Showing 75001 words to 78000 words out of 190771 words
kuma kike shirin fita babu mayafin kirki a jikin ki?"
Shiru tayi tana binshi da ido kamar bata fahimta akan me yake magana ba,
"Eh nace baki da Hajibi ne ke?
tunda kika dawo ban k'ara ganin ki da Hijabi a jikin kiba kullum sai dai ki zura doguwar riga ki yane kanki da figaggen mayafi ki fita haka nan kina yawo a gari ko kunya bakyaji,
ko dama su hijjaban dana dunga ganin kina sawa a can gidan rasuwar na aro ne?"
Sim sim Sultana ta fara takawa sai da tayi d'an nisa dasu kad'an kafin ta tattaro rigarta ta kwasa da gudu ta koma sashen Mommy Hauwa dan tasan yana gamawa da Meenal din wallahi kanta zai dawo,
Ita kanta Al'amarin na yayan su yana matuk'ar d'aure mata kai, tsananin shi yana neman yayi yawa wallahi shi fa ko a can Abuja kannin shi ba wani son zaman shi a kasar sukeyi ba domin dai daya dawo tofa dole kowa ya aro ustazanci ya yafa shima,
shifa komai sanyi ko tsananin zafi bai kaunar yaga kannin shi mata da jiki a bud'e, ah ah in shiga zakiyi sai dai ki kin kima k'aton hijabi sannan kibi da safa hannu da k'afa ga kuma uban niqabi kamar wata ninja,
Shi yasa tunda yazo gidan suke matuk'ar shiri da Fauxieyerh kanwar Meenal saboda ita dai haka nan Allah ya halicce ta duk wuya duk rintsi bazaka rasata da hijjab a jikin taba tana nan kullum jiki a kudundune uwa wata konanniyaπ,
Sab'anin Meenal da tun tasowar ta ita daman kowa yasan mafi yawar suturun ta dogayen rigunan abaya ne sai kuma ta lulllub'e jikin ta da mayafan su, koda tayi aure kuma bawai ta canza shiga bane,
Yanzun kuma data samu cigaba sai ya zamana shigar nata ya canza mai makon dogayen rigunan da take ta'amali dasu a lokacin baya yanzun takan sirka dasu riga da zani ko riga da siket English were tafi amfani dasu ne ranar da take gida shima kuma tafi ta'amali da riga da Sket a gidan Hajiya ne kad'ai take sakewa tayi kalar shigar da tayi ra'ayi tunda can din babu tarin maza kamar nan gidan su,
Mai da kallon ta tayi zuwa ga kayan jikin ta,
Doguwar rigar abaya nefa navy blue a jikin ta sabuwa dal dan yau ta fara sakata yana cikin tsarabar da Momin Abuja ta kawo mata,
kuma ko kad'an babu ta inda rigar ya kamata dan a sake sosai rigar take, kuma gyalen datayi rolling dashi ma yana da girma dan ya sauko sosai ya rufe mata har kasan k'irjin ta,
"Ki koma ciki ki sanya hijjab in fitar ta zama dole!"
"Iyye π³"
tace tana zaro idanuwa cike da mamaki,
Jama'a yau nike ganin mulkin mallaka, to inba haka ba ina ma ruwan shi da itane da zai nemi matsa mata,
Zaman shekaru 6 tayi da Sarki amma ko sau d'aya bai tab'a ce mata ta koma ta canza kaya wai dan zata fita ba, kafin auren ta ma ai tayi zama a gidan nan amma ko Malam bai tab'ayin mata magana akan shigar da takeyi ba, kuma ita a iya hasashen ta bataga ta inda shigar ta ya gaza ba, babu inda ta bari a bud'e komai a lullub'e yake daga kafarta tafin hannu sai fuskarta ne kad'ai fa a waje,
"In kin gama nazarin kina iya komawa daga ciki, baki fita gidan nan har sai kin sa Hijjab na fad'a miki, dokar daya kamata ace kece kike kafama kannen ki sai gashi kema yi kikeyi kamar wata *Yarinyar goye* "
Innalillahi jama'a wai ita Uwar malam ne ustazun nan ke cema tanayin abu kamar wata yarinyar goye,
Aiko yasin ya shirya ganin aikin yara indai ita ne badai ya samu waje yazo gidan su ya zauna har shine yake ganin cewa yana da damar kafa mata wasu sharad'od'i ba.
"Ni bani da Hijjab kuma wannan shigar ita na sabayi tun ban kai haka girma ba, kuma babu wanda ya tab'a cewa dole insa Hijjab dan zan fita dan babu ta inda suturar jikina ta kasa"
"Sune basu ga inda ta kasa d'in ba amma aini gashi na gani, ki koma ciki ki tsaya a gaban mirror ki kalli kanki da kyau"
"To ai dai nace maka bani da Hijjabai anan gidan kayana suna gidan Hajiya sai naje can zan kwaso tunda na aron da nike sawa na baro ma maisu kayanta"
Tsalle daya yayi ya haye saman booth d'in motar dake kusa dashi ya d'auki kiran daya shigo wayar shi ya shareta,
Haushi bak'in ciki da takaici sune suka nemi sata ta jawo kafar shi ya fad'o daga saman motar da yake zaunen,
Kuma wallahi wallahi bai isa ya hanata fita daga gidan nan da shigar nan ba,
Toma waye shi dazai wani ce zai kafa mata dokar da dole tabi, allah ma yasa ba iya wannan ne kofar fita daga gidan ba, dan haka fuuuu ta juya ta koma sashen nasu, tana shirin shiga Sultana ta sawo kai zata fito sanye da zumbulelen hijjabin ta har k'asa mai ruwan kwaiduwar kwai,
"Ya koro ki kizo ki canza shiga kenan? "
Sultanar ta tambaya tana dariya,
"Wannan yayan naku sam bashi da halin kwarai wallahi to wai ma ni kad'aice mace a gidan nan dazai wani samin ido har haka?
Ina ruwan shi da shigar jikina tunda dai bashine yake siyan min sutura ba,
Kuma wallahi bazan canza kayan ko insa Hijjab dinba kuma sai na fita d'in sai dai idan na dawo ya dafani ya cinye"
"Ke Sister karki wani b'ata ranki, akan abunda yace indai Ya Sheikh ne haka yake indai yana waje duk sai ya takura ma rayuwar mutane yake jin dadi"
"Key din motar fa?"
Meenal ta tambaya.
"Gashi nan a cikin jaka ta"
"Ok to jeki kawai zan same ki a kofar gidan su Meelat ko kuma mu had'e a kasar layi kawai dan ta k'ofar baya zan fita, idan ya tambayeki ni kice mishi nayi fushi na fasa fitan kinji"
"Wai da gaske bazaki sa hijjab d'in mu tafi ba? Koni da kikaga nasa ai dan dai kawai a zauna lafiya ne amma muna fita zan cire shi sai zamu dawo zan mayar dashi a jikina"
"Wallahi bazan saba in kuma ya tab'a siyamin kyalle da sunan sutura ne sai ki fad'amin, ke karfa kiga wai dan yana matsayin yayanki kiyi zaton zan d'aga mishi k'afane idan naga zai takura min tam"
Tana gama fad'in hakan tabi ta baya ta fice daga gidan shiko Sheikh yana can yana zaman gadi koda Sultana tazo ta shiga motar harta mishi sallama cewa sai ta dawo bai tambayeta ina Meenal ba domin daga yanda tabar wajen yasan fushi tayi.
Moon kwance take akan gadon d'akin ta misalin karfe 10 na dare, wayane a hannun ta tana chat dasu Meelat da suka bud'e group wanda suke tattaunawa akan bikin Meelat d'in,
Sai dai lokaci lokaci takan fita da group d'in ta amsa sakon da Sarki yake turo mata,
"Mai kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?"
"Nothing important kawai muna hirane nida su Meelat kasan next week ne bikin ta so shirye shiryen bikin mukeyi muna tattaunawa ne"
" oh kuna da biki shine ma babu gayyata?"
Saida ta tura mishi da emoji mai murmushi kafin ta bashi amsa da cewa,
"π wannan kuma tsakanin ka da k'anwar Meenal ne"
"Oh kenan ke bazaki iya gayyata na a mai makon taba kenan? ,
to in haka ne ki shirya sai mu wuce tare gaba d'aya dan nima dama wani abune ya tsayar dani a garin ku da yasa nakai har yanzun ban koma ba kinga sai mu wuce kawai tare inba damuwa"
"Ok to kana ganin har zaka gama naka uzurin kafin lokacin?"
"insha Allah ina sa ran hakan addu'a dai nike tayi har yanzun da kuma neman zab'in Allah,
Kin san me?"
"Ah ah sai ka fad'a"
"Aure nike so in k'ara Moon, kin san wanda ya d'and'ana zama da mata biyu da wahala ya iya rayuwa da mace guda 1 kuma sai in lalura ne ya gifta"
Tun d'azun da suke hirar a kwance take,
Amma tana gama karantar wadannan kalmomin ta mik'e zaune dangal gal gabanta na tsanan ta bugawa,
Innalillahi wa'innah ilairir ta shiga karantowa kasa k'asa a yayinda take jin wani kalar tashin hankali yana yunk'uro mata,
To kenan dama duk kusan ta kanshi da yakeyi da ita bawai dan yana sonta bane?
To in har dama yana da wacce yake so a gefe mai yasa rana d'aya kwatsam ya dawo cikin rayuwarta har yasa zuciyar ta ta samu kusanci dashi,
K'arar kiran daya shigo cikin wayarta ne ya katse mata dogon tunanin da takeyi,
Number din shi da tayi saving da *King* ne ya fito b'aro b'aro a fuskar wayarta,
Bata iya d'aukar wayar ba harta k'ara ci ringing d'in ta yanke,
Sako ya k'ara tura mata ta WhatsApp din yanzun ma inda yake cewa,
"Na kira baki d'auka ba! Koda yikema ba damuwa muyi hirar anan kawai"
"Hummm" shine amsar data tura mishi,
Bai damu ba ya k'ara tura mata da wani sak'on kamar haka,
"Na samu macen da nike ganin zatayi dai dai da tsarina, saboda itane ma nabaro aikina na taho, sai dai har yanzun shakka da tsoron yanda zata amshe ni hakan yasa na kasa fitar mata da abunda yake cikin zuciyata, tsoro nikeji kar sai na tunkare ta ita kuma tace min na mata tsufa, I really don't know how to tell her I'm in love with her, ko zaki iya taimaka min?"
Amsa ita kuma ta tura mishi da cewa,
"Just let her know that you love her, tell her karka b'ata lokacin da wani zai so ya maka shigar sauri, kuma da kake maganar cewa ka mata tsufa indai tana sonka ai bazata tab'a ganin tsufan naka ba, kai dai kabar rai da abunda yake so kawai"
Wani sak'on ya k'ara turo mata kamar haka,
" You are right ok let me practice once on you first,
*I LOVE YOU MAIMOON*"
"I love you too,
You can now go ka fad'amata gaskiyar abinda kake ji a kanta! Zan kashe wayana sai da safe, idan mun had'u zanji yanda kukayi da ita"
Itama ta tura mishi
"Wait please don't go, saboda na riga na fad'amata har ma ta bani reply ko"
Ya aiko mata,
"Wow na tayaka murna"
"Bari in turo miki amsar da ta bani"
Saman chat d'in su ya koma yayi tagging d'in amsar data tura mishi d'azun inda tace "I love you too"
Sai ya rubuta mata "kinga amsar data bani"
π³ zaro idanuwan ta tayi waje cike da mamaki da sauri hannun ta ya typing ta tura mishi cewa,
"Amma wannan ai chat d'in da mukeyi da kaine!"
"Eh ai saboda kece yarinyar da nike so d'in shi yasa, Nagode kwarai da amsa tayin soyayya ta a gareki, a yau kinsa nima ina jin kaina kamar sabon saurayin da bai tab'a aure ba balle har ya haifi yara 4 insha Allah kuma zanyi k'ok'ari zuwa gobe in kawo ma Baba Usman gaisuwa da rok'on iri dan gaskiya ina buk'atar ki a kusa dani kwarai da gaske, ki kwanta kiyi bacci yanzun sai da safe,
*I LOVE YOU TOO SWEATHEART*"
Yana tura mata ya kashe data dan yasan dole zata nemi k'ara jin ta bakin shi.
*Ummiee ce*βπΌ
[9/13, 4:11 PM] Ummiee Zaria: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 26*
Kusan raba dare tayi ba tareda ta iya rintsawa ba, kira ko ta kwatanta kiran shi sau adadin da bata iya lissafi ba, sai daga baya ta gane cewa da gangan nema ya kama tashi wayar ya kashe tunda dole yasan cewa zai sa zuciyar ta a shiga ukun da dole ta kirashin tunda ya sauka a online,
Wai ita Sarki keso!
Bai tsaya iya nan ba kuma har saida ya mata wayau yasa itama ta amayar da abunda ke cikin nata zuciyar duk da cewa ita koda ta rubuta mishi kalmar I LOVE YOU TOO,din ta tura tasan cewa kalmar daga k'asan zuciyar ta ta fito amma bawai da wani manufa ta tura hakan ba,
Wato su maza idan basu nuna ma mace ban bancin yawan shekaru, wayau, da kuma hankali ba basa samun nutsuwa,
Anya ma kuwa ba itace ta kwafsa ta yanda yayi saurin gane cewa itama son shi takeyi ba kuwa?
Ita yanzun duk ba wadannan ne damuwar ta ba irin yanda yace wai gobe zaizo gida ya kawo gaisuwa,
To idan Baba Usman ya tambayeta mai zata ce mishi?
Kai gaskiya fa tana cikin chakwakiyar da bata san wanda zai fidda taba, waye ma wanda ya kamata ta tunkara da wannan maganar wanda zai bata shawarar daya dace?
Meenal ce sai dai a yanzun kuma bata jin zata iya tunkarar Meenal din da wannan maganar dan har yanzun gani takeyi kamar taci amanar meenal din ne, to amma ai indai abun ya tabbata dole meenal din zata sani bai kamata kuma taji a bakin wani ba a dai yanda suke kamata yayi ace itace wacce zata sheda ma Meenal din komai dake faruwa to amma kuma ta yaya?
Shin fitowa fili zatayi tace mata,
Meenal tsohon mijinki wanda kuka rabu ya dawo wajena yana sona da aure ko da wani kalmar zatayi amfani wajen yi mata bayani,
Wallahi Allah ita dai Allah ya sani tana cikin tsaka mai wuya sosai kuwa ga abun murna ya samu amma kuma babu halin yin murnan,
Umman su da hawowarta saman kenan tazo d'aukar wani abunda ta manta bata d'auka a d'akin ta bane ta hango wutan d'akin Moon d'in a kunne,
A gogon wayarta ta kalla wanda ya nuna kusan 1 saura na dare, mamaki ne ya kamata domin tasa Moon din mawuyaci ne ka sameta a farke zuwa wannan lokacin dan ita da wuri take bacci bata dogon hira duk ranar da batayi baccin da wuri ba kuma to tabbas sai dai in suna da wani case mai mahimmanci, dan haka mai makon ta wuce dakin ta kamar yanda tayi niyya sai ta juya akalarta zuwa d'akin Moon din dan ta kashe mata wutan.
Da sallama ta shiga bayan ta tura kofar, tsayuwar cak tayi tana bin Moon d'in da kallo wacce ke kai kawo a cikin d'akin ta kasa zaune ta kasa tsaye mafita kawai take nema ta yanda koda maganar nan ya fita jama'a bazasu kalleta a matsayin maciyiya amanar da take son mijin daya saki yar uwarta ba, cikin yan awanin da basu kai uku ba duk ta firgice ta rasa nutsuwar ta,
"Lafiya kike kuwa? Maiya sameki kike farke har yanzun? Wannan kai da kawowan kuma da kikeyi shima na menene?"
Umman su ta jero mata tambayoyin bayan ta maida kofar d'akin ta kulle,
Da hanzari Moon din ta k'araso inda take tana isowa bata jira komai ba ta rungume ta,
Kukan tashin hankalin da take ta dannewa tun d'azun ne ya kwace mata ta fara rairashi ba kakkautawa,
"Ke wai miye haka? Ya abunda na tambayeki daban baki bani amsa ba kinzo kin kankameni kina min kuka!
So kike nima nawa hankalin ya tashi kamar yanda kika tada naki? Kiyi shiru kimin bayanin abunda yake faruwa da yasa kika kai har yanzun bakiyi bacci ba"
"Umma ina cikin matsala ban san da wani idon zan kalli mutune ba idan abun nan ya tabbata,
Mutane zasu dunga kallo na a matsayin maciyiya amanar da taso mijin yar uwarta"
Kamata Umman nasu tayi suka k'arasa bakin gado suka zauna jin kalaman dake fita daga bakin Moon din wadanda ita bata gane musu ba sam,
Sai da ta zaunar da ita kafin tasa hannun ta ta sharema Moon din hawayen ta kafin tace,
"Kiyi shiru da kukan nan haka kimin bayanin abunda ke faruwa yanda zan gane"
Wayarta Moon din ta d'auko ta shiga cikin chat dinta da Sarki hirar da suka gudanar a d'azun din ta nuna ma Umman nasu tun daga farko har karshe,
"To menene abun damuwa ko tashin hankali anan Maimoon dan wani namiji ya nuna yana sonki?
Yaune aka fara cewa ana sonki da zaki damu kanki ki d'aga hankalin ki nima ki d'aga min nawa hankalin, waneni shi d'in? "
"Umma bazaki gane bane, domin ba kalmar son bane abin tashin hankali a wajena tunda ai ba akan shi na farajin kalmar ba, ah ah shida kalmar ta fito daga bakin shine tashin hankalin nawa a halin yanzun"
"Shi yasa nima ai na tambayeki wane ne shi din?"
Ummah ta k'ara tambaya a karo na biyu,
Sauke ajiyar zuciya mai nauyi Moon tayi kafin ta iya kallon fuskar Umman nasu ta bata amsa da cewa,
"Ya Sufyan Sarki Mijin da suka rabu da Meenal d'in Hajiya,
Shine wanda ya furta yana sona kuma wai aurena zaiyi gobe kuma yake son yazo yaga baba dan ya nemi izini a wajen shi ni ban san ya zanyi ba tun d'azun nike kiran wayan shi ya kashe wayar ban san ya zanyi ba"
Ta k'arasa fad'a da muryar koka kananan hawaye na Saukowa kan kumatun ta,
"Turk'ashi!
Shi mijin na Meenal ko ince tsohon mijin shine yace yana sonki?
To ma a ina kuka had'u ya akayi yasan ki ko dama kun saba dashi ne?
To shi bai san alak'ar dake tsakanin ki da ita Meenal din bane da zai wani zo yace son ki yakeyi ko koh dai salon ya b'ata zumuncin dake tsakanin ku, wannan ma ai ba maganar da ya kamata kunne ya saurara bane dan ana barin halas ko dan kunya inshi namiji ne bashi data ido aike mace ce duk da bawai hakan ya haramta bane amma kusancin yayi yawa, ke mema ya had'aki dashi?"
Kaf abunda ya faru tun daga ranar daya sha gaban ta da mota har zuwa yau Moon ta kwashe tass ta sheda ma Umman su,
"Maimoon kina