Showing 45001 words to 48000 words out of 190771 words

Chapter 16 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1535

bayan ta fito motar ta ta shiga shima kuma ya take mata baya a cikin tashi motar ya bita har zuwa gidan su ba tareda ya bari ta ankare da cewa binta yakeyi ba,

Sai da ya jera kwana 4 kullum zai rigata isa wajen kafin ta fita kuma shima zai rigata fita ya jirata a waje sai ya rakata har gida sannan ya juya, amma fa ya kasa mata magana saboda yanda yake ganin yanda take yarfa shi kullum,
A kuma zuwan da yake wajen ne har ya samu damar yin magana da waiter din da take attending dinta kullum ya mishi yan tambayoyi a kanta kuma gayen ya tabbatar mishi da cewa kullum tana zuwa in kuma bata zoba takanyi order din abunda take so ne su aika mata dashi gida, kuma ko tazo bata kula ko wani saurayi a wajen abunda ya kawo ta shi kawai takeyi tayi tafiyar ta, to a kwana na biyar dai yaci alwashin cewa zai tun kareta ne kai tsaye kawai ko wacce wacce dan haka bayan sunbar wajen a hanya can inda babu yalwar motoci yasha gabanta da motar shi,
Zama yayi kuma a cikin motar yak'i fitowa bayan ya tabbatar da cewa ya to she mata hanyar da zatabi ta wuce,
Ita kuma ganin hakan sai ta fara danna mishi horn tana mishi ishara akan ya bata hanya ta wuce, amma fir ya nuna kamar ma bai san da shi takeyi ba,
Wayarta ta ciro daga cikin jaka ta fito daga cikin nata motar ta fara d'aukar motar nashi hoto, ba tareda ta k'arasa inda tashi motar take ba, shima kuma hango fitowar ta daga mota shine yasa shi balle murfin nashi motar ya fito ya nufo inda take, bata sauke wayar ba haka taci gaba da d'aukar shi hotuna tana gamawa cikin sauri ta tura duka hotunan ma wata number, yana isowa inda take ta maida hannun da ke rik'e da wayar baya,

"Malam lafiya maiya faru zaka zo ka rufemin hanya?"ta tambaya da harshen turanci

Tsaye yayi suna kallon kallon shida ita batare da yace da ita k'ala ba,
Ita dai kallon sani take mishi sai dai kuma gaba d'aya ta kasa tuna a ina tasan fuskar shi,

"Magana nike son yi dake nasan kuma inba hakan nayi ba ba lallai bane ki tsaya ki saurareni duba da yanda bakya sauraron duk wanda zai tunkareki da niyyar gabatar da kanshi a gareki"
Ya bata amsa da harshen hausa, mai makon turancin da tayi mishi magana dashi,

"Bahaushe ne kai?😳" ta tambaya tana zare ido,

"Ga tabbas kin gani,"

Shima ya bata amsa, shiru tayi tana k'are mishi kallo da kyau sai kuma can ta nuna shi da yatsa,

"πŸ‘‰πŸ» SARKI tsohon mijin Meenal πŸ€”?"
Ta tambaya.
Shi kuma ya amsa mata da cewa,

"SUFYAN SULAIMAN LADAN nike Meenal din kuma da kika ambata eh ta tab'a amsa sunan mata ta a baya amma ita din har gobe matsayin k'anwa take a guna!"

"Eh ai dole haka zakace mana tunda ka sakar min yar uwa bayan ka maida ta k'aramar bazawara, wai ma tsaya to ni miye had'ina da kai da kazo ka kulle min hanyar da zanbi in wuce, to bari kaji wallahi in wani abu ya sameni na riga na d'auki pic dinka dana motar ka da Address din inda nike na turama yan uwana in case in sunji shiru ban dawo ba su san wanda ya sace musu ni, dan haka gara ka bani hanya salin alin inyi tafiya ta dan bani da wata alaqa da kai".



Kuyi hakuri yau ma dai babu editing kuma in bakuyi comment ba babu na dare, atohπŸ€·πŸ»β€β™€οΈ


#MEENAL
#MAI JAMA'A
#SHEIKH NASEER
#SARKI
#MOON
#TEEMAH
#MALAM
#HAJIYA.
[8/31, 10:25 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 17*


Da gaske kike kuwa babu wata alaqa a tsakanin mu? Tuna dai ko k'ila kin manta ne!"
Ya ambata a yayinda yake k'ara takowa zuwa inda take jingine da motar ta,

"To wacce alaqar kuma ta rage a tsakanin mu bayan wacce ka yanke ta da kanka?
Naga dai ai koda can ma kafin ka auri yar uwata ina maka kallon Ya'yan mune tunda koba komai ai ka girmeni kila ma ka haifeni, daga baya kuma bayan aure ya had'a ka da Meenal sai naci gaba da kallon ka a matsayin mijin yar uwata, yanzun kuma da komai ya k'are a tsakanin ku naga ai shi kenan koh, auren ai dama na dole ne yanzun kuma daka gaji da zama da ita ka saketa dan haka babu wata alaqa kuma a tsakanin mu!"
Ta k'arasa fad'a tana wani jijjiga jiki da turo baki gaba kamar wacce irin dama can din nan tana da k'umin shi yau kuma sai Allah ya had'asu dan haka bari kawai ta sauke mishi duk abunda ta kunso ko zata huce,

"Yanzun dai idan na fahimta dai dai kenan dai so kike kicemin kina fushine da fushin yar uwarki?"

"Eh eh kwarai kuwa aiko baka tambaya ba kaima ka sani dole ne in tayata daka mayar k'aramar bazawara kishi bayan mu sa'o'inta ko auren bamuyi ba, haka zata dunga shiga cikin mu ana banbance tsakanin mu da ita ana nunata a matsayin bazawara !"ta fad'a amon sautin muryar ta na fitar da fushin da ke cikin zuciyar ta,

"To naji kiyi hakuri koba komai ai dama aure da rabuwa kaddarori ne masu tafiya da lokacin su a tare, a shekarun baya Allah ya tsara cewa zan aureta har muyi zama na adadin wad'annan shekarun, shi yasa akayi auren ba tareda dukan mu muna soba yanzun kuma da lokacin rabuwa yayi sai allah ya raba kamar yanda ya had'a abun cikin kudurar shi, ni bazan ce ina farin cikin rabuwa da ita ko akasin haka ba kawai dai nasan cewa Allah shine yakeyin ikon shi a kan bayin sa shi ya had'a shi kuma ya raba dan haka ni bazanja da ikon shiba, sai dai Nagode allah da yasa bai bani ikon cutar da ita a zaman da mukayi k'arkashin inuwa d'aya tako wani fuska ba dama can Allah ya tsara cewa ita d'in ba matar da zan gudanar da rayuwar aurena da ita bane shi yasa ma rabuwar tamu tazo cikin sauk'i batareda an samu rarrabuwar kawuna ba duk da cewa a hakan ma nasan ita ce zata cutu dan in wani yasan gaskiyar cewar har yanzun tana tareda k'uruciyar ta wani bazai san da hakan ba,
nidai ina mata fatan Allah ya bata wani mijin mafi alkhairi a gareta, wanda zaiyi alfahari da ita har karshen rayuwar shi.

Ina fatan kuma keda sauran jama'ar da suke kallo na a matsayin mai laifi zakumin afuwa domin koba komai nid'in d'an adam ne ajizi kamar ko wane mutum,
Dan haka ina rok'on arzikin a gafarta min kuskuren da ake ganin na aikata kaina bisa wuya na please πŸ™ "
Ya k'arasa fad'a yana mai d'an dukar da kanshi k'asa,

Sanyi gabob'in Moon sukayi, dan ta yards abunda ya fad'a gaskiya ne d'an adam bai isa ya canza ma kamshi kaddarar da allah ya zana a rayuwar shi ba, dan haka itama sai tayi k'asa da kanta kamar yanda yayi tana wasa da da zoben ke sanye a yatsar ta na tsakiya,

Ganin tayi shiru bata ce komai ba sai shi kuma ya d'aura da cewa,

"amma ai ko babu komai ya kamata ace ko gaisuwa ne muyi koh? , ki duba ki gani fa saboda bazan iya ganin wacce nike ma kallon k'anwata in wuce ba tareda na tsaya mun gaisaba hakan ne yasa na biyo dan muyi gaisuwar yaushe gamo ,
Zanfi son ki cire batun wai na tab'a auren Meenal ki ajiye wannan batun a gefe ki d'auka cewar hakan bata tab'a faruwa ba dan nafi son kici gaba da kallona a matsayin wancan tsohon yayan naku na baya inda hali!"

"Tab' lallai ma"

ta ambata tana juya mishi kai irin fad'ama keya d'an kwali ya baka amsa d'in nan,

"Maimoon!!!

Ya kira sunan ta a dake bayan ya k'arema wajen kallo yaga babu wanda ya maida hankali akan tsayuwar nasu a wajen,
Yanzun fa da a can wajen ya tunkareta haka zata mishi a cikin mutane koh? Ikon Allah da girman shi da komai wai ya tsaya da wannan yar abar amma wai sai da ya gama rattafa mata zance na hankali yayi zaton ko natsuwar da tayi dukan hankalin ta ta bashi tana fahimtar me yake cewa ashe ba hakan bane wai ya gama zuba zance shi yarinyar nan wai zata cema *lallai ma*, shi dariya ma ta bashi wallahi Allah, dan da Alama itama d'in dai in ba'ayi da gaske ba bazata biyu ta dad'iba dan daga ganin ta yar daru ce, ,

Juyowa ita kuma tayi ba tareda ta iya kallon fuskar shiba tace,

"Ya Sarki dan Allah ka bani hanya in wuce gida lokacin komawa na gida yayi"

"Ya kike zaton cewa zan barki ki tafi bayan ko arzikin gaisuwa ban samu daga gareki ba, a matsayina na yayanki bayan nasan ba kalar tarbiyar da aka baki a gida ba kenan,"

Har k'asa ta d'uka irin gaisuwar da Yaroba ko Nufawa kewa manyan su ta sauke gwuiwar ta d'aya a k'asa daya kuma ta dafe shi da tafukan hannun ta kanta a k'asa ta shiga gaishe shi, da cewa

"Ina wuni ya Sufyaan?
Ka wuni lafiya?
Ya gida?
Ya aiki?
Ya ka baro mutanen Zaria?
Ya ka samu mutanen nan d'in su kuma?
To barka da zuwa fa, Allah ya maida ka gida lafiya nagode da zumunci Allah ya bada lada"
Tana gama rattafo jerin gwanon gaisuwarta ta mik'e tsaye tana kakkab'e jikin ta bawai kuma dan ta kwaso kura ba,

"Zan iya tafiya yanzun? A taimaka a bani hanya gida zanje"

Allahu Akbar jama'a mutumin kufa ya Lula can nesa wallahi,
Domin dai ita tayi mishi wannan gaisuwar ne cikin gatse amma kuma shi a wajen shi hakan ba k'aramin burgeshi da tafiya da hankalin shi tayi ba domin wallahi a tsayin rayuwar shi wannan shine karin farko da wata d'iya mace wacce ba daga cikin ahalin shi ta fito ba ta martaba shi da gaisuwar girma da mutun tawa irin wannan,

Shifa dama can Allah yayi shi mutum ne mai son girma kuma sai Allah yasa ko a cikin family din shi sai ya zamto cikin manyan yaran da aka fara haihuwa dan haka yake samun girmamawa daga kannen shi haka kuma a wajen aikin shi sosai yake samun girmamawa bama a wajen na k'asa dashi kawai ba harda manyan shi sukan girmama shi duba da yanda shima komai kankantar ka yakan baka naka girman,
Sai dai kuma yayi rashin sa'a na samun macen da zata girmama shi irin yanda yake so domin dai ita matar shi na gida inba wani abun take buk'ata a hannun shiba sau tari sai dai shine in sun kwana waje d'aya idan gari ya waye yake fara gaisheta,

idan ko akayi rashin sa'a shi bai ce mata an tashi lafiya ko ina kwana ba tofa sai dai kowa a cikin su yaci gaba da gudanar da harkokin gaban shi ba tareda anyi wannan gaisuwar na safe ba,

Amma sai gashi yau, k'aramar yarinyar da a haife ya haifeta tuni itace ta girmama shi da gaisuwa irin haka, to dan Allah tun yanzun ta fara daraja shi ina kuma ga ya maida ita mallakin shi ai shi kuma shi kenan sunan shi na Sarki ne zai k'ara tabbata wallahi,
Ita fa a nata ganin ya tabbatar bata d'auki hakan da tayi da wani mahimmanci ba, amma shi a wajen shi hakan da tayi ba kad'an ba yasa fara shin sonta da kimarta ya k'ara hauhawa a wajen shi, dan a yanzun kam ji yake babu wani abu dai taso wanda zai rushe Soyayyar ta da yake jin tana dad'a ginuwa a cikin zuciyar shi dan haka ba zai tsaya Sanya ba dan koba komai ai dama yan magana cewa sukayi da zafi zafi ake dukan k'arfe, gara yayi da jiki ya aure ta ya adana,
Allah dai yayi ma Meenal albarkha domin yarinyar nan shi kam a yanzun tsakanin shi da ita sai dai addu'ar fatan Alkhairi dan gashi dai ta silarta yana ta samun biyar buk'atar rayuwar shi d'aya bayan d'aya,
A ranshi yana da burin ya samu mace mai waye wa, bawai iya bud'ewar ido ba *No* har da cikakken ilimi na boko dana islama kyakyawar mace wacce ko ranshine ya baci kallon ta kadai zaisa nutsuwar daya rasa ya dawo gareshi, mace mai tarbiyar da zata iya kula dashi da tarbiyar yaran shi,
a yan kwanakin nan kuma a nazarin da yayi akan Meenal ya tabbatar da cewa itace sak irin matar auren da ya dad'e yana fatan k'are rayuwar shi da ita sai gashi yau kuma ta k'ara tabbatar mishi da hakan.

"Ya Sarki fa!"

Ta kira sunan da d'an karfi tana tafa tafukan hannayen ta a kusa da fuskar shi dan wannan shine kira na uku da ta mishi bai amsa ko d'aya ba bayan ita kuma a k'age take da son ganin tabar wajen ta koma gida dan dai ita bataga wani dalilin da zai sa ya wani tsareta ba atoh tsohon mijin Meenal nefaπŸ˜’,

Firgigit yayi yana sauke doguwar ajiyar zuciya,

"Muje in raka ki gida! "

Yana gama fad'in haka ya juya cike da takun shi irin na zaratan maza zuwa wajen motar shi,
Itama motar nata ta koma bai bata daman da zata shiga gaban shiba, ita ma kuma bata matsan ta ba haka taci gaba da binshi a baya dan so take taga iya gudun ruwan shi,
tunda dai ai ita tasan ba sanin gidan su yayi ba, sai kuma taga d'an bawan Allah yana shirin bata mamakin daya kusa sumar da ita domin dai a hankali a hankali sai gashi bai zarce da ita ko ina ba sai kofar gidan su,

dan nesa da gidan kad'an ya faka, itama da mamakin daya Sanya ta a ciki ya k'asa b'oyuwa a kan fuskanta kusa da tashi motar ta faka sai ta sauke gilashin motan suka fara kallon kallo a tsakanin su,

Ba tareda da fito daga cikin motar ba ta jefo mishi tambaya kamar haka,

"Ya Sarki dama ka shirya yin kidnapped dina yau ne?"
Ta tambaya muryar da tayi amfani wajen jefo tambayar da kuma yanayin fuskarta suna bayyanar da tsananin mamakin ta,

"Kidnapped kuma wa zanyi kidnapped?"

"Ni mana, to inba saceni ka shirya yiba ya akayi kasan gidan mu? Tsakani da Allah nidai nasan ba mak'iyiyar ka bace ni balle kace binciko maka ni kasa akayi, inba haka ba ya akayi kasan cewa nan ne gidan mu"

"Wa tace miki iya mak'iyi kawai ake bincika ne?
Ai masoyi ma abun bincike ne ki shiga daga ciki sai da safe ki gaishemin da mutanen gidan kafin in kawo musu nawa gaisuwar na musamman"

Bai jira cewar ta ba ya fice a unguwar da gudu ta ribas sai da ya isa bakin babban titi sannan ya juya motar zuwa hanyar da zai mai dashi nashi gidan,

Ita ko kasa gazgata abunda ya faru tayi,
Ganin tana k'ara b'atama kanta lokaci a wajen sai kawai taja motar ta shige cikin gida tana watsar da tunanin
abunda ya faru anan din, wata zuciyar ta na fada mata cewa kil'a dai yana lura da yanayin tuk'inta ne shi yasa ya gane gidan.

*A CAN KADUNA KUWA*

Washe gari tun da asubahin farko Hajiya ta farka,
Al'adarta ne dama da zarar ta farka wanka take fara gabatarwa idan ta shiga cikin makewayi kafin ta d'auro alwallah,
To yau din ma hakance ta kasance domin koda ta tashi saida ta gabatar da dukkanin uzurorin ta, bayan ta fito tayi zaman shafan mai sai da ta shirya tsaf kafin ta shimfid'a dadduma ta gabatar da raka'atainul fijir, bayan ta sallame ma zama taci gaba dayi akan daddumar tana jan carbi har sai da taji ana shirin tada Sallah a masallacin dake cikin unguwar,
Yunk'urawa tayi da carbin ta a hannu ta k'arasa wajen gadon in da Meenal ke kudundune sai baccin ta take sha hankalin ta kwance,

"Meenal ke!
Ke Meenal wai bazaki tashi ba tun dazun sai faman k'ara gyara kwanciya kikeyi kamar ba Sallah ake kira a masallatai ba?,
Kin san dai da wuri zamu bar gidan nan koh dan haka gara ki tashi kiyi abunda ke gaban ki atoh,

"Hajiya yanzun zan tashi fa, kuma ma ai ba'a kira Sallah ba"
Meenal din ta fad'a bayan taja bargon da Hajiya ta yaye daga jikin ta ta k'ara dukunkunewa a ciki,

"Kin san ALLAH idan baki tashi kin wuce kin d'auro alwallah ba da carbin nan zan dake ki"

Babu shiri Meenal ta mik'e zaune tana murza idanuwan ta bawai dan baccin ya saketa ba sai dan sanin da tayi cewa kadan daga cikin Hajiya kamar yanda ta furta tsaf tana iya zabga mata carbin nan wallahi, to ina dalili da asubahin nan baka karya da komai ba ka wani karya da duka,
Mutum ya girma ma amma kullum abu kadan sai hajiya tace zata kai maka duka,

Kafafuwan ta ta sauko kasa tana faman doka hamma da mik'a a tare, sai da ta lalubo hulanta wanda ya fita daga saman kanta tasa a kan nata sannan ta mike ta doshi hanyar makewayin,
Tana rufo kofa shi kuma AK ya bud'e kofar d'akin da Sallama, koda ya leko kanshi cikin d'akin ganin Hajiya tsaye akan dadduma kuma ba kowa akan gadon kawai saiya juya shima ya fice daga gidan zuwa masallaci dan dama ya leko ne dan ya gani ko sun tashi,

Bayan sun idar da Sallah gaisheda Hajiya Meenal tayi ita kuma bayan ta amsa sai ta d'aura da cewa,

'Ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login