Showing 48001 words to 51000 words out of 190771 words
sai ki tashi ki koma cikin makewayin kiyo wanka koh, tunda kinsan dai muna da wajen zuwa da safen nan da gangan kikak'i yo wankan tun d'azun ai duk dai salon mu b'ata lokaci ne na sani"
"Hajiya dan Allah ki barni da batun wankan asuban nan sai kace wata wacce ta kwana cikin fitsari, naga dai ai duk sonki da sammako bazakice mu kama hanya tun yanzun zuwa can gidan ba, duk da dai gidan mutuwa ne amma na tabbata ko su yan gidan ba kowane ya tashi bacci a yanzun ba,
Dan Allah ki koma ki kwanta ki hutama rayuwar ki ki bari har gari yayi haske idan muka karya anjima sai mu koma can d'in ni wallahi bacci ma nike ji"
Jin hajiya na shirin fara jininin ta da bata gajiya sai kawai ta tashi tama fice daga d'akin ko hijabin jikin ta bata samu damar cirewa ba ta koma falon ta kunna TV tayi kwance a doguwar kujera tana kallo,
Daga kallo har bacci ya d'auketa ba tareda ta ankara ba, ita kuma Hajiya jin shiru bata dawo cikin d'akin ba gashi ita kuma ta fara jin yunwa dan dama ita idan har tana gida to kari sau biyu ta keyi inta tashi da safe Zata nemi abinci in hantsi ya daga ma sai ta k'ara wani karin dan haka sai ta fito daga ciki tana tambayar Meenal,
"Ke Meenal ina abincin da Abdul ya siyo mana ne jiya, tashi ki dindumo min shi in samu inci kafin juwa ya fara kamani,
Ai matsalar Kaje bak'on waje kenan wallahi barin ma ace gidan babu macen aure, dan nasan gidan nan bai zama lallai ma a samu kayan abinci a cikin shiba tunda shidai gwanin nasan ko ruwan zafi k'ila sai an tsare shi da bakin bindiga kafin ya iya tafasa su asha tea dasu,"
Muryar Hajiyar shine ya tada ta daga baccin daya d'an fizgeta akan kujerar,
"Oh wai ke ashe ma bacci kike duk wannan surutun da niketa yi ni d'aya?"
"Me kike so Hajiya?"
Meenal ta tambaya.
"Me nike so kuwa banda abunda zan saka a bakin salati, tashi ki gani dan Allah ki shiga kitchen din nan ki had'omin abunda zanci kafin in farajin juwa na kamani"
Mikewa tayi dan tasan halin Hajiya tunda har ta biyota zuwa falon to zaman lafiyan ta kawai tayi abunda tace d'in,
Dan haka tana shiga kitchen din ta d'aura ruwan zafi tea ta fara h'adawa ta kaima Hajiyar sannan ta koma taci gaba da gyara sauran kaza kifi da chips din da suka saka a pridge jiya,
Kayan fruit din data gani shake da fridge din duk sunyi k'ank'ara su da samu ta babballo ka karfin tsiya ta d'iba wadanda take muradi ta zuba su blander ta nika su ta zuba a cikin madaidaicin jug ta had'o da abincin ta fito daga kitchen din,
Jera abincin tayi a kasan kafet din dake tsakiyar falon bayan ta matsar da center table din wajen can gefe,
"Hajiya ki sauko ga abincin bari inyi wanko baki"
"Ai ba iya baki zaki wanke ba ki had'o harda wanka ma na dai fad'a miki ina son mu fita da wuri shina wannan daga zuwa masallaci shiru har yanzun bai shigo ba nasan dai zuwa yanzun ai ko limamin masallacin tuni ya koma gida, in kina fitowa ki fitomin da wayata in kirashi, kafin yace min wani wajen ya wuce ya manta damu a cikin gidan"
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[9/2, 10:06 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 18*
Hajiya bata gama sauke maganar data d'auka ba AK ya fad'o cikin falon da d'an gudu gudu wanda alamu suka nuna cewa daga wajen gudun ya dawo, baiyi tsammanin ganin kowa zaune a falon ba dan haka ma ko sallamar da yayi k'asa sosai yayita wanda iya shi da yayi abunshi shi yasan yayin,
Turus yayi a tsakiyar falon ya tsaya yana bin su da kallo, kamar wani wanda ya mance da wanzuwar su a gida, dan shi ya fad'o ne kawai abunshi baiyi zaton zai samu wani zaune a falon ba,
ya manta shaf cewa Hajiya bata bak'unta duk inda taje sakewa takeyi ta bararraje abinta balle kuma gidan shi, ga al'adarta na yin karin kumallo sau biyu ko yanzun yasan fitowar nan nata baya rasa nasaba da neman abunda zata fara karin kumallon farkon dashi.
"Ka tsaya daga can kana k'are mana kallo kamar wasu sabbin halittun da baka saba gani ba, k'araso ciki mana sai wani bin mutane kake da kallo kamar wanda yayo makuwa, ko ka manta cewa mutane sun kwana a gidan ne tunda ka saba kwana ka tashi kai kad'ai a cikin Sashen uwa wani Dangin mayu, wato dan
haka shi yasa ka fad'o ko sallama babu to fisabilillahi mutum yana shiga waje ba sallama bama dole yayi ta rayuwa tareda shaidanun aljanu ba,
Ke kuma ki fara shiga kitchen din nan ki dubamin duk wani abun da kika san babu na kayan abincin da zamu iya buk'atar amfani dashi kafin mu tafi kizo kimin list din su yanzun nan ki bashi kafin mu fita, dan nidai bazan dunga wayar gari zuru zuru ina tunanin dame zanyi karin safe ba"
K'arasowa yayi ya samu waje daga gefen Hajiyar ya zauna,
"Barka da safe Hajiya ya bak'unta?"
"Barka ka dai, bak'unta kamar wata wacce taje wani bak'on wajen daban, gidan kafa nazo! "
"Ina kwana Ya'ya"
Cewar Meenal daga tsayen da take tana shirin zuwa kitchen duba abinda Hajiya ta Sanya ta,
"Lafiya lau kin tashi lafiya, zoki zauna kiyi karin ki na riga nasa Mansoor yayi cefane tun jiya abubuwan da babu anjima idan na fita zan siyo"
Canza hanya tayi ta wuce d'akin da suka sauka, bakin ta kawai ta wanke sai dogon hijjabin dake jikin data cire ta fito daga d'akin,
Tare suka zauna dukan su Ukun suka gabatar da karin safen dan shima AK da wuri yake son fita daga gidan akwai inda zashi da safen,
Duk jininin da Hajiya ta dungayi akan su samu su fita da wuri hakan bai samu ba, domin shiririta Meenal ta dunga yi kawai dan dai suja lokaci kafin su fitan, karfe 8 da kusan rabi suka fito harabar gidan, Mansoor ne ya k'araso ya gaisheda Hajiya itama Meenal ta gaishe shi,
"Hajiya ai ban san fitan wuri zakuyi ba tun d'azun mai d'akina Hajara keson ta shigo ku gaisa ni kuma nace mata baku riga kun tashi bacci ba, dan Allah da kun d'an koma daga ciki bari in mata magana ta fito ku gaisa kafin ku fitan dan tun d'azun take kitchen tana had'a muku karin kumallo gashi kuma kun fito"
"To haka akayi ai nayi zaton kai kad'ai ne a gidan ashe harda iyali gareka masha Allah gaskiya kayi kyan kai, ai aure daraja ne dashi wallahi, ina dalili mutum yayi ta rayuwa shi kad'ai kwallin kwal ba mace bawai kuma dan bashi da halin auren ba,
ba damuwa kana iya mata magana sai ta fito mu gaisa tunda kaga mudai iya kwana ne kawai zai dunga maidomu gidan kuma nasan a sanda zamu shigo gidan ba mamaki tayi bacci, batun kari kuma ai da baka wahalshe taba wallahi dan yanzun muka gama karyawa a ciki dan dama tun jiyan da guzurin mu muka shigo gidan,kasan gidan da babu mace gara mutum yaje da guzuri koda ko garin kwaki ne atoh,
wucewa yayi yana amsa ma Hajiya da cewa "to Hajiya bari dai in kiratan"
Basu d'auki lokaci mai tsayi ba suka fito shida matar nashi daya kira da suna Hajara sai yaran su biyu mata Babban mai wayan duka bazata haura shekara hud'u ba sai k'aramar dake hannun uwar wacce ita ma dai batayi shekaru biyu ba, shi kuma Mansoor din hannun shi rik'e da basket mai murfi wanda cikin shi ke d'auke da wani madaidaicin jug mai had'e da kananun kofuna guda uku sai wasu madai daitan kuloli guda uku suma,
Har k'asa matar nashi ta duk'a ta gaida Hajiya kafin ta maida gaisuwar kan Mai Jama'a cike da girmama wa suma suka amsa mata a mutunce, k'aramar yarinyar dake hannun matar meenal ta amsa tana murmushi bayan sun gaisa da Maman yaran,
"Kuyi hakuri Hajiya ban san cewa da wurwuri haka zaku fita ba shi yasa ban lek'o tun d'azun mun gaisa ba dan Allah ku koma ku karya kafin ku fita tunda ga abun karin naku ya kammala"
"Kaiya bayan na riga da na fadama me gidan ki cewa mun karya kuma shine sai da ya k'ara tattago kayan abincin ya fito dashi, ya za'ayi haka daga zuwan mu kuma zaku daura ma kanku dawainiya, Meenal amsa kayan kikai mota in mun isa can d'in maci dan bazataji dad'i ba idan bamu amsa ba, angode kunji Allah dai ya muku albarkha,
Sai da suka raka su har bakin motar suka shiga sannan matar ta koma ciki ita da yaran,
AK dake gefe yana amsa waya ne ya zagayo ta gefen da Meenal ke zaune,
Key din motar dake rik'e a hannun shi ya mik'a mata ta window,
"fito ki koma wancan motar ki biyoni a baya dan bai zama lallai anjima in iya zuwa d'auko kuba dan ina da uzurori masu yawa da zanyi"
"To ni ai ba sani kan hanyoyin garin nan nayi ba"
"Eh ai saboda sanin hakan shi yasa zan miki jagora a yanzun ta yanda bazaki sha wahalar gane hanyar dawowa nan d'in ba in dare yayi,"
Bud'e mata murfin motar yayi sai ya mata alamar ta fito da hannu,
"To in ya zama haka kabar mana wannan d'in mana!"
"Ah ah waccan d'in dai zaki hau ita tafi dacewa dake koba kin fison ki hau Babbar Mota ba?,"
ya tambaya yana nuna mata motar da yatsar shi,
"To ai nidai in haka ne ai sai dai a barni in zab'a tunda ai da gangan mutum ya hanani zuwa da tawa motar"
"Oh baki gode ba kenan da na miki tayin wannan d'in?"
"Nidai bance ban gode ba kawai dai ni kayan aro ne bana so, so kake in dunga hawa wannan d'in sai na fara jin dadin hawan ta na kwana biyu sai in tafi in barta!"
"Wa yace miki kayana ba naki bane?, bari in kin dawo sai ki duba duk motar da kike so anan d'in ki d'auka ni kuma na baki ita duniya da lahira"
"Da gaske๐ณ?"
"Da gaske mana!, na saba yin wasa dake ne dama ko na tab'a miki k'arya ne?"
"Ah ah amma nidai bana so mutum yamin kyautar koma d'aka kayi kukane, in kasan kana son motar ka kabar shi kawai wallahi tunda nidai ban rok'eka ba"
Dariya ma ta bashi,wai shine dan yayi kyautar mota take cema karya mata kyautar koma d'aka kayi kuka,
kai jam'a yarinyar nan ba'a tab'a iya mata wallahi Mansoor ya kira ya bashi key din motar da Hajiya ke ciki,
"Kaja motar nan ka biyoni a baya"
"To Yallabai"
Da gudu ta k'arasa wajen motar tana zagayata,
Motar fa ta had'u gaskiya dan motar kai da gani kasan ba kananan kud'ad'e aka salwantar kafin a mallaketa ba gata fara tass sab'anin wancan natan da Sarki ba bata da take bak'a wuluk ita kuma,
"Kai gaskiya ni d'in nan fa mai sa'a ce wallahi na samu kyautar motoci har biyu a cikin watanni kad'an, kuma nadai fad'a maka Allah karma kazo zuwa gaba ka wani ce in dawo maka da motar ka, allah kuwa naci halak,"
Baya ta tayi da gudu ta koma wajen Hajiya bud'e kofar gefen da hajiyar ke zaune tayi cike da jin dad'i daya ke bayyane akan fuskarta take cewa,
"Hajiya fito ki gani yauma na samu kyautar wata motar, taubashi ya bani kyautar mota shima, wuuuu ni yar gata mai yayye da yawa, oh Allah kaci gaba da lullub'e mu da arzikin da zamu amfana duniya da lahira Ameen"
Fitowa Hajiya tayi tana cewa,
"Ban gane ba wai anyi yamma da kare,
Mota dai ta hawa irin wannan itace shi Abdul din ya baki kyautar ta da sanyin safen nan?" Hajiya ta fada tana jin jina wai kyautar motar manyan kudade Ak yayi da safen nan,
Kamo hannun Hajiyar tayi tana dariyar jin dad'i tace,
"eh mana Hajiya gata ma kina gani a gaban ki kuwa, wallahi gashi nan a gaban ki ai sai ki tambaye shi idan k'arya nike miki, Taubashi "
sai kuma ta rufe baki๐,
"Au Ya AK dan Allah ba yanzun ka bani makulin motar kace kuma ka bani motar duka kyauta ba?, itafa Hajiya bata yarda ba ka fad'a mata da kanka"
Kankance idanun ta Hajiya tayi tana kallon AK d'in dake gefe jingine da motar ya rungume hannayen shi a k'irji Meenal kawai yake bi da kallo shima yana murmushin ganin yanda take ta farin ciki dan kawai ya mata kyautar mota,
Matsawa kusa dashi Hajiya tayi, sai da takai hannunta kan goshin shi ta tab'a, jin babu zafi a wajen sai ta cire ta maida hannun kan wuyan shi,
"Kai Abdul zazzabin safe ne ke damun ka ko koh a ah iskokine suka bugeka ka kama kyautar mota da sanyin safen nan?"
Meenal ce ta amsa da cewa
"haba Hajiya iskoki kuma dan kawai ya bani kyautar mota, to shi ya Sarki daya bani wancan Motar kyauta mai yasa bakice shima iskokine suka buge shin ba? "
Ta tambaya tana tura baki,
"Yo shi wancan tsohon mijin naki ai toshiyar bakine yayi miki, wannan kuma babu kare bin damo in kyautar ce fisabilillahi aini ya dace ya bawa ita bake ba, tun yaushe nike cewa ya siyamin tikiti inje umara daga nan in kaima iyayen shi ziyara yana k'i kawai dan baya so idan naje in ma uban shi batun auren da yak'iyi, amma tsabar son kai nida kullum nike d'awainiya dashi bai canzamin motar hawa ba sai ke da yaushe yaushe ma kuka fara shiri a tsakanin ku,rabon ma da yamin kyautar zunzurutu tsabar kud'i harna manta, kullum sai dai ya kwaso kayan abinci yazo ya jibge min uwa wata sauran yunwa,
In ma ba munafunci ba ina ce nan kullum da ke dashi d'in had'uwa goma rabuwa goma saina shiga tsakanin ku kullum sai kun raba hali kamar wasu kaji, amma daga jiya zuwa yau saboda bak'in munafurci kun wani had'e kai kun dunkule uwa wasu kashin awaki"
Dariya ma Hajiya taba Meenal,
"Hajiya kamar wasu kashin awaki fa kikace, to dan Allah wai dama kinfi so kiga muna fad'ane kullum, nidai wallahi na yafe mishi duka laifukan da yayi mun na baya harda na gaba ma, kuma dama can ai yarinta ne yasa muke fad'an yanzun kuma ni na girma, kuma tsakani da Allah ai kece kikace bana a can Saudiya din zamuyi azumi kuma ma ai bakice min kin mishi magana ya biya miki kudin jirgi yakiya ba,"
Juyawa gefen AK tayi,
"To kai yaya me yasa baka biya mata kud'in jirgi ta tafi can d'inba?"
"Oh so kike ta tafi ke kuma sai ki tsaya a gidan ke kad'ai?"
"Eh kuma fa haka ne Hajiya ki bari kawai sai lokacin da kikace sai ya biya mana mu tafi taren koh Ya'ya"
"Oh haka ka zama sai abunda tace maka shi zakayi kuma?
To ai babu
laifi mota koh Allah yasa alkhairi duniya dai Allah yasa nima na haifi yaran da suke tsaye cak wajen ganin sun sharemin hawaye na, yau idan nace motoci kaza nike so sai na zab'i wadanda za'a cikamin gida dasu, dan haka Allah ya Sanya alkhairi a kashe lafiya"
"Ameen"
meenal ta amsa dashi taja hannun Hajiyar ta maidata cikin motar AK din ta rufe mata motar sannan itama ta koma nata motar da tuni AK ya shige ciki ya zauna a gefen mai zaman banza, dan haka sai ta zaga gefen direba itama ta zauna taja motar,
ita ta fara fita daga gidan kafin shima Mansoor yabi bayan su,
sai da suka dakace shi ya rufe gate d'in gidan sannan suka kama hanya, suna tafe AK na nuna mata inda zata bi har suka isa gidan rasuwar,
Ita ko Hajiya mamaki ne yake neman sumar da ita a bayan mota ita d'aya, dai ita dai rainin wayau kawai take gani sanka sanka daga jiya zuwa yau a wajen yaran na, oh wato shi nashi salon soyayyar kenan, yafi k'arfin ya fito ya furta wato siye zuciyar ta yake son da hidimar da yake mata ko miye nufin shi,
"aiko ni nan nice maganin shi wallahi"
"Magana kikeyi Hajiya?"
Mansoor ya tambaya.
"Ah ah Malam Mansoor cigaba da tuk'inka kawai"
Yauma kamar jiya a kofar gidan dukan su suka nemi waje faka,
"Nace to batun abincin sadaqa in akwai inda zan samu wadanda zanba aikin girkawa su kawo nan ina buk'ata"
Cewar Hajiya a yayinda AK ya bude mata kofar mota ta fito
"Abincin sadaqa kuma Hajiya?"
"Kwarai kuwa ko shi kenan dan munzo gaisuwa sai mu share waje mu zauna ana dafawa ana bamu muna cinyewa?",
"Ah ah Hajiya ba abunda nike nufi ba kenan, zan biya ta restaurant din da nike siyan abunci inyi magana dasu sai su kawo abincin ko zuwa da rana ne!"
"To hakan ma yayi Allah ya bada lada, ke kuma zaki fito daga cikin motar mu wuce ciki ko har yanzun baki gama karema motar kallo bane tukun?"
AK Bai bisu zuwa cikin gidan ba ya dai gaisa da mazan dake waje sai su Baba Adamu dake harabar gidan ya musu gaisuwa dan jiya da dare basu had'u da Baba Adamu da Baba Auta ba ya d'anyi zama na mintuna kad'an ya koma cikin motar shi Mansoor yaja suka juya.
Suma su Hajiya sai da suka tsaya suka gaisa dasu Baba Adamu dake harabar gidan dasu Farouq sannan suka wuce sashen Raheenat a can ma wani sabon gaisuwar sukayi kafin suka fito,
Mommy Hauwa ce tayi musu jagora yauma zuwa sauran sashen suma suka musu gaisuwa,
anci gaba da zaman makoki yayinda yan uwa da abokan arziki sukaci gaba da bulbulowa tako ina suna zuwa domin yin nasu gaisuwar suma,
da yawan wad'anda basu samu isowa tun jiyaba sune sukayi sammakon isowa yau d'in