Showing 27001 words to 30000 words out of 190771 words

Chapter 10 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1525

hoton yarinyar nan yaji ya zak'u yakai gareta dan ya ganta a fili dan yasan zatafi kyan kallo a zahiri, kwana biyun da Joseph yace mishi zaiyi dai dai da sanda shima zai koma KD dan haka yana komawa Lagos zai wuce,

Bai tashi daga wannan sak'ar zucin ba har sai da kirar Sa'eed ya riske shi inda yake ce mishi ya dawo mishi da zab'in gidan da yake ganin yafi dacewa,
Babu b'ata lokaci ko ya k'ara jawo laptop d'in ya kunna, a wannan daren dai bai kwanta ba sai da ya kira wanda batun gidan ke hannun shi ya kuma tura mishi Number din Sa'eed akan ya kirashi a gobe suje dashi yaga gidan sai suyi ciniki duk yanda akayi sai su fad'a mishi, ya kuma turama Sa'eed din number din mutumin shima.

Bayan kwana biyu,
Ya samu damar kammala aikin daya kaishi Calaba lafiya lau cikida tarin nasarori, dan haka ya tattara zuwa Kaduna, baiyi yunkurin zuwa Zaria ba yadai kira Sa'eed din shida Salman akan suzo su same shi,
Dan haka a randa ya iso suma suka isa kadunar sun samu wancan mutumin ma da za'a siya gidan a hannun shi har ya rigasu zuwa ma, koda suka isa su d'in ya aika bank suka ciro kud'in gidan millions of Naira, abunda ya Sa'eed matuk'ar mamaki shine ganin takardun gidan d'auke da sunan Aminatu b'aro b'aro, hakan yasa bayan wucewar wanda aka siya gidan a hannun shi Sa'eed ya kasa shiru sai da yayi magana da cewa.

"Sarki kunyi mantuwa fa wajen suna a takardun"

"Bamuyi mantuwa ba Sa'eed sunan da ka gani akan takardar na mamallakiyar gidan ne a yanzun"

"Meenal?"
Sa'eed ya anbata da alamar tambaya.

"Kwarai ita d'in dai domin ta cancan ta shi yasa na siya mata, itama kuma kyauta zatayi dashi ko zaka cemin baka san buri kanta bane?"

Cike da mamakin dabai saki Sa'eed din ba ya amsa da cewa,

"Burin ta uku,
Zama likita
Hawa babbar motar da zata kasance mallakinta
Na ukun kuma shine idan tayi kud'i ta ginama Baba Malam k'aton gida ya koma can shi kad'ai yabar family house"

"Madallah ashe baka manta burukan kanwar taka ba, to cikon na ukun ne na cika mata, sai dai ina rokon alfarmar maganar ta tsaya a tsakanin ni da kai sai ita Meenal din shi yasa kaga na aiki Salman ban bashi daman dazai san komai akan maganar ba dan bana son matsala dan ina gudun kar hassada ya shiga tsakanin ta da yan uwana na yarda da kai shi yasa na damk'a komai a hannun ka, idan ka kai mata ita zata gabatar ma Baba Malam dashi a matsayin daga wajen ta ya fito,
Ban san yaushe zatayi hakan ba amma ina fatan zaka tayani rufe maganar nan?"

"Insha Allah Ya'ya kamar yanda ka yarda dani bazakaga sab'anin abunda kake zato daga wajena ba, mungode ubangiji Allah ya k'ara arziki dan ba Meenal ce kad'ai zatayi godiya ba harda ni nima dan ba ita kad'ai ce take da burin canza ma Malam muhallin zama ba harda mu muna sai dai duk bamuyi yunkurin yin hakan bane saboda munsan bazai amince ba amma idan abun ya fito daga wajen ta tabbas bazai k'i amsa ba dan shima yasan ta rayu da burin gina mishi gidan dama tun tana k'aramar ta,
Mungode kwarai ubangiji Allah ya cigaba da bud'e maka kofofi na alkhairi yasa ka gama da iyaye lafiya, Allah ya raya iyali ya kuma kareka daga sharrin Makiya"
Ya k'arasa fad'a yana dukewa zuwa kasa,

"Kai miye haka tashi mana so kake Salman ya shigo ya fara tambayar ba'asi, dan Allah tashi ko ka manta nima yaron Malam ne tun kafin a haifo ku?"

Bayan dawowar Salman daya aika kasuwa yin siyayyar abubuwan da yasan za'a buk'ata a gidan ne kuma ya had'a musu da tsarabar daya taho dashi daga Calaba, sai da ya ware na gidan su dana gidan Malam sannan suma d'in ya jik'asu da nera sukayi Sallama da juna suka kamo hanya dan jirgin yamma zaibi zuwa Lagos dan haka yana buk'atar hutu sosai kafin yamma.



*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ[8/27, 5:20 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*BOOK 2*


*PAGE 11*


Tun safe Sarki ya k'ira d'aya daga cikin yaran shi dake can Lagos d'in ya bashi umarni akan su gyara mishi gidan kafin ya iso,
Domin dai dama koda ma ace matar gidan tana gidan idan yayi tafiyan daya dad'e baije Lagos din ba to kafin ya dawo su yake turawa su kintsa mishi gidan dan ita dai Teemah haka Allah yayi ta da rashin iya gyaran waje baya tunanin kuma zata iya canzawa,
ita dai barta a tsaftar jikin ta tsaftar muhalli ne dai bata da katabus, dan zata iya wanka sau goma a rana amma ba tareda damu da sharan d'aki ko sau d'aya a rana ba,

dan dama tun bayan barin shi Lagos da aka maida shi KD aiki ya zamana ta samu freedom dan haka tuni ta d'auki yar aikin dake mata komai daya shafi aikin gida sai in Sarki yazo garine shine mai aikin ke dena zuwa idan ya koma kuma saita dawo da ita, duk da yanda zuciyar shi ke azalzalan shi akan ya kirata domin ya shaida mata zuwan nashi k'iyawa yayi, dan tun bayan barin ta zaria dama yayi alwashin cewa bazai kirata ba har sai in itace ta kirashi da kanta tunda har ta iya tsallakewa tabar garin bada izinin shiba, yasan fushin rashin gaskiyar data sabayi a duk sanda suka samu sab'ani koda ko ace shine mai gaskiya ba itaba shi takeyi a yanzun d'in ma,
jira take ya kirata ya kaskantar dakai yana bata hak'uri kamar yanda ta saba ita kuma sai taji dad'in kafa mishi tarin sharud'an da baya iya tsallakewa a wancan lokacin yanzun kam ko kusa bayajin zai iya zubar da kanshi akan abunda yasan cewa koda ya aikata aiba haramun ya aikata ba, tunda ita yarinyar da take tunanin ya kwanta da ita d'in ai matar shice ta aure wanda ya biya sadaki kamar yanda ya biya nata sadakin itama,

Ana cewa mata na kishi amma gaskiya wani kishin yana zarce ka'ida dan kishin teemah akan shi in batayi wasa ba sai ta d'aura ma kanta lalurar da babu mai mata maganin shi,
Duk da yasan cewa a ayyukan da take aikatawa shima yana da nashi kason laifin domin shine tun farko ya sake mata, ta yanda ta samu damar aikata duk abunda take so batare daya takura taba,
Ya sani cewa yana son matar shi sosai domin shi din irin mutanen nan ne da basa iya cusa ma kansu son abunda baiyi dai dai da ra'ayin suba, Teemar shi itace mace ta farko daya fara so,
Yaso ta da dukkan zuciyar shi sai dai baiyi zaton cewa zatayi amfani da soyayyan da yake mata wajen juya akalar rayuwar shiba,bai sani ba ko soyayyar da yake nuna mata ne yayi yawan da take ganin kamar bazai tab'a iya rayuwa da ko wacce mace ba sai ita, ta manta cewar shi d'in namiji ne musulmi kuma wanda Allah ya halatta ma yin mace sama da biyu ma tunda yana da halin da zai auro su,
duk da cewa yana da tabbacin cewa ita ma d'in tana matuk'ar kaunar shi, koba komai ai duk inda kaga kishi tofa yana tafe ne a cike da soyayya, matsalarta d'aya da bata iya sarrafa kishinta a duk sanda ya motsa mata sai kuma daraja da matsayin da miji yake dashi a wajen matar shi wanda ita bata duba wannan darajar in ta tashi magana dashi kai tsaye takeyi babu wani girmamawa ko ladabi,

bata san inta aikata ba dai daiba ta duk'ar da kai ta nemi afuwa, ah ah a kullum ita gani take cewa ita dai itace akan dai dai.
Zaije Lagos da kuduri ne guda biyu,
na farko dan ya samu dai daito tsakanin shi da matar shi, dan a yanzun bayajin zai iya d'aukar wani sabon kalubalen da zata iya kawo mishi, dan haka zaiyi bakin kokarin shi wajen saita ta ta dawo kamar ko wacce macen kwaran da miji zaiyi alfahari da ita,
Miye matsalar ta?
Kud'i sune abunda tafi bawa mahimmanci fiye da auren ta, shima kuma Allah ya wadata shi yana da kud'in dan haka zai sakar mata su inhar zata dawo mishi kalar matar da yake fata, maganar aikin ta a can kuma duk yanda take son shi dole zata hak'ura ne ta dawo KD taci gaba da aikin zai nemar mata transfer in kuma tace a'ah tofa zai bata zab'ine yasan a yanda take son shi bazata yarda ta zab'i aikin ta akan shi ba, idan sun dawo nan Kaduna kuma zasuje suba uwar gida hak'uri ta dawo musu da yaran su a hannun su dan yana buk'atar had'e kan ahalin shi waje d'aya yana son yaran shi su taso da so da kaunar junar da yataso a cikin shi tsakanin shi da nashi k'annen,

Sai kudurin shi na biyu, dan zuwa yaga Moon yarinyar da tunda yayi tozali da hotunan ta suka kafe mishi a kahon zuciya,
Joseph ya Kira shi akan ya kammala duk wani binciken daya sashi yayi a kanta, yanzun sauran aikin nashi ne, shi dai a gefen shi ta mishi % percent bai san koshi d'in zai samu karb'uwa a wajen taba, sai dai kuma zaiyi iya bakin kokarin shi wajen shawo kanta harta amince dashi ba tareda ya nemi taimako daga wajen Meenal ba shi kadai zaiyi ma kanshi yak'i saboda ba iya farin cikin shi yason ya inganta ba harda na Mahaifiyar shi yasan cewa zataji dad'i kwarai inta samu labarin yana neman aure balle kuma idan taji cewa yarinyar tana da alaqa da Meenal,

ร—ร—ร—ร—ร—ร—

Alhamdulillah ya samu isa garin na Lagos lafiya, Joseph daya Kira tun kafin ya taso ya shaida mishi lokacin isowar shi,
Shi d'in ne ya d'auko shi daga Airport sai da suka tsaya a wani restaurant sukayi takeaway kafin suka k'arasa gidan shi,
Envelope d'in da yake kunshe da bayanan binciken da Joseph yayi mishi akan Moon ya gabatar mishi sama sama ya mishi bayani akan ta domin suna cikin tattaunawar ne shi Joseph din ya samu Kira na gaggawa akan an wuce da matar shi asibiti zata haihu, wannan kiran shiya katse komai duk da Joseph d'in yaso Sarki ya zauna dan ya huta shi yaje asibitin amma Sarki ya nuna mishi cewa babu komai su tafi taren kawai,
Dan haka suka rankaya zuwa asibitin, motar Joseph a gaba motar Sarki da d'aya daga cikin sojojin dake gadin gidan yake ja kuma suna binshi a baya a haka har suka isa asibitin, koda suka je sun samu an shiga da Matar Joseph din d'akin haihuwa sai iyayen matar dana Joseph din ne a wajen suna zaman jiran tsammani,
Basu yi tsayuwa na mintuna 20 a wajen ba ya farajin muryar d'an shi Abubakar da suke Kira da Boy yana kwala kiran sunan shi,

"Daddy! Daddy!! Daddy oyoyo ga dady"
Yaron yake fad'a da harshen turanci a yayin da ya k'araso da gudu cike da murna ya rungume uban nashi,
Wanda shima Sarki mamaki yake akan su kuma me sukazo yi a asibitin da daren nan, duk da mamakin da yake ciki hakan bai sa ya kasa nuna farin cikin shi na ganin sanyin idaniyar shi a dai dai wannan lokacin ba koba komai shima yayi kewar yaron nashi, dan haka sai yasa hannu ya d'ago shi yana jefa shi sama yana cafewa,

"Oh my Boy kaida waye kuka fito da daren nan daya kamata ace kana kan gado kaima kana bacci?"
Sarki ya tambaya, sai dai mai makon Boy ya bashi amsa sai shima ya jefo mishi tambaya kamar haka,

"Daddy kaima kazo duba Baby da Smole Mom tace Momy zata haifa ne koh"
Ya tambaya yana shafa fuskar baban cike da farin cikin ganin baban nashi da yayi a lokacin,

"Sabon Baby na Momyn ka kuma? Ita kuma Momyn naka tana ina?"

Ba tareda yaron ya damu ba ya amsa mishi da cewa,
"Ai tana ciki kuma kullum ma anan take kwana ko nace ta tashi mu koma gida bata zuwa"

Sosai kan sarki ya d'aure dan bai fahimci surutan da Boy ke mishi ba inya fahimta dai dai fa yaron yana nufin Teemah tana nan asibitin kuma wai anan take kwana bata komawa gida, ga sabon Baby da yaji Boy d'in ya ambata, to kenan Teemah nada ciki kenan?

"Kai da waye kukazo nan?"

"Smole Momy" ya amsa yana nuna mishi inda Aziza ke can gefe tana amsa waya da alama bata san cewa Boy ya sulale a wajen ba, shi kuma sarki dama tunda yaji yaron ya ambaci smole Momy yasan ita yake nufi dan duka yaran haka suke kiranta,
Excusing kanshi yayi daga nan inda su Joseph suke ya kama hannun yaron suka k'arasa inda Aziza take,
Da gudu Boy ya k'arasa wajen yana fad'a mata cewa ga dadin shi yazo ganin Momy da baby,
Gaisuwa sukayi tsakanin ta da Sarki cike da girmamawa tana mishi barka da zuwa, bai iyace mata komai ba harta mishi jagora zuwa d'akin da Teemah take, wanda isar su yayi dai dai da fitowar Brigadier general Abubakar da matar shi Aunty Rahma daga d'akin na Teemah,
Dan haka babu b'ata lokaci Sarki ya zube zuwa k'asa domin nuna girmamawa ga sirikan nashi da suka rik'eshi tamkar d'ansu,

Anty ce kawai ta amsa gaisuwar nashi tana tambayar shi yanzun ya iso?
Shiko General k'arasawa yayi ya kamo hannun shi ya mik'ar dashi tsaye,

"Baban Junior bana hakana duk'amin irin haka ba,"

"Ayi hak'uri zan cigaba da kiyayewa mun same ku lafiya? Ya mai jikin ta k'araji?"

"Alhamdulillah mai jiki tana samun kulawa dan d'azun danayi magana da Dr yace min zuwa gaba kad'an zasu bamu ita mu koma gida har sai in lokacin haihuwar yazo gab sai mu dawo, ai jiki alhamdulillah taji sauk'i sosai fa, ya hanya da wajen aikin ka kuma?"

"Lafiya lau, ita kuma Allah ya bata lafiya,"

"Ameen" Brig ya amsa dashi kafin ya d'aura da cewa,

"Gashi kana zuwa mu kuma muna shirin tafiya, ko zamu jiraka idan ka dubata sai mu wuce gida gaba d'aya kaga sai ka samu kaci abunci dan nasan kila bakaci komai ba kayo nan, kasan sunan basa barin yan jinya na kwana"

"Ai babu damuwa kuyi gaba kawai Sir na riga naci abinci kafin in fito kuma bani kad'ai bane tare muke da Friend dina shima matar shi na d'akin haihuwa,"

"Oh Allah sarki to allah ya raba lafiya mu bari muyi gaba to sai da safe"

Juyawa yayi sai da ya raka su har mota kafin su wuce kuma sai da suka duba matar Joseph sai dai har lokacin bata sauka ba tana dai ta fama,
Duk yanda suka so Boy yabi su ko kuma yabi Aziza da mijinta Imran yazo d'aukarta k'iyawa yayi akan shi wajen Daddy zai tsaya dole haka suka hakura suka wuce shi kuma ya koma ciki rungume da Boy din dake ta bashi labarai,
Da sallama d'auke a bakin shi ya bud'e kofar d'akin ya shiga,

Kwance saman gadon da aka tanadar dan marasa lafiya take kwance tundaga kafafuwanta zuwa saman cikin ta rufe da farin lallausan bargo ita kuma kuma tana kwance ne amma fuskanta na kallon kofar shigowa,
Domin tun isowar shi wajen taji muryar shi, bata da k'arfin da zata yunk'ura ta fito wajen dan ta tabbatar ko shi d'inne shi yasa kawai taci gaba da kwanciya tana kallon kofar shigowar,
Bayan ta dena jin motsin su a wajen kuma sosai tsoro ya kamata Allah yasa dai ba juyawa yayi suka tafi tareda su Aunty ba, kenan har abunda ta aikata yakai matakin da Sarki zai shigo cikin asibitin amma ya kasa shigowa ya dubata shine ya juya ya koma?
Kenan bai damu da halin da take ciki ba komai yake shirin faruwa da ita?
Tunda ta dawo fa ko sau d'aya batayi sakacin da wayarta ta rasa caji ko kuma wayar tayi nisa da ita ba duk dai a tsammanin ta na ganin kiran shi, amma kullum haka Gari zai waye rana ta k'ara fad'uwa babu amo ba labari,
A sanda batun Sakin Meenal ya risketa a gadon asibitin nan duk da tana kwance ne cikin ciwo amma ta samu sauk'in nauyin da zuciyar ta ke mata na yawan tunanin da take cewa mijinta nacan tare da wata suna cin soyayya ita kuma gata nan a gadon asibiti ciwo ya hanata sakat,
Tayi zaton tunda akayi sakin zai tattaro ya dawo wajen tane sai kuma taji shiru, shine kuma yau d'in daya iso ya kasa shigowa dubata ya juya,

Tana cikin wannan bak'in cikin ne ta k'ara jiyo muryoyin su shida Boy sai kuma gasu sun shigo d'in, ashe dai har yanzun mijinta na sonta,
Hakan kuma yana nufin cewa ita dai Fateemah itace kad'ai zata dauwama a matsayin matar mijin ta, lallai idan taji sauk'i ziyara na musamman zata kaima OBA dan tasan wannan aikin nashi ne, ashe bai manta da ita ba duk da dad'ewar da tayi bata ziyarce shiba gashi kuma shi baya rik'e waya balle ta kirashi.


*****
A gefen Meelat ko tun washe garin ranar da ta amshi key din gidan Sarki a wajen Hajiya suka isa gidan ita da Maryam kamar yanda suka tsara,
Zama sukayi suka ware suturun na Meenal tsaf suka musu screening suka ware mata wad'anda sukafi buk'atar tayi amfani dasu,
sauran kuma suka kimtsa mata su a gefe, duk wani abunda suka san zata buk'ata saida suka d'aukar mata tundaga kan gyale, takalma da jakun kuna, dan sai da suka mak'are manyan akwatuna biyu da kaya, da suka kuma kawo mata kayan harta da kayan ta na nan gidan Hajiyar suma sai da suka tantance su, basu huta ba haka washe gari suka k'ara shiga kasuwa suka sissiyo abubuwan da suke buk'ata,
Badai su sarara ba sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login