Showing 3001 words to 6000 words out of 190771 words
mace zata fara hayayyafa itama,
A sanda ta fara haihuwa itama zatayi kokari ne wajen ganin taba nata yaran kalar tarbiyar data samu tsayin rayuwar ta.
Mace ta kasance halitta mai sanyi ta yanda duk abunda iyayen ta suka gabatar mata koda bashine ra'ayin ta ba, gudun b'ata musu kansa ta amshi abun da hannu biyu takuma rayu dashi tsayin rayuwa,
Sab'anin namiji,
Yara maza suna da taurin zuciyar da idan suka ki abun wasun su ba lallai ne su iya daga idanun su suyi duba da abun ko mai nene ba,
Idan kuma an samu masu biyayya zasu amsa din kamar yanda shi Sarki yayi biyayya ya amsa amma daga karshe ya jingine ta duba da cewa ita d'in ba zabin shi bane na iyayene abunda ya zamar mishi dole dama shine yayi musu biyayya kuma yayi tunda ya amshi auren,
Kwarai ina ma yarana mata auren wuri,
Sai dai kuma kafin auren saina bincika waye shi mijin da zan d'auki yata inbashi?
Shin ya cancanta ko kuma a'ah?
Ya addinin shi? Ya kuma nasabar shi? Shin zaima iya rikemin ita ya faranta mata ya kula wajen sauke hakkokin ta?
Sosai nake tsayawa in nazarci mutum kafin in bashi auren yata ciki kuma harda lura da halin ita yarinyar domin dai bazaka d'auko wuta da wuta ka had'a waje d'aya sannan Kayi zaton samun salama ba,
Tsayin lokaci da muke auran yaran mu babu wacce ta tab'a fuskantar wani kalubalen daga wajen mijin da muka zab'a mata alhamdulillah muna alfahari da hakan,
Amma abun mamaki sai auren da muka had'a a tsakanin yaranmu wanda zamu iya kira da tuwona maina shine a yau muka taru saboda shi,
Wa'iyazubillah wannan abu sam baimun dad'i ba,
Ba kuma na ganin laifin kowa sai ku dai ku biyun nan domin ni dai yata nasan kalar tarbiyar dana bata kuma Alhamdulillah duk da bason d'an ku takeyi ba tayi biyayyar zama dashi na tsayin shekaru ko sau d'aya batayi tunanin kawo min karar shiba"
Ya k'ara sa fada yana nuna uwar gida da malam sulaman da hannu,
Baki malam Sulaiman ya bude zaiyi magana amma malam ya tari numfashin shi da cewa.
"Bana son jin ta bakin kowa tukun ku bari in gama nawa maganar,
Ku kun sani cewa zumunci shine abunda na duba kafin in amince da batun bama danku auren yata domin ko babu komai shima din nawa ne dan ban manta cewa nine na amso mishi auren shi na farko ba,
Duk da tarin nakasun dake gareshi haka na ture na biye muku na b'ata ran uwata badan ina soba sai dai nima a lokacin idanuna sun rufe da son ceto ta daga halin ciwon da likita ya tabbatar da cewa aure shine maganin shi,
Kafin ku nuna kuna buk'atar a had'ata dashi wasun ku da dama sun fito sun nuna kwadayin su nason auren ta,
Amma zumunci yasa haka nan na runtse ido naba na kusa dani nayi amfani da kalmar nan da yan magana ke cewa duk dadin inuwar gemu bai kaiga makogoro ba,
A lokaci na farko dani da kaina na assasa auren zumunci a tsakanin yaran mu, a zatona hakan zai kara zumuntan da iyayen mu sukayi tsayin daka wajen ganin kafuwar shi a tareda mu.
Babban abun bak'in cikin shine yanda ya zaman wai ku iyayen su mata kuka kasa gane wani irin zama yaran nan suke gudanarwa tsayin shekarun nan,
Ni nayi ma yata aure a zatona auren nata zai zama waraka a gareta, ashe aikin banza ne shi mijin ajiyeta yayi kamar ka d'auki kudi ka zuba a asusu kasan babu mai tab'a maka har sai randa kai ka buk'ata,
To Alhamdulillah dukan mu dai nufin alkhairi mukayi, na kuma gode Allah daya tsaremin uwata duk da halin da take ciki amma allah ya kiyaye ta bata fad'a cikin wani halin na daban wanda bai dace ba,
Ke kuma bayan kin fahimci abunda ke faruwa dake da kakarta mai makon ku kawo mana maganar gaban mu mu iyayen su mu d'auki matakin daya dace a ah sai kuka nuna mana halin ku na mata kuka yanke hukunci kai tsaye,
Ita ta d'auke jikarta zuwa gidan ta ke kuma kika sa naki d'an a gaba ya rubuta mata takardar saki, to shin wai ma kafin ya saketa d'in kin tuhume shi cewa yana son ta ko a'ah?"
Ya kare maganar da maida tambayar shi akan uwar gida,
"Ayi hakuri Malam amma nidai nayi la'akari ne da cewa inda yana son ta da ba'a d'auki tsayin shekarun nan suna tare kuma ace babu abunda ya shiga tsakani ba, domin ko ban tambaya ba a bayyane yake cewa harda rashin so ya shiga cikin al'amarin nasu"
Uwar gida ta bashi amsa.
"To ai ba shi kadai yake da hakki ba ita Meenal din kuma kinsan meye a nata zuciyar ne?
Wata kila tana son shine shi yasa har tayi hakurin zama a hakan ba tareda ta sanar da kowa irin zaman da sukeyi ba"
Mai makon uwar gida ta bashi amsa wannan karan Hajiya ce tayi tsalam da cewa,
"Ah ah kam wallah akai gaba jikata ma ba son shi take ba, zaman hakuri dai tayi dashi yanzun kuma mai afkuwa ta afku aure ya k'are dan haka kowa yayi ta kanshi,
Kee Meenal bazaki bud'i baki ki fada musu cewa ba kya son shiba sai sun kara k'ak'aba miki shi abu dai kamar dole?"
Ta fada a tsawace tana kallon meenal din,
"Eh Baba Allah kuwa nima bana son shi dan Allah karku matsa min cewa saina koma, kuyi hakuri in kun bani umarni bazank'i biba sai dai zan koma zama dashi ne kawai badan ina soba kamar yanda shima ya tabbatar min da cewa har yanzun ban canza daga matsayin k'anwa a wajen shiba"
Ta k'arasa fad'a cikin muryar rok'o adanuwan ta a kasa batareda ta iya kallon kowa a cikin suba.
"To kun daiji da kunnuwan ku atoh itama jikar tawa bata so, da dai an mata dole amma yanzun kam babu mai karayi mata dole akan auren wanda tace bata so shima kuma din ba son nata yake ba,
Yanzun kuma kai ka gama jawabin cewa kana bada auren yaran ka mata ne ga mazajen da suka cancan ta, dukan mu nan kuma mun shaida cewa yaran nan basa bukatar auren, saki kuma ya tabbata"
"Tashi kije ciki Mamana babu wanda zai miki dole tunda bakya so, Allah ya miki zabi mafi alkhairi, Allah kuma ya albarkacin rayuwar ki hakika ina alfahari dake"
Da ameen sauran jama'ar dake wajen suka amsa.
Dan haka itama Meenal din ta mik'e da niyyar barin falon,
"Ke jirani mu tafi kinji dan dama ba wani karin arziki nayi ba, gara in koma gida in samu inci in koshi tunda Allah ya taimakeni komai yazo karshe yau dai kam bacci zanyi babu jimami"
"Meenal bazata koma tare dake ba Hajiya nan dai gidan ubanta zata ci gaba da zama inda ta rayu tun bayan haihuwar ta, yanzun kuma dan auren ta ya mutu hakan baya nufin zan barta ta koma wani wajen daban da zama, dan a wajena ita din har yanzun yarinya ne dole ta dawo gaban mu muci gaba da kula da tarbiyar ta kafin allah ya fiddo mata wani mijin tayi wani auren"
Kafar wanda ya zabge fuskar Hajiya da mari haka taji saukar maganar shi a cikin kunnuwan ta,
K'ifi k'ifi ta farayi da ido harshen ta har yana hardewa wajen furta cewa.
"Kai Malam Almu ka kiyayeni ka fita idona in rufe tun wuri,
Harni ce zaka kira gidana da wani wajen, kace wai jikata bazata je wani wajen ta tareba,
Nafa gaji da mulkin mallakar da kake gwadamin tsakanina na jikokina,
In mantawa Kayi bari in tuna maka cewa ni nan dai Hajiya Aminatu da kakeji da gani nice nan na haifo Hauwa'u Jidda uwar data tsugunna ta haifo Meenal, yanda nike da iko da Jidda haka nike dashi akan yaranta,
Tun tuni da nake kauda ido akan hukuncin da kake yankewa a rayuwar yarinyar nan darajar Mukhtar kake ci,
Amma yanzun kam tabbas idan ka matsa a shirye nake domin yin fito na fito da kai, wato taci gaba da zama anan haka nan ita zata k'are rayuwarta bazata samu kula na musamman daga gefen uwa mace ba,
Tunda aka haifo yar nan ka kankame ko ina ka hanata shakuwa da uwarta,
Wanda rashin shakuwar nasu shi ya taka rawa wajen lalacewar auren da kuka mata dan da ace akwai shakuwa tsakanin ta da uwarta tabbas bazataki shaida mata halin da take ciki a zaman auren ta ba,
Ko kai dan kana ganin kafi kowa kusanci da ita a naka zaton duk wani damuwarta idan ta taso kai zata tunkara kai tsaye,
To ga karamin misali nan ai ka gani tunda ga damuwar nan amma duk ta tsallake ku duk yawanku a gidan nan ta bini can wani wajen daka kira ta maida min damuwar ta,
Dan haka komawar Meenal gidana kamar anyi an gama dan koshi uban daya haifeta shi Auta bai isa ya hana ni rikon taba wannan karan atoh"
Baba Adamu ne ya shiga maganar da cewa,
"Kiyi hakuri Hajiya bazamu hana ta zama a wajen kiba tunda kin bukaci hakan Allah ya tayaki riko,
Ya'ya Kayi hakuri dan Allah su tafi d'in koba komai a yanzun nasan ita Meenal din zatafi sakewa acan fiye danan, da in ta zauna tunani ma na iya sata a gaba kuma muma bazamu so ganin ta a wani yanayi ba"
"To sai dai ta zauna na wani d'an lokaci amma ba wai zaman din din din ba, kai ka sani yaran mu basa tab'a zama a wani wajen aure kadai shike rabamu dasu"
"Ka daiji da shi" hajiya ta fad'a a yayinda ta riko hannun meenal da niyyar barin falon,
Har takai bakin kofar falon ta juyo tana kallon uwar gida,
"Nace ba! Kar kuce ban fad'a muku ba cikin satin nan zan tura a kwaso min kayanta dake can gidan, dan ba'a barsu babu kowa a gida kayan makudan kud'i su lalace a iska ba"
Suna fita daga falon motar Hajiyar da direban ta ya tuko su suka shiga ya k'ara jansu domin komawa inda suka fito,
A hanya ko sai mita take akan bazata k'ara yarda Malam yaci gaba da mulki akan jikokin ta kamar wani shine uban su ba,
Yayin da a can falon kuma bayan fitar su Hajiyan suma uwar gida da mai gidan ta hakuri suka k'ara ba Malam din da rokon cewa suna fatan bazai rikesu a zuciya ba balle har hakan ya tab'a zumuncin su,
Malam ya musu nasiha sosai sannan ya k'ara jan hankalin su akan kula da addu'a akan yara, kar kaga cewa yaran ka sun girma Kayi zaton cewa shike nan sunyi hankalin da zasu kula da kansu balle kuma hakan ya d'auke hankalin ka akan yi musu addu'a da nema musu kariya akan sharrin masu sharri,
Domin koda Allah ya hada miji da mata nagari tofa yakan iya haduwa da shedanun abokai,
Shedaniyar kishiya,
Shedanun kawaye,
Mahassada dai suna a ko ina wasu ma yawanci dasu muke rayuwa amma bama tab'a sanin hakan har sai ranar da Allah ya kaddara tonuwar asirin su,
Dan haka ya kamata iyaye suyi tsaye wajen koyama yara addu'a tun daga yarinta har zuwa girma,
A kuma dunga kiyaye azkar safe da maraici, sannan sadaqa tana maganin masifa Allah kuma ya tsare mu da tsarewar sa ameen,
Ya dai musu matashiya sosai sun kuma yaba sunyi godiya kafin suka mishi sallama suka wuce zuwa gida,
Itama kuma Innar yara ta koma cikin gida,
Karfe 12 kamar yanda ya buk'ata duka yaran gidan maza da masu aure da marasa shi ba iya kuma yan cikin gidan nashi ba duk yaran ahalin maza yasa aka kira mishi illah wadanda basa gari ne kawai basu hallata a wannan kiran na Malam ba,
Bayan taruwar su yayi amfani da wannan damar bayan ya shaida musu barakar data kunno kai a cikin a halin na mutuwar auren Meenal wanda babu wanda yaji dadin hakan a cikin su,
Yaja musu kunne sosai tunda masu auren harma da samarin cewa duk fa wanda yasan zaiyi aure to ya d'aura damarar zama da Matar har zuwa sanda mai rabawa zai raba domin su dai a ahalin su ba'a musu tambari ko shaida akan sakin auren ba tun daga kan kakannin su har zuwa kan iyayen su da kuma sudin kan su,
Ba kuma zasu zuba ido hakan ya faru akan yaran suba,
Na Sarki da Meenal sun d'auke shi a matsayin kaddara amma sufa sauran kar suyi duba da cewa ai sarki ya bude musu kofa ne suyi zaton cewa suma zasubi sahun shi babu wannan maganar,
Domin dai su dama yaran maza ba kamar mata bane ko wanne ana bashi damar ya zab'o Matar data mishi ne kafin a aura mishi,
Daga karshe suma Malam ya musu tuni akan rike ibada da kula da addu'a kana kuma ya k'ara jan hankalin su akan rike zumuncin dake tsakanin junan su,
Domin yana fatan zaman lafiya da fahimtar juna ya tabbata a cikin ahalin shi ko bayan kasa ya rufe mishi ido,
Haka dai a ka tashi wannan taro jiki a sanyaye kowa na mamakin ya akayi auren Sarki da Meenal ya mutu,
A wannan rana dai mutuwar auren shine ya zama labari mafi zafin daya dunga watsuwa a tsakanin ahalin.
#No aditing ๐
#Team AK
#Team Sheikh Naseer
#Team Hajiya
#Team Malam
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*~{{ MY FAMILY}}~ BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{{UMMIEE ZARIA}}~*โ๐ผ
*Page 3.*
*AK d'an mai karfi, da Yusuf wase* kuwa kasancewar basu bar garin Kaduna da wuri ba hakan yasa basu samu damar shigowa cikin garin na Zaria ba sai gaban nin magariba,
Hakan nema kuma yasa koda suka iso basu samu damar shiga gidan na Hajiya ba sakamakon tsayawa gaisawa da matasan majalisar nasu da sukayi, wanda gaisuwan nasu shiya kai su har zuwa lokacin sallan Magriba to bayan an idar da Sallah din ma da kyar Mai Jama'a ya samu ya zare jikin shi a cikin jama'ar shi domin Yusuf dama suna fitowa daga masallaci ya wuce cikin gidan bai tsaya a wajen ba.
Kamar wanda magnet ke janshi haka ya samu kanshi da d'aukin zuwa sashen na Hajiya fatan shi dai kawai shine Allah yasa yarinyar nan itace abu na farko da zai fara yin tozali da ita a sashen,
Dan haka gudu gudu sauri sauri haka ya fad'a sashen shi turaren shi ya dauka ya k'ara feffesawa had'ida gyara zaman hulan shi kafin ya fito kai tsaye zuwa sashen na Hajiya cike da takun shi na mazajen dake ji da kansu,
Sai dai tun kafin ya k'arasa ya farajin hayaniyar Hajiya inda take cewa...
"Shike nan duniya ace mutum bazaici abincin kwarai ba rayuwa sai mace tasha tea da safe tea da rana tea da dare uwa dai wata jinin larabawa ko buzaye? Takwara indai baso kike ki k'arasa karmashewa ta yanda ubanki Almu zaiji dad'in fadamin maganar banza ba ai kamata yayi ki ceci kanki ki bani had'in kai ki dunga cin abunci masu gina jiki ta yarda ko mak'iyi yaganki yasan cewa zawarci ya amshe ki, ke bakiga mazan yanzun sun fison mace mai d'an mulmulallan jiki ba, ina amfanin mace ta zauna a rame uwa wata mai cutar yunwa, to nidai Allah ya sani gidan nan babu kishirwa bare ayi batun yunwa, so kike dai sai ubanki ya samu hanyar fad'amin maganar banza in ya ganki a bushe"
Murmushi ne ya subuce mishi a zuciyar shi yake cewa, kuji min tsohuwar nan fa, towa yace mata ni yar lukata nike so matata ta zama me?"
Mai makon yabi ta kofar falon sai ya juya akalar shi zuwa tacan baya yabi ta kofar kitchen, kamar yanda ko yayi tsammani a bud'e kofar take ba'a kulle ta da makulli kamar ko yaushe ba, dan haka ya bud'eta kai tsaye ya shige ciki.
Koda ya bullo cikin falon ta wajen dinning duk Sallamar da yake Hajiya da idon ta ya fure take tama meenal mita wacce ke zaune a kan kafet din dake tsakiyar falon manyan littafan tane na karatu kewaye da ita sai wani littafin dake yin jotting abubuwan da take tsinta a cikin littafan gefe d'aya kuma kofin shayi ne sai wani k'aramin bowl dake d'auke da dambun nama a cikin shi,
Lallai hausa sunyi gaskiya a yayin da sukace kubar rai da abunda yake so,
Domin ko hakance ta faru da Mai Jama'a tun bayan wanzuwar shi a cikin falon idanun shi basu sauka a ko inaba kai tsaye sai akan abar kaunar shi wacce daman ita din itace abunda yake da buri da fatan yin tozali da ita a daidai wannan lokacin,
Bai san yayi kewarta da yawa ba sai lokacin domin kuwa mai makon ya k'arasa inda suke duk da alamu sun nuna cewa sud'in basuji shigowar shi ba,
Ah ah kawai sai ya samu kanshi da gyara tsayuwar shi bayan daya jingina jikin shi da dinning din dake wajen kawai yaci gaba da bin fuskarta da kallo, bakin ta kawai yake kallo a yayinda take amsa ma Hajiya da cewa,
"Wai ke Hajiya waye ma yace miki yawan cin abunci shike sa mutum yin kiba ne? Kuma ni Allah ma ya sani cewa ko kadan bana son k'ibar da kike