Showing 159001 words to 162000 words out of 190771 words

Chapter 54 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1548

baya zuwa a yanda nike son shi? alhamdulillah allah nagode maka daka tsaramin kalar tawa rayuwar a haka,ya allah ka sanyama wannan aure albarkha kasa ya zamto aure na karshe da zanyi a doron kasa, Allah ka bani ikon yima mijina biyayya a zaman da zamuyi ameen ya rabbi" ta fada tana goge hawayen idonta.
Pillow din dake gefenta ta rungume hakika ranar yau tamata zuwan bazatan da batayi tsammani ba haba dan Allah an daura aure babu shiri ai ya dace ace ita kuma a bata damar shiryawa da kyau kafin asa ranar tarewa,
Amma kowa ya azalzala kamar dai dama duk sun gaji da ita, in kayi magana ace kayi hakuri kayi biyayya,
"wato ni Abdul zai munafunta bayan na nuna mishi a'ah shine ya zagaye yaje ya koma ta sama ya nemi aurena ba tareda sanina ba a matsayina na bazawarar dake da yancin zabarma kanta miji shine harda zuwa gabana yana ma yan uwana mugayen addu'a wato tunda shi yasan abinda ya taka wato,hakika kullu yaci amanar koko"
ta fada ina tura baki
"nidai kamar mara gata duk lokacin aurena ba wanda yake damuwa dason jin ra'ayi na,duk yanda suka yanka hakan zanbi.
anyi na farko ba'a bani zabina ba duk da na nuna bana so,shine na biyun ma gashi a haka akayi shi,e mana to bashi gashi ba yanzun din ma bata canza zani ba,shi kenan nidai a kullum bani da zabi kenan? Amma ai ba laifin kowa bane laifin Mai Jama'a ne tunda yaje kai tsaye ya nemi aurena bayan na sanar dashi cewa ban shiryama wani aure yanzun ba,wato ma ni aka hade ma kai a gidan nan aka mai dani kamar wata bare wai daurin aurena ne akayi da yamma kawai dan sun mai dani zawarar da gaske,wai ace harda Sultana duk shegen gulma da tsegumin ta wannan karon ta kasa kwaso gulmar ni ta fad'amin saima aka hada baki aka karamin auren dole! Ita da take kawata ta amana da ita aka shirya aka kara gabatar da komai suka rufe ".
Kalmar auren dolen data furta ne yakara dawo mata yama tsaye a zuciya,
"Shin da gaske auren dole akamin?
Ko auren gata? "
Ta tambayi kanta,
a matsayita na bazawarar da tayi zaman aure na tsayin shekara 6 iyayenta suka kara wanke saurayi dal suka auramata,
saurayin daya kasance saurayin da bashi da tamka a fadar zuciyarta a wannan lokacin,taya zata kira hakan auren dole murmushine ya subuce mata "lallai ni mai sa'ace,to wai ma kukan me nike????? Ba amsa .............
Tana cikin wannan hirar tsakaninta da zuciyarta ta jiyo karar wayarta dake ajiye a gefenta,
mika hannunta tayi ta dauko wayar saidai kallo guda ta ma number din dake yawo akan wayar ne ya kayar mata da gaba,
" shike nan ni Aminatu ta faru ta kare iko da nuna isa kuma tsakanina da mutumin nan ai sai ta Allah maye kawai ka kira har ka gaji baza'a d'auki wayar ba" number din ba suna domin ban ajeta akan wayar ba har yanzun amma ko ciwon mutuwa takeyi kallo guda zata mata ta shaidata,
" Abdul Khareem" ta fada a bayyane tna mai murguda baki
"baza'a dauki wayar ba wato burinka ya cika bari ka kirani" ta fada tana mai kife wayar,ganin ba gajiya zaiyi da kiraba hakan yasa ta cire karar wayar gaba daya yanda koya kira bazata dame ta da karaba,inya gaji ai dole ya hakura da kira shima dauko wayar tayi da niyar in kasheta gaba daya sai gashi kamar mai hasashe tna daukar wayar sako na shigowa cikinta,ko bata budeba tasan dan anacen ne dan babu number din kowa akan wayar sai tashi,
dan tun jiya da Sultana ta amshi nata wayar da sunan zata kira bash tayi mishi albishir har yanzun bata dawo mata dashi ba data matsa da tambaya ma cewa Sultanar tayi wai ita dai ta manta inda ta ajiye wayar wallahi, sai da safen yau ne ta kawo mata wannan sabuwa ce kuma babu komai a kanta.

Tun kiran farko daya shigo wayar taga number din shi yasin tasan shine yasa aka dauke mashi nata wayan, Ba tareda ta karanta sakon ba na kashe wayar baki daya ta koma taci gaba da kwanciya,.

"Hummmm dan samari duk ka gama rawar jikin ka ai bazakusan nasara ya shuka tsiya ba sai zashi ganin gida,ba kana murnar kai angoba aiko ban tarewa yau boyewa zanyi inda babu mai ganina" murmushin mugunta tayi a bayyane tace "shawara mai kyau" harda tsallen jin dadi saida tayi daga kwancen da take
"yo ni hauka nike in tare yau lallai idan na tare yau tabbas gobe a gadon asibity za'azo aci gaba da ganin amarya😒 mugu kawai mai shan bakin Mata"

Ita kadai a daki Yayin da acan cikin gida mata ke cigaba da gudanar da biki babu kama hannun yaro domin dai ita d'ayar amaryar wato Fauxieyerh babu abinda yasha mata kai ta sake abinta tana walwala bata takura rayuwarta ba, bayan an gama walimar da aka nemi Meenal aka rasa can ta kofar baya wajen sashen su ya sa'eed masu kidin kwarya sukaja da'ira suma dai sai faman ihun kiran amarya meenal suke amma babu amarya meenal taki fitowa sai iyayen amaryar ne da su Sultana suketa kara'i domin ranar yau ba bakin ciki domin ko bakama Meenal kara kataka ba kayi Fauxieyerh ustaziyar gidan malam wacce da kyar ta yarda ta fito filin sai dai kamar soja haka ta zamar musu ko dan rausayar nan babu.

A can gidan Hajiya ko shiri sukeyi sosai na tarbar amarya gida ya cika dam da gayyar yan uwa da abokanan arziki bakin Hajiya yau dai yak'i rufuwa,
gefe guda kuma yan mata da samarin gidan ne suka shirya nasu shagalin suma sun rantse cewa baza'a barsu a baya ba dan haka suka ware gefe guda a harabar gidan suka kira masu decorations suka shirya musu shi ganin burgewa a cewar su tunda ya Abdul yace babu casu to sun san bazai hana na cikin gida ba,suma dai sun shirya sun kuma dau wanka duk wanda ka gani sai dai kace masha allah sai zabgaga kamshi sukeyi sunfa wanku,.

~~~~, Su kuma angwaye bayan sun baro gidan Sadeeq sun dawo tudun wada tun daga junction din gidan Hajiya zuwa fadar mai jama'a tarin motocin da suka gani faffake ya shaida musu cewa lallai jama'ar mai jama'a sun taru dan ko ina Abubuwan hawane fake Kama daga mashin keke napep mota da kuma wasu mutanen a waje,musty dayafi sauran bakine ya gaza shiru saida ya tanka "kai AK anya kakanka bai jika maka hatimi kasha a lokacin da yake raye ba kuwa?"
Ya fada tana mai kara bin motocin dake fake da kallo
"lallai halin mutum jarinsa my brother please say Alhamdulillah".. dariya sauran sukayi suna masu mai maita kalmar alhamdulillah di gangarewa yayi ta wani gefen daban ya fito ta saitin masallacin,duk da cewa an kammala liyafar cin abincin amma har yanzun dai akwai jama'a sosai a gidan bai shiga masallacin ba saida ya nufi gefen da motocin shi ke fake sannan yayi amfani da key ya bude motar ya zuba wayoyin shi hula da babbar rigar shi,kulle motar yayi suka karasa cikin masallacin shida su sadeeq da suka idar da alwallah yanzun,. Bayan an idar da sallah da yawa daga cikin abokan shi motocin su suka shige domin komawa unguwan unguwar malamai gaisuwar sirikai daga can kuma idan sun d'auko amarya wajen dinner za'a rΓ nkaya dan gogan yace ba uban da zaisa matar shi tayi dare a wajen wata uwa dinner dan ma maita ne yasa suka dage cewa sai anyi badan shi yaso ba,
sai da yaga da yawa daga cikin su sun wuce tukun shima dasu sadeeq suka shiga cikin nasu motocin suka takema sauran baya,tarin messages din dake wayar ya fara bi bayan ya bude data domin bama sauran sakonnin social media damar sauka suma,
da yawa daga cikin sakonnin na fatan alkhairi ne da taya murnar samun karuwar aure wasu daga ciki kuma na ban hakuri ne daga wadanda basu samu zuwa ba duba da yanda bikin yazo babu shiri,

*******"*******
A gefen hafees kuma bayan sun isa saida suka gabatar da sallah la'asar sannan suka shiga cikin gidan kamar yanda suka tsammata dam gidan yake da jama'a a hakan yaci gaba da kukku tsawa cikin mutanen duk inda yake tunani zaiga Aminatu ya dubafa bai gantaba,dan har maryam ya gani da sauran kawayen su amma wai suma basu san ina ta shigeba tun kafin daurin aure,dakyar ya samu ya gano Aunty Hassana maman Abiey can cikin filin rawa suna cashewa acewar su ko amaryar bata fitoba bazasu fasa abunda suka shirya ba.




*Ummiee ce*
[10/10, 11:24 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 47*


Mom Abiey dan Allah ina Meenal take?
Nasan bazaki rasa sanin inda take ba, wallahi ina zaman zamana ya AK ya tasoni wai in kawo mata waya zaiyi magana da ita kinsan kuma ban isa ince mishi ban ganta ba raina ya b'aci a banza kuma nima yau bazan so in b'ata mishi raiba",
Dariya tayi "kai koh Hafees ai yau dai duk fadan mai jama'a dole ya daga kafa ko ka manta yau din babbar rana ce a gareshi?"

"Nidai taimaka ki kaini wajen ta in sauke wannan nauyin in huta,"

"Muje" tace dashi a yayin da tayi gaba shi kuma ya take mata baya,

Can sashen baba Auta suka wuce domin nan ne kad'ai inda yake da k'arancin cikowar mutane cikin falon suka shiga babu kowa a ciki domin tun bayan da su Baban suka dawo daga sallar juma'a suka shigo cikin gidan abinci kawai sukaci anan falon sai suka koma harabar gidan inda aka kafa rumfuna sukaci gaba da zama suna ganawa da nasu bak'in,
Dan haka sai nan din ya kasance shiru cikin jerin dakunan dake jere na k'arshe Mom Abiey ta kwan kwasa kafin ta bude kofar ta shiga da sallama shi kuma Hafees yana tsaye ta bakin kofa bai shiga cikin d'akin ba,

zaune ta iske ta a bakin gado dan tun bayan data fito daga wanka ta shafa mai take zaune a wajen tana tunanin yanda zatasa kaya ta shiga cikin gidan dan tasan da zarar ta shiga tofa ta shigesu a hannun abokan wasa dan tun jiya basu barta ta sarara ba dalilin sune ma yasa ta dawo nan d'in ta b'oyema ganin su,
ace warsu wai sun bada gari dan sunga alamar karfin jinin su itda Mai Jama'a duk wanda ya tsaya masu a hanya tofa kiyama zai zarce kobabu shiri dan haka sukam sun bada gari dan sunga alamar gara subi yarima susha kid'a dan wanda ya iya zuwa d'aya ya watsar da mazaje har 4 a rana d'aya tofa duk wanda yace zai shiga gaban shi yasan aradu ya tara,
kai gaskiya dai babu irin sharrin da basu mata ba wai ashe tsohon tuzurun dama duk wannan lokacin ita ya tsaya jira shi yasa yaki aure waya sani ma ko dama rabon a jikin shi yake dan haka nema auren ta da Sarki yazo a haka,
Ita kuma data gaji da iya shegen da suke mata sai tace musu "ai mazama ana musu auren dole mai yasa shima basu duba ko a dangi sun hadashi da wata ba? ko tsoron shi sukeji ne?"
kuma ta fada musu sudaiyi a hankali dan ita mutum ko shishshigi yafiye yima abinda take so bazai taba ci gaba ba balle kuma har yace zai so abinta take so sai dai kwabar shi tayi ta ruwa,

shi yasa wasu ma da suka kai hajar su kasuwa ko kallo basu samu ba balle a fara tunanin ta ina ciniki zai fada,hakan da tace musu kuma da wata karamar mara kunya takeyi a wajen dan wata yar balaja'u ce cikin yan uwan Maman AK da sukazo daga maiduguri inba gulma ba kinzo ma uwar ango biki ai sai ki tsaya a inda take koh?
Maye na wani kwaso jiki ki taho gidan su Amarya to ashe wai ita Ramlat din son AK takeyi shi kuma gogan kun dai san hali dan saboda itama gaba d'aya ya dauke kafa zuwa wajen kakan nin shi na gefen uwa,
To da labarin auren yaje musu dai ance wai harda suma tayi shine fa tun zuwan su ta kwaso jiki wai ita wajen Amarya zata sauka a cikin zuciyar ta kuma to take ta zauna da Meenal din dan taga uban miye ta fita da har shi AK ya zab'i Meenal din ya barta, ita kuma Aisha wacce suka zo gidan Malam din tareda Ramlat din itace taba Meenal labarin son da Yarinyar kema AK ita kuma dai dama tun kallon farko datama Ramlat din ta gama raina mata da wayau shi yasa ma ta kasa sake mata fuska,
tunda ta fada musu haka ta shige ta basu waje babu wanda ya k'ara ganin ta,
Kayan da anty fati ta kawomata ta daga doguwar rigane na wani tsadadden material fari tass itafa har yanzun abubuwa basu dena bata mamaki ba wai daga ranar laraba zuwa juma'a mutanen gidan su ashe harda anko sukayi dan munafunci harda su Sultana ayin anko ko wani telan nema ya tsaya ya musu d'inkin ankon oho nata kayan ma da aka gabatar mata bata san daga ina suka fito ba,zura rigar kawai tayi batayi wani kwalliya ba dan haka koda Maman abiey ta shigo zaune ta taddata saman gado kamar wata mai danyen jego inda ta ajiye abincin data kawomata dazun ta nufa tana bubbudewa.

"Ammi me yasa bakici kazar nan da yawa ba bayan nasan yanda kike son naman kaza shi yasa fa ni da kaina na b'ata lokaci na had'a miki ita yanda zata miki dad'in ci?"
Ta juya ta tambaya fuskarta na nuna alamun bataji dadin yanda Meenal din tayi ba,

" Naci ! kuma wallahi ko dadi babu nina gaji da ciyeciyen nan"
ta karasa fada tana tura baki,
"oho yarinya ko kici ko karkici ki sani kanki kika mawa bani ba dan haka ruwanki, insha allah wata rana sai kin kirani kina rokon in taimaka miki nayi miki wannan hadin a lokacin ni kuma zanci miki uwa ranar,"

"Ni din wai? allah ya kyauta wallahi me zanyi da ita?"
"Lokaci na zuwa da zaki san amfanin ta kuma na rantse miki da Allah sai kinci ta, ga kuma hafees nan tsaye a bakin kofa nasan kinyi halin tsiyar naki shi yasa ya'yan ya turoshi ya kawo miki waya kedai Allah ya shirye ki wallahi Allah ya miki gata kina ma mutane iskanci"

"toni Mai zaice min?"
Ta tambaya tana tura baki,
"shigo hafees"
Maman abiey tace tana mai zama a gefen Meenal din kiran maryam tayi akan suzo su same ta a sashin baba sannan ta yanke Wayar,
tunda Hafees ya shigo ita kuma saita daure fuska,
dariya yayi
"amarya kiyi kawai ai lokacin kine nidai bazaki wani layance min ai nasan komai anaso ana kaiwa kasuwa yarinya in gaskiyane mai yasa bakice bakya yiba ko kuma da akace an daura sai ki tada aljannu amma sai mukaji lukus an fad'a miki dan kin hana kanki sukuni za'a fasa wani abune? Kice bakya so wallahi kiga yanda ake buga wawuso wasuma bazasu samu ba sai dai suyi hakuri"
da farko kin kulashi tayi kamar batasan dawa yikeyi ba.
saida ya isheta da surutu sannan tace mishi
"ai kasancewar ko yanzun taimaka muku nayi domin idan lokacin baya ya iya hakurin rashina ka sani a yanzun tabbas idan ya rasani kuma zaku rasa shine a wannan lokacin,
wannan dalilin ne yasa naji zan iyayin jihadi in zauna da shi in ba haka ba ai kai kanka kasan nafi karfin yaro,
inba kaddara ba mema zanyi da tuzuru ni aminatu,"

"Karya kikeyi wallahi! kema kinsan mai jama'a yafi karfin kice mishi yaro ko kice mai zakiyi dashi,dan yafi karfin nan dan batun yau ba kema kinsan yanda mata ke gwagwar maya suna gwabzawa a kanshi kuma har gobe bata canza zanin ba, bakiga Ramlart bace yarinya mai zubin hurul ain har suma tayi da taji ya aure ki kinsan ko yanzun yace yana sonta da gudu zata yarda ta aure shi"
"toni ina ruwa na tama kashe kanta saboda son da take mishi in taso ai duk wanda rai yayi ma dadi ba wallahi bai kaiya maishi ba,
aikin burrr inji tusa ai duk haukan da suke a banza tunda ya tsallake su ya dawomin duk da na nuna bana bukata,kuma sun fadi kasa ba nauyi domin ni dinnan na musu fintin kau domin koba komai ai ni ina ciki su kuma suna waje kuma kamar yanda ada ya musu nisa haka nisar zatayi ta karuwa kamar tazarar sama da kasa mijina baya kamuwa garesu kai ka taba ganin an kama inuwa?"
ka sani cewa mai jama'a ya musu nisa sai gani sai hange ai sun Riga sun bar shiri tun rani, sun kumayi wasa da damar su dan haka daukar dangana dole", ta karasa fada tana murguda baki cike da tsiwa,

" oh yanzun kika san da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login