Showing 270001 words to 273000 words out of 307403 words

Chapter 91 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

mamakin kalaman sehrish basu ta6a tsammanin zata iya furta su ba,gaba ɗaya ammi ta karancesu tsaf,

Gyaran Murya ta ɗanyi,hankalinsu ya dawo kanta,yayin da idanuwanta ke akan Sehrish dake ta faman matsar kwalla,
  "Share hawayenki,kukan ya isa haka!Ae dama nace zanyi maku adalci atsakaninku,To ki kwantar da hankalinki,"jin wannan maganar yasa Sehrish taji hankalinta ya kwanta,

  "Amma inaso ki natsu kiyi tunani kafin ki yanke hukunci,don na lura kina acikin fushi sosai,kada kiyi irin kuskuren da iyayenku suka yi na tursasa mashi akan Ya sake ki,wanda silar hakan ne yasa shi rafayet din Ya huce akanki,daga baya akazo ana danasani,to banaso kiyi danasani daga baya jikata,Tabbas Rafayet bai kyauta maki ba,amma inaso ki sani saboda son da yake yi maki ne duk yajawo hakan,saboda bayaso a rabashi dake,yayi tunanin hakan shi zaisa abarmashi ke sai dai kash Yayi abu cikin fushi,kuma daga baya yazo yana danasani,sannan kuma karki manta da kanshi ya gyara 6arnar da yayi maki,wanda da ace da mugunta yayi maki zai tafi ya barki ne,Kiyi rai ko ki mutu,Amma saboda yasan bai kyauta ba,Ya tsaya har sai daya ga kin samu Lafiya,Ina faɗa maki wannan ne ba don ina goyan bayanshi ba,Sai don ina guje maki yin danasani,musamman idan ya kasance kinason Shi tun fil,azal,"Ajiyar zuciya ammi ta ɗan sauke bayan takai ƙarshen maganarta,ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu,ɗakin yayi tsit baka jin komai sai shessheƙar kukan Sehrish,

Cigaba da magana tayi a tsanake"zan tambayeki a karo na ƙarshe,Amma inaso Ki fara yin tunani kafin ki bani Amsa,kinaji ko"?

Cikin shessheƙar kuka tace"Eh ammi,"
Ita kanta ammin bason rabasu takeyi ba,don ta fahimci akwai soyayya mai ƙarfi atsakaninsu,daƙyar ta iya buɗe baki tace"Har yanzu kina akan bakanki na son rabuwa dashi"?cike da fargaba ammi tayi maganar,ba ita ba hatta su Mommy,kowa hankalinshi ya tashi,Sgr kuwa tuni Ya karaya,ya rufe fuskarshi da tafin hannunshi,

Cike da kwarin guiwa tace"Eh,Nidai arabani dashi,"yadda kasan Ya shako wuyanta haka yake ji,takaishi ƙarshe,tuni ciwon kai ya farmasa,

Duk yadda Abusufyan yaso ta ɗago su hada ido don ya dakatar da ita,Amma yarinyar nan ta kafe,taki kallon kowa daga cikinsu,

Jinjina kai ammi tayi"Shikenan,rafayet ina fata kaji abunda tace!tana buƙatar ka sake ta,"Yadda kasan tayi magana da bango haka Sgr yayi masu shiru,baice uffan ba,domin kuwa baya acikin hayyacinsa,Sama sama yake jinsu,

"Amma kuma wani hanzari ba gudu ba,"ammi ce tayi maganar tana kallon Sehrish,
  "Har yanzu da sauran jikinki kuma shine likitan dake dubaki,ni aganina,me zai hana ki bari kiji sauƙi sosai sai ya sake ki?Ni nayi maki alƙawarin da zarar kinji sauƙi zansa ya sake ki,"
Tunda Ammi taso ma magana,Abba ya fara sakin murmushin gefen fuska,don ya gane wayau ammi takeso tayi mata,don tasan kafin lokacin zaiyi wuya in bata sauko daga fushin da take yi dashi ba,
  "Ki amince Sehrish,kinga baki da lafiya kuma shi kaɗaine zai iya dubaki acikin gidan nan,shi yasan kan abun,kuma kinga da igiyar auran nan kawai zai iya yin hakan,"Hajiya Azeema ce ke yi mata raɗa acikin kunnanta,shiru sehrish tayi da alama tana yanke shawara da zuciyarta ne,ita aganinta za'a iya ɗauko wani likitan yaci gaba da dubata ba dole sai shi ba,tana kokarin bude baki tayi magana Hajiya azeema tayi saurin cewa"Ta amince,"
  Ammi tace"Nafiso naji ta bakinta,"
  Nauyin Hajiya azeema da take ji ne yasa tace"Na amince,"saboda bata son ta ƙaryatata," dama da biyu Hajiya Azeema tayi mata hakan,don tasan Sehrish bazata Iya musawa ba,in har tasa baki,"

  Ajiyar Zuciya kowannansu ya sauke,har Lokacin Sgr bai ɗago ya kallesu ba,

"Shikenan magana ta ƙare,Zamu zuba ido har Allah ya baki Lafiya,daga nan ni kuma zan Kar6ar maki takardar sakinki,"tana kai ƙarshen maganar,Tace ma azeema"Ki taimaka mata,ta koma ɗaki,"
  "To ammi,"ta amsa tare da ruko sehrish ta miƙe daƙyar,suka fuce daga dakin,

Bayan fitarsu ammi taci gaba da magana"kar kuga laifinta,tana cikin wani hali ne wanda dama karshe hakance zata faru,anma ci sa'a da ta dawo hayyacinta don mafi akasarin wadanda irin hakan ya faru dasu sukan fita hayyacinsu tsawon lokaci wasu ma ta6in hankaline ke samunsu,yayin da wasu kuma daga haka sai su fara tsoron maza....." dan dakatawa tayi sakamakon shigowa da Hajiya Azeema tayi,ta koma kan hannun kujeran data tashi ta zauna,

Ammin ta dasa"kamar ita dae,na tabbatar bata rasa son shi kawae abunda yayi mata ne yasa take tsoron cigaba da zama dashi",
"Tabbas Ammi tana son shi wllh don ni shaida ce baki na da nata munyi maganar lokacin da aka daura masu Auren,wanda hakanne ma yasa lokacin da ta gano dalilin da yasa ya auretan ba don yana sonta bane don tayi masa aikine yasa ta shiga wani hali har ta kulle kanta acikin Toilet"Hajiya Azeema ce tayi maganar,gaba daya suka shiga jinjina kai,
Kallon Sgr Ammi tayi wanda har lokacin tafin hannunshi na rufe da fuskarshi,sai dae duk abunda suke fada yana jinsu,

"Rafayet",Ammi ta kira sunanshi,a hankali ya zame tafin hannunshi ya kalleta, blue eyes dinshi sun canja launi don ba karamin sarawa kanshi ke mashi ba,
"Matarka tana son ka tunda ga tabbaci nan daga Azeema,muma kuma ba son rabuwarku muke ba,don haka inason kayi amfani da wannan damar dana samar maka wurin ganin ka shawo kanta daga dokin zuciyar da ta hau,kaima kuma inason na kara jan hankalinka,ba komae ne karfi ke samarwa Mutun ba,wani abun in kace zaka sa mashi karfi to kuwa zaka rasa shine gaba daya kamar dae aurenka yanzu,inason kabi komae a hankali in sha Allah komae zai zama daidai,sannan wannan bakar zuciyar dole sai ka rinka yin yaki da ita,ka rinka neman tsari daga wurin Allah akan ya rabaka da sharrinta don in dae zaka rinka yanke hukunci cikin fushi to wllh ka dinga yin dana sani kenan,A duk lokacin da wani abu ya 6ata ma rae kayi kokarin ganin ka daidaita natsuwarka kafin ka yanke hukunci,Yadda kake yin nasara Akan aikinka haka nikeson ka rinka yin nasara akan zuciyarka aduk lokacin da ta taso maka kaji?" dan jinjina mata kae yayi,
Cike da zolaya ta juya ta kalli su Abba tace"Yakamata a siyo mashi buta ya rinka yin alwala da ita,yana rage sauran ruwan yana sha ya daina yi a famfo ko Allah ya sanyaya mashi ita"gaba daya sukae Murmushi,shi dai still yayi bai tanka ba,

"Ko akwae mai magana?" gaba daya suka ce a'a,kallon Marshal Omar tayi"sai ka rufe mana da Addu'a"gaba daya suka daga hannu harda Mommy,Omar ya shiga jero Addu'oi daga bisani suka shafa.

Daga haka Ammi ta basu Iznin Tafiya,

ƙoƙarin miƙewa Sgr yayi wani irin Jiri ne ya soma ƙoƙarin kwasarshi,da sauri Omar ya ruƙe shi,ya taimaka mashi har suka fita daga ɗakin,

A bedroom ɗinshi Omar ya shigar dashi,Kaitsaye ya faɗa yaraaaf saman gadon,jiki babu kwari,yadda kasan baya numfashi,hawa saman gadon Omar yayi,Yasa hannu ya cire mashi rigar jikinshi,ganin yadda zufa ke tsastsafowa daga jikinshi,

"Bro,Are u not feeling well"?yayi tambayar yana kallonshi,ya runtse idanuwanshi sai faman Cizon pink lip ɗinsa yake yi,daƙyar ya iyacewa"Omar,zuciyata babu daɗi,yarinyar can ta 6ata mun rai,wai har ni zatace bataso?bata ra'ayin zama dani?wacece ita?mata nawa suke neman wannan damar a wurina"?......daƙyar sautin muryarshi
ke fita,da wani irin hucin zafin zazza6in jikinshi,

murmushin gefen fuska Omar ya saki,wato har yanzu rafayet bai gane cewa Ya afka tarkon so ba,babban takaicinshi Yadda Sehrish ta furta bata ra'ayinshi agaban kowa,ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,

"Am sorry bro,just forget about her,idan ka shareta zata dawo maka ne"
  A hasale yace"tafita daga cikin zuciyata mana,"
  Ƙiris ya rage Omar ya fashe da dariya,Aranshi yace"Kaine ka sanyata acikin zuciyarka malam,"
   Miƙewa yayi daga kwancen da yake,Ya sauko ƙafafunshi ƙasa,sumar kanshi duk ta rufe mashi gefe da gefen fuskarshi,
    "Zan shiga toilet,pls before na fito,ina bukatar magani ciwon kai,"yana kai ƙarshen maganar,ya sauko daga saman gadon Ya nufi toilet ya shige,kafin ya fito Omar ya ajiye mashi medicine ɗin asaman side drawer tare robar ruwa,

Sehrish kuwa,bayan mommy azeema takaita ɗakinsu,Saman gadon ta haye fuskarta sharkaf da hawaye,taso ace Sgr ya sake ta,don yanzu batason duk wani abu da zai alaƙantata dashi,ta wani 6angaren kuma taji daɗin hukuncin da Ammi ta yanke,koba komai tayi mata alƙawarin zata amsar mata takardar sakinta,

Tana cikin yin wannan zancen zucin nata,Hajiya azeema ta turo ƙopar ɗakin fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa,xama tayi daga gefen gadon cikin sanyin murya ta soma magana"Why sehrish?Don me zaki nemi ya baki takardar sakinki!Ba kina sonshi ba"?
  cikin shessheƙar tace"Yanzu bana sonshi aunty azeema,bana iya rayuwa dashi,Nidai kawai nafison arabani dashi,"
  "Indan kan abunda yayi maki ne yasa kika yanke shawarar rabuwa dashi,to kuwa zaki tabka kuskure,Domin kuwa Kina sonshi,Kuma shima ba ason ranshi yayi maki haka ba,Kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin so yake yi maki ba,wanda silar hakan yasa shi yi maki haka duk don kada araba shi dake....."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar
  "Aunty azeema,wlh baya sona,bani yakeso ba,kema kinsani yana yin amfani dani ne kawai don biyan buƙatarshi,Sannan don naci gaba dayi mashi aiki,ba amatasayin matarshi ba,tunda nake dashi bai ta6a furta mun kalmarso ba,"tana magana hawaye na wanke fuskarta,
  Shiru azeema tayi tana kallonta,Lamarin Ya fara bata tsoro,don dagaske sehrish take yin maganarta
Cikin sigar lallashi tace"Haba sehrish,duk irin wahalar dana sha wurin ganin na gyara tsakaninki da Sgr saboda in taimaka maki ki samu soyayyarshi,amma shine kike ƙoƙarin lalata mana shirinmu why pls"?cike da takaici tayi maganar,
"Am sorry aunty azeema kada ranki ya 6aci,Wlh yanzu bana sonshi,Ko son kallon fuskarshi ma banayi,"
  Jinjina kai Hajiya azeema tayi"Shikenan,tunda kin nuna baki sonshi,bazan tursasa maki ba,"shiru suka ɗanyi na wani lokacin kafin tace"inaso zanyi wanka,jikina duk yayi mun tsami,"
    "Okey,Yakamata ki dage da yin sit bath,ko kin dawo daidai,naga tafiya ma daƙyar kike yinta,kuma bazan fasa gyaraki ba,kamar yadda nayi niyya,zan ɗaura daga inda na tsaya ne,sannan cikin kayan dana kawo maki akwai wasu sabulai na nan,zasu taimaka maki sosai,idan har kika dage da yin amfani dasu"

"Shikenan,nagode sosai,"saukowa tayi daga saman gadon,a hankali take tafiya,Azeema na binta da kallo harta shige cikin toilet,Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta miƙe ta fuce daga ɗakin,

After some minutes,sehrish ta fito jikinta ɗaure da towel fari,gaban mirror ta zauna,ta jima tana kallon kanta,ta cikin mirror batare data motsa ba,ita kanta ta lura da sauyawar da tayi,kodan saboda jinyar da tayi ne yasa tayi haske sosai,Amma tafi tunanin Jinin Sgr ne da aka ƙara mata, yasa tayi haske,Anata shirmen,hannu tasa tana shafa ƙashin wuyanta daya fito,Ba ƙaramin kyau yayi mata ba,almost 15 mins,Tana zaune,kafin daga bisani ta mike,Ta koma gaban wadrobe ta budeta,doguwar riga ta ɗauko mara nauyi red colour ta zurata ajikinta,Lalla6awa tayi ta koma saman gadon,idanuwanta cike tab da ƙwalla tarasa meke yi mata daɗi,

Yinin ranar daga ita harshi babu wanda yaci abinci,saboda yanayin da suka tsinci kansu,ita tana kukan arabata dashi,Yayin dashi kuma yake neman mafita kafin lokaci ya qure mashi,Saboda tsabar farga duk in agogo ta buga sai gabanshi ya faɗi,saboda lokacine ke tafiya......'acikin bargonshi ya yini kiran sallane kawai ke fito dashi,kamar yadda itama Take ƙumshe acikin bargonta,Kiran sallah ne kawai ke tayar da ita,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 8:30 na dare sehrish na ƙumshe cikin bargo,ita kaɗai ta rage acikin ɗakin,Su jahad da oummansu sun fita wurinsu Mommy dake zaune suna fira a babban palourn gidan,tare da gwaggon katsina dasu hafsat,duk sun hallara a palourn,Hada wasu daga cikin matasan gidan,Gwanin ban sha'awa,

Turo ƙopar ɗakin akayi,Duk a tunaninta Sgr ne yazo dubata,tuni ranta ya 6aci,jin muryar hajiya azeema ne yasa ta leƙo daga cikin bargon,
  "Ya jikin naki"?
"Da sauƙi,"ta amsa mata a yayin da take kokarin mikewa daga zaune,ta sauko ƙafafunta kasa,
"Me zai hana ki koma ɗakin azmee da yin jinyar?nan kamar zaki takura ne,"
  Girgiza kai sehrish tayi"A'a,nafi jin daɗin zama anan,"
  "Gaskiya ni ban goyi bayan ki zauna anan ba,can sai kin fi sakewa,Yanzu haka ma daga can ɗakin nake,Na gyara maki shi,ki taso in taimaka maki ki koma can,kinga nan yayi maki kaɗan,kuma dama can kike kwana ae "
  Ba don taso ba,tace"toh,"
Miƙewa tayi hajiya azeema ta taimaka mata,suka fito daga ɗakin takaita ɗakin azmee,Lokacin da suka shiga cikin ɗakin,An gyara ko'ina tsaf sai ƙamshi ke tashi acikinshi,ita kanta ba ƙaramin kyau ɗakin yayi mata ba,"

Kaitsaye saman gadon ta hau ta kwanta,tana faman sauke ajiyar zuciya,
  'Bari na kawo maki dinner ɗinki nasan kina jin yunwa,"
  "Aunty kona ci,Amayar dashi nake yi,bakomai ke zama cikin cikina ba,bana jin daɗin abincin ma,"ta ƙarasa maganar,tare da jan bargo ta lullu6e rabin jikinta,
  "Kada ki damu,ba wani abu mai nauyi zan haɗo maki ba,in sha Allah,ba zaki amayar ba,". 
  "Toh,"iya amsar data bata kenan,
Bayan Aunty azeema ta fita daga ɗakin abakin ƙopar ɗakin ta tsaya,Hannu tasa cikin aljihun rigar jikinta ta ciro wayarta,

Call log ta shiga,ta danna ma layin Marshal Kira,Tana fara ringing ya ɗaga awayar,
  "Omar,ina rafayet din?Yakamata yazo ya dubata,yanzu haka na dawo da ita ɗakin azmeen,inaga kamar zasu fi sakewa anan,"
  On the other hand Omar yace"Yanzu zanyi mashi magana,nagode ssai,"
Daga haka su kayi sallama,Ta nufi kitchen,

After some minutes harta fara jin bacci,hajiya azema ta turo kopar ɗakin hannunta ɗauke da tray,Wanda ta shirya mata dinner ɗinta,a saman table ta ajiye mata shi,tare da janyoshi izuwa gaban gadon,
  "Ki daure ki ci,Zaki ji sauƙin jikinki,"
  Yunƙuwa sehrish tayi daƙyar ta miƙe zaune,ta sauko da ƙafafunta ƙasa,
   Wayar hajiya azeema ce ta soma ringing,Da sauri tace"ina zuwa,ki fara ci kafin in dawo,"tana kai karshen maganar tayi saurin fucewa daga ɗakin,

Ajiyar zuciya sehrish ta sauke,a hankali ta kai hannu ta ɗauki kofin tea mai zafi,takai bakinta tana kur6arshi a hankali,ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,tana cikin Shan tea ɗinnan,Taji an turo ƙopar ɗakin,Afirgice ta ɗago don taga wanene koda sukayi arba da Sgr,Nan take ta saki kofin hannunta,Ya faɗi ƙasa,ruwan tea ɗin data rage ya zube,

Abakin ƙopar ya tsaya yana kallonta,yayin da ya goya hannunshi asaman ƙirjinshi,wani irin daddaɗan ƙamshine ke fitowa daga jikinshi,Yana sanye cikin Sleeping dress dinshi,blue colour, hasken shi ya fito ssai,ya ɗaure sumar kanshi ta baya,Kyau Iya kyau,

Duk da taji tsoranshi,amma bata bari ya gane hakan ba,tuni ta ɗaure fuska,tare da kawar da idanuwanta gefe guda,

Slowly ya ƙarasa cikin ɗakin tare da samun wuri gefen gadon ya zauna a kusa da ita,gaba ɗaya ƙamshin turarenshi ya cika mata hancinta,sam bata so zuwanshi ba,yayi tunanin zata gaishe shi amma ko kallo wannan bai isheta ba,
  "Ya jikin naki,"?
daƙyar ta iya amsa mashi"da sauki,"
  Shiru su ka ɗanyi wani lokaci,bakomai yake tunawa ba,face maganar dasuka tattauna da Omar,
    "Laifin me na aikata maki da har kike son na sake ki"!
    Wannan tambayar da yayi mata ba ƙaramin 6ata mata rai yayi ba,wato baima son laifin da yayi mata ba,Saboda shi bai ɗauki abun serious ba,
  "Ko don saboda abunda ya shiga tsakanina dake ne"?
  Girgiza mashi kai tayi Alamar a'a,

Ya kuma cewa"I won't hurt you anymore,i promised u"
 Ko uffan bata ƙara ce mashi ba,ranshi ya 6aci sosai,hakanan ya daure yaci gaba da magana,
   "Its Okey,just calm down ur mind,da zarar kinji sauƙi,zanyi maki yadda kikeso,Hakan yayi maki"?.
  ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Hannu yakai tare da ɗaukar cup din data jefar,Ya haɗa mata wani tea din Ya miƙa mata,
  Hannu tasa ta kar6a,har lokacin bata ɗaura idanuwanta akanshi ba,
  Sosai tashiga shan tea din,don ba ƙaramar yunwa take ji ba,
  Abunda zai baka mamaki da kanshi,Ya shiga yin serving ɗinta,bayan ta kammala shan tea ɗin,Ya zuba mata farfesu acikin plate mai zafin gaske,yaso ya bata abaki amma sai ta nuna cewa zata Iyaci da kanta,natsuwa yayi yana kallonta,Daƙyar take ɗaukar Naman tana turawa acikin bakinta,Jurewa kawai yake yi,amma shi kaɗai yasan yadda yake ji acikin zuciyarshi,baisan ya zaiyi ya shawo kanta ba,gashi Omar ya gargaɗeshi akan ya guji 6acin ranta,kuma aduk lokacin da yake tare da ita,ya manta da matsayinshi na Suregon general,

Ganin ya sanya hannunshi acikin plate ɗinne,yasa ta dakata da shan farfesun,batare data ɗago ta kalleshi ba,sai ma cire hannunta da tayi,Har ya harzuƙa zai daka mata tsawa,Sai ya tuna sharuɗɗan da Omar ya bashi,a hankali ya furta Ya salaam,
  Sai da ya cire hannunshi daga cikin plate ɗin tukunna ta mayar da nata hannun taci gaba ci,'abun ya ɗaure mashi kai,Kuma ya kasa yi mata komai,,
   Turo ƙopar ɗakin hajiya azeema tayi fuskarta ɗauke da murmushi,hannunta na ruƙe da ledar magungunan sehrish,Asaman bedside drawer ta ajiye mashi ledar,"kafin ta juya ta nufi ƙopar fita daga ɗakin,A lokacin Amrish na ƙoƙarin shigowa ɗakin,su kayi kici6us da Aunty azeema,da sauri Amrish ta gaishe da ita,
  Fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa mata,
  "Lafiyalou,amrish har an gama firar"?
  "A'a,bacci nake jine,"
  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi,"mu tafi ɗakina ki kwanta,"batare da tayi mata musu ba,tabita suka nufi ɗakinta

Bayan sehrish ta kammala cin abincin,ya bata magungunanta,kafin ta gyara kwanciyarta saman gadon,Sai faman hura hanci takeyi,ita duk atakure take jinta,saboda kallon Da sgr keyi mata,ta kosa ya tafi yabar mata ɗakin,a ƙarshe data lura daɗin kallonta yake ji,Sai ta janyo bargo ta lullu6e jikinta duka hada fuskarta,

Kusan minti 5 ta soma tunanin koya tafi ko yana nan oho,Hannu tasa a hankali ta ɗan zame bargon ta leƙo don taga idan ya tafi,Abun mamaki saita same shi zaune yana cin sauran abincin data rage,ta6e baki tayi kafin ta koma cikin bargon,tayi mamaki sosai,Ko meyasa yake cin kingin abincinta Ohom masa,

Bawan Allah,Duk yinin ranar baici abinci ba,saboda damuwar daya shiga,Shiyasa yake cin sauran abincin data rage,ko zai samu sauƙi acikin zuciyarshi,don ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,Bayan ya kammala cin abincin,Ya kora da ruwa mai sanyi,ita duk a tunaninta zai tafi ne idan ya kammala cin abincin,amma har wurin ƙarfe goma sha biyu na dare,Yana zaune gefen gadon,Ya kasa motsawa,ya saba da ita koda yaushe a irin wannan lokacin suna manne da junansu,ko yaje ɗakinshi bazai iya runtsawa ba,Kwarama ya zauna yana kallonta nannaɗe cikin bargo,zaifi samun natsuwa,


Boss Bature✍️


_Ina rokon Allah Ya bani Ikon Kammala Littafin Nan cikin sati mai zuwa I need ur prayers,ga duk mai buƙatar karanta Littafin abban Sojoji from book one two 3 ya tuntu6i ne,Amma ta whatsapp za'ayi mun magana 08103884440_






 



 
 

 
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖 *ABBAN SOJOJI* 💖
💖💖


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login