Showing 39001 words to 42000 words out of 190771 words
bata wani damu ba sukaci gaba da hirar su ita da yan uwanta, dan rabon da su had'u a waje d'aya irin hakan gaskiya an dad'e tunda ko biki sukeyi a gida duk wacce tazo d'akin uwarta take sauka sai dai a had'u a tsakar gida amma yau gasu kusan su duka dan ma wasu basu samu isowa ba sai gobe wad'anda suke kusan ne dai yau suka samu isowa,
Ita ko Hajiya a gefen ta tun bayan data idar da Sallah ta fito daga d'akin suka k'ara sabon gaisuwa da mutanen dake sashen har zuwa sanda Mommy Hauwa da Innar yara suka mata jagora suka shiga sashen sauran matan gidan suma suka musu gaisuwa bayan sun dawo kuma cikin d'akin da aka sauke tan ta koma aka gabatar mata da abinci taci,
Duk abunda akeyi tana ta lura dan ta kirga d'akunan dake cikin sashen d'akuna ukune a kalla kuma mutanen dake cikin sashen mata wad'anda tasan kwana zasuyi kun kusa ashirin ko fin hakan ma banda yaran su, to idan dare yayi wani irin kwanciya za'ayi har aji dad'in bacci shi take ta lissafi,
Sai dai bazatayi saurin bada kaiba tunda ita ba yarinya bace ta gane cewa shima daya gayyace sun zuwa gidan shi yana da nashi dalilin dan haka shiru zatayi tukun, duk zaman da takeyi lokaci lokaci take kallon agogo taga ko zai kirata, kuma itama koda ya biyo ayari suka shigo falon tsaf taji shigowar nashi kuma bayan Jidda ta shiga wajen tama ta k'ara jaddada mata cewa AK ya shigo ya musu gaisuwa dan ita Jiddan ma bata san cewa shine ya kawo suba tayi zaton ko da motar Meenal sukazo har sai da Hajiyar ta sheda mata cewa ai shine ya kawo su tukun,
Ganin cewa Meenal bata neme ta shi yasa ta share batun duk da dai ta yanke cewa idan 11 tayi taga bai kiraba kuma Meenal bata tada maganar ba ita zata kira shi dan gaskiya tasan in tace ta kwana a gidan bazata sake ba, in yaso ita sai ta bishi Meenal din ta zauna tunda ita zata sake a cikin yan uwan ta,
Sai gashi tun sha d'ayan bata buga ba da yaji shiru shi ya kirata, kuma duk kiran da yake mata tana kallo tsaf sai dai kuma itama sai ta wana shi kafin,
Haka yaci gaba da zama a cikin motar yana duba lokaci daga kan minti d'aya sai gashi anci kusan mintuna 15 ba Hajiya ba Meenal,
kamar ya tada motar yayi tafiyar shi dan yasan da gangan yarinyar nan ta shanya shi sai kuma dai ya daure ya k'ara ba zuciyar shi hak'uri ya danna ma number din nata kira a karo na biyu,
Wayar bata dad'e tana k'ara ba ta d'auka,
"Bakiga Hajiyan bane wai ko ya akayi ne kun shanyani a waje sai jira nikeyi duk mutane sun gama watsewa ko baku san dare yayi bane?"
"Umm nifa bazan bika ba anan zan kwana sai dai ko ita Hajiyar ne zata bika,"
"Oh kenan ma d'an iska kika maida ni tun dazun dana kiraki ma baki fad'ama Hajiyan sakon ba,"
Mtwss yaja tsaki mai tsayi bayan ya yanke wayar dan ranshi fa ya fara baci yanzun kam,
A bayyana ya furta,
"Kunga abinda nike ta gudu tun tuni kenan koh, Soyayya da kana nan yara, to ita wannan ma tun ban furta mata cewa ina son ta d'in ba tasan ta shanya ni a waje kamar wani dan iska anya yarinyar nan duk ranar data gane ina sonta ba sai ta mai dani sakarai ba kuwa?, ina ma amfanin haka gaskiya soyayya bata min adalci ba miye haka mutum duk yabi ya susuce,"
Hannu shi ya d'aura a saman kai ya yamutsa gashin kan nashi yana fesar da huci mai zafi,
"Wai yarinyar nan nufin ta duk zaman da nayi a wajen nan zai tashi a banza ne? Lallai ma naki wasa ne Wallahi baki isa ba, Allah yasa nima ina da gata a cikin gidan bari ma ki gani"
Ya fad'a yana d'aukar wayar shi ya lalubo number din Mommy Hauwa,
Babu b'ata lokaci ko ta dauki wayar da sallama,
"Aunty nace dan Allah kiyi ma su Hajiya magana su fito haka nan mu wuce dare yayi, na kira number din Hajiyar bata d'auka ba ban sani ba ko tabar wayar nata a cikin jaka ne kin san halinta kilama ta manta dani ne"
Ya d'aura da cewa bayan ya amsa Sallamar na Mommy Hauwa,
"Ayya kayi hakuri bayi in mata magana zasu fito yanzun babu mamaki kam in akace maka Hajiya manta tayi"
Ta fad'i hakan tana kallon Hajiyar,
Shi kuma daga can gefen yanke wayar shi yayi hankali kwance dan yana da tabbacin cewa wannan aikin kuma ya kammala ba Hajiya ba har ita d'ayar mara kunyar saita fito, dan haka sai yama kawai ya tada kujerun motar daya kwantar ya gyara parking din motar zuwa dai dai bakin gate din gidan ta yanda suna fitowa shiga kawai zasuyi,
Maida kallon ta wajen Hajiya Mommy Hauwa tayi bayan ta gama magana dashi,
"Hajiya ina kika ajiye wayar ki hala?"
"Me ya faru kike tambayar wayata?"
Hajiya ma ta tambaya kamar bata san akan me zatayi magana ba bayan taji komai na kiran da AK din yama Jiddan,
"Mai Jama'a ne ya kirani yanzun ashe tun tuni yana kofar gida yana jiran fitowar ku, ai dai ya kyauta wallahi da bai wuce ba, dan dama ina ta tunanin yanda za'ayi bacci a sashen nan yau, gashi har daren ma yayi, yace ya kiraki ba'a d'auka ba shine ya kirani ai gara kuje can d'in zakifi sakewa ma, ai dama kayan ku yana cikin motar koh naga baku shigo nan dashi ba?"
"Ke barshi kawai ai dare kuma ya riga yayi kirashi kice nace yaje kawai saida safe zamuyi kwanan mu anan, ai dama ba munzo jin dadi bane"
"Ah ah Hajiya dan Allah kuje kawai tunda har Allah yasa bai tafi ba koni ai dan dai kar aga mun kwasa duka mun tafine da nima binku zanyi can din, bari in kira Meenal itama tunda ta iso suna can sun kule d'aki sai hira suke kamar ba'a gidan mutuwa suke ba, "
Jidda bata fito a d'akin ba sai da ta taso Hajiya a gaba suka fito a d'akin a falon suka had'u da Meenal wacce sai yanzun ne ta fito da niyyar zuwa ta isarma Hajiya sakon AK din,
"Yauwa gara da kika fitoma muje Kunbar min d'a acan waje yana jiran ku ga dare yayi"
Cewar Mommy Hauwa,
"Mommy nifa anan zan kwana ai na fad'a mishi sai dai Hajiya ta bishi"
"Ke dallah can ban son maganar banza, ita Hajiyar ce zata tafi can din ita d'aya ina ce tare kukazo dukan ku, wuce ki d'auko Jakar ki ki fito ku wuce dare na k'arayi"
Badan Meenal taso ba haka ta koma d'akin ta d'auko jakarta ranta a b'ace, lek'awa d'akin itama Hajiya tayi dan yin Sallama da mutanen cikin,
Sai da suka rakasu Hajiyar har bakin motar AK din dake kofar gidan, gidan baya Hajiya ta zauna kamar lokacin da sukazo, Meenal ma gidan bayan ta bud'e zata shiga Mommy Hauwa ce ta hanata da cewa,
"Shi din driver din gidan ku ne da kema zaki koma baya ki kame ku barshi da tuk'aku? Dallah koma baya keda baki san abun arziki ba"
Simi simi ta wuce ta bud'e gaban motan ta shiga ran nan nata a bace, sallama suka musu suka juya cikin gidan shi kuma yaja motar suka bar kofar gidan ranshi fess duk da yana ganin yanda Meenal d'in ke ta faman b'ata rai baibi ta kanta ba tuk'i kawai yaci gaba d'ayi,
Kamar yanda yayi alqawari sai da ya koma ta chawai ya siya musu chips din da Meenal tace tana so da kazar sannan sukaci gaba da tafiya, shida zai d'auke hanya zuwa malali kawai sai ya mik'e zuwa unguwan Sarki koda ya isa inda suke siyar da ice cream din bai tayama Meenal shiga wajen ba fakawa yayi yaje ya siyo musu ya dawo motar ya k'ara bata wuta suka koma daga baya zuwa Malalin,
Sai da yayi ta yawo dasu akan tituna kafin ya d'auke hanyar gidan shi, daga Hajiya har Meenal dai babu wacce ta tanka mishi a cikin su dan ita Hajiya dama tunda ta shigo wayar take amsa wayar Baba Usman dan haka bata damu da sanin ina yake kaisu ba sai dai in taga ya tsaya ta d'ago taga inda suke taci gaba da wayarta,
Ita ko Meenal duk da cewa a cikin zuciyar ta taji dadin yanda ya cika mata alkawarin daya dauka taji dadi amma sai ta fuske abunta taci gaba da hura hanci duk da dai daurewa kawai take amma wallahi ta matsu su isa gidan nashi kafin ta bada kanta sakamakon kanshin chips dana kazar da suka mamaye cikin motar basar wa kawai takeyi amma da lafiya lau ne tabbas da tun a cikin motar zata fara aikasu zuwa masaukin su,
"Bieeee" din daya danna ne ya dawo da hankalin ta kan kofar gidan da yake tsaye saboda tunda suka shigo cikin layin take faman bin gidajen layin da suka shigo din da kallo, gidaje a tsare lafiyayyu wanda kai bawa ko baka tambaya idanuwan ka ne zasu shaida maka cewa unguwan bana yaku bayi bane, dan gidajen sun jeru ne wannan yana wane wannan dan kyau,
Waigawa tayi dan ganin ko Hajiya ta lura da abunda ita take kallo sai taga Hajiya ko a jikin ta hirar ta kawai takeyi,
Sulalawa da motar yayi zuwa cikin gidan bayan an bud'e mishi gate d'in,
Tun kafin ya faka take faman k'arewa gidan kallo,
Hajiya dake bayan motar ita ta fara fita ba tareda ta jira ya bud'e mata kofa ba wannan karan,
Mutuniyar ko sai da ta kwamuso ledar kaji dana chips din ta kafin ta fito daga cikin motar.
[8/30, 3:18 PM] zainabusmanummiee584: ๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆโ๏ธ๐ฑ
*BOOK 2*
*PAGE 16.*
Shiko AK bayan ya faka motar baya ya koma zuwa wajen mai gadin dake bakin gate ya na ta kokarin kullewa,
"Assalamu Alaikum Malam Mansoor barkan mu dare fa ya gida?"
Ya fad'a yana mai dafo kafad'ar Mansoor d'in bayan ya bashi hannu sunyi musabaha irinta maza,
"Alhamdulillah Ranka ya dad'e barka da dawowa, ai ina ta zuba ido tun bayan da muka gama waya da kai sai kuma naji shiru, wallahi kaga yanzun hakan ina batun in kiraka a wayane inji ko dai ka fasa dawowa yau d'in ne sai kuma gaku, to barkan ku da isowa fa dafatan an baro mutanen gidan lafiya ya hanya kuma? "
"Alhamdulillah ai mun ma shigo garin tun d'azun wallahi dan a cikin Unguwan Dosa ma muka gabatar da sallan Magriba da yike rasuwa akayi mana a can d'in, mu k'arasa ku gaisa da Hajiya tare muke dasu anan zasu dunga kwana kafin su tafi"
Ba tareda ya saki hannun Mansoor din ba sukaci gaba da tafiya har suka isa bakin kofar dasu Hajiya ke tsaye suna jiran ya k'arasa ya bud'e musu kofar,ita dai Meenal tunda ta fito daga cikin motar take ci gaba da bin gidan da kallo, ba wani wargajeje bane wajen girma sai dai kuma gaskiya ya tsaru dan sosai ya d'auki hankalin ta sai faman kalle kalle take duk kuwa da cewa dare ne amma kana iya ganin komai da aka kawata gidan dashi a zahiri sakamakon kwayayen wutar lantarkin da suka haska gidan,
Har k'asa Mansoor din ya duk'a ya gaishe da Hajiya ta kuwa amsa mishi cike da kulawa, Meenal dai bata jira ya gaisheta ba ita ta fara gaidashi dan ko babu komai ya girme mata nesa ba kusa ba,
AK ne ya bud'e kofar suka shige ciki shi kuma mai gadin ya musu sai da safe ya koma,
A falon gidan dukan su suka zauna,
"Wash Allah na gaji wallahi" cewar Meenal a yayinda takai kwance,
"Ai zaki gaji kam daga dawowa makaranta baki ko huta ba mun kamo hanya sannu ki samu kiyi wanka da ruwa masu dumi kafin kiyi bacci sai kiga kin warware koda gari zai waye bazakiji gajiyar a tare dake ba"
Cewar Hajiya,
"Hajiya d'an wannan tafiyar ne har kike cewa sai tayi wani wanka da ruwan zafi?
Nida na d'auko hanya mai nisa na taho abinci ma a daddafe aka bani shi naci ga kuma shanyani da kukayi a kofar gidan mutane bayan na tuk'o ku daga Zaria zuwa Kaduna ko sannu baki min ba, ai dama na lura wallahi tunda yarinyar nan ta koma wajen ki kika dena tunawa ma kina dani, ni kuma na kasa zuciya in gyale ku keda itan nima in koma inda za'aji dani! "
Ya k'arasa fad'a rannan a had'e shi a dole an mishi ba dai dai ba,
Dariya Meenal ta fashe mishi dashi harda kyakyatawa tana nuna shi da yatsa,
"Kai amma wallahi Allah taubashi kana da abun ban dariya, to wai dama kishi kakeyi dani ashe ban sani ba"
Juyawa gefen da Hajiya take tayi tana ci gaba da dariyar nata take cewa,
"Hajiya to ga autan kinan fa yana kishi dani dan Allah shima kice mishi inyaje bacci yayi wanka da ruwan zafi saboda kar gobe ya kasa zuwa masallaci sallan asuba saboda tsabar gajiya, kujimin fa Babban shi dashi wai yana kishi dani, to ma ce maka akayi dama kai kad'ai Hajiyar tafi sone?"
Murmushi kawai Hajiya keyi tana binsu da kallo,
Shiko cewa yayi,
"Hajiya kina kallon ta koh a gaban ki fa take min rashin kunya amma bakice komai ba yanzun kuma idan nace zan tattaka ta kice na fiye cin zalin, to ai shi kenan Hajiya muje ki kwanta"
Ya fad'a yana mikewa,
"Toni me kuke so ince bayan d'azun ina kallon ku kuke ta hirar ku kun ma manta dani a cikin motar gaba d'aya sai yanzun ne zaku zo kuna wani yimin kurari, to wallahi ku kiyaye ni"
Tsaye yayi cak shida Meenal suna kallon kallo,
"Hajiya waye yace miki mancewa mukayi dake a cikin motar?"
Meenal ta tambaya,
"Ke dallah rabu dani nikam in dai kuna abunku ku dena sakoni cikin sirmen ku na fad'a muku,
Shiko ledojin ya kwasa,
"Hajiya muje kici abunci kinji kiyi wanka sai ki kwanta dare yayi fa kuma nasan gobe cewa zakiyi zaku wuce gidan gaisuwar da wuri"
"Kai ni kyaleni da wani ciye ciye yanzun da daren nan ita dai data sakayin siyayyar sai tayi ta fama ni na riga naci tuwon dare na koshi kuci naku ku ajiyemin nawa in Allah yasa muna da rayuwa zan karya dashi da safe, ka koma ka ciro min kayana a bayan motar ka in canza wadannan na jikin nawa"
"To muje in raka ki d'akin"
Ya fad'a bayan ya ajiye ledojin,
Gaba Hajiya tayi shi kuma yana take mata baya Meenal kuma na gefen shi suna jerawa sai wani uban d'age takeyi a dole wai so take ta jera tsayin ta da nashi, girgiza kawai yakeyi idan ya kalketa batareda yace da ita komai ba har ya isa d'akin dake gefen nashi ya bud'e musu kofar suka shiga, d'akine madaidaici wanda yake d'auke da set din gado 6 by 6, dukan su suka shiga cikin d'akin wanda ke gyare tsaf an lailaye gadon da zani mai kyau d'akin sai tashin kamshi yakeyi, gefen gadon Meenal ta zauna ita kuma Hajiya cikin makewayi ta shige kai tsaye,
Juyawa yayi yabar d'akin bayan hajiya ta shige, ita kuma Meenal din sai ta biyo bayan shi tana cewa,
"Matar gidan bata nan ne Autan Hajiya?"
Kuji wani tambayan neman magana fa wajen yar gidan Malam fisabilillahi,
Shiko ba tareda ya tsaya daga tafiyar da yake yiba ya ansa mata da cewa,
"Dama akwai wata matar gidan ne bayan wacce tazo yanzun?" Shima ya tambaya,
"Wacece tazo yanzun kuma? Oh Hajiya wai kake magana? "
"Wacce take magana mana dai"
"Tab badai niba kam"
Kara sauri tayi ta cimmashi sukaci gaba da jerawa,
Kafin tace "Allah taubashi gidan ka ya min kyau masha Allah, komai Cass wallahi Allah yasa a mora,"
"Duk kyan shi ai bai kai naki gidan da kika baro kyau ba koh?"
"Aini wancan gidan ba nawa bane na maishi ne baga shi na baro can d'inba kuma wata ce zata maye gurbina, nifa kasan idan abu yamin kyau bana ma mutum hassada sai na fad'a wallahi shi yasama ban tab'a maka hassadar kyan da Allah ya maka ba sai dai ina danjin haushi kadan fa wani lokaci"
Tsayawa yayi cak ya juyo yana kallon ta,
Giraren ta duka biyun ta d'age mishi tana wani fari da idon ta, "ya akayi ne?" Ta tambaya tana ci gaba da kallon shi,
"Yarinyar nan zata k'arar min da ruwan kai" ya fada kasa sosai ta yanda bazataji me yace ba, dan Wallahi yanda take dage gira da fari da idon nan ji yakeyi kamar ya wafto ta ya cusata a cikin jikin shi ko zai samu nutsuwa,
"Muje mana ka tsaya kuma" ta furta ganin yayi tsaye sai faman binta da kallo yake shi baiyi gaba ba kuma baiyi baya ba,
Maganar da tayi shi ya dawo dashi cikin hayyacin shi,
Taku d'aya biyu yayi ya matso dab da ita kamar zai had'e jikin su waje guda sai kuma ya dakata ya d'an koma baya kadan duba da irin kallon da take mishi,
"To me yasa kike jin haushi na dan ina da kyau? Bayan nima kyan tashi nayi na ganni dashi bani ne na zab'arma kaina kasancewa cikin maza masu kyauba?"
Shiru tayi tana kifi kifi da ido dan yanda ya matse mata waje sai takejin faduwar gaba yana kamata,
'Uhummn fad'amin dalilin ki najin haushi na"
"Aiko ban fadaba kaima ka sani, ai dan saboda kana da kyau din ne yasa yan mata ke binka, kuma ai nasha ganin ka in kana cikin majalisar ka sai kayi ta dariya da murmushi bayan akwai mata a wajen amma mu idan