Showing 24001 words to 27000 words out of 190771 words

Chapter 9 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1523

da zakiyi dashi amma kina da uwar da zakiyi da kud'in shi"
Maryam ta fada tana dariya,

"Aini ban tura mishi katin gayyata ba, idanuwan shi ne suka gano mishi ruwan da yayi zaton suna iyayi mishi wanka, bai san cewa wannan ruwan maliya bane in ya sake ya shiga bai zama dole ya fito a raye ba,ina fatan dai baki fada mishi ainihin suna na ba?"
Tayi tambayar tana kallon Maryam.

"Kina da wani sunan da yafi Zuwairat ne a duk lokacin da tarko ya kama kurciya dama?"
Itama ta tambaya tana dariya,

Dariya suka kara fashewa dashi,
"Kai Zubaida ashe baki manta sunan nawa ba?"
Inji Meenal.

"Ke wai ma da muka barki tare dasu me wancan yake fad'a miki?"

"Ah ah ai shi rakiya kawai yayi abokin ne ya gano abinda ya gano shine yasa suka biyo mu a baya, shi dai yace min sunan shi Auwal kuma wai d'an Malali ne a garin gomna (kd take nufi)"

Basu isa gidan hajiya ba sai da suka tsaya Meenal ta siya kajin da ta amshi kudin su a hannun Ya Mashkur,

Bayan ta faka motar nata a harabar gidan baya ta koma ta tambayi Isah,
"Mai Jama'a yana gida koya fita?"

"Ai Hajiya tun fitan da yayi na safe ina tabbatar miki da cewa har yanzun bai dawo ba, su Sadeeq ne kawai a gidan suma d'azun nan suka shigo"

Juyawa kawai tayi bayan ta gama sauraron abunda yake cewa domin su Meelat sunyi gaba zuwa Sashen na Hajiya dama,

Sai da sukayi shagalin cin kajin nan kafin suyi zaman ware kayayyakin kowacce ta d'auki nata suka cirema Moon da Aisha nasu, dan a gobe suke so su fara rabon ankon,

Suna cikin ware kayan ne kuma Allah yama Hajiya shigowa dan ta shiga wajen Dada Turai kakar Billyn Ya Sa'eed,

"Wa nake gani yau a gidan kamar Amaryar Mustafa na?"

Da dariya Meelat ta tareta tana cewa,

"Wallahi Hajiya kamar kin san cewa ke nike jira dama"

"To ai gani na dawo ya akayi ne hala"
Ta tambaya a sanda take zama a kan kujera,

"Hajiya yaushe za'a kwaso kayan Meenal na can gidan ne? In kuma ba'asa ranar kwasowan ba ki bani key dan Allah muje gidan nida Maryam mu d'ibo cikin kayan ta wad'anda bata dinka ba, mukai mata d'inki, ki kalli shigar da takeyi fa har yanzun Hajiya bayan ita din a yanzun da bata da aure kamata yayi ta canza kalar shigar ta,"

"Eh to kema kince wani abu dama so nayi in hayaniyar Sakin ya lafa sai insa a kwaso kayan, amma yanzun bari in d'auko muku mukullin sai kuje ku d'auko abunda kuke buk'ata din kafin a kwaso kayan"

"Yauwa Hajiya aiko mun gode, kinga ko ga kayan ankon ki kema na ware miki dan kema ai k'awar amarya ce"

Sun kai har bayan la'asar a gidan suna ci gaba da tattauna wa sai yamma liss Musty ya kwashe su ya mai da gida kafin su tafi kuma sai da Meelat ta amsa key d'in da tayi ma Hajiya magana aikai,

har lokacin kuma AK bai dawo ba dan tun Meenal na d'ar dar da tunanin haduwar su har ta sake taci gaba da harkokin ta,

A wannan ranar dai basu ba had'u da AK din ba dan da wuri ta haye sama ta kulle d'akin ta bata kara gigin Saukowa ba har dare, kuma ranar dashi dasu Sadeeq dukan su anan Sashen Hajiyar sukayi hirar dare,
Tunda baiga wulkin Meenal din ba yasan kunyar ganin shine ya hanata Saukowa dan haka sai kawai ya share shima,

*BAYAN KWANA HUDU*

A gefen Meenal sosai ta d'auki matakin hana kanta zama a falon Hajiya inko har zata zauna tofa saita tabbatar da cewa ta rufo kofar falon dana kitchen,
Anayin knocking kuma da bazata bud'e ba sai ta tambayi waye, inko har taji muryar AK ne tofa bazata bud'e mishi kofar ba juyawa zatayi ta koma d'aki idan kuma anyi katari Larai na kusa ita ke bud'e mishi kofar Yanzun,
Ya kuma yi tambaya akan dalilin menene yasa yanzun ba'a barin kofar a bud'e ?
Larai kuma ta fad'a mishi Hajiya k'arama ce ke kulle kofar,
Tun daga ranar ya gane cewa da biyu take kulle kofar kenan hakan na nufin cewa har yanzun kunyan had'uwa dashi takeyi,
Sai dai kuma gaskiya shi tana matuk'ar cutar dashi ta wannan hanyar, ita bata san cewa saboda itane yazo garin nan har ya kwana biyu ba amma haka nan ta tsiri hora shi da rashin ganin ta,
Kwana biyun nan kama kanshi fa kawai yakeyi akan rashin ganin ta dan ma yakan lab'e daga falon shi aduk sanda zata fita haka zaiyi ta kallon ta har saita fice, gashi gobe yake son yin tafiya zuwa Jos a kallah kuma zaiyi kusan sati baya nan,
A haka a babu yanda zaiyi din haka ya shirya washe gari yabar mata garin,
Yana tafiya ita kuma ta koma kan harkokin ta kamar yanda ta saba a baya,
Duk wannan abun a idon hajiya yake faruwa dan itama tasha tambayar dalilin da yasa meenal din take kulle mata kofar falo amma bata samu amsa gamsasshiya ba, sai dai kuma bata matsa mata ba ta kyaleta,
Yusuf kuma yakai ma Hajiya Ziyara na musamman a wani dare bayan ya tabbatar Meenal na cikin d'akin ta shi kuma Ak baya ma unguwar gaba d'aya a lokacin dan sun gama yanke hukunci shida su Musty aka cewa gara ya sanar da Hajiyan komai kawai tun yanzun kar in abu ya lalace a gaba tace dan me yasa basu sanar da ita tun da wuri ba,

To dai koma me suka tattauna zamuji shi zuwa gaba, ta amince ko ah ah nima dai ban sani ba, dan washe gari Yusuf din da AK suka wuce Jos Musty da Sadeeq kuma suka koma bakin aiki suma duk da dai yanzun Musty baya wani zama Sosai a Kaduna saboda hankalin shi dake kan ginin gidan da Meelat zata zauna a ciki da yaketa faman kokarin ganin ya kammala kafin lokacin bikin da kullum k'ara matsowa yakeyi,
Wannan kenan,


*BARI MU LEK'O SARKI*


Yauma kamar kullum tunda ya dawo daga wajen aikin daya kawo shi garin yake zaune a cikin d'akin shi na cikin barrack din da aka sauke su,
Zaune akan kujera mai mazaunin mutum d'aya ya mik'e duka k'afunshi sai ya daura su akan center table din daya jawo zuwa gaban shi kad'an,
Laptop ne a kan cinyar shi yana cigaba da duba hotunan gidajen da yayi magana da wani abokin shi dake can ZARIA ya turo mishi akan Maganar gidan da sukayi da Meenal cewa tana son ta siya ma Malam gida,
Domin bai baro garin ba a ranar sai da ya bada cigiya akan yana son gidan, kamar yanda yaba Salman umarnin kawo mata motar a ranar,
Tun zuwan shi bai samu zaman da zai duba hotunan ba duk da cewa abokin nashi yasha kiran shi dan yaji ko ya duba gidajen daya tura mishin domin duka a kasuwa suke,
Mamaki yake son bata dan haka sai ya yanke hukuncin turama Sa'eed hotunan Kawai akan ya taya shi zab'en gidan, sai da ya aika mishi hotunan kafin ya kirashi ya bashi umarnin son yake ya zab'a mishi d'aya a cikin gidajen daya tura mishin,
Rufe Laptop din yayi ya ajiye shi a gefe dan sai lokacin ne ya tuna da tonunan da Meenal din tace ta tura mishi a cikin wayar,
Dan haka sai ya d'auko wayar ya gyara zama bayan ya shiga cikin ma'ajiyar hotuna ya fara bincike,
Hotunan daya gani kusan kala 10 ne kuma dukan su na mutum d'aya ne sai guda biyun da sukayi ita da Meenal din ne hakan ya tabbatar mishi da cewa sune wanda meenal din ta tura mishi dan haka sai ya fara bin su d'aya bayan d'aya yana karema hotunan kallo,
Ya dad'e yana kallon hotunan bai iya furta komai ba sai kuma zuwa can yace,

"Meenal kenan wato saboda taga Teemah tana da d'an jiki kad'an shine yasa take son had'ani da wannan kenan?"

Eh kam gaskiya yarinyar cikin hoton tadan d'auki hankalin shi duk da a iya hoto ya ganta amma yana jin cewa zatayi dai dai da tsarin shi dan ya lurada cewa ta mallaki dukkan abunda yake buk'ata a wajen macen da zai zauna da ita a matsayin matar shi na aure, wato wayewa kyan fuska cikakken diri da wasu abubuwan wadanda shi ya barma kanshi sani,
A bayyane kuma ya k'ara furta cewa,
"Koma batayi ba ai dole in amsa haka da hannu bibbiyu ma kuwa tunda ta fito daga wajen abunda nike matuk'ar girmamawa a yanzun,
Inma batayin ba duk ni zan saita ta zuwa tsarin da nike muradin ta kasance min.


*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ
[8/23, 9:51 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*BOOK 2*


*PAGE 10*


Shi kam a Yanzun gani yake bashi da kalmar da zaiyi amfani wajen nuna godiyar shi ga Meenal,
Domin dai duk da kasancewar ta yarinya k'arama da ya tabbatar da cewa a haife zai iya haifan ta sai gashi ta sanadin ta ne yau ya kasance cikin nutsuwar daya rasa tsayin wasu shekaru a yanzun Allah da ikon sa zai kwanta yayi bacci lafiyar Allah kuma ya tashi ba tareda yayi wani mugun mafarki ba sab'anin lokutan baya da baya samun isshen bacci, rashin baccin nashi kuma bazai sa yace ya tashi ya gabatar da nafila koda raka'a biyu bane, domin a lokacin nema yake jin wata irin muguwar kasala haka zai b'ata dare a banza shi baiyi bacci mai dad'i ba shi kuma bai raya daren ba, sai gashi yanzun Allah da ikon sa a cikin k'asa da wata d'aya komai ya canza ciki kuwa harda ibadan shi dan ya k'ara kusanta kanshi ga mahaliccin shi sosai ga kuma azkar da yakeyi akoda yaushe, yasan kuma yawan farin cikin da yakeji a zuciyar shi duk suna da na saba ne da hakan,

Yasan ya aikata kura kurai da dama a baya, domin dai adah can baya tunawa da damuwar kowa sai na matar shi kad'ai baik'i yab'ata da kowa ba indai har ita zatayi farin ciki to bazai tab'a damuwa ba wanda dalilin hakan ya b'ata mu'amalan shi da mutane da yawa bayaga abokan shi da sukayi kokarin ganin sun dawo dashi kan hanya ciki harda wasu daga cikin yan uwan shi wad'anda ya shatawa layi duk akan matar shi sai yanzun ne kuma yake jin bak'in cikin hakan ya kuma d'aura aniyar gyara kuskuren shi da yardar Allah,

Adah can baya yakan manta cewa akwai hak'k'in uwa da uba ya'ya da kuma k'anne ciki harda hak'kin ita kanta matar da iyaye suka aura mishi da take zaune cikin gidan shi a matsayin matar shi,
ya nisan ta da kowa babu mu'amala mai kyau balle akai batun shak'uwa dan harta yaran daya haifa duk da a Yanzun sunyi girman da zuwa gaba kad'an yasan maganar auren su za'a fara amma suma bai samu damar da zai zauna ya jasu a jikin shiba balle har yasan damuwar su da kuma abunda suke buk'ata na yau da kullum dan a lokacin uwar yaran ita kad'ai ce a gaban shi ta yanda baya iya tuna kowa sai ita, ita kad'ai dai itace a lokacin yake gani kamar duk wani farin cikin shi yana tare ne da ita,
Sai gashi Yanzun Alhamdulillah dan ba iya nutsuwar zuciya yake jin cewa yasamu ba harma da nutsuwa ta cikin gangar jiki domin a Yanzun mazan takar shi ta dawo ta yanda akoda yaushe yake jin kanshi a matsayin cikakken namiji kamar wani saurayin da yake cikin lokacin kuruciyar shi sab'anin shekarun baya da inba yana tare da Teemah bane bayama tuna cewa shi din namiji ne,

Abun mamaki ashe abundai daya raina itace warakar shi zai fito a sanadin ta, dan hakan yasa yake ganin me nene ma wanda Meenal zata nema a wajen shi har ya kasa cika mata shi?
Dan a Yanzun ta wuce neman abu a gunshi shi dai da yake matsayin Babban yayan ta shine zaiyi tsayin daka wajen ganin cewa bata rasa komai na buk'atar rayuwa ba,
Duk da ko a Yanzun bawai matsayin daya bata ya canza bane,
Ah ah sai dai yana d'aukar al'amarin ta da girma ne sosai ya kumayi imanin cewa ita d'in tun farko dama ba matar tashi bace shi yasa yake mata fatan Allah ya had'ata da wanda zai kaunaceta kamar fitar numfashin shi,

Ya d'ade zaune yana cigaba da kallon hotunan Moon tunawa da paper din da Meenal ta rubuta mishi sunan yarinyar ne yasa shi mik'ewa dan tun a ranar yana dawowa ya cire shi a cikin aljihu ya saka shi a cikin wallet din shi gudun kar ya salwanta,

Inda wallet din yake ajiye akan side drawer ya nufa yana budewa ko ya zaro shi a inda ya soke shi,
Babu b'ata lokaci ya bud'e ya karanto, a bayyane ya furta,

"Maimoon, Lagos, ah lallai zuwa Lagos ya kamani,"

Address dinta da Meenal din ta tura mishi ya k'ara dubawa, kafin ya d'auko wayar shi yayi saving number din dake rubuce a jikin takardar da sunan "Moon"
Sai da yayi kamar ya danna ma number d'in kira sai kuma ya fasa, domin kafin komai ya fara shiga tsakanin su zai so ya Santa da kyau ta yanda zai san ta inda zai fara dan ganin ya kamo zuciyar ta cikin kwanciyar hankali, kuma ma gani yake ai yanzun yayi wuri ace ya kirata.

Komawa kan kujerar daya taso yayi ya zauna yana k'are mata kallo,

"Wannan yarinyar da wuya itama inba irin halin kawarta take da ba, daga ganin bakin nan nata sai tayi yawan surutu, wai zata ma so tsoho kamata kuwa?, Allah ka dafamin in samu shawo kanta cikin sauki"

Ya fad'a a bayyane, can kuma kamar wanda aka tsungula sai ya fita daga wajen hotunan ya koma wajen ajiyar lambobi,
Number din da yayi saving da suna Joseph ya aikama kira,
Number din bata dade da shiga ba aka d'auki wayar da harshen turanci suka gaisa,
Da harshen kuma sukaci gaba da magana inda shi Sarki yake tambayar Joseph din cewa yana gari kuwa? Shi kuma Joseph din ya amsa da cewa eh yana nan,
"Zan turo maka pic din wata yarinya da address a kanta ina son sanin komai a kanta, idan nace komai ina nufin komai", ya jaddada mishi,

"Babu damuwa sir duk abunda kake buk'ata zaka sani akanta cikin kwana biyu"

"Ok zan tura maka pic da address din yanzun"

Bayan Joseph ya amsa ne kuma Sarki ya yanke wayar sannan ya tura mishi,

"Ina ganin lokaci yayi da zan waiwayi Lagos"

Ya furta a bayyane domin tun kafin faruwar komai dama ya dad'e baije garin ba, ga shi kuma yanzun Zaria bata zuwuwa gaskiya dan ido da kunya wallahi,
Bai san da wani idon zai kalli baban shi da Malam ba idan yaje dan ta uwar gida mai sauki ne domin tuni suka dai daita tsakanin su, ba iya ita kad'aiba ma harda yan uwan shi yanzun shida kanshi yake kok'arin kiran su,
Shima kuma baban nashi suna waya dan shine ma ya shaida mishi komai daya wakana bayan ya gama mishi wankan tass a randa shi Sarkin ya kira shi, ya kuma ce mishi ya kira Malam ya bashi hak'uri,

Ranar daya kira Malam d'in sai Allah ya rufa mishi asiri wayar bataje ba dan wayar Malam din yana rufe,
Ranar daya k'ara kira kuma ya samu malam d'in yayi zaton zaiyi mishi fad'a ne ko ya nuna b'acin ranshi kamar yanda Baban shi yayi,
Sai malam ya bashi mamaki dan nasiha Kawai yayi mishi sosai mai shiga jiki ya kuma tunasar dashi akan rik'e ibada daga k'arshe kuma ya kora mishi warning akan ko kusa ko alama koda wasa shi Malam din yaji cewa Sarki ya saki Teemah tofa babu shi bashi,
Dan bayan mutuwar auren da maganar ta fita su dangi duka kowa tsinuwar shi akan Teemah ya k'are a zaton su ko itace silar da auren ya mutu shi yasa duk suke ganin laifin ta, yasan kuma tunda uwar gida tasa ya saki Meenal tana iya cewa ita ma Teemah sai ya saketa, dan haka Malam ya fad'a mishi cewa yayi na farko yayi na k'arshe idan ya samu matsala da matar shi inyaga cewa abin yafi k'arfin shi to yakai maganar gaban mahaifin ta tunda Allah yasa har yanzun yana raye,

Sannan ko dan darajar ubanta yaci a d'aga mata k'afa ga kuma yara har 4 Allah ya basu a matsayin zuri'a dan haka shi Sarki yayi hakuri daduk abunda ya faru a baya sai kuma a kori gaba,

Wannan abu sosai ya k'arama Malam kima a idon Sarki, domin dai a wannan lokacin da muke ciki bako wani uba bane za'a cutar da yarshi ya kauda kai balle kuma har ya rok'ama wacce ta cutar da yar nashi arzikin cigaba da zama da mijin data raba da yarshi alhalin yasa yana da ikon rabata da nata mijin itama,

To dai shima Sarki har yanzun fa bawai ya dena son matar nashi bane, domin dai ita d'in ita ce mace ta farko da zuciyar shi ta fara mata wankakkiyar kaunar da babu algus a cikin ta har yanzun kuma baya dena son nata bane,
Sai dai muce kaunar ta sauka daga kaso d'ari zuwa kashi 45,
Ya yanke hukuncin hukunta ta shi yasa ma har yanzun bai gwada neman ta ko a waya ba, tunda ya binciki mai gadin gidanta ya shaida mishi cewa bata gidan yasan tana gidan su dan haka bai damuba dan shima yana buk'atar suba juna space kowa ya sarara, dan yasan idan ya tunkareta a yanzun ana iya haihuwar uwar da bata da ido,
To gashi kuma yanzun uzurin zuwa Lagos ya kamashi dan yau d'ai daga ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login