Showing 240001 words to 243000 words out of 307403 words
Chapter 81 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
ta kar6i cup din da abu ke miƙa mata,
"Ince ko Mahaifiyar ƴan ukun nan ce"?tayi tambayar tana nuna su jahad dake zaune wurin gwaggon katsina,
Abba ne ya bata amsa da cewa"Itace oummansu"
Murmushi ammi tayi tare da kallon abusufyan,A hanzarce ya kawar da kanshi gefe yana murmushi ƙasa ƙasa,
"Alhamdulillah Naji daɗi sosai,mun samu ƙaruwa acikin zuri'armu Allah ya ƙara hada kawunanmu,"atare suka amsa mata da ameen
Kasa haƙuri Talal Yayi"Abba Ya jikin junaid da fawan?na kasa samun natsuwa,Burina in sanyasu acikin idanuwana na,"
Tunkan yakai ƙarshen maganar Gwaggwon katsina tace"Allah sarki junaidu bawan Allah,An ji jaki,Amma Allah wadaran me hali irin na Azmee,Matar nan ta cuce mu,Munafuka mai zuciya irinta Kafiran farko,Yadda kasan A jahiliya period aka haife ta dama ni banyarda da ita ba,Shisshiginta yayi yawa,Sumumu kasau macijin sari ka noƙe.....Wannan matar tafi bomb bala'e,Wlh bazamu yafe mata ba,Allah ya ɗebe mata sauran albarkar dake......"bata ƙarasa maganarba,Abbba yayi hanzarin cewa"Gwaggo,Dan Allah adaina tuna abunda ya wuce,Azmee yanzu bata atare damu,Tana can prison tana kar6ar sakamakon abunda ta aikata,
Tunkan yakai ƙarshen maganar tace"Haba hossein,Ai ni banso kuka kaita prison ba,So nayi ku kulleta acikin akurki irin na kaji har mu dawo,Wlh data yaba ma aya zaƙinta,Azmee bata kyauta mana ba,Kaga fa matar nan kamar tafi kowa tsoron Allah,Kullum Zaka ganta cikin zumbulelen hijabi kamar matar liman,Hannunta ruƙe da zungureran cazbi kamar duka kenan"cika da takaici tayi maganar,.
"Wlh ni dama banyarda da ita ba,shiyasa tun farko banso Yaya hossein Ya bata rainon junaid ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,babu yarda zamuyi,Allah Ya kyauta gaba,Yanzu sai musan dawa zamu yarda,"Azeema ce tayi maganar ranta a 6ace,
"Ae azmee ta bamu mamaki,Ta koya mana hankali wlh,ɗan adam ba abun yarda bane,Mutun mugun icce ne,duk irin halarcin da akayi mata tarasa dame zata saka magana sai da wannan,"acewar abba,
Gyaran Murya ammi tayi kafin ta soma magana a tsanake,
"Kuskure ne tun farko an riga da an tabka,sai dai fatan Allah ya tsare gaba,bai kamata kuna tada maganartaba,tunda yanzu babu ita,amma duk da haka ina me ƙara jan hankalinku Akan ku daina saurin yarda da mutane,musamman bare a zamanin da muke ciki Na jikinka ma ana iya haɗa baki dashi a cutar dakai balle kuma wanda baku haɗa komai dashi ba,Iya cuta dai Azmee ta cutar damu,Amma mu gode ma Allah da bata kaiga yi mana illa ba,Don da taso da tuni ta jima da halaka wasu acikin gidan nan,Allah ne ya tsare mana ku,"bayan takai ƙarshen maganar,ta ɗan sauke ajiyar zuciya kafin taci gaba da cewa"Yanzu a wani Hali jikokina suke ciki?Fawan da junaid,Ya jikin nasu,"
"Alhamdulillah suna samun sauƙi sosai,Junaid yana kwance a bedroom ɗinta fawan kuma yana a dakinshi"miƙewa tayi tare da nufar ɗakin Talal ma Yabi bayanta,Gaba ɗayansu ma suka miƙe domin zuwa duba jikin nashi,Lokacin da suka shiga ɗakin,A zaune suka same shi,Ya sauko ƙafafunshi ƙasa,Da alama so yake yayi tafiya,jin an buɗe ƙopar ɗakin Yasa ya ɗago da manyan idanuwanshi yana kallonsu,
Farin ciki ne Ya lullu6esu,Musamman Abba,jiki na rawa ya ƙarasa gefenshi ya zauna,rungumoshi yayi xuwa jikinshi,Yana shafa bayanshi,
"Alhamdulillah,Da alama Jikin nashi yayi sauƙi,ba kamar yarda aka bani labari ba,"acewar ammi fuskarta ɗauke da murmushi,
Zuƙunnawa Talal Yayi saitin fuskarshi"Junaid ɗan uwana,Ya jikin naka"?zuba mashi ido junaid yayi yana kallonshi batare da yace uffan ba,Yaƙi buɗe baki yayi magana,Sae dai kallonsu da yake yi ɗaya bayan ɗaya kamar baison su ba,
"Allah yasa baiyi loosing memory ɗinshi ba,Naga ko magana ma ya gaza yi mana Sai dai yabi mu da ido,"acewar captain adam,
Osman yace"nima abunda nake tunani kenan,Junaid dana sani kullum fuskarshi ɗauke da murmushi kamar Gonar auduga"
"Kada ku damu,Yanzu ya fara jin sauƙi,Nasan zuwa gobe zai warware in sha Allah,shikaɗai yasan me yake ji acikin zuciyarshi,"yayi maganar yayin da yake cigaba da shafa sumar kanshi,
Kowa sai da yayi mashi yajiki,Kafin suka Yi mashi sallama suka koma Falon,basu jimawa da dawowa ba,Mommy ta fito hannunta ruƙe dana Fawan,Daga shi sai short ajikinshi,ba ƙaramin jiki yaji ba,Amma yanzu da sauƙi jikin nashi,
Tunkan su ƙaraso,Talal da najeeb suka miƙe,Da sauri suka ƙarasa Wurinshi,Suna yi mashi yaji,murmushi ya sakar masu"Alhamdulillah Am really glad to see you,nayi missing ɗinku sosai,"
Rungumeshi su kayi,Kafin suka ruƙo hannunshi zuwa cikin falon,Saman Sofa suka zauna,Kowa ya soma Yi mashi Ya jiki,fuskarshi asake yake amsa masu,a tsaye mommy ta gaisa dasu,Kafin ta nufi kitchen donta shirya masu abunda zasu ci,Abu ta samu acikin kitchen ɗin tana shirya masu abinci,Taimaka mata tayi suka shirya abincin atare,
Abba kuwa still Yana a wurin babynsa ya ƙankameshi ajikinshi,ɗago da junaid yayi daga jikinshi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi
"Junaid Anya lafiya kuwa?Sai dai kabi kowa da ido kamar baka sanmu ba,dan Allah kayi mun magana,Kona ji sanyi acikin zuciyata,
Zuru yayi mashi sam yaƙi ya tanka mashi,Duk ya shiga damuwa,Jan kumatunshi yayi"Haba babyn abbansa,Ko murmushi ne to kayi mun,"
Still bai tanka mashi ba,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,
"Dan Allah junaid,ka kwantarmun da hankalina mana,duk na damu da rashinka,Nasan Nayi maka laifi amma dan Allah Kayi hakuri kaji My baby Boy,"hada ɗan murmushinshi yayi maganar,junaid kuwa sai binshi da ido yake yi,
"Me kake son ci in kawo maka"?yayi tambayar yana shafa sumar kanshi,
Sai lokacin Junaid ya buɗe bakinshi,Yana nuna mashi teeth ɗinsa,Sunyi dauɗa sosai,
Murmushi Abba yayi"Saboda teeth ɗinka sunyi datti shine kaƙi yi mun magana,to menene aciki"sunnar da kansa ƙasa yayi,
Ruko hannunshi Abba yayi tare da miƙar dashi tsaye,Toilet ya shiga dashi,A gaban sink suka tsaya,Brush ya ɗauko bayan ya matsa maclean asama,Yace"Ha bakinka inyi maka brush ɗin dakaina,"buɗe bakinshi yayi,Abba ya tura brush ɗin cikin mouth ɗinsa,a tsanake yake goge mashi hakoran,Yayin da idanuwansu ke kallon cikin na juna,
Calmly Abba ya soma magana"Nasan sunyi hurting ɗinka sosai,But pls we should forget about the past,Komai ya wuce,babu wanda Allah baya jarabtarshi junaid,Ka gode ma Allah da basu yi maka illa sosai ba,Nasan ka shiga damuwa ne sosai saboda rashina dakuma ƴan uwanka,ka rayu atare da wasu mugaye marasa imani,Ka tsorata sosai,Shiyasa harka zauce,Amma Yanzu Alhamdullillah,Jiki yayi kyau,"ya ƙarasa maganar tare da kunna tap,zuƙunnowa junaid yayi,Abba ya tarfa hannunshi Ya ɗebo ruwan yana kuskure mashi bakinshi,Bayan ya kammala kuskure mashi bakin,Ya wanke mashi fuskarshi,Kamar wani ƙaramin yaro haka Yake treating dinsa,
Hannunsu ruƙe dana juna suka fito daga cikin toilet ɗin,Zaunar dashi yayi gefen gadon,
"Yanzu fadamun me kakeson Ci,"
Daƙyar ya iya cewa"Abbana,"
Murmushi abba ya saki tare dacewa"Na'am babyn abbansa,"murmushi gefen fuska junaid ya ɗan saki,
"Repeat it pls,"
Sake ambaton sunanshi yayi kamar yarda ya buƙata"Abbana,"
Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarshi"Na'am sanyin idaniyata,tell me me zaka ci,in kawo maka,"
Yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana Jahad ta turo ƙopar dakin,Sam batayi tsammanin Abba na aciki ba,da sauri ta juya zata koma,Abba yayi saurin dakatar da ita"Ina zuwa"?kunyace ta rufeta,Har takasa juyowa tayi magana,
Murmushi abba ya saki tare da cewa"Yana jin yunwa ki kawo mashi abunda zaisa ma cikinsa,"
"Toh abba,"ta amsa tare da buɗe ƙopar ta fuce,
Mayar da idanuwanshi yayi kan fuskar junaid"Faɗamun har yanzu kana sonta insa a ɗaura maku aure,"
Sunnar da kanshi ƙasa yayi batare daya tanka mashi ba,ya lura da canzawar da junaid yayi dama Ya mu'allim yace Ba lallai ne ya dawo yarda suka sonshi ba,tunda yanzu babu sihiri ajikinshi,Ya dawo Normal yadda Allah ya halicce shi,Wato Namijin gaske,
Cike da zolaya abba yace"Oh ni junaid,Allah yasa ba irin rafayet bane,naga magana ma wuya take yi maka,Fuskarka kuma a ɗaure babu annuri,"
Turo ƙopar jahad tayi hannunta ɗauke da tray ɗan madaidaci,Food stuffs ne ta dauko asaman shi,
Mikewa Abba yayi"Yawwa My daughter,zoki zauna kusa dashi,ki taimaka mashi yaci abincin,Ni bari na koma wurinsu Ammi,"Ta amsa mashi da toh,Juyawa abba yayi yabar masu ɗakin,
Tunda ta shigo junaid bai ɗago ya kalleta ba,tuni tasha jinin jikinta,Yadda kasan ba wannan junaid ɗin ba,mai yawan fara'a ga surutu kamar aku,
Ajiye tray ɗin tayi saman table,ta janyoshi izuwa gabanshi,
"Me zan zuba maka,"daƙyar ya iya buɗe bakinshi ya furta"Cornflakes nakeso,"
"Bari naje na haɗa maka,yanzu zan dawo,"cike da kulawa tayi maganar,A hanzarce ta fuce daga ɗakin,
After some minutes,Ta dawo hannunta ɗauke da Cup ta sanya mashi spoon aciki,Gefenshi ta zauna tare da miƙa mashi cup ɗin,ganin yadda yatsun hannunshi ke kerma yasa tace"In baka abaki,"
ɗaga mata kai yayi alamar Eh,ɗaukar cokalin tayi a tsanake ta soma ɗebo cornflakes ɗin tana tura mashi abaki yana sha,Natsuwa tayi tana kallon lips ɗinsa sunyi red sosai,yadda kasan na jinjiri,ba ƙaramin missing ɗinshi tayi ba,gashi yanzu ya sauya mata,ko son kallonta ma bayayi,balle aje ga magana,.
"Junaid"da wata irin kasalalliyar murya ta ambaci sunanshi,
ɗago da idanuwanshi yayi akanta batare daya amsa mata ba,murmushi ta ɗan sakar mashi tare da cewa"Ashe da rabon zan sake sanyaka acikin idanuwana?nashiga tashin hankali sosai lokacin da motar nan ta danne motarka,duk a tunanina kana acikin motar,har zaucewa saida nayi,Allah ne yayi zan rayu a lokacin,mun shiga tashin hankali sosai,Nidasu Ya omar...."tunda ta fara zuba yake kallon bakinta,Labari ta soma bashi na abunda ya faru bayan mutuwarshi har zuwa bayyanarshi,hada ƴan hawayenta,
"Da ace narasa ka a wannan lokacin bana tunanin zan iya son wani ɗa namiji,zan ƙare rayuwata ne batare dana auri kowa ba,"
Sai da takai ƙarshen maganarta,Tukunna yace"WHO ARE YOU"?
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rass kakeji!Waro ido waje tayi a tsananin firgice take kallonshi,
Hankalinta a matuƙar tashe tace"Junaid!Kana nufin baka sanni ba?i know u are just kidding me"
"Pls who are you"?Ya kuma tambayarya again,
Abun yayi mugun ɗaure mata kai,
"Junaid nifa ce,Jahad ɗinka,Your juliet,"
Girgiza kanshi yayi"Ni bansanki ba,Bansan wacece ke ba,kin zauna sai zuba kike yi mun kamar radio,"
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa Ya nufi cikin toilet ya shige,tare da jan kopar ya datse ta,
Fashewa tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,yana acikin toilet yana jiyo shessheƙar kukanta,A jikin ƙopar ya tsaya can kuma ya buɗe ƙopar yana leƙenta,daga zarar yaga tana ƙoƙarin juyowa sai ya garƙame ƙopar,in ta kawar dakai tana shessheƙar kuka sai ya buɗe yana cigaba da kallonta,miƙewa tayi da ƙyar ta buɗe ɗakin ta fuce,Ajiyar zuciya ya sauke tare da buɗe ƙopar ya fito,Saman gadon ya koma ya zauna,fuskarshi ɗauke da ƙayataccen murmushin side face,
Lokacin da jahad ta fito daga ɗakin Abban,A falo ta samu Ammi tare da matasan gidan dasu Abba da daddynsu,Sae nasiha take yi masu,tare da yi masu addu'a suna Amsa mata da Ameen,
Corridor ɗin ɗakinsu ta shige,a ƙopar ɗakin ta tsaya tare da sanya hannayenta biyu tana goge hawayenta,kafin ta tura ƙopar ɗakin ta shige daga ciki,a kwance ta samu hosana tana ta sharar bacci,Oummansu kuma tana a zaune gefen gadon hannunta ruƙe da qur'ani tana karantawa,jiki asanyaye Jahad ta ƙarasa saman gadon ta haye tare da rufe idanuwanta,Allah kaɗai yasan yarda take ji acikin zuciyarta,
*Boss Bature*
A 6angaren Sehrish kuwa,Yanzu sun koma kwana bedroom ɗin Azmee ita da Amrish,taso suyi magana da mommy azeema amma lokacin da taje ɗakin da ta sauke bacci ta samu tana yi,da alama ta gaji sosai,ba don taso ba,ta dawo ɗaki,Amrish ta samu a tsaye tana ta faman zarya ta kasa runtsawa,da alama tana zullumin wani abu,
"Lafiyarki kuwa?Meyasa baki fita waje ba kun gaisa da ƴan uwanmu da suka dawo,"
Fuskarta ɗauke da matsananciyar damu tace"Tsoron haɗuwa nake yi dasu,gani nake kamar in suka ganni zasu kore ni ne in suka ji ko ni wacece,"
"Kina da matsala Amrish,nafa ce maki ki saki jikinki,Family ɗinmu ba kamar yarda kikayi tsammani bane,suna da mutunci sosai,kowa zai kar6eki hannu bibbiyu ne,"
"Nidai kawai ina fargaba ne,"ta ƙarasa maganar tare da komawa gefen gadon ta zauna,
Cigaba da magana tayi"Har yanzu ina jin raɗaɗin abunda dangina suka aikata,abun yana ƙonamun rai duk in na tuna,Ina jin kunya sosai,Yanzu bani da kowa,nikaɗai na rage acikinsu,Labarin rayuwata sam babu daɗin ji,Yanzu wata rana idan nayi aure na haihu ƴa'ƴana zasu tambayeni game da dangina me zance masu?Idan ma ban faɗa masu fa dole suji a wurin mutane,koda yake nasan ma babu wanda zai aure ni,bakowa ne zaiso ya haɗa zuri'a dani ba,saboda gudun kada ƴa'ƴanshi su taso gur6atattu....."daƙyar takai ƙarshen maganarta,hawaye sharkaf Akan fuskarta,
Zama gefenta sehrish tayi tare da dafa kafadarta"in sha Allah hakan ma bazai ta6a faruwa ba Amrish!Ki manta da duk wani abu daya faru a rayuwarki,ki manta da wasu dangi dakike dasu,Family ɗina sun zama naki,Miji kuma in sha Allah kin samu,muda muke da Zaratan samari,Kika sani ko ɗaya daga cikinsu wani yayi Wuff dake..."duk da tasan ba abu bane maiyuyuwa ba sai da ta ɗanyi murmushi kalaman sehrish sun ɗan sanyaya mata zuciya,
"Fadamun babu wanda ya kwanta maki rai acikinsu,Yanzun nan inje in sanarwa Abba,In aka tashi aurensu Ya omar a haɗa da naki"
Murmushi amrish ta saki batare da tace komai ba
"Kinsan fa muna da gagarumin biki a cikin gidan nan,Abba yace kowa sai ya ɗaura mashi aure,Ran nan najisu suna tattaunawa da daddy,Kuma kinsan wani abun farin ciki,Yawancin matasan gidan nan duk basu kula ƴan mata,abba yace duk wanda bai da budurwa,Zai haɗashi da ɗaya daga cikin ƴa'ƴan abokanansa ne,ina saran kema Abba zai haɗaki da wani ne acikinsu,Ya kike gani idan Yaya yusif ya aure ki"?Tayi tambayar tana kallonta,Yau ta dage sai zuba takeyi mata,duk don saboda farin cikinta,
Murmushi ta ɗan saki Still bata tanka mata ba,
"Ko baki son shi"?
Sai lokacin amrish ta tanka mata"idan ina sonshi,Shi yana sona ne?
"Kuma fa haka ne,Ae ko bashi ba,akwai su Yaya fawan ga twins ga Yaya adam shima fa ya haɗu,"
"Sehrish ni yanzu ba soyayya bace damuwata ba"tayi maganar a yayin da take gyara kwanciyarta saman gadon,
"Are u missing someone"?
ɗaga mata gira tayi alamar eh,kafin tace"Bansan a wani hali ya haroon yake ciki ba,bawan Allah baida kowa mu kaɗai muke rage,Ni nasamu dangin da zan rayuwa cikinsu,Shi kuma fa?wazai kula da rayuwarshi?tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,
Ita kanta Serish ta damu sosai akan Haroon,tun lokacin da suka ji cewa ba yin kanshi bane,
Jinjina kai ta ɗanyi kafin tace"In sha Allah,zan yi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin nayi magana da daddy akan su nemo shi,duk da ina fargabar in tunkareshi da maganar....."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar,
Kafin taci gaba da cewa"inaso na nemi alfarma a wurin Yaya rafayet,amma nasan daƙyar yayi mun"
"Wata alfarma kenan"?Amrish tayi tambayar tana kallonta,
"Hukuncin da aka yankewa Aunty azmee yayi tsauri sosai,a ɗakin duhu aka kaisu,zaiyi wuya suyi watanni idanuwansu basu raunata ba,sun ƙuntata sosai,zuciyarsu ma zata iya bugawa su mutu......"
"Sehrish ashe baki da hankali?duk girman zunubin da suka aikata maku a haka har kike tunanin nema masu sassauci,Wlh karma ki fara,Ni hukuncin da akayi masu yayi mun kaɗan,So nayi da aka kaisu court nan take alƙali ya yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya"rai a6ace take magana,Sehrish kuwa sakin baki tayi galala tana kallonta,Sai kace ba akan mahaifiyarta take magana ba,sai da takai ƙarshen maganarta sannan sehrish tace"Kece baki da hankali Amrish,Iyayenki fa nake nema ma sassauci,Bawai ina nufin su fito daga prison ba,Inaso ne a fito dasu daga wannan ɗakin duhun, sannan arage shekarun da aka sanya masu sunyi yawa,abunda nakeso ki gane shine,Basu kashe mana kowa ba,Zunubin da suka aikata tsakaninsu da Allah ne,Kuma Allah gafurin rahim ne"
Wani irin kallo Amrish ke yi mata, a ƙarshe ma saita juya mata ƙeya,tasanya pillow ta tsoshe kunnuwanta,
Dariya sehrish tayi tare da kai hannu ta dunguri kan Amrish"kar Allah yasa ki ji,"miƙewa tayi daga zaunan da take gefen gadon,ta nufi toilet ta shige,
Shigarta keda wuya,Wayarta dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,Amrish ce ta ɗauki wayar tare da duba mai kiran naga
*My Boss Man*
shine sunan da ta gani akan screen ɗin wayar,bata ɗaga kiran ba,harya katse,after one minute Text message ya shigo cikin wayar,Hannu tasa ta janyo message ɗin ya buɗe,ta soma karantawa,
"Am on my way,"shine abunda ya rubuto mata,murmushi amrish tasaki,duk da batasan saƙon wanene ba,Amma tana da tabbacin cewa Yana da kusanci da sehrish sosai,"mayar da wayar tayi saman drawer ta ajiye,
"Ko meyasa take yawan yin wankan dare,Oho"tayi maganar tana murmushi,within mins bacci yayi awon gaba da ita,
Lokacin da Sehrish ta fito ɗaure da towel a ƙirjinta,wall clock ta fara kallo ƙarfe 12 na dare,Sgr ya sanar da ita cewa daga yau ya gama zuwa aiki,cos aikinshi Ya ƙare a nigeria,zuwa gobe za'a basu lambar yabo,Sannan za'a ƙara ma matasan gidan matsayi wurin aikinsu sakamon Namijin ƙoƙarin da sukayi wurin kawo ƙarshen miyagun da suka addabi ƙasar,
Acikin month ɗin da muke ciki,Za'a ɗaura aurensu Omar kafin su wuce U.S,duk in ta tuna zai tafi wani iri take ji acikin zuciyarta,ba don taso ba,Amma taci alwashin bazata ta6a binshi U.S ba,kuma bazata ta6a neman ya tafi da ita ba,ko ta nemi soyayyarshi ba,ta lura ba sonta yake yi ba,yana yin amfani da itane don ya biya buƙatarshi kawai,in kuwa har hakane baisan darajarta ba,
Jiki asanyaye ta zauna gaban mirror,tajima a haka kafin ta ɗauko handryer,Ta jonata ajikin socket,Nan take iska ta soma busowa buuuu da ƙarfin gaske,Busar da gashin kanta taci gaba da yi,Yanzu tsayin gashinta ya dawo fiye dana da,har waist ɗinta,Ga cikowar da yayi,daga gaban goshinta kuwa wani kwantaccen gashi ne wanda ya ƙarama fuskarta kyau,bayan ta kammala busar da gashin nata,ta shafe ko'ina na jikinta da waɗannan mayukan da aunty Azeema ta bata,Bayan ta kammala,Light make up tayi akan fuskarta,powder tasha fa,ta murza man baki,har wani ƙyalli lips ɗinta keyi,
Miƙewa tayi daga gaban mirror ɗin ta koma wurin wadrobe ɗinsu,wata matsiyaciyar baby doll ta ɗauko,Shara shara wadda da ita da babu duk ɗaya ne,net ne kawai ajikin rigar,black color kana hangen komai muraran A bayyane,Iya guiwa rigar ta tsaya mata,komawa tayi gaban mirror ta ɗauki turarurrukan nan da hajiya azeema ta bata,tabi ko'ina ta feshe wani irin shu'umin ƙamshine ke fita daga jikinta,hatta Amrish dake bacci sai da turaren nan yakai mata karo,
Ribbom ta ɗauko,nan fa ta soma kiciniyar ɗaure sumar kanta,yayi yawa sosai gashin,sai tasha wahalar tattare sumar zata ɗaure,gashin Ya kubce mata,tuni ta fara haɗa gumi,tana cikin yin damben ɗaure gashin kanta,Tajiyo sautin shigowar motocinsu,
A jere suka shararo da gudu izuwa cikin gidan,Bayan sunyi parking ɗin Motocin Amstrong Ya buɗe murfin motar,Tare da zagayawa ya buɗe mashi,saukowa yayi daga cikin motar,Jikinshi na sanye da Army trouser,Light green Shirt,ta ɗame jikinshi sosai,Sumar