Showing 162001 words to 165000 words out of 190771 words
hakan? wato tunda anyi mai wuyar an d'aura koh, Naga kema ai baki duba hakan ba tunda ai ba ko tausayi haka kika dunga Jan mana shi a kasa ko ce miki akayi bamu da labari saboda cin zalin an d'aura auren ma tuni amma bazaki bar mana shi ya huta ba amma ai karashen tuka tuki tik, yanzun kam komu ma zamu samu mu sarara tunda ya kauce a layi muma sai mu yunkuro allah yayi aure da mara kwabo,"
"Munafuki kace aure kake so shi yasa kake ta kame²"
Bai kulata ba dialing din number din Ya Abdul din yayi sai ya mika mata Wayar ,
karba tayi ganin kallon da anty fati ta ke mata ne yasa ta kai wayar kunne "Assalamu Alaikum" ya fada daga can gefen shi cikin sassanyar lafazi da kwantaciyar muryar shi da saida ya tsirga mata har cikin cikinta.
batayi tsammanin cewa tayi kewar muryar dama mai muryar kanshi ba sai yanzun dan a kalla yanzun kwana 2 kenan data toshe duk wata kafa da zai ganta ko yaji muryata gaskiya dai AK ya gama da ita wallahi,
fita su Hafees sukayi daga dakin suna hira shida Mom Abiey tasan kuma sunyi hakan ne saboda ta samu sakewar yin magana da Abdul din amsa sallamar tayi kamar yanda yayi itama din cike da kasalar data gaza boyuwa a cikin murya ta,
"Ammina"
Ya kira sunan ta
"uhmmm" ta amsa
" ina yini," ta gaidashi sai ya amsa da cewa
" lafiya lau ya akaji da jama'a?"
shiru tayi bata amsa mishi ba,
"Wife me yasa kike min haka ne? Yanzun fisabilillah abunda kikeyi kina kyautawa kenan? , Allah ne kadai yasan irin matsanan cin farin cikin dana shiga daga ranar laraba zuwa yau bayan tabbatuwar dauruwar igiyar aure a tsakanina da ke,
naso matuka ace na raba wannan farin cikin tare dake amma a dai dai lokacin ke kuma nike ta kiran wayar ki amma ko tausayi na bakiji ba kikaki daukar min waya bayan haka na tura miki text message shima ba amsa,
Wai dan allah me yasa kika daina sona ne yanzun? fushi dani kiyeyi akan maganar ranar nan? to miye laifina dan na jajirce wajen ganin na mallake ki dan ki zamo uwar yayana?
Ke din nan sheda ce akan ban taba soba sai akanki a kanki na san so idan dadi naji ko akasin hakan kinfi kowa sani,
amma abun mamaki wai saida aski yazo gaban goshi sannan kike kokarin juyamin baya me yasa? Shin ban cancanci in mallake ki bane kome? wallahi ina sonki³"
Saida ya maimaita cewa yana sonta sau uku kafin ya d'aura da cewa
"karki manta cewa karfin son da nike miki shi ya rikeni tsayin shekaru ba tareda na iya kallon wata diya a matsayin mace ba balle har inyi sha'awar kai kaina gareta,
akan hakan har wasu sun faramin kallon ko bani da lafiyar alkalami ne babu irin mummunar fassarar da ba'a munba duba da yanda su Musty ke mu'amala da yan mata amma ni duk yanda matan ke bina sam basa gabana,
Amma ko sau daya ban tabajin bacin raiba, to taya kike ganin yanzun zanyi wasa da damata in bari ki kara kubuce min a karo na uku kamar wanda akama baki inaa haba yarinya kema kinsan rashin ki a gareni yanzun sai dai a kirashi da ganganci".
gaskiya itama tasan tadan so ta tsaurara to amma ai mu mata dama dajan aji aka sanmu,
amma kalaman shi sunyi tasiri kwarai a zuciyarta har sunsa taji ban kyauta ba a yanda ta wofantar dashi na kwana biyu,.
"Yanzun fisabilillah da bance a kawo miki wayaba shi kenan koh? Niko Ammi?nidai kikeyi ma wasa da zuciya koh?"
" Kayi hakuri" tace,
shi kuma sai yace "da kyau nidai koh,"
"kayi hakuri" ta kara cewa,
"bazan karaba"
Shi kuma sai yace
"ya wuce kinci abinci? "Ya tambaya
gyada kai tayi kamar yana kallonta,
"ba kai nace ki dagamin ba ki bani amsa da baki"
"eh naci maman Abiey ta kawo min naci"
" kina inane haka?"
" Sashen baba,"
"to muma gamu a hanya zamu zo gidan yanzun,"
to tace,
" ki shirya kafin mu iso"
to ta kara amsawa dashi,
"Ke yarinya ya nike jinki kasa² ne ko har kin firgitane?
Haba yarinya tun kafin su kawo ki su baroki ai gara ki a dana tsoron zuwa dare kinji",
tura baki tayi kafin tace "tsoron me kuma ni zanji?
kuma ni mutum ya dena cemin yarinya tam,
kuma albishirin ka ai aure dai aka daura tarewa sai nasa lokaci ba nace maka ni ban shirya yin wani aure yanzun ba",
"keeee"
ya fada cikin daga murya
"wasa kikeyi yarinya ni zaki maida dan iska a daura auren kice wai zakici gaba da zama a gida!,
wasa kenan to wallahi karkija ma kanki yanzun muna isowa ince a wuce dake wato ga Abdul din banza duk uban jama'ar dana tara kawai sai su watse basu kaimin mata gida ba,kai aiko da anji kunya wallahi ke kimayi istigfari dan wannan k'aton sab'one wai kice tarewa ba yanzun ba ashe ma ba auren aka daura ba",
kunkuni ta fara
"Dawa kike?"ya tambaya a dake,
" Bada kowa ba".
"da kyau" shi kuka ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya,
yanke Wayar tayi kai wallahi Abdul Khareem dan bala'ine.
Shiko mugun a gefen shi dariya yayi kafin a bayyane yace "Kai wallahi yarinyar nan tafa rainani Dan ma ta daukeni sakarai nine zata latsa kujimin wani bankada wai ba zata tareba, amma ba damuwa very soon duk zan tsitstsige miki gashin rashin kunyar da naga sun tsiro miki zaki shigo hannuna,"
Tana yanke Wayar su Maryam suna shigo d'akin su hudu ne Maryam, Maimoon Meelat sai Aisha,maryam ce ta zauna a gefenta
"Amma wallahi amaryar AK kinci uwar rainin wayau ashe dama kina cikin gidan nan muke ta faman neman ki duk wanda ya tambaya sai dai muyi karyar kin dan fita dan iskanci kuma kika kama waya kika kashe"
Inji Maryam
Moon kuma tace "Dallah shareta gudowa tayi saboda taji dadin yin celebrating din samun cikar burin ta da kyau ba tareda an takura ta ba ku baku ganewa ne wai?
nidai bama wannan ba kinsan dai muna binki bashin kazar amarcii....idan mun yafe na baya wannan kam k'arya da ciwo muce mun yafe" ta fadi kalmar amarciii a iskance, fashewa duka sukayi da dariya harda ita Meenal din da ta daure fuska da farko,
"koba kazaba ki bari har inci naki tukun kafin in biya" tace cikin dariya.
"Yasin saiko kin biyashi" cewar Meelat batare data dena dariya ba tace
"ban taba sanin ana biyar bashin kazar amarciii ba sai yau,ai shi kenan sai in bada kudi a siyo kazar muci" ta fada tana musu kallon kasan ido,
"aiko wallahi baki isa ba,"suka hada baki wajen fada,
Aisha ce ta d'aura da cewa
"wanda dai ango zai kawo miki muma shi din zamuci ai wallahi ba wacece aka kwara irina nawa kazar da ko dandana ta banyi ba kukazo kuka dauketa,"
"kika bamu dai" Meenal ta fada tana dariya ta kuma ci gaba da cewa
"aikin banza kuma rashin cin kazar baisa ta canza zani ba dan haka muka isko amarya an mata cin koshi "
ta fada suna kara fashewa da dariya,
kai jama'a wallahi tunda aka fara hidimar bikin nan batayi dariya irinta yau ba,
shi yasa take mutuwar kaunar an matan nan nata dan indai muka hadu sai sunyi nishadi,
"gara ma kusa ranku a inuwa dan yanda bakuci waccan kazar ba wannan ma bata ciyuwa muku dan nidai ban sa ranar tarewa ba,"
kallon juna sukayi suna fashewa da dariya
"lafiya"Meenal ta tambaya tana binsu da kallon dariyar me kukeyi?
Maryam ce tace "haba kawata ke dan rashin imani har tunanin rashin tarewa ma kukeyi? To aiko indai tarewa ne anyi angama allah ya kaimu dare ki gani,"
marairaicewa tayi ta koma tsakiyar su ta zauna jingina kainta tayi a kafadar Maryam sannan ta dago fuskarta ta fuskance su saida ga kare musu kallo su duka 4 sannan ta kara shagwabe fuskarta
Tace " yanzun dan allah duk dasa hannun ku kuna goyon bayan wannan auren dolen da aka k'ara yimin?......"
Kallon juna sukayi kafi sukaja tsaki kamar hadin baki tureta maryam tayi daga jikinta ita kuma Meenal saita kara rungume ta,
"Meenal auren dole ko auren gata? Ke yanzun nan har kina da bakin cewa an miki auren dole bayan duk duniya ta shaida bakida masoyin daya kama kafar Abdul acikin zuciyar ki,duk yanda kika kai ga boye matsayin da yake dashi a cikin zuciyar ki duk wanda ya zauna dake sai ya gane haka,
ke yanzun a tunanin ki akwai wani d'a namijin dazai miki kalar soyayyar da mai jama'a yake miki ne?bance baza'a samu ba amma dai da kamar wuya gaskiya kar kuma kiga dan kina da tarin samari, ah ah tarin samari bashi bane wanda zai soki tsakani da allah ya kamata ki hanga"
Aisha ce ta dafa kafadarta "Amina mu masoyan kine na gaskiya dan haka dole musu duk wani abunda zai kawo cigaba a rayuwar ki kuma dole mu fada miki gaskiya,koda ace ya Abdul ba dan uwana bane dole ne in jinjina mishi irin jajircewar da yayi akanki,
Wallahi³ inda kin rasa mai jama'a to ko wanda ya kama kafar shi ba zaki samu ba
bari in tuna miki wani abunda nike ganin kamar kin manta Amina kefa bazawara ce auren ki kuma ba zama na wata 6 kikayi a gidan mijin ba shekarun 6 ake lissafi sannan ke yanzun baza'a kiraki yarinya ba domin ko akallah koba komai kinba kin dad'e daba 20 baya,
amma duk wadannan basu hana mai jama'a zage damtse wajen ganin ya zame miki mijin aure a karo na biyu ba duk da shi din saurayi ne matashi ga kuma arziki ke kanki sheda ce akan yanda mata ke binshi tun tale² balle kuma yanzun dako ba'a fad'iba kema kin san cewa arzikin bana ya zarce na bara,
amma a hakan duk ba wacce ya kallah a cikin su ke din dai da zuciyar shi keso ke dince dai ba canji, sannan karamin misali ki duba yanda ya gabatar da Neman aurenki,duk da zumuncin dake tsakanin ku wanda yasan da ace ana bada kyautar mace to ko kyauta ya cancanci a dauke ki a bashi,amma duba ki gani duk wani abu da ake gabatar wa wajen Neman aurenki bai ban²ta dana budurwa ba.."
"wallahi yan matan da yawa ma basu samu hakan ba"
cewar Sultana dake shigowa cikin d'akin yanzun,
"kawata kiji tsoron allah ki rike mijin ki da kyau,dan wallahi in kikayi wasa kece da kuka danko yanzun kinsan akwai yan hassada a gefe"
" Ai yan hassada nasu wasa ne ina kika baro kurayen dake ta faman dana mishi tarko basa ko gajiyawa?" Meelat ta amsa ma Sultana
Tura baki Meelat tayi
"to me yasa tun wancan lokacin basu aura mishi niba sai yanzun?"
"Saboda yanzun ne lokacin da Allah ya tsara muku yayi shi yasa Allah ya tabbatar ba tareda kinyi tsammani ba kuma lokacin kanki na hayaki nasan tsoro kikaba shi shiyasa bai iya bari an gane yana sonki ba"
cewar Maimoon
Maryam ce ta riko hannu ta "kawata kinsan a duniya dukan mu muna taya juna son abunda wanin mu keso,kinsan babu ta inda zamu zuba ido muna gani ki kara subucewa ya Abdul a wanna karan
aurenki na farko dana ki dauka kaddarar kuce tazo a hakan amma a yanzun idan kika guji Abdul Khareem hakika kin zalince shi dama ke kanki nasan yanda aka gabatar da komai a gaggauce ne yasa kike neman hanama zuciyar ki abunda take muradi amma ai shima baya da masaniya akan komai kuma meye burin masoyi wanda ya wuce ya mallaki abinda yake so, amma ki sani mai jama'a fa ba kwallon mangwaro bane balle kice gara kiyar ki huta da kuda wallahi Abdul Khareem bai taba fita a zuciyar ki koda ace Sheikh aka aura miki mu mun shaida hakan,
to akan me zaki nemi ki zalinci zuciyar ki?
kimana alfarma ki ajiye komai a gefe tunda dai har shi da yake matsayin saurayi yace yaji ya gani aimu abun tunkaho ne a wajen mu ki dena ganin cewa wai ai har yanzun baki da banbanci da budurwa tunda baki san Namiji ba ki sani sunan mace yana canzawa ne daga ranar da aka tabbatar da igiyoyi uku akanta na auren wani koba haka ba?"
Takai karshen zancen tana tambayar su Meelat "kwarai kuwa "suka amsa ta,.
" Allah kawata ni mamaki ma kike bani wacce macene zata samu hadadden saurayin da mata kala² suke binshi gida da office tace wai bata so?"cewar Meelat
" To ai kinji matsala ta farko wadannan tsinannun matan da suke binshi a kullum Kamar kuda ta ina zan fara fisabilillah" ta fada tna kallon su,
"ke dallah matsa inda ace suna gaban shi kema kin san da baiyi zaman tuzurancin da yayi zuwa yanzun ba,
Gaskiya kin bani mamaki to wai shi dan uban tsuntsun soyayyar ina ya tashi yaje harda kike neman juyama Abdul baya ki nuna bakya yayin shi bayan munsan duk karya ne to dan haka in ma laifin wani zaki gani ki fara ganin nawa nida nakai ma Hajiya labari dan naga kina Neman ki mai damu mutanen banza,
kuma alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu ke nan kin saki jiki cewa haka zaisa miki ido bazai nemi aurenki ba har sai kin gama boko, toke wai gidan ubanwa ma zaki kai bokon da idan yau kika fad'i kika mace shi kenan ya tashi a banza? Mtwss" taja tsaki
"gaskiya saura kadan ince ban yafe ba dan kin gwara mana kai" ta fada tana kai mata duk zabura tayi ta goce,
"to ni da kaina na bud'ema Bash gaskiyar cewa AK kike so bashi ba duk da nasan shima yana sonki amma banga amfanin boye mishi komai dake tsakanin ki da Mai Jama'a ba kuma ni na rokeshi akan yayi hakuri ya janye dan idan yayi kuskuren auren ki to tabbas gangan jikin ki ya aura amma zuciyar ki tana tareda mai jama'a,kuma alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu dan shima baija zaren da tsayi ba ya saki,
hakan nema yasa kikaga harmu mun fita sabgar ki dan munsan cewa gata aka miki,
haba yarinya tayama zamu yarda ki mana bakin ciki ai insha allah yau sai kwanan dakin mai jama'a"
ta karashe fada tana ran gwada guda ayyiririiiii haka dukan su suka dauka,
" wallahi sai mun kaiki"
Ita dai zuwa yanzun bata da ta cewa fa bada gari. atoh dama itama kin auren da takeyi bawai har zuci bane,
irin dai a tauna tsakuwa dan aya taji tsoro ne,.
Sultana ce ta fara waka,. "Ranar muke jira yau gashi tazo muma da tamburan mu gashi munzo ango mukeyima shida amarya.......haka suka dunga wakoki suna rawa,
gaskiya taji dadin kasancewar su tareda ita a wannan lokacin har saida taji haushin kanta yanda tazo ta wani zauna a dakin ita kadai da farko,
Saida maimoon ta fente mata fuska ta tsatsomata duk wani boyayyen kyauwunta sannan Sultana tamata d'aurin d'ankwali yar yayi basu hutaba saida suka tabbata ta fito a amaryar sak, Masha Allah kunsan Yan magana sunce amarya kota buzuzuce..............
To itma dai yau ko hasidin iza hasada dole ya bata hanya idan ta doso!
Saida sukayi hotuna dasu videos na tarihi injisu sannan Aunty fati ta iso tana cewa su fito angwaye sun iso tun d'azun,
Basu fita daga dakin ba saida suka kara fesheta da kalolin turare masu dadin shaka sannan suka mata jagora bayan sun lulluba mata gyale a saman kai,
tun kafin su fita daga sashen kamshin turaren su ya gayama sauran jama'ar dake kusa dasu cewa gamai gayya mai aiki nan wato amarya da kanta,
Bakajin kalmar komai daga bakin mutane a dai dai wannan lokacin sai dai masha Allah!!!!
Gogan nata tafara hangowa domin kunsan zuciya da zarar ta iso waje Wanda ke cikinta take fara ganewa, balle kuma gogan nata dama ya lafiyar giwa ko banza dama shidin gayun ne da kanshi balle kuma yau ranar tashi ce,
Yafa hadu yasha wanka ya gaji wallahi ita dai allah ya sani bata gajiya da kallon mai jama'a batun yauba, "Tubarkhallah"
Ta furta kasa², tana cigaba da kallon shi ta cikin gyalen ta kuma ta tabbata shima din ita yake kallo dan taji nauyin idanuwan shi a jikinta.
Lallai alkawarin Allah baya tashi, ta sani taso Abdul son da bata tab'a kwatanta shi akan kowa ba, amma allah ya sani bata tab'a kawo auren su a kusa irin haka ba, Amma gashi ta zama matar AK alhmadulillahi......
Koda Abdul ya gama waya da Meenal suna kofar gidan, bayan sun gama gaishe²n iyayen da sukazo yi wasu daga cikin abokan shi mota suka shiga suka wuce wajen da za'a gudanar da dinner domin karasa shiri dinner din zai gudana ne bayan magrib, daga wajen dinner ne kuma za'a sada amarya da dakin ta.
Sunyi sunyi da Abdul akan su shirya wani program din bayan dinner Amma sam yaki,