Showing 291001 words to 294000 words out of 307403 words

Chapter 98 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

6oye a ƙarƙashin Table ɗinsu,Nan ya zauna,yana jiran Sgr Ya kammala masu girkin"'sam abbansu bai Lura da mayafin sehrish dake yashe kasa ba,ga kuma slippers ɗinta dake a ƙasan ƙafafun Sgr,bai kuma Lura da kaskon da Sgr ya sauke ba,
"Rafayet wai ƙaurin me nake ji ne"?
"Albasa ce ta ƙone,"
Yatsina fuska abba yayi"ƙaurin ba daɗin ji,dan Allah karka bari abincin ya ƙone,"
Amsa mashi yayi da "toh"

Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin ƙafafun abba masu sanye da slippers,sai faman karkada kafafun yake yi,duk fargaba ta kamata,ta ƙanƙame jikinta a ƙarƙashin table ɗin,tuni zufa ta wanke fuskarta,har rage numfashinta tayi duk don kada abba ya ganta

Daƙyar Sgr ya samu ya matsa,Ya ɗauko plate mai faɗi Ya zuba masu chicken papper soup ɗin da sehrish ta kammala,duk baiji daɗi ba,baiwar Allah tasha wahalar Girka abunta don tana jin yunwa,Ga abba yazo zai cinye mata kazarta,

Duk wani motsinshi akan idon abbansu ya kafe shi da ido yana kallonshi,dama saida ranshi ya bashi cewa Shi yake kallo,a sukane ya juyo hannunshi ruƙe da plate ɗin,haɗa ido su kayi da abbansu da sauri Sgr ya kawar da idanuwanshi,
Wani irin kallon ƙurulla abbansu keyi mashi,Duk yabi ya tsargu,murmushi yagani akan fuskar abbansu me haɗe da dariya,ɗaure fuska Sgr yayi tare da samun wuri ya zauna,Suna fuskantar juna shi da abban nasu,Sauke plate ɗin yayi asaman table ɗin ya turama abbansu"Gashi nan,bismillah,"
"Kai bazaka Ci ba"
Girgiza kai Sgr yayi"Na ƙoshi"
ɗaure mashi fuska abba yayi"In har bazaka ci ba,nima na ƙoshi,tun ɗazu na lura dakai sai wani shan mur kakeyi saboda kawai nace ina jin yunwa,gobe fa zaku tafi ko irin missing ɗina baka yi,"ya ƙarasa maganar yana harararshi,
Jin haka yasa Sgr ya saki fuskarshi don ya faranta mashi
"Am Sorry dad..let's eat together,'yakai ƙarshen maganar tare da zura hannunshi ya ɗauki cinyar kazar yakai bakinshi yana tauna,abba ma ya sanya hannu suka soma Ci atare,sai faman lashe baki yake yi"Wai dagaske kai kayi girkin nan?
Jinjina kai Sgr yayi alamar Eh,
Abun ya ɗaure mashi kai"Danasan haka ka iya girki,da tun farko ban ajiye azmee a gidan nan ba....."
Sakin baki Sgr yayi sototo yana kallonshi,shikuwa sai jin daɗi yake yi Sgr ya iya girki,.
sehrish dake la6e ƙarkashin table ɗin,ƙamshi duk ya cikata,Kamar ta fashe da kuka,saboda yunwar da take ji,ta kwalla fa rai sosai,"
"Kasan wani abu"?girgiza kai sgr yayi alamar a'a
Abba yaci gaba da cewa"ɗanɗanon girginka Sak irin na azmee ya akai haka"?
Yatsina fuska Sgr yayi,kafin yace"May be dan inacin abincinta ne,yasa taste ɗin yazo ɗaya dana ta,"
Murmushi abba yasaki"U are right...ka manta baka kawo mana abunsha ba?ƙishi nake ji,'

Har ya yunƙura zai miƙe,Abba yayi saurin dakatar dashi"koma ka zauna,Kasha wahalar yin girki nasan duk ka gaji,bari naje na ɗauko mana,"

Ajiyar zuciya Sgr ya sauke tare da komawa saman kujerar ya zauna,Abba ya mike yabar wurin,Kafin ya dawo Sgr yayi saurin ɗebo naman Ya zurama Sehrish ta kasan teburin,har saida ta tsorata ganin hannunshi,da sauri ta sanya hannu ta kar6a,ta shiga turawa abakinta tana ci,ƙasa ƙasa da murya ya furta"Am really sorry duk laifina ne,da banzo ba da duk hakan bata faruwa ba,"
Murmushi ta saki batare da tace mashi komai ba,sake ɗebowa yayi ahannunshi ya miƙa mata,ta sanya hannu ta kar6a,ta tura abaki ta lamushe,cikin sanyin murya tace"Ƙishi nake ji,kuma ina jin bacci,"_
Kafin ya bata amsa sai ga abba ya dawo hannayenshi rungume da bottle waters masu Sanyi,hada na Lemu ya haɗo masu,

Ajiyesu yayi asaman table ɗin,Ya zauna idonshi akan plate ɗin,A ruɗe yace"kai!ya akai naga an kwashe?duk kai ka cinyesu"?
Ɗaga mashi kai Sgr yayi alamar eh,Sam abba mai yarda da maganarshi ba,saboda tun da suka fara ci ko cinya ɗaya bai iya ci ba,Amma daga zuwa ɗauko lemu da ruwa harya Cinye saura kaɗan kazar ta rage,

Tura mashi lemun yayi agabanshi'Take it,"
"Ruwa nake buƙata"ya ambaci hakan tare da kai hannu ya ɗauki robar ruwa mai sanyi,mai maimakon yasha sai ya tsaya yana jiran abbansu ya fara kafa baki zai sha nashi,Shi kuma sai yayi dabarar mika mata ruwan,
Lemu abba ya ɗauka ya buɗe shi ya kwafa abakinshi yana sha,A hanzarce Sgr ya zura hannunshi ƙarƙashin table ɗin ya miƙa mata robar ruwa,ta sanya hannu biyu ta kar6a,buɗe murfin tayi kafin ta kwafa a baki tana sha,

Bayan abba ya kammala shan lemun ya ajiye robar ruwa,
Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"kai Ina ɗayar robar take ne?Guda huɗu ne na kawo mana,"hankalin Sgr ba ƙaramin tashi yayi ba,
"Daddy uku ne fa ka kawo,"girgiza kai Abba yayi a'a,guda huɗu ne Ta lemu biyu ta ruwa biyu,Kodai ta faɗa ƙarƙashin table ne....'yakai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin leƙawa ƙarƙashin teburin,A Ruɗe Sgr yace"karka kuskura ka leƙa......"tashin hankali sam baisan Ya furta hakan ba,tsabar ruɗi ne

A ruɗe abba ya ɗago yana kallonshi"Rafayet ni kake ce ma kar in kuskura in leƙa?Saboda me"?
Muryarshi na kerma yace"bansan nace haka ba,"
"Kodai kayi ajiya a ƙarƙashin taburinne"?
Da sauri yace"A'a,
"To meyasa kace kada na leƙa"?
Shiru Sgr yayi batare daya ce komai ba,"
Sehrish dake ƙarƙashin table ɗin duk ta furgita,jikinta sai kerma yake yi,batasan ya zatayi ba idan abba ya ganta,

"Shikenan,tunda baka so na leƙa,Amma ɗayar robar fa?ina ka kaita?
Wani irin wahalallan yawu ya haɗiya,
"Abba baka jin bacci ne?dare fa yayi sosai"
"Na kasa yin bacci ne saboda tafiyar da zakuyi gobe,zanyi missing ɗinku sosai,".
Murmushin yaƙe sgr yayi"but u ave to sleep,gobe zamu airport ba zaka rakamu ba"?
"Kada ka damu da wannan,rashin baccina bazai hana in rakaku airport ba,"
Jiki asanyaye Sgr yace"shikenan ae,"
Dariya ce ƙumshe abakin abbansu,kar yake kallonshi don tunda ya shigo kitchen ɗin ya gane cewa bashi kaɗai bane aciki,zuba mashi ido kawai yayi don yaga iya gudun ruwanshi,

Wata dabara ce ta faɗo mashi,A hankali Ya sanya hannu tare da Cire murfin robar ruwan Daya kammala sha,Sgr Duk bai Lura ba,Janye hannunshi yayi zuwa ƙasan table ɗin yasan tabbas indai macace a ƙarkashin table ɗin da zarar ya wurga murfin zata fasa ƙara,tayi tunanin Ko wani mugun abunne ya faɗo,

Daddagewa Abba yayi da ƙarfi ya wurga murfin Robar ruwan kaitsaye ya faɗa saman ƙafafun sehrish,Aikuwa A gigice ta fasa ƙara tana faɗin"Wayyo Allahna Ya rafayet 6era 6era...."
Tuntsirewa Abba yayi da dariya hada dafe ciki,Sgr dake zaune tamkar an dasa mashi aya,Sam ya kasa motsi,wata irin kunyace ta rufe shi,ya kasa ɗagowa su haɗa ido da abbansu,sosai abba keyin dariyar hada hawaye akan fuskarshi,Miƙewa tsaye yayi daga saman gujerar,Ya nufi hanyar fita daga kitchen ɗin yana tafiya yana dariya har yakai bakin ƙopar fita,ya ɗan dakata da yin tafiyar ya juyo ya kalli Sgr dake zaune Ya sanƙare duk yabi ya dabarbace,
Gyaran murya abba yayi mashi Ya ɗago suka haɗa ido dashi,
"Ɗan rainin wayau,da kace bakaso"?
Ƙayataccen murmushin gefen fuska Sgr ya saki har dimple dinsa ya lotsa
"Ashe kana nan ƙumshe da ƴar mutane,A kunnan abusufyan saina faɗa masa"yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar kitchen ɗin yana dariya tare da girgiza kai,"

Ajiyar zuciya Sgr ya sauke,A hankali ya ambaci Sunanta"Reesh...."cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi"Na'am ya rafayet,"saukowa yayi daga saman kujerar Ya zuƙunno kasan table ɗin,cikin sanyin murya ya soma magana"ya tsorata ki ko?"?
Jinjina mashi kai tayi,fuskarta sharkaf da hawaye,sai faman shessheƙar kuka takeyi,ruƙo hannunta yayi tare da fito da ita daga karkashin table ɗin,Hugging ɗinta yayi ajikin shi,Yana shafa sumar kanta"Am really sorry,if u are still hungry i can cook for u...".
"A'a na ƙoshi,bacci nake ji,"
ɗaukarta yayi asaman kafaɗarshi ya nufi hanyar fita daga kitchen ɗin,upstairs Ya wuce da ita part ɗinshi,ko'ina a gyare tsaf,A bedroom ɗinshi Ya sauke ta,
"Zan shiga toilet,"tayi maganar tare da juyawa ta nufi toilet ɗin,bin bayanta yayi"lemme help u....'bata yi mashi musu ba,atare suka shiga toilet ɗin,bansamu damar leƙawa ciki ba, balle in gano maku me ke wakana,saboda sun rufe ƙopar,

After some minutes Sgr ya fito ɗauke da sehrish,irin ɗaukar da akeyiwa Jariri,su duka biyun Suna ɗaure da towel a qugunsu,launi ɗaya farare,

Kaitsaye ya sauketa Asaman gadonshi,Yana ƙoƙarin miƙewa ta sanya hannu ta damƙi towel ɗin jikinshi gaba ɗaya ta warwareshi,kamar jira yake yi dama bai gamsuba abba ya katseshi,komawa yayi samanta,yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinshi,Sam basu gajiya da juna, kamar zasu kashe kansu,sai da suka raba dare,kafin Allah ya kawo bacci yayi awon gaba dasu,ƙankame da juna,sai da ana kiran sallar asuba,ya tashi sehrish ya ɗauko mata kayan baccinta da kanshi ya zura matasu ajikinta,cikin sanɗa ta fito daga part ɗinshi ta sauko downstairs,sai da tafara zuwa kitchen ta ɗauki mayafinta tukunna ta wuce ɗakinsu,

Bayan Kammaluwar Sallar asuba,matafiya suka shirya tsaf,domin tafiya Airport,Dukansu matan suna sanye cikin jallabiya baƙa,Sun laga gyale akansu,Sgr Da Omar suna sanye cikin Shadda,Junaid kuma yana sanye cikin suit farare,

Gaba ɗaya mutanan gidan Sun hallara a babban Falon gidan, lokacin da kowa ya kammala fitowa,Suka ɗunguma izuwa Wajen da motocinsu suke,kusan dukansu zasu yi masu rakiya,Amma banda Amaren Gidam,tun anan Sukayi bankwana dasu,Amrish tasha kuka sosai,haka Amal ma,

A motar dr harris,gwaggon katsina da abu suka shiga,tare da saude wadda ke zaune A gefenshi
Abba kuma tare da mommy suka shiga motar Fawan,

osman da adam a motar kanal Yusif suka zauna,

Najeeb kuma a motarshi Talal Da junaid suka shiga,

Sehrish da Jahad da hosana,Suna zaune a motar abusufyan Dakanshi zaiyi driving ɗin ya'yanshi,

Hajiya azeema tana acikin motar su twins,Jahan ne ke a mazaunin driver Ayaan na a gefenshi,

Akwai motocin Security dake gaba da bayan motocinsu,
Sgr yana acikin motarshi,motarsu Marshal Da major tana a bayan tashi,

Slowly motocin suke tafiya ajere har suka fito daga cikin babban gate ɗin gidan,koda su Jahad da sehrish suka ga An fita daga gate ɗin gidan sai suka fashe da kuka atare,Abusufyan sai lallashinsu yake yi,Shi kanshi daurewa kawai yake yi,idanuwanshi cike suke tab da kwalla,

Lokacin da suka ƙaraso Airport ɗin at the same time su kayi parking ɗinsu,A tsanake duk suka fito daga cikin motocin,idanuwan kowannansu Yana akan Katafaren Privet jet ɗin da aka tanadar masu,wanda ya kasance Mallakin Rafayet ne,jigunannan gaske,Mai ɗauke da Sunanshi Ajiki da manyan haruffa akayi rubutun SGR

Tunkafin su iso Airport din junaid keta kukan rabuwa da abbansu da ƴan uwanshi,Kowa jikinshi yayi sanyi,

Rungumeshi abba yayi sosai ajikinshi yana shafa sumar kanshi,
"Junaid so kake nima inyi kukan ko"?
Cikin shessheƙar yace"Abba bansan na tafi nabarka,"
"Junaid aduk inda kake a faɗin duniyar nan,inaso ka sanya aranka cewa Muna atare da juna,zan dinga zuwa akai akai ina ganinka,"daƙyar abba ya samu ya lallashe shi,bayan ya saki abbansu Ya rungume Fawan yana kuka,kowa yayi tsaye cirko cirko gwanin ban tausayi,
Bubbuga bayanshi fawan yayi"be a man mana,Kada ka bani kunya,dan Allah kadaina kukan nan,"
"Ya fawan,tafiya fa zamuyi,"
"Tafiya ae ba mutuwa bace junaid,just calm down ur mind,Da zarar babynka ta haifu zan wanko ƙafa inzo suna"cikin raɗa yayi mashi maganar a kunnanshi,har sai da junaid yayi dariya,bayan ya rabu da fawan ya rungumesu twins atare yana raira masu kuka,
"I love u so much Ya jahan da Ya ayaan,Zanyi missing ɗinku sosai,"
Atare suka haɗa baki wurin cewa"We love u so much Our shagwa6a boy,"
Bayan yabar wurinsu Ya nufi kanal Yusouf yayi hugging dinshi"yaya yusif yanzu shikenan.....'
"Junaid banaso kana zubar da hawayenka,inda rai da lafiya wata rana zamu zo,kaima kuma zakazo,"
"Amma ae bazan dinga ganinku kullum ba,"ashagwa6e ya ƙarasa maganar,ba wanda junaid ya bari,ɗaya baya ɗaya sai da ya rungume kowa hadasu uncle da hajiya azeema dasu Osman da Najeeb,

Bayan ya kammala nashi,Su Sehrish suka Soma bin kowa suna yi mashi sallama,Gwaggon katsian hada kukanta,Za'a tafi da ƴa'ƴan abusufyan ɗinta,Sosai ta rungumesu ajikinta,Suna kuka tana kuka,babu mai lallashin wani,daga wurin gwaggo wurin hajiya azeema suka wuce,Ta haɗasu duka ta rungumesu,tana lallashinshu,daga wurinta suka nufi wurin Mommy,Itama ta rungumesu ajikinta,daga wurin mommy suka nufi wurin saude ta rungumesu,Sai da suka gama da kowa tukunna suka nufi Oummansu,ta haɗasu duka ta rungumesu,hawaye jaga jaga akan fuskokinsu,bayan sun gama da matan suka nufi wurin Daddynsu da abbansu,Kowa ya sanya masu albarka,ɗaya bayan ɗaya suka bi mazan suna yi masu bankwana,a lokacin Junaid yana manne da oummansu,ta rungumeshi sosai,kamar zai koma cikin cikinta,

Sai daga bisani Omar da Sgr suka soma bin kowannansu suna yi mashi bankwana,Lokacin da suka zo wurin abba Ya shafa sumar kan kowannansu kafin yace"Omar Rafayet"ya ambaci sunansu,Suka amsa mashi,
Kafin yaci gaba da cewa"A matsayina na mahaifinku babu abunda banyi maku ba,duk wani nauyi naku dake akaina na sauke shi,Saura ku ya rage naku,Ga Amanar ƴan uwanku nan,Ku kula da rayuwarsu,saboda ƙaunar dake a tsakaninku dasu yasa zasu bar kowa nasu,iyayensu danginsu,zasuyi rayuwa daku a inda basu da kowa sai Allah daku ɗin nan,Ku ruƙe amana,kada ku bari koda kwallarsu ce ta zuba kasa,Ku share masu hawayansu,in suna da damuwa kuyi ƙoƙari wurin faranta masu,da zarar kun bar ƙasar nan basu da wani makusanci daya wuce ku ɗin nan,Kune a matsayin Iyayensu, kuma danginsu........"sosai amma yayi masu nasiha,duk ya kashe masu jikinsu,

Lokacin da suka je wurin abusufyan,Ya kirasu Su jahad suka jera dasu,ya kuma kira junaid shima Yazo,Ruƙo hannun junaid yayi idanuwanshi cike tab da kwalla ya ruƙo hannun Jahad ya haɗasu wuri guda,Muryarshi na kerma yace"junaid ga amanar Jahad nan na baka,"kallon juna Junaid da jahad su kayi,idanuwan kowannansu cike tab da ƙwalla
"Na yarda dakai sosai,Nasan Zaka ruƙe mun amanarta,"
Jinjina kai junaid yayi"in sha Allah uncle,zan ruƙe maka ita amana,bazan ta6a bari tayi kukan rashinku atare da ita ba,"
Kowa dake a wurin saida ya saki murmushi,Jin abunda junaid yace,Yayi magana ta hankali,

Sakin hannunsu Abusufyan yayi,ya kuma ruƙo hannun Omar Ya ruƙo hannun hosana dake ta kuka ya haɗasu wuri guda,
"Omar Na yarda dakai sosai,na yaba da kyawun halayanka,Ga amanar ƴata nan,na baka,"
Tuni idanuwan Omar suka ciko tab da kwalla,daƙyar ya iya buɗe baki yace"In sha Allah Uncle,Zan maye gurbinku a wurinta,Zan bata kulawa fiye da yarda zan kula dakaina,"

Murmushi abusufyan yayi bayan ya saki hannun Omar ya ruƙo hannun Sgr,tare dana Sehrish wadda ke ta faman shessheƙar kuka ya haɗa hannayensu cikin na juna,Kallon Sgr yayi yayin da shima Idanuwanshi na akan fuskar Uncle ɗin
Cikin Zolaya abusufyan yace"Surukina nakaina"murmushin gefen fuska sgr ya ɗan saki,
Mayar da idanuwanshi yayi kan Sherish"My daughter,"cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi"Na..na...am daddy.."

"Rafayet Bana kokwanto akanka,Na yarda dakai kuma na yarda da irin ƙaunar da kake yi mata,Ga amanar Sehrish nan na damƙa maka,"

In sha Allah Uncle,i will take care of her,bazan ta6a bari tayi maraici atare dani ba"
Murmushi abusufyan ya saki tare da cewa"Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku,"sosai yayi masu addu'a,Kafin daga bisani su kayi Sallama da kowa,Omar na ruƙe na hannun Hosana suka nufi stairs ɗin jirgin,Junaid yana abayansu hannunshi ruƙe dana Jahad,Sgr na ruƙe da hannun Sehrish,a haka suka hau matattakalar jirgin, sai da suka kusa shiga ciki,Suka juyo su dukansu suna kallon Iyayensu da ƴan uwansu,Atare suka ɗaga hannu sunayi masu bye bye,


Suma su Abba suka Ɗaga hannuwansu suna yi masu bankwana,da gudu abu ta shige cikin motar abusufyan tana kuka,komawa su kayi cikin motocinsu,A jere suka bar Airport ɗin,Tun suna akan titin komawa gidan,Jirginsu Sgr Ya gifta ta Saman iska,Suna jin ƙararshi,🛫😭


Bayan sun koma gidan babu wanda ya iya cin abinci acikinsu,tamkar anyi mutuwa,gidan duk babu daɗi,Babu Junaid babu Ya Omar babu Babban Yaya,Babu Sehrish babu hosana babu Jahad,Kewarsu duk ta kama ƴan gidan,oummansu har maganin ciwon kai tasha Saboda kukan da tayi,


Los Angeles

California🛬




💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫

*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI KYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327

_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_

Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻

Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata

Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki

Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci

Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji

Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji,

Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima

Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida

Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki

Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi

Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu

Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu'umar humra
Turaren AL'AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k'afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k'arfi)



Muna dahuwar Kaya kamar haka💫💥💫💥👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Dahuwar zabo (mallaka)
Kazar Yar gata
Yan shila
Ciccibi
Dambu
Zuciya
Yan ciki
Kwai ukku
Tsoka Tara
Kifi
Da sauransu


Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata

Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah

Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,

Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd

07069711327
[3/19, 9:44 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*


*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*


Zazzafar haja daga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login