Showing 210001 words to 213000 words out of 307403 words
Chapter 71 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
ɗinta Ya ruƙo tare da Janyeta daga jikinshi,Miƙa hannunshi yayi gaban drawer chest,Ya curo biro tare da jotter,
Miƙa mata yayi tasa hannu biyu ta kar6a
"Ki rubutamun duk wani abu dake damunki anan,"
Hannunta na kerma ta buɗe empty page ta soma rubutu,bayan ta kammala ta miƙa mashi jotter ɗin
Hannu yasa ya kar6a yana karantawa
_Oumma tasan komai,Ka tambayeta zata faɗa maka abunda ke damuna_
Wannan shi ne abunda Sehrish ta rubuta mashi,
ɗagowa yayi tare da kallonta suka haɗa ido,hannu ya zura cikin front pocket ɗinsa Ya zaro wayarshi,Nan take ya kira Fawan ya sanar dashi cewa Ya kira Mashi Oummansu,
Miƙewa Yayi ya nufi cikin ɗakin,sai gashi ya dawo sanye da sleeping dress ɗinshi riga da wando Maroon colour,Gefen gadon Ya koma ya zauna yana jiran zuwan Abu,
Kusan 15 mins,Abu tayi sallama a ƙopar ɗakin,
"Assalamu alaikum,"
"Wa'alaikum salam,"ya amsa mata tare da bata izinin shiga daga ciki,
Tana sanye da hijab ajikinta,Tunkan ta ƙarasa Sgr ya mike tare da janyo mata chair ɗin dake gaban dressing mirror ɗinshi ya ajiye mata ita,Tunda ta shigo ɗakin idonta ke akan Sehrish,Ba ƙaramin daɗi taji ba da sehrish ta farka,da alama jikin nata da sauki duk da akwai sauran ciwo atattare da ita,
"Ya jikin naki"?tayi tambayar bayan ta zauna,shiru Sehrish bata ce uffan ba,Hakan yasa ta ɗan tashi hankalinta,
"Kada ki damu,ba zata iya magana a yanzu ba,saboda raunin dake abakinta,
Ajiyar zuciya abu ta sauke kafin tace"Allah ya baki lafiya,"
"Ameen"ya amsa mata amadadin Sehrish ɗin,don ita sai dai ta ɗaga kai,
gaisar da ita Sgr yayi cikin girmamawa,ta amsa mashi fuskarta asake,
"Inaso ki faɗamun meke damunta ne"?
Buɗe baki abu tayi zata yi magana kenan taji anshaƙe mata maƙoshinta,runtse idanuwanta tayi tana ambaton Sunan Allah acikin Zuciyarta,
"Be calm and answer me pls"Ya faɗi hakan ne don Ya lura tamkar bata a cikin natsuwarta,Sehrish kuwa hankalinta ya tashi ganin Oummansu ta kasa buɗe baki tayi magana,tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla,
Wasu addu'oi abu ta shiga jerowa acikin bakinta,da ƙarfi da ƙarfi,bata daina ba har sai da Maƙoshinta Ya buɗe,nan take zufa ta wanke mata fuskarta,miƙewa Sgr yayi cikin sauri ya shiga palour,within secs ya dawo hannunshi ɗauke da bottle water,zama yayi tare da cire murfin ya miƙa ma Abu,hannu biyu tasa ta kar6a,kusan rabin ruwan ta shanye,janye robar tayi daga bakinta,har lokacin tana cigaba da karanto addu'o'in neman tsari a wurin ubangiji don ta gane cewa so ake a hanata magana,gashi ita kuma gwana ce wurin yin ibada, da kuma yin azkhar da sauransu,zaiyi wuya sihiri ya kama irinsu wani lokacin sai dai suci wahala,
Lokacin da taji zata iya magana,da sauri ta soma bayyana mashi halin da sehrish ke ciki"tun jiya da ta shiga ɗakin Azmee bata ƙara samun natsuwa ba,ta sanar dani cewa tana ƴan gane gane,wasu abubuwa nayi mata gizau,kamar ɗazu da safe lokacin da muke cin abinci,Sehrish ta dinga sambatu tana faɗin tsutsotsi ne acikin plate ɗinta,har tayi wurgi da plate ɗin ta watsa da gudu ta shiga ɗaki,wannan ne silar data rikice ta shige toilet tana wanke bakinta da Omo da soso,kamar yarda ka gani....."
Dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana faman sauke ajiyar zuciya,Sehrish sai murmushi take yi farin ciki kamar ta miƙe ta rungume Oummansu,
Shiru Sgr yayi yana kallonta yayin da yake nazarin wani abu acikin brain dinshi,bakomai ya faɗo mashi arai ba face daren jiya da Sehrish tazo ɗakinshi ta tsorata harta yi wurgi da plate ɗin hannunta,tana fadin Ya rafayet maciji kunama zasu harbeka,anan ya gane cewa Bayan ta fito daga ɗakin Azmee ne ta shigo ɗakinshi,
Jinjina kanshi ya ɗan yi tare da cewa"Kina Zargin Azmee"?
Da sauri abu ta ɗaga mashi kai Alamar eh,
"Meyasa kike zarginta"?
"Saboda na santa,lokacin dana haifi su Sehrish,Itace Ƴar uwar sayyadi wadda tazo yi mun wankan jego,"
Tunkan takai ƙarshen maganar Sgr yace"Kenan ita ƴar uwar shi ce?",
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,murmushin takaici Sgr ya saki,
Yana ƙoƙarin buɗe baki ya kuma tambayarta,Yaji Sehrish ta ruƙo hannunshi,da sauri yakai idonshi wurinta,
Da hannu ta dinga yi mashi Alamar ya miƙo mata jotter dinnan zata yi rubutu,
Hannu yasa ya dauki jotter ɗin tare da mika mata,dama biron na hannunta,
Zane yaga tana yi maimakon rubutu bayan ta kammala ta mika mashi jotter ɗin,
Hannu yasa ya kar6a tare da kallon abunda ta zana,Zobe ne ta zana,bai gane me take nufi ba,
"Zan iya ganin me ta rubuta?"abu ce tayi tambayar,
Miƙa mata jotter din
Yayi tasa hannu ta kar6a,koda abu taga zanen sai ta tuna da binciken da Sehrish ke yi dangane da Junaid,dayake ta bata labarin mutuwarshi,baiwar Allah tana so tayi mashi maganar Junaid ɗin ta kasa,Gashi ita kuma abun ta manta bata sanar dashi ba,
"Kin gane me take nufi"?
Jinjina kai abu tayi kafin ta ɗaura da bayani"Ta sanar dani komai daya faru dangane da mutuwar ƙaninku Junaid!"tunda sgr yaji ta ambaci junaid,hankalinshi gaba ɗaya ya koma kanta,
"Akwai wata rana da ta shiga ɗakin Azmee,zatayi sallah tana ƙoƙarin ɗauko hijabi acikin wardrobe ɗin ita azmeen,Sai ga zoben ƙaninku na Diamond ya faɗo daga cikin wardrobe ɗin,A binciken da sehrish tayi ta gano cewa tare da zoben nan Shi Yaron ya fita aranar da al'amarin ya faru kuma abun mamaki Zoben nan nashi baiyi komai ba!babu alamar wuta taci shi!"
Gaban Sgr ne ya faɗi rasss!ya ware idanuwanshi gaba ɗayansu,Abun ba ƙaramin girgiza shi Yayi ba,jikinshi har kerma yake yi,aruɗe yace"Taya akai Ita reesh ɗin tasan cewa tare da zoben Ya fita aranar'?
"Ta hanyar hotunan da suka ɗauka tare da Junaid a wayar Jahad,"
A hanzarce Sgr ya ɗauki wayarshi tare da dannawa Fawan kira,tana fara ringing ya ɗaga kiran,
"Fawan Am sorry na takura ka ko"?
On ther hand fawan yace"A'a babban Yaya,baka takuramin ba,"
"Idan kana kusa,pls inaso ka kira mun Jahad,ka sanar da ita cewa tazo mun tare da wayarta da kuma wayar Sehrish ina buƙatar ganinsu,"
"Toh babban Yaya"yana kai ƙarshen maganar ya ajiye wayar,zuciyarshi sai faman tafarfasa take yi,ita kanta daurewa kawai takeyi saboda maƙoshinta da ake ƙoƙarin shaƙewa ta dage sai ta faɗi gaskiya,koda kuwa Rai zaiyi halinsa,
Bayan wasu mintuna,Jahad ta faɗo ɗakin da sallama a bakinta,jikinta sanye da dogon hijabi,yayin da hannunta ke ruƙe da wayarta da kuma wayar sehrish,
Atare suka amsa mata sallamar,shiga cikin ɗakin tayi,gaba daya idanuwanta na akan Sehrish zaune tana ta murmushi,wani irin farin ciki ne ya lullu6e Jahad,
"Sehrish Ya jikin naki?na damu sosai akan halin da kika shiga"
"Jahad Rishi bazata iya magana ba a yanzu,ki tayata da addu'a,"acewar Oummansu,
Jikin Jahad ba ƙaramin sanyi yayi ba,miƙa mashi wayoyin tayi,Yasa hannu ya kar6a,danna wayar Jahad ya shiga yi,direct ya shiga Gallery ɗinta,
ɗagowa yayi tare da kallon Jahad"Ina hotunan da kukayi keda junaid aranar da kuka fita shan ice cream"?
"Suna acikin Gallery ɗina,daga ka shiga zaka gansu,"
"I did not see anything,ko kin gogesu ne"?
Gaban abu ne ya faɗi rass,Ita kanta Sehrish saida hankalinta ya tashi,
Jahad tace"Wlh ya rafayet ban gogesu ba suna acikin wayata,ko yanzu haka kafin nazo nan hotunan nake kallo"
Miƙa mata wayar yayi"nuna mun su,"
Bayan Jahad ta kar6i wayar,ta shiga neman pictures ɗin gaba ɗaya an goge mata su har vedios din daga cikin wayarta,
Tamkar zata fashe da kuka,"Ya rafayet wlh an goge munsu,bansan ya akai ba,"
"Wani ya amsa wayarki ne"?
Girgiza kai tayi"a'a,duk yinin yau wayata tana a hannu na,"
Mayar da idanuwanshi yayi kan abu"taya zan gane cewa,Junaid ya fita da zoben a hannunshi?ina yin amfani da shaida ne,kafin na yanke hukunci,"
Gaba ɗaya sunyi shiru,jikin kowa yayi la'asar musamman Sehrish domin kuwa harta fara zubar da kwalla,Azmee tayi masu tsiya suna ƙoƙarin fallasa ta ita kuma ta hana hakan,Shi kuma Sgr bai yarda da sihiri ba,koda zasu fada mashi cewa tana amfani da sihiri zaiyi wuya ya yarda,
Hannu Sehrish tasa tare da ta6o shi,juyawa Sgr yayi yana kallonta,Nuna mashi wayarta tayi da yatsanta alamar tana buƙatarta,
Miƙa mata wayar yayi,tasa hannu ta kar6a,
Tana kunna Power din wayar ta kawo haske,Sai ga text message Ya shigo ta layin AMRISH!
Yaushe rabon da ta samu layin Amrish harta manta,kullum in ta kira kashe take samun wayar,Yanzu haka da ta kar6i wayar Amrish take so Ta tura ma saƙo akan ta nemo mata number Ya mu'allim ɗinsu,
Shiga message ɗin tayi,ta ƙura ido tana kallon jagwalgwalon Rubutun da aka turo mata,Na haruffan da aka cakuɗesu,abun ya ɗaure mata kai!Nikaina Boss Ya ɗaure mun kai!
Duk maison Karanta Littafin Abban sojoji Yayi mun magana ta Layina amma whatsapp kawai banda kira 08103884440
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Ta jima tana kallon haruffan nan bata fahimci me aka rubuta a saƙon ba,layin Amrish ta kira nan take aka sanar da ita cewa wayar a kashe take!sam bata so haka ba,ɗagowa tayi tare da kallon Sgr dake magana da Oummansu,
"Nagode sosai da bayanin da kika bani,duk da ban samu evidence ɗin da nake buƙata ba,but i wll try my best wurin ganin nayi investigation akanta,Zaku iya tafiya,"cikin girmamawa Yayi mata maganar,miƙewa Abu tayi"mun gode sosai Allah Ya taimaka,Ya baku sa'a..."sosai ta shiga yi masu Addu'a yana amsa mata da Ameen,"
Ruƙo hannun Jahad tayi atare suka fuce daga ɗakin,Sae da suka fito palour sannan Oumma tace"Jahad ya akai ba'a ga hotunan a wayarki ba?ko kin gogesu ne batare da kin sani ba"?
"Wlh Oumma ban gogesu ba,Nikaina abun ya ɗaure mun kai,"
Jinjina kai Abu tayi"bakomai akwai Allah,Amma Sehrish ɗin fa?Anan zata kwana?ba ɗakin shi bane"?dama abun ya tsaya mata aranta shiyasa ta tambayeta,
"Bedroom dinshi ne Oumma,kada ki damu mu tafi kawae,"
Bayan fitarsu ɗakin,Sgr ya mayar da hankalinshi kan Sehrish,har lokacin hannunta ruƙe da wayarta yayin da idanunta ke kallon Screen ɗin wayar,
"What are u looking at"jin muryarshi yasa ta ɗago da kyawawan idanuwanta tana kallon fuskarshi,
"If u need something pls lemme know"cike da kulawa yayi maganar,miƙewa tsaye yayi sai da ya fara ɗaukar Laptop ɗinshi sannan ya fita palour,Ji take kamar ta dakatar dashi,Saboda tsoran da take ji,
Yatsun hannunta na kerma Ta shiga danna wayar call log ta shiga ta kara dannawa Amrish kira,Nan take aka kara sanar da ita cewa Layin akashe yake,tamkar ta fasa ihu haka taji,runtse idanuwanta tayi tare da ɗan buɗesu kadan,yanke shawarar zuwa whatsapp group ɗinsu tayi Na Classmates ɗinta,Akwai kuma Na general wanda kowa ke aciki students ɗin da kuma malamansu ne aciki,A Group ɗin teachers kaɗaine zasu Iya tura saƙo banda students,tana fatan Allah yasa Ya Mu'allim yana acikin group ɗin,profile ta shiga daga ƙasa wurin da List ɗin Malaman dake group ɗin suke ta fara duba sunayensu tundaga kan Admins,Gasu nan sunayen birjik amma bata ga Numbar Ya mu'allim ba,Sai dai wasu numbobi da aka rubuta sunansu da harshen Larabci,shiru tayi tana tunanin kowanne ne aciki nashi,A ƙarshe dae duka numbobin masu ɗauke da rubutun Larabci ta turama Saƙon,bayan ta kammala rubuta saƙon ta ajiye wayar a saman bedside drawer,
Wuraren ƙarfe 2:30 na dare Lokacin masu bacci sunyi nisa a baccinsu,kamar yarda suka saba kwanciya a saman gadonsu su ukku,Hosana na a tsakiyarsu Abu na a ta 6angaren hannun dama inda yake fuskantar ƙopa,Jahad nata Can 6angaren hannun hagu,kwatsam Suna cikin Baccin nan,Abu ta soma jin wani irin gurnani gurnani asaman Gadonsu,a hankali ta buɗe idanuwanta tana ƙoƙarin ganin menene,har sai da gabanta ya faɗi rass,Wata Mummunar mage ce baƙa wulik mai Uban gashi ajikinta Hakoranta dogaye irin na Vam pires,Kafin abu tayi wani Yunƙuri Magen nan ta daddage ta kai Mata suka ta dira akan wuyan Abu,wasu Manyan ƙumbuna ta fiddo a hannunta tana ƙoƙarin Caccaka ma Abu akan fuskarta,A firgice Abu ta damƙi wuyan magen,Kokawa ta 6arke a tsakaninsu,duk yarda baƙar magen nan taso ta cutar da abu amma abun ya faskara,Domin kuwa Allah yaba Abu sa'a tunda ta damƙi wuyan magen nan ta dinga Jibgarta batare da jin shakkun wani abu ba,A jikin side drawer abu ta dinga buga kan magen nan bugu bana wasa ba,Har sai da magen ta fara kuka tana faman ambaton Miyau miyau,A faɗace Abu tace"Zaki ci ubanki ne,Baki ga komai ba,Nasan cewa ke ce Azmee,kika zo mun da suffar mage don ki kashe ni,Saboda kinga Asirinki na shirin Tonuwa ko?
Tunda abu ta ambaci hakan sai Magen nan ta bace 6aaat babu ita tamkar bata ta6a bayyana ba,ajiyar Zuciya abu ta sauke tana mai godiya ga Allah,daya bata nasara Akan Azmeee,
Saukowa tayi daga saman gadon,ba ƙaramin daɗi taji ba dasu Hosana basu farka ba,duk wannan badaƙalar da akayi suna ta shan baccinsu,
Toilet ta shiga,Bayan wasu mintuna ta fito ɗaure da alwala,Hijabi ta ɗauko tare da darduma ta shimfiɗa ta kabbara Sallah
A 6angaren Sehrish kuwa kasa samun natsuwa tayi acikin ɗakin,har sai da Sgr ya shigo sannan hankalinta Ya kwanta,ruwa tace mashi zata sha don duk yadda taso kin sa wani abu a bakinta ta kasa yunwa take ji sosae,bayan ya kawo mata bottle water cike da zullumi ta kafa baki,sai da tasha kusan rabi sannan ta cire roban ta mika masa ya amsa ya rufe ya ajeta saman side drawer,saman gadon ya hau tare da janyota jikinshi ya rungumeta sosai har bacci ya ɗaukesu,
Wuraren Sallar Asuba da suka fita masallaci,Ya rage ita kaɗai acikin ɗakin,cikin bargo ta shige tana ta addu'a,tana jin motsin wasu abubuwa acikin kunnanta amma taƙi yarda ta buɗe bargon,Sai dai komai zai faru ya faru,
Lokacin da Sgr ya dawo daga masallaci,tare da fresh milk ɗin da ya ɗauko mata acikin Fridge ya shigo bedroom ɗin,abakin gadon ya tsaya yana kallonta ta cikin bargon sai kerma take yi kamar wadda sanyi ya kama,Saboda ita har A.c ɗin ɗakin ya kashe gaba ɗaya don ya lura tana da jin sanyi,
Zama yayi daga gefen gadon,Ya ajiye fresh milk ɗin asaman drawer sannan ya sanya hannunshi tare da yaye bargon jikinta,duka hannayenshi ya sanya wurin ɗaukkota ya ɗaurata asaman laps ɗinshi kamar wata jinjira,tunda taji ƙamshin turarenshi ta shaida cewa shine ya dawo,ba ƙaramin daɗi taji ba,kwantar da kanta yayi asaman ƙirjinshi,A hankali yake shafa sumar kanta yayin da idanuwanshi ke kallon long eyelashes ɗinta, ta rufe idanuwan sosai taƙi buɗesu,
"Ya jikin naki"?
"Da sauƙi,"ta amsa mashi daƙyar,bakin nata ya ɗan lafa,
"Kina jin yunwa"?
jinjina mashi kai tayi alamar eh,
Dogon yatsan hannunshi ya zura mata abakinta,sai gashi ta buɗe Small mouth ɗin tare da kama yatsan hannun nashi,wani shock yaji da sauri ya zame yatsan don baiso ya shiga wani yanayi a wannan halin da take ciki na jinya,
Fresh milk ɗin Ya ɗauko tare da cire murfin ya ɗan kafa mata robar abakinta,a hankali ta shiga shan madarar,natsuwa yayi yana kallonta shi kanshi mamakin yanda ya damu da ita sosai ya ke yi,Yadda take shan fresh milk ɗin ba ƙaramin sha'awa ta bashi ba,Sai da ta shanyeta tass,Sannan ya janye robar daga bakinta,
.."kin ƙoshi"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ba don ta ƙoshi ba,Amma taji sauƙin cikinta,
"Zaki yi wanka,"?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,Tayi tunanin zaice ta tashi ta tafi bedroom ɗinsu,Ba zato ba tsammani taji ya ɗauketa asaman kafadarshi Ya wuce da ita toilet,wata irin kunyace ta rufe ta,musamman Lokacin da ya cire rigar jikinta yayi mata naked,batasan meke wakana ba amman taji ya kwantar da ita cikin jacuzzi,da sunan wanka Sgr ya shiga da ita cikin kwamin amma sai da ya gama shafe jikinta da hannunshi,da sunan yana goga mata Sabulu,ga soap ɗin nashi wani irin ƙamshi tamkar turare haka sabulun yake,zuba mata ido yayi yana kallon fuskarta,ganin tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta yasa shi yin saurin goga mata sabulu saman idanuwan,hakan yasa ta fasa buɗe idon,baison ta raina shi ne shiyasa yayi mata hakan,Wani irin ruwa ne mai ɗumi ga daɗi yayi mata amfani dashi,kamar karta fito daga cikin Jacuzzin nan hake ta dinga ji,
Bayan wasu mintuna Sgr ya fito ɗauke da Sehrish saman kafaɗarshi ya ɗaura mata towel,zaunar da ita yayi saman front chair ta gaban madubinshi,
Saitin kunnanta ya duƙo a hankali yace"in shafa maki ne ko zaki iya shafawa,"?da sauri ta ɗaga mashi kai Alamar eh,
"Okey,"ya miƙe tare da juyawa ya shige toilet ɗin don ya samu yayi wankan shima,Tana jin ya rufe ƙopa ta buɗe idanuwanta,Sae faman zabga uban murmushi takeyi,bata ta6a tunanin Sgr zai iya caring ɗin mace ba irin Yarda yayi mata a yau,Ko jinjira albarka,bakomai yafi burgeta ba fa ce Yarda yake ɗaukarta asaman kafadarshi,daɗi take ji sosai,Ajiyar zuciya ta ɗan sauke tare da kai hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin body oils ɗinshi ta soma shafawa ajikinta,Bayan ta kammala ta feshe ko'ina da turarenshi ita ma yau ta ɗanɗana turaren Babban Yaya,Zasu yi ƙamshi iri ɗaya,
Miƙewa tayi daga saman kujerar ta nufi gadon tana ƙoƙarin ta gyara mashi,zanin gadon ta cire ta musanya da wani sabon da ta ɗauko ta jera pillows ɗin,Tana cikin gyaran nan tajiyo alamun motsin ƙopa tasan shine zai fito,A hanzarce ta haye saman gadon ta zauna tare da jingina bayanta ta kuma rufe idanuwanta saboda kunyarshi da take ji,Ya gama gane mata jiki saƙo da lungu,"
Sako fararen ƙafafunshi yayi masu sanye da slippers,A saman ƙaramin carpet ɗin dake bakin ƙopar toilet ya cire slippers ɗin,towel ya ɗaura asaman waist ɗinshi,Slowly ya ɗago da blue eyes ɗin shi yana kallon Sehrish,takawa yayi izuwa gaban dressing mirror ɗin ya tsaya don ya gyara jikinshi,satar kallonshi Sehrish ta dinga yi ta wutsiyar idonta,ba ƙaramin kyau yayi mata ba,ya saki kwantacciyar sumar kanshi ta baya,natsuwa tayi tana kallonshi,Ashe Sgr ya gane tana satar kallonshi,
Da gangan ya sanya hannunshi asaman ƙugunshi ya warware towel ɗin jikinshi,Aikuwa a ruɗe Sehrish ta kifa kanta saman pillow Jiki na kerma,duk a tunaninta babu short ajikinshi,Ƙayataccen murmushi Sgr ya saki,Shi kanshi baisan ya kubce mashi ba,razanar da tayi ne yaso bashi dariya,
ɗago da kanta tayi daga jikin pillow ɗin don ta saci kallonshi,karaf suka haɗa ido dashi,wani irin kallo taga yanayi mata,murmushi ta saki tare