Showing 102001 words to 105000 words out of 190771 words
ce kana so a cikin sashen,"
"Hajiya ban gane ba wani irin magana kenan kikeyi? Kenan dan Meenal tana zama anan tare dake shi kenan ni kuma bazan dawo in zauna anan d'inba,
To miye laifin zaman nawa tunda dai ni ba dodo bane balle kice zanbi dare in cinye miki ita"
Ya fad'a rai bace tsohuwar nan fa ya lura da cewa magana kawai take nema dashi,
"Ah ah fa koma me zakace sai dai kace wallahi, amma ni bazaku mai dani sakarya ba bayan kasan yanda allah ya daura min saurin yin bacci,
So kake ni ina can saman gado ina baccin asara kai kuma kaida ita kuna zaune falo kuna hira, kai din nan dai mai ido a tsaitsaye Allah kadai yasan abunda zaka iya aikatawa a bayan idona,
Dan haka maganin kar ayi tofa kada a soma shi yafi"
"Kenan dai Hajiya kina nufin so kikeyi kice baki yarda dani ba wato ga d'an iska ya dawo sasanki koh?"
Saurin tarar numfashin shi tayi da cewa,
"Ah wallahi karkayi min k'age kasa min magana a baki kasani fad'in abinda ba shine a cikin zuciyata ba, nidai gaskiya nike fada maka dan kar kayi zaton wai ko rashin yarda ne yasa bazanyi shedar kaba,
Ah ah kulawa dai nike nunawa dan yanda naga kana nan nan da ita tofa ana iya samun matsala badai fata nikeyi ba Allah ma dai ya kiyaye dan ni ban haifi dan iska ko yar iskaba insha Allah kuma zuriata bazaku lalace ba,
Duk ma abar maganar badai kace zaman kwanaki kawai zakayi ka koma naka sashen ba, to ga sharud'a,
Na farko babu doguwar hirar da za'a raba dare ba'aje an kwanta ba, na biyu kuma baka ba haura sama ko magana kake so kayi dani sai dai ka jira idan na sauko ko kuma ka kirani a waya na uku kuma kowa ya zauna a inda yake atoh dan mu a zamanin mu ko hannun ki kika sake kikabar namiji ya rike sai dai ki wayi gari kiganki da ciki riki riki,"
Wai dan Allah jama'a mai Hajiya ta d'auki shi, bawan Allah dashi har shine za'a kafama wasu sharud'a dan kawai zaiyi zama na kwana biyu a sashen daba nashi ba,
To yasin Hajiya bata san shi bane yanzun ne zai gwada mata cewa da gaske fa auren yake so, ko dai ta tashi tsaye ta tura a nemo mishi auren jikarta ko kuma shi yayi gaban kanshi.
Hakan ne kuma yasa a wannan safen zaman da sukayi na karin ya tsiri nuna kulawar shi akan Meenal din da gangan a gaban Hajiyar,
Tea Meenal din ta had'a da niyyar karyawa dashi kamar koda yaushe domin so takeyi ta gama da wuri ta wuce unguwar malamai dan rashin Sultana a gidan yasa tanajin gidan ba dad'i dan in Sultana tana waje ta iya d'aukema wanda take dashi kewa saboda barkwancin ta,
Sai gashi ita data had'a tea ma kanta sunyi raba dai dai din shi da Ak domin idan ta d'aura ta kurb'a tana ajiyewa shima zai d'auki cup din ya daidaita dai dai bakin ta yasha, da suka shanye tea d'in kuma kunun gyad'ar da Hajiya ta zuba mishi shi ya koma yana bata a baki har ma in kunun da d'an dangwali gefen bakinta saboda tsabar iya hege yatsar shi yake kaiwa wajen ya goge kunun dashi sai ya lashe da hakorin shi,
Duk wannan iskancin da yakeyi Hajiya kin kulashi tayi dan tasan wani abun ma yanayi ne saboda d'azun tayi magana to bazata biye mishi ya nemi maida ita sakara'u ba,
shiko kunyar ta bayaji wai a gaban idon ta AK ya zauna yana cida Meenal abinci baki,
Ita dai ido da baki kawai ta sake tana binsu da kallon ikon Allah saboda yanda shi uban gayyar ya nuna kamar ya manta da zaman ta a wajen,
Abincin ya d'ibo a cikin spoon ya k'ara nufo bakin Meenal dashi,
"Haaa nace Allah kuwa ina fad'a miki idan baki tsaya kinci abincin nan ba babu inda zakije yau a gidan nan"
"To Yaya ai na fad'a maka na koshi, nifa tea kawai nike sha da safe amma Kali ka gani fa tun dazun kake duramin cous cous din nan bayan nasha tea nasha kunun gyad'a Allah idan ka matsamun amai zai sani"
Ta karasa fada a marairaice dan Wallahi shi dai ke aikatawa amma ita kunyar ke kamawa,
"Kalli ki ganifa saura kad'an ya rage daure kawai ki cinye sai kije ki kwanta abinki dan yau babu zuwa yawo ni dake a gidan nan zamu wuni muna d'ebema Hajiya kewa, Hajiya mai zaki dafa mana anjima "
Banza dashi Hajiya tayi kamar bataji mai yake cewa ba,
"Hajiya nidai dan allah kice mishi ya kyaleni haka wallahi na koshi"
"To dan ubanka tace ta koshi ai sai ka gyaleta haka ko ana dole ne? Gaba d'aya kabi ka matsama yarinyar mutane saboda tsabar rashin kunya ma a gabana ka ajiyeta kana bata abinci a baki, wai yaushe ka zama haka bani da labari Abdul?
Ke kuma dayar munafukan inace tun d'azun baki yake kina karb'a kamar bakisan da zamana a wajen ba sai yanzun ne zaki sakoni a shirmen ku, kai kuma Allah ina fada maka idan baka dena wannan b'are b'aren jikin ba tofa tattara ta zanyi ta koma gidan ubanta dan bazaku dunga abubuwan ku a gabana ba idan ku baku san kunya ba to ni ku barni da jin kunya"
Haka dai suka gama karin safen Hajiya nata faman mita,
A wannan ranar kasa wa AK yayi ya tsare ya hana Meenal zuwa ko ina kamar yanda yace, dan tunda ya tattaro ya tare a sashen Hajiyan idan kunga ya fita to masallaci zaije yana dawowa kuma zai koma dan harta baccin da yace Meenal tayi bai barta tayi ba dashi suka shiga kitchen da rana Larai nata mishi tsiyar cewa kar ya bada maza fa in dan in yace haka zaiyi to kafin aure zai zama mijin tace,
tun Meenal na nokewa dan dole ta gaji ta sake jiki saboda yanda yake nuna damuwa da kulawar shi mad'aukaki akanta, motsi kad'an zatayi ya fara tambayar ta miya faru?
Haka ya dunga riritata irin riritawar da bata tab'a tunanin samun kwatan kwacin shi a tareda shiba,
duk da hakan ya matuk'ar faranta ran Hajiya amma sai bata nuna ba sai ma kushe su data dungayi akan in basu kama kansu ba dukan su zata kora subar mata gidan da dare yayi shida kanshi ya fita bayan ya tambaye su abinda suke son ci yaje ya siyo ya dawo suka zauna su ukun suka ci karfen 10 na dare Hajiya ta raka Meenal har d'aki saida ta tabbatar da cewa Meenal din ta rufe k'ofar ta da key kafin itama ta shige nata d'akin.
washe gari ma bai fita ba yana manne da Meenal d'in har su Meelat Maryam Sultana da kuma Maimoon suka iso gidan domin koda Moon ta iso can gidan su Meelat ta sauka abunta acewar ta ko zata koma gidan Hajiya sai sun gama biki.
"Hajiya nayi ma su kabir magana gobe zasu gyara sashen saukar bak'in gidan nan dan anan gidan nike son mu sauke bak'in mu tunda muna da isasshen masauki basai mun kaisu Hotel ba dan haka ki shiga ki duba abubuwan da ake buk'ata wanda babu a sashen sai a siyo a saka,
Abincin da za'aci kuma har a gama taron bikin kowa ya watse munyi magana da Hajiya Yar ba'u itace zata dunga girkawa,"
"To kayi kyan kai kam dan dama nima naso inyi maka magana Allah yasa dai agama taron lafiya, kunyi magana da iyayen ka sun fada maka ranar da zasu iso kuwa?"
"Ba muyi magana dasu ba" ya bata amsa,
Tunda Meenal taji kukan motar ta tasan Sultana ce ta dawo gidan, dan ta fada musu cewa AK ya hanata fita ko ina gashi kuma gobe ne zasu gabatar da event din su wanda suka shirya gabatar dashi a makaranta dan haka tasan dole dama zasu biyo ta,
Sai dai ga mamakin ta koda suka shigo sai taga harda Moon a cikin tawagar nasu,
da gudu Sultana da Moon suka kwaso ita Sultanan Hajiya ta nufa tana fad'in tayi kewarta ita ko Moon wajen Meenal ta nufa Ak yana ganin hakan yayi saurin shiga tsakanin su ya maida Meenal din bayan shi yana d'aure fuska,
"Ke miye haka kukeyi daga shigowar ki zaki kwaso gudu kice wani zaki rungume ta? Bakiga kin fita girman jiki bane ko salon dukan ku ku fad'i kujama mutane aiki?"
Ak manya shifa ba komai yasa ya shiga tsakanin nasu ba sai kishi, tayama zai yarda yana zaune yana kallo ita moon din kawai ta wani kwaso gudu tace zata rungume mishi mata, ah ah fa sam ba wannan maganar kuma itama Meenal zaija mata layi ne da yanda yaga sunayi,
Karma Sultana taji labari dan ya lura da yarinyar nan shegen son jiki gareta ko zama zatayi saita jingina ko ta kwanta a jikin Meenal din duk ta sakar mata nauyin ta shifa bazai yarda da hakan ba, abu indai nashi ne yafi so yaci gaba da zama a matsayin nashin kawai.
"Kai Yaya dan Allah mun dade fa bamuga juna ba ai kaima kasan dole in so rungumar ta kodan inji dumin jikin bloody na a nawa jikin,"
"Aiko bazaki jishi ba, dallah can nemi wajen zama ki zauna ku kun girma amma har yanzun kun kasa dena behaving irin na yara,"
Tura baki tayi ta mik'a hannun ta ta kamo na Meenal wacce take mik'o mata,
"Ke yar nan ke kuma daga ina kika fad'o nike ganin ki daga sama babu labari?"
Hajiya ta tambaya tana bin Moon din da kallon mamaki,
"Daga Lagos mana zuwa Zaria, kuma dan zanzo ai bai zama dole sai na kira na fad'a miki ba, kuma ni biki nazo shi yasa ma ban sauka anan ba na sauka acan"
"Ikon allah ita uwar taki itace duk ta kitsa miki hakan kafin ki baro garin naku? Wato har ankai matakin da zaki shigo garin nan amma ki kasa sauka a gidan nan sai dai ki sauka acan wani gidan da baki had'a uwar komai dasu ba koh to ko kinki ko kinso nidai nice dolen ki dan ubanki, babu dangin iya balle na baba kinje gidan mutane kin tare to uwar me kikazo yimin anan d'in tunda nidai ai ban tura miki katin gayyata ba, yara iyayen ku sun barku a gaban su sunki su aurar daku nidai wallahi in ma bakin jini ke gareki ba a wajena kika d'auko ba sai dai can gefen uwar ki, kuma insha Allah su iyayen naki zasu iso su sameni basu barin garin nan sai sun tsaida zancen auren ki da koma waye inba haka ni dasu ne"
"To wai Hajiya ni ce miki nayi na shirya auren a yanzun ne?"
"Aikin banza dama waye zai tsaya biye miki? Wacece ke da kike zaton cewa dole sai abinda kike so za'a miki aure dai ko baki tashi ba ni na tashi aurar dake,
inba ma rashin zuciya da rashin sanin ciwon kaiba ku kenan kullum kuna siyan ankon biki kuna zuwa bikin kawaye amma ko kishin ace kuyi auren kuma bakwayi,
To gata nan dai ita naki yar uwar daga mutuwar auren ta harta samu wani mijin ke koh kina nan kullum sai k'ara girman jiki da yawan shekaru kikeyi amma shiru babu mashin shine kiji da kyau to bana na shirya tsaf babu yaro ko yarinyar da zan k'ara bari su shekara a gaban iyayen su indai sun isa aure kuma suna da halin yi sai sunyi, duk ku gama tsalle tsallen ku nice maganin ku.
*UMMIEE CE*โ๐ผ
[9/25, 11:03 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 34*
No editing ๐
*INA MAI BA MASU KARATU HAK'URI AKAN SHIRUN DA SUKAJI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON MATSALAR RASHIN WUTA DA MUKA SAMU,*
*~Ina kuke masoya kuma yan uwana makaranta?,~*
~shin kuna da labarin cewa gwanar ku kuma gwanata *JAMILA MUSA MARUBUCIYAR SHAHARAR REN LITTAFIN NAN MAI TAKEN KWARATA* tak'ara dawo muku da wani zazzafan labari mai cike da sark'ak'iyar hassada makirci munafunci bita da kulli kai harma da tsantsar SOYAYYAR da a dare d'aya ya juye ya koma wutar kiyayyar juna?~
*WUTAR K'IYAYYA* ~ce keci take kuma gudana a cikin rayuwar wani ahalin da suke jini d'aya ma'ana uwa d'aya uba d'aya?~
~idan baku manta ba a baya itace dai wacce ta rubuta muku littafan nan masu d'auke da tsantsar fadakantar wa gami da nishad'in da har yanzun da yawa daga cikin mu nasan bama gajiya da karanta shi,~
~ina magana ne akan littafan ta kad'an daga ciki irin su~ *KWARATA, BOYAYYAR SOYAYYA, ZAWARCI, SO MUGUN WASA Dama wasu wad'anda ban kira sunan suba*
~wadan nan littafan dana lissafo ko banyi k'ari bayani akan suba nasan kun san me suka k'unsa~
~To wannan karan ma dai so nike ku shirya tsaf ban kuma ce kuyi garaje gurin karatu ba, ah ah karatun littafin Hajiyata nutsuwa yake buk'ata, littafin~*WUTAR K'IYAYYA* ~zai zo muku a kyauta ne kedai qawata daure ki loda ma wayar ki data da kuma isashshen caji domin ki samu damar karantu a natse na tabbata zakiji dadin shi domin ko namu ba irin nasu bane~
*karku manta littafin WUTAR K'IYAYYA kyauta ne ga masu buk'ata daga farko suyi magana dani kai tsaye ta wannan number din* 08061358462 *ni kuma zan an taya su cikin group din zaku same shi daga farko kuma batareda kunsha wahalar nema a wani wajen ba*
************Kunga kutashi muje ciki dan Allah,"
Meenal ta fad'a tana tarar numfashin Hajiya saboda jin da tayi Hajiyar tana neman mai da chapter din ya juya kanta shiko dama AK tunda ta fara surutun ya mik'e yabar musu falon dan Wallahi ya sani tsaf Hajiya tana iya kwafsa mishi a gaban yaran nan bai kuma bar falon ba sai da yakai bakin shi dai dai kunnen Meenal ya shaida mata cewa bai fa yarda da wani rungume rungume ba sannan ya fice abinshi jin Hajiya naci gaba da surutun ta na fama,
inba haka ba dan Allah miye kuma nayi masu terere daga zuwan Moon din zata wani fara shelanta mata cewa ita Meenal ta samu miji?
Itafa Hajiya matsalarta kenan duk maganar da yazo bakinta fad'in shi kawai take bata wani lura dako su waye ke wajen salon duk tasa kananun yara su gama raina mutum,
Basar da kashe din da AK ya mata Meenal tayi dan tun bai bar falon ba ta fuske taje ta rungume Moon d'in irin rungumar da akema mutum na gefe tana mai cigaba da cewa,
"Kema dai kamar wata wacce baki san halin Hajiya ba da zaki wani biye mata kina son b'ata ranki daga shigowar ki ko hutawa bakiyi ba ku wuce muje ciki kafin ta huce dan Hajiya kwana nan bata dako wani magana sai na aurar da mutum"
"Eh lallai kam ai dama dole ki goyi bayan yar uwarki ni ki kwaye min nawa bayan!
Kwana nawa ne dududu ita Maimunan zatayi ta tafi tabar ni dake a gidan nan? Batun aure kuma dan uban mutum ko yak'i ko yaso dole yayi shi in mutum baiyi ta arziki ba aiba abun kunya bane in kunji shela a masallaci ana sanarwa dan mu bayau farau a kan muba yima mace auren bazata,
Oh wato ma ga azababbiyar tsohuwa koh shine har kike cewa ku wuce to karko ku sake kuce zaku hau min sama gara duk ku tattara kuzo ku fice min a sashe dan babu wacce na gayyato dama a cikin ku"
Tsam suka mik'e ganin abun na hajiya bamai k'arewa bane suka fice daga sashen zuwa side d'in Hajiya Jummai acan suka baje hajar su ta firar yaushe gamo tunda dai ba laifi an dad'e ba'a had'uba kullum sai dai chat da kuma kiran waya,
Suna cikin hirar nasu ne kuma Meelat ta kawo zancen zuwan da Bash yayi wajen ta da kuma labarin Meenal din daya tambayeta duk saida ta bata Meenal labari sannan kuma Meelat din ta tambayi Meenal ko bash din yazo wajen ta?dan allah ya sani ita dai bata so Bash din ya bayyana ba taso ace ko zai bayyana sai komai ya k'an kama tsakanin AK da Meenal din ba kuma wai dan bata son Bash d'in bane ah ah ita dai tafi son ace AK ne ya samu Meenal din akan duk sauran wadanda suka nuna ra'ayin su akan Meenal d'in.
Sosai jikin Meenal yayi sanyi ba tareda ta iya ba Meelat dasu Maryam din da suka zubo mata ido suna jiran amsa daga gareta ba,
Tayi matuk'ar mamaki dajin cewa har yanzun ashe Bash dinta Bash dai nata a shekarun baya d'an gidan master wai ashe har yanzun bai manta da ita ba tunda gashi har ya iya neman ta a ranar daya ganta,
Allah Sarki rayuwa kenan a baya bata tab'a zaton cewa zasuyi rabuwa ta bazata irin rabuwar da sukayi dashi wanda ko sallama basuyi a yayin rabuwar ba, bayan auren ta kuma tunda ta tabbatar da cewa shi kenan ta rasa shi sai ta rungumi kaddarar ta duk da cewa a lokacin tana da number din wayar shi akai amma bata tab'a gwada kiran shi ko sau d'aya ba saboda bata san me zata ce mishi idan ta kira shi d'in ba,
A wajen Aisha ta samu labarin halin daya samu kanshi a ciki yayin zuwan shi gidan Hajiya kuma bata tab'a tattauna maganar dasu Meelat ba suma kuma tun bayan auren ta babu wanda ya k'ara tada hirar wani daga cikin samarin ta a cikin su, sun tona k'asa sun burne komai saboda basa son hankalin ta ya tashi, daga bayane ma takejin cewa wai baya k'asar lokacin data samu labarin hakan ta bishi da fatan alkhairi saboda Bash mutum ne yana daga cikin mutanen da bazata iya mantawa dasu ba dan ya nuna