Showing 12001 words to 15000 words out of 190771 words

Chapter 5 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1593

kin wani bi kin b'ata rai,
To kiyi hakuri ni banyi tambayar dan ranki ya baci ba"
Bata hanya yayi ta fito,

Tana shirin tura kofar motar da niyyar rufewa ne kuma kayan dake hannun ta suka watse a kasa ciki harda ledan pad din da take ta b'oyo dan kar ya gani,
Duk'awar shi da niyyar ya kwaso mata kayan yayi dai dai da sanda itama ta duka dan haka a bazata goshin su ya had'u dana juna ji kake kummm,

"Waiyo Allah goshi na,"

Ta fad'a dan haka shima babu shiri ya d'ago,
Kamo kanta yayi da hannun shi guda,
d'ayan hannun kuma ya fara amfani dashi da niyyar ya murza mata goshin nata data bugu,

Kici kicin kwacewa takeyi tana bori take cewa.

"Nidai ka sakar min kaina ai kaine kaja mukayi karo, waiyo Allah nidai ka kyaleni wallahi akwai zafi idan na shiga zan goga mishi Robb,"

"Oh so kike in bar miki kan yayi tsini uwa goshin jirgi? Salon in gari ya waye hajiya ta nemi ba'asi"

"Eh nidai bana so ka bari zanyi da kaina"

Bai yarda ya saketa ba duk da yanda take harbin shi da kafarta tana dukan shi da hannayen ta sai da ya murza mata goshin ita ko harda kwalla sai da tayi, kafin ya saketa,
Dafe goshin tayi da hannu guda d'ayan hannun kuma tana murza idon ta dashi a dole nan wai ita kuka takeyi,
Shi kuma ganin hakan sai ya duk'a kasa ya tattaro mata kayan.

"Ke wai ma ina kikaje ne da kika fito? "

"Shago"
ta bashi amsa da shagwababbiyar muryarta,
Ledan dake hannun shi ya bud'e wanda pad d'in ke ciki kafin yace

"bari muga mai aka siyo nasan bazai wuce kayan kwadayi ba," budewar ko yayi ba tareda ya jira amsar taba,

"Wallahi Allah nidai karka bud'emin abuna, aiba kai ka aikeni ba ina ruwan ka da abunda na siyo, ka bani abunna karka budemin bana so"

Sai dai duk har gaginta a banza danya riga ya bud'e, dan son ya k'ara kular da itama sai kawai ya wani cire pad d'in daga cikin ledan, ya d'aga pad d'in sama zuwa wajen fuskar shi yana k'are mishi kallo da kyau,

"Miye wannan d'in wai naji shi da taushi ko buredi ne, bakya son inci ne kike wani b'oyewa ba akwai buredi a cikin gidanba shine kikaje kika siyo wani"

"Koba buredi ba nidai kaban kayana bacci nike ji inba haka ba saina had'a ka da Hajiya"

"Allah ya baki hakuri ga kayan ki, karki manta kuma idan kin shiga ki kulle kofar,"
Mika mata yayi, harya juya da niyyar tafiya kuma sai ya juyo.

"Ke..."
Bata amsa ba duk da kuwa tasan da ita yakeyi.

"Kina jina fa"

"Ni ai suna na Ameenatu in ya maka nauyin fad'a ka kirani da Meenal ko Meenat"

"Ai na fad'a miki sunan Mamana ne kike da dan haka bazan iya kiraba, kuma dole duk sunan dana kiraka dashi ki amsa,
Duk bama wannan ba, karki yarda in k'ara ganin ki da yan iskan kayan dana sameki dasu a jikin ki d'azun, bazan hanaki zama tsirara in kina cikin d'akinki ba amma koda wasa karkice zakici gaba da fitowa da wannan shigar zuwa falon Hajiya dan bake kad'ai bane a gidan, ke ko kunya ma bakyaji bayan kinsan bak'i na iya zuwama Hajiya ko wani lokaci"

"To aikai ka shigo mana babu sallama tunda kafin in zauna sai da na kulle kofar falon"

"Na dai fad'a miki kar in kara gani,"
Yana gama fad'in hakan yayi gaba ita kuma ta take mishi baya babu wanda ya k'ara cewa komai a cikin su har suka kai kofar falon yana tsaye harta shige ciki ta kulle kofar falon da key kafin shima ya juya zuwa nashi sashen.


*** *WASHE GARI*


Kamar yanda Sadeeq ya fad'ama Yusuf cewa zai shigo garin na Zaria hakan ce kuwa ta faru,
domin kuwa da dukuยฒn asuba tun gari bai gama waye ba ya baro garin abuja dan tun jiyan dama Musty ya kyankyasa mishi cewar abokin su fa ya fad'a soyyaya dan haka a zak'e ya kwana yana fatan yaga asuba dan ya kama hanya,

Su ukun suke Zaune a Fadar na mai jama'an wanda yake nan kofar gidan wato,
Yusuf
Musty
Da kuma Sadeeq din,

"Wase ka dubi girman Allah ka bamu labarin nan! Kasan cewar daren jiya bacci barawo ne kawai ya saceni amma k'arfe 4 tana bugawa na bud'e ido na fara shirin tahowa, sai yanzun kuma na iso ka wani tsaya kana ja mana rai,
Gaskiya wallahi alhakin mu kawai kake d'auka"

"Ba wani d'aukar alhaki ai na riga na rantse cewa bazan fad'a muku ba sai kun bani tukuici"

"Munji fad'a tukuicin me kake so Allah kuwa zamu baka"
Cewar Musty da yakejin cewa da da hali cikin zuciyar Yusuf din kawai zai shige dan yajiyo ko me nene cikin sauk'i dan Yusuf din tun safe yake mishi iya shege ko satar amsa ma yaki bashi balle ya gane ko wacece abokin nasu yake so,

Paper Yusuf ya dauka da biro ya rubuta musu account number din shi yayi rubutun manya ta yanda dukan su zasu iya hange daga inda suke,
Sannan ya ajiye musu a tsakiyar su,

"Gashi nan in fara ganin saukar alert masu nauyi a account dina tukun ni kuma in fad'e muku biri har wutsiya"

Yana fad'a yana yarfe hannuwa alamun ko a jikin shi dan haka sai ma ya d'auki remote din tv ya fara canza channels,

Tsaki mai kauri dukan su biyun sukaja kamar masu shirin rufe shi da duka,

"Eh kuyi tsakin ku gama na dai fad'a muku sharadina,"

Kusan a jere karar shigowar sakon nin ya sauka a wayar shi dake ajiye akan center table,
Dan haka babu b'ata lokaci ya mika hannu ya d'auko wayar alert din ne kuwa,

"Oh dama kun gama shawara akan nawa zaku siya labarin nawa ne da naga kun turo min amount d'aya a tare?"

"Kai Yusuf idan kud'in basu maka dawo min da kayana d'an fashin tsakar rana kawai inma banda rashin tsoron Allah muda keda hidimar biki a gaban mu mune wai zaka tasa kana mana sata"

Cewar Musty.

"Oh sata nema? To dan uban mutum nine nace mutum yaje ya tattago aure? In kasan baka tara kudin hidima ba ai sai kace su d'aga auren kawai,
Kunga ni bacci ma nike ji bari in koma ciki idan kun shirya jin labarin sai ku tasoni"

"In ka isa shege nike, mune zaka maida wasu yan iska bayan ka danni kud'i a account dinka ne zakace kuma bacci kakeji"

Sadeeq ya fad'a a yayin da ya mike yana huci yaje ya rufo kofar falon harda murza key,

"Allah ya baka hakuri, atoh bawai dan kunga kun fini girman jiki bane zaka wani rufo kofa waton kuci min uwa babu mai kwata na, to zoka zauna in baku labarin komai dan musan ta yanda zamu bullowa abun dan gaskiya nidai bana son muyi sanya gudun samun ko wacce irin tangard'a daka iya tasowa"

Ya k'arasa fad'a yana gyara zaman shi bayan yaci serious sosai,
Kowama Sadeeq din yayi ya zauna suka sa Yusuf din a tsakiyar su,

"Nasan dukan ku kun lura da canjin da AK yayi wanda a lukuta da dama munsha tambayar shi amma sai yace mana wai stress ne?"

"Kwarai anyi haka"
Suka amsa mishi dashi,

"Tun a shekarun baya nina lura da cewa AK yana da damuwa, na kumayi iya bincike na ban gane miye silar damuwar nashi ba sai daga baya na lura da cewa yawancin lokuta yakan shiga damuwan ne idan yazo garin nan,
Wanda idan kun lura a lokacin zakuga cewa sam koda wani abun ya taso anan bazai zoba sai dai cikin ni daku wani ya wakilce shi,
Daga baya kuma sai abun yayi kamar yayi sauk'i duk da ni na tabbatar da cewa yana kokarin boyewa ne kawai a duk lokacin da muke tare saboda gudun amsa tambayoyin da yasan zamu mishi,
Sai dai duk yanda ya boye ni na san damuwar nashi tabbas tana da alaqa da soyayya sai dai nima ban matsa mishi ba amma ina dai ta binshi da addu'a,"

"Wai kana nufin tsawon lokacin nan dama son wata ya mace ne yake faman wahal dashi? "
Musty ya tambaya.

"Kwarai kuwa ina da tabbacin hakan domin da farko daya fara sonta shima kanshi bai gane son ta yake ba,
A lokuta da dama idan naga yanda yake mata nakan tsaya inyi ta kallon shi dan na gane cewa yar tsamar dake gudana a tsakanin su sosai yake sashi nishad'i,
Amma ban ce mishi komai ba dan nasan da zarar nayi magana musamin zaiyi ko kuma yama fita a sabgar ita yarinyar,
Dan haka a boye wani lokacin nakan aika a kirata dan tazo inda yake dan nasan baza'a kwashe lafiya ba dan ita ma bata da hakuri kuma ita ce kadai macen da naga tana da zarar tsayawa a gaban shi ta mishi maganar da taga dama amma kuma sai ya kasa d'aukar ko wani mataki a kanta sab'anin hakan ma sai dai kawai yayi ta binta da kallo idan kuma ta tafi sai yayi ta murmushin da ba halin shi bane,"

"Ikon Allah"
Sadeeq ya fad'a yana rike baki,

"Kana mamaki koh?"
Cewar Yusuf.

"Ci gaba please Yusuf so nike in san ina aka kwana"
Musty ya Fad'i hakan yana dungure ma Sadeeq hannun daya dafe hab'ar shi dashi,

"A dai dai lokacin da shi yake rainon soyayyar ta, a lokacin da canji ya shigo rayuwar shi kawai sai rana d'aya muka tsinci mummunar labarin cewa Baban yarinyar ya fidda mata mijin aure, wanda a lokacin shi kuma a boye AK yake ta yak'i da samarin yarinyar dan ya rabata dasu,
Kun san me?"

"Ah ah sai ka fad'a"

"Wallahi lokacin har k'aramin ciwo sai da yayi ninayi jinyar shi a asibiti na kwana biyu ko Hajiya bata sani ba balle ku, duk da kuwa cewa ko a wancan lokacin yaki yarda ya fad'amin dalilin ciwon nima kuma ban iyace mishi komai ba, dan ban san ta inda zan fara rarrashin shiba, bayan yaji sauk'i ne kuma ya tattara yabar kasar gaba da goyon bayana dan nasan idan baya kasar yawan tunata da yakeyi zai ragu sab'anin idan yana nan da zaici gaba da ganin ta ciwon sonta yana taso mishi alhalin ita d'in kuma matar wani ne"

"Innalillahi wa'innah ilairir raju'un"
Suka tsinci bakunan su da maimaitawa,
Musty ne yayi k'arfin halin bude baki ya jefama Yusuf tambayar dake cikin zuciyar shi cewa,

"Kenan matar aure yako so?"

"Ah ah ba matar aure bane domin kuwa a yanzun dai auren nata ya mutu sun rabu da mijin nata"

"Alhamdulillah kenan dai akwai hope dake nufin cewa Abokin mu zai iya samunta a matsayin mata?"
Sadeeq ya tambaya yana kallon Yusuf.

"Eh kusan hakan ne if we act quickly, idan kuma muka tsaya sanya tofa tabbas zamuji a salan sane dan ita yarinyar baban ta shike zab'ar ma yaran shi mata miji a yanda wanda nasa shi yamin bincike ya tabbatar min da hakan,
Sannan kuma shima din adai yanda ni daku muka sani ba lallai bane ya iya tunkaranta kai tsaye ya furta mata cewa yana son ta ba,
Wannan nema dalilin da yasa nace kuzo mu tattauna dan musan ta yanda zamu bullo ma al'amarin, jiya naso inyi maganar da Hajiya sai kuma dai nace bari in farayin magana daku biyun tukun, ya kuke ganin zamuyi?"

"Wai kenan kana nufin har yanzun bai gayama yarinyar cewa yana sonta ba?"
Sadeeq ya k'ara tambaya da mamaki,

"Eh bai fad'aba"

Shiko musty cewa yayi

"Ikon Allah lallai AK son gaskiya yake ma yarinyar nan inba haka ba mace taje tayi aure a wani wajen harta fito amma ka kasa cireta a cikin zuciyar ka yanzun data riga ta zama bazawara, wai ma wacece yarinyar nan ne?"

Dariya Yusuf yayi yana kallon musty yace "mamaki kakeyi kenan, to ai soyyaya tafi gaban nan kuma ita yarinyar inda zaka ganta yanzun a gaban ka na tabbatar da cewa kana iya d'aura alwallah ka dafa qur'ani akan cewa budurwa ce, dan yarinya ce k'arama har yanzun dan tana da yarinta sosai akayi mata auren ba kuma son juna suke ita da mijin ba dan haka nema shi sakaran ya sakota ba tareda ko sanin ta a matsayin mace yayi ba, wannan labarin kuma duka a safiyar yau na same shi a wajen wanda nasa ya bincikamin, duk da kuwa ita yarinyar yar uwar AK ce ta kusa"

"Kai tsaya dan Allah Yusuf wai badai akan Meenal kake magana ba? "
Cewar Musty a yayinda ya mik'e tsaye ya fara kaida kawo a cikin falon.

"Ita fa jikar hajiya yarinyar aunty Jidda wacce yanzun haka take zaune tareda Hajiya"
Yusuf ya bashi amsa.

"Ikon Allah wai meenal ce dama AK keso?"
Sadeeq ya fada cike da tarin mamaki,

"Babu wai a cikin maganar nan" Yusuf ya bashi amsa.

"To amma me yasa mu bamu gane hakan ba tuntuni? "

"Saboda baku sa kanku zaku gane ba amma ni tuni na harbo jirgin shi"

Dariya sosai suka fashe dashi,
Musty ne mai cewa
"Shegen gora mutumin dake cewa allah ya kyauta yayi soyayya da karamar yarinya,
Wai kum ma san da sunan da yake kiranta?
Jaririya fa yake ce mata saboda tana da sunan maman shi shi kuma yafi karfin ya kirata da meenal,"

Ya k'arasa fada yana dariya sosai,

"Aiko sai naci uban shi wallahi yanda ya dunga mana maganar banza muma gashi alhaki ya kamashi zai kare a karamar yarinya bazawara ma"
Inji musty

"Kai wallahi in kana ce maka bazawara matsala zaku samu,
Dan jiya cemin yayi ba zawara ba ko duniya ta haifa shi dai yana sonta a haka balle kuma itama din budurwa ce,"

"Kai gaskiya naji dadin labarin nan sosai gaskiya koba komai shima ya samu abunda zuciyar shi keso zanso kuma ace wannan karan ya mallaketa a matsayin mata karta k'ara kucce mishi kuma mu shiga uku dan yasin AK yana iya haukacewa idan ya rasa ta"

"Kwarai kuwa, amma dai yanzun muyi hakuri zuwa gaba kadan duk da dai bawai zatayi iddah bane amma mud'an jinkirta har abun ya saketa tukun,
Hajiya kuma ni zan mata bayani da kaina, shi kuma na mishi bayani akan yayi kokari ya dunga jan yarinyar a jiki bawai irin yanda ya saba d'aurema yan matan shi fuska zai mata ba, kuma muma zamu taya shi wannan yak'in a bayan fage dan Wallahi wannan yarinyar yanda take nasan da zarar maza suka gane bata da aure tofa bashi kadai ba muma mun shiga ukun mu dan ba matar yara bace wallahi"

"Wai shi yana ina ma?"

Sadeeq ya tambaya,

"Ina zaka ganshi yana can falon Hajiya tun safe daya d'auki wanka can yaje ya kasa ya tsare yana kallon rabin ran shi"

Fashewa sukayi da dariya, lallai aiki ya samu ga masuyi,
To Allah ya sanya alkhairi, sun dade suna tattaunawa....

Yayinda suke nan suna tattaunawa shi kuma gogan yau tunda safe ya k'ara d'aukar wani wankan cikin wasu fararen kayan wani yadi mai d'an karan taushi uwa auduga idanun ka kad'ai sun isa sheda wajen fada maka cewan tsadadden yadine, kasancewar shi mara nauyin shi da kasancewar shi mara kaurine yasa ake iya hango best din daya saka a ciki, kamar koda yaushe kuma sai da ya tabbatar da cewa ya feshe jikin shi da turare kafin ya doshi sashin Hajjaju to dai tunda ya shiga dama yake ta faman ware idon dan son ganin ta inda gwanar nashi zata fito sai dai kuma harya share kusan minti Biyar baiji motsin saukowar taba,
Dan haka ya tashi kai tsaye ya nufi kitchen sai dai koda ya lek'a Larai ce kadai a kitchen din,
Bayan sun gaisa yake tambayar ta "mutanen gidan basu tashi bacci bane?
Ita kuma ta bashi amsa da cewar sun tashi basu dai sauko bane duk da dai ita Meenal bata jima data sauko ta had'a tea ta koma saman ba,

Komawa da baya yayi kafin ya haye saman, d'akin Hajiya ya shiga da sallama sai dai ita kuma a gado ya hangota lullub'e da bargo tana bacci,
Gudun karya tashe tane kuma hakan yasa ya koma da baya ya fita daga d'akin ya rufe mata kofa,
Har yayi gaba da niyar sauka sai kuma zuciyar shi ta kasa bashi had'in kai dan haka sai kawai ya koma da baya ya murd'a kofar d'in nata da sallama d'auke a bakin shi, sai da yayi sallama sau uku kafin a amsa mishi ana hud'u shi kuma jin ta amsa hakan ya bashi damar Sakai cikin dakin ba tareda jiran izinin shiga daga mai d'akin ba,

Shigar da sai da yayi dana sani kwando dubu cewar daya sani da baima shigo Sashen ba balle har ya hauro saman........

*Allah kuwa idan banga comment ba babu na dare*๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€๏ธ.

Kuma banyi editing ba๐Ÿ˜œ
*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ

#Mai Jama'a
#Sheikh Naseer
#Meenal
#Hajiya
#Malam
[8/21, 9:44 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2
ยฉยฎ *UZ-2023.*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ


----- *Page 5*


Da wani irin sauri mai cike da zafin nama irin na zaratan maza ya juya ya fito daga d'akin nata idanuwan shi a rufe ruf, bayan ya runtse idanuwan shima sai da yayi amfani da hannun shi ya k'ara rufe fuskar shi da tafukan hannun nashi,
Sai dai kuma har zuwa lokacin bai daina ganin hoton abunda yaci karo dashi a cikin kwayar idanun shiba, to wai shi me zai kira wannan ganin? Farin gani ko bak'in gani,
"Subhanallah Masha Allah lallai Allah yayi halitta a wajen can wai wai wai dank'ari",
Gaba daya fa ya rud'e dan bai tab'a zato ko tsammanin cewar gamon da zaiyi kenan a cikin d'akin ba, rawan da jikin shi keyi ne kuma hakan yasa dole ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login