Showing 207001 words to 210000 words out of 307403 words

Chapter 70 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

kallon Mommy"ina kwana mommy an tashi lafiya,
  "Lapiya lou Daughter,"
Komawa tayi kan Daddynsu"Ina kwana daddy kun tashi lafiya,"
Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya amsa mata"lafiya lou daughter,An sha bacci ko"?
  Dariya sehrish ta ɗan yi tare da kallon Oummansu ta gaisar da ita,Sai da tabi kowa ta gaisar dashi,tana ƙoƙarin zama Abusufyan yace'baki ga Aunty Azmee bane?naga kamar baki gaisar da ita ba,"
  Jimm ta ɗanyi kafin ta wurga eye balls ɗinta kan fuskar Azmee dake tsaye,murmushi ta samu akan fuskarta,
Ba don taso ba hakanan ta daure ta gaisar da ita"ina kwana Aunty Azmee,"
"Lafiya lou Sehrish,Yanzun nan nake shirin zuwa na taso ki sai gashi ma kin fito"
  Baki asake Abu da sehrish ke kallonta,Ta ƙware wurin iya kisisina da munafurci,
  Banza sehrish tayi,batare da ta tanka mata ba,
  Zagayowa Azmee tayi wurinta tare da kai hannu ta ɗauki plate,Warmer ta buɗe mai ɗauke da farfesun Ƴan cikin shanu,Ta zuba ma Sehrish ta tura mata shi agabanta,
  Zuƙunnawa tayi daidai saitin kunnan sehrish cikin raɗa tace"Nasan zaki ji daɗin shan farfesun nan,"
  Tana kai ƙarshen maganar ta miƙe daga tsaye,kallon Oummansu tayi da ido tayi mata alamar ta kwantar da hankalinta,
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke tare da zura yatsun hannunta cikin plate ɗin,A tsanake ta soma shan farfesun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,

Sai da ta nutsa cikin shan farfesun ta dinga jin motsin wani abu a hannunta,duk in takai hannu zata ɗebo ƴan cikin sai taji suna kufce mata daga hannunta kamar abu mai rai,hakan yasa takai idanuwanta cikin plate ɗin,Tsutsotsi ta gani suna yawo acikin plate ɗin manya manya,A wani irin firgice Sehrish tayi wurgi da plate ɗin ta fasa Uwar ƙara,Nan take ta shiga kwarara Amai,
Gaba ɗaya hankalin Kowannansu Ya tashi haiƙam,Mikewa tsaye su kayi suna kallonta,kowa na tambayar Lafiya,Da ƙarfi take ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Wayyo Allah na,Na bani na lalace Daddy,Oumma ku taimake ni,Naci tsutsotsi acikin cikina,
Tana magana amai na zuba daga bakinta,duk ya 6ata gaban rigarta jaga jaga,duk tabi ta gigice ta rikice,Watsa wa tayi da gudun gaske tana kuka ta nufi bedroom ɗinsu,A guje Suka bi bayanta
Toilet ta faɗa cikin fitar hayyaci ta nufi basin,Cigaba da kwarara aman tayi har saida takai ga babu abunda ke fitowa bakinta sai ɗigon jini ta ƙarar da koma da taci ko ruwa babu a cikinta,
  Soso ta ɗauko tare da detergent ta zazzaga shi abakinta,Adai dai lokacin suka ƙaraso ƙopar toilet ɗin,sunyi ƙoƙarin su tura ƙopar amma ƙopar ta datse sakamakon Bugata da sehrish tayi bayan ta shiga,Ƙwanƙwasa ƙopar suka shiga yi kowa na ambaton sunanta,
  'Sehrish!kizo ki buɗe mana ƙopa,kada ki Lahanta kanki fa,"muryar Oummansu ce keyi mata magana,tamkar zata fashe da kuka
Abusufyan ma murya na kerma yace"Wai baza ki buɗe mana ƙopa ba?meyake damunki ne?Dan Allah Daughter ki fito kiyi mana bayani,"
Kwata kwata Sehrish bata jinsu domin kuwa ta jima da makancewa,Ta fita hayyacinta,abunda ta gani a plate ɗinta keta dawo mata cikin kanta,
  Tura soson tayi abakinta,Ta dinga gurzar bakin,har saida Le6enta suka faffashe jini ya soma zuba ta ko'ina abakinta,daga waje suka dinga jin Azababben kukan da Sehrish ke yi,na tashin hankali,
  Da gudun gaske Abusufyan yabar ɗakin kaitsaye ya nufi upstairs don ya sanar da Sgr,Suzo su 6alle ƙopar kada ta kashe kanta,

Lokacin da ya shiga Part dinshi ko sallama babu,faɗawa kawai yayi gudu gudu sauri sauri ya shiga bedroom ɗinshi,Sai faman haki yake yi,A kwance ya sameshi yana bacci jikinshi sanye da jallabiya,
  Tun kafin ma Ya ƙarasa wurin gadon ya shiga ƙwala mashi kira"Rafayet!Rafayet!!"
  Farkawa Sgr yayi lokaci guda ya wurga idanuwanshi masu ɗauke da bacci kan Abusufyan dake ta kwala mashi kira,
  "Uncle lafiya"?
"Ina fa lafiya!Ga sehrish can zata kashe kanta acikin toilet,bamu san meke damunta ba,sai ihu take tana kuka,Munyi munyi mu buɗe ƙopar ta datse ta,"
  Tunkafin Ma Abusufyan yakai ƙarshen maganarshi,Sgr ya sauko daga saman gadon,da wani irin sauri ya fito daga part ɗin,gudu gudu sauri sauri Ya nufi bedroom ɗinsu,Abusufyan kuwa bai baro Upstairs ɗin ba sai da ya wuce ɗakin Omar ya taso shi daga baccin don abun kowa ta shafa,

Lokacin da Sgr ya ƙaraso ɗakin abun ya tashi hankalinshi sosai,Tunda ya shigo corridor ɗin ɗakin Ya fara jin sautin kukan da sehrish keyi,Tamkar ana zare ranta daga jikinta,
  A sukwane ya faɗa cikin ɗakin,Ganinshi yasa suka matsa mashi daga wurin ƙopar,A zafafe ya daddage ya bangaji ƙopar da ƙafaɗarshi,Nan take ƙopar ta buɗe,Faɗawa cikin toilet ɗin yayi a lokacin Harta yanke jiki ta faɗi ƙasa,jinin da ya gani jaga jaga ajikin basin ɗin ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,inda take kwance kasa ga soso nan a gefenta ga kuma ledar detergent ɗin da ta fasa,Bakinta yayi jaga jaga da jini fatar le6enta ta munana duk rauni,
  Jikinshi Yayi mugun sanyi,yaso ace tun lokacin da ta fara haukan suka sanar dashi,slowly ya zuƙunna agabanta,tare da kai hannu ya tallabo kanta,da hannu ɗaya,Ɗayan hannun kuma zura shi yayi cikin bakinta Ya buɗe shi,runtse idanuwanshi yayi yayin da zuciyarshi ke ta faman tafarfasa,harshenta gaba ɗaya ya faffashe,detergent ɗin yayi mata illa sosai,duk ya sale fatar harshen nata,Yaji raɗaɗin abun har cikin zuciyarshi,miƙewa yayi azafafe ya juya yana kallonsu dayake duk sun shigo cikin toilet ɗin,Oummansu sai kuka takeyi,Haka su Jahad da Hosana ma,
  "Tun yaushe ta fara wannan abun?meyasa ba'a sanar dashi ba!"a ruɗe yayi maganar
  "Rafayet yanzu duk ba lokacin wannan bane dan Allah ka taimaka,kada mu rasata,"Abbansu Yayi maganar fuskarshi duk a hargitse

Juyawa yayi tare da sanya duka hannayenshi ya ɗaukota tare da ɗaurata saman kafadarshi,Ya fuce da ita daga ɗakin,A hanzarce Ya haura da ita Upstairs part ɗinshi,A saman gadonshi ya kwantar da ita,da sauri ya kuma saukowa down bayan ya ɗauki key Ya nufi medical Room ɗinsu,da kanshi Ya shiga duba Sehrish koda ta farfaɗo tana koke koke Allurar bacci yayi mata,


kowa ya shiga damuwa,abincin ma duk sun ƙoshi dashi,A ƙarshe saman Sofa kowa ya zauna cike da jimamin halin da Sehrish ta shiga,Abun ya ta6a masu zuciyarsu sosai,
Har lokacin abu bata daina kuka ba,Haka Jahad da Hosana ma
  "Dan Allah ku kwantar da hankalinku,In sha Allah Sehrish zata samu lafiya,"acewar Kanal yousouf,
  "Kusan kashe kanta tayi fa,Omo ta zuba abakinta ta wanke da soso,Ni bansan meke damunta ba,Sae faman ambaton tsutsa takeyi ni banga komai ba a plate ɗin abincinta,"Abusufyan ne yayi maganar idanunshi cike tab da kwalla,
"Dole akwai wani abun dake damunta,ni tsorona ma kada ta Zauce"
Abba da Mommy sai kwantar musu da hankali suke yi,
 
Hannun Abu sae kerma ya ke yi,acan ƙasan zuciyarta kuwa,tunanin yarda zata fallasa Azmee take yi don tasan cewa itace Silar Halin da Sehrish ke ciki,tayi jinkiri ne saboda bata jima da zuwa gidan ba,ba lallai bane su yarda da maganarta ba,

Miƙewa Tayi tare da kama hanyar zuwa kitchen,tana shiga ta samu Azmee tana gyara kitchen ɗin,hankalinta kwance,
"Meyasa kika yi mata haka"?ɗagowa Azmee tayi tare da kallon abu dake tsaye,lokaci guda ta saki murmushin gefen fuska tare da cewa"Bangane akan me kike magana ba"
  "Amma baki da Imani!munafuka mai fuska biyu,kina son ki cutar da ita ne saboda kina tsoran karta tona maki asiri,shiyasa kike ƙoƙarin kashe mun ita"tana magana hawaye na zuba akan fuskarta,,
  Girgiza kai azmee tayi"ko kusa ni bani da alaƙa da Abunda ya faru da Sehrish!kada kiyi mun ƙazafi,Ni bazan iya cutar da Sehrish ba,Saboda ina jinta tamkar ƴar cikina....."
Tunkan takai ƙarshen maganar a fusace abu tace"karki kuskura ki ƙara kwatanta sehrish da ƴar cikinki!mushirika kawai,muguwa kuma azzaluma!Makira!Ni bana jin tsoronki,Da Allah na dogara ba da wani tsubbace tsubbace ba irin naku,waɗanda suka jahilcewa addininsu,har yaushe ne zaku gane gaskiya ku daina aikata irin wannan mummunan zunubin da kuke aikatawa ne?Kuna ɗaukar kanku tamkar wasu shaggu saboda kawai kuna taƙama da tsafin da kuke dashi,In banda ma daƙiƙanci da jakkanci da jahilci irin naku,Kun manta cewa Allah shi ya halicce ku kuma a kowani lokaci zai iya ɗaukar ranku,Kuma zaku koma gareshi sannan ku gir6i abunda kuka shuka,akwai ranar da wannan sihirin da kuke taƙama dashi bazai ta6a amfanarku ba!tunda baku isa ko mutuwa ku hana kanku ba....."
Tunkan ta ƙarasa Maganar Azmee ta daka mata tsawa har sai da abu ta girgiza"Ya isa haka!ke baki isa ki ce zakiyi mun wa'azi ba!Idan ilimin addini kike taƙama dashi,ko ƙafata baki kama ba!ke kinsani basai na faɗa maki ba,Idan da naso tun lokacin dana zo gidanki yi maki wankan jego da tun lokacin Na murƙushe ki ke da ƴa'ƴan naki,Amma banyi hakan ba don baki acikin ainihin abun hari na,Idan har kika cika zaƙewa Wlh Zaki rasa Rayuwarki ne!Zanyi silar da zaki bar duniyar nan ne!
  "Raina ba ahannunki yake ba!A hannun Allah yake,Idan har kinga na mutu to lokacina ne yayi,kuma koda ace Na mutu ta silarki,inaso ki sani kema wata rana zaki zo inda nake ne,kuma zaki yi bayani ne,banza kawai,ina ilimin da kike taƙama dashi ne?ai dake da dabba duk ɗaya kuke dan wlh ƙwara dabba dake Azmee,ita haka Allah ya halicce ta,Amma ke fa?mutunce wadda ta sani ta take sanin,ko yau kika faɗi kika mutu kinsan makomarki,babu ruwan Allah da ilimin da kike dashi,in har bakiyi aiki dashi ba,Toh ya tashi abanza don azabar da za'ayi maki ranar gobe ƙiyama tafi azabar da za'ayiwa kafiri,"
  Lokaci guda Azmee ta juye tamkar ba ita ba,ta fito da ainihin suffarta ta mugaye marasa Imani,Idanuwanta sunyi jawur dasu wani kalar huci ke fita daga bakinta da hancinta,Kalaman Abu sun ƙona mata rai,Kamar ta shaƙo wuyanta haka take ji,
  "Ki fita ki bani wuri Zainab!tunkafin Nayi maki Illa"
  A harzuƙe abu tace"kiyi duk abunda kika ga dama Azmee,Wlh bazan ta6a karaya ba,koda kuwa zan rasa rayuwata saina tona maki asiri mushirika kawai,"abu nakai ƙarshen maganar,taja dogon tsoki ta juya a fusace tabar kitchen ɗin,

Komawa Azmee tayi saman ɗaya daga cikin kujerun dining na kitchen ɗin ta zauna,maganganun abu ta shiga tariyowa acikin kanta,tunda take a rayuwarta Wani ɗan adam bai ta6a fuskantarta ba,Ido cikin ido ya gaya mata baƙaƙen maganganu ba,in ba abu ba,Itace ta farko kuma ta ƙarshe don taci alwashin duk wanda yayi yunƙurin exposing ɗinta saita Kashe shi har LAHIRA,

Runtse idanuwanta tayi lokaci guda ta shiga tunanin Sehrish,sam bataso hakan ta faru da ita ba,ta ƙetare Iyakarta ne shiyasa Ta jefa ta a halin da take ciki,

Da sallama Omar ya shiga part din nashi,A lokacin Sgr yana ta Zarya acikin bedroom ɗin,lokaci bayan lokaci yakan juya ya kalli Sehrish dake kwance tana bacci,Ba ƙaramin jiki taji ba,don ma Allah Yasa ta samu emergency treatment a wurinshi,Da ba'a son me zai biyo baya ba,

Sam baiji sallamar da Omar yayi mashi ba,har saida ya Ambaci sunanshi"Rafayet"tukunna ya juyo tare da kallonshi,
  Ƙarasawa wurinshi Omar yayi tare da dafa kafadarshi,
  "Ya jikin nata"?
"tana samun sauƙi,nayi mata allurar bacci ne,in ba haka ba bazata daina firgitar da take yi ba,"
  Ajiyar Zuciya Omar ya sauke tare da cewa"Allah ya bata lafiya,amma meke damunta ne?
"I don't even know,jira nake ta farka,Don in tambayeta,nasan zata faɗamun meke damunta,me take gani ne da yake razanar da ita,"
  "Haka ya dace,ƴan uwanta na son ganinta,Zasu iya shigowa yanzu?"Omar yayi tambayar yana kallonshi,
  Girgiza mashi kai yayi alamar a'a,sannan yace"sai dai zuwa anjima idan taji sauƙi,"
  Omar yace"Okey,"harya juya zai fita ya kuma juyowa,
  "Ya maganar Haroon"?
Sgr yace"Still bai farfaɗo ba,Nasan zuwa anjima zai tashi,"
  Gyaɗa kai Omar yayi tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,'
 

Wuraren Sallar Azhar gaba ɗaya suka tafi masallaci,Ya rage saura matan Acikin gidan,

Abu sam ta kasa samun natsuwa,gashi batasan ina aka kwantar da Sehrish ɗinba balle taje dubata,basu jima da kammala sallar Azhar ba,Abu ta mike tare da kallon Jahad"Inaso naga sehrish,gashi bansan inda aka kwantar da ita ba,
  Jahad tace"Tana a ɗakin Ya rafayet,nima inason na ganta,"ta ƙarasa maganar tare da miƙewa,hosana ma ta miƙe"Nima zanje ganin rishi ɗin,"

Kowannansu sanye da hijabi,Atare suka nufi upstairs,Da sallama suka shiga falon babu kowa,kaitsaye suka wuce bedroom ɗinshi,daga ciki suka shiga,gwanin ban tausayi haka suka tsaya cirko cirko abakin gadon suna kallonta,Tana bacci tana firgita,Numfashinta na fita daƙyar daƙyar,

Zama Oummansu Tayi daga gefen gadon Yayin da su Jahad ke atsaye,idanuwansu cike tab da kwalla,
  "Oumma wai meke damun rishi ne?duk tabi ta furgice ta fita hayyacinta,"
Hosana ce tayi maganar cikin shessheƙar kuka,
  Abu tace"ku tayata da Addu'a in sha Allah zata samu sauƙi ne,"
  Jahad tace"wlh dama ciwon ya dawo jikina,ita ta huta,Saboda taji jiki ba kaɗan ba,"
   Hannu abu tasa tare da shafa fuskar Sehrish,aikuwa kamar jira take yi taji an ta6ata nan ta fara sambatu da muryarta da bata fita sosae saboda ciwon cikin bakinta tana faɗin"ku kira mun shi,dan Allah ku kira shi,Ya mu'allim nake son gani,"lokaci guda kuma tadaina sambatun
  Kallon juna sukayi cike da mamaki,har suna haɗa baki wurin cewa"Ya mu'allim kuma?Wanene Shi"?
"Jiya tayi mun magana akanshi,Wai wani malaminsu ne Ya mu'allim,Ta sanar dani cewa Ya ta6a taimakonta,ko kunsanshi ne"?Tayi tambayar tana kallonsu jahad,
  "Ni ko sunan ma banta6a ji ba,"acewar hosana,
  Jahad tace"bazamu iya sanin malamin da take magana akai ba,tunda ba wurinmu ɗaya ba,"
  Addu'a suka shiga yi suna tattofa mata ajikinta,basu bar ɗakin ba sai wuraren sallar La'asar,Suka tafi banda hosana,tana zaune gefenta,ta kasa ta tsare sai rishi ɗinsu ta farka,

Bayan sallar La'asar,Abusufyan tare da Abba Suka shigo cikin ɗakin,a bakin gadon suka tsaya suna kallonta,A lokacin hosana ta fita daga ɗakin
"Banji daɗi abunda ya faru ba,Allah Ya bata lafiya,"cike da jimami Abba yayi maganar,
Abusufyan yace"tabbas akwai abunda ke damunta,tana faɗin abunda mu bamu gani ba,kuma a sanadin hakan ta kusa lahanta kanta,In har bamuyi kokarin gano abunda ke damunta ba,za'a iya samun matsala,"yana kai ƙarshen maganar Abba yace"in sha Allah hakan ma bazata faru ba,Yanzu dai ita muke jira ta farka sai muji daga bakinta,Tayi mana bayanin abunda ke damunta,"

Sunjima suna tattaunawa,Anan su kanal Yousouf da sauran matasan gidan suka same su,Kowa ya shigo ɗakin sai ya yi ma Abusufyan ya jikin Sehrish,daga bisani bayan Sgr Ya dawo ne suka ɗan basu wuri,Ya jima yana jiran farkawar Sehrish Amma babu alamun baccin nata zai ƙare,

Wuraren karfe 8 na dare,Sgr da Omar suka nufi Medical room ɗinsu Wurin Haroon,Lokacin da suka shiga a kwance suka same shi yana ta faman Jan numfashi,Idanuwanshi sunyi jawur dasu jikinshi sai kerma yake yi,

Tsayawa Sgr yayi tare da goya hannayenshi saman ƙirjinshi,Omar kuma wuri ya samu gefen gadon Ya zauna yayin da idanuwanshi ke akan Haroon
   "Ya jikin naka"?
Ba ƙaramin mamaki yayi ba,jin Omar yayi mashi ya jiki,yayi tsammanin da bugu zasu fara tambayarshi,
  Daƙyar ya iya buɗe baki Yace"babu sauƙi,Naji jiki sosai,Rafayet baiyi mun da sauƙi ba jiyan nan,dan Allah Ya Omar ka taimaka mun nasan kafi shi sauƙin kai,wlh ni babu ruwana kashe Junaid da nayi ma kuskure ne,Sharrin shaiɗanne,In fact ni bayin kaina bane....."a fusace Sgr Ya daka mashi tsawa"Idan ka kuskura ka sake ambaton shaiɗan a wurin nan saina Canza maka kamanni,akwai wani shaiɗanin daya wuce kaine"?
  Shiru yayi batare daya kuma cewa komai ba,Don bazai manta da lugudan wahalan daya shaba Adaren jiya,
A tsanake Omar ya soma magana"amsa ɗaya kawai nakeso a wurinka!Wanene yake baka Umarni?
  "Wlh bazan Iya faɗa maku ba,Ae ko ban sanar daku ba,in har rafayet zai iya sanin duk wani abu da nake aikatawa,Sanin wanda ke bani Umarni bazai gagare shi ba,Yasan Komai"
Haushi kamar ya shaqe shi haka yake ji,daƙyar ma yake magana saboda raɗaɗin ciwon da yake ji,Ga Yunwar da yake ji,ba don Omar ya hanashi Dukanshi ba,da ba abunda zai hana ya karairaya ƙasusuwan Jikinshi,ya tsani haroon kamar mutuwarshi,
  "Rafayet baisan komai ba,kai nakeso ka sanar dani!Haroon ka amsa mun tambayata,kai da Uban wanene kuke aika aika acikin gidan nan?"
Shiru haroon yayi,A hasale Sgr ya ɗaga Hannu zai mauje mashi kai,Omar yayi saurin ruƙoshi,"just leave him,Idan bai amsa mana ba,Wayar shi zata bamu amsa,"
  Basu bar ɗakin ba sai da suka ɗaure haroon jikin gadon sosai,Suka rufe bakinshi,Yarda baza aji Sambatun shi ba"
Datse ƙopar ɗakin Sgr Yayi,Sun jima suna tattaunawa da Omar kafin Ya wuce upstairs,Omar kuma ya nufi sashen su Abbansu,

Lokacin daya shiga bedroom ɗin,Still Sehrish bata farka ba,toilet Ya shiga,After some minutes ya fito sanye da bathrobe da alama wanka yayi,gaban mirror ɗinshi Ya tsaya yana kallon kanshi ta mirror,Abubuwa dayawa suna yi mashi yawo akanshi,yanzu baida burin daya wuce ya kawo ƙarshen maƙiyansu cikin kwanakin nan,da zarar ya gama dasu Zai fara tunanin komawa U.S,

Yana cikin zancen zucin nan,Ya fara Jin numfashin Sehrish dake fita da ƙarfi da ƙarfi,Da sauri Ya koma gefen gadon Ya zauna yana kallonta,A hankali ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,biji biji ta fara ganinshi,har sai da ta sanya hannunta saman fuskarta tana mutsustsuka idanuwan tukunna ta samu damar ganin shi da kyau,kwata kwata Jikinta babu ƙwari daƙyar ta samu ta miƙe zaune,Ciwo na yini ɗaya amma duk ta rame,idanuwanta duk sun faɗa,lips dinta sun dan kumbura,jikinta sai kerma yake Yi,

"How was ur body"?yayi tambayar Yana kallon Clavicle ɗinta,
Shuru bata bashi amsa ba,Sai dai zuba mashi ido da tayi tana kallonshi,Sake maimaita mata yayi"Ya jikin naki,"nan ma shiru bata bashi amsa ba,Cike da mamaki yace"Baki ji ina magana ba"
  Tunawa da ciwon bakinta ne yasa shi yin shiru,don yasan bazata iya magana ba sai a hankali,
  "If u can't talk to me,zaki iya yi mun alama ta yarda zan fahimci abunda ke damunki,"
Lumshe idanuwanta tayi tare da buɗesu a hankali
  "Are u hungry"?.
Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a,ba don taso ba,ita kaɗai tasan halin da take ciki,Ga matsiyaciyar yunwa tana ji amma fargabar abunda zata ƙara gani acikin abincinta take ji,
  Moving yayi kusa da ita,tare da sanya tafin hannunshi ya ruƙo kanta,A saman ƙirjinshi ya kwantar da ita,nan take taji natsuwa ta zo mata,hawaye ne suka soma zarya akan fuskarta,taso ace zata iya buɗe baki ta sanar dashi ainihin abunda ke damunta amma ta kasa,harshenta Ya raunata sosai,magana ma wuya take yi mata,
Shafa sumar kanta ya soma yi har izuwa tsakiyar bayanta,sosai ta manne mashi tana shaƙar kamshin jikinshi,
  "I really worried about it,pls Tell me what scared you?meyasa kike firgita"?
  Yayi maganar tare da mayar da hannunshi saitin zuciyarta dake ta bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunda ya aza hannun kuma sai heartbeat ɗin nata ya dai daita,
  Ƙanƙameshi tayi sosai,tana ji aranta kamar bazata rayu ba,tun da ta fara wannan ƴan gane ganen na tashin hankali,
  Waist


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login