Showing 132001 words to 135000 words out of 190771 words
da ake buk'atar shi a wajen sun gabatar dan haka aka tsaida rana nan da wata uku idan Allah ya kaimu da rayuwa,
Sai bayan da komai ya kammala kafin shima Baba Usman ya bijiro ma da Baba Adamu zancen son zuwan da sukayi can wajen su ayau dan su nema ma AK auren Aminatu suma,
Sun d'anyi maganganu dan ya shaida musu cewa Malam baya nan amma tunda har Allah yasa su sunzo nan ai basai sun basu wani wahala ba kuma tunda dai har su yaran sun dai daita a tsakanin su zaiyi ma Malam bayani idan sun tashi zuwa sai suzo suma kamar dai haka da duk wani abun buk'ata na sanya rana shi dai ya basu Meenal duk da cewa dama Meenal din tasu ce.
To an dai watse taro cike da tarin farin ciki na murnar arzikin da ake shirin kullawa, tare dukan su suka wuce wajen d'aurin auren ana gama wa kuma su brigadier suka juya basu kwana ba duk da cewa Sarki yayi musu tayin kwanan,
A gurguje.....
Gefen Amarya da k'awayen ta lafiya lau sukaci gaba da gudanar da shagulgulan bikin su an d'aura auren Jamila da Angonta Mustapha da rana bayan an sauko daga masallacin juma'a da yamma aka gudanar da kayatacciyar walima wanda ango da amarya suka halarta tareda abokan su,
anayin sallan magrib kuma angwaye suka kawo mota suka kwashi Amarya da kawayen ta zuwa GRA gidan amarya anayin sallan ishsha'i kuma suka k'ara kwasan su bayan an k'ara shirya amaryar zuwa wajen dinner, sai da aka kwashe yan uwa kaf kafin Amarya da kawayen ta suka fita daga k'arshe gaskiyar yan magana da suke cewa ko wacce mace ranar auren ta ana k'ara mata kyau domin dai wani irin kyau mai d'aukar hankali Meelat ta tsatso a wannan ranar, a cikin wad'anda suka zo d'aukar amarya har da AK sai dai shi ya shaida musu cewa ba d'aukar Amaryar Musty yazo ba ah ah shi yaxo d'aukar nashi amaryar ne tunda har ubanta yace ya bashi ta riga ta zama nashi kuma yanda kuraye sukayi yawa a wajen gara ya kula da kayan shi,
Sultana da Maryam ne suka rik'o Meelat tareda wata yar uwar su Meelat din suka fito da ita Musty dake cikin motar da zasu saka amaryar da kanshi ya fito ya tari abinshi ya janye ta zuwa cikin motar, AK dake cikin nashi motar ne shima ya fito a sanda ya hango Faisal na k'okarin sa Sultana da Meenal su shiga cikin motar shi,
Gaban Meenal din yasha fuska a d'aure yake cewa "ina kike shirin zuwa da wannan kwalliyar na fuskar ki"
"Me kwalliya na yayi yanzun kuma?"
"Amma ai nace miki bana son kina goga wannan abun a bakin ki a sanda zaki shiga cikin mutane koh?"
Hankacin shi ya ciro daga cikin aljihun rigar shi,
"Nidai dan Allah karka goge min ina son abuna a haka" ta fad'a tana tura baki,
"Aminatu" wata daga cikin kawayen su dake tareda Maryam a wajen motar Sadeeq ta kirata, dan haka saita juya da sauri tabar wajen tana mishi gwalo, shi kuma sai ya k'arasa wajen Faisal suna magana,
K'awar nata ce ke tambayan ta bayan ta k'arasa inda suke,
"Friend amma dai wannan yayan ki ne koh?" Ta tambaya tana nuna mata AK,
"Eh Yayana ne" meenal ta bata amsa,
"Yana da mata?" Ta k'ara tambaya,
"Ah ah"
"Oh saurayi ne kenan bashi da mata?"ta k'ara tambaya tana gyad'a kai,
"Eh saurayine" meenal ta k'ara amsa mata,
"To dan Allah friend kid'an gabatar dani a gunshi mana wallahi nidai ina son shi yamin shine dai dai kalar mijin da nike son aure" ta k'asa fad'a tana karye wuya alamun rok'o,
Fuuuu Meenal ta wuce tabar wajen a fusace zuwa wajen da motar AK yake tana isa ta bud'e bayan motar ta shiga ta kullo k'ofar motar da k'arfi a fusace,
Sultana ce ta k'arasa inda Yarinyar take tana dariya ta dafa kafadarta take cewa,
"Ke baki san shine mijin da zata aura ba shine zaki wani kirata kice kina son mijinta, gaskiya dai baki kyauta ba"tana gama fad'ar hakan ta wuce abinta ta shige motar Faisal,
Shiko AK ganin da yayi ta wuce su a fusace da kuma yanda ta bud'e bayan motar ta shiga hakan ne yasa ya juya zuwa wajen motar shima ya bud'e bayan ya shiga ya sameta tana ta faman cika tana batsewa,
"Ya akayi ne? Meya sameki?"
Sai da ta watsa mishi harara mai lafiya tana turo baki tace "duk ba kai bane,"
"Ni kuma mai nayi?"
"Eh ai haka zakace da ace baka fito daga cikin motar ka shiga cikin yan mata ba ai da bazata ganka ba balle harta wani cemin wai tana sonka" ta fad'a tana kauda kai gefe,
Murmushi yayi ita kuma Sautin murmushin nashi ne yasa ta juyo taci gaba da masifa,
Shidai bai kulata ba hartayi ta gaji ashe wai shirun da yayi mata kuma yayi laifi dan haka sai kawai ta kama murfin kofar da niyyar bud'ewa ta fice,
Fincikota yayi ta fad'o cikin jikin shi kuma yasa hannu ya kulleta gam a jikin nashi,
"Yi hakuri to naji nayi laifi in ma kince karmuje can d'in ai sai muyi zaman mu basai munje ba"
"Tab duk wannan kwalliyar da nayi ne zan wani zauna a mota bikin Meelat dina akeyi fa"
"Oh dama kwalliyar badan ni akayi ba kenan anyi ne dan wasu su gani, ai kin tunanin ma d'azun nace a goge jan bakin nan kika k'i"
Mutsu mutsu ta fara a jikin nashi tana son kwacewa,
"Nidai kabar min kwalliya ta kuma kana ganin duk sun wuce fa"
Sakin ta yayi da sauri ya fice daga motar ya zagaya gefen direba ya zauna bayan ya gyara rigar shi data fara yamutse wa sakamakon mutstsukan data sha a wajen Meenal,
"Anan zaki zauna ko zaki dawo nan ne?" Ya tambaya batareda ya waigoba ya kunna motar, tsallakowa ita kuma tayi batareda ta fita ba ta dawo gaban motar,
Tissue ta yago bayan ta zauna ta goge jan bakin dake bakinta sai da ya fita tass kafin ta maye gurbin shi da lips glows ta d'an k'ara goga hoda kad'an ta kuma gyara zaman d'aurin kanta, da gefen ido yake kallon ta harta gama basu yi tafiya mai nisa ba suka isa inda ake gabatar da Dinner d'in koda suka isa amarya da ango sun shige babu wasu mutane sosai a waje,
Bude kofar shi yayi yafita kafin ya zagaya ya bud'e mata nata side din ya mik'a mata hannun shi ta kama ya fito da ita, gefe ya maidata ta jingina da jikin motar shi kuma yasa kanshi cikin motar wani chain ya ciro a cikin dashboard ya fito dashi a hannun shi sai da ya maida kofar motar ya rufe kafin ya riko hannun ta na hagu ya mak'ala mata chain din da aka k'awata shi da wasu irin duwatsu masu gyalgyali, d'ayan chain din dake tare dana hannun ta makala a nashi hannun shima sai kuma ya cire wani d'an karfe k'arami dake matsayin mabud'in chain din ya saka a cikin aljihun shi,
"Menene wannan d'in?"
Ta tambaya,
"Idon ma tambayi kin d'auka zan barki hannu sake ne in mun shiga kiyi ta yawo idon kowa a kanki?"
"Wai shi yasa kasamin ankwa a hannu? Kai dan Allah yaya to haka zamu shiga ciki mutane suna kallon mu kuma fa harda yan gidan mu a ciki"
"Eh haka na yanke kinga idan muka shiga a hakan duk wanda yagan ki yasan cewa matata ce a tareda ni"
Kamar ta bude baki tayi ta kurma ihu haka taji sai dai kuma idan tayi mishi kuka ai ta bada kanta dan haka kawai ta bud'e yar k'aramar Purse din dake rik'e a hannun ta ta ciro face mask guda biyu, ta mik'a mishi guda d'aya itama tasa d'aya,
"Me kikeyi da facemask a cikin purse kuma?"
"Shi nasa d'azun da zamuje wajen walima dan ni bani da niqab,"
"Kuma sai kikafi yin kyau ma a hakan"
Sun gudanar da Dinner lafiya har zuwa kusan 12 dare kafin taron ya tashi masu komawa gidan Amarya aka wuce dasu tare da amaryar sauran jama'a kuma suka koma unguwar malamai, andai yi biki lafiya an kuma watse yan nesa dana kusa kowa ya koma inda ya fito,
*Muje a gurguje*
Bayan kwana biyu su Baba Usman suna ta jiran kira daga Baba Adamu dan suji yaushe ne zasu je tunda dai Malam ya dawo,
Shi kuma a gefen Baba Adamu abubuwan ne suka d'an sha mishi kai dalilin hakan ko zama bai samu sunyi da Malam ba balle kuma ya shaida mishi yanda sukayi a yayin zuwan su tudun wada neman auren Moon dan ko labarin neman auren ma a bakin Baba Lawal jama'ar gidan sukaji haka ko suka dunga kucin cina zancen da cewa ba'a kyauta ma Aminatu ba taya Sarki kuma zai koma yace yar uwarta yake nema da aure kuma,
Sun daiyi maganganu wanda hatta da uwar gida bata so hakan ba sai dai kuma tunda an riga an gabatar da komai har an tsaida ranar biki sai kawai ta bisu da addu'a allah yasa ita Moon d'in ta zama cikon farin cikin da Sarki ya rasa tsayin shekaru,
A gefen Salman ko ya riga ya gama yanke hukuncin tun karar Malam tunda gashi daga uwa har uban shi babu wanda ya d'auki maganar shi nason auren Meenal da mahimmanci balle wanin su ya shige mishi gaba amma gashi shi ai Sarki yaga yar uwar Meenal din yana so har an bashi,
Gafen Aliyu daya Hashim suma duk sun shirya tsaf dan zuwa gabatar da kai a gaban Malam domin suma sun bincika anan gida sun gane cewa har yanzun ba'a fara zancen auren Aminatu a cikin gidan ba dan haka kowa ya yanke hukuncin gabatar da kanshi kawai wata kila shine mai rabo,
A gefen Sheikh Naseer da Meenal kam Alhamdulillah yanzun abubuwa sun d'anyi sauk'i ba kamar kwanan baya dako zaman inuwa d'aya bata son yi dashi ba,
Tun dawowar ta gidan lokacin bikin Meelat bata yarda ta koma gidan Hajiya ba har yanzun dan yanzun ya zama gidan sirikan ta, kullum safe da yamma da ita ake karatu a falon Baba Malam kuma Sheikh ne Malamin, sosai malam yasa ido yake lura da yanayin kusancin dake tsakanin ta da sheikh d'in yanda suke mu'amala ya matuk'ar kwantar mishi da hankali dan haka yanzun ne dai dai lokacin daya dace ya agabatar da nashi tsarin a kansu,
Dan haka ba tareda ya nemi shawara da kowa ba kawai wata rana bayan sun kammala karatun su da maza keyi da dare kamar kullum idan an idar da karatun wanda Sheikh ke gabatar wa shi kuma Malam sai ya rufe da addu'a,
To yauma dai bayan sun kammala karatun anyi addu'a har mazan sun fara shirin fita malam ya dakatar dasu, dan haka duk suka dawo cikin masallacin suka zazzauna suna jiran jin me zai gabatar musu,
Gyarar murya yayi kamar yanda ya saba aduk sanda zaiyi magana kafin ya daura a yayinda ya maida kallon shi kan Sheikh yake cewa,
"Nasan zakuyi mamakin yanda na dakatar daku daga tafiya kuyi hakuri wani d'an sanarwa nike son yi"
Ba komai Malam duk sukace suna cigaba da sauraren shi,
Shi kuma yaci gaba da cewa,
"Alhamdulillah nasan dukan ku nan dai kun wayi wannan bawan Allahn da a yanzun shine mai gabatar mana da karatun tukan da mukeyi, to masha Allah ga wadanda basu san ko waye shi d'in ba shi d'in dai yarona ne domin ko d'an da kanwata ta haifane a can k'asar larabawa ya gabatar da karatun tukan shi, dan haka nike son yau a yau a gaban dukan ku ku shaida ni Malam Al mustapha na bashi auren d'aya daga cikin yayana mata dan bazan yarda yaci gaba da zama a matsayin gwauro ko kuma yabar garin nan batareda mata ba"
Kabbara gaba d'aya masallacin ya d'auka jama'a na fatan alkhairi da cewa kwarai hakan ne ya dace dama bai kamata abar Babban mutum babu mata ba, wani dattijo ne shima ya mik'e yake k'ara sanarwa cema shima yana da yan mata a gidan shi yana kuma rokon alfarma ko sheikh zaizo gidan shi ya duba cikin yaran shi shima, tunda koba komai ai Babban mutum kamar Sheikh mace d'aya bazata wadace shiba,
Duk fa yanda sheikh yaso ya zame sun hana shi damar hakan dan wani ma daya tashi cewa yayi shi kuma ya bashi gidan da zai zauna da matan anan cikin garin Zaria, kai kyaututtuka dai kala da kala Sheikh yasha shi a wannan rana data zame mishi tsaka mai wuya dan shi dai bai san ko wacce yar malam yake nufi ba tunda bai kira suna ba,
Wai shi da yake batun tattarawa ya koma Abuja shine ake batun yi mishi tarko a Zaria shi ina shi ina auren mata har biyu fisabilillahi.
Haka aka watse karatun ranar kowa na farin ciki shi kuma aka barshi cikin jimami, a wannan daren kaf unguwar ya d'auka cewa ai Malam yaba Sheikh mata kowa idan ya tambaya cewa wacece a cikin yaran gidan aka ba sheikh din sai kowa yace bai sani ba,
Kafin gari ya waye labari ya isa kunnen Salman Aliyu harda Hashim,
Dan haka gari na wayewa Salman ne ya fara isa falon Malam ya gabatar da kanshi matsayin mai neman auren Aminatu,
Shigar shi d'akin da gabatar da kanshi babu jimawa sai ga Hashim koda ya shiga ya samu Salman kuma hakan bai hanashi gabatar da kanshi ba shima a gaban Malam matsayin mai neman auren Aminatu shima,
Babu wanda Malam yaba amsa a cikin su har Aliyu shima ya iso shima dai yanda suka gabatar da kansu hakan shima yayi,
Sai da gama jin ta bakin su dukan su kafin yace musu duk suyi hakuri su koma zai nemi ganin Aminatun zai neme su daga baya,
Ana cikin wannan al ajabi ahalin gidan master suma suka iso gidan da rana tsaka,
Bash ne da iyayen shi hudu maza,
Sun gabatar da kansu a matsayin masu neman auren Aminatu suma sun kuma k'ara daba Malam din labarin abinda ya faru a baya wato lokacin da shi Bash ya rasata da irin jinyar da yayi ta sanadin rashin ta,
Sannan suka shaida mishi cewa su dai a shirye suke suna fatan kuma wannan karan za'aba d'an su.
*Ummiee ce*
[10/3, 10:34 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 42*
To suma dai daga bash d'in har iyayen nashi bayan malam ya gama sauraren bayanan su hak'uri ya basu akan zai nemi jin ta bakin Meenal din dan haka zai neme su daga baya,
Jin hakan sai su kuma suka rok'e shi akan ko Bash din zai iya fara zuwa wajen Meenal d'in?,
Malam yasan ko yace musu ah ah indai yaran yanzun ne yasan sai shi Bash din ya nemi hanyar da zai samu ganawa da Meenal din dan haka sai kawai yace musu babu damuwa yaba Bash din damar zuwa ya gana da ita,
To sudai sun tafi da hope d'in cewa za'a dace dan haka suka tafi cikin farin ciki.
A cikin gidan Malam d'in ko dama tun cikin dare har zuwa wayewar gari kowa hasashe kawai yakeyi akan wacece Malam zai had'a aure da Sheikh domin dai yanzun haka a cikin gidan Malam kawai yanzun haka suna da yan mata guda d'ai d'ai har 5 wadanda dukan su sun isa aure, duk da a cikin su akwai wad'anda aka fara zancen auren su amma sun sam tsaf Malam yana iya canza ra'ayin shi,
Tun cikin daren har gari ya waye musu kawai akeyi wannan idan yace wacce malam zai ba sheikh sai wani kuma yace ah ah wacce kaza dai sukafi dacewa ita da Sheikh sudai iyayen su mata babu wacce tace ko kanzil su yaran gidan da sirikan gidan ne kawai keta faman yin hasashen su,duk wannan hasashen babu wanda ya kawo zancen had'in Meenal da Sheikh dan a ganin su tunda akwai yan mata a gidan bai zama lallai malam ya kawo ta a lissafi ba,
Sai gashi basu gama hasashen nasu ba suka fara ganin jerin gwanon da akema falon na Malam yau,
Duk abinda ya faru a gaban Farouq da Sa'eed ya faru saboda zuwan Salman yayi dai dai da suma suna cikin falon na Malam kuma har sai da Malam ya sallami su Salman din suma suka bar falon dan haka su biyun su suka shiga da labarin cikin gidan,
Koda suka shiga falon Mommy Hauwa musu kawai akeyi dan tun safe Sultana ta tasa Fauxieyerh a gaba da tsokana akan cewa tasan had'in da malam yayi ita yaba yayan ta, suma kuma sauran yan falon duk sai suka yarda da maganar Sultana duba da cewa kowa yasan cewa akwai shiri sosai a tsakanin Sheikh da Fauxieyerh dan haka sai suka sata a gaba da tsokana cikin masu tsokanarta kuma harda Meenal da Moon ita dai Moon cewa tayi wannan had'i yayi dai dai dan dama mace inba irin Fauxieyerh ba babu wacce zata iya zama da Ya Sheikh ta dadin rai haba shikenan mutum ya maida kanshi ina zaka masallaci ina ka fito islamiya, dan haka sun san Fauxieyerh cema ba kowa ba duk da cewa
A sashen Baba Auta akwai Fauxieyerh da Fatima, sashen Baba Adamu kuma Rayhan, sai can sashen Malam kuma Akwai Aisha da Asma'u, amma duk sauran dai basuga dacewar su da Sheikh ba sai Fauxieyerh,
Suna cikin hirar ne su ya Sa'eed suka shigo ko zama basuyi ba Sa'eed ya fara kiran sunan Meenal,
"Kai yayan mu tun baka zauna ba daga shigowa ka faramin kiran mafarauta gani nan fa ko ka fara makanta ne dan na lura idan Maman twins tana kusa baka gane mutane"
Ta fad'a daga inda take zaune akan kujera Sultana na tsaye ta bayan ta tana mata kitson kalaba a kanta,