Showing 117001 words to 120000 words out of 190771 words
dai yayi shi,
Idan kika sake kema kika shiga sahun su kika ce a duk sanda kuka samu sab'ani haka kema zaki dunga jera mishi kira dan ki shawo kanshi tofa gani zaiyi baki da banbanci dasu,
Ki saurareni da kyau, bawai ina nufin cewa koda ace kece kikayi laifi kiyi mursisi ba, ah ah in kinyi laifi dole ki bayar da hakuri amma bada rawar jiki ba, ke macece kina da naki darajar dole kuma ki rik'e darajar ki, dan haka dole salon ban hakurin ki ya banbanta, akwai banbanci wajen ban hakuri tsakanin saurayi da budurwa da kuma mata da miji, ke yanzun bakuyi aure ba dan haka salon saurayi da budurwa zamu d'auka, kamar yanda nace d'azun sak'on text zaki tura yanzun ki d'auki wayar ki, ba rubutu mai tsayi zakiyi ba ki rubuta mishi cewa (kana lafiya) sai ki tura mishi,
Idan ya maido amsa hakan yana nufin cewa fushin nashi bamai nisan zango bane, idan kuma mukaji shiru sai muje mataki na gaba ina fatan kun ganeπ€·π»ββοΈ"
Ta k'arasa fad'a tana kai gorar fanta bakin ta ta kurb'a,
A yayinda Meenal ta d'auki wayar ta tana rubutu itama Moon nata wayar ta d'auka ta rubuta same abinda Sultana tace ta tura ma Sarki itama kamar yanda Meenal ta tura ma AK,
Ita ko Meelat tasowa tayi tsam ta zauna a inda Sultana take zaune tana jiran Meenal ta cika umarni ta k'ara d'aura mata wani karatun,
Dafa kad'unta Meelat tayi "Sultana a ina duk kika san wad'an nan abubuwan? Abubuwan da kikeyi suna bani mamaki da kuma d'aure min kai manyan cen ki yayi yawa"
Hannun Meelat din sultana ta kama ta sauke shi daga kan kafad'arta, tana yatsina fuska tace "ku dai da kuke son mai da kanku baya sai kuyi ta zama waye yace muku iya ilimin boko da islamiya kad'ai mace take buk'ata dan ta rayu cikin salama ne?
Baku san dole mutum yana bukatar ilimin zama da mutane ba, to ilimin zama da mutane ne wannan domin yana da kyau kasan dawa kake zaune ko dawa zaka zauna dan kaci maganin zama dashi,
AK bai tab'a soyayyar gaskiya da gaskiya ba sai a yanzun Meenal itace first love d'in shi amma sai wasa takeyi da damarta ta kasa gane cewa abubuwan da takeyi shi Sabon abune a wajen shi domin dai tsayin rayuwar shi ya saba mata ke kod'ashi suna kware mishi,
Sai gashi yanzun da take da damar d'aurashi akan nata tarbiyar ya kuma biyu mata yanda take so shegen wauta yasa tun tafiyar batayi nisa ba tana ta faman kwafsawa, wallahi ina jiye miki kar abubuwan da kike mishi susa yayi dana sanin fad'awa soyayyar ki.... "
Katseta Meenal din tayi cikin fushi da cewa,
"To ni uban me nayi mishi kedai dama tuntuni na gane kinfi son shi dani" wayarta da yayi k'arar shigowar message ne ya katseta itama har rige rige sukeyi wajen d'aukar wayar su duba ko sakon shine ya shigo,
Maryam ce tayi nasarar d'aukar wayar,
"Wallahi shine" ta fad'a har hannun ta yana rawa a yayin bud'e sakon,
"Did you miss me?"
Shine abunda ya tura, dan haka a fili Maryam ta karanta dukan su suna sauraren ta,
"Kinyi kewar shi? " itama Sultana ta maimata da k'aramar dariya a muryar ta,
"Wallahi AK yana sonki sosai Meenal karki yarda kiyi sakacin da zaki rasa shi kinga nifa tsayin lokacin nan tsumayin kira ko sak'on ki kawai yakeyi gashi dai kin gani sakon ki na isa gareki ya dawo miki da martani alamun da ke nuna shima yana cikin kewar ki"
Rufe fuska Meenal tayi da tafukan hannayen ta tana dariyar jin dad'i, koba komai tunda har ya dawo mata da amsa tasan cewa yana lafiya dama damuwarta tasan ya yake,
Daga gefen Moon itama nata amsan Sarki ya dawo mata dashi ga abunda nashi sakon ya kunsa shi kuma,
"I miss you soo much My Moon please allow me to come and see you, can i call to hear your voice now please"
Yalwataccen murmushi ne ya bayyana a fuskarta itama, sai dai bata bashi amsa ba tana jiran jin tabakin sultana tukun na,
D'aurawa Sultanan tayi da cewa yanzun dai tunda mun tabbatar yayi kewa shima to ki gyale shi karki maida mishi ko wani amsa mu bashi mintoci mu gani ko zai k'ara turo wani sak'on"
"Kumaπ³ to idan kuma ya k'arayin fushi fa?" Meenal din ta fad'a tana kallon Sultana a marairaice,
"Bazaiyi fushi ba ina mai tabbatar miki da cewa kodai ya kiraki ko kuma ya turo wani sak'on"
Kamar yanda Meenal ta natsu tana jiran tsammani haka ita ma Moon dukan su tsammanin suke jira, maryam ce ta yanke shirun da cewa "Sultana kina gani har hanji ne?"
Dariya sosai Sultanan ta fashe dashi, "ni kuna bani mamaki wallahi"
"Ah ah kedai kike bamu mamaki abin mamaki kuma wai a hakan baki da tsayayyen saurayi to me kike jira" Moon ta tambaya,
"I am waiting for Mr right, nima mijina nike son in aura kamar ku dai wanda bazaiji nauyin ko kunyar nuna kaunar da yake min a ko ina ba kun gane ai dan nidai bana son ustazu wayayyen namiji nike so shi yasa har yanzun ban gama tantancewa ba, kunsan kwanaki wani abokin Ya Sheikh ne yaxo wai shi nan ala dole ni yake so" fashewa tayi da dariya tana dukan cinya tace "wai wai wai wayaga Sultana matar ustazu ninja kenan Allah dai ya raba bawa da wahala" dariyar suma suka tayata,
Moon ce ta amsa da cewa "kai gaskiya sultana kuna fama da wancan yayan naku, wai Sheikh fa in fad'a muku tunda na sauka a gidan nan wallahi ko sau d'aya bai yarda mun tab'a had'a ido ba, ke ko a hanya muka had'ufa duk'ar da kanshi yake shekaran jiyama wai harda Fauxieyerh yayi wai me yasa ni bana sa hijjab idan zan fita kuma wallahi yanzun ya dena zuwa sashen mommy Hauwa wai saboda ni bak'uwa ce, gaskiya dai yayan nan naku sufofin yan aljannah sak gareshi Allah dai ya bashi mata dai dai shi"
Hirar Sheikh din suka d'auko sukaci gaba da caccakan shi sultana tana basu labarin abokin shi da idan zaizo hira wajen ta saiya kwaso littafan addini wai da hirar banzan da zasuyi gara ya d'aura mata karatu abudai kamar a zamanin annabawa,
Suna cikin hirar ne wayar Meenal ya k'arayin k'ara sak'on AK ne ya k'ara shigowa wannan karon ma,
"Tun ba'ayi auren ba har kin fara yaji daga tudun wada zuwa unguwar malamai, to karki kiyi dare da yawa yau ki dawo da wuri I love you too" ya rubuta daga k'arshe,
"Hohoho dan Allah kuzo kuga yanda ake gudanar da wata sassanyar soyayya anan to wallahi yau nikam gidan Hajiya nika kwana yo ina dalili zan tare anan ga inda ake shan madarar love jama'a karfe nawa yanzun?"cewar Sultana
Shiko Sarki cewa yayi,
"ki shirya tarbata ayau idan na iso zan kiraki see you soon"
Hohoho dad'i kamar ya sumar da Moon haka ta dunga ji murmushin fuskarta kwata kwata yak'i d'aukewa,
"Kai ku tsaya! Waiku dan Allah baku lura da Moon ba wallahi akwai abunda take boye mana bata so mu sani tunda tazo na lura da hakan yanzun kuma ku kalli yanda take murmushi barrister me kike b'oyewa ne ko kema kin rufta cikin kogin ne?"
Maryam ta tambaya tana kada kai da nuna Moon din da yatsa,
"Yarsa ido kawai ke dai kika sani ni babu wani abunda yake damuna"
Meenal ce ta amsa da cewa "dan allah kyaleta ai kallonta kawai nake ki barta idan tayi wari ai zamuji yarinya in ma fargaban aure kike gara ki bari dan tunda Hajiya ta matsa kema kin san ba fashi gara ma ki zayyano mana naki samarin mu bajesu a teburin shawara mu tayaki zab'e atoh in kuma babu ni zan miki mijin"
Ita dai Moon shiru ta musu bata kulasu ba lallai yau idan Allah yasa Sarki ya iso lafiya ga da ga zasuyi shida ita tagaji da boye boye matsayin ta kawai take son sani a yau basai gobe ba,
Anayin Sallan Magrib Sultana da Meenal suka wuce tudun wada, ita kuma Moon cigaba da zama a gidan su Meelat tayi saboda idan ta koma gidan Malam bata san yanda zatayi ta fito su had'u da Sarki ba dan ko babu komai itama bazata yarda wani yagan su tare ba, ta kuma tura mishi sak'on Allah ya kawo shi lafiya,
A gidan Hajiya ko su Meenal suna isa Sultana tayi mata jagora suka shiga kitchen shinkafa suka samu an girka a gidan dan haka sai ta d'aura mishi tuwo raba hannu sukayi sultana ta dafa tuwon na masara ita kuma ta mishi miyar kub'ewa d'anye bayan sun kammala komai sama suka haura ita dai Hajiya kallon su kawai takeyi bata tambayesu dalilin shigar su kitchen ba balle suce ta fiye gulma gyara zaman ta dai tayi da kyau a falon ta dan tasan dai in ma bak'o zasuyi dole gidan zaizo dan tunda taga Meenal ta dawo gidan da wuri tasan ba'a banza ba,
Kwalliya na musamman yau Sultana tasa Meenal tayi itace kuma ta zab'ar mata kayan da zata sanya atamfa d'inkin riga da siketa ta kuma gyara mata fuska da kwalliya duk da kwalliyar bamai yawa bane daga hoda mascara sai jan baki Sultana tayi tayi ta sanya kwalli ita kuma tace a'ah wai bata son ta zaqe da yawa ya raina ta, k'in Saukowa k'asan sukayi sukaci gaba da zaman su a d'aki Sultana tana k'ara ba Meenal d'in shawarwari,
Karfe 9 saura sak'o daga AK ya shigo wayarta,
"Ki fito ki sameni nan da minti biyu a haraba"
Sultana ta mik'ama wayar bayan ta gama karantawa jiki na rawa ta tashi ta isa gaban mirror soson shafa hoda ta d'auka tad'an k'ara gyarawa ta d'auki turaren ta shima ta kara feffesawa ta zura takalmi, jiki na rawa ta fice daga cikin d'akin dan gani takeyi kamar idan ta tsaya b'ata lokaci minti biyun suka cika komawa zaiyi batareda ta ganshi ba, dariya sosai Sultana take mata, wai ba saban ba an fad'a soyayya.
Da gudu ta sauko ta fice daga falon ko Hajiya dake tambayar ta lafiya ta sauko da gudu gidan uban wa zataje da daren nan take shirin ficewa bata saurari Hajiyar ba ta fice dan itama tasan tana tsayawa lokaci kawai zata b'ata mata,
A harabar gidan taci burki tana gyara zaman rigarta ta kuma yafa gyalen nata a gefen kafad'un ta ta rife k'irjin ta, tana waige waige taga ta inda zai bullo,
Shiko dama tunda ya iso gidan shida kanshi ya karkashe wutan tsakar gidan ya kuma ce kar wanda ya sake ya kunna, ita ta fito daga cikin haske ne shi yasa koda ta fito duhun wajen yasa bata ganshi ba yayin da shi kuma yake can gefe yana k'are mata kallo daga cikin d'an kankanin hasken daya rage a tsakar gidan a hankali ya dunga takowa harya k'araso inda take yayinda ita kuma ta hango kawai sai kunyar kanta ya kamata dan tasan da zarar yaga kwalliyarta yasan cewa dan shi tayi dan haka sai ta juya baya taja gyalenta ta rufe fuskarta tana murmushin da bata san dalilin yin shi a wannan lokacin ba, shin najin dadin ganin shi ne ko koh dai,
Shiko yana isowa babu b'ata lokaci ya tsaya a bayan ta hannayen shi ya d'aura akan kunkumin ta ya rik'ota ya matso da ita zuwa jikin shi sai dai bai bari bayan ta ya tabi jikin shiba ya kwantar da kanshi a kad'arta daidai kunnen ta ya rad'a mata cewa,
"Likita did you missed me?" Ya tambaya da wata irin murya kwantacciya kamar baya son yin maganar,
Yummm haka ta dunga jin jinin jikin ta yana gudu daga wannan jijiyar zuwa wata,
Wallahi ji tayi kamar ta juyo ta rungume shi tace mishi nayi kewar ka AK, sai dai kuma ita d'in kunya ce ta haifeta dan haka bazata iya aikata hakan gareshi ba,
"Ki amsa min mana kewar nawa ne yasa kika gaza hakuri sai da kika nemo ni?"
Da sauri ta amsa mishi da cewa "ah ah kamannin fuskar kane dai ya fara bacemin shi yasa nace bari in tab'oka gashi kuma yanzun kazo naga fuskar naka"
"Da alama soyayyata ta rikita miki tunani shi yasa kika kira inzo ki ganni ko zaki dawo hayyacin ki kenan"
Juyo da ita yayi suna kallon juna ido cikin ido bayan ta d'an sauke gyalenta da tayi amfani dashi ta rufe fuska saiya zamana iya idanuwan ta yake gani, da kad'anΒ² ya dunga matsar da fuskar shi har ya zamana goshin su ya had'e dogon hancin shi ya goga akan nata hancin yana cigaba da kallon tsakaiyar idanun ta,
K'asa ya k'arayi da uryar shi, "toya yanzun kin d'auki hoton fuskar nawa dan so nike ki adana shi da kyau a cikin memoryn ki ta yanda bazaki k'ara mantawa ba"
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana kankame jikin ta dan Wallahi ba k'aramin jarumta take gwadawa wajen hana kanta bashi kyakyawan runguma ba, wani iri take ji sosai a jikin ta natsuwar data rasa ne takejin yana dawo mata har bata san ya zata kwatanta yanda takeji ba,
Baya ya matsa yana mata dariya kafin yace "to likita na gane wato bazaki iya rikewa ba koh? Nima daurewa nikeyi muje daga ciki kafin a sab'a lamba" ya k'arasa fad'a yana kashe idon shi d'aya da d'age mata giraren shi,
Kai jama'a wallahi AK bayaji, dan ba karamin kunya ya bata ba har sai da taji kamar ta nutse a wajen.
*Ummiee Zaria*
[9/29, 10:49 PM] Ummiee Zaria: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 38*
A daidai k'ofar falon Hajiyan yaja ya coge hab'ar shi ya dafe kamar mai tunani kafin yana wani fusgewa cike da basarwa yace,
"Ni anyama zan shiga nifa da nace sai nayi sati ban shiga falon nan ba kuma adadin kwanakin satin basu cika ba har yanzun dan haka kije kawai saida safe, damuwar ki ai dama na rashin ganina ne koh to gani kin ganni hankali ya kwanta"
Juyawa yayi da niyar barin wajen ita kuma da azama ta tari gaban shi, boyayyar murmushin da bata bayyana a fuskar shiba yayi dan dama yayi hakan ne dan yaga shin zata hana shi tafiya ko zata tsaida shin? Da gaske dai itama ta kamu ashe? Yake tambayar zuciyar shi, a fili kuma sai ya fuske yake tambayar ta da cewa,
"Yane akwai wani abun ne kuma?" duk'ar da kanta tayi tana wasa da yan yatsunta batareda ta d'ago sun had'a idoba tace,
"To bakai bane kawai daga zuwan ka ko zama bamuyi ba zaka wani ce zaka tafi, kuma fa ku lafiyata baka tambaya ba bayan kayi kusan sati ban ganka ba Allah kuwa har ciwo saida na kusayi"
Subhanallah ta furta tana rufe baki dan Wallahi subutar bakine ba abunda taso cewa kenan ba, wai miye haka yake faruwa da ita ne duk tabi ta wani rikice a gaban shi kamar wata sabon shigar soyayya salon duk ya gama raina ta,
Daure fuska tayi ta kauda kai gefe dan karma ya raina ta ehe,
Takowa yayi zuwa inda take ya rik'o hannayen ta duk da yanda take k'okarin kwace wa ya hanata,
"Fad'amin meya sameki da baki ganni ba? Baki da lafiya shine bazaki kirani ba? Meke miki ciwo yanzun ko kin warke? Idan baki da lafiya ki dunga kirana kina fad'amin kinji ni kuma komai nikeyi zan barshine in dawo inzo in dubaki lafiyar ki tafiye min komai karki k'ara yarda kiyimin wasa da lafiyar ki" hannun shi d'aya yakai kan wuyanta wai shi nan a dole so yake yaji ko jikin ta akwai zafi,
Baya ta matsa kad'an shi mai yasa ya kasa gane cewa ita bata son yana garajen kai hannun shi jikin ta ne? Duk sanda ya tab'a ta jikinta sanyi kalau yakeyi kamar an cirota daga cikin k'ankara,
"Nifa na warke kuma nace ka dena tab'ani bana son,"
"Kin warke?"ya tambaya yana binta da kallo bayan ya cire hannun shi a wuyan nata,
"Na warke fa,"
"To sannu Allah ya k'ara sauk'i yanzun kije ki kwanta saida safe"
Ita da take cewa bata son yana tab'ata sai gashi ta rik'o hannun shi a shagwabe, "to zaka wuce kuma baka shiga cikin ba, nayi maka girki fa ko bazakaci abincin dana b'ata lokaci na girka maka ba?" ta tambaya a marairaice,
Da mamaki yake kallon ta kafin yace "ni kikayi ma girki wai?"
Shiru tayi ba amsa,
"Me kika girka min koda yike koma menene ci zanyi tunda ke kikayi, ashe dai ana sona har haka amma da sharad'i bazan shiga inciba har sai kinyi alqawarin cewa zaki bani abincin a baki in kuma ba haka ba ink'i shiga wallahi" ya karasa fad'a yana d'aure fuska,
"Kai dan Allah" ta fad'a tana bubbuga kafa a kasa,
Shi kuma saiya kauda kanshi gefe kamar bai ganiba,
"Nidai dan Allah muje gaskiya in bakaci ba zanji babu dad'i kuma zanyi fushi, indai zakaci naji zan baka a bakin"
"Kinyi alqawari? Kuma kar ganin idon Hajiya yasa kice bazaki bani ba idan mun shiga" ya fad'a yana kamo hannun ta suka shiga falon da sallama a tare,
Gilashin dake taimaka ma Hajiya wajen ganin kananun rubutun dake cikin littafin addu'oin dake hannun ta tana dubawa tasa yar tsarta ta sauke zuwa kan hancin ta, ta saman gilashin taci gaba da kallon su bayan ta amsa sallamar da sukayi girgiza kai tayi tana tab'e baki kafin ta gyara zaman gilashin taci gaba da karatun ta,
AK bai saki hannun Meenal ba har suka k'araso inda Hajiya take kafin ita Meenal din ta zame hannun ta a cikin nashi ta wuce kitchen ta fara kwaso abincin data shirya mishi ta barshi suna gaisawa da Hajiya, fira suke a tsakanin su akan isowar su Abba Ahmad da su Baba Usman dama sauran ahalin gidan da zasu iso gobe,
Sai da ta gama shirya abincin