Showing 303001 words to 306000 words out of 307403 words
Chapter 102 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
kowa sakat da koke kokenta,Har sai da Oummansu tayi mata nasiha sosae ta nuna mata in ta gode da wannan Allah sai ya bata fin dayan in zata kara haihuwa,amman in tana yin hakan tamkar bata gode mashi bane kuma hakan yana iya sawa taki ma kara haihuwar,jin hakan yasa ta haƙura,Ga Jinjirinta kyakkyawan gaske,Kamanninshi sak irin nata,Komai na Hosana yaron ya ɗauko Omar ba ƙaramin farin ciki yayi ba,Allah ya kar6i addu'arshi ya samu ɗa Namiji,A 6angaren Junaid kuwa,Lokacin da aka nuna mashi twins ɗinshi saboda tsabar farin ciki har sume masu yayi,da aka yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo kuka ya dinga yi hawaye jaga jaga akan fuskarshi,Abbansu Ya bashi shawarar ya ɗauro alwala yayi salla,Ya nuna godiyarshi ga Allah,
Aranar Sunansu Jahad,Tagwayen Junaid,An raɗa masu sunayensu Macen Aka sanya mata Sunan Auntynsu AZEEMA,namijin kuma Aka sanya mashi sunan Uncle,Wato abusufyan,murna a wurin Mommy azeema da Uncle abusufyan kamar waɗanda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,tagwayen junaid kamar yayi kakinsu Saboda kamanninshi da suka ɗauko,
Ɗan wurin Hosana kuwa Yaci Sunan babban yayansu,Wato Rafayet,Sgr Yayi murna sosai,ranar suna anyi shagali sosai,sun samu kyaututtuka a wurin ƴan uwansu da abokanansu Omar,Har kyautar Motoci Suka samu,Bayan wasu kwanaki da haihuwarsu,Gaba ɗaya suka ɗunguma zuwa Nigeria hada masu jego,A can zasu ƙarasa wankan jegonsu,Daga nan zasu zaga dangi,A sada zumunci kafin su dawo America,Sam Sgr da Omar basu so tafiyarsu ba,Junaid ma anan aka barshi saboda University ɗin da ya fara zuwa,Yana karantar Medicine & Surgery,duk cikinsu shi kaɗaine bai gaji Abbansu ba, yana ji yana gani aka tafi da Jahad da twins ɗinsa har da ƙwallarsa
Bayan sun kammala wankan Jego,suka shirya zuwa kai ziyara,Wurin danginsu,damaturu suka fara zuwa,Sukayi sati biyu acan kafin Suka wuce zariya wurin dangin Abbansu,duk inda sukaje hannu bibbiyu ake tarbarsu,Kowa sonsu yake yi,daga zariya suka wuce Kano,Ziyarar bazata sukayi ma su Maman Sadeeq,Sunyi farin cikin ganinsu sosai,kusan sati ɗaya sukayi a kano,Harsu Hayaam saida suka zo Gidansu Maman sadeeq wurinsu Jahad don su gansu,Hafsat ce ta sanar masu da zuwansu kano ta basu Numbar wayar Sehrish,Ita tayi masu kwatancen gidan sukazo,Hayaam tayi kuka sosai lokacin da taga Ƴan ukun Sehrish,Tabi ta ruɗe ta susuce,Kyawawan gaske,kamar Sgr yayi kakinsu saboda tsabar kamanceceniyar dake tsakaninsu,kafin Su sehrish su koma America,wasu daga cikin amaren Gidan suka haihu,matar Yusuf Amrish,da matayensu Twins da fawan,Amrish ta haifi tsaleliyar budurwa,Yuhana matar Ayaan ta haifi Namiji,Amal Ta Haifi twins maza,ɗaya yaci sunan Irfan,Ɗayan kuma Yaci sunan kakansu Salahudeen,sauran amaren wasu suna ɗauke da tsohon ciki,Sai bayan da akayi shagalin sunansu Amrish,Kafin Su Sehrish suka koma U.s,wurin mazajansu,Sunsha soyayya ranar da suka koma,kusan First night ɗinsu Sgr ya maimaita,Dama sunsha gyara wurin Mommy azeema,musamman saboda zuwansu Nigeria,tazo gidan don ta Gyarasu kafin ta koma ɗakin Mijinta,tamkar amare haka suka koma,
Sgr ya bada shawarar Ayi masu Family planning saboda su samu damar yin karatu,Omar yayi na'am da maganarshi,atare aka sanyasu Makaranta,private school ɗin Mommy matar Uncle Donald,gaba ɗaya S.s.one aka kaisu,duk da su Jahad basu kaiba hanyace kawai akayi masu ga kuma girman da su kai,da taimakon mommy aka yi masu komai.
Tabbas Family ɗin Salahuddeen sunyi babban rashi,wanda Yayi matuƙar girgiza su,na Kakarsu AMMI,Bayan Tayi jinya ta ɗan lokaci,ta koma Ga mahaliccinta,mutuwar Ammi ta girgiza su sosai,Sunji mutuwarta,A ranar Alhamis Ta rasu,A washe garin ranar da ta rasu,Su Sgr suka zo Nigeria,a Damaturu suka sauka don duk suna can zaman gaisuwa,satinsu ɗaya suka Koma America,
Kullu nafsin za'ikatul maut,
Ammi bata dade da rasuwa ba akayi bikin Haroon da Hayaam da farko taki amincewa dashi sai da suka yi waya da hafsat take sanar da ita komae game da haroon ta kuma sanar da ita cewa shi din jinin Abba ne,daga baya ta amince mashi aka daura masu aure,at last dae hayaam ta zama surukar Abba,ba'a dade da yin aurensu ba Allah ya Albarkaci Amani da haihuwar da Namiji sunyi matukar farinciki sun gode ma Allah,abunda suka dade suna nema,da farko amani har ta fidda ran haihuwa taba Abbas shawarar ya kara aure don ta san yana son yara,yace zai yi tunani cikin hukuncin Allah kafin ya yi tunanin sai ga ciki,indeed,Mahakurci mawadaci ne.
Bayan wasu shekaru,Alokacin sauran Amaren duk sun haihu, Kowa da ƴa'ƴanshi,Hada Hajjaju ta haifama Ishaq santalelan ɗa Namiji,Hafsat kuma ta haifi Ƴa mace taci sunan Mahaifiyarta wato Laila,Oummansu Sehrish itama Allah ya albarkaceta da samun Twins Maza sunci sunan Mahaifinta marigayi Baba buzu,Ibrahim da sunan mijin gwaggon katsina wato Nuraddeen,ba karamin farin ciki gwaggo tayi ba harda Dr harris ma yaji dadi sosae,shima suna katsina Saude ta haifa mashi budurwa har yarinyar ta d'an girma sunan gwaggo taci wato Ameenatu,ƙannansu Sehrish Masu kama da Oummansu sak,Jama'a gida ya cika maƙil da jikoki,Dama burin Abba kenan,duk inda ya waiga ƴan jikokinshi ne,Ƴan dugui dugui dasu,tun da yayi retired,Kullum Yana zaune cikin Jikokinshi,Yana wasa dasu,Ya Manyata sosai,kanshi Duk hurhura,Idan yana wasa Da Yaran Abun saiya baka sha'awa ya saka dariya,Har wasan Ƴar 6urun 6urun suke yi dashi,Sun saba da kakansu Fiye da iyayensu,Ya sangartasu sosai,daga zarar wani ya 6ata masu rai,Zasu zo wurinshi kawo ƙorafi saboda Yana goya masu baya,Mafi yawancin lokutta a garden Yake yin wasa dasu,ba ƙaramin nishaɗi yake samu atare dasu ba,sam bai da wata damuwa irin yadda wasu in suka yi ritaya sukan shiga damuwa saboda rashin zuwa aiki kullum sai zaman gida,
*Boss Bature*
*Ga duk Mai buƙatar Karanta Littafin Abban Sojoji Daga Complt a jere Daga Book One zuwa 3 Suyi mun magana ta whatsapp 08103884440*
[3/19, 10:00 PM] +234 810 388 4440: *💋ABBAN SOJOJI💋*
*💃LAIFIN DAƊI ƘAREWA💃*
*FINAL EPISODE*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags
Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃
*Boss Bature*
Bayan Wani Lokaci,
Alhamdulillah junaid Ya samu damar kammala Karatunshi,Ya zama ƙwararran Likita,batare Da 6ata Lokaci ba,Sgr Ya sama mashi Aiki a katafaren Asibitinshi na L.a,A 6angaren Su sehrish Kuwa Suma sun taƙarƙare karatun Secondry ɗinsu,Sgr Ya sama masu gurbin karatu a College of Nursing and Allied Health dake anan Los angeles,Rayuwa fa Tayi kyau,Ta ko'ina Sai sambarka,Hankali kwance suke yin karatunsu,Mazajansu suna ƙarfafa masu guiwa,Ƴa'ƴansu kuma Akwai Nannies ɗin dake kula dasu,hosana tana ɗauke da ƙaramin ciki,saboda takurar da take yiwa omar akan tana son baby tunda ita ɗaya gareta,a dole aka dakatar da planning din da take yi,
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 9 na dare,Kwance suke a katafaren gadonsu,Komai na bedroom ɗinsu Pink colour ne,An ƙawata shi da duk wani abu na more rayuwa wanda yaro zai buƙata,triple bed ne,Guda uku A jere,da alama sunyi nisa acikin baccinsu,Kowannasu na sanye cikin Night dress ɗinsa,Mazan suna sanye ciki riga da wando White colour,Ƴar macen tana sanye cikin riga da wando Pink colour,ba ƙaramin kyau suka yi mata ba,Sumar kanta dark brown very smooth,kamar yarda Zainab take da dogon gashi haka mazan ma,domin kuwa sun ɗauka irin sumar kan Sgr,Gashin kansu ya sauko har saman kafaɗansu,A ƙalla yanzu sunkai shekara Biyar a duniya da ƴan watanni a duniya,da farko a gado ɗaya suke kwana,Amma saboda rashin jituwarsu yasa Aka kawo wasu bed ɗin biyu,abunda ke faru aduk lokacin da Iyayensu suka kwantar dasu,da zarar sunbar ɗakin,Ƴar macen zata Soma tsokanar mazan faɗa,Gasu miskilaine,Don hossein Halinshi sak irin na Sgr,ko kallo wannan Mutun bai isheshi ba,mugun jan ajine dashi,bai ɗaukar raini ko kaɗan,Mugun miskiline,Suna kiranshi da Gentle Ƙwara Little Omar,Shiya ɗauko Halin Sehrish,Hatta tsoran nan na Sehrish haka yake shima,Ko tsawa akayi sai ya gigice,Yaci ka sanyi,Bai bar komai na daga halinta ba,Zainab kuwa Tafi ƙarfi 6angaren Sgr,Sai dai ita ba miskila bace,mafaɗaciyace,Kamar ƴar dambe haka take,dama tun suna jarirai,In ta fara tsala ihu,Sai ta firgita kowa,Pretty suke kiranta,Allah yayi mata ƙarfi,tun tana ƙanƙanuwarta inaga inta girma,
A hankali ta turo ƙopar ɗakin sai kayi tsammanin babban mutunne zai shigo sai ka kalli ƙasa tukunna Zaga iya hangenta,azeema ce ƴar wurin Jahad Wadda suke kira da Beauty Saurin Shiga rai gareta ta,saboda sanyin Halinta,matsalarta ɗaya muguwar sangartacciyace,Ga shagwa6a Komai nata irin na junaid ne,hannunta na ruƙe dana ƙaninta Littafin abusufyan,shi halinshi Sak na jahad ne,Kowannansu na sanye Cikin kayan baccinshi yadda suke tagwaye haka kayan jikinsu ma Suka kasance Launi ɗaya,Riga da wando brown colour,wannan ɗabi'arsu ce duk mun dare bayan iyayensu sun kwantar dasu,In har suka farka to sai sun nemi ƴan uwansu,Abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yake yi ba,kamar masu iskokai,Sunfi son kwana ɗaki ɗaya kamar yadda suka saba yin wasa atare,
Suna shiga ɗakin suka saki Hannun Junansu,Da gudu Little Ya haye Gadon Omar ya kwanta gefenshi,don sunfi shiri dashi,Beauty kuma ta nufi gadon Hossein zata kwanta,Tana ɗaura hannunata Ya ware Manyan blue eyes ɗinshi akanta,Gaba ɗaya ta furgice,Ashe idonshi biyu tun lokacin da suka shigo,Wani irin kallo yake binta dashi,Ko Uffan baice mata ba,Ya juya mata baya,Don karma su fuskanci juna,Bai hanata kwanciya ba,lalla6awa tayi saman gadon ta kwanta,
Basu jima da shigowa Ba,Sai ga Little Rafayet,Hannunshi ruƙe da ƙaton teddy ɗinsa har yaso yafi ƙarfinshi,Farin cikine Ya lullu6eshi ganin ƴan uwanshi duk sun haɗu guri guda,da gudu Ya ƙarasa Saman Gadon Zainab Ya haye ya kwanta,Tare da ɗaura mata teddy ɗinshi asaman Jikinta,Cikin bacci tajishi,aikuwa a harzuƙe ta farka,Tayi wurgi da teddy ɗin tare da ɗunƙule hannunta zata kai mashi naushi,koda tayi arba da fuskar Little Rafayet,Sai ta janye hannunta,Tana faman Cizon le6enta Allah yaso shine dayasha Naushi,juyawa tayi ta ɗauko mashi teddy ɗinshi ta miƙa mashi"take it,"a tsanake tayi maganar,
Cikin harshen turanci don dashi suka taso amma suna jin hausa,Iyayensu nayi masu,saboda Suna yini a school,yasa suka fi ƙarfi ta 6angaren turancin da french,
girgiza mata kai yayi"Naki ne,Na kawo maki,"murmushi tasaki har dimple ɗinta Ya lotsa,a tsakiyarsu ta ajiye teddy ɗin,a haka suka rungume juna,da ƙaton teddy a tsakiyarsu,cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dasu,
*Reeshraf*
A hankali take saukowa daga saman stairs ɗin da zai sadaka Da Swimming Pool area ɗinsu,A yayin da Sgr Yake tsulundun acikin ruwan yana jiran ƙarasowarta,Ƙayataccen swimming pool ne mai faɗi,Ruwan cikinshi yayi blue sky,wata irin ni'emace ke sauka a wurin,Jin motsinta,Yasa shi yin saurin kai idanuwanshi akanta,tun ɗaga ƙasa ya fara kallonta,Swim suit ne Ajikinta(Kayan wanka),Ƴar rigace me haɗe da pant,red colour,tabi shape ɗin jikinta,gaba ɗaya ta tafi da imaninshi,Santala santalan Cinyoyinta ba ƙaramin fusgarshi suke Yi ba,Iska sai kaɗa sumar kanta takeyi,Yalwataccen gashin kanta sai kaɗawa yake yi saman iska,yana ƙoƙarin rufe mata fuskarta,A hankali take kai hannu tana Janye gashin,Yadda kasan bata ta6a ɗaukar Cikin ƴan uku ba,Jikinta yayi kyau sosai,ba ƙaramin gyara take yi ma Jikinta ba,tana kiyaye duk wani abu da zai 6ata Shape ɗin Jikinta, kuma Tana yawan motsa jikinta,Ga mayukan gyaran jiki da take Using dasu kullum,duk cikinsu ita kaɗaice bata yi jiki ba,Duk da suma Su Jahad basu 6uttuke ba,
Lumshe idanuwanshi yayi a yayin da yake kallonta,A ƙagare Yake data ƙaraso Ya rungumeta Ajikinshi,da wata irin kasalalliyar murya yake ambaton Sunanta"Reesh....pls come quickly"sai ja mashi rai take yi,Koda ta ƙaraso Gaban pool ɗin,Zagayeshi ta shiga yi,duk in tayi taku ɗaya sai jikinta Ya girgiza,
"Pls reeesh why kike yi mun haka?bazaki shigo ciki ba"?maƙe mashi kafaɗa tayi alamar bazata zo ba,sai faman haɗiyar yawu yake yi,
"Kada ki bari na hasala,Zan damƙo kine,"
Kashe mashi ido ɗaya tayi"Nafison haka,Kafin ka fito daga cikin ruwan ni kuma zan watsa a guje"
ɗaure fuskarshi yayi"haka kike ce"?
ɗaga mashi gira tayi,Kamar ta ƙara tunzurashi,batayi tsammanin zai fito ba,sai dai kawai taganshi akan ƙafafunshi,daga shi sai short ajikinshi,Faffaɗan ƙirjin nan nashi a buɗe kamar zaiyi dambe,A firgice Ta juya da gudu zata Koma Saman benen,Sai dai ina kafin takaiga stairs ɗin tuni sgr Ya cimmata,ƙwaƙƙwarar damƙa yakaima Qugunta,ya ɗago da ita sama ya nufi Pool ɗin da ita,Kamar tasan abunda zaiyi tadinga bubbuga bayanshi tana faɗin"Am Sorry Ya rafayet zanyi biyayya,"
Wurgi yayi da ita cikin ruwan Ruwan tsulundum ta faɗa ciki,Kafin shima Ya daka suka ya faɗa ciki,Tare da janyota jikinshi,suka fiddo da kawunansu daga cikin ruwan,Sae faman haki take yi,natsuwa yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta,fuskokinsu sharkaf da ruwa,hakan ba ƙaramin kyau yayi masu ba,Hasken Electric bulbs ɗin dake a wurin sun haskakasu sosai,Babu kowa,dama babu mai zuwa wurin,Wannan swimming pool ɗin nasu ne musamman saboda jin daɗinsu,bashi kaɗai bane acikin gidan,Akwai wasu kusan guda biyu duk acikin gidan,
"Reesh..."daƙyar ta iya buɗe idanuwanta akan fuskarshi,ruwan ya tsaya mashi adai dai stomach ɗinshi,ita kuma yakusa taddo chest ɗinta
Zuba ma juna ido sukayi Tamkar zasu haɗiyi junansu,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,fuskarta akwai light makeup,hada janbaki tashafa red colour,duk da ruwa Ya jiƙa fuskar hakan baisa kwalliyar ta goge ba,slowly ya zagayo da hannunshi asaman ass ɗinta Ya ɗaura tafin hannunshi,tare da janyota,Ya haɗe gabansu sosai tun suna kallon juna,har yakai ga Haɗe bakinsu wuri guda,sosai suke kissing ɗin juna,moving ya shiga yi da hannunshi acikin rigar jikinta,Martani ta shiga mayar mashi tafara sarrafashi da hannuwanta,lokaci guda yabi ya ruɗe ya susuce mata,Zame hannun rigar jikinta yayi,Ya sabule ta,Zuwa waist ɗinta Yadda zaiji daɗin ganin komai muraran,Bakinshi yakai ya kama nipple ɗinta,Sosai ya shiga sucking ɗinsu,duk ta fita hayyacinta,a lokacin ta dawo da hannunta cikin sumar kanshi,ƙara ƙanƙameshi tayi sosai,cos she is enjoying it,a ruɗe take Ambaton sunanshi"ya rafayet"ƙasa yayi da kanshi can can,Yana bin ko'ina na jikinta,Yana licking ɗinsa,rurruƙeshi tayi sosai saboda yanayin daya jefata kamar tayi hauka,batasan lokacin data fashe da kuka ba,wuta sosai yake bata,lokacin daya ɗago komawa jikinta yayi,Ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta,yana mayar da numfashi,bata bari Ya gama mayar da numfashin nashi ba,Taso ma nata Salon,Zame mashi short ɗin jikinshi tayi,Tashiga sarrafashi,Ta gigitashi ya soma yi mata wannan sambatun nashi Aruɗe yake faɗin"keep!keeep!keeep doing it Reesh,You're giving me fire........."
Saida saukayi mai isarsu,Kafin suka dakata kowa Yana mayar da numfashi,sam idanuwansu sun gaza tsayuwa,Sae faman lumshewa sukeyi,a hankali Ya zura hannu cikin ruwan Ya janyo short ɗinshi Ya mayar,Ya ruƙo rigar jikinta,A hankali Ya janyo ziririn hannun rigar Ya mayar mata da ita,rungume juna sukayi sosai,A hankali Ya shirga furta"Reesh Allah yayi maki Albarka,daga ke ba ƙari,banga mace a duniyar nan ba,in bake ba,"kalamansa ba ƙaramin daɗi sukeyi mata ba,musamman idan ya sanya mata Allabarka,daɗi take ji sosai,
"Allah ya faranta maki,Kamar yadda kike faranta mun,"
"Ameen Yayana mijina,"
bacci sosai suke Ji su dukansu,So yake ya ɗauketa gashi Jikin nashi duk kasala ta baibayeshi,Daƙyar Ya tattara dukkan ƙarfinshi Ya sa6eta asaman kafaɗashi ya nufi stairs ɗin da zai kaisu kaitsaye Upstairs,part ɗinsu,Lokacin daya shigo da ita ɗakinsu ya sauketa,Shaf shaf suka Shirya kansu cikin Night dress ɗinsu Ash colour,Hannunsu ruƙe cikin na juna suka nufi ɗakin triplet ɗinsu,time din da suka shiga ɗakin,Basuyi mamakin ganinsu Little rafayet ba,Kallonshi tayi suka haɗa ido,Murmushi suka saki at same time
"Ina mamaki wannan al'amarin nasu,sunfiso su kwana cikin ƴan uwansu,ko tsoro basa ji,Su kwaso ƙwafa Don ma akwai haske ko'ina acikin gidan Shiyasa basa fargabar komai,"sehrish ce tayi maganar,
"Ƙuruciyace da kuma Shaƙuwar dake tsakaninsu,nan da wani lokaci zasu daina ne,"yakai ƙarshen maganar tare shigewa cikin ɗakin itama tabi bayanshi,Agaban gadonsu suka tsaya suna ƙare masu kallo,
"Yanzu wannan duk namu ne"?tayi tambayar tare da kallonshi"Are doubting"?girgiza kai tayi"a'a,Kawai tsabar farin cikine shiyasa na furta hakan,
Ƙayataccen murmushi ya saki,kafin ya kuma cewa wani abu, sai ga Hosana ta faɗo ɗakin jikinta sanye da night gown doguwa,ta yafa mayafi akanta,juyowa su kayi atare suna kallonta jin shigowarta,
Bayan tayi masu sallama suka amsata,sai ta tsaya shiru tana hangen little rafayet dake akwance saman gadon pretty,
Murmushi sehrish tasaki"kinbiyoshi ne halan"?ɗaga mata kai tayi alamar eh,
"Kawai na farka naga babu shi,daga ni har ya Omar bamusan lokacin daya fita ba,a tsakiyarmu muka kwantar dashi,Shi sarkin wayau hada sanya mana teddy a tsakiyarmu don kada muyi saurin gane ya fita,"
Dariya sukayi gaba ɗayansu,Sgr Yace"its okey,kibarshi kawai tunda yafi so Ya kwana tare da ƴan uwansa,nan da wani lokaci zasu daina dakansu,"
Jinjina kai tayi"shikenan,Sai Allah yakaimu,"
"Mu kwana lafiya"juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin,murmushi sehrish tasaki,6ata ta6a tunanin irin wannan ranar zata zo ba,Yanzu hosana ta natsu,hankalinta ya dawo kan saiti,
Ruƙo hannunta sgr Yayi"Bacci nake ji fa,"
"Me too"
Kamar yadda suka Saba,Atare suka soma yi masu addu'a suna tofa masu ajikinsu,Bayan sun Ja masu lallausan blanket dinsu,ta Kashe masu hasken ɗakinsu,Hannunsu ruƙe dana juna suka koma bedroom ɗinsu,Saman katafaren gadonsu suka kwanta,yayi hugging ɗinta tighly,then Ya Janyo lallausar blanket ɗinsu Ya lullu6esu,
Bayan komawar Hosana ɗakinsu,a zaune ta samu marshal daga shi sai short,
"Ae dama saida na faɗa maki,"
Murmushi tasaki"ashe yana acan,Yaron nan yaci ka wayau,"
Dariya yayi yana girgiza kai,Saman Gadon ta hau,Suka gyara kwanciyarsu rungume da juna,
"Ya Omar"Ya amsa mata"Na'am My baby"
"Kayi mun kalaman Soyayya mana kafin muyi bacci".
Gyara muryarshi yayi cike da zolaya yace"Yake akuyar dake cin ciyawar zuciyata"gaba ɗaya suka tuntsire da dariya,
*JunHad*
Tayi mamakin ganinshi zaune saman gadon,Ya jingina bayanshi jikin headboard ɗin gadon hannunshi ruƙe da hoton abbansu,ya ƙura mashi ido yana kallonshi ko ƙyaftawa baiyi,
"My romeo,"ta ambaci sunanshi,batare daya juyo ba,Ya amsa mata"My juliet,"
"Meyasa ka barni ni kaɗai"?
Murmushi ya ɗansaki"Am sorry,Yanzu nake shirin kwanciya,ina kallon Sanyin idaniyata ne"
Miƙewa tayi ta zauna gefenshi,hannu takai tare da shafa fuskar Abba mai ɗauke da murmushi"Allah sarki Abba,we really missed you Ni da babyna,tayi maganar tana shafa sumar kan Junaid,
"My Juliet"ya ambaci sunanta
" na'am My romeo,"
"Idan su babban Yaya suka ajiye aiki zamu koma nigeria da zama,Ni nafison can,"
"Nima nafison mu koma Nigeria,ba don bana jin daɗin nan ba,sai dan saboda ƴan uwanmu"acewar Jahad,
ɗaura hoton yayi a ma'ajiyarshi saman drawer,
"Yaushe zamu ƙara samun baby"?
"Duk lokacin daka shirya,My doctor"
"Ae ni kinsan koda yaushe a shirye nake,ko yanzu ma,ko kina ganin wasa"?
A'a,Na yarda da maganarka,Ae kai ɗin bana wasa bane tayi maganar tare dakai hannu ta ɗan bugi ƙirjinshi,murmushi yasaki"duk da haka bazan ƙyaleki ba,'tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,Yayi saurin haɗe bakinsu wuri guda,Ba halin Yin magana,Sosai ya ruƙota ajikinshi,Romancing ɗin juna sukayi kafin daga bisani ,Suka gyara kwanciyarsu rungume da junad,A ƙanƙame,
Wuraren sallar asuba,yana cikin bacci Yaji shessheƙar kuka acikin kunnanshi,Gabanshi ne ya faɗi,A hanzarce yakai hannu yana shafa gefenshi saman mattress,Jin wayam babu ita Yasa ya ware