Showing 144001 words to 147000 words out of 307403 words

Chapter 49 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

dannawa Sgr kira,Bayan ya amsa kiran anan yake sanar dashi cewa Zasu wuce Dawanau Psychiatric Hospital,Sgr yace su haɗu acan,"

A back seat na motar Baban Sadeeq tare da Maman Sadeeq suka shiga suka zauna,Yayin da Abusufyan ya shiga mazaunin driver,Sehrish na a gefenshi,ganin yadda hannunshi ke ta kerma wurin ƙoƙarin tashin motar yasa tace"Daddy,Anya zaka iya driving ɗin nan"?
  A ruɗe yace"Daughter,ki ganni kawai,ba zaki gane halin da nake ciki ba,Am so eager to see her,Kamar nayi fiffike,"
Murmushi ta ɗan yi,Ita kanta ji take da ace tana da fiffike da ta tashi sama don ta ƙarasa asibitin da wuri,

da gudun gaske ya fisgi motar kamar zasu tashi sama,cikin ƙankanin lokaci suka ƙarasa asibitin,

*DAWANAU PSYCHIATRIC HOSPITAL*

A dai dai lokacin da Abusufyan yake ƙoƙarin shigar da motarsu cikin asibitin,Sai ga Motocin Sgr da jiniya mai sautin gaske,sun shararowa a jere,Jibga jibgan sojoji ne a saman motocin bana wasa ba,ko shugaban ƙasa albarka,tuni mutane suka dare aka bar masu hanyar su kaɗae,
A daidai bakin gate din aka tsaida jiniyar,kafin motocin suka shiga cikin Asibitin, Motar Abusufyan ce ta fara shiga sannan nasu suka rufa masa baya,wasu daga cikin sojojin dake a motar ƙarshe ne suka diddiro suka ƙame a bakin gate din shiga sai faman mazurai suke yi kowannansu hannunshi na riƙe da ƙatuwar bindiga gwanin ban tsoro,parking ɗin motocin su kayi,buɗe motar Abusufyan yayi tare da fitowa daga ciki,ya zagaya ya buɗema Su Baban Sadeeq motar suka fito,Sannan itama Sehrish ta fito,tana ƙarewa asibitin kallo,tun kafin ma su shiga ciki,ta fara ayyana yadda zata samu mahaifiyarsu,duk da tana cikin damuwar halin da zasu same ta,

Fitowa Armstrong yayi daga cikin Motarsu,ya zagaya tare da bude mashi,A hankali ya zuro ƙafarshi daga cikin motar,Kafin ya ƙarasa saukowa daga cikinta Masha Allah,Open shirt ce sanye a jikinshi white colour,rigar ta bayyana Ƙirar faffaɗan ƙirjin nan nashi,Cos bai sanya button ko ɗaya ba,a buɗe yabarta sai farar vest,Dogon wandon jikinshi black colour ne,Wankan black & white ya ɗauka,ƙafarshi na sanye cikin oxfords shoes,daga saman sumar kanshi kuma ya sanya facing cap black,Eyes ɗinshi na manne da Sunglasses,Wa'iyazubillah Ya haɗu iya haɗuwa,kamar a buga a jarida,
Duk da yanayin da suke ciki hakan baisa sun ƙi kallon wankan nashi ba,Musamman Babban sadeeq da kuma Maman sadeeq,tare da sauran jama'ar dake zarya a cikin asibitin,Yayi matuƙar jan hankalinsu,Ita kanta Sehrish sai da ta girgiza da irin wankan da ya ɗauka,

Kama hanyar shiga ciki su kayi,Baban sadeeq ne agaba shi da Maman sadeeq,Abusufyan da Sehrish na abayansu,yayin da Sgr tare da Armstrong suke a biye dasu,sai wasu daga cikin security,mutum biyu dake ruƙe da jibga jibgan bindigogi,suna take mashi baya,a bakin OPD suka ƙame,yayin da Sgr da Armstrong wanda ƙugunshi ke manne da bindigu pistol guda biyu suka shiga ciki,batare da sunsha wahala ba saboda su Maman Sadeeq sun san asibitin,suka nufi wurin da nurses suke,wato nurses station,Anan suka taras da Nurses ɗin dake Duty,koda nurses ɗin nan sukayi arba dasu,gaba ɗaya hankalinsu ya koma akan Sgr,kallon ƙurulla suka shiga binshi dashi,
Gyaran murya Abusufyan yayi masu hankalinsu ya koma akanshi,A natse ya soma magana"Sannunku da aiki,"
  Atare suka haɗa baki wurin amsa mashi"Yawwa yalla6ai,munayi maku barka da zuwa,"
   gabatar masu da kanshi yayi tare dasu Sehrish kafin yace"akwai patient ɗinmu dake anan asibitin,munzo dubata ne,'
  ɗaya daga cikinsu ce,ta kai hannu gaban drawer chest ɗin dake a jikin table ɗin gabansu,tana ƙoƙarin zaro roster ɗinsu,tace"Zan iya sanin sunan mara lafiyan naku,"
Abusufyan yace"Sunanta Zainab ibrahim buzuwa,"yayi maganar tare da kallon baban Sadeeq,don yaji idan ya faɗa dai dai,jinjina mashi kai yayi alamar eh,
  A saman table ɗin gabansu ta ajiye patients roster ɗin,tana dudduba sunan marasa lafiyan,
  "Last week,an canza ma wasu daga cikinsu wurin zama,bansan ko kuna da masaniya akan hakan ba,"acewar nurse ɗin
  Kallon juna sukayi hankalinsu aɗan tashe fargabarsu kar ace,an ɗauke abu daga asibitin,
  "Yawwa,itace Zainabu ibrahim buzu ko"?
Har suna haɗa baki wurin cewa "eh,itace,
Murmushi Nurse ɗin tayi tare da cewa"Zainab tana a female ward B,"kallon abokiyar aikinta dake a gefenta tayi tare da cewa"kiyi masu jagora izuwa ɗakin da Zainab buzuwa take,"Amsa mata tayi da toh,sannan ta fito tare da nufar wani corridor,gaba ɗaya suka bi bayanta,kowa da abunda yake saƙawa aranshi,jikin Sehrish dana Abusufyan sae kerma yake yi,duk sun sha jinin jikinsu,

Tun kafin su ƙarasa ward ɗin,mahaukatan dake a killace suka fara kwala masu kira,
  "Yalla6ai,yalla6ai,"Sehrish ba ƙaramin tsoro taji ba,gasu nan gwanin ban tausayi,sae faman zuru hannuwansu suke yi daga cikin bars ɗin,
  "Baiwar Allah!"wata mahaukaciya ce ta kwala ma Sehrish kira,tana nuna ta da hannu,a firgice Sehrish ta juya tana kallonta,Washe mata haƙora tayi tana kashe mata ido ɗaya tace"ki ce wa mijinki ya dinga sanya Niƙabi a fuskarshi,in ba haka ba wlh za'ayi maki kwacenshi,Don mu nan da kike ganin mu ba cikakken hankali ne damu ba,"

  Ba sehrish ba,hatta Sgr sai da ya ɗan murmusa,ba ƙaramin dariya ta basu ba,
  Suna cikin tafiya wata mahaukaciyar kuma ta ƙara kwala masu kira tana fadin"Wayyo Allah,Farin namiji ko maye ne nidai inaso,Ya Allah ka bani fari dogo kyakkyawa,kalan yan kasan waje,In biya sadakin shi ayi mana aure,"tana magana miyau na zalala a bakinta,
  A rude Sehrish tace"Nashiga uku,Wannan wani irin kyau ne da har mahaukata ma suke santinshi"?acikin zuciyarta tayi maganar,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,tajiyo wata mahaukaciyar kuma tana tambayar wai nawa ne farashinshi,
  "Yalla6ai..."hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,jin yadda suke ta kwaɗa mashi kira,duk da jikinta yayi sanyi,tsananin tausayin mahaukatan ne ya kamata,nan take ta shiga tunanin ko awani hali zasu samu oummansu,
  Tana cikin wannan yanayin na damuwa taji hannun Sgr a cikin nata,ɗan juyawa tayi tare da kallonshi,adai dai lokacin shima idon nashi na akan fuskarta,kallon juna suka shiga yi,bakomai ne ya faɗo mata aranta ba,face irin haukan da yayi mata adaren jiya na sauraye,yayin da shima abunda yake tariyowa kenan acikin kanshi,yadda ta tsaya kore mashi saurayen nan,ta ba shi kyakkyawar kulawa har ya samu bacci,ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba,
  Gaba ɗaya sun shagala da kallon junansu,
  Muryar wata mahauciyarce ta kuma katse su da cewa"Ranka shi daɗe,Amma dai sabon aure ne ko?Wlh kunyi kyau kun dace da juna sosai,Wlh har kun tunamin da mijina...."tana faɗin hakan ta fashe da kuka mai sauti,atare suka kai idanunsu wurinta suna kallonta,Cikin shessheƙar kuka tace"Yalla6ai dan Allah ka kula da matarka kuyi zaman lafiya,kada ka wulaƙantata,ka bata kyakkyawar kulawa,Musamman in tasamu ciki,"ta ƙarasa maganar tana matsar kwalla,
Wata irin kunyace ta rufe sehrish,
Maman sadeeq ce ta kalli mahaukaciyar tare da cewa"baiwar Allah,meya faru da mijin naki?baki bamu labari ba,".
  Hannu tasa ta ɗan share hawayenta kafin tace"Naso shi sosai,Munyi aure har mun haifi ƴa'ƴa dashi,babban abun takaici,A wurin haihuwarshi mahaifiyarshi ta mutu da cikinshi,"tana kai ƙarshen zancen nata ta rushe da kuka,. 
  Gaba ɗaya suka fashe da dariya,hatta Abusufyan dake acikin damuwa sai da ya ɗan yi murmushi,Haka Sgr shi kanshi baisan ya saki wannan kyakkyawan murmushin nashi ba,Zuba mashi ido Sehrish tayi tana kallonshi,dimple har biyu suka lotsa asaman fuskarshi,abun yayi matuƙar tafiya da hankalinta,koda ya gane cewa shi take kallo,nan take ya ɗauke murmushin ya tamke fuskarshi,
  A dai dai lokacin da suke ƙoƙarin karya corner su shiga wani ward ɗin,kwatsam suka ji hayaniya na tunkarosu,da sautin takalman mutane,hankalinsu a matuƙar tashe suka kai idanuwansu wurin don suga meke wakana,
  Wata mahaukaciya ce,ta 6allo daga wurin da aka killaceta,da gudun gaske,blue uniform din jikinta duk sun yayyage sun fita hayyacinsu,ƙafafunta ba takalma,gashin kanta duk ya hargitse ya rufe fuskarta gaba ɗaya,a bayanta kuwa likitoci ne da wasu ma'aikata suka biyota suma a guje,suna ƙoƙarin dakatar da ita,
  "Ki tsaya!ki dakata anan!dan Allah ataimaka ataro mana ita,mara lafiya ce ta kufce mana,"ɗaya daga cikin likitocin dake biye da ita ne yayi maganar,hannunshi na ruƙe da syringe,yayi annoucement ɗinne don asamu wanda zasu taimaka wurin damƙo masu ita,
  Duk tabi ta firgita ta ruɗe,ko kallon gabanta batayi,da dukkan ƙarfinta take yin gudun gashi sumar kanta duk ta zubo ta rufe mata har idanuwanta,ita kanta batasan wurin da zata dosa ba,burinta kawai tabar hannun masu fararen kayan dake biye da ita,
  Sai gara likitocin takeyi duk sun galabaita,gadan gadan ta tunkari wurin da su Sehrish suke,Naɗe hannun riga Abusufyan ya shiga yi,haka Sgr ma he's ready to help,ba'a maganar Armstrong da yayi shirin yi mata ɗaukan jariri, jira kawai suke ta ƙaraso wurinsu,su cafke ta,
  Tunkan ta ƙarasa wurinsu,ƙafafuwanta suka harɗe gaba ɗaya ta tafi a karkace zata kife ƙasa,da sauri Abusufyan ya damƙota,ta faɗa ƙirjinshi ta tsorata sosai,ƙankame shi tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,jikinta sai kerma yake yi,
  Ƙarasowa likitocin su kayi suna faman sauke ajiyar zuciya,
  "Yalla6ai,mun gode sosai,ba ƙaramin taimako kayi mana ba,baiwar Allah nan,daga shiga yi mata Allura ta kubce mana,ta bamu wahala sosai,"ɗaya daga cikin likitocinne yayi maganar,
   Ɗayan doctor ɗin dake a gefenshi yace"Allah ya taƙaita wahala,Da bamu son inda zata dosa ba,"
..su uku ne likitocin sae Nurse ɗaya dake a biye dasu,
  Hannu Abusufyan yasa yana ƙoƙarin 6an6arota daga jikinshi,ae kuwa a tsorace ta ƙara ƙankameshi tana faɗin"dan Allah kada ka bari su tafi dani,wlh ni ba mahaukaciya bace,da hankalina,ƴa'ƴana nake nema,dan Allah ku kaini wurin ƴa'ƴana kar a kashe mun su suma,koda sau ɗaya ne in sanyasu acikin idanuwana,"
  Rasss! yaji gabanshi ya faɗi,Hatta Sehrish sai da gabanta ya faɗi,saboda jin muryar Mahaukaciyar da tayi maganar,"
  Ƙarfi yasa ya ɗaɗɗago da kanta,daga saman ƙirjinshi,Hankalinshi a matuƙar tashe yake kallonta,ta runtse idanuwanta jikinta sae faman kerma yake yi,
    Bazai ta6a mantawa da fuskar abunshi ba,haddar da yayiwa fuskarta bamai gogewa bace,Bazai ta6a mantawa da ita ba,duk irin canzawar da zatayi,
  Muryarshi na kerma ya ambaci sunanta da ƙarfi"ABU"!gaba ɗaya hankalin Sauran ya dawo kansu,
   da ƙarfi Sehrish ta Ambaci sunanta"OUMMA!!"a firgice mahaukaciyar ta juya tana kallon Sehrish da tayi magana,duk tabi ta ruɗe,hannu tasa ta dafe kanta wani irin jiri ta dinga gani acikin idanuwanta,Nan take jikinta ya soma kerma,sumewa tayi gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa,da sauri Abusufyan ya dawo da ita jikinshi sosai ya ƙanƙameta,Lokaci guda hawaye suka shiga wanke mashi fuskarshi,Sehrish kuwa tuni ta fashe da matsanancin kuka,Na farin cikin ganin Oummansu,
   Kowa fuskanshi ɗauke da farin cikin ganinta da su kayi batare da sunsha Wahala ba,likitocin da suka biyota,duk jikinsu yayi sanyi,musamman yanayin da suka ga mutumin ya shiga,tare da yarinyar dake a gefenshi,ta wani 6angaren kuma fargaba suka fara yi kada ace wa'adin zaman abu ya ƙare a asibitin,Saboda sun saba da ita,ko acikin mahaukatan dake a Gidan,
  Gyaran murya Sgr yayi tare da cewa"We don't ave time to waste here,Uncle zamu wuce da ita gida ne,idan yaso Dr ɗin dake kula da ita,Sai ya bi mu can,"
  Hankalin ɗaya daga cikin Dr ɗinnan ba ƙaramin tashi yayi ba,yanayin yadda ya furta"tafiya za kuyi da Zainab"?
  Jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"Zamanta acikin asibitin nan ya qare,"ya ƙarasa maganar har lokacin hawayen basu daina sauka akan fuskarshi ba,gashi ya ƙanƙameta ajikinshi,ko warin jikinta baiji,
  A ruɗe Dr ɗin yace"Haba yalla6ai,mezai hana ku barta anan acigaba da duba ta,har Allah ya Bata lafi......."kasa ƙarasa maganar yayi ganin irin kallon da Sgr yake yi mashi,duk sai ya sha jinin jikinshi,
Sai lokacin Baban sadeeq ya tsoma baki,
  "Doctor,Wannan da kake gani Mijinta Ne!wannan kuma ƴarsu ce,yaran da take yawan ambato acikin bakinta,To wannan ɗaya ce daga cikinsu,Ƴan ukune gare ta,ƙaddara ce ta rabasu da ita,Yanzun kuma Allah ya haɗasu da ita,"
  Yana kai ƙarshen maganar,likitocin suka haɗa baki wurin cewa"Allahu akhbar!Amma mun tayata Murna sosai,Allah yasa silar samun saukinta kenan" gaba ɗaya suka amsa da Amin,
  Sun jima suna magana,a tsaye kafin daga bisani,Abusufyan ya ɗauketa asaman kafaɗarshi,Sai da suka fara shigar da ita medical room likita ya duba ta sosai,tare da yi mata allurorin da aka saba yi mata,aciki hada na bacci,Tsayawa suka yi acikin asibitin suna ciccike wasu mahimman bayanai da ake bukata a wurinsu,harda Malam nura su da suka kawo ta asibitin,kafin Aka mallaka masu ita, 😍

*Boss Bature*

  *Hayaaam*

Tun da Aunty babba tabarta a asibitin nan magashiyan rai hannun Allah,Sai yau ta dawo cikin Hayyacinta,duk ta bushe ta dishe ta ƙanjame,jikinta duk faci,kamar wadda tayi hatsarin Mota,Komai nata ya ƙare,tayi mamakin ganinta a asibiti kuma babu kowa atare da ita,daƙyar ta iya miƙewa zaune,jikinta sae kerma yake yi,lokaci ɗaya ta shiga tariyo abunda Haroon yayi mata,fashewa tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,duk taji ta tsani kanta kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu,cikin shessheƙar kuka take faɗin"Meyasa na farka ban mutu ba?me yayi mun saura acikin duniyar nan,Natsani kaina,Natsani komai ban sha'awar cigaba da zama acikinta!bazan ta6a yafe mashi ba,mugu azzalumi ya cutar da rayuwata,hannu tasa ta yaye farin yadin da aka rufeta da shi,riga ce ƴar dai dai guiwa aka sanya mata blue colour kamar uniform,yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin ƙoƙarin ɗage rigar don taga menene a wurin,don tana jin kanta kamar ba dai dai ba,
  Slowly ta tattare rigar,ta dage ta,koda tayi arba da gabanta,A rikice ta mayar da rigar ta rufe tare da fashewa da wani kukan mai cin rai,
  Tana cikin kukan nan,Dr ya shigo tare da Nurse abayanshi,
   Lallashinta suka shiga yi har suka samu ta lafa,Sannan Dr ɗin ya soma magana a tsanake,
  "Baiwar Allah,Ya jikin naki"?_
Cikin shessheƙar kuka tace"da sauƙi,dan Allah ku faɗamun wanene ya kawo ni asibitin nan,yaushe aka kawoni,"tana magana hawaye na wanko fuskarta,
  "ƴar uwarki ce,ta kawoki asibitin nan,Tun last week,Sai dai tun ranar da ta kawoki,Ta gudu tabarki anan bamu ƙara jin ɗuriyarta ba,Mun nemeta sosai ba mu same ta ba,A ƙarshe sai muka samu wannan wasiƙar a gefen gadon ki,bamu karanta abunda ke ciki ba,"ya ƙarasa maganar tare da miƙa mata wasiƙar,
Tunkan ta kar6a gabanta ya shiga faɗuwa rasss!rass!buɗe paper ɗin tayi ta soma karanta abunda ke cikinta,tun da ta fara karantawa tafin hannunta ɗaya ke rufe da bakinta,hawaye sai shararowa sukeyi daga cikin idanuwanta,ƙiris ya rage zuciyarta ta buga saboda tsabar takaici,Ba ta ta6a tsammanin cewa Aunty laila zata iya guduwa tabarta a asibitin ba,Taji ciwon kalmar nan da ta kirata,Wato karya wadda ba'a rabata da maza,ta yanke mata hukunci batare da tasan ainihin abunda ya faru da ita ba,"
Dunƙule takardar tayi ta cukuikuyeta a hannunta,sai faman matsar kwalla take yi,wasu nabin wasu,
"Lokacin sallamar ki bai yi ba,Amma ya zama dole muyi discharge ɗinki saboda kuɗin gado da aka biya sun ƙare,Sannan akwai wasu bayanai masu mahimmanci game da lafiyarki,da muke so mu samu wani makusancinki mu sanar dashi,Gashi baki da kowa,Bayan wannan akwai alluran da kike buƙata da kuma magunguna domin bunƙasa lafiyar jikinki,Ko kina da wani wanda zai iya taimaka maki"?
  Kuka sosai hayaam take yi,tunani ta shiga yi wa zata kira yanzu don ya taimake ta?Waye take dashi wanda zaiji tausayinta,A iya saninta bata da kowa,in ma akwai babu wanda zai agaza mata saboda sanin Mugun halinta,Shiyasa a koda yaushe akeso mutun ya kasance yana aikata abun kirki a rayuwarshi,ba ka son awani hali zaka tsinci kanka ba a nan gaba ba,duk wani abu da kake taƙama dashi,Walau kyau ko dukiya ko mulki,wata rana Allah zai iya kwace abunshi,Hayaam tayi dana sanin rayuwarta gaba ɗaya,abun ya tsaya mata arai,Wai har ƴar uwarta wadda suka fito ciki ɗaya,Zata iya guduwa tabarta a gadon asibiti rai hannun Allah,ta rayu kota Mutu wannan badamuwarta bace,Wannan wace irin rayuwace?ɗan uwa na gudun ɗan uwanshi,koda yake ɗa ma ya kashe ubansa,Sau nawa akayi?

"Baiwar Allah,kin yi shiru ba kice komai ba"?Dr ɗinne ya katse mata zancen zucin da takeyi,
  Cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah,ku taimaka mun da waya,inaso na kira ƴar uwata ne,"_
Hannu Dr ɗin yasa a aljihun wandonshi ya zaro wayar shi,Infinix ya miƙa mata,jiki na rawa ta kar6i wayar,sai da ta ruƙeta a hannunta ta shiga tunanin wa zata kira,Bakowa ya faɗo mata aranta ba,Fa ce AMANI,duk da tana jin fargabar kada Amani,ta balbale ta da faɗa sakamakon irin wulaƙancin da sukayi masu,daƙyar ta iya danna numbobin wayar Amani,da yake ta haddace numbarta a kanta,Danna mata kira tayi,nan take ya shiga,gabanta sai faɗuwa yake yi,almost 3 times Amani bata ɗaga ba,

A lokacin tana a kitchen tana shirya lunch,tajiyo muryar Amaal tana kwala mata kira,fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin ta tunkarota tana tambayar wanene ke kiranta a waya,
Amal dake saukkowa downstairs,tace"New number ce,bansan wanene ba,ta ƙarasa maganar tare da miƙa mata wayar,zuba ma numbar ido tayi tana kallonta,a ƙa'ida bata cika ɗaukar bakuwar number ba,amma tunawa da yadda Amal tazo hannunta,ta hanyar kira da bakuwar number,yasa tayi tunanin ɗaga kiran kada ace wani abu mai mahimmanci ne,Sanya wayar tayi a kunnanta bayan ta amsa kiran,sallama tayi"Assalamu alaikum,"
  On the other hand Hayaam na jin an ɗaga kiran,jiki na rawa ta kara wayar a kunnanta,cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunanta"Aunty Amani,"
  Cike da mamaki Amani tace"To fa,kamar muryar Hayaam nake ji,"
Murya na kerma tace"Ni ce,"shiru amani ta ɗan yi kafin tace"Lafiya kika kirani?fuskarta a ɗaure tayi tambayar kamar tana agabanta,
  Cike da fargaba hayaam tace"Aunty Amani ina gadon asibiti,nayi fiye da sati a kwance,babu wani a kusa dani,"
   Murmushi Amani ta saki tare da cewa"Sai akai yaya kenan?menene amfanin kira na?ina Laila ne?inasu Abrah?
  Jiki asanyaye Hayaam tace"Duk basu atare dani,Aunty laila itace ta kawoni asibitin,Amma ta gudu ta barni ni kaɗai,gashi ina cikin mawuyacin hali,kamar zan mutu,"
  tana kai ƙarshen maganar Amani tace"Oh Allah sarki,Allah ya baki lafiya,"
  "Dan Allah Aunty Amani ki taimaka mun,Nasan kina da kyakkyawar zuciya,"
  Fashewa Amani tayi da dariya mai sautin gaske,hada yin shewa kafin tace"Sai yau kika san inada kyakkyawar zuciya?Kin manta irin rashin mutuncin da kuka shuka mana?Ashe akwai rana irin wannan da zaki nemi taimako a wurina?bakiyi tunanin hakan ba?Saboda tsabar rashin kunya a haka kike tunanin cewa zan taimake ki,Koda yake dama ae ba kunya gare ku ba,"guntun tsoki taja mtswww kafin ta ɗaura da cewa"Karki kuskura ki ƙara kiran layina da sunan taimako,don da in taimaki Mugaye masu kafirar zuciya irin taku,wlh ƙwara na tattara duk wani abu dana mallaka,na kaishi gidan marayu,ko Allah ya bani Lada,Amma taimakon irinku,bakomai zai janyomun ba,fa ce Zunubi!"tana kai ƙarshen maganarta,tun kan taji me Hayaam zata ce mata,Nan take ta katse kiran,
  "Aunty Amani meyasa zakiyi mata haka"?Acewar Amal,wadda tuni tausayin hayaam ya kama,
  Harara Amani ta watsa mata tare da cewa"Oh harkin manta irin Muguntar da su kayi mana kenan!waɗannan mutanen da baƙin cikinsu mahaifiyar mu ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login