Showing 66001 words to 69000 words out of 190771 words

Chapter 23 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1549

ya kamata ta gano komai amma bata maida hankali a wancan lokacin ba.


Shiko Salman yana kokarin k'ara kiran wayar na Meenal ne shima kira ya shigo cikin wayar shi ana neman shi da gaggawa,
Bayan sun gama magana da wanda ya kirashi sai da ya k'ara gwada kiran number din yaji wayar a kashe sai kawai ya juya,
A zuciyar shi yake cewa shima dai bayan su zaibi gara aje can Zarian ayi duk wacce za'ayi dan shima fa a yanzun aure yake so ba kuma da kowa ba sai da Meenal dan haka in ita tak'i sauraron shi To cikin biyu ne zaiyi d'aya ko dai ya tunkari Baba Adamu ko kuma ya kai maganar wajen Malam kawai kai tsaye.

No editing 😣


*Ummiee ce*✍🏼
[9/10, 9:21 AM] Ummiee Zaria: πŸ”±βšœοΈπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦βšœοΈπŸ”±
*BOOK 2*

*PAGE 23*


Alaqa tsakanin Sarki da Moon zuwa yanzun zamu iya cewa abubuwa sun fara kan kama,
Domin da fari yayi zaton abun na wasa ne, irin ai tunda k'aramar yarinya ce kwana nawa ne zai shawo kanta idan ya gabatar mata da abunda ke cikin zuciyar shi a kanta,
Sai gashi kamar ita kuma tasan manufar shi a kanta domin dai tun ranar daya sha gaban ta da mota sai ta fara wasan buya tsakanin ta dashi,
Wanda hakan ne kuma yasa dole badan yaso ba ya nemi hutu a wajen aikin shi ya zauna a Lagos d'in domin ya kuduri aniyar yad'a manufar shi da kyau bazaiyi wasa da damar shiba har sai ya samu abunda yake muradin mallaka, dan wani irin so da kaunar ta mai tsanani ne yake jin suna azalzalan shi.

Acan Kaduna kuma tuni ya nemi muhallin da Teemah zata zauna a ciki in sun koma saboda ya faranta mata kamar yanda ya shaida mata kuma gidan irin wanda take da muradi ya shiya sai dai kuma abunda bata sani ba Sassa ukune a gidan wato dai d'aya nashi biyun kuma na matan shi,
Salman ke kula da gyaran gidan dan yana son inya tashi tafiya su koma gaba d'aya kawai kafin nan kuma zaiyi k'ok'arin saito kan Moon kai shi in so samu ne ma baik'i a fara tsaida magana kafin ya koma ba,
Sai dai ita gimbiyar da alama zai sha fama da ita, saboda yanda take nuna mishi bata son wata doguwar alaqa wacce ta wuce na gaisuwa ta shiga tsakanin su,
Sai dai kuma duk yanda Moon d'in taso yakice shi hakan ya gagara dan sosai yake nuna nacin shi a kanta,
Sai gashi a hankali a hankali Sarki ya dunga cusa kanshi wajen Moon d'in harta fara sake jiki dashi batareda ta ankara ba,
Ya zamana tun tana basar dashi dan bataga dalilin kulawan da yake nuna mata da kuma yawan bibiyar al'amuranta da yake yiba har tazo dan dole ta fara sakin jikin dashi ganin ko sun had'u iya gaisuwa hirar wajen aiki dana karatu sune kad'ai hirar dake gudana a tsakanin su sai kuma wani lokacin yakan tuna mata kiriniyar da sukayi a shekarun baya lokacin daya fara sanin ta,

A kance zuciya bata manta abunda take so koda ta manta shi na d'an lokaci ne, hakan ne yaso faruwa da Moon domin dai a wannan yawan had'uwar da yanda Sarki ke k'okarin cusa kanshi wajen ta dan ganin ta sake jikin ta aduk lokacin da suke tare, sai gashi bata ankara ba shi d'in ya fara zama wani b'arin farin cikin da zata iya cewa ta rasa a rayuwar ta,

Bazata ce bata da farin jini ko kuma ta rasa masoya ba,
Ah ah ita dai ra'ayin kanta ne yasa har zuwa lokacin bata wani sake ma maza fuska, ita d'in lauya ce mai kare hakkin mata dan haka a kullum suke had'uwa da cases kala kala na matsalolin da mata ke fuskanta a gidan aure su wanda zakuga wani baza'a samu dai daituwar kaiba har sai an kashe auren,
Wannan dalilin shi yasa ta quduri aniyar bazata iya auren namijin da bata yarda dashi ba, tana son namiji wanda zai sota ya kuma zama mai tausayinta wanda zai kula da ita wanda zai tsare mutuncin ta dana iyayen ta ya kuma bata farin ciki ita da yaran da zata haifa mishi,

Tana da k'ira irin na manyan mata masu cikakkiyar diri, hakan ne kuma yasa ko kad'an a tsarin ta babu auren Saurayin da baikai irin 38 zuwa 40 ba, tsayayyen namiji take son aure ba muna maza ba, sai gashi a yanzun da take jin cewa lokaci yayi daya kamata itama ta fidda mijin aure shi kuma Sarki ya fad'o cikin rayuwar ta yana neman yayi mata Kane Kane,
To ina dalili fisabilillahi idan ana ganin ta tareda shi koda yaushe ai d'auka za'ayi ko saurayin ta ne,
Kunga kenan duk masu shirin zuwa su gabatar da kansu a wajen ta ai sare musu guiwa zaiyi yasa su fasa fito mata da abunda ke cikin zuciyar su shi kenan ita kuma bawan bawan,
Dan haka dole ta nemi matakin d'auka tunda wuri,
Dafari matakin data fara d'auka shine d'auke k'afa ta hana kanta zuwa wajen da yasan tana zuwa kullum tunda anan yake samun ta,

Sai ya zamana shi kuma daya fahimci cewa saboda shine ta d'auke k'afa da zuwa wajen kafin lokacin tashin ta aiki yayi yake zuwa wajen ya siya mata abubuwan da take buk'ata wanda yaron wajen ya shaida mishi sai ya aika mata dashi har office,
Idan kuma akayi rashin sa'a bata office ta koma gida har gidan yake kaiwa yaba masu gadi su bata inji shi,

Wannan abu da yakeyi ya k'ara jefa zuciyar ta cikin mamakin shi kwarai,
Ya akayi yasan cewa tana yawan zuwa wajen?
Ya akayi yasan gidan su?
Ya kuma akayi yasan wajen aikin ta?
Wadan nan amso shin duk tana buk'atar jinsu daga wajen shi,
Domin dai inba wanda ya maka farin sani ba ko kuma yasa aka mishi bincike akan ka bai kamata ace mutum yasan yanda kake gudanar da rayuwar kaba.
Duk yanda taso ta boye mishi kanta babu hali domin wani lokacin sai tana office dinta tana aiki zaije yasa a kira mishi ita, har ya zamana yan office d'insu sun sa musu ido da zarar yaje ake ce mata ga bak'onta ya iso,
Ganin babu sarki sai Allah kawai sai itama ta share taci gaba da zuwa can d'in data dena zuwa saboda shi,
Sai ya zamana tun tana d'ariΒ² dashi har aka kai matakin da dan dole tazo ta sake dashi,
Sai dai kuma koda ta tambaye shi yanda akayi yasan gidan su dama wajen aikin ta, bai wani tsaya ya bata amsa gamsasshiya ba, iya ka dai yace mata,

"Aiba ku lauyoyi kad'ai bane kuka san kan yanda ake gudanar da bincike ba"
Ita kuma tun daga ranar bata k'ara tada maganar ba, dan tasan dai bazai shigo rayuwarta dan ya cutar da ita ba duk da dai ita tana cutuwa da hakan, dan a kullum abubuwan da takeji a kanshi k'aruwa sukeyi daurewa kawai takeyi bata tab'a yarda ta nuna mishi ba shi yasa sau tari take gujema had'uwa dashi.
Tunda ya fahimci cewa soyayyar ta ga wajen da take zuwa kullum sai ya zamana shima ya maida gun wajen zuwan shi,
Can suke had'uwa zasuyi odan abunda suke so suci in lokacin tafiyar ta gida yayi zai rakata har kofar gida kafin ya juya ya koma,

Daya fahimci cewa Teemah ta fara sa mishi ido akan yawan fitan da yake yi kusan kullum sai ya canza salo saboda dai a yanzun da take d'aukar al'amarin shi da mahimmanci shima kuma bazai so yayi wani abun na rashin kyautawa a gareta ba kodan saboda halin da ciki da take d'auke dashi ya ke jefata na yau lafiya gobe kuma babu tunda take haihuwa bata tab'a yin ciki mai tafe da zazzafar laulayi ba irin wannan dan haka shi kanshi ba k'aramin tausayinta yakeji ba, dan kullum addu'a takeyi Allah dai yasa yan biyune kuma mazaπŸ₯°,
Ganin tana damuwa da yawan fitan nashi, sai ya zamana wani lokacin ma tareda ita zasu fita sukan isa can d'in da wuri kafin Moon ta iso, duk ranar daya je wajen da Teemah baya tab'a bari Moon ta gansu domin kujerun dake can cikin lungu yake kama musu sai dai shi yakanyi zaman ne yana kallon kofar shigowa wajen,
bazasu bar wajen ba kuma har sai ita Moon ta wuce tukun,
Ita kuma idan bata ganshi ba wani lokacin takan d'an bata lokaci bata barin wajen da wuri,
Bata da number din shi har yanzun balle tace ta kira wayar shi dan taji ko lafiya,
Koda ma ace tana da number din bai zama lallai ta iya kiran ba dan har zuwa lokacin bata san matsayin da zata ajiye sabuwar alaqar daya ke kulluwa tsakanin ta da Sarkin ba,

Sai dai ta sani tana matuk'ar tsintar kanta cikin farin ciki da jin dadi aduk lokacin daya nuna kulawar shi a kanta, kullum takan hana kanta zak'ewa a kan yawan tunanin shi, duk da dai har yanzun bai fito fili shima yace ga abunda ke cikin zuciyar shiba amma tana matuk'ar tsoron ranar da zai bayyana mata hakan, ita dai kawai tana tareda shine amma bazata ce tana son alaqar su ta yanke ko kuma alaqar tayi tsayi ba saboda idan har hakan ta faru to bata san da wani idon zata kalli yar uwarta Meenal ba ace ita Moon d'in tana soyayya da tsohon mijin yar uwarta,

Dan haka sai kawai tayi waje na musamman ta ajiye shi a matsayin Ya'ya kuma abokin shawarar ta.


*A can garin Kaduna kuwa, Washe gari*

Koda asuba tayi duk yanda Hajiya takai ga iya sammakon tashi yau Meenal wacce tayi bacci rabi da rabi ta riga Hajiyar tashi tuni,
domin dai Allah ya sani ta dad'e bataga daren da yayi mata tsayin da gari yak'i wayewa da sauri ba irin wannan dare,
Domin dai gaba d'aya ji tayi kamar kanta na neman juyewa, akan tarin kalaman daya zazzage mata shi ko kananun shekarun ta bai duba ba zai ajiyeta ya dunga zaro mata kalaman da tunda Mommy ta haifota wani namijin bai tab'a furta mata suba,
Tasan tayi soyyaya a shekarun baya, amma kuma babu soyayyar da yafi tsaya mata a rai kamar Soyyayarta da Bash, Allah Sarki ko yana wata duniyar yanzun Allah ne masani,
Sai dai koshi iya kanshi da ita kalmar I love you Meenal su sukafi yawa a cikin kalaman shi,
Bai tab'a zaunawa ya karanta mata kalaman soyayya mai tsumawa da tsotse ruwan jiki irin wanda AK ya zazzage mata har takejin kanta yana neman fashewa ba,
Koda ace manya na zagewa idan sun samu waje su shek'a k'arya son ransu ta tabbatar da cewa AK bazai tab'a zaunar da ita dan ya k'aranta mata zantukan nan a matsayin k'arya ba dan ta hango tsantsar gaskiya a cikin idanuwan shi, sai dai ita kuma abun yazo mata a haguncen da har yanzun take ganin kamar bai kamata tayi saurin yarda ba,
Ita wai wani tsautsayi nema ya kaita zuwa ta fad'a mishi abunda Sultana tace nema wai?
Kenan da gaske ne kishin nashi takeyi? To in kishin ne mai yasa sai shine k'adai zatayi kishi ne wai?

tun cikin daren da bacci ya gagari idon ta saboda tsabar firgicin data shiga sai kawai ta tashi ta had'a komatsanta tsaf ta killace su a waje d'aya kafin ta koma ta k'ara kwanciya ita da a kullum Hajiya ke fama da ita akan wankan wuri a yayinda ta tashi yin sallan asuba,
sai gashi yau koda ta shiga da niyyyar alwallah kawai kamar yanda ta saba wannan ranar dai bata fito ba sai da ta sheqo wanka,

Saida ta tashi Hajiya wacce ke baccinta a tsanake kafin ta koma gaban mirror tayi zaman shafan mai kafin Hajiya ta fito tuni ta shirya tsaf,

Koda aka fara kiran Sallah ta tabbatar da cewa lokacin fitowar AK zuwa masallaci yayi kuma bazai fitaba har sai ya lek'o su sai itama ta haye kan dadduma ta kabbarta nata sallan,
Bayan ta idar da raka'atainul fijjir ta tabbatar da cewa zuwa lokacin ya isa masallaci sai ta mik'e kayan Hajiya ta had'a suma tsaf sannan ta kwaso kayanta itama ta fito da akwatin ta dana Hajiyar takai cikin mota ta adana tana dawowa saida ta biya ta d'akin su Meelat dan tabbatar da cewa sun tashi,

sama sama sukayi gaisuwa a tsakanin su kafin ta shaida musu cewa su shirya fa dan yau da wuri zasu wuce gidan rasuwar,

"Me zamuje muyi da wuri kuma bayan ance sai zuwa karfe 10 za'ayi addu'a?,
Gaskiya inaga dai sai dai in kece zakiyi gaba domin dai ni ina buk'atar ganawa da mai gidan nan ayau kafin mu tafi,ai laifin kine tunda kin san halin da nike ciki tun jiya naso in gabatar mishi da abunda ke cikin zuciyata akan shi amma kika janye shi, ke shikenan tunda baki shirya amsar soyayyar kowa ba nima bazaki bari in gwada sa'ata ko zan dace ba"
Sai da ta matsa kusa da Meenal sosai kafin taci gaba da cewa,

"Sister ki taimaka min kisa baki tunda naga kina da kusanci dashi sosai nidai ina son shi, amma in shi yace baya sona zan hak'ura, sai dai kafin in hak'uran sai na gwada sa'ata,
Yanzun kuma idan na yarda nabar gidan ba tareda nasan matsayata ba ai kuma rashin nasara tace kawai zata tabbata"

Cewar Sultana wacce fitowarta daga cikin bathroom kenan taji Meenal din na sheda musu batun fita gidan da wuri.

"Wannan kuma damuwar kice ke d'aya babu ta inda ta shafeni, tunda dai kince kinji kin gani aiga fili ga mai doki, nidai karma kisani a cikin maganar nan kinji na fad'a miki"

Tana gama fad'in hakan ta fice daga d'akin, koda ta koma d'akin data kwana makewayi ta shiga ta kuskure baki bayan ta fito ta koma kan daddumarta ta tayarda sallan asuba,

Bayan sun idar Hajiya ce ta d'ago tana kallon ta bayan ta amsa gaisuwar da Meenal din ke mata,

"Ya akayi ne wai naga sai faman shiri kike da sassafe, ko wani abu ya faru ne?"

"Ah ah Hajiya so nike dai mu wuce da wuri muje ko akwai aikin da zamu iya kama musu tunda kinsan karfe 10 ne za'ayi addu'ar"

"Oh Allah yau kuma keda kanki kike batun zuwa ki kama ma wasu aiki Meenal?
Indai dan aikin ne ai gara ki nemi waje kiyi kwanciyar ki dan tun jiyan sun riga sun d'auko masu aiki ko munje yanzun sai dai mu zuba musu ido dan haka gara muyi zaman mu kinga zuwa k'arfe 8 haka sai mu fita,"

Duk yanda ta tasa Hajiya a gaba da magiya k'iyawa tayi dan dole tanaji tana gani taci gaba da zama a cikin d'akin ita d'aya,
Gudun karma ta fita su had'e dashi dan bata san kalar kallon da zata mishi ba,
dan Hajiya komawa falo tayi ita dasu Meelat sukaci gaba da gudanar da harkar gaban su,

Zama taci gaba dayi a d'akin tana chatting da wayarta karfe 8 dai dai ta fito daga cikin d'akin rataye da hand bag d'inta a kafad'a ga mamakin ta sai taga wai a lokacin nema suke jera kayan kari akan dinning bayan kuma tun asuba take jin zuruntun su,

"Wai dan Allah har yanzun baku gama ba dama?,
miye kukeyi tun d'azun dana muku magana ne bayan nace muku ina so mu wuce da wuri, Hajiya kefa kikace zuwa karfe 8 sai mu fita yanzun kuma karfe 8 harda mintoci amma ko karyawa bakuyi ba"
Ta k'arasa fad'a tana b'ata fuska.

"Yauni nike ganin ikon Allah wajen yarinyar nan, Meenal wai ko akwai abunda kika manta dashi a gidan rasuwar can jiya ne?
Inba haka ba nidai banga dalilin wannan azalzalawan da kikeyi mana tun da garin Allah ya waye ba, to in zamu takura kine ai gara kiyi gaba koh, mu in yaso mazo daga baya in kuma zaki jira harmu gama mu tafi taren to wannan kuma ya rage naki!"

Hajiya ta fad'a tana cigaba da shan kunun gyad'a da kosan da Hajara matar Mansoor ta kawo mata shi d'azun nan.

"Taimaka ki lek'a d'akin yayan ku ki tasomin shi yazo yasha kunun nan tun yana da zafin shi dan yana son kunun gyad'a sosai,
Tunda ya dawo daga masallaci ya shige bai k'ara fitowa ba"Hajiya ta fad'a batareda ta kira sunan kowacce a cikin suba,

"Hajiya bari in kira miki shi ita sai ta zauna ta karya d'in kafin ta wuce tunda sauri takeyi karmu b'ata mata lokaci nidai Hajiya kin san bazan yarda mubar gidan nan batareda kin gabatar dani a wajen shiba dan Allah kinji Hajiya,"
Juyawa tayi gefen da Meenal take tana tambayar ta

"Sister me zaki sha kunun gyad'an ko Tea zan had'a miki?"

Fuuu Meenal ta juya zuwa d'akin nashi a fusace bata ko kalli inda Sultana take ba,
Tana wucewa su kuma suka fara mata dariya.

"To wai ku nace dama haka akeyi shi kenan da zarar namiji yace yana son mace sai ta fara fushi kamar zata kaima mutane duka?
Naga dai tun jiya sai wani faman kumbureΒ² take ma mutane in bata son shi basai ta shaida mishi ba ko ana yin soyayya dole ne?"
Hajiya ke tambayar su,

"Kishin shi dai takeyi ba komai ba wallahi, ke kuma Sultana ya kamata kid'an sarara mata haka kafin ta kasa rik'e fushin ta akan ki"
Cewar Meelat

"Allah babu wani sararawar da zan mata har sai ta furta cewa da gaske itama tana son shi tukun dan nima ina taya shi kishi,
amma muddin bata amsa cewa tana son shiba nima bazan barta ta huta ba, so nike inga hankalin ta ya tsayu a waje guda tukun"

Ita kotanayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login