Showing 267001 words to 270000 words out of 307403 words

Chapter 90 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

Ya fara ganin Canji atare dashi,'
"Kanason magana dani ne"?yayi tambayar yana kallon fuskarshi,.
ɗaga mashi kai yayi alamar eh
"Okey,Ina sauraronka,"yayi maganar tare da matsowa Ya sauko da ƙafafunshi kasa,Kafin Ya mayar da hankalinshi kan Sgr,
"Uncle,"ya ambaci sunanshi,tare da saukowa daga saman gadon,Ya tsugunna agabanshi,abun mamaki abun al'ajabi,Kamar a mafarki haka abusufyan ke kallon lamarin,Yau Sgr ya sauke girman kan nan nashi,Ya zuƙunna agabanshi,Lallai yau babba rana ce agareshi,

Ruƙo hannunshi yayi acikin nashi,Calmly Ya soma magana"Pls uncle,Kaina bisa wuya na,ka yafe mun,Nasan nayi hurting dinka sosai,wlh na gane kuskurena.........'tun da ya fara magana,bai bari sun haɗa ido da abusufyan ba,shi kuwa ya kafe shi da ido yana kallonshi,
"Ka yanke mun duk wani hukunci daya dace dani wlh i will accept it,amma dan Allah uncle,kada ku rabani da ita,bazan iya jure rashinta ba,atare dani,na saba da ita sosai......'tunkan yakai karshen maganar,Abusufyan ya katse mashi hanzarinshi dacewa"Zaka tafi da ita a matsayin mai aiki ko kuwa"?
Da sauri yace"A'a,Zan tafi da ita,A matsayin matata,in har kun amince mun,"

Murmushin gefen fuska abusufyan ya ɗan saki,batare daya bari Sgr ya gani ba,ci gaba da magana abusufyan yayi"Naji daɗi daka gane kuskurenka,Dama ni can ban ruƙe ka araina ba kawai banji daɗin abunda ka aikata mata ba,Amma bbu komai,komai ya wuce Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu ƴan adam,Don haka na yafe maka rafayet,Allah ya yafe mana gaba ɗaya,Sannan bazan ƙara shiga tsakaninka da matarka ba,Yanzu ya rage tsakaninku da Ammi ne,tace zata yi adalci atsakaninku idan har ku duka kun amince da junanku toh,idan kuma har ɗaya daga cikinku ya musa,to zata raba aurenku ne,"
Cikin sanyin murya yace"bansan da wasu kalmomin zanyi amfani wurin gode maka ba uncle......"
"Kada ka samu damuwa,komai ya wuce,Allah ya baku zaman lafiya kaida matarka......."daga haka Abusufyan ya zarce dayi mashi nasiha,duk ya kashe mashi jikinshi,fuskarshi ɗauke da murmushin nasara ya futo daga ɗakin Abusufyan ya nufi bedroom ɗin abbansu,knocking ɗin ƙopar yayi,
"Wanene"?Muryar abbansu ce,
"Ni ne abba,"
Buɗe kopar abba yayi jikinshi sanye da jallabiya da alama shirin zuwa masallaci yayi,
Tunkafin yayi magana abba ya ruga shi cewa"kaje wurin abusufyan ɗin"?
"Eh,daga can nake,"nan ya kwashe duk abunda suka tattauna a tsakaninsu ya sanar dashi,farin ciki ne ya lullu6e abba,har baisa lokacin daya rungumo Sgr ajikinshi ba,
"Allah yayi maka albarka My son,"
"Ameen abbana,"
"Nima na yafe maka,"
Har cikin ranshi ba ƙaramin sanyi yaji ba,
Bayan ya raba jikinshi daga nashi,Ya ruƙo hannunshi zuwa cikin ɗakin"mu shiga daga ciki,in bakayi alwala ba,kayi sai mu tafi masallaci,'
Ba ƙaramin daɗi sgr yaji ba,Mommynsu na kwance tana bacci lullu6e da bargo,toilet ɗin ɗakin ya shiga,Abba ya tsaya a tsaye yana jiran fitowarshi,After some minutes Ya fito,
Suna hada ido da babansu Ya sakar mashi murmushi,mayar mashi da martanin murmushi yayi tare da cewa"inaso zan canza kayan jikina"
Shikenan,Zan jiraka a palour,Daga nan ka tashi su Omar,su fito mu tafi masallaci,"
Amsa mashi yayi da toh,kafin ya futo daga dakin,Jiki na rawa ya haura upstairs bai nufi ko'ina ba sai bedroom ɗin Omar,tunkafin ya shiga ya soma kwala mashi kira,
"Omar,Omar,"a firgice Omar ya farka,tare da miƙewa zaune yana tambayarshi lafiya,fadawa saman gadon Sgr yayi tare da rungumeshi ajikinshi,Yana dariya,
Tun da yaga haka,Ya gane cewa Sun yafe mashi
"Omar ka tayani murna,Uncle da abba sun yafe mun,kuma yace bazai ƙara shiga tsakanina da reesh ba,Ya amince na tafi da ita,"
Omar yayi farin ciki sosai,Amma kuma akwai sauran rina akaba,idan su sun amince mashi,Itafa Yarinyar!!!

Shafa bayanshi Omar yayi"Am so happy rafayet,ashe da rabon asha shagalin bikina tare dana ka,Kafin mu wuce U.s,tare da matayenmu,Alhamdulillah My dream will come true,

Zuciyar kowannansu a wanke take da tsantsar farin ciki mara misaltuwa,
"Amma wani hanzari ba gudu ba,jiya kaje wurin Sehrish kuwa?naji kayi magana akan maganinta"?
"Bansamu naje ba,amma idan muka dawo daga masallaci,Zan je na duba Lafiyarta,"
"Hakan ma yayi,bari na je nayi alwala sai mu wuce masallaci"acewar Omar,yakai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon,Toilet ya shiga Sgr kuma Ya wuce part ɗinsa,don ya canza Kayan jikinshi,

Batare da 6ata lokaci ba suka hallara gaba dayansu matasan gidan a babban falon gida,atare suka wuce masallaci,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 8 na safe a lokacin Su oumma sun hallara a kitchen suna shirya breakfast ɗin gidan tare dasu Mommy,da hajiya azeema,

A wannan lokacin ne Sgr ya shirya tsaf cikin fararen suit,wankan ya hau dashi sosai,fitowa yayi daga part dinsa Ya nufi corridor din dakinsu Sehrish,a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya,tare da sanya hannunshi yayi knocking din ƙopar ɗakin,
Daga ciki yaji ance"Wai wanene"shiru bai tanka ba,Ya sake kwankwasa kopar,Da ƙarfi yaji a bude ƙopar,a ruɗe ta sanya hannu abakinta,ido ya raina fata,sam batayi tsamanin Baban yayansu bane,
"Yaya rafayet,ashe kaine,wlh nayi tunanin wanine daban"abun ma dariya yaso ya bashi,
"Rishi kake nema"?tunkafin ya bata amsa taci gaba da cewa"In ma oumma kake nema,tana a kitchen,Jahad kuma ta tafi wurin aunty hafsaf,Ni kaɗaice nake jinyar sehrish,baiwar Allah wlh saita baka tausayi,duk ta rame,duk taji ciwo abakinta,abinci ma daƙyar take iya ci ......'
Surutunne ya ishe shi"its Okey,Zan wuce,"matsa mashi hanya tayi ya nufi cikin ɗakin,
"Tayi breakfast"?yayi tambayar yayin da idanuwanshi ke akan sehrish dake kwance magashiyyan tana bacci,
"Inafa,bataci komai ba tun jiya da daddy yabata farfesu tasha,tare da ɗan tea bata ƙara cin komai ba,koda daddare sai da oumma ta bata abinci ta amayar dashi duka......'
Surutun Hosana ba ƙaramin mamaki yake bashi ba,Amsa kaɗan yake buƙata amma sai zuba takeyi mashi kamar radiyon da bata da saiti ,lallai Omar zaiyi fama,
"Its okey,Kije ki amso mata breakfast ɗinta yanzu ina jiranki "
"Toh,"ta amsa tare da fucewa daga cikin dakin

Xama yayi daga gefen gadon ,ya zuba mata waɗannan sexy eyes ɗin nashi yana kallonta,tsananin tausayinta ne ya kamashi, hannu yasa ya zame bargon data lullu6e half body dinta dashi,Still blue gown ɗin nan ce ajikinta,bata canza kayan jikinta ba,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,har baiso ya ƙyafta idanuwanshi daga kan fuskarta, hannu yakai saman side drawer inda ya ajiye ledar allurorin nata tare da magungunanta,shaf shaf Ya ɗura ruwan allurar acikin syringe,so yake ya tayar da ita daga baccin amma ya kasa,Saboda baison Ya katse mata shi,don ya lura da yadda take yinshi cikin kwanciyar hankali,

Ajiye injection ɗin yayi sama drawer din,slowly yakai hannu yana ƙoƙarin shafa wuyanta,Hosana ta banko ƙopar ɗakin hannunta ɗauke da tray,A firgice Sehrish ta farka,Tana kokarin mikewa zaune,duk ta rikice,har yanzu bata daina jin fargababa,
"Reesh are u okey,"?jin muryarshi yasa ta mayar da eye balls ɗinta akanshi,koda suka haɗa ido lokaci guda Ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri ko misƙala zarratin,janye idanuwanta tayi daga kan fuskarshi,hankalinshi ya ɗan tashi da ganin irin kallon da tayi mashi mai cike da tsantsar tsana,kuma wani abu daya ɗaure mashi kai lokacin da suka haɗa ido,Sai yaga tana gyara wuyan rigarta,saboda ƙirjinta daya fito sosai,kamar taga wani wanda ba muharraminta ba,Tashin sense,

Miƙa mashi tray ɗin hosana tayi"Gashi Ya rafayet,Mommy ce ta haɗa mata breakfast ɗin ,"
"Okey,"ya ambaci hakan tare da sanya hannu ya kar6i tray din,ɗan madaidaici,ya daurashi akan lap ɗinshi daya haura saman gadon,
Juyawa hosana tayi da gudu tabar dakin saboda taje taci abincinta,
"How was your body?hosana ta sanar dani cewa jiya baki ci isasshen abinci ba,haka ne"?
Rai a6ace tace"eh,saboda bana jin yunwa,"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin yace"okey,Yanzu ya kamata kici,ko don saboda maganinki da zaki sha,"
Bata tanka mashi ba,ta sauko daga saman gadon dakyar take iya taka ƙafarta,toilet ta shige,yana jiyo nishinta daga inda yake zaune,wahala take sha ba ƙadan ba,idan zatayi fitsari,sai data wanke fuskarta ta kuskure bakinta,Tukunna tafito daga toilet ɗin,ta koma saman gadon ta zauna,batare data kalleshi ba,
cup ɗin dake ɗauke da Tea ya soma kokarin kwafa mata a bakinta da nufin ya bata da kanshi,da sauri tasa hannu ta kar6e kofin,Tasa abaki tana sha,abun ya bashi mamaki,kaf ta shanye tea din,
"Bari na baki abaki....naga hannunki na kerma "
A ƙule tace"Zanci dakaina,"bata jira ya ƙara magana ba,ta sanya hannu ta bude plate tana cin abincin da kanta,natsuwa yayi yana kallonta,yadda take moving lips ɗinta wurin taunar abuncin ba ƙaramin yanayi take jefa shi ba,bawan Allah ya kafe ta da ido yana kallonta,a tsiyace take cin abinci,kafin ta haɗiye wani ta tura wani abakinta,Har ce mata yayi taci a hankali karta shaƙe,Amma ko sauraronshi batayi ba,Ita burinta ya tashi ya tafi shiyasa take sauri ta gama cin abincin yayi mata allurar koya tafi ya bata wuri,

Bayan ta kammala cin abincin ,ta miƙa mashi hannun sai kace ba ita bace wannan me tsoron Allurar ba,Yau dai yaga abubuwan ban mamaki atattare da ita,ajiye tray ɗin yayi,Kafin ya ɗauko sirinjin allurar,ya tsira mata a cikin jijiyar hannunta,Tsabar raɗaɗi yasa ta runtse idanuwanta,tana fidda sauti"Wash Allahna,"Lumshe idanuwanshi yayi a yayin da yake kallonta,A hankali ya zame allurar daga hannun, ya ajiyeta,Magungunan ya shiga miƙa mata,ta dinga turasu abaki tana korasu da ruwan dake hannunta acikin kofi,

Bayan ta kammala shan magungunan Ya tattarasu ya mayar acikin ledar,ya ɗauke sirinjin allurar da sauran tarkacen Ya mike ya nufi dustbin ya zuba su aciki,
Komawa yayi gefen gadon ya zauna yana kallonta,har lokacin babu annuri akan fuskarta,So yake ya bata hakuri akan abunda yayi mata ba,data ga ya ƙura mata ido,Sai ta rufe idanuwanta tamkar maiyin bacci,ba zato ba tsammani taji saukar kiss ɗinshi a saman neck ɗinta A harzuke ta buɗe idanuwanta,tamkar zata rufeshi da fada,Amma sai ta kasa,

Yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,Wayarshi dake ajiye cikin trouser pocket dinshi ta soma ringing,da sauri ya lalubo wayar tare da cirota Ya duba mai kiran nashi,
Abbansu ne,picking call ɗin yayi kafin ya kara wayar a kunnanshi,tunkafin yayi sallama,Muryar abba ta katse mashi hanzarinshi,
"Kana ina ne"?
Kallon sehrish ya ɗanyi,ta kawar da idonta gefe,
"Nazo duba jikin reesh ne,"
Abba yace"Okey,Dama ammi ce ke son ganinku"
Hakanan Yaji gabanshi ya faɗi rass,




(ga duk mai buƙatar Littafin Abban Sojoji from book one to 3,Yayi mun magana,Sannan idan mutun nada tambaya dangane da littafin nan shima yayi mun magana,Saboda masu yaɗa jita jita,Da kuma mahassadan dake kokarin 6ata mun suna,its better mutun ya tunkareni idan ma tambaya gareshi,Su kuma munafukan dake kokarin shiga gonata Allah Ya basu sa'a,tamkar taki suke agare ni)
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*


*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*








Tunkafin ma yaji dalilin kiran Na Ammi har ya fara jin fargaba,duk da baya tunanin Sehrish zata bashi matsala,Ajiyar Zuciya ya ɗan sauke Still Eyes dinshi na akan fuskarta,

Yana kokarin sanar da ita kiran da Ammi ke yi masu,Mommy Azeema ta shigo cikin ɗakin da sallama abakinta,"Assalamu alaikum",

Har suna haɗa baki wurin Amsa mata sallamar"Wa'alaikum Salaam,"tunda ta shigo idanuwanta na akan Sgr daya tsare Sehrish da ido,

Gyaran murya ta ɗanyi"Rafayet Ya mai jikin"?
  Daƙyar ya iya amsa mata"jiki Alhamdulillah,fatan kun Tashi lafiya,"
  "Lafiya lou,"kafin ta mayar da idanuwanta kan Sehrish"Ya jikin naki Daughter"?
  Cikin sanyin murya tace"da sauƙi Mommy,"
  "Allah ya ƙaro sauƙi,"
"Ameen,"ta amsa mata,

Miƙewa Tsaye Sgr yayi a tsanake Ya soma magana"Ammi nason ganinmu yanzu,"
  Hajiya azeema tace"Eh dama Daga can nake,nazo ne don in taimaka mata mu tafi,Sai kuma na same ku atare,"
  "Okey,"ya ambaci hakan tare da kama hanyar fita daga ɗakin,

Daƙyar sehrish ta sauko daga saman gadon,Da taimakon Hajiya Azeema ta canza rigar jikinta zuwa jallabiya baƙa,Ta yafa mata gyale,Yadda kasan balarabiya saboda hasken da tayi,

Dafa Hajiya azeema tayi itama ta tallabota don ta samu damar yin tafiya,Fitowa suka yi daga ɗakin,kaitsaye suka Nufi bedroom ɗin Ammi,Lokacin da suka Shiga,sun tarar da Abba da Abusufyan Zaune gefen gadon Ammi,Mommy na zaune saman Sofa tare da Sgr duk ya kame kanshi,Yayin da Ammi ke zaune Saman Kujerar gaban Madubin ɗakin ta juyo da ita,Yadda zata samu damar ganin kowannansu,

Ganin sun shigo Yasa Mommy ta mike ta koma gefen Abba ta zauna,da hannu ta nuna ma Sehrish gefen Sgr,Ba don taso ba,ta zauna kusa dashi,ƙamshin turarenshi duk ya cika mata hancinta,a hannun Sofa ɗin Hajiya Azeema ta zauna ta 6angaren Sehrish,cike da girmamawa Sehrish ta soma gaishe dasu,Fuskar kowannansu asake suke Amsa mata gaisuwarta,haɗi da yi mata Ya jiki,daƙyar take amsa masu da sauƙi,daga haka Ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta,sai da kowa ya natsuwa,tukunna Ammi ta soma magana atsanake,
  "Muyi ma Annabi salati" gaba daya suka amsa da Sallallahu alaihi wasallam,bayan sun gama Ammi taci gaba"Alhamdullilah,Naji daɗin ganin kowannanku,ko ban faɗi ba nasan kunsan dalilin kiran naku da nayi,dafarko dai kuskure ne anriga da an yishi,tun daga kan iyayenku da suka yanke shawarar yi maku aure batare da sunyi shawara dani ba...."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana mayar da numfashi,kafin ta ɗaura da cewa"kamar yarda nace zanyi adalci atsakaninku,in har kun amince zaku cigaba da zama da junanku to falillahil Hamdu,ba wanda zai raba ku,In kuma ɗaya daga cikinku Ya nuna baya ra'ayin auren to za'a rabashi,'

Hankalin Sgr ba ƙaramin tashi yayi ba,don har saida ya ɗago ya kalli Ammi dake kora jawabi,hakanan ya dinga jin zuciyarshi na bugawa,

"Amma kafin In fara jin ra'ayoyinku,zan yi maku wata ƴar nasiha,"kowa ya kasa kunne yana sauraronta,sosai tayi masu nasiha akan Kuskuren da kowannansu Yayi,tun daga kan Abusufyan da Abba da suka haɗa auran har izuwa kan tursasa mashi akan Ya saketan da sukayi,Sgr ma tayi mashi faɗa sosai Akan abunda ya aikata,jikin kowannansu Yayi sanyi sosai,

Bayan ta kammala Yi masu nasihar Ta kalli Sgr tace"Inaso naji ra'ayinka game da yarinyar nan,Shin kana ra'ayin cigaba da zama da ita amatsayin matarka ko kuwa.... ?"

Jim ya ɗan yi kafin ya jinjina kanshi tare cewa"zan cigaba da zama da ita a matsayin matata,"Sehrish tayi mamakin amsar da ya bayar,kuma bilhakki dagaske yayi maganar,On a serious matter,
  Nunata Ammi tayi da sandar hannunta"Saura ke,Shin kin amince zaki cigaba da rayuwa dashi A matsayin mijinki......?"gaba ɗaya ido ya dawo kan Sehrish ana jiran jin amsarta,musamman Sgr duk da bai ɗago ya kalleta ba,Amma a ƙagare yake da yaji amsarta,haka hajiya azeema ma duk ta ƙosa taji amsar da Sehrish zata bayar,itama Mommy idonta na akan Sehrish,

Jin tayi shiru Yasa Abusufyan Ya tanka mata"Daughter amsarki muke son ji,"

A ruɗe tace"Ni banason shi,bazan cigaba da rayuwa dashi ba,Dan Allah a rabani dashi,"

A firgice Sgr ya ɗago yana kallon fuskarta,tashin hankali,Ko a mafarki bai ta6a tunanin Sehrish zata iya furta waɗannan kalaman ba,

Ita kanta Hajiya Azeema sai da gabanta Ya faɗi jin amsar da sehrish ta bayar,Babu wanda ya tsammaci hakan daga gareta,

Daƙyar Sgr ya iya daurewa Ya cije Ya soma magana cikin sanyin murya ta wanda ya karaya"Idan har akan laifin da nayi maki ne,inaso ki sani ba'a son raina nayi maki hakan ba,kuma ina baki hakuri akan hakan,'

Girgiza kai ta shiga tana fadin"Dan Allah Ammi a rabani dashi,Ya rafayet bai ta6a sona ba,yana so yaci gaba da zama dani ne saboda wata manufa tashi,ya fadi hakan ne saboda Yaci gaba da ƙasƙantar dani a matsayin ƴar aikinshi ba matarshi ba......'

Jikinshi har tsuma yake yi,ba don Allah yasa Manyanshi na akusa ba,da ba abunda zai hana ya ham6are bakinta,just speechless Yama rasa me zaice!!

Ƙasa ƙasa da murya Hajiya Azeema ta soma yi mata magana"Ki shiga natsuwarki,sannan ki gyara kalamanki,ban hanaki ki faɗi ra'ayinki ba,Amma ina guje maki kizo kiyi abunda zakiyi danasani,"

Mommy kuwa cewa tayi"har yanzu yarinyar nan bata dawo hayyacinta ba,tundaga kan yarda take magana babu natsuwa atare da ita,nasan ta faɗi hakan ne saboda Abunda Rafayet yayi mata,"

Shidai Abusufyan bai tanka masu ba,sam baiji dadin abunda Sehrish tace ba,Saboda yanzu kowa Shi zai zarga,za'ayi tunanin koshi ya tunzurata ne,Kamar kuwa ya sani tunda Sehrish ta fara surutannan idanuwan Abba na akanshi,Kallon tuhuma kawai yake yi mashi,

Duk wannan abun dake wakana Akan Kunnan Omar,wanda bai jima da shigowa ba,Yana atsaye Ya goya hannayenshi Asaman kirjinshi,Hankinshi ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda Sehrish take faɗi,dama sai da yakawo hakan aranshi,ta tsorata ne sosai,gani take kamar in taci gaba da rayuwa dashi zai kasheta ne wata rana,

"Sure i know initially nayi accepting aurenta don tayi mun aiki,ko wannan lokacin banyi don na ƙasƙantar da ita ba,kuma na amince da aurenta ne,don ina ra'ayin zama da ita,Ba amatsayin contract ba"tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla,duk ya muzanta a idanuwansu,tun da yake arayuwarshi bai ta6a tunanin wata ƴa' mace zata Iya rejecting dinshi ba,abun Ya girgiza shi fiye da tunanin me tunani don tuni zazza6i Ya rufar mashi,duk da Sanyin A.c ɗin dake shawagi a ɗakin,Hakan bai hanashi Yin zufa ba,fuskarshi sharkaf take tamkar an watsa mashi ruwa,kowa Ya lura da Yanayin da Sgr ya shiga,

"Ni shaida ne Ammi,wlh Rafayet Yana sonta sosai,da ace baisonta ko aurenta bazai kar6a ba,kuma abunda ya faru atsakaninsu tsautsayine,ba don son ranshi yayi mata hakan ba"Marshal Omar ne yayi maganar,duk ya shiga damuwa,Sehrish naso ta 6allo masu aiki,

"Ki fadamun me nayi Maki da har kike guduna?Na ta6a cutar dake ne hakanan,bayan wannan abunda ya faru"?yayi maganar muryarshi tamkar zai fashe da kuka,yayin da idanuwanshi ke akan fuskarta,kwata kwata babu annuri akan fuskar Sehrish,ta canza tamkar ba ita ba,

"Idan har akwai abunda nake yi maki,wanda bakyaso ki fadamun zan daina,"cikin lalama yake lallashinta,

Ammi dai ta kasa kunne tana sauraron kowannansu,tana jira su gama,Ta zartar da hukuncin daya dace,

Fashewa Sehrish tayi da matsanancin kuka,tamkar ranta zai fita,cikin shessheƙar kuka take cewa"Don Allah A sanya ya sake ni,shi dakanshi yace duk hukuncin dana yanke mashi zai kar6a hannu bibbiyu don haka inaso Ya bani takardar Sakina,kuma bayan aurenmu saida ya bani damar cewar Zan iya kula duk wanda nakeso koda Namiji ne shi bai damu ba,don haka Ni Ina da wanda nakeso Yanzu haka ......... ."
  Gaban Sgr ne Ya faɗi rasss!lokaci guda yabi ya susuce ya dabarbarce,jikinshi sai kerma yakeyi,Zuciyarshi sai faman tafarfasa take yi,Ya harzuƙa sosai but he's trying to control his anger,don ta fara wuce gona da iri,

Kowa na wurin sai da yayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login