Showing 171001 words to 174000 words out of 190771 words
nan gado fa zan hau bacci nikeji"
bataja da tsayi ba ta mika hannu wajen turarukan da suke laye akan mirror din taci gaba da fesa ma Meenal bayan ta tabbatar komai ya kammala gyalenta ta yafa,
"Sister bari mu wuce dare yayi yau a unguwar malamai zamu kwana" shiru tayi ba amsa tana binta da ido, dariya tayi "Bari in kara miki tuni wallahi kazar mu!
kazar mu!!
Kazar mu!!!
Kinji sau uku na maimata koh to wallahi ki adana mana ita da kyau, Dan ba yafiya tsakanin mu da wannan kazar tunda allah yasa muna da rabon ganin ranar biyan bashi to a biya a huta,
Yauwa kuma kiji tsoron allah banda rowa, kin daiji wa'azin da malamai sukayi akan hakkin miji akan mata Dan haka yasa kikaga na canza zanin gado dan wancan yan ganin amarya sun dakuna shi,
Ubangiji Allah kasa nan da wata Tara mu dawo taron suna Ameen ya rabbi "
ta k'arasa addu'ar tana shafawa a fuska,
"Asha amarci lafiya kidai tausaya ki daga mishi kafa kin san dai saurayine ba sabawa da buga wasan yayi ba sai kin bishi ahankali,"
"Kutmelesi amma wallahi gaba d'aya kin gama dani dan wulakanci nine ma zan d'aga mishi kafa?
Gaskiya allah saiya sakamin wannan katon sharrin da kikamin, ke wuce ma ki tafi nagode allah ya huce gajiya, kuma sai Allah ma ya saka min,
Kai gaskiya kin kwareni wainice zanbi tsohon tuzuru a hankali to yasin kofar dakin ma zan rufe inba hakaba nasan tabbas gobe a asibiti za'aci gaba da zuwa ganin amarya muguwa dake kawai"
Dariya ta fashe dashi bata kara kulata ba ta bude kofar ta fita Hijab Meenal ta zira ta take mata baya domin gidan yanzun tsit yake ba jama'a a side din amma tanajin hayaniya a farfajiya kilan angwayen ne suka dawo,
Saida ta taka mata har zuwa bakin kofar falon kasa, ta bude kofar kenan najiyo muryar Mai Jama'a,
Ai da gudun besfa wallahi bibbiyu ta dunga tsallake benen Allah dai ya tsare batasha kasa ba,
Tana shiga daki ta maida kofar ta rufe tana numfarfashi, ta baya ta fada gado tana ma Kanta dariya,
itadai bata san abunda ya sameta ba tunda aka yi auren nan gaba daya wani irin shakka da tsoron Mai Jama'a takeji,
Yana daga cikin manyan dalilan da suka sa ta tsiri wasar buya dashi, wallahi ita kadai gasan kalar jidalin da take hangowa a cikin kwayar idonshi,
Nima dai mai rubutun na tausaya mata shi din tun fil azal dama ya lafiyar kura bare kuma yanzun!
"Lallai dole in zage damtse dan dazarar ya gane abunda nike ma tsoro na kade har ganye na"
Tashi tayi ta koma cikin makewayi ta kurkuro baki sannan ta koma gefen da aka ware domin ganawa da ubangijin al'arshi,
Bayan ta idar ta dade akan dadduman tana gabatar da addu'o'in samun zaman lafiya tsakaninta da mijinta sannan nltayima iyayen su addu'a dama sauran musulmai baki daya.
Hijab dinta ta cire ta ninke shi sannan ta karasa ta kashe hasken wutar daya cika dakin gabar wanda yake a gefen gadon,
saida tayi addu'ar bacci ta shafema jikinta sannan ta kashe sauran hasken data bari tabi lafiyar gado,
A gefen mai Jama'a kuwa....
Bayan su Amina sun wuce sadeeq yama magana akan ya sallami duk wata mace da take wajen baya bukatar ganin su,
sai da ha tabbatar da sun wuce din sannan ya fito daga mota cikin hall din suka koma da sauran abokainshi,
Abunda ya dauremai kai a lokacin shine ganin wajen dund'um wato babu haske a cikin hall din duk da kasancewar ga haske ko ina a waje,
"mutane sun gama watsewa ne? " ya tambaya sai dai bai samu amsa daga wajen kowa ba kutsa kanshi yayi cikin hall din dan haka nan hikejin kamar wani abu suke shiryawa,
yana shiga yaji fashewar Abu a saman Kanshj a dai² sanda wasu kana nan abubuwa masu kyalkyali suka fara zuba a jikinshi wutar wajen ya dawo.
Happy married to you!
Happy married to you!!
Happy married, happy married, happy married to youuu...........
Haka suka hada baki dukan su wajen fada,
Bude idonshi yayi baki sake yna kallon su, dan yayi zaton koda zan iske mutane to zasu kasance tsiraru ne a wajen Amma ga mamakin shi sai yaga wajen cike yake dam da mutane kuma mazane zallah ba jinsin mata, wasu daga cikima bai gansu wajen ba sai yanzun,
Lallai gayun nan sun shammace shi wai dan fitan nan da sukayi shine har sun canza docoration d'in dake wajen sun kara gyara wajen ga kuma kayan kida a gefe ba wanda akayi amfani dasu dazun ba,
gaskiya dai yayi farin ciki matuka domin abun yazomai unexpected Ashe sun san Abunda suka shirya shi yasa da yace musu ba wani event basuja zancen da tsayi ba,
Ganin yayi tsaye cak ne yasa suka jawoshi zuwa cikin fili bayan sun umarci DJ daya basu sauti, gaskiya sunyi kokari domin wai wankan ango suka shirya ba tareda sani shiba sun kuma wanke shi da turaruka da tarin kudade,
Duk wani turaren da suka san AK na so saida suka yayyafa mishi duk son shi da kamshi saida yaji yana hawa mai kai a yau,
( gaskiya dai anci amanar turare haka akayi ta feshe turarukan makudan kudade a iska, yo suba kudiba balle in kwaso mu raba damasu karatu)
Gaskiya kamshi abun sone daure ko turaren durine ki siya ki dunga shafawa kawata, karki yarda ki dunga shiga mutane kina tsami please!!!
Sunyi k'ok'ari kuma yaji dad'i ya kuma yaba musu basu bata lokaci sosai a wajen ba sukayi sallama da dayawa daga cikin su suka kuma raka wasu masauki,
sannan Yusuf da Sadeeq suka daukoshi zuwa gida,
bayan sun iso nan din ma dai bamu samu mutane ba domin dare ya farayi a lokacin,
" Yane anan zaku kwana ne ko wucewa zakuyi?"
Dariya musty yayi
"kai malam me kake nufi? Muda muka rako ango ai kasan bama tafiya sai mun damka ka a hannun Amarya Dan haka muje ciki mutumina ya fada yana kallon Sadeeq,"
"Wa zaku raka dakin amarya kamar wani yaro?"
"Sabon shiga zamu mik'a" cewar Yusuf Gyara zama hayi akan kujerar motan haci gaba da latsa wayarshi yana kallon hotunan Meenal da yasa Hafees ya dauko mishi ita dazun ba tareda sanin taba,
Har sun fita sun fara tafiya yana ganin dai sun lura ban biyo bayan su bane shi yasa Sadeeq juyowa Amma ga mamakin shi koda ya dawo bayan motar ya bude ya fiddo ledoji daga ciki,
su kuma sauran motar daya hango su hafees a ciki suka k'arasa,
motar Maryam kenan Maryam dince ta tambaye su "Ina angon"
nuni suka mata da motar da suka iso a ciki, fitowa tayi ta iso inda yike nocking din side din da yake zaune Maryam tayi bayan ya sauke glass din gefen gaishe shi tafarayi
"Mai Jama'a Barka da dare ya akaji da taron jama'a? "
"Alhmadulillahi "ya amsa dashi
"ya naku gajiyan mun godefa ubangiji Allah yabar zumunci ya kuma saka muku da gidan aljannah,"
Murmushi tayi "zamu wuce ne dama nace sai na jira isowar ka dan allah Ya Abdul duk da nasan ko ban baka amanar kawata ba zaka riketa da amana,
sai dai ince kayi hakurin zama da ita sannan ka kula mana da ita ubangiji Allah ya baku zaman lafiya yasa ace gara da akayi"
"Ameen ya rabbi" ya amsa dashi yana mata godiya fitowa yayi suka jera har zuwa inda motarta sannan yama sauran godiya suma Musty yama magana akan ya sallami kawayen Amarya a yayin da Maimoon ke fitowa daga cikin gidan,
in baku mantaba jin muryar shine yasa Aminatu komawa cikin gidan da gudun besfa.
Bayan wucewar su Maryam ne Sadeeq cikin dariya Yake cewa
"kai ai da munyi katuwar mantuwa fa a shiga dakin amarya ba tareda kazar amarci ba aiko dai da anji kunya wallahi,"
Yusuf na dariya yace "Aiko dai yau da amarya ta kullema ango kofa kuma wallahi tafiyar mu zamuyi mubar ango yayi kwanan keso",
Shafa kai Mai Jama'a yayi bayan sun kai bakin kofar falon yana murmushi kasa² yake cewa
" wai yaushe kukayi wannan cefanen?" Yayi tambayar yana mai tsaresu da idanuwanshi,
musty ne yace
"Dan Allah Mai Jama'a kadena tsareni da wadannan idanuwan naka to gudun mawar na Faisal ne dan nima na shafa'a shine ya aiki su Ahmad dazun suka siyo kafin mu taso daga wajen can,"
" nagode" yace yana mai rungume su gaba dayan su,
sadeeq ne cikin shashsheka yake cewa "wallahi ji nike Kamar a mafarki wai yau Abokina yayi aure da burin zuciyar shi har gamu munyo rakiya zamu damka ango ga amaryar shi ya fada yana share hawaye, lallai rabon kwado baya hawa sama ko yahau saiya sauko.
Congratulations once again friend ubangiji ya dauwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auren ku,"
ameen suka amsa dashi baki daya,
Shiko Yusuf daurawa yayi da cewa
"nasan mai Jama'a yana matukar kaunar Amina Amma tun aurenta na farko sai nayi zaton tunda ya rasata a lokacin shikenan zai kulle babin ta duk da gaskiya na bashi laifi sosai a lokacin domin shi yayi nauyin baki harta subuce mishi, Ashe tukun na dai Wasa farin girki ban kara tabbatar da kaunar da yake mata ba sai yanzun Alhmadulillahi gashi yau komai yazo karshe, shi dama mahakurci akace mawadaci yau Kam ba burin mai Jama'a ne kawai ya cikaba burin mune gaba daya ganin abokin mu cikin farin ciki dauwa mamme,"
Oh! Oh!!
Wadannan abokai sunsa sassan jikina yayi sanyi, nasan masu karatu ma sun yaba!
"Kai!
Kai!!
Kai!!! Dan allah ku cikani kun wani bi kun dukunkune ni Kamar sabon kwabo a hannun kuturu, bayan kun san amaryata na jiran shigowa ta"
Dariya suka fashe dashi dukansu sannan suka karasa cikin falon matakala suka hau zuwa sama,
falon dake saman sukayi ma kansu masauki sadeeq ne yace ma mai Jama'a Dan allah kirata mu samu mu wuce dare yayi.
Ok yace yana mikewa "wallahi nasan tayi bacci yanzun Amma bari in d'auko muku ita"
ya karasa fada yana mai shigewa cikin corridor din da dakunan bacci ke jere kofar dakin da yake a matsayin nata ya karasa handle din kofar ya murda da niyyar bude kofar baiyi mamakin jin kofar a kulle ba domin yasan dama za'ayi hakan, murmushi yayi
"lallai ma yarinyar nan waima ni ta rufema kofa kai! "
Juyawa yayi zuwa nashi dakin Bude kofar yayi da key sannan ya shiga da sallama a bakin shi kofar closet din dake dakin nashi ya bude ya shiga sannan ya danna wani madanni ga mamakina kofa naga tana budewa,
shiga yayi sai gashi a cikin wani daki duhun daya rufe dakin ne yasa banyi saurin gane ko inane wajen ba,
Da wayar hannun shi yayi amfani wajen haska dakin harya isa inda gadon dakin yake, gefen side drawer yaje ya kunna lamp sannan haske ya haska dakin duk da hasken bamai yawa bane bai hanashi hango kyakyawar fuskar masoyiyar nashi ba dake baccin ta hankali kwance.
Gefen gadon ya karasa ya zauna sannan ya mika hannun shi ya sauke bargon data rufe jikinta dashi zuwa kasan cikin ta ya maida bargon sannan yayi amfani da hannun shi guda wajen gyara mata gashinta da suka fita a cikin hulan dake kanta daya zame duk da bawai hulan ya cire bane Amma gashin tadai kusan rabi yana waje,
Cigaba da shafa fuskarta yayi a hankali har zuwa kan kananun lips dinta da suke nan fresh,
dukawa yayi a saman kanta saida ya manna mata kiss a goshi sannan ya sauko da bakin shi kasa zuwa dai² bakinta yana daura bakin shi a nata ita kuma ta bude idanuwanta suka fada cikin nashi ya kuwa riketa gam da idanuwan shi yana cigaba da kissing dinta a yunwace, motsawa ta farayi alaman tana son tashi, dagowa yayi daga jikinta yana marai²ce fuskar shi, "Yanzun fisabilillah kissing din ma bazanyi shi hankali kwance ba,
to tashi muje falo su musty da sadeeq suna jiran ki in mun dawo sai mu daura a inda muka tsaya dan yau No gyangyadi!
No bacci! Yarinya zatayi kwanan bautan Aure..........."
Gyara kwanciyar ta tayi "Allah ni bacci nikeji" ta fada tana Kara jan bargon rike bargon yayi,
"wai ta ina ka shigo?" Ta tambaya tana tashi zaune,
" ke to miye nufin ki? Ai wai Kenan nufin ki kin rufemin kofa ne in kwana a dakina ko me?
Kedai a jiki gashi kin girma amma har yanzun yarinta ne cike da kanki ai dai na fada miki ba bacci koh?
Wallahi in baki sauko ba daukarki zanyi Dan allah sai kinje" ya fada yana dauko mata hijab din da tayi sallah dazun, haka nan dai ta sauko tana tura baki rikota yayi yadan rungumota ta gefen kafadar shi,
Kallonta yayi da gafen idon shi
"waike nima zaki rufema kofa Dan kin gama raina nikoh?"
Tura baki tayi ba tareda ta bashi amsa ba,
"Da kyau"ya fada shima yana kauda kai,
"to kayi hakuri" ita kuma tace,
shareta yayi bai amsa taba,
"Kayi hakuri Dan allah," ta k'ara fada
"ki rike hakurin ki dan ke zanba hakurin anjima kad'an dan kinsan dai yau dagani saike koh ?"ya fada yana dage mata giraren shi biyu da wani munafukin murmushi a fuskar shi,
"ko bazaki sha sweet ba? halshen shi ya fidda daga cikin bakin shi yana dan karkada shi,
"zaki sha koh?" Ya kara tambaya yana tsareta da idanuwan shi da suka fara kankancewa,
Kauda kai tayi tana murmushi
" Yauwa yar kanwata ai nasan bazaki ki shaba koh? "
Ya kara fada yana mai k'ara rungumota sosai zuwa cikin jikin shi ya sunbace ta a goshi
"ina fa sonki da yawa yarinyar nan kinga yau ko bugun da zuciyata keyi in kina kusa dani ya ragu," ya fada yana mata hararar wasa,
Kara langwabewa tayi a jikin shi domin wallahi duk wata gaba dake jikinta saida ta mace a wannan lokacin.
"Yarinya Ai kema kin san nayi shekaru ina taraki dan haka yauce ranar kwasan adashe ki gode Allah yau din babbar ranace a gareni dan haka zan dan sassauta miki kad'an nasan kema zakiyi farin ciki ko Matataa... ?
Itadai bata k'ara samun zarafin magana ba domin ko idan dai har mai Jama'a yace zaiyi Abu tofa ko za'a mutu sai yayi,
Dan haka yau dai ta sadakar sai yanda allah yayi da ita kuma........ Karku manta tuzuru nefa,,,,,
Koda suka k'arasa falon mikewa tsaye su sadeeq sukayi,
Barka da fitowa amaryar mu suka fada a tare, rufe fuskata tayi da tafukan hannunta tana k'ok'arin janyewa daga jikin AK Amma gayen nan sai ma kara chachume ta yayi da gayya,
ina ruwan ba saban ba ko kuma ince Dan kauye yayi agogo,
Kujeran dake daura dasu 2 sitter ya masu masauki akak,
Yusuf ne ya bude taron da addu'a,
Sannan suka masu yan nasihohi bayan doguwar addu'ar da ko wannen su ya masu sannan suka kuma gabatar mata da wata jakar briefcase a matsayin kyauta daga abokanan su a gurguje dai sukayi masu sallama suka wuce,
" Ki jirani anan "
yace yana maiyi musu rakiya, gyara kwanciya tayi a kujeran dan wallahi har yanzun baccine cike da idonta baiji maba ya dawo bayan ya kulle kofa ya kashe fitulun dake kasan sannan ya hauro sama bai kulata ba ya jawo ledojin nan ya bubbudesu,
kayan ciye² ne a cikin su sai kayan sha a wata ledar daban
" tashi ki zauna muci abinci yunwa nikeji" ya fada yana zama a kasa saman kafet din dake malale a wajen,
saukowa itama tayi ledar da kaji ke ciki ya tura mata gabanta,
Waiyo Allah hajiya kaza tun kan ta sauko kamshin su ya tadomata da duk wata tsohuwar yunwar dake boye cikin hanjinta,
Kajin nan fa sunsha hadi sannan sun samu lafiyayyar gashi gasu luka² ko ina tsokace kwance sai kyalli suke, mukut fa hadiye miyau, itadai allah ya sani tana matukar so da kaunar Aunty kaza soyayya mai danko ne a tsakaninta da kaza Dan haka batajin zata iya wuce tayin ta.
Amma dai duk da haka batayi saurin bada kai ba saida ta latsa shi,
Duk wannan sakar zucin da take shi hankalin shi yana kan cin chips din shi da yikeyi, mika hannu tayi zan diba chips din ya janye
" haba Amarya ai yau ranar cin kazace Bari ki gani" ya fada yana janyo ledar kajin gaban shi,
"gashi ko kamar sun sanki da maitar kaza suka kwaso miki kici ki gaji,"
bata rai tayi
"ni bazanci kazar ba,"
" Iyeee" yace da dan karfi yana kallon ta
"me naji kince? "
" Cewa nayi bancin kazar"
dariya ya fashe dashi
" karya kikeyi wallahi haba An mata ni