Showing 81001 words to 84000 words out of 307403 words
Chapter 28 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
bugunki ba,saboda ba halayyarsa bace,"
Haɗiyar yawu tayi,tana sauraronshi,ɗan dakatawa yayi da yin maganar,kafin ya ɗaura da cewa"daga yanzu inaso,ki cigaba da aiki a ƙarkashinsa....' tunkan ya ƙarasa maganar Sehrish tace"Amma daddy,ka hanani zuwa part ɗinsa fa"
"A yanzu na soke wannan!inaso ki yi mashi biyayya,ki bishi sau da ƙafa,komai yake so kiyi mashi kawai!part ɗinsa kuma koda wani lokaci zaki iya zuwa ki shiga,even in the midnight,indai ya buƙaci ganinki ki je kawai,"
Gaba ɗaya Abusufyan ya gama ruɗar da ita,la66anta har kerma sukeyi wurin cewa"dad..dy!bangane me kake nufi ba,dan Allah ka fahimtar dani,"
"Ki tafi kawai kiyi duk abunda nace maki,idan lokaci yayi zan sanar maki,"
Juyawa tayi tare da zura ƙafarta,tabar bedroom ɗin nashi,lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu,ya ƙurama ceilling ɗin sama ido yana kallonshi tamkar mai karanta wani abu ajikinshi,tunani ya shiga yi acikin zuciyarshi,ya shiga tariyo abunda yaji a kunnuwansa,
_Na amince zan aureta,bana son abun ya ɗauki lokaci,bana son taron mutane,kuma banaso kowa ya sani,saboda ba auren dundundun bane,nan da wata uku zan sake ta,zan aureta ne ba don ina sonta matsayin matata ba,sae don tayi mun aiki kafin na bar nigeria_
Hannu Abusufyan yasa tare da ɗaukar wata takarda dake ajiye saman side drawer ɗinshi,zuba ma takardar ido yayi yana kallonta,Agreement paper ce (Takardar yarjejeniya)mai ɗauke da signatures na mutun uku,"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da zura ta cikin drawer chest ɗin daya fiddo akwatin nan da ya bama sehrish ya sanya takardar aciki ya ajiyeta,sannan ya mayar da ita ya datse,rufe idanunshi yayi bakowa bane ya faɗo mashi arai ba face ABU,nan take yaji kewarta ta lullu6e shi,Allah sarki abu,tana raye kota mutu?
A 6angaren Sehrish kuwa bayan fitarta daga bedroom ɗin Abusufyan,a ƙopar ɗakinsu ta tsaya,warware mayafin da ta laga akanta tayi,sannan ta lullu6e small box ɗin dake hannunta don kada wani ya gani,tura ƙopar ɗakin tayi sannan ta shiga daga ciki,babu kowa acikin ɗakin,sautin ruwan da taji ne daga cikin toilet ya tabbatar mata da cewar Jahad ce ke wanka,cikin sauri ta lalla6a gaban dressing mirror ɗinsu,ta zuƙunna gaban drawer ɗin dake ɗauke da mirror ɗin,ta janyo gida na ƙarshe,ta tura small box ɗin acikinsa can ƙurya ta turashi,sannan ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,miƙewa tsaye tayi har lokacin bata daina mamakin abubuwan da Uncle ya faɗa mata ba,abun ya ɗaure mata kai sosai,
Safa da marwa ta shiga yi acikin ɗakin,takasa zama saboda yanayin da ta tsinci kanta aciki,
*Boss Bature*
❤🤍❤
AMRISH,
Tun jiya da daddare data farka,tana bullayi asaman gadon bayan an samu nasarar ceto rayuwarta,doctor yayi mata allurar bacci bata ƙara farkawa ba,yini tayi a kwance tana bacci kamar matacciya,hankalinsu zeenatu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,musamman Mommyn Amrish ɗin,bata ta6a tunanin amrish zata rayu ba,amma cikin ikon Allah sae gashi taji sauƙi sosai,poison ɗin da tasha bai kaiga yi mata illa ba,sunyi gaggawar kaita asibitin kuma likotoci sun taru akanta wurin ceto rayuwarta,wannan ne yasa bata jigata ba sosae,amma still da sauranta don ba ƙaramin galabaita tayi ba,yanzu haka ma ƙarin ruwa ne aka sanya mata,
Mommynta na zaune asaman plastic chair din dake agaban gadonta,fuskar nan tayi jawur da alama ba ƙaramin kuka tasha ba,ga rashin baccin da basu samu ba adaren jiya,gaba ɗaya hankalinta na akan Amrish dake kwance magashiyan tana bacci,
Zeenatu na a zaune daga gefen gadon da amrish ɗin take kwance,duk sunyi zuru suna kallonta,tunda safe Sofia ta koma gidansu,ita kaɗae ta rage saboda tace bazata koma gidansu ba har sai Amrish taji sauƙi sun koma gida,
Suna cikin zaman nan,kwatsam Amrish ta buɗe idanunta ta zazzaresu a wani irin firgice ta sanya hannu ta fizge robar ƙarin ruwan da akeyi mata,hankali atashe Zeenatu tace"Mommy amrish ta farka!ta cire ƙarin ruwan da aka sa mata,"jin wannan maganar yasa Mommyn yin firgit ta dawo cikin hayyacinta daga zurfin tunanin da ta shiga,sai dai kafin suyi wani yunƙuri,tuni Amrish ta diro daga saman gadon,ta watsa aguje,zeenatu na ƙoƙarin tarota,takai mata wani kakkwaran naushi a saitin Cikinta,nan take zeenatu ta zube ƙasa hannunta dafe da cikin,ta fasa uwar ƙara tana faɗin"Wayyo Allah na!cikina!nashiga uku,
Ko waiwayonta amrish batayi ba,hanyar fita kawai ta nufa,da gudu ta fice daga ɗakin,bin bayanta Mommyn tayi tana yarfa hannu a ruɗe take faɗin"Help!help!!dan Allah jama'a ataimaka a taro mun ita!mara lafiyace zata gudu,'
Da gudu wasu nurses suka bi bayan amrish,hada wasu daga cikin masu zuwa dubiya,
"Amrish dan Allah ki tsaya!wai meke damunki ne!bakiji ina magana ba!ina zaki je ne!," hankali tashe mommyn ke magana,amma ko sauraronta amrish bata yi ba,duk wanda ma yayi ƙoƙarin tarota bugu take kai mashi kamar ƴar wrestling,gashi wani irin ƙarfine da ita kamar na Doki,in ta daki mutun sai ya kusa zaucewa,duk yadda suka so su kama amrish,amma abun yaci tura,domin kuwa 6att suka neme ta suka rasa acikin asibitin,saƙo da lungu babu inda basu duba ba,amma babu ita babu alamarta,ko mai kama da ita ma babu,nan fa hankalin kowa ya tashi,hatta security guards ɗin dake tsaron gate ɗin asibitin,sae da aka tambayesu,sun tabbatar da cewar basu ga fitarta daga asibitin ba,sae dai ko a wani wurin ta 6oye,Hatta Cctv footage sae da aka bincika,amma ba aga ta hanyar da Amrish tabar cikin hospital ɗin ba,kuma ba'aga wurin da ta 6oye ba,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,yarinya kamar mai iskokai?babban abunda zai baka mamaki ƙarfin daya zo mata,mutumin dake kwance magashiyan a gadon asibiti,amma ya tashi farat daya da irin ƙarfin nan a jikinshi❓
Saboda tsabar tashin hankalin da Mommyn Amrish ta shiga,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume,sai dai nurses suka cuccu6eta aka shiga da ita ciki,suka kwantar,itama zeenatu sae da suka kwantar da ita don kuwa ba ƙaramin buguwa tayi ba,naushi ɗaya tayi mata aciki,amma sae da jini ya zuba a bakinta,
*ANA WATA GA WATA!JAMA'A INA AMRISH TA SHIGA NE*?😳😳😳
*Aunty Babba*
Fitowarta kenan daga cikin toilet tana faman dafe cikinta,ɗagowa tayi tana kallon hayaam dake zaune gefen gadon ta zabga uban tagumi da hannayenta biyu,Hafsat kuwa na asaman gadon kwance ta lullu6e da bargo jikinta sae kerma yake yi,wani irin zazza6ine mai zafi ya rufar mata,tunda rana tagaza motsa jikinta,abun gwanin ban tausayi,
Kwatsam!sukaji an banko ƙopar ɗakin nasu,dafe ƙirji Aunty babba tayi tana kallonshi,sae faman huci yakeyi yadda kasan mayunwacin zaki,da ƙafarsa ya tura ƙopar ɗakin ta rufe,hayaam na ganinshi a razane ta haye saman gadon,jiki na rawa ta wuntsila daga ƙasan gadon ta 6oye,tana faman zazzare ido,
Cikin inda inda ta ambaci sunan shi"I..ishaq!"
A zafafe ya ƙarasa inda take,kwakkwarar damƙa yakai ma wuyanta,ya shaqeta sosai,yadda ko ihu bazata iyayi ba,saboda tsabar raɗaɗin da taji nan take ta saki fitsari a wando,wani irin gumi ne ya shiga tsattsafowa daga gefen fuskarta,idanunta sunyi jawur cike tab da kwalla,ƙwayar idon tamkar zata zazzago ƙasa,
A ruɗe hafsat ta fasa uwar ƙara,ganin abunda daddynta ke ƙoƙarin yi,gadan gadan so yake ya kashe Mommynta,da gudun gaske ta duro daga saman gadon tana kuka,
"Kafin ki kashe su!Ni zan fara kashe ki!muguwa kawai!Nayi danasanin aurenki laila!nayi danasanin saninki da nayi,Nayi danasanin haɗa zuri'a ɗaya dake,Allah ya isa tsakani na dake!Na tsaneki!kin fita araina!ban sonki!bansan ganinki!"daƙyar sautin muryarshi ke fita saboda tsabar 6acin rai,a fusace ya buga kanta jikin bango,nan take Aunty babba ta baje ƙasa a sume,'
Juyawa yayi tare da aza idanunshi akan hafsat dake tsaye tana faman zabga uban kuka fuskarnan tayi jaga jaga da hawaye hada majina,nunata yayi da yatsan hannunshi sannan yace"dake da uwarki!ku tattara kayanku ku bar gidan nan!tun kafin inyi sanadin mutuwarku!muguye kawai waɗanda ba Allah aransu,"
Hannu hafsat ta aza akanta tana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!"
Juyawa ishaq yayi da sauri zai bar ɗakin,da gudun gaske ta ruƙo rigar jikinshi tare da zubewa saman guiwowinta tana kuka tana yi mashi magiya akan,karya koreta,
"Daddy dan Allah kayi haƙuri ka yafe mun!wlh ba laifina bane,nasan mun cutar dasu,amma inaso ka sani daga baya na ƙaunace su,Daddy ka yarda dani Mommy itace take azabtar dasu,kuma itace tayi silar barin....'bata ƙarasa maganar ba sakamakon bugun daya kai mata da ƙafarshi,da sauri ta dafe gefen bakinta daya buga wurin har ya fashe,jini ya shiga ɗiɗɗigowa,dogon tsoki ishaq yaja tare da cewa"Kada ki kuskura ki ƙara kirana da sunan daddy!don ni ban haifi wata ƴa mai suna hafsat ba!tunda har kin za6i ki bi mugun hali irin na mommynki,don haka gaki ga ita,duk in da zata je ƙafarki ƙafarta,karku kuskura Dare yayi maku acikin gidan nan!don wlh sai kunyi danasanin haihuwarku da akayi acikin duniyar nan!don bazan raga maku ba,tamkar ban sanku ba,haka zan hukunta ku!kuma idan ta farka daga suman da tayi ki sanar da ita cewa NI ISHAQ NA SAKE TA,!!!!
Wani irin bugu zuciyar hayaam tayi ji kake daramm!!kamar an buga ganga,nan take ido ya raina fata,sae faman mazurai takeyi abayan gadon da ta la6e,Na shiga uku Ni hayaam An saki Aunty laila!Shikenan komai ya ƙare komai ya lalace!mun gama yawo!!
Ya ƙarasa maganar tare da kai hannu tamkar zai 6alle ƙofar ya fuce,Amani dake la6e tana sauraronsu da gudun gaske ta watsa,sae cikin ɗakin da suka sauka,Tana shiga cikin ɗakin ta daka tsalle,bakinta awashe saboda tsabar dariyar mugunta hada hawaye ke fita a idonta,Amal dake zaune saman gado tana buga game a wayar amani,ganin yadda amani keta dariya kamar wata zautacciya,yasa ta ɗan dakata da buga game ɗin tare da cewa"Aunty Amani meya sanyaki farin ciki har haka"?
Daƙyar ta iya dakatawa da yin dariyar tace"Amal ba zaki gane bane,Wani buri da nake dashi ne ya cika ayau ɗin nan!!waɗanda suka jima suna ƙuntata rayuwarmu,tun yau zasu fara gir6ar abunda suka shuka," tana magana tana dariya,
Murmushi kawai Amal tayi tare da mayar da hankalinta kan game ɗin da take bugawa,
General ishaq na fita daga ɗakin,hayaam ta lalla6a ta fito,yadda kasan lagwanin fitila haka take tafiya,jikin taƙaura yayi la'asar wannan hada magriba ma,zuƙunnawa tayi gaban Aunty babba dake baje ƙasa,ta fashe da wani irin matsanancin kuka,Hafsat na kuka itama tana kuka,babu mai lallashin wani,kowa takansa yake yi,
Cikin shessheƙar kuka hafsat ta soma magana"Allah ya isa tsakanina dake Aunty hayaam,kun cuci rayuwata duk don saboda ku ne mommy ta aikata abunda ta aikata don taga ta cika muku burinku,gashi nan yanzu abun ya shafe ni,kunja daddyna ya kore ni,Ni bansan ku wasu irin mutane bane!sam baku da zuciya kare ya lashe,kun nace kun liƙe dole sai kunyi arziƙi da gumin wasu,ku bazaku tashi ku nemi na kanku ba,sam babu Allah aranku,mugunta kawai kukasa agaba,shiyasa har yau babu wani cigaba acikin lamurranku!wlh yanzu ma kuka fara gani!indai bazaku koma ga Allah ba,,ku tsaya a iya matsayin da Allah ya ajiye ku,ku daina hangen na wasu,wannan dogon burin da kwaɗayin abun duniyar ba inda zai kai ku face ya jefa ku ga halaka....."
Itadae hayaam bata tanka mata ba,saboda bata da abun cewa,har wani zazza6i take ji ajikinta,saboda tsabar tashin hankalin da take ciki,komai ya jagule masu,
Miƙewa hafsat tayi,jiki ba ƙwari ta ƙarasa tare da janyo trolley ɗin kayansu da suka zo dashi,janshi tayi izuwa gaban wardrobe ɗin hayaam,ta buɗeta,kayansu dake aciki tashiga fitowa tana ninkesu,Cikin trolley ɗin take jerasu,
Miƙewa hayaam tayi tana tunanin inda zata samu ruwa ta yayyafa ma Aunty babba,saboda babu ruwa acikin ɗakin,kuma tana jin tsoron ta fita waje suci karo da mutumin,tana cikin wannan tunanin ta tuna da akwai fanfo cikin toilet,da sauri ta shiga ciki a tafin hannayenta ta tarbo ruwan,da sauri da sauri tazo ta yarfa mata shi a fuskarta,dogon numfashi Aunty babba taja,tun kafin ta buɗe idanunta ta shiga fadin"Ruwa!Ruwa!" jin haka yasa hayaam yin tunanin ta fita waje ta samo mata ruwan,buɗe kopar dakin tayi cikin sanɗa ta fito tana tafiya acikin corridor din dakunan nasu,cikin sa'a ta taras babu kowa a main palour din,ƙarasawa tayi wurin fridge ɗinsu,ta bude jikinta na kerma ta ɗauko robar ruwa,da gudu ta koma cikin ɗakin,
Ƙarasawa tayi tare da taimaka ma Aunty babba ta tashi zaune sannan ta miƙa mata bottle water ɗin,A tsiyace ta 6alle murfin robar,ta kafata a bakinta,yadda kasan zata haɗa da robar duka ta cinye,abun kamar yaƙi,ta damƙi robar,sae kwankwaɗar ruwan take,kwatt!kwatt!!har sae da ta shanye ruwan duka tass,sannan ta saki robar ƙasa,sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi,hannunta na dafe da kakkauran wuyanta sae faman Murzarshi takeyi,wurin sae raɗaɗi yake yi mata kamar an barbaɗa mata attarugu,idanuwan nan nata sunyi jawur luhu luhu,sae da tadawo cikin hayyacinta sosai sannan ta kalli Hayaam tare da cewa"hayaam meya faru dani ne?ya akai na ganni akwance ƙasa?
Kafin hayaam ta buɗe baki tayi magana,tuni hafsat ta katse mata hanzarinta da cewa"Mommy!kina nufin cewa kin manta duk abunda ya faru?idan ma kin manta bari na tuna maki,Dadddy ne ya damƙi wuyanki ya shaqeki,sannan ya bugaki ajikin bango har saida kika suma,"
Shiru aunty babba tayi tana tariyo abunda ya faru,
"kuma yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan,kada mu bari dare yayi mana,bayan haka kuma ya dankara maki saki ɗaya"rai a6ace hafsat ke maganar,
Wata irin mahaukaciyar dariya Aunty babba ta kwashe da ita kamar wata zautacciya,hakan ba ƙaramin mamaki ya basu ba,miƙewa tsaye tayi tana gyara ɗaurin ɗankwalinta tace"Da sauƙi ma,Ni nayi tunanin wani mummunan hukunci zai yanke mun,sai me don ya kore ni?sakin ma da yayi mun wlh ko ajikina,yayi a banza Ae akwai sauran igiyoyi guda biyu,Ni nasan cewa muddin Abbansu yaji cewar ya sake ni,sae yasa ya mayar dani,Ae ni wlh gaba takaini gobarar titi A jos!" To fa,
sakin baki hafsat tayi galala tana kallonta,ba ita kaɗae ba hatta hayaam abun ya ɗaure mata kai,sunyi tunanin cewa in taji ishaq ya sake ta,xata haukace masu ne,amma sae gashi ko ajikinta!zuciyar ta bushe,
Sae faman tiƙar dariya takeyi kamar sabon shiga a fagen hauka,lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta,tare da kallon hayaam tace"Maza ki tattara kayanki,don atare dake zamu tafi,"
Hankali tashe hayaam tace"Ni kuma?saboda me zamu tafi atare"?
Shu'umin murmushin nan nata tasaki kafin tace"Saboda inaso,muje wurin bokan nan baba ibliss!wannan karan ba fashi,Dole in kawo ƙarshen auren Amani!kamar yadda zanyi zawarci itama haka nakeso tayi shi,sannan waccen mahaukaciyar yarinyar da tayi silar tona mun asiri har ishaq ya sanya hannunshi ya shaqe mun wuyana na kusa sheqawa barzahu wlh saina yi Ajalinta!!!sannan kuma aurenki da Sgr ba fashi!Wlh ko ta halin ƙaƙa!ko suna so ko basa so sai an ɗaura shi!In har kika ga ba'ayi auren nan ba!To sai dai in bana a doron duniyar nan!ko kuma shi RAFAYET ɗin Ya daina numfashi ne acikinta!sai dai kowa ya rasa wlh!da alama har yanzu basu san wacece Ni ba!zan nuna masu true colour ɗina!Ni dasu shege ka fasa!!" tana magana tana fitar da huci,
Mugun abu kokayi bacci?yace idona biyu 👀!ANA WATA GA WATA,
Zuru hafsat tayi tana kallonta,abun yafi ƙarfinta,lamarin Mommyn nata sae addu'a,tunani ta shiga yi anya Mommynta bata fara shaye shaye ba?kodai tana da iskokai ne?
Suna cikin wannan tsayuwar,aka kwankwaso ƙopar ɗakin nasu,a tsiwace Aunty babba tace"Wanene"?
"OMAR NE" koda jin muryar marshal Omar nan fa kowa ya shiga taitayinsa,
"Hayaam je ki buɗe mashi ƙopa,muji dame yazo!in shima zuwa yayi don yaci mutunci na to bismillah!kowani shege dai dai nake dashi,"kamar wata ƴar daba haka take maganar,
Buɗe mashi ƙopa Hayaaam tayi,tun daga irin kallon da taga Omar ya watsa mata tuni tashiga ƴan kame kame tana sunnar da kai,
Shiga cikin ɗakin nasu yayi,yayin da idanunshi ke akan Aunty babba wadda ke tsaye ta ruƙe qugu,sae faman jijjiga jikinta takeyi kamar wata ƴar bori,
Janye idanunshi yayi daga kanta ya mayar dasu kan hafsat,wadda ke tsaye ruƙe da trolley ɗin kayansu,ganin yana kallonta ne yasa ta ɗukar da kanta ƙasa cike da jin kunyarshi,
"Ina zaki je ne"? Yayi maganar fuskarshi a ɗaure,
Muryarta na rawa tace"dad..dy ne yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan kada mu kuskura mu bari dare yayi mana anan,"
"Ban da ke!su kaɗai zasu tafi,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,har ta gaza rufe bakinta saboda tsabar farin ciki,"
Mayar da idanunshi yayi kan Aunty babba dake tsaye ruqe da qugu yace"Major na awaje yana jiranku,idan kun kammala shiryawa ku same shi,Nayi mashi magana zai kai ku hotel ɗin da zaku kwana kafin gobe da safe sae ku wuce maiduguri,Amma fa in kuna so kenan,sannan kuma....'ya ɗan dakata da yin maganar tare da zura hannunshi cikin aljihun jeans ɗin dake ajikinshi ya zaro bendir ɗin kuɗi na ƴan dubu dubu,a ƙalla zasu yi dubu ɗari ɗaya,ya miƙa masu,jiki na rawa hayaam ta kar6e kuɗin tana yi mashi godiya,
...murmushi Marshal Omar ya saki tare da cewa"No,ba sai kin gode mun ba,nayi ne don Allah,'
Yana kai ƙarshen maganar ya juya tare da fucewa daga dakin yana dariya gami da girgiza kanshi,
Bayan fitarshi aunty babba ta buga tsoki,tana faman hura hanci tace ma hayaam"maza ki shirya mana kayanmu,naji ana kiran sallar magrib,zae fi mu lalla6a mu fuce daga gidan batare da kowa ya ganmu ba,nasan duk sun tafi salla,"
Amsa mata hayaam tayi da toh,sannan ta juya tare da shigewa cikin toilet,
Hankalin hafsat ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana faman sakin murmushi,dama babban tashin hankalinta shine idan tabi su Aunty babba maiduguri bazata iya rayuwa cikin gidansu ba,sau ɗaya ta ta6a zuwa,bataji daɗin zama agidan ba,muggan talakawa ne,babu wani abu na more rayuwa acikin gidan,sae ma abun haushi da takaici da zaka taras,
Kusan minti Goma shabiyar sai ga aunty babba ta fito daga cikin toilet ɗin,da alama wanka tayi,xanin atampar jikinta ne tayi ɗaurin gaba dashi,ya jiƙe sharkaf saboda ta ɗauraye shi acikin toilet da ta shiga,
Batare da 6ata lokaci ba,suka shirya tsaf ita da hayaam,dogayen riguna suka sanya ajikinsu,sannan suka aza mayafi daga sama,kama hanyar fita daga ɗakin sukayi,ɗan juyowa aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace"sannu hakima yayi maki dai dai wato hankalinki kwance zaki rabu da Mommynki ko rakiya babu"?
Miƙewa hafsat tayi tare da bin bayansu,suka fuce daga cikin ɗakin,ta ƙopar baya suka bi don kada wani yaga fitarsu,a waje suka samu Major tsaye jikin motarshi,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,yana ganin sun fito da sauri ya buɗe masu motar,
"Allah ya kiyaye hanya mommy,in sha Allah gobe da safe kafin ku wuce maidugurin zan kiraki a waya,"
Harara aunty babba ta watsa mata kafin tace"Munafuka!Hada wani raku6e fuska kamar irin zakiyi kewata ɗinnan!Ae kada ki damu ki sha kuruminki in dai ni ce zan dawo ne!nan bada jimawa ba,"tayi maganar tare