Showing 1 words to 3000 words out of 190771 words

Chapter 1 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1505

๏ปฟ[8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
~{{MY FAMILY }}~
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*BOOK 2*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ

*Bismillahir Rahmanir Rajeem*

*Ina mai mik'a yabo da godiya na ga Allah mad'aukakin Sarki wanda bai hafa ba kuma ba'a haifeshi ba Ubangijin sammai da kassai,
Sannan ina k'ara salati zuwaga shugaban mu d'an gatan Allah, Annabin mu Muhammad (S.A.W), tareda iyalansa da sahabban sa baki d'aya.

*SADAUKAR WA*
A wannan tafiyar gaba d'aya littafin tun daga farkon shi har zuwa karshen shi zai zamo sadaukarwa ne ga d'aukakin masoya da suka jure wajen bibiyar labarin in daga farko har zuwa yanzun,
Ku d'in kun kasance abun alfaharina, na fara rubutu banyi zaton labarin zai zaga har zuwa inda banyi zato ba, sai gashi a sanadin littafin *DANGINA* na had'u da mutane kalaยฒ wasu iyayena wasu yayye wasu kanni,
Lallai na yaba da kaunar ku gareni, tun daga kan Marubuta dama makaranta da a kullum kune ke bani gwarin gwuiwar ci gaba da rubutu,
Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan zano sunayen ku ba, ina dai so ku sani cewa na yaba matuk'a๐Ÿ’˜.

*Ga masu buk'atar littafin daga farko zaku iya tuntub'ana kai tsaye da wannan number d'in* 08061358462.
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ma makaranta ba, dan haka karkuji d'ar kuba duk wanda kuke so.



*Page 1*



``````` Tunda Allah yama Malam isowa da maraicen nan gaba d'aya bai samu zama ba, domin bayan tafiyar shi anyi wani rashi na d'aya daga cikin d'aluban shi da sukayi karatu a k'ark'ashin shi, dan haka koda ya iso babu jimawa ya shirya ya wuce can wajen iyalan mamacin domin yi musu ta'aziyya bashi ya samu sukuni ba dai har sai zuwa dare.

A gefen Baba Adamu kuwa tun a sanda Baba Auta yama shi sallama akan zai wuce Abuja a ranshi yaji cewar gudun hijira ne kawai Adamun zaiyi dan baya son gamon su da Malam, domin dama tun zamanin k'uruciya ma in sukayi ma Malam d'in laifi shi Auta Hijira yake yabar gidan har sai Malam yayo bikon shi kafin ya dawo.
Bai matsa mishi ko tambayan dalilin da yasa zai wuce d'in ba dan yasan Auta dannewa ne kawai yakeyi amma shi a matsayin shi na wanda yake gaba dashi yasan dole abunda ya faru ya dake shi, domin dai babu uban da zaiyi alfahari da kasancewar d'iyar shi bazawara,

Malam bai shigo cikin gida ba har sai misalin karfe 9 da wasu mintuna na dare, a yayin da shi kuma Baba Adamu ya kasa ya tsare a farfajiyar gidan yana jiran isowar shi dan gara ya gabatar mishi da komai a daren nan dan Malam mai iya mishi sai Allah yana iya idan shi yace ya bari sai gobe ya tunkare shi da batun, shi kuma Malam d'in yahau shi da fad'a akan wani dalilin ne ya hana shi gabatar mishi da takardar a yau?


"Ah ah Adamu kai kad'ai zaune a waje lafiya kuwa? Ko kodai jiran shigowa na kakeyi ne?"
Malam ya tambaya a yayin da hankalin shi yakai kan Adamun dake zaune a kan d'aya daga cikin kujerun da aka ajiye dan zama a kofar falon Malam,

"Eh Malam barka da dawowa an dawo lafiya ya hanya da gajiyar tafiya?"

"Alhamdulillah lafiya lau muka iso, kai kuma kazo kayi zaune a nan kai kad'ai ai ko sauro bazasu barka ka sarara ba, da kasan kana jirana ai da ko a waya ka kirani, tunda dai ba komai nikeyi a wajen ba na dai tsaya ne muna gaisawa da makota tunda kwana biyu bana nan abubuwa sun d'an faffaru, kuma ai da ka bud'e falon ma ka shiga"

"Ba komai Ya'ya na daiji zaman a nan d'in ne dama shi yasa ban shiga cikin ba"

"To madallah bismillah mu shiga daga ciki koh!"
Malam ya ambata a yayin da ya tura kofar falon da sallama suka shiga,
Bayan sabuwar gaisuwar da suka sake da tambayar bayan saduwa ne malam ya d'aura da cewa,

"D'azun auta ya kirani cewa sun wuce abuja shida mai d'akin shi zasu d'an kwana biyu kafin su dawo, wato dai Auta take taken shi so yake dai yabar gidan nan dama garin baki d'aya, ni ban san me mutane suke so su zama ba gaba d'aya dai da zarar mutum yaga ya d'an tara yan kud'ad'e sai kaga ya manta da gidan su sai ya ware kanshi can a gefe shi d'aya, niko gani nike mai yakai zama cikin ahalin ka dad'i fisabilillahi fa, amma yanzun da zarar nayi magana sai ayi min wata fassara ta d'aban, tunda aikin shi ya koma Kaduna ya fara wannan galantoyin tsakanin kaduna da zaria nasan cewa gaba kad'an zaice ya gaji da yawon zai kwashe iyalanshi ne su koma can, yanzun nan fisabilillahi in banda abun Muntari a kadunar har za'a samu wata makaranta data d'ara ita wannan ABU d'in daya bari ne? Ni dai bazan k'ara magana ba ma balle aci gaba da cewa na fiye takura"

Duk surutun da Malam keyi Adamu baice komai ba sai dai d'an murmushi da yakeyi,

"To ina ce dai lafiya? dafatan dai babu abunda ya faru a gidan bayan tafiya na? Koda yake ko wani abun ya faru nasan zaku magance shi basai kun jira dawowa na ba"

Daga kanshi yayi ya kalli agogon dake mak'ale a jikin bangon falon nashi,

"Ashsha ashe dare ya fara haka gashi gaba d'aya na manta dana ware tsarabar uwata ban ce yaran nan su mik'a mata ba harna fita,
Baiwar Allah nasan babu mamaki ta shigo bata iskoni gida ba"
Wayar shi dake gefe ya d'auka kafin ya lalubo Number din Innar yara kira d'aya biyu ta d'auka,

"Na shigo fa tun d'azun amma babu wacce tazo dubani a cikin ku"
Daga can gefen Ita kuma ta amsa mishi da cewa,
"Ayi mana afuwa Malam ita Dije nan wajena ta amshi maganin ciwon kai tasha to nasan babu shakka bacci ne ya d'auketa ni kuma ban san ka shigo ba shi yasa amma zan iso yanzun"

Sai da ya yanke wayar sannan yace da Adamu,

"Kaga halin matan nan koh? Mata biyu amma na shigo tun d'azun an rasa wacce zata shigo ta bani abunci a cikin su"

"Ayi musu uzuri ya'ya indai abinci ne ai koni sai in had'a maka tunda gashi can ai naga an ajiye"

"Allah mai iko, aiko kaga ni sam ban kula da cewa an ajiye abincin ba, to d'auko sai ka zuba mana muci ai mun kwana biyu dama bamu samu damar cin tuwon dare tare ba"

Duk da cewa Baba Adamu yaci nashi abincin hakan bai hana shi zuba musu wannan d'in ba suna ci suna hira a haka har Ameena ta shigo ta same su,
Koda ta iskosu itama zama tayi sukaci gaba da hiran Malam na basu labarin yanda tafiyar shi zuwa Mai duguri ta kasance,
[8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ


*Page 2*


A wannan dare sam Malam bai samu sukunin yin bacci cikin salama ba, domin kam sosai fa abun ya dake shi bai tab'a zato ko hasaso cewa hakan na iya faruwa a cikin ahalin shi ba sakin aure fa ake magana, auren kuma daya zama auren had'i na farko da suka had'a tsakanin yaran su da fatan karin dankon zumunci a tsakanin su, shine daga tafiya ya dawo ya cimma wannan irin k'atuwar iftila'in.
Duba da cewa suma iyayen su basu kasance mazaje masu sakin aure ba, haka kuma suma da suke a matsayin iyayen nasu yaran sam babu wanda a cikin su ya tab'a tsinke igiyar d'aya daga cikin matan shi,
Amma sai gashi yau an wayi gari nasu Yaron da suke kallo mai nutsuwa da hankali shine ya aikata hakan,
Duk da jawabin da Adamu ya mishi na dalilin da yasa uwar gida tayi tsaye akayi sakin sam shifa bai wani gamsu ba, dan haka ya k'agara gari ya waye ya samu zama dashi Yaron dama iyayen shi, dan bazai yarda da d'abiar saki a cikin zuri'ar shiba, koda ko ace sakin ba akan Meenal ya fad'a ba dolene yabi kadun dalilin sakin balle kuma abu ya fad'o akan ta.

Kamar yanda Malam ya buk'ata cewa Auta ya kira Hajiya akan a dawo mishi da Meenal gida, to dai shi Auta a wannan daren kasa kiran Hajiya yayi har sai washe gari,
Washe garin ma bashine ya kirata ba Mommy ya rok'a domin dai koda kiran Malam din ya riske shi taji sakon da Malam din ya bayar tasan kuma shi Auta bazai iya kiran Hajiya ba dan haka ita da kanta ta kira ta take shaida mata cewar Malam yana son ganin Meenal din a gida saboda zasuyi zama,

Hajiya ko dama tuni damar hakan ta dad'e tana jira dan haka babu musu ta amsa da cewa zasu isa gidan da wuri kamar yanda ya buk'ata,
Duk da cewa Meenal din nada class din safe a ranar amma hanata zuwa Hajiya tayi domin a cewar ta, yanzun lokaci ne na kwatar y'ancin kai bawai lokacin karatu ba.

Shima a bangaren Malam Sulaiman tun daren da kiran Malam ya riske shi sam ya kasa samun sukuni,
Domin shi yasan halin Malam tunda har ya gaza hakurin wayewar gari ya kira shi a daren nan tabbas yasan ba komai bane illah sakon takardar Meenal daya dawo ya riska,
Yayi fad'a sosai dan Wallahi shi dama yasan hakan yana iya biyo baya, dan haka tun daren yake ta kokarin kiran Sarki a waya domin ya shaida mishi cewa koma ina yake to yayi kokarin dawowa Zaria a washe gari dan shidai wallahi uwar gida da d'anta sunja mishi, yana zaman zaman shi bai san farkon matsala ba sai da suka jagwalgwala komai sannan yanzun sun d'auko shi sun sashi a tsakiya,
yanzun haka gobe zaije gaban Malam yayi tsuruยฒ fisabilillahi kai dai ka haifi mutum kawai amma baka haifi halin shiba,
Rashin samun Sarki a waya hakan yasa dole a daren ya aika mishi da sakon Text message,
Washe gari ma yana tashi haka yaci gaba da kiran Sarki a waya amma har zuwa lokacin wayar bata zuwa.


Karfe goma sha d'aya 11am na safiyar wannan rana tayi ma,
Malam Sulaiman,
Uwar gida
Baba Adamu
Innar yara
Hajiya Innah
Meenal
Dama shi kanshi Malam d'in ne a cikin falon shi inda kuma ya bama yaran ahalin maza kaf sallahun cewa dukan su yana neman su da Misalin 12 na wannan rana wato dai bayan ya gama da iyaye kan yaran zai koma.

****

Malam Adamu ne ya bud'e taron da addu'a bayan anyi yan gaisheยฒ ne Malam yayi gyaran murya kamar yanda ya saba,

Duban shi ya maida kan Malam Sulaiman dake zaune daura dashi kanshi a duk'e kafin ya mayar kan uwar gida.

"Sulaimanu hak'ika da kai da Matar ka kun bani mamaki matuk'a domin kun aikata min abunda ban tab'a tsammanin riskar shi daga gareku ba, musamman ma ke Uwar gida!"
Ya k'arasa fad'a yana nuna ta da hannun shi manuniya.

"Shin kun manta shekarun bayane da kuka dunga min zarya a wannan falon nawa kuna rok'on arzikin in d'auki auran Mamana in ba d'anku?"
Ya karasa kalaman shi da tambayar su yana mai jiran jin amsar da zasu bashi,

Malam Sulaiman ne ya amsa da cewa.

"Ayi hakuri ayi mana aikin gafara Yaya, abunda ya faru baya nufin cewa mun manta da alfarmar da Kayi mana na bamu auren ita Mai sunan Hajiya duk da mun san cewa darajar zumunci mukaci, sai dai lamarin muma bamuyi zatan cewa zai juye zuwa gabar da muke kai a yanzun ba sai dai ka haifi mutum ne baka haifi halin shiba"

Yana rufe baki itama Uwar gida ta karb'a da cewa,

"Tabbas abunda ya faru ba abune mai dad'i ba, abune wanda dukan mu bamu tab'a tsammani ba, sai dai na sani cewa laifin duk nawa ne,
Nice naso kaina da nayi zaton cewa idan na aura ma d'ana mata daga cikin Dangin shi hakan zai karkato da hankalin shi zuwa gareni dama yaran shi dake tare damu,
Gaba d'aya son kusanci da d'an da nike ganin yamin nisa yasa na manta cewa rayuwar yarinyar da muka aura mishi zai iya zama cikin kunci,
Nayi zaton cewa d'a mai biyayya na haifa wanda zaiso abunda na bashi ya kuma tattala abun koda zuciyar shi bata so,
Sai dai ina ashe ba haka bane, domin ya nuna min cewa bako wacce zuciya ake cusa ma abinda bata muradi kuma ta k'arb'a hannu bibbiyu ba,
Hakika nayi kuskure naso kaina domin a lokacin baya idanuwa na ya rufe ta yanda bana hango komai sai rayuwar d'ana banyi la'akari damai zaije ya dawo ba,
Ashe shi ya amsa ne kawai dan yamin biyayya bawai dan yana soba wannan dalilin yasa koda muka aura mishi ita yakai ya ajiye ba tareda ya damu da kula da sauke hakkokin ta wadanda suka rataya a kanshi ba, mafi hatsarin kuma shine rashin sauke hakkin shimfid'a"

Katseta Malam yayi da cewa,
"Kenan kina nufin cewa dama tun da fari shi Sarki bai amsa batun auren ba kece kikayi ruwa kikayi tsaki kika dunga taso min keyar Mijin ki a gaba kuna min jele da rokon in baku auren uwata?"
Malam ya tambaya.
Ita ko Hajjaju dake gefe salati ta d'auka tana tafa hannuwa cike da mamaki take cewa.

"La'ilaha illahlahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam,
Ke koh dai wagga mata akwai ki da son kai dama na zuciya!
Yo ashe ba iya jikata kad'ai kuka tilastawa auren dole ba shima kanshi mijin cusa mishi ita kukayi! Yo ba dole tak'iyin daraja a wajen shi, ku a wajen ubanwa kukaji cewa anawa maza auren dole? kodan dai kunyi sabon yin ma yaran ku mata auren dole shine wannan karon kuka juya kan maza?,
To dan Allah jama'a ku tayani ganin wannan al'amari fa inba son kai ba in d'anki yayi nesa dake saboda Allah ya had'ashi da wata can k'atuwar mushirika ta shiga tsakanin ku miye na jikata a ciki da zaki sakota cikin dambarwar gidan ki?,
Kai wannan mata wannan mata da son kai kike, lallai ashe alhakin jikata ne ya bibiye ki shi yasa auren yak'i yayi danko, inba haka ba jama'a kina matsayin uwa ace d'anki na cikin jafa'i mai makon ki tashi tsaye kema ki yaki Matar tashi da karfin kudurar ubangiji kisa a taya shi da addu'a kema kuma ki dage, shine kike zaton yi mashi aure ne mafita bayan ita shed'aniyar Matar nashi na raye tare dashi?,
Ashe konton b'auna kukayi min kuka sa na yarda da cewar za'ama jikata auren ne kawai saboda a samu mafitar ciwon marar dake damu ta a wancan lokaci, dan cin amana ashe shigo shigo babu zurfi aka min, yanzun shi yayi saki ya tattara yayi wucewar shi wajen Matar shi ita kuma jikata an barta da zawarci, niko yar iya harda dagewa na wajen nemo mishi maganin sammu, to kowa yaje da halin shi wallahi mu dai bamu nufi kowa da sharri ba wanda kuma ya kullace mu cikin shi tayi"

Baba Adamu da Innar yara na suka dage wajen ba Hajiya hakuri dan sosai fa ta nemi burgewa sai faman maganganu take,

Sai da tayi shiru sannan shi kuma Malam ya amsa da cewa.

"Duk ma masu cewa munayi ma yaran mu mata auren dole ko kuma auren wuri, suna fadane kawai saboda jin dadin bakin su,
Nidai abunda na sani shine hakkin ubana wato ya zab'o ma yarshi miji na gari, sannan ni a wajena ban tab'a hango illah a wajen aurar da ya mace da wuri ba, duba da zamanin da Allah ya kawo mu a yanzun,
Bawai muna ma Allah wayau bane, ba kuma muna gadara akan kasancewar mu Malamai bane balle muyi tunkaho da hakan cewa mu yaran mu bazasu iya fadawa wani halin na rashin d'a'a ba,
Ita ya mace tamkar glass take koda ka adana ta a waje d'aya tofa sai Kayi kata tsan tsan domin abun kadan ne zai iya ture ta ta fado ta tarwatse,
Zaka iyayin ajiya na kayan kwaras na tsayin shekaru a waje d'aya amma fa duk ranar da tsautsayi ya amfa musu lallai zaka sha mamaki domin da zarar sun rushe fa babu wani tsafin da zakayi wanda zaisa su koma dai dai yanda suke tun farko,
Alhamdulillah a hakan muke kokarin bama yaran mu mata kula har zuwa lokacin da muke ganin sunkai kun zalin da zamu aurar dasu su koma hannun mazajen su, su kuma su d'aura da nasu tarbiyar,
Ita diya mace inka dubi rayuwarta kacokam zataga tun daga tashin ta har zuwa tsufanta komai nata a takaice yake, in an haifeta zata samu tarbiyar farko a gida, a tashin ta bata san kowa ba sai yan gidan su, ma'ana uwa uba yayye kanni da kuma sauran Dangin dake tare da ita, soyayyar farko da take tashi dashi shine na ahalin ta,
Mataki na biyu tarbiya na biyu kuma sai ya koma a hannun mijin auren ta da nashi ahalin, a hakan muke bakin kokari wajen zab'o mai tarbiyar da muka san zaiyi daidai da namu tarbiyar da muka d'aurata akai, wanda shi kuma zai daura mata nashi ciki harda yanda zata so shi su kuma rayu a tare,
Mataki na uku kuma shine matakin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login