Showing 96001 words to 99000 words out of 190771 words
shi guda biyu ya nuna ta dashi, janye shi Hajiya tayi tana kai mishi bugu da mitan cewa bamashi da kunya a gaban idonta yake aikama jikarta kiss wato shi ga fitsararre sirikin zamani tana cigaba da mitan suka k'arasa fita daga d'akin tana cema Meenal ,
"Ki taso ki kulle k'ofar ki kuma dunga kulleta da key kina ji na fad'a miki karki yarda ki dunga kwanciya baki kulle kofa da makulli ba "
Bata iya mik'ewa daga inda take ba har sai da ta tabbatar da cewa sun sauka k'asa kafin taje ta tura k'ofar d'akin ta rufe da key ta koma kan gado ta kwanta a rigingine tana kallon silin din dakin,
murmushi ne ya kwace mata sai tayi saurin kai hannu ta rufe fuskarta tana mai jin kunyar kanta da kanta,
Wai yau ita Meenal itace ta furta cewa tana son wani, harma ta bashi daman zuwa ya nemi a auren ta a wajen iyayen ta,
Sam batayi zaton cewa hakan zaizo mata da wurwuri ba, lallai AK ya shammace ta da yawa, ita da taci buri mai girma nayin rayuwar da take so ta yanda zata biya bashin Yarintan ta da aka dakushe mata, sai gashi tun ba'aje ko Ina ba da alamu burin nata dai bamai cika bane.
*UMMIEE CE*βπΌ
[9/20, 10:20 PM] Ummiee Zaria: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 32*
No editing π
Daga ABU kai tsaye Unguwar Malamai Bash ya wuce dan dole yana buk'atar yin bincike akan Meenal daya gani yau, da gaske auren nata ya mutune har take shirin yi wani auren ko ya abun yake?
Idan yayi nazari akan maganar da yarinyar can mai kama da yar tsana ta fad'a mishi kenan hakan yana nufin auren Meenal ya mutu zawarci takeyi a yanzun haka!
To amma in haka ne mai yasa bata neme shiba,
Yayi zaton cewa a yanda komai ya kasance a tsakanin su suka rabu suna masu kewar juna ba tareda sun shirya rabuwa a lokacin ba ai bai dace ace yanzun auren ta ya mutu kuma harta kasa neman shi dan ta shaida mishi ba,
yanzun ashe da ace baiyi katarin ganin ta a yau dinba da shikenan har saita k'arayin wani auren kafin in yana da rabon jin zance yaji daga baya?
Anya Meenal tasan cewa rashinta ne ya hana shi yin wani auren har yanzun kuwa?
Yaso Meenal irin son da bai tab'a tsammanin cewa zai iya hak'urin rashin ta ba, sai gashi a daidai lokacin daya gama tsara yanda zasu gudanar da rayuwar su a karkashin inuwar aure bak'in labari ya iske shi a ranar d'aurin auren ta,
Sumewa yayi fa tsaf a sanda iyayen ta suke fad'a mishi cewa yau din shine za'a d'auren ta,
*BARI MU D'AN KOMA BAYA KAD'AN*
Idan baku manta ba a ranar d'aurin auren Meenal da Sarki wancan lokacin Aunty Hassana ta amshi Number din Bash a wajen Meenal da sunan cewa ita zata kira shi ta shaida mishi halin da ake ciki,
In baku manta ba kuma a wannan lokacin shi Bash din yana ta fama da Meenal din ne akan ta amince mishi ya turo magabatan shi dan shima ya gabatar da kanshi a gaban Malam amma sam tak'i a cewar ta karatu zatayi.
Abinda bata sani ba ita kuma shine tunda yabitaΒ² akan ta bashi dama tak'i shine kawai ya yanke hukuncin cewa a ranar d'aurin auren nasu Raheenat shima zai tura nashi iyayen,
Dan haka koda kiran Aunty Hassana ya riske shi akan idan yana da hali yazo gidan Hajiya tana neman shi baiji wani d'arba dan koda ta kira dama shima yana tare da nashi iyayen ne da zasu tafi wajen d'aurin auren tare dan so suke idan an gama daura auren su kuma sai su nemi ganin malam dan su gabatar mishi da abinda ya kawosu wato neman auren Meenal,
Ba karamin dadi yaji ba a sanda yaji cewa kiran daga yayan Maman Meenal ne, kawai sai tunanin shi yake bashi cewa k'ila Meenal din ce ta gabatar dashi a wajen su tunda inba haka ba ta ina Yayar mamanta zata san da zaman shi balle kuma harta samu number din shi ta kira shi kai tsaye haka,
Dan haka daya tashi tafiya gidan sai bai tafi shi d'aya ba suka wuce tare da Kanin Maman shi d'aya da kuma wani Yayan Baban su wanda idan yaran mazan gidan su zasuyi aure shine yake shigewa gaba.
Tarba na girma da mutunci akai musu duk da cewa ita Aunty Hassana batayi zaton cewa tare zaizo da iyayen shiba, sai bayan data fito ne taga bashi kad'ai bane dan dole suka koma sashen Hajiya domin dai bazai yuwu abar iyayen nashi a mota suna jira ba,
Kuma koba komai tunda abun ba wanda za'a tsaya ana boyewa bane tasan dole zasuji dan haka sai tayi musu iso suka d'unguma zuwa
Falon Hajiya gaba d'ayan su,
Bayan sun gama gaishe gaishe ne Yayan Baban Bash din ya gabatar da kanshi a matsayin waliyin Bash da cewar dama a yau din sun shirya da sunan idan an gama d'aurin aure ne suma zasu gabatar da nasu neman auren sai kuma ga kira shi Bash din ya samu shine yasa suka d'unguma sukazo gaba d'aya tunda dai suma nan d'in ai iyayen Meenal ne tunda sun san da ace har wannan lokacin Prof Abdul Khareem yana raye dashi da kanshi yana iya bashi auren Meenal din,
Jikin kowa yayi sanyi a wajen saboda jin abinda yake tafe dasu, Hajiya ko harda yar kwallanta dan ita wallahi da ace tasan da batun bash d'in nan da wuri da tabbas zatayi tsaye wajen ganin auren nan bai tabbata ba amma ina sai gashi ya bayyana mata a cikin kuraren lokacin da babu abunda zata iyayi dole saidai tayi hakuri,
dukan su a wajen rasa kwarin gwuiwar shaida musu zancen auren Meenal din da za'ayi a ranar sukayi,
Ita Anty Hassana dama tunda ta musu iso ta lallab'a tabar falon Abba Ahmad daya kasance shine Babba a yaran Hajiya shi Hajiya ta wakilta akan ya shaida musu halin da ake ciki,
Saida yayi ma Bash doguwar nasihar data jefa Bash d'in cikin kokonto kafin ya shaida musu halin da ake ciki na auren ita Meenal din da Bash din keso, ya kuma fad'a musu gaskiyar cewa itama kanta yarinyar bata samu labarin d'aurin auren ba sai a jiya sannan aka shaida mata, tun jiyan kuma har yau bata cikin yanayi mai dad'i faruwan hakan ne kuma yasa ta shaida musu cewa bash d'in ne yake neman ta da kuma cewar ya dade yana son ta bashi damar gabatar da kanshi a wajen iyayen ta amma sai batayi hakan ba,
Sun san cewa a yanda yake sonta dole zaiso ace ya kasance a wajen d'aurin auren kannin ta yau d'in sai dai kuma su bazasu so ace ya riski labarin a wajen daurin auren ba shi yasa suka kira shi dan su shaida mishi abunda yake faruwa,
Tashin hankali irin wanda yake zuwa babu zato bare tsammani shine ya faru a wannan rana domin dai tuni fa Bash ya d'auke wuta, abu kamar wasa sai gashi ya zama gagarumi domin dai tunda suka fahimci ya suma suke faman sheqa mishi ruwa a k'okarin su na ganin ya farfad'o sai dai shiru, ya sheme kawai abinshi babu rai ba alamar shi, dan haka hankali tashe da iyayen nashi nasu Baba Usman suka rankaya asibiti,
Hajiya ko a wannan rana tayi ma Malam Almu allah ya isa yafi cikin carbi dubu, a cewarta ga wani yana shirin sheqe nashi rayuwar akan jikanta amma mugun Yayan uba ya d'auki auren yar kanin shi da kullum yake ikirarin cewa yana sonta ya aura ma d'an d'an uwan shi wanda kowa yasan cewa ba lallai bane tayi daraja a wajen mijin ba tunda dai tuni tun Ana rade radi har kowa ya tabbatar da cewa matar Sarki ce Sarkin shi kuma bafade,
Gaskiya Hajiya taji bak'in cikin wannan aure sosai sai dai kuma bata da yanda zatayi ta hana ko tasa a d'aura da Bash da yake can kwance s asibiti dan koda Allah yasa ya farfado rikicewa jikin shi yayi dole iyayen shi sai da sukayi jinyar shi mai tsayi,
Bayan ya dawo hayyacin shi taso ganin Meenal kwarai sai dai kuma babu hali saboda dai tuni aka kaita d'akin Mijinta, gaskiya Bash yasha wahala sosai duk wanda ya ganshi a lokacin nan sai ya tausaya mishi domin sam ya kasa jure rashin Meenal,
Wannan dalilin shi yasa Maman shi ta matsama Master akan gara Bash d'in ya tafi k'asar waje ko sa samu ya mance da Meenal badan yaso ba haka ya shirya suka bar k'asar,
Shekara uku yayi a London ya matsa akan shi dai zai dawo Nigeria ganin da iyayen sukayi cewa zuwa lokacin ya cire batun Meenal sai suka yarje mishi dawowar, sai dai kuma tunda ya dawo Mahaifiyar shi ta fara matsa mishi akan maganar aure a cewar ta tunda Meenal tayi auren ta ai gara shima yayi, duk ta inda ta bullo mishi shi kuma sai ya kucce daga k'arshe daya gane cewa indai fa zaici gaba da zama a k'asar tofa bazata barshi ba ko auren dole ne sai ta mishi dan haka a sirrance ya had'a nashi ya nashi ya gudu yabar k'asa, Malesia ya koma wannan karan sai da yayi kusan shekara kafin iyayen shi suka gano inda yake, dan haka da suka tashi tafiya inda yake ita Maman tashi ita tayi tsaye saida aka d'aura auren shi da yarinyar yayan ta ikram sannan suka wuce mishi da amaryar shi can kasan,
Wannan abubuwa da suka faru na doguwar jinyar da yayi da kuma yanda ya gudu yabar gida ba tareda sanin kowa ba sune dalilan da suka sa ita uwar shi ta tsani Meenal dan ita a ganin ta ai kawai Meenal din ce ta yaudareshi dan da ace tana son shi tun farko da bazata hana shi zuwa wajen iyayen ta ya gabatar da kanshi ba,
Gashi yanzun ita tana gidan Mijinta hankali kwance ta manta dashi shi kuma har yanzun ya kasa cireta a ranshi balle ya maye gurbin ta da wata a cikin rayuwar shi,
Todai a dole a babu yanda zanyi dole haka nan ya amshi auren iklima bayan iyayen ta sun kaita da sati d'aya suka tattaro suka dawo gida Nigeria,
Zamane wani iri yake gudana a tsakanin ma'auratan domin dai shi tunda aka kai mishi ita gidan shi ko sau d'aya bai tab'a kallon ta a matsayin mata ba yanda ya saba gudanar da rayuwar shi tun farko haka yaci gaba babu abinda ya canja sai dai kuma yana dawowa gida da dare yake kulle k'ofar d'akin shi saboda yanda take ta faman kai mishi far maki abin ya isheshi, ace a kawo maka Amarya kuma wai budurwa amma tun baka nuna bukatar ka akanta ba ita ta fara kawo maka farmaki, dan haka sai ya d'auki matak'in k'in zaman gidan daya dawo kuma yake rufe k'ofa haka zatazo tayi ta bugu yayi mata banza,
Ita ko baiwar allah dama tun tuni ta dad'e tana renon soyayyar shi sai dai kuma a sanda ta bayyana mishi lafiyayyen mari ya wanke mata fuska dashi da kuma gingimemen gargadi kan cewa koda wasa idan harta bari wani yaji zancen sai yaci mata uwa,
Dan dole tayi hakuri ta kama kanta dashi badan taso ba sai gashi kwatsam daga baya suka samu labarin wai jaririyar yarinyar dashi bash din keso iyayen ta sun mata auren dole, ita Ikram ta girme ma Meenal nesa ba kusa ba sannan tana da waye da budewar ido dan kwata kwata bata da kunya, wannan halin nata shi yasa shi kuma Bash baya shiri da ita tun farko dan shi baya son auren macen da idanun ta suka riga suka bud'e irin haka yafi son karamar yarinyar da shine zai reneta da kanshi ya tafiyar da ita yanda yake so,
Watanni aka share Ikram tana ta faman son ganin ta shawo kanshi kodan saboda bala'in dake cin jikin ta na kayan mata na bala'i da ta d'ud'dura ma cikin ta tunda aka fara zancen auren ta dashi sai gashi an kawota amma har lokacin ba'a samu cigaba ba,
Ganin idan ta zauna a gida tofa wata rana sha'awa na iya sheqeta sai kawai ta dena zaman gidan, domin da zarar ya fice itama take yin nata shirin ta fice a binta,
A haka sukaci gaba da rayuwa bai rageta da komai ba illah harqallah na kwanciyar aure, itama kuma tunda ta zama yar gari ta samu masu d'ebe mata kewa ga kuma kud'ad'en da yake tura mata na kula da komai na gidan duk wata sai kawai ta tattara shi da auren shi ta watsar, da auren ta idan taga dama zatabi saurayi suyi tafiyar kwanaki bata gida, har taje ta dawo kuma ba sani yakeyi ba kamar yanda shima har yabar k'asar yaje wani wajen ya dawo bata sani, sai dai in tayi katarin ji a bakin uwar shi ko kannin shi,
Haka sukayi ta zama cikin wannan rayuwa har sai da suka shekara biyu da watanni da aure kafin ranar bacin rana ya risketa, domin dai tsautsayi ne yasa ranar ta gayyato d'aya daga cikin samarin ta har cikin gidan bata damu da cewa Bash yana nan ko baya nan ba tunda tasan ko yana gari idan ya riga ya fita gida da safe to sai tsakiyar dare zai dawo,
Abinda bata sani ba shine a wannan satin shi gaba d'aya ma baya k'asar Nigeria yazo saboda rashin lafiyan daya kama Master dole ya ajiye komai ya wuce Nigerian bai saba sallaman ta idan zaiyi tafiya ba dan haka koda zai tafi bai shaida mata ba, sai dai kuma zuwan shi gida a wannan lokacin nasihan dashi Master ya mishi na cewa ya rik'e matar shi da kyau kar yace wai dan ya rasa Meenal hakan zaisa ya wulakanta Ikram domin koba komai ita din yar uwar shice, koda Master ya mishi wannan nasihar yana cikin Zafin ciwo shi kuma Bash ya ma Baban nashi alqawarin dai daitawa da itane saboda bazaiso ace ya kasa bin nasihar da mahaifin shi ya mishi a cikin halin rayuwa ko mutuwa ba domin sosai Master yake jin jiki babu wanda yayi zaton zai tashi a wannan ciwon hatta da iyalan shi sun cire rai,
Sai dai kuma da yike ran bawa a hannun Allah yake sai gashi ya samu lafiya, a dawowar shi yaso ya fuskance ta su gyara zaman su dan ya shirya amsarta zai kuma gudanar da rayuwar auren su kamar na sauran ma'aurata sai gashi yana dawowa yayi mummunar gani,
Domin dai ita Ikram tunda tasan cewa gidan ta bawai gidan da bak'i ke yawan zuwa bane dan haka bata wani damuwa da kulle kofa saboda unguwar da suke akwai tsaro sosai kuma su can ba kamar mu nan Nigeria bane da zakaji tsoron barin kofa a bude,
Mummunar gani idanuwan shi sukayi mishi ganin da saida yayi silar yankewar numfashi daga k'irjin shi, a sanda ya farfado ko tuni kwarton daya tarar tare da matar auren shi ya cika ma wandon shi iska ya gudu ita k'adaice zaune a falon tana faman rusa mishi kukan munafunci da rokon shi akan ya taimaka ya rufa mata asiri shairin shed'an ne,
Duk hakurin da take bashi bai iya ce mata komai ba yadai samu ya lallab'a duk da duhun da jirin da yake d'ibar shi haka yakai kanshi d'aki,
Yayi kuka sosai domin yasan shima yana da laifi saboda da ace bai wofantar da itaba da babu yanda za'ayi tayi tunanin bin wasu mazan balle harta kawo mishi su gidan shi, shekaru kusan uku fa ake magana da auren su amma ko sau d'aya bai tab'a zama shida ita sukayi magana na fahimtar juna a tsakanin suba sosai yayi dana sanin irin rik'on sakainar kashin da yayi ma auren nasu lallai ya cutar da ita,
Kwana biyu yayi a cikin d'akin ba tareda ya fito ba ita kuma tsoron shi da kuma abinda take tunanin zai aikata akanta sune suka sa ta tattara duk wani abunda ta mallaka tsayin zaman da tayi a k'asar ta tattaro komai tabi jirgi ta dawo Nigeria, sai dai kuma koda ta dawo bata fad'ama kowa ainihin dalilin dawowar nata ba, tadai ce musu shine yace tazo gida dan dama tun auren ko sau d'aya bataje gida ba sai sukayi zaton kawai ko ta kawo ziyara ne,
Bayanda ya gama jinyar nashi ya fito domin yana son yin magana da ita ne ya tadda bata a gidan ganin babu kayanta a d'akin ta komai nata ta kwashe ne kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa gida ta koma,
Bai tab'a zaton cewa zata koma gidan ba dan yaso ne kawai tunda komai ya riga ya faru shi yaji ya gani zai rungumi kaddara abinda yaso suyi shine suje asibiti a fara duba mishi lafiyar ta,
Idan har an tabbatar mishi da lafiyarta kalau to zai sa tayi istibra'i ne idan ta gama sai ya nemi wani Malamin da zai d'aura musu wani auren anan tunda bai san ko tun yaushe take mu'amala da wasu mazan ba, sai gashi kuma hauka da rashin hankalin ta yasa ta kwashi jiki ta koma gida,
Ya kuduri aniyar bazai bita ba tukun zai zauna yasa mata Idone tukun har zuwa sanda zata dawo, idan kuma iyayen su sun neme shi to yasan cewa ta tona ma kanta asiri kenan, dan haka sai kawai yaci gaba da harkokin shi,
Sai da tayi kusan wata biyu da tafiya kafin ya samu kira daga wajen Mahaifiyar shi akan cewa me ya hanashi zuwa bayan Ikram ta shaida musu cewa shine yace ta zauna har sai yazo sannan zasu koma tare,
To bai zoba