Showing 186001 words to 189000 words out of 190771 words

Chapter 63 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1594

dai mijin bazai fasa auren ba sai ma hujja na k'arin auren daya samu tunda dai ko babu komai dole zai auro wacce zata kula dashi da yaran shi,

ta rufa mishi asiri domin yanzun idan tace zata d'aga hankalin da wani abun zai sameta bayan hawan jinin da take fama dashi na masu ciki tofa su iyayen ta da y'ay'anta su zasufi kowa kokawa dan su sukayi rashi mafi girma sab'anin sauran al'umah,
Sun mata nasiha da jan hankali sosai shida abokan shi akan tayi hak'uri karta d'aga hankali,
ta sha kuka sosai harta gode Allah dan Allah ya sani bata tab'a hasaso cewa wai Sarki zai k'ara batun wani auren a yanzun ba, ta d'auka cewa shi kenan ita da kishiya sunyi hannun riga ashe akwai sauran rina a kaba to haka dai itama Mahaifiyar ta ta kira tayi ta bata baki har suka samu ta sarara dan duk tambayoyin da uwar ta mata akan ko taga wani canji daga wajen Sarki ita dai bataga wani canjin daya mata ba yana nan kullum a matsayin Sarkin ta mai sonta ako wani yanayi tayi alkawari cewa insha Allah zata daure zuciyar ta wannan karon bazata yarda tace zata koma bin ko wani boka ko Malam akan wannan auren ba tana kuma fatan Allah ya yafe mata tarin laifukan ta na baya,

Zata dai shirya ma zuwar koma wacece zatazo su zuba wacce duk ta iya allon ta ta wanke ai bata da fargaba tunda tasan cewa mijinta yana sonta dan haka bazata d'aga hankalin taba ,
kodan saboda abinda ke cikin ta wanda aka tabbatar mata da cewa biyu ne take d'auke dasu inko wani abun ya same su ai itace tayi asara ba kowa ba,

Dan haka duk kiran da yan gulma suka dunga mata bata bi takan ko d'aya ba daga karshe ma duk watsa number din su tayi a blacklist tayi blocked shegu,

Da Sarki ya dawo ma tayi zaton ko zai boye mata sai gashi shi da kanshi ya zauna ya warware mata komai harda alaqar Moon da Meenal na zamowar su yayan wa da kanwa bai boye mata komai ba ya kumayi mata alkawarin cewa insha Allah baza taga ko wani canji a gareshi ba sai dai na alkhairi dan kamar yanda bai wulakanta ta a wancan auren nashi ba wannan karon ma bazai tab'a bari ta wulakanta ba dan shi dai har gobe yana sonta kuma yana alfahari da ita,
Koda wasa kartayi zaton ko gazawarta ne yasa yayi sha'awar k'ara aure ah ah dukan su yana son su shi yasa zai zauna dasu yana fatan kuma zata bashi had'in kai wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin su a matsayin ta na babba wato uwar gida sarautar mata.

Da lokacin bikin Sultana yazo tun ana sauran kwana uku Meenal taso tafiya can Abuja saboda yan zaria da suka kwasa tunda wuri suka wuce amma sam AK ya murza nashi kambun yace mata bai san wannan zancen ba,
Kuma fa shi bawai yana Zarian bane dan a wannan satin yana yana kano ma amma saboda wulakanci ya hanata tafiya wai sai dai ta jira har sai ana gobe biki sai Kabir ya kaisu Abujan ita da Hajiya,
tayi naci tayi magiya akan ya barta tabi Maryam su tafi tare amma yak'i dan haka tayi fushi sosai dashi suka koma share juna shi kuma da yaga idan ya kirata bata d'auka sai yazo ya dena kiran nata gaba d'aya,
Hakan da yayi kuma sai ya k'ara kuleta wato ma ya nuna mata cewa bai damu da fushin ta ba irin taje tayi tayi din nan ko fushi ta d'auka dashi sosai kamar ta ciji kanta, sai ana jibi biki kafin ya k'ira Hajiya akan su shirya gobe Kabir ya wuce dasu Abuja,
Ita kuma Meenal tayi fushi dan haka koda Hajiya ta shaida mata yanda sukayi da AK sai tace bata zuwa bikin ta fasa ai dama ko bataje ba babu abinda za'a fasa taso taje da wuri ne dai saboda koba komai dai ai zancen auren Sultana akeyi ance kuma wanda yayi maka kaima sai ka kamanta,
Yanda Hajiya taga ta kafe akan bata zuwa ne yasa ta ja jikin ta tabi gayyar yan unguwar malamai wanda suka rage basu tafiba sai a ranar sukayi tafiyar su ta kuma shaida ma AK cewa Meenal din tayi fushi ita kuma bazata iya tsayawa lallasa mishi mata ba tunda dai ba itace takar zomon ba,

Ita ko Meenal tun bayan data tabbatar da cewa Hajiya ta wuce Abuja ta koma sashen ta ta k'ule a d'aki tana kukan bak'in ciki da takaici wai ita AK zaima haka dan kawai yaga an bashi ita a arha,
Mai yafi wannan haushi dan Allah dan kawai ana auren ka shi kenan sai ayi tayi maka iko da isa,
In ma zaiyi mata iko akan komai ai bai kamata ya mata iko akan wannan ba, Sultana fa Sultanar da itace silar auren ta a ranar da bata shirya ba wato da abinda AK zai saka mata kenan dan kawai ya mata magana akan tarewar ta a KD ita kuma tace mishi bata shirya ba yayi hak'uri har su k'ark'are komai na makaranta inta kallama komai sai ta bishi su koma saboda yanzun zirga zirga zai mata yawa mata shine fa kawai ya wani d'auki fushi da ita, ai yasan tana karatu tun kafin a d'aura auren su ah ah sai yanzun ne yake son tsiro mata da wani tsirfa na daban,
To dan Allah nata karatun da shima yasan shine burin ta na karshe da yayi saura take k'ok'arin ganin karshen shine zata tattara ta watsar ta bishi bayan aski ya riga yazo gaban goshi,
Wannan ma ai kowa yasan fushin rashin gaskiya yakeyi to yaje can yayi tayi ta hak'ura da zuwa bikin kuma bazata tare a kadunan ba,
Sosai tasha kuka ita kad'ai a cikin d'akin k'arin bak'in cikin ma sai da su Meelat suka dunga kiranta a waya dan suji yaya dan tuni ita Meelat tabi Musty Abujan wai har Moon dake Lagos ta isa Abuja tun jiya sai ita shak'ik'iyar Sultanar ce shiru har yanzun gata a cikin garin Zaria hummm Inba aure ba jama'a waya isa,

Zazzabi mai zafi ne yayi mata dirar mikiya inda ta dunga kwarara amai tun tana iya mikewa zuwa makewayi tayi har k'arfin jikinta ya k'are takoma yin shi daga kwance anan k'asan tiles din da take mulmula babu komai da yayi mata saura a cikin dan kwana biyun nan sam bata da nutsuwar zaman cin abinci saboda halin da AK ya sanya su na d'auke mata wuta da yayi akan abunda bai kai ya kawo ba,

Da kyar ta samu ta iya jan jikinta ta mik'a hannu ta d'auko wayarta,
Larai ta fara kira dan tasan Hajiya Jummai bata isa dawowa daga wajen aiki ba yau alhamis Hajiya kuma bata nan Laran ce kad'ai zata iya taimaka mata a yanzun,
Da kyar ta samu ta iya lalubo number din ta danna mata kira wayar bata dad'e tana ringing ba ta d'auka,

"Aunty Larai dan Allah kizo sashena yanzun bana da lafiya"
Ta samu ta iya fad'a da kyar kafin ta yanke wayar,

Daga can gefen Larai ko bata jira komai ba ta saki abinda takeyi ta garzayo zuwa sashen Meenal d'in, tun daga k'asa take kiran sunan Meenal din tana tambayar d'akin da take ciki,
Ita ko tsabar wahala ne yasa sam bata iya bud'e murya ta amsa ma Laran dan haka sai kawai Larai taci gaba da bud'e kofofin dakunan saman tana dubawa ganin bata a d'akin ta, d'akin dake gefen na AK ta sameta a ciki kwance a kasa babu yanda take, dan haka da gudu ta k'arasa shiga cikin falon,

"Ke Meenal meya sameki haka?
dama baki da lafiya ne kuma kila dawo kika zauna anan ke kadai? Sannu lallaba ki taso muje ban daki ki gyara jikin ki ai bakyayi ta zama cikin kazanta ba"

Kamo Meenal d'in tayi a hankali suka k'asara cikin bayi ta wanke mata fuska tasa mata ruwa a baki ta kuskure ta gyara mata jikin ta inda aman ya tab'a ita dai sai rawar sanyi takeyi har suka fito,

Lallab'awa tayi ta kwantar da ita a gadon kafin ta fice d'akin taje ta d'auko tsintsiya da parker ta kuma had'o da tsumma ta gyara wajen daya b'aci tsaf kafin ta fitar da komai ta dawo da burner ta jona shi a soket tasa turaren wuta,
Yana fara aiki Meenal ta zabura tana to she hanci,

"Waiyo Allah me yasa kika sa turaren nan wallahi wari yakeyi shi yasa na gudo daga wad'ancan dakunan fa na dawo nan dan jiri da ciwon kai yake sani "
tun bata k'arasa ba ta fara yunkurin amai a haka jikinta ba k'arfi ta sauko daga gadon bayan ta rufe hancinta da bargon data yaye ta rufama jikin ta saboda sanyin da takeji ta kama hanyar fita daga cikin d'akin,
Da kallon kurullah Larai ta bita bayan ta zare socket d'in tana son tabbatar da zarginta akan Meenal din,

"Kamar fa ciki ke jikin yarinyar nan?
Allah mai iko lallai ko in cikine sai muce rabo ya rantse, to ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi"
Bayan Meenal d'in ta biyo,

"To ina zakije yanzun kuma? " Larai ta tambaya ganin Meenal na sauka daga bene zuwa k'asa,

"Sashen Hajiya zan koma nan wari yakeyi wallahi ke bakiji ba?" Ta juyo tana tambayar Larai,

"Ah wallahi nikam kamshi naji, kece dai hancin ki ya shak'o miki warin"

"Oho nidai bazan zauna anan ba"

K'arasowa Larai tayi ta rik'e ta suka k'arasa sauka a benen suka fice daga sashen Meenal din zuwa na Hajiya kamar yanda Meenal ta buk'ata,

"To me zakici yanzun in kawo miki kici sai kisha magani ki kwanta?" Larai ta tambaya,

"Ni bana jin yunwa bacci kawai zanyi dazarar na tashi zanji na warware"

"Ki daure dai ko tea in kawo miki kisha"

"Ah ah sai dai in zaki dama min kunun tsamiya kuma ina son yayi tsami sosai kula kar asa sugar a cikin kunun"

"To yanda kike so haka zan miki shi"

Kitchen Larai ta koma bayan ta raka Meenal din tsohon d'akin ta, da yike suna da komai na had'in kunun nan da nan sai gashi ta dama dan haka ta zuba a kofi takai ma Meenal din wacce har bacci ya fara figarta,

"Tashi ga kunun kisha"

Yunk'urawa tayi ta tashi zaune sai Larai tasa mata pillow a bayan ta ta jingina,
Amsar kofin kunun tayi ta k'afa kai tana sha tana hutawa har saida ta shanye shi tass kafin ta mik'ama Larai kofin,
"Nagode Aunty Larai anjima shi zaki k'ara damamun dan Allah kinji"

"Mai zai hana in dama miki tunda kina so, yanzun dai koma ki kwanta Allah ya baki lafiya kinji"

Bayan fitan Larai kowama tayi ta k'ara kwanciya can cikin bacci take jin kamar Hannu a saman fuskar ta yana shafa ta dan haka a hankali ya dunga bud'e idon ta tun tana gani dishi² har dai ta ware idon tass akan shi,
Bata san daga ina kuka ya taso mata ba kawai dai ta tsinci kanta da mashe mishi da kokane sosai ta kuma murgina ta juya mishi baya,

"Subhanallah My Baby what's wrong with you?
Meya sameki"

Ya tambaya yana k'ok'arin tattarota zuwa cikin jikin shi,

"Don't you dare touch me ina ruwan ka da abinda ya sameni ko yake damuna?"
Ta fad'a tana kai mishi duka tako ina kamar wata mai shirin tada bori,

Daga hannuwan shi sama yayi alamun yayi surrender a sanda ya saketa,

"Allah ya huci zuciyar ki ya baki hak'uri"

Ficewa daga d'akin yayi ya sauka k'asa zuwa kitchen,

"Ah ah Babban mutum yanzun ka iso?"

"Shigowata kenan dafatan na sameku lafiya?"

"Alhamdulillah ya hanya? Ka shiga daga ciki Meenal din tana nan a kwance bata jin dad'i d'azun ma amai tayi tayi shi yasa ta dawo nan wai can sashenta yana mata wari,"

"Tun yaushe ne bata da lafiyan?"ya tambaya

"Ah ah gaskiya ban sani ba sai dai ko zaka tambayeta dan nasan da ace Hajiya ma tasan bata lafiya da bazata wuce Abuja ta barta ba"

"Taci abinci ne?"

"Eh to d'azun dai kunun tsamiya tace tana so dan haka shina dama mata tasha ban san me zatace tana so yanzun ba kuma"

"To dan Allah ki taimaka min kije can d'akin ta kid'an had'amin wasu daga cikin kayan ta wucewa da ita zanyi"

"To ai baida damuwa Allah dai ya inganta"

Wucewa yayi ya koma d'akin Meenal d'in kuma har yanzun bata dena kukan ba sai ma k'arfi da kukan nata ya k'ara bayan daya bar d'akin a ganin ta mai yasa yana ganin tana kuka ya tsallake ya fice bai tsaya ya saurareta ba,
Koda ya shiga duk yanda Sautin kukan nata ke yakusar mishi zuciya daurewa yayi yana zuwa ya yaye bargon jikin nata ya cusata a k'irjin shi ya matse, duk yanda taso ta kwace hakan ya gagara sai ma hannun shi da yayi amfani dashi ya zage zif din rigarta ta baya ya rabata da rigar shima ya cire rigar jikin shi ya k'ara kankame ta a jikin shi zafin jikin ta yana ratsa shi,

"Shishshsh yi shiru kukan ya isa haka nan ba gani nan a gaban kiba me yayi saura kuma? Bakiga har kofa sai da na rufe ba saboda kar a jiyo ihuna a yayinda kike hukunta ni,
Am sorry nasan nayi laifi amma kiyi hakuri"
Tsakanin mata da miji sai Allah dai haka AK ya sata a gaba da lallashi saida ya tabbatar da cewa ya goge duk wani fushi nashi data d'iba kafin ya shammace ta suka buga wasa zagaye d'aya badan ya koshi ba haka ya kwashe ta sukaje sukayi wanka tuni zazzabin jikinta ya kama gaban shi suna fitowa ya shirya ta shima ya maida nashi kayan ya rik'o hannun ta suka sauko k'asa,
Kunun da Abincin da Larai ta dafa duk a kula ta zuba musu sukayi guzuri kafin suka mata sallama suka bar gidan tabi su da fatan Allah ya kiyaye hanya.

Sun sauka Abuja lafiya tuni kuma Meenal ta shige cikin yan uwa da kawayen ta akaci gaba da shagalin biki da ita, anyi biki lafiya Amarya ma ta tare a gidan mijinta cikin aminci kwana uku Meenal tayi a Abuja AK ya tattaro ta suka zarce KD abinsu anan suka k'arasa cinye satin sai ranar juma'a kwana 7 da barin su Zaria sannan Meenal ta shawo kanshi da kyar ya maidata gida,

Tun shigar su kina Hajiya kebin Meenal din da kallon k'ak'a uwar ka ta haifeka dan bayan dawowar ta Larai ta bata labarin ciwon da Meenal din tayi harda amaye²n data dunga yi,
Sai da ta gama mata kallon tsaf kafin hannun ta rike da baki tace,

"Larai fito daga kitchen din nan dan Allah ki tayani gani wallahi ciki nike hangowa a jikin takwarata"

"Waima ciki ana zaman lafiya, yaushe nayi auren da har zaki wani fara kiramin ciki dan Allah"
Meenal tace tana tura baki, shiko AK da kallo shima yabi Meenal din yana son ya gano cikin,

"Allah Hajiya nima dai cikin nike hasashe" Larai data fito ta amsa ma Hajiya,

"Ke taho nan inji ina da ina ke miki ciwo? Koda yike aike wani cikin fa baya nuna alamu har sai ya fito, amma kedai kam nasan cewa shine a jikin ki"

Shashantar da zancen Meenal tayi akan itafa bata da komai,
A kwanakin ko sosai AK yasa mata ido yana lura da ita dan akwai wasu abubuwa wadanda batayi a baya yanzun kuma ta tsiro dasu ciki harda abincin da bataci ada yanzun ta fara cin su sai dai tun ranar datayi amai din nan bata k'arayi ba bata kuma yawan laulayi sai dai cikin kankanin lokaci jikinta ya bud'e ta cika tayi dam kamar ba ita ba sai shegen kwad'ayi da cikin yasa mata tsakanin ta da miji ko yanzun ne ake zuba tsantsar love dan tunda ya lura da yanda ta amshi ragamar filin wasa ya tattaro ya dawo Zaria sai yanda tayi dashi,
Ga alamun ciki tako ina sun bayyana amma har yanzun ita tak'i yarda cewa cikin gareta kuma ko ance ta auna sai tace ba wani awon da zatayi bayan ita tasan bata da komai,

A haka Allah yakai lokaci aka shiga cikin hidimar auren Moon da Sarki inda akayi hidima sosai a lokacin ne kuma cikin jikin Meenal ya tona kanshi kowa yasan da zaman shi murna ko a wajen dangi har baka tantance wa yafi wani murna karma uban cikin yaji labari sai kuri yake ma Musty cewa sunan dai ya riga shi aure ne kawai amma gashi nan shi zai riga shi haihuwa ko iya haka aka tsaya sun san shine gaba dasu,

Malam ma yayi murna sosai dan har gidan Hajiya sai da ya tako ya duba jikin Meenal Hajiya kuma sai da ta yad'a mishi magana a ranar cewa,
"Ai wannan aure ita dai babu abinda zatace ma Allah sai godiya, domin gashi dai Allah ya nuna musu cewa wani baya auren matar daba tashi ba haka kuma rabon wani baya zama a gidan wani, dan hakan nema yasa ba'aso mutum yayi jayayya akan zancen aure dan bai san me Allah ya boye a cikin al'amarin ba, ita dai ta gode Allah da yasa rabon dake jikin su ya zamo silar gaggautuwar auren su"

Duk da cewa Malam yasan dashi take bai kulata ba har taci ta sud'e,
Tun bayan da aka kammala bikin Moon Amarya ta tare a gidan ta shi kenan ciwo kuma ya taso ma Teemah ganga² wanda dole likitoci suka basu shawara akan ayi aiki a cire yaran dake cikin ta gudun kar a rasa ita ko yaran,
Hakan ko akayi anyi aikin cikin nasara an ciro mata yara biyu duka yan maza sai dai gaskiya itakam uwar sosai take jin jiki duk da cewa bawa baya cire rai da rahamar ubangiji amma ita dai ta fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login