Showing 189001 words to 190771 words out of 190771 words
sarewa dan haka ta roki alfarmar a kira mata iyayen ta dasu Uwar gida dan ta rok'i gafarar su,
Hankalin Sarki daduk na wani wanda yake kusa dasu sosai ya tashi dan jinin Teeman ya haye sosai ga kuma zubar jini da takeyi,
Washe gari Brigadier da ahalin shi suka sauka a garin Kaduna kamar yanda yan Zaria suma sukayi sammako ciki harda Moon suka taho dan duba jikin nata,
Wallahi duk wanda yaga yanda Teemah ta koma a lokacin take sai ya zubda mata hawaye dan kallo d'aya zaka mata ka tabbatar da cewa tana jin jiki dan ta d'ashe tass kamar babu d'igon jini a jikinta,
Ta rok'i gafara mijinta dana iyayen shi kafin nata iyayen da yayan ta,
Ta kuma tambaya cewa ko Meenal tazo dan itama tana son ta rok'i gafarar ta dan itama ta cutar da ita sai dai kuma Meenal bata samu halin zuwa ba dan haka sai ta rok'i Sarki ya kira mata Meenal din a waya ya had'asu ta roki Meenal din gafara,
Meenal kuma tace ita dama bata rik'e ta a raiba dan haka karta wani damu kanta allah dai ya yafe mana baki d'aya,
Waje ta nemi a basu tana so zatayi magana da Sarki da Moon dan haka yan d'akin suka fita aka barsu su uku,
Kamo hannun Moon d'in tayi ta had'a dana Sarki ta runtse su a cikin nata,
"Maimoon nauyi nike so in d'aura miki,
Nauyin kula da mijina da kuma tarbiyar yara na, tun daga sanda likitoci suka tabbatar min da cewa ina d'auke da ciki nike fata da addu'ar cewa Allah yasa cikin namiji Allah ya bani wannan karon,
Kinsan saboda me nike ta wannan addu'an?"
Girgiza kai Moon tayi ba tareda ta iya bude baki ta amsa ma Teeman ba,
Ita kuma saita d'aura da cewa,
"Saboda tun haihuwa na na farko nike ta fatan Allah ya bani Namiji dan a nawa zaton haihuwar namiji shine zai bani damar mallake mijina dama duk wani abunda ya mallaka,
Amma Allah da ya duba zuciya ta yaga ba niyyar alkhairi ne dani ba sai ya nuna min ikon shi wajen bani haihuwar akai ² sai da na jera yan mata har uku amma duk ban nuna godiya ta wajen Allah ba alhalin wasu nacan da arzikin su lafiyar su suna yawon neman haihuwar amma har yanzun Allah bai nufa sun samu ba,
Haka na haifi yan matana amma kaf cikin su babu wacce naja a jikina na nuna mata kauna har zuwa sanda uban su ya gaji da gani ya kwashe su ya dawo dasu gidan kakan su,
Wallahi ko damuwar dana nuna a lokacin bawai har ciki zuciya ta bane dan ni dadi ma naji dan dama gani nike kamar suna takura min, bayan haka kuma Allah ya bani cikin Boy, ina son yarona sama da yanda nike son kaina domin a duniyar nan daga shi sai uban shine Allah ya jarrabe ni daso idan aka cire iyayena,"
Tana shashshaka taci gaba da cewa,
"Ki duba ki ga yanda rayuwar ta juyamin a sanda buri na ya cika yau ni Fateemah nice na zama uwar yara maza har biyu a lokaci d'aya,
Sai dai kash damar haihuwar kawai Allah ya bani domin bani da tabbacin cewa zanyi rayuwa dasu balle har in tarbiyar tar dasu daga nan har zuwa girman su,
Jikina yana bani cewa tafiya zanyi in barsu ba tareda sun san dadina na uwa a wajen suba, dan haka zanyi amfani da wannan damar in damk'a amanar su a hannun ku keda uban su ina fatan zaku kulamin dasu bayan ba raina,
Dan Allah ki rik'e min yarana kamar yanda zaki rik'e naki karki duba cewa su din yayan kishiya ne kice zaki kuntata musu,
Ina fatan zaki kula dasu ki kuma tarbiyar tar dasu fiye da yanda nima zanyi idan ina tare dasu... "
Bata kai k'arshen bayanin taba numfashin ta ya fara sauka dan haka da gudu Sarki ya fita waje ya kira likita suka shigo suka cigaba da dubata,
Babu wanda yayi zaton cewa Teemah zata k'ara kwana a raye amma da yike Allah ne mai kashewa da rayawa a hakan tayi kwana biyu a asibitin ganin jikin yak'i sauk'i ne kuma yasa Brigadier ya rok'i alfarma wajen Sarki akan cewa zasu wuce da ita Lagos washe gari shima baik'i ba dan ko ina sukace zasu kaita indai zata samu lafiya bazai hanaba,
Sai dai kafin dare kuma jikin yaran duka biyu ya rikice aka rasa mi yake damun su dan kowa dai yasan lafiya lau aka haife su sai gashi kafin ace a gama bincike a gano abinda ya same su dukan su biyun Allah ya k'arbi abinshi,
Mutuwar da babu wanda bata sa kuka ba a wajen,
Ba'a yarda uwar ta sani ba dan tuni dama ta fice a hayyacin ta akaje akayi jana'izar su zuwa gidan gaskiya, ita kuma washe gari iyayen ta suka wuce da ita Lagos kuma harda Sarki da Moon suka bisu yan Zaria kuma suka koma sukaci gaba da amsar gaisuwa acan,
Anyi bikin Maryam lafiya kuma itama a zaria zata fara zama kafin in sun kammala karatun su ta tare a Abuja,
Bayan wani lokaci jikin Teemah yayi sauki sosai dan har an sallameta daga asibiti ta dawo gida,
Koda ta samu labarin rasuwar yaranta kuma sai Allah ya daura mata wani irin dakiya da dangana,
A yanzun kuma da suke zaune gida d'aya ita da Moon lafiya kalau suke zaune babu maijin kansu dan idan ka shiga gidan ma bazaka gane ko wacece keda girki ranar ba a cikin su, had'uwar kansu kuma ba k'aramin kwanciyar hankali ya saukarwa Sarki ba dan yanzun haka yana shawarar ajiye aikin shine ya dawo gida kawai yaci gaba da kasuwancin shi ya zauna cikin iyalan shi ya basu cikakkiyar kulawa yanda ya dace.
Alhamdulillah su Meenal karatu ya kammala a yau dai ta amshi kwalin karatun ta na zama likita ita da su Maryam dan haka bayan an kammala shagalin makaranta suka dawo gida suka d'aura sabon celebrating na kammaluwar cikar burin ta guda uku,
Ta kuma amshi kyaututtuka masu yawa daga hannun mijinta da *danginta* tako ina kauna kawai ake nuna mata ita da d'an cikin ta a satin ne kuma akayi masu rakiya zuwa kaduna sabon gidan ta kuma Hajiya ma tattarawa tayi ta bisu dan tace bata zama a Zaria ta zauna su kuma suje can jarabar su yasa su k'arkad'o mata tattab'a kunne,
An sanya ranar auren Salman tareda kanwar Raheenat wato yarinyar Baba Adamu kuma shi Salman din ne yagan ta yace yana so dan haka Malam ya bashi dama suka dai daita kansu,
A lokacin dai kusan biki takwas aka had'a akayi a lokaci d'aya harda na Raheenat da Ya Abakar Alhamdulillah *dangi* sai kara fad'ad'a yake tako ina,
*Bayan shekara uku,*
Nagode Allah daya kawo ku, to wallahi ku shirya k'afarku kafar yaran ku in kun ta shi wucewa ku wuce da abunku na gaji da hutun haka zaman da sukayi min na kwanaki ma Allah ya bani ladan surutun da sukayi ta sani, yo jama'a ina dalili ku da haihuwar yara ni kuma dayi muku wahala dasu? Kun san zasu dameku kukayi tayin cikin su kuna haihuwa?
In gaskiya ne ai sai ku tura ma iyayenku can su tayaku raino bawai ni tsofai tsofai dani ba nayi dawainiyar iyayen ku nayi naku yanzun kuma ga yaran ku"
Hajiya ce ke wannan surutun a yayinda AK ya rik'o hannun Meenal suka shigo cikin falon da k'aton cikin ta a gaba,
"Amma dai Hajiya kece ki kace a kawo miki su fa,"
AK ya fad'a a yayinda ya zaunar da Meenal saman kujera,
"Ai boyemin gaskiya kukayi tun farko da sai kuce min haka yaran ku keda shegiyar b'arna harda na mugunta,
Wallahi tunda sukazo na dena samun damar yin baccin rana in kaga na huta a gidan nan to saifa in nasa Kabiru yakai can gidan Malam shine nike hutawa kafin su dawo"
Da gudu yaran suka fito daga cikin kitchen ko wanne da filet din abinci a hannun shi,
Oyoyo daddy suke ta fad'i a sanda suke k'okarin k'arasa wa inda AK da Meenal suke shi kuma AK sai ya bud'e hannu ya taresu dan yasan suna iya isa su afkama Meenal din dake fama da kanta,
"Baku ganin abinda ke gaban Mommy ne kuke kokarin danneta?"
"Daddy Hajiya tace mana Mommy zata haifo mana wani mommy irin na khairat"
Ahmad wanda suke ma lakabi da Ayman yaron Meenal na farko ya fad'a,
"Eh dady na ai kaima kana son k'anin koh?"AK ya maida tambayar nashi kan Usman yaron su na biyu wanda suke kira Akram,
"Mommy babies da yawa zaki aifo mana muma koh?"Akram din ya tambaya da hausar shi da bata fita sosai,
"Eh ai gara ta haifo da yawan ko itama ta samu ta huta da haihuwar da takeyi duk bayan shekara d'aya,
Ni Inba a kan kuba kaf dangin ma babu wacce ta tab'ayin gwarne wallahi amma ku tsabar jaraba kafin yaro yayi kwari kin kwaso wani"
"Hajiya ba gara mutum yayi haihuwar ya gama da wuri ya huta ba" cewar Meenal tana b'ata fuska,
"Eh aifa shi yasa kike ta sauri to allah yasa a gama lafiya"
Sultana da Bash tuni suka bar k'asa suka koma Malesia can inda ya baro, itama kuma ta haihu yarinyar ta guda d'aya wacce bash din yama Aminatu takwara, kuma har gobe zumuncin su yana nan babu abinda ya girgiza,
Moon ma a shekarar farko da auren ta Allah ya bata k'aruwar yan biyu duka maza, biyun da suka koma ne suka dawo ta jikinta kuma itama har yanzun lafiya lau suke zaune ita da teemah da yaran su ga kuma Salman da matsar shi da suke tare dasu a gida d'aya,
Maryam da Meelat mutanen abuja suma dukan su Allah ya basu Meelat yaranta biyu mace da namiji maryam kuma tana da yaro d'aya.
*ALHAMDULILLAH ANAN ZAN DASA AYA, ABINDA NA RUBUTA DAI DAI UBANGIJI ALLAH YASA MISHI ALBARKA, AKASIN HAKAN KUMA INA FATAN ALLAH YA YAFE MINI*
*YAN UWA MARUBUTA DA MAKARANTA WADANDA SUKA TAYANI TURA LITTAFIN ZUWA SAURAN GROUPS INA FATAN ALLAH YA SAKA MUKU DA MAFIFICIN ALKHAIRIN SA NAGODE KWARAI DAN NA YABA, KUNA DA YAWA SHI YASA BAZAN RUBUTA SUNAN KU BA,*
*XIEYERH NAGODE KWARAI DA KAUNA🥰*
*Ni ZAINAB USMAN UMMIEE ZARIA dana shirya labarin na tsara na kuma rubuta ina yima d'aukakin makaranta littafin DANGINA fatan alkhairi, allah ya bamu ikon yin koyi da abinda littafin ya kunsa mai kyau mu kuma watsar da marar amfani.
*UMMIEE CE*