Showing 51001 words to 54000 words out of 190771 words
cikin su harda k'annen Malam biyu Mata wato Aisha da suke kira da (Momin Abuja) da kuma Fatima (Momi Zahra) wacce take aure a kano wato Maman su ya Abakar wanda yaso Raheenat a shekarun baya,
Mutanen Zaria su suka fara isowa kafin na kano su, Meelat da Maryam sai misalin 12 na rana suka samu damar isowa su kuma Musty ne ya kawo su,
Yau dai Raheenat tayi dauriya sosai wajen hana kanta kukan data wuni tanayi a jiya, ga kuma yan uwanta da suka cika sashen nata tako ina ta juya su take gani, motsi kad'an zatayi a fara tambayan ta
"Me take so? Me yake mata ciwo, "
Gaba daya basu bar mata fagen da zata samu nasa kanta a cikin damuwa ba, dan haka ganin yanda suke mata yasa itama ta sake a cikin su duk dadai bawai hirar take taya suba tana dai zaune ne da carbinta a hannu tana ja,
Iso war mutanen Abuja ne yasa falon ya k'ara daukar harami domin kuwa duk da cewa ana cikin jimamin rashin da akayi hakan bai hana yan uwan baiyana farin cikin su na ganin juna ba,
Babbar mota mutanen Abujan suka ciko mai d'auke da Momin Abujan ita da ahalin ta yara da manya, dan duk wanda yaji batun rasuwar shima sai yace zaije dan haka duk ta kwaso su suka taho tare,
Misalin k'arfe 2 da wani mintuna ne kiran AK ya shigo cikin wayar Meenal inda yake shaida mata cewa ta fita kofar gidan abincin sadaqar da Hajiya ta buk'ata ya iso wato ta fita tayima matan iso su shiga da abincin cikin gidan,
Hijjabin ta ta saka bayan tayi magana dasu Meelat akan su rakata kofar gida daga nan ta nuna musu kyautar data samu yau da sanyin safiyar Allah, suko basu musa ba suka rufa mata baya dan dama sun gaji da zaman waje d'ayan da sukeyi a cikin d'akin tun d'azun , Hajiya ta fara nema ta fad'a mata isowar masu abincin kafin ta fice tare dasu Maryam,
da kuma wata yarinyar Momin abujan mai suna Amina itama amma suna kiranta da Sultana wacce tun isowar su ta mak'ale ma Meenal dan basu tab'a ganin juna ba domin ita Sultanan ba a hannun Momin Abujan ta tashi ba, rasuwar marik'iyar ta ce yasa ta dawo gida dan haka ba kowa ta sani a cikin mutanen Zaria ba wannan dalilin nema yasa suka kwaso suka taho dan daga nan kadunan Zaria zasu wuce suyi Zumunci kafin su koma ta yanda zasu san yan uwa sosai dan kaf a cikin ahalin yan Abuja ne kad'ai wad'anda ba kowa ya sani ba suma kuma hakance a wajen su .
Suna shirin wuce inda su Baba Auta ke zaune Baba Adamu ya kira Meenal din da cewa,
"Ke Meenal ku zonan"
Karasawa wajen sukayi ita dasu Sultanan,
"Sultana koh?"
Baba Auta ya tambaya yana nuna Sultana d'in,
"Eh Baba" ita kuma ta amsa,
"Lallai ba shakka girman d'an mutum babu wuya, kin san wadan nan?"
Ya tambaya yana mata nuni da su Ya Farouq dake zaune a wajen gefen su Baba Adamun,
Girgiza kai tayi kafin ta amsa mishi da cewa,
"Ah ah a iya hoto kawai na sansu, kuma suma ai nasan basu sanni ba"
"Gaskiya ne kam ko kun santa?"
Shima baba Adamu ya tambaya yana kallon su,
wasu daga ciki sun amsa da cewa sun Santa lokacin tana k'arama wasun su kuma suka amsa da cewa basu Santa ba,
"Ke kuma fa Uwata kin san wannan?"
Baba Adamun ya tambaya yana nuna mata wani mutum dake zaune a gefen dasu Ya Farouq ke zaune tana lura dashi tun da sukazo wajen yake amsa waya ba kajin komai sai labarcin shi dake fita a tsaftace daga bakin shi kamar wani bak'on balarabe,
Wanda shima jin ana tambaya akan ko an san shine ya sashi d'agowa, ido cikin ido suka kalli juna shida Meenal kafin ta kauda kanta ta amsa tambayar na Baba Adamu da cewa,
"Ah ah ban san shiba, ban ma tab'a ganin shiba sai yau, wane ne shi d'in? "
"Kunga irin ta ko ana zaune cikin k'asa d'aya illah banbancin gari kawai amma ace an wayi gari d'an uwa bai san d'an uwan shiba, tun yanzun da muke raye hakan yana kasancewa, anya in muka shud'e zaku iya rik'e zumuncin ku kamar yanda mu iyayen ku mukayi kuwa?,
Koda yike ba laifin ku bane duka laifin Aisha ne da bata son turo Yayan ta in anyi hutu su zauna tare damu, su mutanen kano waye zaice bai san suba tunda lokaci zuwa lokaci ko babu sha'ani suna shigowa cikin yan uwa ayi zumunci dasu, to kin ganshi nan yayanki ne shima bayan shi akwai wasu ma Sunan shi Naseer shi kam duk da baya zama a k'asar duk yafi sauran yan uwan shi zumunci ga kanwar shi nan itama Sunan ku d'aya kinga itama sai yanzun data girma sannan ta nemo mu"
"Ayya Baba aini Wallahi dan dai bana kusa daku ne da idan na fara muku jelen zuwa hutu sai kun gaji kunce in zauna a gidan mu, kuma ko yanzun tunda har Allah yasa na dawo to wajen ku zan tare kaga koh Baba shi yasa da zamu taho fa na kwaso kaya masu yawa saboda in zauna tare daku"
Ta fad'a da sauri tana katse baba Adamu,
"Ah to in ko hakane kin kyauta gaskiya" cewar Baba Auta shima,
Su Fauxieyerh kanwar Meenal da suka shigo gidan yanzun ita da Sauran yan matan dake tasowa na gidan Malam din ne Meenal ta kira,
su taba umarnin su koma wajen su duba motar wad'anda suka kawo abincin sai su shigo dasu,
Komawar kuwa sukayi suka shigo dasu tace su musu jagora zuwa wajen Hajiya,
Su d'an bata lokaci kad'an tare dasu Baba Adamun ana hirar zumunci kafin suka fito kofar gidan,
Daya bayan daya ta bisu da kallo fuskarta cike da murmushin da yak'i daukewa a fuskar nata yau tace
"ku duba cikin jerin gwanon motocin nan ku ganomin wacce tafi kyau a cikin su, "
"Bebs wannan ai jan raine da d'aukar alhaki dallah ni bana son wulakanci in zaki nuna mana kawai ki nuna mana atoh"
Maryam ce tace haka,
Key d'in dake hannun ta ta latsa k'arar da motar tayi ne yasa suma saka saki k'ara harda tsallen murna a tare,
"Wai Allah Qawata wane d'an aljannan ne ya baki kyautar wannan lafiyayyen motar? Kai gaskiya ko waye yaci a jinjina mishi Allah ni wannan ma har sai tafi min waccan da Sarki ya baki kyau ko Meelat?"
"Ke dallah barni ni ina zan wani iya tantancewa wannan surprise duk ya rud'ani, gaskiya nayi miki murna sosai wallahi Qawata ubangiji Allah ya tsare ya kare,amma dan Allah waye da wannan k'atoton dawainiyar haka? Ko toshi aka fara mana tun yanzun ne bani da labari dan wannan motar ai tafi k'arfin ayi kyautar ta haka nan babu wani Babban dalili kawata fad'amin wani Babban kifin ne kika kamo mana kin san wallahi ke me sa'a ce duk inda kika shiga haka nan Allah ya yiki"
Meelat ta tambaya tana dawowa da baya inda Meenal ke tsaye tana musu dariya,
"To yanzun tambayar wanda ya siya motar zakuyi ko zaku shigane mu d'an zaga gari?"
Ta tambaya tana d'age musu girarta guda d'aya ta wani kashe musu idon ta d'aya,
"Kema ai kin sani dole ne ma mu d'ana ta wallahi, amma ni zan tuk'a"
Cewar Sultana da itama ba'a barta a baya ba wajen tayasu murnar sabuwar motar,
Key din Meenal ta mik'a mata ita tajasu suka bar unguwar, Maryam dake gaban motar ita ke nuna mata inda zasubi dan ita kam tasan kan garin na Kaduna sosai sab'anin su Meelat da Meenal daba wani zuwa garin sukeyi ba in ma sunzo abunda ya kawo su kawai sukeyi su juya,
"Qawata wai bazaki fad'a mana waya miki kyautar motar nan ba?"
Meelat ta tambaya tana marairaice wa,
"Humm ki bari kawai my sister idan na fad'a miki ke kanki sai kinyi mamaki, ke Hajiya mafa sai da takai hannun ta jikin shi ta tabbatar da cewa lafiyan shi qalau yana a cikin hayyacin shi yayi kyautar sannan ta yarda,"
"Ke tsaya wai taubashin kine ya baki motar nan kyautaπ³ kowa? "
Maryam dake gaba ta juyo tana tambaya cike da mamaki,
"Kin cinka dai dai An mata,
shi din dai yau kam naci mota halak malak dan Wallahi bai isa kuma zuwa anjima yace wasa yake min ba Allah ma yaso ni a gaban Hajiya da wanda yake zaune a gidan nashi akayi komai"
"Ke Meenal anya Yayan nan naki ba sonki yakeyi ba kuwa?π€"
Meelat ta tambaya tana rike baki,
Ita dai Sultana tunda ba sanin wanda suke magana akan shi tayi ba shi yasa ba tasa musu baki ba,
"Umm umm baso ba aurena zaiyi, kawai shi kenan mutum bazai baka abu tsakani da Allah ba sai in akwai so a tsakanin ku, iskancin banza ina ce ni daku turaren shi muke fesawa me yasa tun da yake siyan turaren yana bani bai tab'a cewa yana sona ba, keni rabani me zai Kaini auren taubashi inba so nike hawan ruwa ya kamani ina zaman zamana ba"
Meenal ta bata amsa tana harar ta.
"Ameen ya rabbi Allah yasa ya aurekin, yo ai mu bazamu k'iba wallahi dan mu abun farin ciki ne ma a wajen mu ace yanda muke mu ukun nan muna auren Aminan juna, ba shike nan ba kuma zumunci sai illah masha Allah me yafi hakan dad'i,
Nidai zan baki shawara da zuciya d'aya wallahi Qawata ko da wasa AK ya bud'e baki yace son ki yake ki rufa mana asiri kiyi saurin Amincewa da wur wuri kai in so samu nema sai a had'e bikin mu wallahi"
"Ah ah ba biki ba suna"
Ta fad'a tana kaima Meelat dake dariya duka.
"My Sister Allah kuwa inhar abunda suka fad'a ya tabbata da gaske ki amsa kawai, dan Wallahi ina fad'a miki ba k'aramin mutum bane zai miki irin wannan kyautar"
Cewar Sultana da sai yanzun tasa musu baki.
"Rabu dasu kinji shima bazai wani fara cewa yana sona ba, dan ni mijin kaina nike so ba wanda zan dunga rabashi da yan mata ba, ai tunda kina nan zaki ganin ma idon ki ni inani ina auren mijin da idan ya fita gida zuciya ta zatayi ta hailala da salati har sai ya dawo".
Sunyi yawo sosai gidajen kawayen su dake cikin gari basu suka koma unguwar dosa ba har sai bayan la'asar liss,
Dare nayi kuma suka tattara ita dasu Maryam din da Hajiya suka wuce gidan AK dan yanda gidan ya k'ara cika yau abun harba masaka tsinke,
D'ayan d'akin dake gefen wanda suka sauka ita da Hajiya suma su Maryam suka sauke nasu kayan, Hajiya dai da wuri tayi bacci sakamakon ciwon kan da tace yana damunta, wanda hakan ne ya basu damar shiryawa suka fice daga cikin gidan bisa jagorancin Maryam da kuma Meenal data Sanya musu kwad'ayin Ice cream din da AK ya siyo mata jiya,
Yawo suka sha abunsu sukayo siyayyar abubuwan da suke so, basu suka dawo gidan ba sai wajen 11 da wani abu,
Shiko AK yau da wuri ya dawo, sai dai ga mamakin shi Hajiya kawai ya samu a d'aki tana bacci, dan haka bai tashe taba ya fita daga sashen wajen Mansoor yaje ya tambaye shi
"tun yaushe Meenal ta fita daga gidan nan"
"Tun bayan da akayi sallan isha'i suka fita"
"Suka fita ba ita kad'ai bace kenan?"
"Eh su 4 ne ita da kawayen ta"
Komawa ciki yayi ya kunna TV din dake falon yana kallo lokaci lokaci kuma yakan daga kai ya kalli agogo,
Karfe 10 nayi ya d'auki wayar shi ya kira number d'inta,
"Kuna ina ne har yanzun baku dawo gida ba kun san kuma dare yayi?"
Ya tambaya bayan ta d'aga wayar daga can bangaren ta,
"Mun d'an fita ne amma yanzun zamu dawo insha Allah"
Daga karfe 10 zuwa 11n nan ya kirata a waya yafi k'arfin sau goma daga karshe ma tsoro ya faraji ko Sunje sun shiga wani unguwar da suka bace hanyar komowa gida ne,
Dan iskanci kuma daga baya ma sai ta dena d'aukar wayar shi, sai yayi yunkurin fita ya nemo su sai kuma yayi tunanin ai baima san ainihin inda suke ba,
Gagara zama a falon yayi ya fito tsakar gidan yana ta faman zuwa da dawowa, ba karamin salama ne ya ziyarci zuciyar shi a sa'ilin da yaji karar horn d'in motar su a kofar gate d'in gidan ba,
Mansoor ne ya bud'e musu gidan domin shima yanda yaga AK ya damu sai ya kasa sukuni shima.
*Kuyi hakuri uzurine mai k'arfi ya d'auke hankali na shi yasa bakuji niba*
#MEENAL
#MAI JAMA'A
#NASEER
#SARKI
#MOON
#TEEMAH
*UMMIEE ZARIA*βπΌ
[9/3, 10:35 PM] Ummiee Zaria: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 19*
Gyara tsayuwar shi yayi fuskar nan tashi uwa ta shanun da Meenal take yawan fad'a yaci gaba da bin motarsu data shigo gidan da kallo har zuwa sanda Maryam da itace ta tuk'o motar zuwa gida ta gyara parking,
"Kinga abinda kikaja mana ko Meenal shi yasa tun d'azun nike ce muku mu koma gida haka nan amma kuka k'i gashi nan duk kunsa hankalin bawan Allah ya tashiπ" cewar Meelat, wacce dama ita tun tuni ta damu akan suyi su dawo gidan amma su gwanayen sukak'i.
"Ke dallah can kyaleni inace ke mu ke ma duk wannan gatan!
Kwana nawa ya rage miki ki rasa yancin da kike dashi a matsayinki na budurwa zuwa matar auren da zamu kai gidan miji mu baro,
daga nan kuma keda yawo sai dai na zuwa unguwa shima sai da izinin isasshe baki ba damar fita kai tsaye a duk sanda ta raya miki dan kin riga kin zama d'aurarra, ke inya so nuna isan shi a kanki ma sai ya bari kin shirya fitan ya murza kambum iko yace miki bai san wannan, dan haka yarinya wannan shine damar ki na k'arshe dan haka karki wani damu da fad'an da zaiyi, dan ko gobe ma sai mun fita wallahi ko yana so ko baya so,
to haka kawai dan mutum ya fita bai gama abinda yakeyi ba za'a wani matsa mishi da kira, bari kigani yanzun muna fita zai rufemu da fad'a kalli fuskar shi ki ga yanda ya d'aureta Allah ni ban fiye son takura ba wallahi, shi kuma babu abunda yafi kwarewa irin yaga ya takura ma mutum"
Maryam ce ta fara bud'e gaban motar ta fito sai Meelat dake gefen mai zaman banza kafin Sultana dake baya tare da Meenal itama ta sauko daga cikin motar ita ko oganniyar gyara zama ma tayi abunta bayan ta d'aga kiran da Salman ya mata dan dama tun da yamma da suka had'u a gidan gaisuwa yace mata zai kawo mata yawo inta koma masaukin ta, to d'azun daya kira ta fad'a mishi cewa bata gida sun fita dasu Sultana shine yanzun ya k'ara kira yaji ko sun koma gidan, inda haka banza ne ba lallai ta d'auki wayar nashi ba zatace dare yayi bata son damuwa dan ta lura dashi kwanan nan baya tashi kiranta sai dare yayi inta tambaye shi dalilin kiran kuma sai yace mata wai kawai ya kirane dan yaji ya take,
Ita kuma bata tab'a daukar hakan a bakin komai ba,
domin dai tun kafin ta auri Sarki dama shida ita suna shiri sosai,
Bayan auren ta da Sarki kuma sai shirin nasu ya k'aru dan Sarki da kanshi ya bata damar komai take buk'ata tayi magana da Salman d'in kai tsaye, sai ya zamana duk cikin K'annin Sarki tafi shiri da Salman d'in.
kowaccen su idan ta fito simi simi sai dai ta nemi waje ta rab'a a gefen yar uwarta ta tsaya haka nan suka jeru a gefe guda uwa wasu wad'anda ke tsayuwar assembly babu wacce ta iya cewa dashi komai a cikin su kamar yanda shima bai tanka musu ba,
sai ma takawa da yayi gefen da ita oganniyar ke hakince tana amsa waya ko alamun damuwa babu a tare da ita, yana bud'e gefen da take zaunen abu na farko daya farayi shine zare wayar dake cikin hannun ta wanda ta k'ara a kunne tana maganar da tsabar munafunci koshi dake kusa da ita bayajin me take cewa,
Latse kiran yayi ya kuma kashe wayar gaba d'aya, bai tsaya b'ata ma kanshi lokaci ba ya janyo hannunta ya fito da ita daga cikin motar itama ya jerata a kusa dasu Meelat wadanda suka wani duk'ar da kai k'asa, uwa wad'anda aka tsare a gaban alkali,
k'asa k'asa suke satar kallon shi ko waccen su ta kasa d'ago kai ta kalleshi balle kuma su samu damar furta wani abun har zuwa lokacin saboda tsabar kwarjinin daya musu,
K'ara daure fuskar shi yayi sosai kafin ya bud'e baki a kame sosai yace,
"Daga ina kuke?"
Bai tsaya jiran amsa daga kowaccen suba yaci gaba da jero wasu tambayoyin kamar haka,
"Ina kuka je? Nace
Kuma da izinin wa kuka fita gidan nan?
Mai kuma ya hana ku dawowa dawuri tun tuni sai yanzun k'arfe 11 da wani abun, shin kun manta cewa ku matane da har zaku fita kukai irin wannan lokacin a waje?
Ina kuka sani da har zaku fita, Ah ah ko dai salon ku fita wani abu ya sameku kusa mutane a shiga uku, idan da ace kun b'ace kuka kasa gane hanyar dawowa gida kuma fa? Ke kuma Jameela saboda kema ba hankalin kika fisu ba shi yasa kema da kike shirin zama macen aure kika biye musu kuka kai har wannan lokacin a waje, baki san cewa Amarya tsautsayi ne yake binta a duk inda ta