi mata cuf cuf sun bi shape ɗin jikinta,Ɗinkin ya fito da ita sosai,kashe ɗaurin kallabi tayi,bayan ta ɗaure gashin kanta da ribbom,Gaban mirror ta koma ta zauna ta fara yin make up,murza wanccan shafa wancan manna wancan,kamar Aljana haka ta koma tayi kyau Over,
Wayarta ta ɗauka,ranta ne ya bata cewar ta