Showing 105001 words to 108000 words out of 190771 words
mata kauna tun zamanin da take cikin k'uruciyar ta ta kuma yarda cewa Allah yayi cewa ba shine Mijinta ba shi yasa tun farko bata bashi damar zuwa gidan suba,
Sai gashi kuma yanzun kwatsam yana son dawowa gareta a dai dai lokacin data amsa soyayyar wanin shi bayan kuma shi ta dad'e da mishi delete all a cikin memory d'in ta,
Yanzun idan ya dawo ya k'ara gabatar da kanshi a karo na biyu ya zatayi?,
da wani fuskar zata tarbeshi alhalin ita tuni ta dad'e da yima nashi soyayyar kabari ta birni a matsayin matacce.
Shiru tayi domin gaba d'aya ta riga ta tayi b'acewar b'at a cikin tunanin halin da take ciki a yanzun yanda abubuwa suke neman jagula mata lissafi duk yanda take kamewa amma abun mamaki kamar wacce akayi shelar mutuwar auren ta domin dai kullum mazaje ne ke kawo mata hari ba'a makaranta ba ba kuma cikin gari ba kamar dai ita kad'aice bazawara a gari,
Ga AK, ga Salman, ga Aliyu, ga kuma Ya Hashim sannan kuma yanzun ga bash ya dawo bata ma sa sauran samarin dake faman biyayyar ta wad'anda bata da alaqa dasu a lissafi ba dan har yanzun wasu ma basu san katamai man gidan suba balle su kawo mata hari,
"Allah Sarki Bash nayi zaton ko ya manta dani tuntuni ai?" Ta furta kalmar a sanyaye,
Tab'e baki Sultana tayi kafin tace,
"Shidai kam alamu sun nuna cewa bai manta dake dinba har yanzun, gashi kuma ke tuni kin dad'e da mantawa dashi ni kam na gode Allah da yasa gayen nan ya dawo a makare, dan haka bari kiji duk ma ranar daya sake ya kawo kanshi wajen ki karki wani tsaya yin mishi muna muna ko munafunci ki fito fili ki fad'a mishi gaskiyar cewa tafiyar sa'ar ki da nashi basu jera hanya ba tunda gashi a wannan karon ma dai yana ji yana gani zai k'ara rasaki, zaifi mishi sauk'i idan ya tafi wani wajen ya k'ara lalube ko zai dace da samun abokiyar tafiya, kai ni ina rokon allah ma ya mantar dashi ke gaba d'aya wallahi Allah yasa kuma k'in tunkarar naki da yayi hakan ba yana nufin cewa zaiyi miki shigar k'arfi bane wannan karon ,
Dan yana iya komawa gefe yace zai tura iyayen shi kai tsaye wajen su Baba Malam kafin ya gabatar da kanshi gareki a karo na biyu, duba da abinda ya faru a shekarun baya sanadiyar rashin gabatar da kanshi da yayi a gaban iyayen ki"
Ta k'arasa fad'a tana watsa hannuwa dan itafa tsakani da Allah duk wani wanda zai fito yanzun yace Meenal yake so to dole nema ta taya AK adawa dashi domin ba karamin dacewa take ganin Meenal tayi na samu AK ba, dan haka bazata yarda wani can yazo yace zaiyi takara da AK ba,
Ba iya Meenal bace kad'ai taji saukar kalmar da Sultana ta fad'a a cikin k'irjin taba har su Moon sai da suka zazzaburo,
"Kina nufin idan saurayi yaga kamar ke idan ya nemeki zaki bashi ciwon kai shine zaisa ya wuce wajen iyayen ki kai tsaye ya gabatar da kanshi a wajen su?"
Moon ta tambayi hakan a k'age da son jin amsar da Sultana zata bata,
"Eh kwarai kuwa kusan hakan ne amma shi ni a nawa tunanin ina ganin kamar tunda ai tun farko yasan dokar gidan su Meenal din shine yake so ya koma yabi tsarin duba da cewa rashin bin tsarin yana daga cikin dalilan da sukayi jagoran cin daya rasata a shekarun baya,
Kuyi nazarin magana ta da kyau zaku fahimta, Meenal kinga dai ban san wani irin so kikama Bash din nan a baya ba, amma koma dai yayane ni zan fad'a miki gaskiya duk wanda zai soki a yanzun bana tunanin zai miki so irin wanda AK yake miki a yanzun kai ni banma ga uban meye ya hanaki kiba bawan Allan nan damar gabatar da kanshi a gidan kuba wai so kike sai an k'ara miki wani auren dolen ne kafin ki dawo cikin hayyacin ki?"
Hummm suka dunga fad'a suna gyad'a kai cike da nazarin kalaman Sultanan dan dukan su sun san cewa gaskiya ta fad'a,
Ita ko Moon a gefen ta ba k'aramin tashin hankali takeji a cikin k'irjin taba, kenan idan ta auna kalaman Sultanan hakan yana nufin cewa shima Sarki yana iya zagayewa yaje ya nemi aurenta ta baya batareda ya nemi jin nata ra'ayin ba?
Duba da cewa tun sanda ya mata magana da farko ta nuna mishi ah ah bai k'ara tada zancen ba kuma ko a fuska bai nuna mata damuwa ba, ita kuma nauyin shi da takeji yasa har yau ta kasa k'ara tada maganar, to idan kuma tayi shiru har yaje ya zagaya ya nemi auren ta ta bayan gida maganar ta fito daga baya da wani idon zata d'aga ta kalli Meenal wani kalan bayani zata mata waiyo Allah ta shiga uku, zufa ta dunga had'awa ta ciki duk da sanyin fanka da ac din daya cika falon na Hajiya Jummai.
Abinda ya faru a Lagos kafin ta taho,
Tsakanin ta da Sarki lafiya lau sukaci gaba da ganin juna babu wani abunda ya canza a tsakanin su domin dai duk da cewa bai k'ara taso mata da maganar zuwa neman auren ta wajen Baba Usman ba hakan bai hana shi cigaba da nuna mata kauna da soyayyar da yake mata ba,
Da farko had'uwar su iya waje biyu suke yin shi kodai a wajen aikin ta ko kuma da yamma a can inda suka saba had'uwa amma sai gashi daga baya kuma har gidan su yake binta,
Ranar farko daya fara zuwa gidan tayi mamaki kwarai dan batayi zaton cewa shi d'in ne da gaske ba domin dai ko a ranar yaje can wajen aikin ta ya sameta sai dai bai dad'e sosai ba ya mata Sallama ya tafi a matsayin cewa sai sun had'u da yamma, da yamman tayi bai samu zuwa can wajen ba dan ya kirata ya sheda mata ta kirasu tayi order din abinda take buk'ata kawai sukai mata gida dan yayi busy bazai samu damar had'uwa da ita ba amma idan ya kammala abinda yakeyi d wuri zai neme ta,
To itama jin hakan da yace sai bata damu kanta da cewa sai taje d'in ba sai tayi zaman ta kawai a gida,
Daren ranar suna zaune a falo suna hira ita dasu Umma da sauran k'annin ta kiran shi ya shigo cikin wayar ta,
Tashi tayi tsam bayan ta d'aga wayar ta koma d'aki saboda bata son tayi wani abunda zaisa Umman tayi zargin cewa har yanzun ashe suna tare ita da Sarkin duba da yanda ta fito k'iri² ta nuna mata rashin amincewar ta akan alaqar tasu dan ita dai tace bata yarda da auren cin amana ba, ta ina ma za'a fara ace wai mijin daya auri Meenal ya saka shine zai auri Moon a yanzun bayan dukan su kowa yasan bayan k'awance harda alaqa ta jini a tsakanin su,
Tunda ta amsa sallamar daya mata bata yarda ta k'ara furta komai ba sai da ta tabbatar da cewa ta maida k'ofar dakin ta ta kulle shi da kyau,
"Barka da dare dafatan ka wuni lafiya"
"Alhamdulillah ya kike?"
Ya tambaya
"Ina lafiya"
"Me kikeyi ne?" Ya k'ara tambaya,
"Ba komai"
"Ok to fito gani a farfajiyar gidan ku"
"Na'am" ta amsa dashi bayan ta ciro wayar daga kunnen ta ta duba Number din domin tantancewa,
"Eh ki fito nace ko insa ayi min iso ne in shigo ciki?" Ya fad'a ko a jikin shi,
"Uhmm uhmm wai nan gidan kake magana"
"Kuna da wani gidan bayan wannan ne anan Lagos dama?"
"Ah ah amma ai baka cemin zaka zo ba, umm bawani nan nasan ma wasa kawai kakeyi min"
Murmushi yayi daga can gefen shi, murmushin da harta cikin wayan sai da ta jiyo shi, kafin ya daura da cewa,
"Yanzun dai koma wasa ne ko gaske duk idan kika fito zaki tabbatar in kuma kika b'ata min lokaci wallahi cikin gidan zan shigo kinji dai na rantse miki dan haka ki fito yanzun" yana gama fad'in hakan ya yanke wayar shi,
Sororo tayi da wayar a kunne,
Cike da mamaki to wai ma meyazo yi a gidan su da daddaren nan salon ya tona mata asiri a wajen Umman su, yanzun in Umman su tasan cewa Sarki na cikin gidan nan yazo hira wajen ta ya zatayi?
Tunawa da rantsuwar da yayi cewa idan ta b'ata lokaci zai shigo cikin gidan ne hakan yasa dole ta fito daga cikin d'akin ko mayafi bata d'auka gudun karma Umman su taga fitan ta, ta k'ofar baya tabi a sace kamar b'arauniya sai da ta fice kafin ta tsaya ta warware dan kwalin rigar dake jikinta ya yafashi tana sauke ajiyar zuciya tun daga nesa ta hango shi zaune akan fararen kujerun dake farfajiyar gidan, gabanta naci gaba da fad'uwa haka dai ta daure taci gaba da taku harta isa inda yake wanda shima hango tahowar nata ne yasa shi mik'ewa dan ya tarota,
"Shine kazo nan bayan kuma baka fad'amin cewa zaka zoba" shine kalmar data fara furtawa tun bata samu zarafin zama ba,
"Bakiyi farin cikin ganina ba kenan? Niko kinga na kasa daurema zuwa gida in kwanta batareda nayi tozali da wad'annan fararen idanuwan naki ba shi yasa na biyo dare na taho kawai dan in ganki,nayi zato zakiyi farin ciki kema amma tunda bakiyi farin ciki ba kiyi hakuri kina iya komawa ciki tunda na ganki"
Juyawa yayi da niyar tafiya tayi saurin shan gaban shi,
"To ni ai bance ka tafi ba kawai dai nayi mamaki ne da kace min gaka tunda naga ko d'azun munyi waya kuma baka cemin zaka zo ba"
"Ai nace miki kawai nazo ne dan in kalli fuskar ki a zahiri kuma na gani hankali ya kwanta kije ciki sai da safe"ya fad'i hakan yana zura hannayen shi a aljihun wandon jikin shi,
Bata samu zarafin cewa komai ba Baba Usman ya bayyana a wajen daga cikin gidan ya fito da alama fita zaiyi, ba karamin tashin hankali ne ya risketa ba sai dai kuma ta danne hakan dan ba lallai bane a zatonta ya gane Sarki, kasa tayi da muryar ta,
"Kagani kaja min ko ga Baba nan ya firo"
Bai kulata ba saima wucewa da yayi ya k'arasa wajen baba Usman din sukayi gaisuwar da bataji me sukace ba dan Sarki bai tsaya ba sai da ya raka Baba Usman din har mota sannan ya koma inda take tsaye,
"To yane yanzun dai bari in wuce kar in shiga lokacin ki da yawa"
"Me kace ma Baba?"
Ta tambaya tana bin shi da kallo a sanyaye,
"Babu" kawai ya bata ansa dashi,
"Babu me? " ita kuma ta tambaya,
"Bance mishi komai ba, me kike tunanin zance mishi bayan gaisuwa, amma ke idan ya dawo ya tambaye ki cewa me nazoyi wajen ki wani amsar zaki bashi?"
Ya tambaya yana tsareta da ido,
Juyawa tayi sai da tayi taku d'aya biyu ba tareda yayi yunk'urin tsaidata ba kafin taci burki ta juyo ba tareda ta kalli idon shiba tace,
"Sai da safe"
Tana gama fad'in hakan ta juya tayi cikin gidan da sauri gabanta yana tsanan ta fad'uwa dan batasan me zai biyo baya ba kuma,
Sarki bai gusa daga inda ta barshi tsaye ba harta shige cikin gidan, shi dariya ma ta bashi wallahi dan Allah kuga duk yanda tabi ta rud'e shifa gaba d'aya baiga abun tashin hankali a cikin al'amarin nan ba da take ta faman son ta hana ma kanta abinda zuciyar ta keso wanda kuma bawai hakan ya haramta a gareta bane, aiko mai kankat zai mata Allah dai yakai su Zaria lafiya,
Cikin masu gadin su ya kira guda ya bashi sako yace ya mik'a mata cikin gidan,
Ranar kwanan d'ar d'ar tayi domin motsi kad'an idan taji sai taga kamar Baba Usman ne zai aiko ayi mishi kiranta dan yaji ko waye yagan su tare, ko sakon da Sarki ya bayar aka biyota dashi bata bi ta kanshi ba k'annen tane sukayi didima a kanshi,
Tun daga ranar Sarki ya tsiri yi mata zuwan bazata bazai tab'a fad'a mata cewa zaizo ba sai ya shigo cikin gidan sannan zai kirata cewa yana jiran ta, ita kuma ta kasa fitowa ta fad'a mishi cewar ya rufa mata asiri ya dena zuwa gidan, kuma bayan ganin farko da Baba Usman ya musu sau biyu ya k'ara ganin su tare bai kuma yi mata magana ba har sai ana gobe zata wuce Zaria a gaban Umman su ya kirata yake tambayar ta cewa,
"Maimoon wanene wanda naga yana zuwa wajen ki hira a yan kwanakin nan?"
Tsuru² tayi uwa an jijjiga bera a cikin buta,
"Hira kuma Baban su ai a dai cikin kwanakin nan bana jin akwai wani saurayin dake zuwa hira wajen ta" cewar Ummah
"Kece dai baki san ana zuwa hira wajen nata ba amma ai gata nan zaune a gaban ki kinji ta musa abinda nace ne? Ke Maimoon dake nake magana"
"Abokin aikina ne"ta tsinci kanta da furtawa dan tasan yau ta shiga uku idan har Ummah tasan Sarki na zuwa hira gidan nan wajen ta,
"Shi abokin aikin naki yake zuwa gidan nan har kike Rita ni ina gidan nan bani da labari" umman su ta fad'a cike da mamaki,
"Kiyi hakuri" Moon tace kanta a k'asa,
Shi kuma Baba Usman d'aurawa yayi da cewa,
"Kin san me yasa na kiraki nan?"
"Ah ah " ta furta tana girgiza kai,
"Masha Allah to dama kiranki nayi dan in baki hakkin ki a matsayin ki na budurwa, shin akwai tsayayyen saurayin da kika tsayar a cikin samarin kine? Ina nufin wanda kike da burin aure?"
"Baban su kaima dai kamar baka san hali ba, ina ma take kula samarin balle harta tsaida tsayayye nidai dama ai tun tuni nike ta maka magana akan Lukman d'an wajen Hajiya Hasiya ka sani sarai tun tuni yake bibiyarta take mishi wulakanci amma har yanzun yaron nan ya kasa hak'ura ya nemi wata ya aura, ita kuma da kullum take ikirarin cewa bata son shi ta fitar da wani mijin tayi aure tak'i tasa har yan uwana sun fara ganin kamar nice bana son in had'a zuria dasu to nidai tunda abin ya zama haka gara aba shi Lukman din komai koba komai dukan mu mun sheda yana son ta...."
Saurin tarar numfashin ta Moon tayi da cewa,
"Wallahi Umma nidai bana son shi, dan Allah karki matsa kice sena aure shi"
"To Moon in baki auri Lukman ba wa kika tsayar ne bayan kullum nan ko mazan sun biyoki har gidan nan ma ba kulasu kikeyi ba, so kike mu zuba miki ido kici gaba da zama a gaban ki dan kawai muna zaune a kudu? Kina zaton inda a arewa ne har zamu yarda ki kawo uwar haka ba tareda mun aurar dake bane?
Abban su nidai ina goyon bayan ka tunda tace bata son lukman d'in to kai ka duba a gefen ka kawai tunda ruwan ido yasa ta k'asa tsaida tsayayye"
Kuka Moon din ta fashe musu dashi, cikin kukan take cewa "Dan Allah Baba karka min auren dole"
"To Maimoon ya kike so muyi dake? So kike musa miki ido kiyi ta zama babu aure ne?"
"Ah ah ai zan kawo mijin auren idan na samu"
"To kiji ni da kyau, sati d'aya kacal na baki daga yau kije ki zauna kiyi nazari da kyau ki tantance a cikin samarin ki ki fidda gwani, koma waye shi ina so ki gabatar mana dashi idan mun isa Zaria yazo gida ayi magana saboda Abban ku Ahmad zai shigo k'asa ina buk'atar tabbatar da tabbatuwar zancen auren ki kafin sanda zai koma kinji na fad'a miki, tashi ki tafi"
Jiki ba kwari ta mik'e tabar falon cike da tashin hankali,
Dan Allah ita ta ina zata vara fidda miji a cikin sati d'aya kachal, sati d'aya fa kuma tasan kome zatayi bazai canza daga yanda yace sati d'ayan ba,
Bayan fitan ta ne Baba Usman yake ba Umma labarin cewa akwai wad'anda sukazo neman auren Moon din a wajen shi baya son taga kamar ya mata dole ne shi yasa ya bata dama in akwai wanda take so to ta gabatar dashi dan babu fashi indai Allah ya kawo Abba Ahmad lafiya tofa bazai bar k'asa ba sai sun kammala zancen auren da yaran,
Sai dai kuma kids Umma ta tambaye shi waye ke neman auren na Moon bai fad'a mata ko waye ba sai ma k'okarin d'auke hankalin ta da yayi da wani hirar a sanda ya shaida mata cewa yanzun hakan isar su Zaria Hajiya ke jira dan suje su nemar ma AK auren Meenal a wajen iyayen ta maza,
Ita ko sosai tayi farin ciki dajin labarin cew AK ne keson auren Meenal wannan karon,
Taso ta kawo mishi zancen Sarki da yake son Moon sai kuma ta hana kanta,
Bayan Ummah tabar wajen Baba Usman wajen Moon ta wuce dan tana buk'atar magana da ita,
"Maimoon kin daiji abinda Baban ku yace koh? Sanin kanki ne kuma sati d'ayan nan daya diba miki yana ciki babu wani sauran uzurin da zai miki,
Maimoon nidai nayi miki sha'awar ki auri Lukman bama wai dan saboda kasancewar shi yaron yayata ba ah ah sai dan na yaba da tarbiyar shi da kuma soyayyar shi gareki, amma tunda kince bakya son shi bazan miki dole ba sai dai zan baki shawara duk mijin da zaki gabatar a gaban iyayen ki ina son ki fara natsuwa ki tabbar da cewa shin kina son shi har cikin zuciyar ki ko ah ah"
Ta d'an bata shawarwari kafin ta fice tabar mata d'akin,
Ita dai wallah tana cikin tsaka mai wuya domin dai tunda Sarki ya shigo cikin rayuwarta tayi