Showing 156001 words to 159000 words out of 190771 words

Chapter 53 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1566

bisu d'aya bayan d'aya ya rungume su yana musu godiya akan jajircewar su na ganin sun samar mishi abinda yake so Hajiya dai sashen ta tawuce bayan itama ta gama amsa gaisuwar jama'ar dake harabar gidan,

Shi kuma Musty da sauran abokan su sai suka janye AK zuwa kofar gidan cikin sauran matasan da suka cika unguwar suna taya shi murna,

Taro ne ya had'u na ban mamaki a wajen nan domin shi kanshi AK yayi mamaki da ganin yawan mutanen dake wajen, koda ya shigo gidan fa a d'azun dai dai kun mutane ne a wajen amma yanzun duk inda ka kalla jama'a ne tako ina, lallai AK ya tabbata mai jama'an na gasken gaske wai a hakan ma ba kowa yaji labarin zancen auren ba,
Matasa sunyi kara gaskiya dan duk wanda labarin yaje kunnen shi baya zama sai yazo dan k'ara samun tabbaci dan da farko da yawa wasu sun karyata zancen auren,
Dan haka kafin ka ankara unguwar ta cika mak'il dan ko abincin da Hajiya tasa aka dafa a cikin gidan kafin a fito dashi waje har ya k'are dan ma shi Musty tun dawowar su daga wajen d'aurin auren ya k'ara bada order a wad'ansu gidajen abincin banda na restaurant din dake nan kofar gidan nasu,

Ko kafin ace karfe 8 na dare tuni Yusuf da iyalan shi harma da Sadeeq sun hallara a gidan Hajiya suma kuma tareda nasu mutanen suka taho domin dai duk wanda akace ma an d'aura auren burin shi kawai yazo ya tabbatar ne dan kowa mamaki yakeyi wai AK aka d'aura ma aure babu gayyata to dan uban shi inma sune bai son gani wajen bikin shi sai sunje shagali sosai fa aka gabatar a kofar gidan Hajiya rana suma kuma matan suna ciki suna nasu,

A can gidan Malam ko bayan an gama d'aurin aure Hajiya da gayyarta sun wuce suma dai haka sukaci gaba da k'arbar bak'i yan zuwa Allah sanya alkhairi yan uwa nakusa suma dai tuni suka hallara duk da kuwa yanda abin yazo musu a girshe,

Baba Auta bai samu shigowa gidan ba sai gab magrib dan Baba Adamu ne ya kirashi ya shaida mishi abinda ake ciki,

Bayan an idar da sallah suna shiga gida Malam ya had'a kan Baba Adamu dashi Baba Auta a falon shi,

"Auta nasan ka samu labarin abinda Hajiya tazo tayi min a falon nan koh!
To Alhamdulillah ta gama nata nima zanyi nawa ikon, domin mu dai gidan nan tunda mukayi wayau bamu tab'a ganin inda aka gudanar da neman aure irin wanda ita ta jogoranta a yau ba,
Inda kuma nace zan tsawata a dazun din nasan kowa laifina zai gani to Alhamdulillah na bata dama itama kuma ta dama sai dai kuma tunda suka sa aka d'aura auren a yau tofa bazasu jingine min yarinya taci gaba da zama tana yawo da auren d'an su ba,
Kai Adamu kai da kayi jagora kaine zaka kira su ka shaida musu cewa yau labara ni kuma na tsaida ranar juma'an nan mai zuwa a matsayin ranar yinin biki da tariya dan haka su fad'i inda d'ansu zai zauna da ita gobe za'aje ayi mata jere, shi kuma Sheikh ka tambaye shi idan bashi da inda zai ajiye Raheenat d'in to akwai takardar gidan da Alhaji Mai Kud'i ya bashi jiya ya kawo min takardun tun a daren jiyan sai aje gidan aduba in akwai gyara kunga sai ya hak'ura da tarewa acan su zauna a wancan sashen dake gefen nasu Sa'eed tunda a gyare wajen yake kafin lokacin dazai koma Abuja,yauwa kuma karka manta kasa mai d'akin ka tayi list na duk abubuwan da basu had'o dashi ba na auren budurwa ciki harda lefe dan kar suga an d'aura aure suyi zaton ko sun sha, a kuma je a d'auko min ita Meenal din a can gidan ta dawo nan, sai abu na k'arshe karku manta ku kira sauran mutanen da basuji auren ba dan ranar juma'an dai za'ayi yinin biki dakai amare d'akin su, kuna iya tafiya na gama magana"

Yana gama fad'in hakan ya mike ya shige cikin bedroom din shi ya barsu da binshi da ido,
Baba Adamu ne ya fara mikewa kafin yace "muje koh auta dan kasan dai dole yanda yace din shi za'ayi muje in zauna da maman nin su inji yanda za'ayi batun kayan d'akin su in yaso sai muyi magana da Hajiyar kano tunda ga yanda abun yazo"

A daren Baba Auta yaja Mommy Hauwa zuwa sashen Baba Adamu basu tashi a zaman nasuba sai da suka kira Hajiyar kano suka gama magana akan kayan d'akin su Meenal din akan duk yanda ake ciki batun wajen zaman su Meenal din zasu kirata a yayin zaman nasu ne kuma suka kira itama Momin Abuja dan suji ko akwai inda Fauziya zata zauna acan din an kuma samu dan ashe tuni shima Sheikh ya tanaji gidan da zai zauna da nashi iyalin batun auren ne dai yaki maida hankali, Baba Usman suka kira akan batun wajen zaman Meenal shi kuma daya tambayi Hajiya sai tace mishi a sashen marigayi zasu zauna kafin ya k'arasa ginin shi su koma Kaduna, a cikin daren komai na shirin biki ya kammala a gidan Malam Sa'eed aka tura can gidan Hajiya ya taho da Meenal da Sultana,

a gefen Meenal tun bayan data haura sama bata k'ara marmarin saukowa ba, a sanda kuma ta fara jiyo hayaniya a cikin gidan ta dauki hakan kawai a matsayin gayyar hajiya ne dan haka sai bata wani damu kanta cewa sai ta sauko ta duba abinda akeyi ba, su kuma daga Moon har Sultana babu wacce ta neme ta har saida Meelat ta iso gidan sune kuma suka kira Maryam suka bata labari saidai koda suka haura saman sunyi bugun kofar d'akin da meenal ke ciki har sun gaji amma haka tayi kunnen uwar shegu dasu tak'i bude musu kofar har suka gaji suka juya,

Bayan anyi sallan ishsha'i har d'akin Hajiya tabi Meenal d'auke da takardar gidan da Sarki ya siya da sunan Aminatun, tana zama Larai ta shigo da abincin da Hajiya tasa ta d'iboma Meenal din tana ajiye mata ta fice ta barsu,
Ita kuma Meenal tun shigar Hajiya d'akin dama ta wani d'aure fuska dan karma Hajiya tace zata wani bata labarin yanda sukayi acan gidan su,

"Kina nan kin kulle kai a d'aki uwa dai wata matar mamaci kinaji ana hayaniya kin kasa fitowa Sarauniya Aminatu to ni dana matsu ai gani na biyo sahu, d'auki takardar nan ki dubamin ko takardar menene?"
Hajiya ta fad'a tana mika mata takardar, amsa tayi ta fara dubawa tun bata kammala ba ta d'ago kanta tana maida kallonta kan Hajiya,

"Hajiya... Tarar numfasjin ta Hajiya tayi da cewa,
"Eh abindai da kika karanta a rubuce haka yake, ba kullum burin ki shine ki siyama Baban ki Malam gida ba? To ga gida nan yau kin mallaka dan haka sai kije ki mallaka mishi sai me kuma kike da muradi yanzun? Iye uwar malam"

"Hajiya gida na?"

"Kwarai kuwa gidan ki yanzun nidai tukuici kawai ya rage ki bani tunda na isar da nawa sak'on"

Rungume takardar Meenal tayi tana dariya sosai cike da jin dadi tace,

"Hajiya kece kika siyamin gidan?"

"To da dai nace bazan fad'a miki gaskiyar wanda ya siya gidan ba saboda shi dai dan Allah yayi kuma yana son hakan ya zama sirri ba tareda kowa ya sani ba amma dai yanzun naga babu amfanin boyewa"

"Waye ya siyamin gidan to?"
Ta kara tambaya, ita kuma Hajiya ta amsa mata da cewa Sarki ne ya siya gidan kuma yace kar a fad'a miki amma ni nasan zaki rik'e wannan sirrin dan ko Moon bana so taji labari haka ma sauran mutanen gidan ku idan iyayen ki sun tambaya ki fad'a musu cewa kudin kayan ki dana siyar ne muka hada aka siya gidan dashi "

Duk da bayanin da Hajiyar tayi mata amma haka taso ta botse kan cewa ita ai tana da kudin ta kuma dasu zata siyama Malam din gidan, sai da suka hau sama suka sauko kafin Hajiya tace,
"Ki shirya Sa'eed zaizo ya maidake gida"

"Gida kuma Hajiya saboda me?"

"Saboda kin zama matar aure in kuma zakiyi zaman kine kawai basai munyi wahalar zuwa d'auko ki mu dawo dake nan din ba ai shike nan"

"Waima matar aure"ta fad'a tana tab'e baki dan bata d'auki maganar da mahimmanci ba,
Ficewa Hajiya tayi kuma itace da kanta taja kunnen Sultana akan koda wasa karta ta yarda zancen auren a gaban Meenal kuma koda Sa'eed din ya iso Hajiya da kanta tama Meenal din jagora suka fita ta kofar kitchen har suka bar gidan babu wanda ya lura da Meenal din,

*muje a gurguje*

Washe gari komai da Malam ya buk'ata tun daga kan lefe zuwa duk wani abun buk'ata haka su Hajiya suka shiryo suka kawo gidan Malam kaya bani da kaya ba abin ma dai kamar da gayya sukayi shi dan su nuna ma Malam cewa basu gaji tsiya ba na bakin hajiya,
Suma kuma gidan Malam din a ranar sukaje suka shirya ma Meenal sashen da aka ware mata a gidan Hajiyan matsayin inda zata zauna harka dai na arzik'i rab'a rab'a haka yake gudana tsakanin gidajen dan kowa baya son aga gazawar shi,

A ranar da Meenal ta koma gida ba k'aramin bori tayi ba,
Kenan dai ya tabbata ita kenan bata da gatan da za'aji ta bakinta aduk sanda zancen aurenta ya tashi, dan Allah yanzun hakan da suka aikata mata shi basai yayi zaton ko dama can an gaji da ita bane shi yasa kawai daga zuwa tambaya za'a wani ce an d'aura mata aure,
Haka dai tayi borin ta gaji babu wanda yabi ta kanta sai Fauxieyerh ce ta koma ban baki dan ita Sultana cewa tayi wai karyar iskanci Meenal din keyi,

Baki fa duk sun hallara yan nesa dana kusa sai harkar arziki kawai akeyi kai in kaga nima bazakace wai bikin da yazo babu shiri akeyi badan kowa ya saki jiki ana harkoki amma banda Meenal wacce ta d'auke ma kowa wuta ciki harda kawayen ta, suko basu wani damu ba dan sun san fushin ta bazai sauya komai ba,

*Ranar juma'a*

murmushin gefen baki yayi yana mai cigaba da kirar wayar sai dai har yanzun daga can gefen ita da yake aikama kiran bata dauki wayar ba,
Da alamun damuwa akan fuskar shi ya bude kofar motar da yake ciki ya zuro kafar shi daya waje daya tana ciki,
fita yayi daga gefen kira zuwa gefen tura sakonni yaci gaba da rubutu......

Abokan shi dake daura da motar da yake ciki a zaune ne suka karaso dukan su cikin shiga na Alfarma sunsha wanka har ba'a tantance kalolin turarukansu,daya daga cikin sune ya bude murfin motan ta gefen mai zaman banza sai dai duk da yaji sanda suka karaso da kuma surutun da suke mishi akai hakan baisa ya dago kai ya kalle suba har saida ya kammala rubuta sakon ya kuma turashi zuwa inda yake so in bata dauki kiraba ai dole zataga sako,
Fuskarshi cike da murmushin da yaki rabuwa da fuskar tashi tun daga ranar laraba zuwa yau daya kasance juma'a duk da cewa dama yakan dan saki fuskar ta shi sai dai sam baza'a sashi cikin mutane masu yawan fara'a ba,
amma yau kam kowa ya shaida yawan fara'ar tashi tana da nasaba da samun cikar burin zuciyar shi da yayi a wacce yake da tabbacin tarewar ta a d'akin shi yau dan hakan ne zai kara tabbatar da kasancewar su ma'aurata.
"Abakar ya akayi kun sallame sune?"ya tambayi wani abokin shi bayan ya gama shan kamshi,
"Eh kusan hakan Dan su abba sun wuce tun dazun nasa su hafees suyima sauran jagora gamai bukatar zuwa"
"ok" kawai ya iya fada yana mai kara duban wayan shi a zaton shi ko zai samu amsar sakon daya tura mata sai dai har yanzun dai ba wani sako daga wannan lambar,
"Da kyau Dr"
ya fada a bayyane yana mai fita daga cikin motan mika mishi hannu sauran abokan sukayi suna masu tayashi murna dafatan dorewar zaman lafiya da fatan samun zuria masu albarkha! shi kuma yana amsa musu da "ameen nagode" Abakar ne ya matso gefen shi hannu ya mika mishi
"congratulations once again my brother". . Thanks abuu nagode sannu da kokari allah yabar zumunci, ya fada yana mai runguman abakar din ta gefe.

(jar uba) aka fada daga gefe "
lallai kullu yaci amanar koko, wai gayun nan tun ban mutuba zasu fara wareni" karasowa yayi ya hada su duka biyun ya rungume haka suma sauran abokan su Yusuf Musty Sadeeq Faisal kamar da sauran su suka karaso suma suka rungume su abun dai gwanin burgewa.
"Kai! Kai!! Kai!!! Kai Dan allah ku cikani duk kun wani dakune ni kamar sabon jariri a hannun juya kar ku taramin gajiya tun daren baiyi ba ku cikani dallah"
Fashewa abokan sukayi da dariya baki daya,
" Ah to eh mana gaskiya kunsha dani nida ya dace in rungumi yar amaryata kawai wasu gaddawa daku kunzo kuna dakunata,gaskiya duk wanda ya k'ara rungume ni sai nayi mishi Allah ya isa"
sadeeq ne yakai mashi duka shi kuma saiya goce

"Eh lallai Mai Jama'a amma ba komai ai munyi mai wuyar tunda munyi tsayin daka har an daura amma zakaci ubanka wallahi ai daurawa akayi bata tareba. idan banje na zugata ba kacanza min suna, kai imba banda Allah yana sonka ba taya har zaka rigani yin aure nema?"
ya karashe fada yana rike haba irin abun ya kai mishi ko ina din nan,ba tareda yadamu da abun da sadeeq din yace ba ya kalli Abuu yana me cewa,.
"Wai kunsan yarinyar nan tunda gari ya waye nike kiran ta taki daukar min waya?kuma fa tun ranar laraba da tayi min rashin kunya bamu k'ara had'uwa ba ta gudu gidan su" ya karashe maganar yana mai girgiza kanshi dan abinda ta mishi fa ya bashi haushi,
Murmushi abakar yayi musty ne kuma yace " kai haba mai jama'a karka wani bata ranka shareta kawai ai duk wayon amarya ko taki ko taso dole dai sai ansha manta balle wannan amaryar da tazo a lokacin da ake cikin halin rabbana atinaa.....kai da kake cike da yunwanta, share kawai AK yau dai insha allah bamu ba baccin dare har sai mun kai amarya dakinta"

"ko a kafadane kuwa", wani daga cikin su ya karasa mish,
wani kuma daga cikin su yace "kaga koh zance wasan buya,
kin daukar waya,
dama duk wata dojewa ya kare yau dole kuturu yasha ladan aski" Haka dai sukaci gaba da sakin layi suma,
kun san mazama sun iya sakin layi wani lokacin kamar dai mu mata 😅.
Basu bar harabar masallacin ba sai da yawancin jama'a suka watse sannan suma suka shiga cikin nasu motocin suka dauki hanya a tsanake kuma a jere suke tafe gwanin burgewa ba tareda wani ya wuce wani ba, tun daga tudun wada har zuwa GRA gidan Sadeeq . """"""


""""Meenal kuma a gefeta gaba daya ta kasa masalta yanayin da zatace ta tsinci kaita a ciki yau juma'a da take da tabbacin cewa yau za'a mik'ata d'akin ta dan yanda taga ana ta shirye alamun sun nuna mata hakan,
a kasan zuciyarta ta sani bata bakin ciki ko kadan amma a gefe guda kuma cike take da fargaban auren nan da yazo babu shiri dan haka tun safe take gujema idanuwan mutane badan komai ba sai dan yanda abokan wasan su suke neman saki ta gaba da tsokana dan haka ta gudu can gefen Baba Malam dan nan ne bashi da cin koso bata baro can d'inba sai da aka taso daga masallacin juma'a saboda bak'in da tasan zasu cika sashen dan haka sai ta fice ta lallab'a ta dawo sashen su ta shige d'akin Baba Auta.
Kwance take a kan gado tunani ne kawai ya cika mata kai sai faman mulmula take daga farkon gado zuwa karashen shi kamar mai nakuda ko kuma ciwon mara,
a dai dai lokacin da hayaniyar mutane ya karu saboda walimar da ake gudanar wa na mata anan cikin gidan haka itama zuciyarta taci gaba da gudu bata kara sarewa ba har sai sanda kunnuwanta suka jiyomata shelan da malaman keyi cewa a fito da Amare Bata karasa jin karshen zancen ba tafashe da matsanan cin kuka tana mai ambatar innalillahi wa'ainnah ilaihir'raju'un........ Haka naci gaba da maimaitawa tun ina kukan da karfi harya zamana hawaye ne ke fita ba muryar ihu,
Ita Allah ya sani ba'a yanda ta tsara abubuwa suke zuwa mata ba, ita shikenan bata da halin da zata more nata rayuwar shi kenan kullum sai aureta yayi ta zuwa mata a hagun ce babu wanda yake damuwa da ra'ayi ko abinda take muradi, "Allah sarki su Meelat sudai sunji dadi wallahi komai nasu a tsare ba irin naga da yake zuwa da arangizo ba".
Ta fada tana mai cigaba da zubda hawaye "me yasa komai nawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login