Showing 237001 words to 240000 words out of 307403 words
Chapter 80 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
Amrish ce ta ambaci hakan tare da ɗaura hannunta asaman kanta,Tana kuka,
Hankalin kowa Ya koma kanta,Muryarta na kerma ta nuna Azmee da hannunta tana faɗin"Dama ke kikasa aka kaishi gidanmu dan baƙin zalunci?Wacece ke?Ni bansan meya haɗani da ku ba,Wlh duk na tsani kaina,In har abunda nake zargi ya tabbata,wlh saina kashe kaina,"sosai ta fashe da kuka
Tunda Azmee taji hakan nan ta gane cewa wani abu ya faru acan gidan,tabbas Junaid Ya ku6uta daga wurinsu,.
Gyaran murya Ya Mu'allim yayi,hankalinsu ya dawo kanshi,Anan Yake labarta masu duk abunda ya faru kamar yarda Amrish ta sanar dashi,Har zuwa kaishi asibiti da su kayi,
Yana kai ƙarshen maganar,Azeemi tace"Naji daɗi da Junaid ya dawo hannunku,Amrish ke bakowa bace face ɗiyar saratu matar ƙanina Ya Sayyadi,Da saratu dani ƴa'ƴan wa da kanine,Don haka ke jininmu ce gaba da baya,babu yarda zakiyi haka Allah Ya ƙaddaro maki,Ki gode ma Allah da baki ɗaukko irin mugayen ɗabi'un mahaifinki da mahaifiyarki ba wanda hakan ne ma yasa ba'a bayyana maki mahaifin naki ba,"
Waro ido waje Amrish tayi,idanuwanta sunyi jawur dasu,a fujajan ta watsa da gudu ta nufi Glass cups ɗin da suka faffashe a wurin,ta ɗauko ta daddage zata Caka shi a ƙahon zuciyarta da sauri Kanal Yusuf yayi hanzarin damƙar hannunta,ƙoƙarin kwacewa tadinga yi don ta Caka ma kanta,Amma ya hana hakan,Fisge glass ɗin yayi tare da jefar dashi ƙasa,Ya ruko kafaɗunta ya jinjigata"baki da hankali ne?Saboda me zaki kashe kanki?saboda Iyayenki sun kasance Gur6atattu!Laifinki ne?ko kin manta da ayar da Allah subhanahu wata Allah ke cewa"Yana fitar da mai rai daga matacce kuma yana fitar da matacce daga mai rai,kuma yana rayar da ƙasa a bayan mutuwarta,Kuma haka ake fitar daku,acikin suratul rum Ayata 20,Bayan ita akwai surar da tayi magana makamancin wannan acikin suratul Ahli'emran Aya ta 28,don haka ki kwantar da hankalinki,Ki rungumi ƙaddararki,Bakanki farau ba,Sau nawa cikakken malami ke haihuwar 6arawo ko kasurgumin dan fashi?Ba yadda Allah bai ikonshi,kuma bawai don baya sonku ba face don Ya jaraba imaninku,Sannan Laifin da iyayenki suka aikata bazai ta6a shafarki ba,ki gode ma Allah da baki ɗauko irin ɗabi'unsu ba,Ke tsarkakkiyace,Allah ya tsarkake ki daga faɗawa halaka.......'jikinta ba ƙaramin Sanyi yayi ba,Kalaman kanal Yusuf ba ƙaramin sanyaya mata zuciyarta su kayi ba,Har taji ta haƙura da kashe kanta da tace zata yi,Jiki asanyaye ta juya ta koma wurin Sehrish,rungumeta Sehrish tayi ajikinta,gaba ɗaya suka fashe da kuka maicin rai,dole Amrish taji ba daɗi,very heart touching ace iyayenka su dukansu gur6atattune kuma 6atattu,dayawa mutane zasu dinga yi maka wani mummunan kallo,Ya Allah kasa mu dace,
"Nasan bazaku ta6a yafe mun ba,Ku yanke mun duk hukuncin da ya dace dani,wlh zan kar6eshi hannu bibbiyu,Amma dan Allah ina neman wata alfarma ɗaya agare ku,"Azmee ce tayi maganar,yayin da kwalla ke cigaba da zubowa akan fuskarta,
Kasa kunne su kayi suna sauraronta,
"Dan Allah,Kada ku ta6a Haroon,Duk hukuncin da zaku yi mashi,Ni kuyi mun saboda ba laifin shi bane,tursasa mashi akayi,Bayan tafiyarku asibiti,Na same shi acikin mawuyacin hali ɗakin da kuka kwantar dashi,Na kwanceshi sannan na fitar dashi daga cikin gidan nan,Saboda gudun kada ku kashe shi nasan bazaku ƙyaleshi ba"
"Azmee kin bani mamaki,Kin karya mana zuciyoyinmu,Bakisan irin raɗaɗin da kika sanya mana acikin Zuciyoyinmu ba,Why Azmee?Duk don saboda daukar fansa Yasa kika shiga jikinmu!Ina iliminki ya tafi ne?Ke fa musulmace,bakiyi imani da ƙaddara bane?Meyasa Laifin wani zai shafe mu ?ballantana ma Ba wani abu akayi maku ba,Komai ya faru da family dinku laifinku ne,Saboda kun kashe ne shiyasa aka kashe naku,Da baku ta6a kowa ba,babu wanda zai ta6a naku,Kuskure ɗayane na kashe mijinki da akayi wanda shima don ya taka sahun 6arawo ne,Tsautsayine ya rutsa dashi....."daƙyar yake magana,sauke ajiyar zuciya yayi kafin yaci gaba da cewa"Almost 20 years Azmee kina tare damu ashe ba don Allah bane,Wlh tausayinki nake ji,Kin 6ata wayonki,kuma kinyi asarar Rayuwarki,Yanzu komai da kikayi ya tashi abanza,hatta ibadar da kikeyi itama ta tashi abanza,Idan yanzu kika faɗi kika mutu me zaki ce ma Allah?ya ƙarasa maganar yana kallonta,Sosai Azmee ta fashe da kuka kamar ranta zai fita
"Da ace kinyi hakuri,kin rungumi ƙaddara,Yaya kike tunanin Rayuwarki zata kasance?yadda kowa ke sonki,Kina da farin jini sosai,Ko abokanaina in suka zo gidan nan har santin girkinki suke yi,Kowa yabonki yake yi,Why Azmee?Kin ɗauki alhakin mutane dayawa,Kin cuce mu kin yaudare mu,kin kuma zalunce mu,Amma inaso ki sani,Wlh duk kanki kikayi mawa!"abun ya ƙona mashi rai sosai,
"Ni wlh da tun farko kin sanar dani cewa kina sona,a yadda na yaba da kyawun halayanki a wannan lokacin,Da ba abunda zai hana in aure ki!"
Ɗagowa tayi da idanuwanta waɗanda su kayi jawur dasu,tana kallon Abba dake magana,
Rai a6ace Mommy tace"Ni bansan me kuke jira da ita ba,Banason ganin matar nan,Rayuwarta bata da amfani,ta mutu kowa ya huta,"
Gaba daya sun fusata,ganin suna ƙokarin zame belt ɗin wandonsu don su jibgeta,Abba yayi saurin dakatar dasu"Innallaha ma'assabirin!Kubarta da Allah Shiyasan yarda zaiyi da ita,ban amince ɗaya daga cikinku Ya ta6a lafiyar jikinta ba,Azmee bata kashe mun kowa ba,Iya cuta dai ta cutar damu,Ina neman alfarma a wurinku,daku miƙata wurin hukuma su yanke mata hukuncin daya dace da ita,Sannan kuma Ina umartarku da ku hanzarta Ruguza ƙungiyarsu,Da duk wani wanda ke cikinta,Kamar yarda kakanku salahudeen yayi,haka nakeso kuma Kuyi,Kada ku raga masu,banaso daya daga cikinsu Yasha,gawawwakinsu kawai nakeson Gani,"Yana kai ƙarshen maganar,Ya juya tare da barin wurin Ya koma bedroom ɗinshi,Idanuwanshi cike tab da kwalla,a ƙopar ɗakin ya tsaya yayin da idonshi ke akan Junaid dake kwance saman gadonshi Yana ta sharar bacci abunshi,Har cikin ranshi baiso Azmee Ta kasance haka ba,Koma miye ita taja ma kanta,Ya Allah kakare mu daga aikata Aikin dana Sani,
Bayan tafiyar Abba,Ya Mu'allim Yace"Shawarar da zan baku shine,Kuyi amfani da Azmee wurin kama sauran masu aikata laifin,saboda tasan komai,Tasan inda ƙungiyarsu take Inyaso daga bisani Sai a miƙata ga hukuma,zamu tayaku da Addu'a akan Allah ya baku nasara,"
Sosai sukayi ma Ya mu'allim Godiya,domin kuwa ya basu shawara mai kyau kuma Ya taimakesu,batare da 6ata Lokaci ba,suka tasa ƙeyar Azmee zuwa Ɗakin horonsu,Tambayoyi suka shiga jero mata,tana amsa masu,In tayi kuskuren yi masu taurin kai kuwa,zazzafan Mari take sha,Anan suka samu bayanin inda Ya sayyadi Yake,Ashe baya ƙasar tun Lokacin da abu ta kashe mashi idanuwanshi,Suka fiddashi ƙasar waje,Don a duba lafiyarshi,Da wayar Azmee sukayi amfani wurin gano Duk wani mugun abu da suke aikatawa,A ranar suka shirya tsaf cikin kakin Sojojinsu gaba dayansu domin fara yaƙar ƙungiyarsu,Manya manyan makamai suka ɗauka,Sai da Abba ya fara sanya masu Albarka,Yayi masu addu'a,Mommy ma tayi masu tare da sauran Mutanan gidan Kafin Su kayi masu sallama,A tare da Azmee suka tafi Asaman Helicopter kusan guda shida Ya ɗaga dasu,
Kasa samun natsuwa su Sehrish su kayi,kowa zullumin yake yi game da tafiyarsu Babban Yaya,wurine mai matukar haɗarin gaske acikin wani ƙurmamin daji,inda suka kafa ƙungiyarsu ta matsafa,kodai su kashe ko akashe su,Allah kaɗai yasan wanda zaiyi nasara,
Abu kamar wasa har goma sha ɗayan dare basu dawo ba,babu wani labari dangane dasu,Wayoyinsu kuma duk in aka kira bata shiga,Hakan Ya ƙara tayar masu da hankalinsu,shi kanshi Abba sai daga baya ya fara danasanin turasu,Mommy kuwa tuni ta fara zubda kwalla,tsoranta kada ta rasa Ƴa'ƴanta,
A 6angaren su Sehrish kuwa,Babu wanda ya runtsa acikinsu,kwana su kayi saman darduma sunayin sallah akan Allah ya basu nasara ya kuma dawo dasu Lafiya,abu kamar wasa Tsawon kwana biyu kenan su Sgr basu dawo ba,lamarin ya fara tsoratar dasu,Gashi ba'a samun Layinsu balle asan awani hali suke Ciki,
Sai adaren Rana ta biyu ne,Allah yayi suka dawo,Sunyi nasara sai dai sunyi babban rashi na mutun ɗaya acikinsu,Irfan Allah yayi mashi rasuwa,sunji mutuwar nan kamar kamar me,tare da gawarshi suka dawo,wasu daga cikinsu kuma sun raunata sosai,Dan Fawan Allah ne yayi zai rayu,Twins kuwa sun jigata sosai,kowa Yaji ajikinshi,Nasarorin da suka samu sune sun ruguza Ƙungiyar matsafan,sun lalata masu komai,Sun kuma kashe mutanan cikinta gaba ɗayansu,don sunyi masu zuwan bazata,kuma sunci sa'a adai dai lokacin suna kan yin meeting ne,kowa Ya hallara,Hada shugaban nasu Ghali,Da taimakon Azmee suka kashe shi,Yanzu mutun ɗaya ya rage masu su kamashi Wato Ya Sayyadi,
A washe garin ranar akayi jana'izar Irfan,Abba Yafi kowa jin mutuwar nan,Abubuwa sunyi mashi yawa,Ga Junaid dake kwance yana jinya,Ga kuma fawan shima Yana ƙarkashin kulawar likitoci,
Bayan kammala Jana'izar Ifran,Batare da 6ata Lokaci ba,Sgr Ya tura Armstrong tare da wasu daga cikin sojojinshi,Suka hau jirgi zuwa ƙasar Malaysia,Don bala'e har asibitin da aka kwantar da Ya sayyadi suka Cafko shi,idanuwanshi Na manne da uban bandegi,da Alama aiki akayi mashi a wurin,Cikin jirgi suka sanyoshi,Sannan Suka dawo dashi Nigeria,har cikin gidan suka taso ƙeyarshi gaba,a garden ɗin gidan Sgr ya sanyasu suka Kwantar mashi dashi,kafin ya yanke mashi hukunci,Sai da Ya fara kiran Abusufyan tare dasu Jahad,da oummansu gaba ɗayansu suka hallara a garden ɗin,
Abusufyan yace"dama saida na faɗa maka,Wannan ranar zata zo,kuma gata Allah ya nuna mun da raina da lafiyata,Gani ga kuma Yaran daka zalunta,Ga kuma mahaifiyarsu,Kaji haushin rayuwarka Sayyad,A yau ƙarshenka yazo,tun a gidan duniya zaka fara ɗanɗani raɗaɗin azaba,kafin ka koma Ga Allah," gaba ɗaya yabi ya ruɗe,jikinshi sai kerma Yake yi,daga yayi ƙoƙarin buɗe baki zai basu haƙuri,Sai Sgr ya Kai mashi naushi a kuncinshi,duk saida Ya zubar mashi da haƙoran bakinshi,Jini jaga jaga A bakinshi,
"Mugu azzalumi,Ni Ko kaɗan banji tausayinka ba,Allah yaji ƙanka don nasan cewa taka ta ƙare,Allah ya ƙara nauyin ƙasa,"Abuce tayi maganar,
Jahad da sehrish basu ce komai ba,Hosana dai ce Ta tofa mashi Miyau Asaman fuskarshi,bayan sun gama gaya mashi magana,Sgr Yaba sehrish umarnin ta kawo mashi tafasasshen Mai,
Jiki na rawa ta juya ta koma cikin gidan,Oummansu dasu Jahad suka bi bayanta,Bada jimawa ba ta dawo hannunta ɗauke da ƙaramar tukunya,Tafasasshen mai ne aciki sai tartsatsi yake yi,
Umarni yaba Su armstrong,Su cire wandon jikinshi,Ganin haka yasa Sehrish ta ajiye man,ta watsa da gudu ta koma cikin gida gabanta na faɗuwa,
Bayan sun cire wandonshi,suka yi mashi zirr,sojoji guda biyu suka tale ƙafafunshi,Abun nan da yake takama dashi yana yi ma mutane iskanci dashi,Sgr ya ɗauki tafasasshen man nan ya kwarara mashi agabanshi gaba ɗaya,
Wa'iyazubillahi!Wata irin kururuwa Ya sayyadi yayi,lokacin da gabanshi ke ƙonewa,wani irin raɗaɗin azaba Ya dinga ji,Gaba ɗaya ya zauce ya gigice Ya fita hayyacinshi,
Umarni Ya basu Su ɗauke shi su kaishi can cikin ƙurmin daji,ko namun dawa sun samu abinci,A ƙarshe dae Ya sayyadi A cikin daji rayuwarshi ta ƙare,gawarshi A wulaƙance A ƙasƙance abun ba kyan gani,
Ita kuma Azmee Tare da Saratu,Jami'an ƴan sanda ne suka tafi dasu,Bayan an tattara hujjoji,Suka miƙasu Court domin Yin shari'a,A ƙarshe Aka yanke masu hukuncin zama gidan Yari,A ɗakin duhu na tsawon shekara 20,Sehrish tasha kuka,Saboda har lokacin tana son Azmee,Lokacin da aka kammala shari'ar za'a tafi dasu gidan Yari,Daƙyar aka rabasu,Sun rungume juna sosai suna kuka,ita da Sehrish,ita kam Amrish kin zuwa tayi wurin Mommynta balle ma ta rungumetan dama dakyar ta biyo su kotun,kowa baiji daɗin halin da Azmee ta jefa kanta ba,ba lalle ne lokacin da zasu fito ɗakin duhu ba,su dawo da idanuwansu ba,zaiyi wuya in basu makance ba,idan ma sun rayu kenan,'
Lokacin da Labarin mutuwar Irfan ta riski danginsu,Lokaci bai cika kwana biyu da rasuwa ba,Gidan Ya cika fam da masu zuwa yi masu jajen abunda Ya faru,Da kuma Yi masu gaisuwar rashin da suka yi,Mutane dayawa Sunyi mamakin jin cewa Azmee ce take ɗaukar fansa akan mutanan gidan,Sunyi Allah wadai da halinta,Tasha Zagi wurin jama'a don wasu da suna da halin da zasu ganta sai sun kasheta da bugu,Yanzu Alhamdulillah basu da wata sauran fargaba,NO MORE TENSION,
Kowa yayi dakyau don kanshi,
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 6 na marece,A jere motoci suka dinga shararowa izuwa cikin gidan,dankara dankaran gaske,Bayan sunyi parking ɗin motocin,Mota ta farko,Wani sergent Ya fito tare da zagaya Ya buɗe gidan baya,A hankali ta sauko daga cikin motar,jikinta sanye da code lace fari,Bakowa bace face Hajiya Azeema,fuskarta ɗauke da murmushi,other side ɗin hafsat ce ta fito jikinta sanye da atampa,Ta ruƙo hand bag dinta,
Motar bayansu,Ammi ce tare da Gwaggon katsina,Dr harriss ne yayi driving dinsu,Saude na a gefenshi,
Daga Motarsu kuma sai Motar MG Osman,Tare da Captain adam,basu kaɗai bane a motar,Akwai Ƴan matan da suka zo dasu kyawawan gaske daga Gani ƴan uwansu ne,
Motar dake bayansu Motar Captain Najeeb ce,su biyu ne aciki shi da Talal autansu na biyu,
Babu wanda yasan a ranar zasu dawo,
A lokacin gaba ɗayansu sun hallara asaman dining suna Cin dinner ɗinsu,banda mutun biyu Omar da Sgr basu kaiga dawowa daga wurin aiki ba,They're busy for work ga prepation ɗin da suke yi Na Komawa U.S tafiya ta kankama,kowa ka kalli fuskarshi daurewa kawai suke yi akwai sauran jimami,Yanzu babu Azmee sai dai Abu dasu Jahad ke girka abincin gidan,
Sehrish ta zabga uban tagumi,Bakowa take tunani ba,face Aunty azmee,Duk in oummansu Nayi serving ɗinsu abinci,Sai ta dinga tunawa da ita,
Binsu da kallo ta soma yi ɗaya bayan ɗaya,tun daga kan mommy dake ta faman jujjuya cokali acikin abincin gabanta,Abba kuwa tunda ya zauna Bai ta6a komai ba,Lemu kawai yake tasha,
Su twins Da ɗan dama,Sun saki jikinsu suna cin abinci,Haka kanal yusif ma sosai yake Cin abincinshi,Irfan da jabeer still sai a hankali,Duk sun kasa sakewa saboda rashin Irfan da su kayi acikinsu,
Kallon Hosana tayi,Cinyar kaza ta ɗauko ta tura abakinta sai tauna take yi kamar akuya ta samu ciyawa,Murmushi sehrish ta ɗanyi tare da ɗan girgiza kanta,Mayar da idanuwanta tayi kan Amrish dake zaune daƙyar take tura abinci abakinta har yau ta kasa sakewa acikinsu,ɗagowa tayi suka haɗa ido Da sehrish atare suka sakarwa Juna murmushi,
Miƙewa Jahad tayi,"Where are u going"?Abusufyan ne ya tambayeta ganin ta miƙe tsaye bata kammala cin abincin ba,
Sunnar dakai ta ɗanyi kafin tace"Zanje na duba jikin junaid ne"
Murmushi ya saki,kafin yace"Je ki abunki,Allah yabar ƙauna,"
Kunyace ta rufe ta,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta,da sauri tabar wurin ta nufi bedroom ɗin abba,
Bayan tafiyar Jahad mommy ta mike"Zanje na duba jikin fawan,Inaso naji idan akwai abunda yake buƙata sai in kai mashi,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kama hanyar bedroom ɗinshi,
Lokacin da jahad ta ƙarasa bedroom ɗin a ƙopar ɗakin ta tsaya,tare da sanya hannu ta ruke handle ɗin ƙopar,Slowly ta tura ƙopar ɗakin ta ɗan leƙa,har yanzu bawan Allah a kwance yake baisan inda kanshi yake ba,Da alama Ya samu bacci,kullum sai Ya mu'allim yazo duba shi,yanzu ya zama tamkar ɗan uwa agaresu,
A hankali take tafiya harta ƙarasa gefen gadon ta zauna,Zuba mashi ido tayi tana kallonshi,Yanzu bata da burin daya wuce taga junaid Ya dawo cikin hayyacinshi,Fargabarta kada Ya manta da soyayyarsu,
A hankali ta kwantar da kanta gefenshi,Allah ya baka Lafiya My Romeo,ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta,Unexpect Taji Saukar hannunshi acikin Sumar kanta,A firgice ta ɗago da kanta tana kallon fuskarshi,slowly ya buɗe dara daran idanuwanshi farare ƙyal akan fuskarta,La66anta na kerma Ta ambaci Sunanshi JUNAID! da mamaki akan fuskarta,Binta da ido yayi yana kallonta,Matsawa tayi saitin fuskarshi,
Cike da tsantsar farin ciki ta kuma ambaton sunanshi"Junaid"
Lumshe mata idanuwanshi yayi tare da sake budesu akan fuskarta,Saboda tsabar farin Ciki,Da sauri ta sauko daga saman gadon ta watsa da gudu ta fito daga ɗakin,Jin takun takalmata yajanyo hankalinsu akanta,
Tunkafin ta isa ta soma magana"Abba Junaid ya farka,Ya dawo cikin hayyacinshi,"Gaba ɗaya suka miƙe Fuskar kowannansu ɗauke da tsantsar farin Ciki suke kallonta,Adai dai Lokacin Gwaggon Katsina Ta dako masu Sallama da ƙarfin gaske tana fadin"Gafara dai,Mai wuri yazo Me tabarma ya naɗe,Masu Gidan sun dawo,"
*Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Koda su kayi arba dasu Ammi wani irin farin ciki ne Ya lullu6esu,Watsawa Hosana tayi da gudun gaske tana faɗin"Ga gwaggo!Ga gwaggo!"Washe baki gwaggon katsina ta soma yi"Yawwa ya'yan abusufyan ɗina,Nayi kewarku sosai,"Rungumeta hosana tayi,Tana ta faman tikar dariya,Sehrish kuwa Tana yin arba da hajiya azeema,Da gudu ta nufeta,Murmushi Hajiya azeema ta saki tare da janyota jikinta,Ta rungumeta sosai tana shafa bayanta"I really missed u My daughter,Nasan kinyi kewata sosai,"
ƙarasowa wurinsu Jahad tayi kaitsaye ta nufi Hafsat,wani irin farin cikine ya lullu6e hafsat ganin ta tunkarota fuskarta ɗauke da fara'a tayi tunanin har lokacin fushi suke yi da ita,Rungume juna sukayi sosai,
"Wato kowa nashi ya sani ko?kun manta da kakarku,"Abba ne yayi maganar fuskarshi ɗauke da murmushi,Ya ƙarasa wurin Ammi,ta rumgume shi ajikinta,Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke,lokaci guda yaji idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla,
Shafa bayanshi Ammi tayi"Nasan ban kyauta maka ba,nayi nesa dakai a lokacin da kake buƙatar kulawata,Kayi haƙuri hossein Banji daɗin abubuwan da suka faruwa ba,abun ya ta6a zuciyoyinmu"Sosai ammi tashiga tausarshi,
ƙarasowa Su Kanal yusif su kayi,Abusufyan ya rungume Dr harris,Yusif kuwa Wurin Captain adam Ya nufa rungume juna su kayi,Jabeer ya rungume Mg Osman,Kowannansu fuskarshi ɗauke da murmushi,
"Mu shiga daga ciki,Kun kwaso gajiya,"abba ne yayi maganar tare da ruƙo hannun Ammi,Suka nufi cikin Falon,
"sassannunku da zuwa,Ya hanya Ya gajiyar tafiya,Ya kuka baro su"?acewar abusufyan
Hajiya azeema tace"Lafiyalou,duk suna gaisheku,"
Bayan ta ƙare maganar,Mg osman ya soma magana"ashe irfan Lokaci yayi,Allah yaji ƙanshi,Ya gafarta mashi zunubbanshi,Wlh naji mutuwarshi"yakai ƙarshen maganar tare da curo hanky daga aljihunshi Ya rufe fuskarshi,jikin kowa dake a wurin yayi sanyi,
Talal tuni ya fara zubda kwalla"Abba ashe haka abu ya faru?munyi babban rashin na irfan acikinmu,Allah yasa ƙarshen wahalarshi kenan,Allah Yaji ƙanshi,"
"Ameen ameen,"daƙyar abba yake amsa masu saboda yanayin da suka jefa shi,Dama dauriya ce kawai yake yi,
"Yaya hossein,Ya haƙurin rashin da mu kayi"?hajiya azeema ce tayi maganar yayin da take kallonshi,daƙyar ya iya amsa mata,Kowa dake a wurin sai da yayi masu gaisuwa,Hatta Ƴan matan da Ammi tazo dasu,
Shigowa palourn Abu tayi hannunta ruƙe da faffaɗan tray,Cups ne asama mai ɗauke da Lemu mai sanyi,sai da ta fara yi masu sannu da zuwa,kafin ta soma ƙoƙarin raba masu abunshan,.
Gyaran Murya abusufyan yayi mata,Da sauri takai idanuwanta kanshi,da ido yayi mata nuni da Ammi alamar ta fara miƙa mata,Murmushi tasaki kafin ta nufi sofa ɗin da ammi ke zaune tare da Abba,cikin girmamawa ta gaishe da ita"Sannunku da zuwa Ammi,Ya gajiyar tafiya,"
"Alhamdullillah,"tayi maganar tare da miƙa hannu