Showing 111001 words to 114000 words out of 190771 words
tasan da rana AK bai cika zama gida ba,
"Shi kuma Aliyu fa?" Ya k'ara tambaya, "to ai shi cewa kawai yayi insa rana zaizo mu gaisa,"ta fad'a tana tura baki,
"OK tunda abin ya zama haka shima ki tura mishi sak'on yazo gidan gobe ya sameki"
"To kai Ya'ya idan dukan su sukazo a lokaci d'aya kuma fa?"
"Uhumm Meenal kenan to ke zaki bari suzo duka a lokaci d'ayan ne? Ai kowa lokaci zaki bashi, na tabbatar da cewa dukan su zasu kiraki a goben dan ki basu lokacin da zasu zo su sameki ke kuma saiki basu lokacin daya dace"
Suko Ya Sheikh da Ya Naseer suna hira ne akan walimar da aka gabatar a gidan Sarki domin shi Ya Sheikh shi Malam ya wakilta zuwa walimar a maimakon shi sabida daga Sarki har Ya Sheikh din basu wani san juna sosaiba, yanda Sarki ya nunajin dad'in shi da zuwan su gidan nashi da kuma yanda ya dunga nan nan dasu shine abinda ya burge Sheikh d'in har hakan yasa yanzun ya d'auko hirar suke tattaunawa,
Koda Sultana ta shiga falon bayan gaisuwa gefen da Meenal take itama ta rab'a ta zauna, a kunne ta rad'ama Meenal cewa "ko dai shima Yayan mu ya shiga sahun zawarawane"tana nufin ya Sa'eed ko shima son Meenal din yake,
"Dallah can matsa OK kibani waje yar rainin wayau kawai kuma sai Allah ya saka min"
"Allah ya baki hak'uri"cewar sultana tana gyara rik'on wayar dake hannun ta,
Sun dade a falon suna hira har zuwa sanda Malam ya shigo kafin sultana ta janye Meenal din daga falon suka koma wajen Moon wacce ke falon Mommy Hauwa rik'e da waya tana dakon jiran kira daga Sarki,
Wallahi Sarki yayi mugun bata mamaki wai ita maimoon itace Sarki ya banzatar tun rabuwar su a airport daya tura mata massage lokacin suna hanya har yanzun bai Kara bi takanta ba domin ko message d'in daya saba tura mata unin yau gaba ko sau d'aya bai tura mata message ba kuma bai kirata ba,
Tayi tayi ta danne ta nuna irin bata damuba d'in nan amma wallahi maganar gaskiya ta kasa danne hakan, idan ita kuma ta d'auki waya da niyyar ta kirashi sai taji kai inah, ai in ta kirashi to ta fad'i ba nauyi wallahi, dan shirun da yayi ita ta d'auke shi ne a matsayin cewa wato tunda ya koma sabon gida ya tare cikin iyalinshi shi yasa ya manta da ita to ai ba komai domin a sanda zaiyi lokacin ta itama kuma zata rama ne.
Washe gari Meenal ta koma gida a daren jiya kuma sam koda wayar ta tayi caji bata damu da cewa bari ta kira AK ba tak'i kiran shine saboda tasan yana iya cewa ta koma gida a wannan daren,
Koda ta isa ta tarar da motar shi a cikin gidan ta kuma ji dad'in hakan dan ko babu komai itama tayi kewa, gaza shigewa sashen Hajiya tayi har saida ta juya akalar tafiyar ta zuwa side d'in shi, hannu takai ta bud'e k'ofar amma sai tajita a kulle ta nocking ta farayi wai ko Allah zai sa ya jiyota daga ciki yazo ya bud'e mata, sai dai kuma har ta gaji da dukan k'ofar baizo ya bud'e mata ba, jikinta yayi sanyi sosai harta fara tunanin to kodai yayi fushine tunda tun jiya data fita babu kiran waya ba sak'o, to amma ai koma menene bai kamata yace zaiyi fushi da ita har haka ba koba komai ai yasan dole zatayi busy a jiyan ba gashi yanzun yau ta dawo ba, shine dan wulakanci har ita zata zo tana buga mishi k'ofa amma yak'i zuwa ya bud'e mata dan kawai ya samu tazo ganin shi, aiko yayi da y'a wallahi, juyawa tayi jiki a sanyaye ta wuce sashen Hajiya,
Shiko AK dama sunyi da Sultana cewa idan Meenal ta baro unguwar malamai ta kirashi, dan haka tana wucewa Sultanar ta kira shi ta shaida mishi cewa Dr fa tana hanyar komowa zuwa gida, sai da ya duba agogo ya auna dai dai lokacin isowar ta kafin ya taso daga cikin bedroom din shi ya fito falon ya murzama k'ofar falon key, sannan ya koma ya nemi waje ya zauna wayar shi a gefen shi yana jiran isowar ta.
Kamar yanda ya kiyasta bata wuce adadin lokacin daya d'iba mata ba ta iso gidan yana kuma jin shigowar motar ta ya mik'e zumbur zuwa bakin window ya yaye labulen wajen yaci gaba da tsayuwa yana kallon ta harta fito daga cikin motar, yalwataccen murmushi ne ya kawata fuskar shi a yayinda yaga ta nufo sashen nashi dan haka sai kawai ya saki labulen ya koma kan kujera ya d'aura kafa d'aya kan d'aya kuma duk bugun da takema k'ofar yanajin ta dan daga karshema tasowa yayi ya lab'e a wajen window yana lekota har zuwa sanda ta gaji da dukan k'ofar ta juya, yayi mamaki da yaga ta k'ara dawowa bakin k'ofar kuma yayi zaton ko zataci gaba da nocking ne sai kuma yaga ta fara danne danne a wayarta babu b'ata lokaci kiran ya shiga, tabbas da ace bai sanya wayar shi a silent ba da asirin shi ya tonu a lokacin dan yasan tabbas zata iyajin k'arar wayar nashi, kira uku tayi bai d'auka ba dan haka dole tabar wajen a fusace.
Kamar yanda ya sa'eed yayi hasashe hakan ne ya faru domin da Aliyu da Hashim dukan su sun kirata da safen dan suji lokacin da zasu zo gidan su sameta,
Ta shaida ma Ya Hashim cewa zuwa 12 shi kuma Aliyu zuwa k'arfe 2,
Dan haka 12 dai dai kamar mai auna lokaci domin ko 12 nayi Isah ya sallama falon na Hajiya cewa Meenal d'in tayi bak'o, bata wani damu ba tunda ai ta riga tasan da zuwan shi dan haka sai kawai tacema Isah ya shigo dashi ita kuma ta haura sama wajen Hajiya dake d'aki ta shaida mata cewa ga ya Hashim yazo gidan zasu gaisa,
Hajiya bata wani nuna damuwa ba sai ma cewa da tayi tana mishi barka da zuwa taci gaba da abinda takeyi,
Fitowa Meenal din tayi ta sauko k'asa shiko Hashim tun daga kan benen yake binta da kallo dan shifa dama Allah ya sani batun yauba ya dad'e yana kwad'ayin yarinyar nan abinda ya hana shi motsin k'arfi a shekarun baya yasan ko ya nema Malam bazai bashi ita ba,
Amma yanzun da take matsayin bazawara yasan bazai sha wahala wajen shawo kan dangiba wajen ganin sun goya mishi baya,
Da fara'a ta sauko,
"Barka da zuwa ya Hashim ya aiyuka, kayi hak'uri na barka kana jira koh?"
"Ah haba dai babu damuwa ai dafatan kina lafiya ya likita ya gidan ya karatu kuma?" Alhamdulillah wallahi ba kasha ruwa ba" ta fad'a tana nuna center table d'in gaban shi wanda aka jera kayan motsa baki,
Ruwa kad'ai yakai hannu ya d'auka ya bud'e murfin ya tsiyaya ma daidaici a cikin kofi kafin yakai kofin bakin shi yasha ruwan,
"Alhamdulillah" ya fad'a bayan ya gama shan ruwan sai ya maida kofin ya ajiye,
"Ina fatan dai zuwan nan nawa bazai zama takurawa a gareki ba"ya furta hakan yana mai kureta da idanu,
"Ah haba dai ko d'aya ai saboda nasan bazan takura ba shi yasa nace kazo yau dan yau ne nike da damar zama a gida cikin satin nan ina da bikin Aminiyata"
Gyara zaman Babbar rigar dake jikinshi yayi yana k'ara gyara zama da kyau ya fuskance ta,
"Wato ainihin abinda yasa kikaji na nemi son ganin ki domin mu dai daita Meenal ba komai bane sai dan in shaida miki sirrin dake cikin zuciyata"
Da kallo ta cigaba da binshi tana jin abun wani iri, abun ya mata bambara kwai dan Wallahi shifa Hashim din ba yaro bane amma jibi yanda yazo yasata a gaba ko kunya wai shi a dole yaxo fad'a mata cewa yana sonta,
"Kina jina koh Meenal? Kinga dai ni ba bak'on ki bane kin san ni kin san waye ni kin san iyayena, gidana, matana, yara na dama komai nawa duk kina da masaniya akan su, to abinda nike so in shaida miki shine nidai na ganki kuma kinyi min dan haka ina son ki da aure, kar kiyi zaton ko yanzun ne na fara sonki ah ah tun kafin Malam ya badaki ga wancan wanda ya kasa rik'ekin nike son ki ina tabbatar miki da cewa da ace nasan cewa rik'on sakainar kashi zai miki da tun lokacin na fito mun kara mai rabo ya d'auka a tsakanin mu, amma da yike Allah yace ked'in rabona ce shi yasa ya sako min ke salin alin, dan haka nidai yanzun kin san cewa niba yaro bane dan haka bazan juri zuwa hira ba na dai fara sanar miki ne kafin inkai maganar gaban Baba Malam dan bana son abin ya d'auki lokaci"
Ku nemo ruwa ku an taya ma yar gidan malam dan zantukan bak'onta dai sun sumar da itaπ€£.
*Ummiee ce*
[9/28, 10:54 PM] Ummiee Zaria: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 36*
No editing π.
Lallai ma mutumin nan,
Dan Allah kuga yanda yake magana wani isaΒ² kamar ba wanda yazo neman yardarta ba, ah ah magana kawai yakeyi kanshi tsaye abinshi kamar mai bata umarni wai yazo ya fad'a mata ne kafin yakai maganar gaban Baba Malam, to me yake nufi? Kenan so yake yace shi bai damu dajin ko tana son shi ko akasin hakan ba kawai shi gaban kanshi yake son yi, aiko bai isa ba gara ta taka mushi burki tun yanzun wallahi,
Dan haka sai kawai itama ta gyara zaman ta tad'an yo gaba kad'an akan kujerar da take kai a zaune,
"Ya Hashim ban fahimci zancen kaba, ko kuma dai ince ban gane inda ka dosa ba, naji kana maganar kai zance gaban Baba Malam?" Ta k'arasa kai zancen nata da alamun tambaya itama tana kallon shi,
"Eh hakan nike so Meenal tunda har nazo na gabatar da kaina kuma to me za'a jira ai sai akai maganar gaban manya kawai su shiga ciki a tsaida ranar d'aurin aure kinga a kallah ko sati biyu ko uku aka sanya aiba laifi tunda dai ba auren budurwa bace balle ace za'ayi wani dogon shirye shiryen biki"ya k'arasa fad'a yana wani washe baki uwa kwarton daya hango wawan zama,
Kai innalillahi wa innah ilaihir raju'un wallahi yau dai da badin tun a gida ba'ayi musu tarbiyar zagin na gaba dasu ba da sai ta duba kafin ta zak'ulo gingimemen k'aton zagin da zata sauke ma bawan Allahn nan, tsabar takaici da bakin ciki ne suka rufe mata ido har bata san lokacin data d'ago kanta tana kallon shi ido cikin ido ta furta mishi cewa,
"Nagode kwarai Ya Hashim da yanda ka nuna kana sona tunda gashi har ka iya biyoni inda nike ka shaida min hakan baka b'ata lokaci ba, sai dai ka sani nima bazan b'ata maka naka lokacin kafin in baka amsar kaba, dafari dai kayi hakuri kace ka soni tun kafin aurena da tsohon mijina sai dai kafin kayi wani yunk'uri na subuce maka, a lokacin allah yayi kai ba mijina bane shi yasa ka rasani,
To a yanzun ma ina mai bakin cikin sanar dakai cewa hak'urin da kayi a karon farko shi zaka k'arayi a karo na biyu domin tuni wanin ka ya riga ya gabatar da kanshi kuma harma na amsa mishi dan haka kayi hakuri domin dai yanzun d'in ma ka rasani a karo na biyu, dan haka basai kayi wahalar kai maganar gaban iyayen muba na riga na baka amsar da kake buk'ata" tana kaiwa dai dai wajen tayi shiru tana shaqar turaren AK wanda ta tabbatar da cewa duk yanda akayi yana kusa dasu tunda har kamshin turaren shi ya iso hancin ta,
Sam bataji dad'in dawowar nashi gidan a dai dai wannan lokacin ba dan ko kusa bata so yazo ya sameta da bak'o a dai dai wannan lokacin ba dan haka duk da yanda idanuwan ta ke kwad'ayin son kallon shi zuciyar ta kuma ke bata umarnin ta d'aga kai ta kalle shi d'in k'iyawa tayi,
Yayinda shi kuma Hashim da jikin shi yayi sanyi kalau sakamakon jin kalaman ta ya bud'e nashi bakin ya fara mata magiya da cewa,
"Meenal karkice zakiyi saurin yanke hukunci domin kuwa ita mace allura ce a cikin ruwa mai rabo ka d'auka, wata kila shi wanda kike so d'in kila ba alkhairi bane a gareki kuma koma yayane duk yanda wani bare zai soki ba zai soki kamar mu yan uwan kiba, nidai ina sonki shi yasa harna taso na fad'a miki duk da sanin da nayi cewa acan gida kafin Namiji ya tunkari mace dole saiya gabatar da kanshi a gaban iyaye sun amince mishi, koda kikaga nazo nazone saboda in baki naki hakkin a matsayin ki na bazawara wacce ta tab'a aure"
A fusace ta yanke shi da cewa,
"Eh naji, naji ni bazawara ce basai kayi ta mai maita min ba Ya Hashim amma ka sani kai kaine kake min kallon bazawara su sauran masu nuna son aurena basu tab'a kallona a matsayin zawara ba, soyayyar ka kuma nace bana buk'atar ta domin dai na riga na tsayar da zuciyata waje d'aya ni mace ce ba namiji ba balle ace ina da damar zama da miji sama da d'aya, ina kuma tabbatar maka da cewa koda ace Allah da kanshi ya halatta wa mata auren miji sama da d'aya su zauna dasu a lokaci d'aya to kai dai baka cikin jerin mazajen da zanyi ma kaina fatan yin tarayya dasu,
Kai d'an uwana ne dan haka dole in baka girman ka, kayi hakuri ka tafi amma kafin nan ka tabbatar ka cireni a cikin jadawalin matan da kake burin mallaka kana da matan ka har biyu da tarin yara idan k'arin auren ya zama dole babu laifi ka nema a wani wajen amma nidai na yafe dan haka ka gaida gida,"tana gama fad'in hakan ta mik'e ta haye sama abinta ta barshi anan zaune mamakin kalamanta yasa ya gaza tsayar da ita,
Shiko AK tunda Meenal ta shaida ma Hajiya zuwan Hisham din ita Hajiya itace tayi kiran shi akan yazo tana son magana dashi,
Dalilin Hajiya na kiran shi kuma tayi hakan ne dan yazo ya ganema idon shi Hisham din saboda ma girman kai yasa yayi zaton cewa shi shikad'ai ne yake da burin mallakar Meenal d'in, sauran dalilan ta na aikata hakan kuma ita tasan kayan ta, idan taso muji zuwa gaba zata fad'a da bakin ta kamar yanda har yanzun bata shaida mana yan da sukayi da Yusuf a lokacin da ya kai mata labarin son da AK yakeyi ma Meenal ba,
Shiko AK shi yayi kyakyawan ji da gani domin dai Allah ne yaso shi dan saura kad'an jinin shi yayi hawan da babu shiri a sanda ya kunno kai cikin falon ya iske Meenal d'in shi zaune wani garjejen k'ato na koro mata bayanan soyayya, jinginewa a bango yayi ya samu yayi tsayuwar d'aukar posta dan haka duk abunda suka tattauna kaf a cikin kunnen shi,
Tana shigewa ya juya ya fita a falon shima can bakin gate ya koma yana jiran fitowar Hashim d'in,
Shiko Hashim ciccibawa yayi ya mik'e bayan ya fito motar shi ya bud'e ya d'auki ledar kayan siyayyar daya mata ya k'ara komawa cikin falon Larai data fito daga kitchen dan kwashe kayan motsa bakin da aka ajiye mishi yaba ledan yace ta kaima Meenal shi kuma ya fice daga falon ya koma motar shi ya kunna yabar gidan,
"Tun yaushe mutumin nan ya fara zuwa gidan nan bani da labari?" AK ne yake tambayan masu gadin gidan,
"Wallahi yallabai mudai yau muka fara ganin shi bai tab'a zuwa ba sai yau"
"To daga yau sai yau so nike wannan ya zama zuwan shi gidan nan na farko kuma na k'arshe, kuna jina koh" ya fad'a yana rike kunnen shi guda d'aya,
"Sorry Sir" suka had'a baki wajen fad'a,
"Bana so in k'ara ganin shi yazo gidan nan ko yazo karku bud'e mishi gate duk kuma wanda ya yarda ya taka dokar nan to ya shirya barin gidan nan domin daga ranar ya gama aiki a gidan nan kunji na fad'a muku"
Fuuuu ya juya ya wuce sasan shi duk da hakurin da suke ta faman jera mishi,
Koda ya shiga d'akin shi kasa samun nutsuwa yayi sai faman jeka dawo yakeyi,
Wai dama haka masoyi yakeji idan ya tarar da wani a tareda masoyiyar shi, domin dai shi d'azun ji yayi kamar numfashin ne yake son barin cikin k'irjin shi,
"Kai ina wallahi bazai yuwuba bazai tab'a yuwuwa in cigaba da zuba ido maza suna kaima Abinda Nike so farmaki ba," ya fad'a a fusace yana shurin kujerar dake kusa dashi da kafar shi da karfi har sai da kujerar ta matsa daga mazaunin ta,
Ruwan sanyi ya d'auko ya kafa gorar a baki sai da yaji ruwan ya k'are sannan ya yarda gorar, shi bai san me yasa da zarar ranshi ya baci sai mak'oshin shi ya k'afe ba har sai ya nemi ruwa yasa kafin yake jin damaΒ²,
Yaso ya fita yaje ya doka mata warning itama sai kuma yaga to ai a cikin abunda ya faru babu laifin ta tunda gashi da kunnen shi yaji sanda ta fad'ama mutumin cewa ta fidda miji, tashi yayi ya fice daga gidan gara ya shiga cikin mutane k'ila hakan zaisa zuciyar shi ta sarara,
Ita ko Meenal koda ta shiga d'aki Allah ya sani kalaman Hashim sun b'ata mata rai dan har kuka saida tayi, babu kalmar daya b'ata mata rai irin yanda ya dunga maimaita kalmar bazawara a kanta,
Eh taji ita zawara ce amma aiko zawarar tana da yancin da namiji zai bita da lalama wajen neman soyayyar ta bawai ta karfin tsiya ba,ita dai wannan aure ya zame mata auren bacin suna da ace ba'ayi mata shiba