Showing 78001 words to 81000 words out of 190771 words
son shine?"
Shiru Moon tayi kafin ta amsa da cewa,
"Nima ban san yanda zan kwatanta abun ba, amma nasan ina matuk'ar kokarin kame kaine akoda yaushe indai ina tareda shi,"
Riko hannun ta Umman tayi,
"Moon bazance karki soshi ba domin ban san ya kikeji akan shi ba, sai dai zan miki tuni ne akan zumuncin dake tsakanin ki da yar uwarki Meenal ki d'auka cewa kece kika rabu dashi sai kuma kwatsam kikaji cewa ya koma sonta duk da kawancen dake tsakanin ki da ita ya zakiji, kibar batun cewar da akayi babu abunda ya hada su na auratayya koma dai yayane ita d'in tayi zama na shekaru a matsayin matar shi dan haka koda bata nuna a fuska ba tabbas ba lallai bane hakan ya mata dad'i a cikin zuciyar ta, ni dake dukan mu mata ne kuma ciwon ya mace na d'iya mace ne abinda bazan so ya faru dani ba indai zumuncin dake tsakanina da wata na gaskiya ne shima bazan so ya faru a kanta ba dan haka ina mai baki shawara da kisan yanda zakiyi ki cire son shi a cikin zuciyar ki in ma kin fara son nashi,
In kuma babu soyayyar falillahil hamdu sannan karki yarda ki barshi yazo gidan nan a gobe kisan duk yanda zakiyi ki hana shi zuwa ganin abban ku dan su maza kusan tunanin su d'aya ne basu fiye damuwa da abun da ke iya zuwa ya dawo ba kinji dai na fad'a miki dan in hakan ya tabbata ban san da bakin da zan kare kaina wajen Hajiya ba dan haka babu ruwa na ki kuma kwanta kiyi bacci dare yayi"
Tana gama fad'in hakan ta fice daga d'akin bayan ta kashe ma Moon din haske,
Wannan dare dai sam baiyi ma Moon dadi ba domin sosai kalaman Umman su ya k'ara sanyaya mata jiki, kamar kuma yanda Umman nasu tace ta d'auki hakan a matsayin cewa a kanta ne abun ya faru itace ta rabu dashi sai ya koma yana neman yar uwarta ya ita zataji,
Gaba daya sai takejin ai in itace hakan ya faru da ita tofa tabbas bazata iya d'auka ba, to waima miyasa tun farko tayi saken da har ta bar zuciyar ta ta kusantu dashi har haka? Lallai ita soyayya batayi mata adalci ba me yasa?
Me yasa?
Me yasa? Zuciyar ta zata kamu da son shi.
Tsabar yanda tasa damuwa a ranta ne hakan yasa washe gari ta tashi da zazzafar zazzabin dako aiki bata iya fita ba dan sai da aka kira likita yazo har gida ya dubata,
Fad'a sosai umman su ta mata sai dai duk abunda ke faruwa Umman bata nuna ma Baba Usman komai ba,
Ita kuma Moon d'in duk da yanda take jin jiki haka tayi ta neman Sarki a waya amma bai kunna wayar shi ba gashi kuma ita ba sanin gidan shi tayi ba balle taje ta same shi,
Wajen da suke had'uwa kuma tasan ko zaije wajen sai yamma yau kuma batama da tabbacin cewa zai yarda su had'u tunda gashi yak'i kunna wayar shima, tana ta addu'a ko baba Usman zai fita gida amma sai gashi yau tunda gari ya waye bak'i kawai yake tayi wad'an nan na fita wasu ke shigowa kuma duk in bak'in sun shigo sai ta aika kannnen ta su dubo mata,
Daga ita har umman su babu wacce ta samu nutsuwar zuciya dukan su a tsorace suke.
****
A gefen Sarki ko lafiya kalau yayi bacci a wannan rana cike da farin cikin kololuwar da zuciya ce kad'ai zata gane hakan, a yau daya fitar dake abunda ke cikin zuciyar shi akan Moon sai yakeji kamar ai har anyi angama dan haka kamar yanda ya kudurta dole a goben zai isa ga Baba Usman dan haka kwana yayi yana shawara da zuciyar shi akan shine zaije ko koh wani ya kamata ya wakilta yaje mishi ne?
To wani wa zai wakilta?
Brig, Gen, zuciyar shi ta bashi amsa,
To amma idan yaje ma brig da maganar nan hakan bai zama cin fuska ba kuwa?
Yaushe yaushe ya rabu da Meenal harda zai fara neman wani auren ga kuma Teemah ba wani lafiya take dashi ba kullum fama takeyi da kanta, kuma shi brig din fa uban matan shine,
To amma idan bashi din ba ana ai bashi da wani shak'ik'in da zai tura, kuma koda Brig baiji maganar nan yanzun ba dole zaiji zuwa gaba dan haka gara ayi ta ta k'are kawai tun yanzun yasan cewa tunda brig namiji ne zai gane halin da yake ciki,
Da wannan shawarar daya yanke ya samu bacci kai d'adi ya d'auke shi,
Washe gari ko yana k'aryawa bayan ya gama abubuwan da zaiyi ya d'auki Boy yama Teemah sallama akan zasuje Barracks,
Sun tattauna sosai tsakanin shi da Brigadier abunda bai tab'ayi ba shine yau yayi wato zauna wa ya labarta shima irin zaman da sukayi da Teemah dama abubuwan daya faru harma da dalilin rabuwar su da Meenal harda hukuncin daya yanke na k'ara aure dama yarinyar da yake son auren,
Brigadier yayi fad'a sosai akan me yasa tsayin shekarun nan shi Sarki baizo ya shaida mishi irin rayuwar dake gudana a cikin gidan shiba, ranshi ya baci sosai dan haka bai b'ata lokaci ba shi da kanshi ya shirya bayan ya amshi adireshin gidan su Moon ya kira Aminan shi mutum biyu suka shirya suka tafi dad'i kamar ya sheqe Sarki dan baiyi zaton hakan zaizo mishi da sauk'i ba,
Su brigadier sun isa gidan su Moon a wannan rana sun kuma samu damar ganawa da Baba Usman,
Bayan gaisuwa sunsha hira sosai a tsakanin su domin ashe d'aya daga cikin abokan na Brigadier tsohon Abokin Baba Usman ne wanda suka dad'e basu had'u ba hasali ma dukan su basu san cewa gari d'aya suke zaune ba dan haka sai aka shiga hira da tuna baya irin na tsofaffin abokai kafin suka gangaro kan abunda ya kawo su gareshi, wato neman iri, anan ne shi brigadier ya gabatar da kanshi a matsayin uban Sarki a kudu kuma uban matan dashi Sarki d'in yake aure ya kuma k'ara dayi mishi fashin bak'i neman auren Moon din da suke so duk da kasancewar ta yar uwa wajen Meenal,
Da yike kasancewar su maza hakan bai wani dame suba sai dai Baba Usman ya sheda musu cewa shi dai shine uban Maimoon kawai amma neman auren ta da bada shi yana hannun d'an uwan shi Ahmad ne wanda a halin yanzun kuma baya k'asar yana zaune a Saudiya ne tare da nashi iyalan,
Jin hakan sai suka rok'e shi akan ko zai basu number din waliyin natan in yaso sai su neme shi suji ta bakin shi dan sufa da zafin su sukazo,
Hakan ce ta faru domin a nan falon Baba Usman ya kira Abba Ahmad sukayi magana su brigadier suka kawo maganar neman auren da suka zo,
Shi kuma ya shaida musu cewa suyi hakuri har ya shigo k'asar a sati mai zuwa dan neman auren yarshi yafi k'arfin ace ayi shi ta waya suyi hakuri har sai yazo sai ayi komai daya dace,
A haka suka rabu kowa cikin farin ciki,
Bayan brigadier ya koma ne ya kira Sarki ya sheda mishi yanda sukayi, shima dai yayi farin ciki da jin haka koba komai yana da hope akan samun Moon din tunda yanzun maganar taje gaban Manya dan shi dai zuwa yanzun yana jin cewa bazai iya b'ata wasu watan ni masu tsoho ba tareda ya mallaketa ba,
A ranar da wuri Moon ta k'arfafa jikin ta bayan zazzabin ya d'an saketa ta fita zuwa inda suke had'uwa da Sarki sai dai kuma abun takaici haka tayi ta zama har gabannin magrib Sarki bai zoba kuma bai kunna wayar shi ba, gajiya tayi ganin dare ya kunno kai ta taso haka nan ta dawo gida jikinta a sanyaye,
Da dare yayi koda Umma tama Baba Usman magana akan bak'in daya dungayi a yau d'in a zaton ta najin ko zaice mata Sarki yazo ko wani abun makamancin hakan sam bai d'auko mata hirar ba dan ce mata yayi abokanan kasuwancin shine kawai,
Shi kuma yak'i fad'a mata gaskiya ne dan yasan a matsayin ta na mace bai zama lallai tama abun kyakyawar fahimta ba, dan haka ya yanke hukuncin gara yayi shiru har sai Abba Ahmad ya shigo k'asar zasu yanke hukuncin sannan su san ta yanda zasu shawo kan Hajiya akan maganar dan nata rikicin yasan yana gaba akan na kowa,
Daga wayewar gari zuwa dare Moon ta aikama Sarki sako mara adadi tana rokon shi akan dan Allah karyace zaije ya samu Baba Usman akan maganar nan ita bazata iya auren mijin da suka rabu da yar uwarta ba, lokaci zuwa lokaci take dubawa ko ya dawo mata da amsar sakon nin ta amma babu wani motsi har aka kwana aka hantse,
Bashi ya kunna wayar shiba sai da aka kwana biyu koda ta dana maganar kawai sai ya nuna mata ba komai bazai je wajen Baba Usman din ba har sai sanda ita da kanta ta bashi dama,
Amma fa kullum safe rana dare baya gajiya da kiranta a waya kawai dan yaji muryar ta ya kuma tambayeta ya take,
Ita kuma Umma ganin Moon din ta sake kuma shima Baba Usman baice mata komai ba sai tati zaton ko Moon ta shawo kan Sarki ne ya hakura dan haka itama sai tayi watsi da komai ta dukufa dama Moon din addu'ar Allah ya fito mata da miji na gari tati auren ta ta huta zaman gidan ya isa haka.
A gefen AK ko tun bayan barin su Meenal Kaduna bai samu zama ba a kokarin shi na ganin ya kammala komai kafin ya wuce Zarian dan yanzun shirye shiryen bikin Musty shine abunda yake gaban su,
Tunda Meenal tabar garin basu k'arayin waya ba koya kirata haka wayar zatayi k'ara harta gaji ta yanke bazata d'auka ba,
Daya fahimci horashi take son yi ta nan gefen sai ya daina kira ya koma tura mata sakon ni, shi kanshi mamakin kanshi yakeyi ta yanda yake iya zama wajen tsara tausasan kalaman soyayya masu tsuma zuciya wadanda ke fitar da gaskiyar abin dake cikin zuciyar shi ya tura mata,
Ko wani safe rana dare da kallar sakon da yake tura mata masu zafi kuma komai yakeyi in lokacin tura sak'on yayi zai ajiye ne ya rubuta sai ya tura mata ya tabbatar sakon ya tafi kafin zaici gaba da al'amuran shi,
idan kuma yana son jin muryar Meenal d'in number d'in Sultana da yasa Musty ya amsa a hannun Meelat ya tura mishi yake kira,
Ita kuma sai ta ajiye wayar a kusa da Meenal tayi ta janta da hira bayan ta d'auki wayar haka zaiyi ta saurare har sai ya gamsu zai yanke wayar,
yawan jin muryar ta da yakeyi ta wayar Sultana ba kad'an ba yake rage mishi kewar ta duk da haka Allah Allah yakeyi ya iso Zaria tunda dai har yanzun bai san me nene gaskiyar abinda yake cikin zuciyar ta akan shiba,
To itama dai Hajiyar taku a gefen ta tun tanajin wani iri a duk sanda zata ga sak'on shi har ya zamana yanzun Allah Allah take taga sak'on nashi ya shigo wayarta dan ta samu inda zata lab'e ta karanta, tsaf ta haddace lokutan da yake turo mata sakon sai dai duk rok'on da yake mata akan ta amsa mishi wato ta maida mishi amsar sak'on nashi tak'iyin hakan zata dai karanta tana murmushi amma babu amsa,
Mutum biyu sune sukafi takura mata a rayuwarta yanzun na farko Salman wanda take ma kallon tabab'b'e tun daga ranar daya wanko k'afar shi yazo har gida ita ta d'auka wani abun arzikin zai fad'a mata amma wai gayen nan sai da ya karkace ya gyara tsayuwar shi kafin ya kalli tsabar idonta ya fad'a mata wai shi dai Salman shine yake sonta kuma ma abun bai tsaya nan ba harda wani ikirarin wai aurenta yake son yi abundai kamar a duniyar mahaukata wallahi,
To dai ai ko daga dawanau ya kwato ya fito ai bai kamata ita tana matsayin matar da yayan shi ya aura ya sake ba shi kuma yazo ba kunya ba tsoron Allah yace wai shima sonta yakeyi zai aureta,
Ita wallahi bata tab'a sanin cewa k'aton mahaukaci ta dad'e tana ma kallon mai hankali ba sai ranar dan rasa amsar da zata bashi ma tayi sai kawai ta juya ta shige cikin gida ta barshi a wajen yana kwala kiran sunan ta ko waigen shi batayi ba,
Tasan in tace ta bud'e baki tayi magana a lokacin tofa tabbas tana iya lailayo k'atoton zagin da zata d'ura mishi ko kuma ta sheqe fuskar shi da mari ko ya dawo hayyacin shi, koda ta fad'a ma Sultana abunda ya faru tsakanin ta da Salman din dariya kawai tayi kafin tace mata,
"Ai na fad'a miki dama cewa sonki yakeyi amma kikak'i yarda, wallahi in kikayi sake jan ajinki yasa kika k'i yarda ki amshi soyayyar AK tofa sai dai kiji ana shelar d'aurin auren ki a masallaci bayan an d'aura,
Muko mik'aki zamuyi mu fito muna fatan Allah ya kawo yan hud'u"
"Sultana kibar wannan maganar ki barni in fama mamakin abunda gayen nan yamin,
Waini zai kalla yace yana so wato so sukeyi shida yayan shi su mai dani kwallon wasa wato yayan ya saki shi kuma bari ya kunno min kai, insha Allah ni kuma duk ranar daya k'ara shawo kayan mayen shi yazo ya k'aramin hauka sai nayi tsalle na tsatso karfi kafin in kakkafta mishi mari"
Dariya sosai sultana take mata,
"To ki yarda mana kawai tunda dai shi AK kince bakya son shi... "
Yanke ta tayi da cewa uban wa yace miki bana son shi,
Ko ban so da aure ba ai dai shi din dan uwana ne, kuma amsa soyayyar ne ban tashi ba tukun, kece baki san halin shiba na rantse miki da allah ina sakewa nace na yarda ina son shi tofa na shiga uku kenan bani ba k'ara shakar numfashi cikin kwanciyar hankali,
Kinga wancan ustazun yayan naki da kike ganin yana matsa mana? To yasin nashi kad'an ne ni kuma yanzun bana buk'atar kowa ya takura min, kuma ai nace musu ni ba yanzun zan k'arayin wani auren ba"
Wayarta data d'auki karar kira ne ya katse mata zancen bakin ta,
"Sultana kin san wake kira?"
"Waye"Sultana ta tambaya,
"Mutumin mu na ranar nan wanda muka had'u dashi a kofar doka"
Dariya sosai sultana ta fashe dashi tana cewa,
"Sister kiji tsoron Allah kibar mutumin nan tunda ba auren shi dai zakiyi ba shima da shegen naci nayi zaton ya dena kira ai!"
"Ki barshi kawai ai inya iya naci ni kuma nice maganin shi, kin san tun jiya yake nacin wai yana son zai gaishe da Mommy tunda na hana shi zuwa gida nace sai zuwa gaba tukun,
To tun jiyan yake kirana wai in bata waya ni karan hauka ne ya cijeni dazai had'asu tab',
Wai kin ma san me?"
"Ah ah"
"Wai tambaya na yake nawa nake buk'ata kudin da zanyi hidimar biki,"
Dariya sosai Meenal ta fashe dashi kafin ta d'aura da cewa,,
"Kibar mugun wai ni zaima gatse harda wani cewa yaji shiru ban tura mishi da account number ba kona raina abunda zai bani ne, ni kuma tunani nike in tura ko in kyale shine to gashi dai kin gani sai faman kira yake tun d'azun"
"Kawo wayar ki gani, da fari dai ki fara tura mishi account number din, idan ya tafi sai ki kira shi kice mishi Mommyn bata kusa ne amma gata ni kuma zan gyara muryata irin ta manya sai inyi magana dashi a matsayin Mommy muci kudin banza wallahi"
"Allah dai yabar min ke My Namcy bari ki gani yanzun kuwa zamu gabatar da komai kamar yanda muka shirya"
Amsar wayar tayi ta fara tura mishi account number d'in sai da ta tabbatar da cewa ya isa tashi wayar kafin ta danna mishi kira,
Ita kuma Sultana tana gefe sai faman gyara murya take dan ko kad'an bata son su kwafsa, tsun tsune fa suka samu daga sama gasasshe dan haka ai suci rabon su kawai,
Din din din karar da wayar keyi kenan alamun dake nuna wayar na ringing tacan gefen,
Yanke wayar akayi cikin kankanin lokaci ya maido da kiran zuwa wayar Meenal d'in,
"Ke gashi yana kira wallahi" cewar Meenal tana nuna ma Sultana,
"To ki dauka mana kar kiran ya yanke kuma"
" Assalamu Alaikum hello" ta ambata bayan ta daga kiran sai ta danna wayar a speaker,
"Ameen Alaikis Salam Baby girl barka da war haka ya kike?"
"Ina lafiya Yallabai, dama nace bari in kirane in had'aku da Mommyn kamar yanda ka buk'ata"
"Ok ok aiko kin kyauta naji dad'i sosai ki bata wayar to"
"Ok Mommy gashi zaku gaisa"
Cewar Meenal tana tura ma Sultana wayar,
Gyara muryar ta Sultana tayi sosai ta yanda ya koma kamar na Babban mace ba kuma na tsoffi ba ta rik'e wayar a hannun ta tana cewa,
"Wanene kuma zaki had'ani dashi Yar Malam keda ko maganar samari bakya son ana miki a gidan nan wani kai sa'an ne wannan?"
Ta tambaya kamar irin bata san shi na cikin wayar yana jin me take cewa ba,
"Ni dai Mommy gaisawa kawai zakiyi dashi bance kice mishi komai ba atoh dan so nike sai mun k'ara shakuwa kafin in gabatar dashi kuma ke kad'aice ma yanzun zan had'aku"
"Haba Meenal ko baki fito fili kin fad'aba ai nasan kina son shi Allah yasa dai ya rik'e min ke da amana kema kiyi auren nan dai"
Sultana ta karasa fada kafin tace,
"Assalamu Alaikum"
"Ameen Alaikum Mama ina wuni"
"Lafiya lau d'an nan ya gida ya aiki da wajen iyayen ka dafatan duk kuna