Showing 147001 words to 150000 words out of 190771 words

Chapter 50 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1568

wajen cewa "nine zan biya mishi"
Musty Farouq da abokin Musty da kuma Ya Sarki wanda basu ma san da tsayuwar shi a wajen tun d'azun ba sune suka fad'i haka,

"Kai masha Allah kunji yan albarka to kai Adamu ai sai ka yanke mana sadakin auren yarka kaga masu jiran a fad'a su biya ma suna da yawa ashe, kaga dai alamun kowa nason wannan had'in kenan, oho wanda baiso bama dai In allah yaso sai anyi balle kuma rabon ciki da haihuwa basu bar kowa ba.


*Ummiee ce*✍🏼
[10/7, 10:40 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜
*BOOK 2*

*Page 45*


Bud'ama Sarki hanya sukayi ya shigo cikin falon shima tareda Ya Sheikh wanda shima dawowar shi gidan kenan dan tun safe ya fita a gidan zuwa gwargwaje inda yakai ma wani abokin shi ziyara dawowar shi gidan yayi dai dai da shima Sarki zai shigo dan haka sai kawai suka shigo gidan a tare,
koda suka iso kofar falon Sarki yaso ya juya ya koma shi Sheikh ne ya hanashi akan gara su isa suji me yake faruwa dan daga ganin taron ga kuma motocin da suka gani a farfajiyar gidan sun kasan abune mai mahimmanci ake tattaunawa a falon wanda ya had'a kan ahalin gidan,
suma kuma ai ahalin gidan ne dan haka su k'arasa kawai ayi dasu suma.

basu san abubuwan da aka tattauna akai daga farko ba jawaban da Hajiya ta gabatar daga k'arshe kawai sukaji dan haka sai shi Sarkin baiyi k'asa a gwuiwa ba dan dama yayi niyyar cewa in batun auren ya tashi shine zai shige ma AK gaba duk da cewa yar gida za'ayi ,
yanzun kuma da yaji bayanan Hajiya dole ya bata goyon baya kodan a kawo k'arshen rarrabuwa da kawunan ahalin yake son yi akan zancen auren Meenal d'in daya tashi a yau kamar tashin Bomb yake shirin tarwatsa kan ahali wanda babu wani yayi zaton haka,

Shifa bawai yana ma Salman bakin ciki bane danshi Salman d'in yana son matar dashi ya saka ba,
ah ah shi dai kawai cancanta yake dubawa kuma koba komai ita Meenal AK take so bai kamata a k'ara tauyeta akaro na biyu ba dan in akayi hakan itace zata cutu tunda su mazan dukan su koda ace sun aureta hakan bazai hana su k'ara wani auren baya itaba kenan dai duk wanda aka aurawa a tsakanin su Salman din ba'a mata adalci ba,

yama gode Allah da Allah yasa ya shigo gidan a dai dai dan shigowar shi dama yazo ne dan yaba Malam hak'uri akan abinda Salman yayi shi kuma yayi amfani da damar ya kawo zancen AK ga Malam to ashe ma Mai gayya mai aiki ta gaji da jiran gawon shanu ko kuma dai itama labarin jerin gwanon neman auren ne yaje kunnen ta shi yasa ta kwaso nata iyalan ta taho? Komai dai ya akayi shi hakan ya mishi dai dai yau yana bayan Hajiya tuk'uicin kyautar datayi mishi ne shima zai maida mata.

Shifa Sarki dalilin aika²r da Salman ya aikata da safen na zuwa wajen Malam kai tsaye bayan tun farko saida iyayen shi suka tsawatar mishi amma yayi kunnin uwar shegu dasu yayi gaban kanshine yasa shi barin komai dake gaban shi a yau d'in ya taho Zarian bayan Uwar gida ta kirashi ta labarta mishi abinda ake ciki,

Domin bayan da Salman ya bar wajen Malam gida ya koma dan ya riga ya k'una baya tsoron wuta dan haka yana zuwa kafin ma labarin ya koma kunnin su Uwar gida shi da kanshi yakai musu labarin ya kuma kafa musu hujja da cewa inhar mutanen tudun wada da suma suke matsayin iyayen Meenal ta gefen Mahaifiyar ta zasu iya ture komai daya faru a baya suba Sarki auren yarsu a karo na biyu,
to shima baiga dalilin da zai sa anan suce zasu hana shi auren Meenal ba tunda dai shi yace yaji ya gani yana sonta,

dan haka tunda su sun kasa tambayo mishi shi yakai kanshi kuma su sani babu abinda zai hana shi auren Meenal inhar ta amsa tana son shi yasan Malam zai aura mata shine dan koba komai yafi su Aliyu da Hashim kwarin gwuiwa koba komai a cikin su shine Saurayi yasan Malam bazai bata mai mata ba,

Fad'a sosai Malam Sulaiman da Uwar gida suka rufe shi dashi akan me zai aikata haka amma bai saurare suba sai ma ficewa da yayi yabar gidan kuma a yau basai gobe ba zai k'ara komawa wajen Meenal su daddale kafin Malam ya nemeta domin jin ta bakin ta,

K'ananan surutan da gidan Malam Sulaiman din ya d'auka ne yasa ita Uwar gida ta kira Sarki a waya dan gara yazo ya tsawata ma Salman d'in dan ita dai bata san da wanne zataji ba da surutun kishiyoyi da facalolin ta keyi akan maganar ko kuma da iskancin da Salman din ya tsiro musu dashi na k'in jin maganar su,

Itama fa bawai tana k'in auren bane, ah ah tadai san cewa ko kowa zaiso auren tofa bai zama lallai malam yayi murna da had'in auren ba kilama laifinta zai k'ara gani ko kuma yace itace ma ta tura mishi Salman d'in,

tunda itace dai tayi tsaye aka ba Sarki Meenal ga kuma abinda ya biyo baya yanzun kuma ace Salman wannan ai laifinta kawai Salman din yake son Malam ya cigaba da gani wallahi.

Sarki bai zauna ba sai da ya k'arasa har gaban kujerar da Hajiya take bayan sun mik'a gaisuwar su ga mutanen da suka tarar a cikin falon shi Sheikh a bakin k'ofa su Sa'eed suka gyara mishi ya zauna anan ne kuma yake tambayar su
"me yake faruwa ne? "
su kuma suka d'an labarta mishi komai a gajarce,

Sarki ko hannu yasa a cikin aljihu duk wata takardar Naira dake jikin shi sai da ya zubeta a gaban Hajiya tundaga kan yan dubu zuwa k'ananan canjin dako shi bai san nawa ne a dadin kud'in ba,
Yana gama zube mata su ya koma da baya shima can dai gefen da su yaran gida suke Abdul ne ya tashi a inda yake yaba Sarki wajen ya zauna,
Tun sarki bai kai ga zama ba Musty da Kamal suma suka mik'e yanda Sarki yayi ma aljihunan shi kwal haka suma sukaje suka zazzage nasu nauyin aljihun a gaban Hajiya wacce take ta faman washe baki ranta fess sai albarkha take sanya musu,

Malam ko a lokacin idan ka mishi kallo d'aya bazakayi marmarin k'arawa ba saboda ya d'aure fuska sam babu alamun fara'a ido kawai yasa yana kallon ikon Allah,
Dan wallahi yasani sarai cewa da biyu Hajiya tayo mishi gangami saboda yace wani abunda bai dace ba a gaban sirikai girman shi ya zube,
wai shi za'a biyo har cikin d'akin shi a nuna mishi isa akan Yar da ubanta ma a k'ark'ashin ikon shi yake, wallahi da yasan haka ne zai faru a yau da ba sanarwar bada auren Meenal d'in ga Sheikh zaiyi a daren jiya ba auren kawai zai d'aura in yaso sai yaga uban da zai kashe auren.

Abun mamaki sai gashi harda ya Sheikh shima yabi ayari cikin masu juye tattalin arzikin aljihun su a gaban Hajiya kafin ka an kara kud'i sun taru domin kaf d'in yara mazan dake falon sai da suka juye aljifan su bayan sun gama kuma haka suma iyayen Maza sukabi ayari, shi dai Malam kallon ikon Allah kawai yakeyi,
Alhaji hamza ne ya fara fidda nashi kudad'en sai Alhaji Musa,
Shidai Baba Adamu cewa yayi yaga alamun yaron nasu d'an gatane dan haka bazai sa musu ko sisi ba dan kud'in shi tattalawa zaiyi ya Siyama Meenal din gadon bacci,

Farantin da aka d'aura ruwan da Abdul ya kawo musu Hajiya ta juye kayan cikin farantin a k'asa,
Sai da tasa gyalen ta ta goge farantin kafin ta kwashe kud'ad'en nan kaf ta zuba a farantin ta k'arasa gaban Malam ta ajiye,

"To Malam Almu ga sadakin takwarata nan yan uwan ta sun biya,
Nasan dai ko kud'in zaku yanke bazaku yanke wanda zaikai adadin wannan ba dan haka gashi nan shima in bai wadatar ba zamu k'aro ninkin adadin su saboda ta cancanta"

Mai da kallon ta ga sauran jama'ar falon tayi saida ta k'arewa kowa kallon tsaf kafin ta tsaida duban ta akan Sheikh,

"Malam Naseer"
Ta kira sunan shi a sanyaye,
"Na'am Hajiya" shi kuma ya amsa mata fuskar shi a sake,

"Kai kuma bawan Allah daga zuwa kaima sai kabi ayarin masu tarbace? Tun baka san ko sadakin wa ake had'awa ba, to da fari dai hakuri zan baka kayi hak'uri nazo nayi maka shigar sauri ina fatan bazaka kullace ni a cikin ranka ba?"

"Ah ah Hajiya me yayi zafi da harni zan k'ullace ki kuma?"

"To dai batun in tsaya yi maka kwana² ma duk bata taso ba,
Zanyi magana ne akan sanarwar da Malam ya bada jiya cewa ya baka mata shin kai kasan wacece aka baka ne?"

Sai da yakai duban shi kan Malam kafin ya amsa mata da cewa
"ah ah Hajiya ban sani ba sai dai koma wacece ina farin ciki zan kumayi maraba da shigowar ta cikin ruyuwata tunda har kyautar ta hannun Baba Malam ya fito yasan na cancanta shi yasa ya bani na kuma gode ubangiji Allah ya k'ara girma yasa a gama lafiya"

"Ameen..... "
D'aukakin jam'ar dake cikin falon suka amsa gaba d'aya,
Ita kuma Hajiya sai taci gaba da magana bayan ta amsa da Ameen din itama,

"Masha Allah lallai ka cancanci a baka mata ako ina ne kuwa Naseer, To a jiya dai shi Baban naku ya sanarda cewa ya baka Meenal sai dai sunan tane bai k'ira acan d'in ba dalilin rashin kiran sunan nata a jiyan kuma wannan shiya barma kanshi sani,
Amma mu dai ya fad'a mana cewa itace ya baka a wannan zaman da mukeyi,
Ba bayarda ita din da yayi gareka ne damuwar ba, ah ah damuwar shine daya k'ara d'aukar ta ya bayar a karo na biyu ba tareda yayi shawara da kowa ba bayan ita din ai kowa yasan cewa tana da uwa a raye koba komai in ba'aji ra'ayin ita Yarinyar ba tunda ana ganin cewa an isa da ita to ita kuma uwarta fa?,
ko har yanzun dai ita uwa nata alaqar kawai na haihuwa ne amma in anzo batun hukunci akan abinda ta haifan shikenan sai kuma a nuna mata cewa bata da ikon ko isar da za'a iya jin ta bakin ta?,
Humm koda yike ba wannan maganar nike son fad'a maka ba kana jina koh?"
Ta tambaya tana kallon Sheikh d'in,

Baba Usman ne yayi saurin tarar numfashin Hajiyar jin da yayi ta fara sauka akan layi dan shidai bazai so ta raba halin ta a falon kafin subar gidan ba dan haka sai yayi saurin d'aurama Sheikh da cewa,

"Kayi Hakuri Naseer shi Baban ku bai san da batun neman da d'an uwan ku yakema ita Meenal din ba nasan shi yasa yayi kwad'ayin baka ita saboda cancantar ka, sai dai mu kuma tun kwanaki muka gabatar ma Baban ku Adamu da batun neman shi kuma sai Allah bai bashi ikon kawo ma Malam zancen ba sai yau.
zuwar mune kuma Malam yake sheda mana cewa kai yaba Meenal duk da cewa daga safen yau zuwa yanzun bayan kai daya ba a jiya mu mune mutane na biyar da mukazo neman auren ta a yau,
Bamu san abinda ke cikin zuciyar ka akan ita Yarinyar ba barin ma kuma daya zamana Malam bai kira suna ba tun jiyan sai dai mu muna da tabbacin cewa ita da d'an uwan ta suna son junan su shi yasa suka had'a kansu k'arewa ma itace ta buk'aci shi d'an uwan nata ya kawo zancen nan gaban iyayen ta shi kuma ya wakilta mu a matsayin mu na iyayen shi maza,
muna fatan koda ma ace kana son ta to zaka iya sadaukar da son da kake mata dan ganin ta samu abinda take so a wannan karon?"

Tunda Baba Usman ya fara magana kan Sheikh yake k'asa domin idanuwar kowa a kanshi yake kowa so yake yaji mai zaice kuma,

Shiko a zuciyar shi mamaki kawai yakeyi, shifa wallahi koda Malam ya bada sanarwar tun jiya bai kawo kowa a cikin zuciyar shiba sai Fauxieyerh saboda kaf gidan kowa yasan da cewa yafi shakuwa da kuma sakewa da ita,
dan haka shi yasa koda suka dawo gida a jiyan bai nemi jin ta bakin Malam din ba dan shi bai tab'a kawo zancen Meenal a cikin kanshi ba,
Jama'a shi wani tsautsayi ne zai sa shi auren wancan Yarinyar data iya cinye maza da kalaman bakin ta? Yarinyar dazai ce ta koma tasa hijab ita kuma tabi ta wani k'ofar ta fice daga gidan ba tareda ta sanya hijab din ba,
Ah ah wallahi shikam Meenal tafi k'arfin shi garama da akayi walkiya inba haka ba da haka zai saki baki shi a ranshi yana tsammanin Fauxieyerh a gefe kuma ana shirin aura mishi Meenal,
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke kafin ya d'ago kanshi yana kallon Malam yace

"Baba dama ba Fauxieyerh bace Yarinyar daka bada sanarwar zaka bani auren ta a jiya?"

Dagowa shima Malam yayi fuska d'aure yace

" Meenal ce Yarinyar dana sanar da cewa na baka a jiya kuma har yanzun ban canza ra'ayi ba Naseer kuma nasan daga kai har ita babu wanda zaiyi yunkurin bijire min a cikin ku,
idan ma baka son ta a yanzun ina mai tabbatar maka da cewa tana da kyawawan halayen da idan ka zauna da ita zaka sota saboda su,
kamar yanda nake da yakini kan cewa itama bazata k'ika ba,
ina fatan kuma ko yanzun bazaka watsa min k'asa a ido ba dan na riga nayi niyyar baka ita tuntuni k'arewa ma har nayi sanarwa jama'a sunji dan haka babu wanda zai sa in sauya magana a cikin ku"

Shiru falon ya d'auka kowa yana jimami da mamakin kalaman malam Wannan karfin hali har ina! ,
Hajiya ko wani irin kallon wasa ma kake yi Almu take aika ma Malam din,

Ganin haka sai shima Sheikh d'in yaci gaba da cewa
"Amma Baba Meenal ita d'in tana da wanda take so kuma nima Fauxieyerh nike so in har za'a canza min da ita zanfi yin farin ciki da hakan ayi hak'uri a duba al'amarin nan wallahi ban tab'ajin soyayyar Meenal soyyaya irin ta aure a cikin zuciyata ba balle har inyi kwad'ayin auren ta....."

"Yi shiru abin ka d'an nan aika gama magana, Fauxieyerh dai kace kana so koh?"
hajiya ta tambaya,
Bata jira amsar shiba taci gaba da cewa,

"Ni nan dai nice na haifi Jidda ita Uwar su Meenal da Fauxieyerh dama sauran yayyen su dake zaune a gefen ka dan haka na baka Fauxieyerh, tunda ko nace na baka nasan ko uban Fauxieyerh Mukhtar bazai kalli idona yace zai k'alubalance niba,"

Harar gefen ido ta aikama Malam tana fatan Allah yasa ya kulata, wallahi silleshi zatayi tass dan ta gaji da halin shi haka nan,
Sai dai shima yau kamar yasan abinda ta shiryo sai ya kama kanshi,
Ita kuma sai taci gaba da magana
"Adamu ka shirya amsar ma d'anku auren Jikata Fauxieyerh ayau kamar yanda zaku bamu auren Yarku Meenal ayau ko baku shirya ba? In kun shirya ga uban Fauxieyerh nan a gefen ka nasan ko Mukhtar yana yana raye koya mutu tsaf zai iya wakilta yayyen matar shi wajen aurar da yaran shi mata dan haka ni a matsayina na uwa na wakilceshi na wakilta Usman ya amshi auren Fauxieyerh"
Yanda Hajiya tasha kunu take faman bada umarni zakayi zaton ko gidanta a kaxo bawai itace taje gidan sirikai ba, ko mantawa tayi ne oho🤔

Kai jama'a Hajiya yar bala'ice wallahi, inba karfin hali ba kizo cikin gidan iyayen yarinya kuma kice wai zaki basu auren ta😠,

"Na shirya Hajiya indai za'a bamu ai bazamu k'i amsa ba" Baba Adamu ya amsa mata,

Malam fa bai tab'a sanin cewa da ranshi da lafiyar shi har za'a iya had'a kai da ADamu aci mishi amana ba sai yau, to cin amana mana tunda gashi dai yau shi Adamu ya juyama baya ya koma tsagin dangin matar kanin shi,
Domin dai abin mamaki yana zaune Hajiya tace wai a raba kayan da suka kawo kashi biyu ta sadaukar da kaso d'aya ga Adamu tukuicin kyautar da zai basu na auren takwarar ta sannan ta nad'a Abba Ahmad a matsayin mai bada auren Fauxieyerh kuma kaf falon nan aka rasa wanda zai iya takama Hajiya burki,
haka aka rabe kayan biyu kud'in sadak'in da aka had'a ma tasa aka k'irga aka raba biyu, sai da komai ya kammala kafin tace to kowa ya kira yan uwan shi wad'anda suke kusa idan suna da halin da zasu iso a gabatar da d'aurin auren a gaban idanun su dan sallan da za'a gabatar na la'asar a masallacin su Baba Malam d'in take so ana idar da sallah a gabatar da d'aurin auren,

Auren kawai take so a d'aura yau daga baya sai ayi duk sauran tsare tsaren da za'ayi na tarewa da kuma taron biki,
Malam dai ganin babu wanda ya k'arabi ta kanshi sai kawai ya tashi ya shige cikin d'akin shi yabar musu falon suci kansu ,

Suko nan fa suka yunkura aka fara kiraye kirayen waya ana sanarda zancen d'aurin auren, dan sai a lokacin ne kuma Baba Adamu ya kira mutanen abuja wato can gidan su Sheikh din ya shaida musu halin da ake ciki suma kuma sun bada goyon baya akan cewa gobe zasu shigo garin dan k sun taso yau bazasu iso akan lokaci ba, shima kuma Abban su Sheikh din ya kira mutanen shi dake nan Zaria ya sanar dasu zancen auren dan su wakilce shi,
Abba Ahmad da Baba Usman sunyi² da Hajiya akan tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login