Showing 72001 words to 75000 words out of 190771 words
har zuwa sanda zata gama wanka in yaso sai ta koma gidan tunda dai ita ba takabar mutuwar zatayi ba sakamakon haihuwar da tayi,
A haka aka rabu sai dai anbar mata Innar yara da kuma wata mace yayar Aunty Murja sune zasu zauna da ita yaranta biyu kuma dama Babban da mai bi mashi tun kafin rasuwar mijin nasu rik'on su ya koma hannun kanin mijin da matar shi da suke zaune a Abuja wad'anda Allah bai basu haihuwa ba,
A lokacin da duka ahalin suka fito da niyyar tafiya ne Meenal ta gabatar musu da sabuwar Motar ta da AK ya bata dan Farouq ne da yake ta ganin tana zirga zirga da motan a yayin zuwa gidan rasuwar yau ya gaji yake tambayar ta, ina ta samo d'anin mota,
Hajiya ce ta ceceta ta bashi amsa da cewa,
"Yayan ta ne ya bata ita tunda shi ya tara su da yawa baya hawa, sunyi mata Allah sanya alkhairi kafin suka kama hanyar komawa Zaria daga garin na Kaduna.
*BAYAN WASU KWANAKI*
Kamar yanda Sultana tace wajen Meenal zata sauka hakan ne ya faru domin sati d'aya kacal sukayi a unguwar Malamai family house shima dan kunyar da Meenal takeji na Hajiya ne yasa ta yanke hukuncin su sauka a can d'in ga kuma yan uwan su na kano da mutanen Abuja wad'anda suke gidan har yanzun basu koma ba,
Matan auren ne kawai Malam ya kora gidajen su washe garin ranar da suka dawo daga kadunan,
A kuma ranar da suka dawo Baba Adamu yayi amfani da wannan damar na had'uwar ahalin waje d'aya wajen had'a kan ahalin kwansu da kwarkwata ya k'ara ja musu kunne akan kulla da zumunci dan kar suga cewa basa gari d'aya suce zasu yarda zumuntan dake tsakanin su da sauran yan uwan su da suke zaune a wani wajen ya lalace, dukan su sunji dad'in wannan zaman domin anan suka k'ara sanin juna suka tantance wannan shine wane d'an wane yana zaune a waje kaza, sun kuma yanke hukuncin bud'e WhatsApp group wanda zasu cigaba da zumunci a ciki da tattauna abunda ya shafesu a cikin shi dan haka sai da sukayi exchanging numbers din junan su kowa ya ajiye number din dan uwan shi a wayar shi.
A kuma wannan zaman na kwanaki da Meenal tayi a gidan ne suka fara yar tsama da Yayan su Naseer wato yayan Sultana wanda kowa ke kira da Sheikh,
Abu na farko daya fara had'asu shine irin yanda tana malam yana nan nan dashi,
Magana d'aya biyu zaice a kira mishi Sheikh,
In dare yayi koda zataje cin abinci wajen Malam d'in kamar yanda suka saba a baya zata iske shi Sheikh din a hakimce a falon ko yana duba littafai ko kuma yana yin wani abun mai mahimmanci,
Tun ba'aje ko ina ba ta fahimci cewa ba k'aramin kusanci ne tsakanin Malam dashi Sheikh din ba dan haka tuni kishin ta ya motsa da gayya wani lokacin idan ta shigo falon taban shi zaune kuma malam baya nan sai tak'i gaishe shi tayi komawar ta, dan a farko in tazo ta kan zauna ta jira malam shi kuma na bakin ta da iyayen shi a wannan zaman zaiyi ta jefo mata tarin tambayoyin shi da basa k'arewa, abun haushin kuma bazai tab'a zama da kai kuyi hira dashi na minti goma da yaren hausa ba,
Ah ah magana d'aya biyu da kun fara dashi zai fara sako mata runkuma runkuman labarcin shi badan Allah yasa Malam yayi tsaye a kanta tun tana k'arama wajen ganin ta iya larabcin ba lallai da ba k'aramin kunya zata shaba,
To fisabilillahi larabcin nan dai tunda ba yaren da aka haifi mutum dashi bane ai sai ya tsaya a iya nashi yaren koh?
To shi da gaske so yake sai yakai k'arshen nata larabcin da take riritawa, to jama'a ita dake karatun likitanci yare nawa ake son ta rik'e ne?
Kuma dan wulakanci ko turanci kake mishi shi bazai tab'a amsa maka ba sai ma yayi uwar shegu dakai kamar bai san me kake cewa ba,
Da farko tayi zaton ko turancin ne bayaji sai daga baya data tambayi Sultana shine take ce mata wai ai Ya Sheikh yana jin yare sama da goma saboda k'asashen da yake karatu duk yanayin yaren su,
Ita kuma tun ranar sai ta kuduri aniyar cewa sai ta rama wallahi, dan haka koya mata magana da larabci ita kuma sai ta maida mishi da yaren hausa,
Daga baya sai ya tsiro musu da karatun safe dana dare,
Da zarar an idar da sallan asuba dana ishsha'i duka yaran gidan zasu taru a falon Malam ayi karatun,
Taso ta doje tak'i zuwa amma ba hali dan Mommy Hauwa da kanta take korata dan da ita ake karatun,
Amma wai duk yawan yaran gidan nan d'an bawan Allahn nan idan ya tashi jefo tambayan shi bazai jefa akan kowa ba sai a kanta ita marainiya wayon shi salon in bata amsa dai daiba yasa yara su rainata,
Dan haka dan dole ta zak'ulo littafan ta da suke karatun tare da baba malam a shekarun baya tana musu maraji'a gudun kar a samu bacin rana aji kunya,
Abu dai kamar wanda ya asirce ahalin gaba d'aya domin kowa zancen shi shine ya sheikh,
Ya sheikh kaza ya sheikh yayi kaza, dan haka kowa ma a gidan ya fara bata haushi,
Wata rana sun shigo gidan ita da Sultana daga gidan su Meelat suke domin tunda suka dawo suke cigaba da gudanar da shirye shiryen bikin su babu kama hannun yaro,
Har sun gota parking lot d'in gidan ta jawo Sultana suka dawo daga baya sakamakon Muryar Sheikh da taji cikin harshen turanci yana magana a waya,
Sun dade tsaye a wajen tana k'ara sauraren yanda yake fitar da lafiyayyen turancin yana kuma had'awa da wani yaren da bata san ko na wani k'asa bane,
Ita dai Sultana da taga tsayuwar bamai k'arewa bane gashi kuma ita fitsari ya matse ta kawai sai tayi wucewar ta ciki tabar Meenal d'in a wajen,
Nauyin ido yanaji ya mishi yawa ne yasa shi kuma ya yanke wayar ya juyo dan yaga waye a wajen,
"Me kikeyi anan?"
Ya tambaya da harshen larabci kamar yanda ya saba,
Ita kuma sai ta amsa mishi da turanci cewa,
"Kallon ka nikeyi mana ina kuma sauraron ka kana turanci bayan kuma ni kullum idan nayi maka magana da yaren nuna min kakeyi kamar bakajin me nake cewa"
Murmushi yayi kafin ya taso daga inda yake ya matso kusan ta sai da ya gota ta kafin yaci burki, bai juyoba ya amsa mata da cewa,
"Yaren turanci ba shine yaren da zamu tashi dashi bayan mutuwar muba, shi yasa sam baya burgeni"
"To amma kuma ai gashi nan naji ka iya sosai kanayi kamar a cikin su ka rayu!"
"Ke da kika iya kikeyi a cikin su kika rayu ne?"
"Ah ah ta bashi amsa tana girgiza kai,
"Ok niko kinga a cikin larabawa na rayu shi yasa na iya yaren su, kuma ko ba komai ai yaren shugaban annabawa ne koh?"
Yana gama fad'in hakan yayi gaba abinshi ya wuce ya barta a nan tsaye tana binshi da kallo cike da burgewa,
Malam daya shigo tun d'azun tsayuwar Sheikh din ya hanga a kusa da Meenal k'arasowan shi inda suke hakan yasa yaji duk abunda suka tattauna sai shima yaji Sheikh din ya k'ara daraja da kima mai girma a idon shi koba komai dai gashi duk tarin ilimin bokon da yake dashi hakan bai sa ya yarda yaren addinin shiba.
Wallahi babu editing kwana biyun nan rubutun kawai nikeyi, kuyi hakuri da mistakes
*Ummiee ce*โ๐ผ
[9/11, 10:31 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*Page 25*
Wani abu mai girma ne ya d'arsu a cikin zuciyar Malam a dai dai wannan lokacin,
domin dama tunda Sheikh d'in ya iso garin na Zaria Allah yasa shakuwa da fahimtar juna a tsakanin shi da Malam domin Allah ya wadata Sheikh Naseer d'in da tarin ilimin addini sosai har gobe kuma yana kan neman ilimin ne bawai ya dena ba,
dan haka da yazo sai ya sauke kanshi yake cigaba da d'aukar karatu a wajen Malam duk lokacin da Malam din yake gida,wani lokacin ma shine yake wakiltan Malam wajen karantar da dattawan dake d'aukar karatun bayan ishsha'i a wajen Malam d'in,
Idan kuma Malam ya fita zai zauna yayi ta nazarin tarin littafan da suke falon na Malam, wannan halin nashi da Malam ya lura dashi na jajircewa wajen neman ilimin addini ne kuma yasa ya k'ara kusanci sosai a tsakanin su,
Irin su Sheikh dole duk mutumin daya mu'amalance su yayi sha'awar had'a zuria dasu
Domin dai babu ta gefen da yake da tawaya a rayuwar shi, matashin saurayi ne mai jini a jika dan duka duka bazai wuce shekaru 34 zuwa da 6 ba dan gatan da tun tashin shi bai san wahalar komai ba sai na neman ilimin da yasa a gaba,
Wannan dalilin ne kuma yasa har yanzun ko tsayayyar budurwa baya da ita dan ko batun auren ma bai farayi ba tukun duk da cewa yanzun haka kannin shi maza biyu dake bi mishi duk sunyi aure sun barshi, iyayen shi kuma basu matsa mishi da zancen auren bane saboda sun san ko yayi auren tofa matar bazata samu kusancin dako wacce macce take samu tsakanin ta da mijin ta ba, saboda shi dai wani irin mutum ne mai matuk'ar son sirri a rayuwar shi kwata kwata baya son wani abu da zai had'ashi da jama'a balle kuma wani ya takura mishi,
Yafi gane ya keb'e kanshi waje d'aya yayi ta karance karancen shi,
Sai dai kuma shidin dan ka'idane dukan rayuwar shi yana gudanar da ita ne akan koyarwar addini d'an boko ne na gidi sai dai gaba d'aya baya mu'amalah irin tasu ko a sutura yafi ta'amali da kayan mu na hausawa in basu ba kuma to koda yaushe zaka same shine sanye cikin jallabiya inba a cikin d'akin shi ba bazaka tab'a samun shi cikin shiga ta k'ananun kaya ba,
hakan ne kuma yasa duk wanda zai zauna dashi dole saiya zama mai kiyaye iyakoki domin abu k'ank'ani zaka aikata yanzun nan ya zaunar da kai ya fara karanto maka Allah yace annabi yace,
Shifa tun tashin shi bai yarda yayi aboki ko d'aya ba, abokan shi sune kannin shi,
Yana da fasali da k'ira mai kyau ga kuma cikar halitta kyakyawan namiji ne sosai sai dai bashi da hasken fata,
Domin kaf yaran gidan su farare ne tass amma shi sai ya surka kalar tashi fatar batayi haske irin nasu ba amma kuma tashi sai tafi tasu d'aukar idon mai kallo shi ba bak'i bane ba kuma zamu sashi cikin sahun bak'ake ba ah ah yafi kama da bak'aken larabawa kamar yanda mutane da dama suke fasalta shi,
Ganin farko idan ka mishi zaka hango tsabar hutu da tsaftar dake tare dashi dan shi saboda tsabar sanin ciwon kai ko d'an guje guje ko d'aga karfen da matasan zamani keyi bayayin su baya da kiba ko kadan ba kuma zamu kirashi da siriri ba komai nashi dai dai shi Allah ya mishi,
Tun daga wannan ranar Malam yake ta neman hanyar da zai k'ir k'iri kusanci tsakanin Meenal da Sheikh domin shi dai yana ganin cewa Sheikh ne irin mijin da ya cancan ci auren Meenal dinshi, yasan idan har suka had'a kansu babu wanda bazaiyi farin ciki da hakan ba dan ya tabbatar da cewa idan Meenal ta auri Sheikh zataji dad'in zama dashi sosai ga soyayyar da zata samu daga dangin shi kuma domin ya tabbatar da cewa Momin Abuja zata kula da Meenal d'in kamar yanda zata kula da Sultana,
sai dai bazaiyi gaggawa ba saboda baya son yayi wani abun dazai k'ara kawo nakasu a cikin rayuwar Meenal d'in a karo nabiyu zaifi kowa farin ciki idan ya kasance cewa sune suka had'a kansu bawai auren had'i ba.
Dan haka sai ya zamana shima Sheikh din duk in suna tareda Malam sai malam yayi ta yabon kyawawan halayen Meenal d'in a gaban shi haka zaiyi ta bashi labaran daya shafi Meenal d'in harda irin yanda tayi nata yarintar da kalar rikicin da tayi tayi kafin auren ta, har rikicin da tayi lokacin auren ta da Sarki duk sai da ya bashi labari,
Wannan dalilin ne kuma yasa shima Sheikh d'in yake kokarin nuna kulawar shi aka Meenal din dan ya tabbatar da kaunar da Malam yake mata kamar yanda ya dad'e yana jin ana fad'a, abunda shi kuma bai sani ba shine wannan kusancin dake tsakanin shi da Malam shine abu na farko daya fara jawo mishi bak'in jini a wajena Meenal dan gaba d'aya zaman shi a sashen malam din yasa gaba d'aya kota shiga wajen ita kuma bata sakewa.
kullum idan Meenal taje wajen Malam sai yasan yanda yayi ya sako mata zancen Sheikh kullum Malam cikin yaba kyawawan halayen shi yakeyi a gaban ta, a kokarin shi na ganin ya cusa musu ra'ayin juna sai ya zamana duk wani abu daya shafi sheikh d'in Meenal yake sawa tun daga gyaran d'akin da Sheikh d'in yake kwana wanda yake anan cikin sashen na malam abincin da sheikh d'in zaici kai wani abun haushin ma ko aike malam zaiyi sai ya had'a meenal din da sheikh yace suje tare,
Ita kuma gaba d'aya abun nan ya kai mata ko ina bata dai da yanda zatayi ne kawai, dan sosai fa sheikh yake shiga mata hanci da kudundine ba dama yaga ta zauna tana kallon films dannar waya ko wani abun zai wani fara mata wa'azi cewa da zaman da takeyi da qur'ani ko wasu littafan ta d'auko ta karanta,
kai mutumin nan fa ya kai mata ko ina kamar akan shi aka saukar da ustazanci shi yak'i ya saki jikin shi yayi enjoying life din shi haka yake son duk wanda yake rayuwa a kusa dashi ya rayu kamar shi dai, haba dan jama'a a ina ake gudanar da rayuwa babu nishad'i naga dai ko abinci bashi ciyuwa sai an sarrafa shi da kayan d'and'ano.
Wai saboda tsabar sa ido irin na ustazun nan wata rana sun shirya tsaf zasu fita ita da Sultana Tudun jukun suke son zuwa ita dasu Maryam a wannan ranar, har sun sallami Mommy Hauwa suna shirin fita sai Ya Sa'eed ya shigo sashen nasu,
Bayan sun gaisa ne yake tambayar ta cewa,
"Meenal yaushe zaki koma Tudun wada dan akwai sakon ki a hannu na amma nafi so sai kin koma sai inzo muyi magana ko kin dawo nan d'in kenan gaba d'aya?"
"Ah ah wallahi nikam ban dauwa ma a gidan nan indai wancan sabon ustazun na cikin shi, komawa na kuma yana iya kamawa ako wani lokaci, duk Anbi an tara yan sa ido a cikin gidan ne zan zauna tab'
In maganar tana da mahimmanci ka bari idan na dawo zanzo sashen ku sai kuyi maganar acan"
"Ah ah sirri ne bana so kowa yaji shi yasa ki bari kawai idan kin koma can sai inzo,
Ina zakuje yanzun? "
"Tudun jukun zamuje daga nan zamu wuce G R A gidan Sa'adatu mukai mata anko kasan mu yanzun kuma ba zama, yauwa Yayana nace tunda dai kamin allah sanya alkhairi na mota har yanzun baka bani kud'in sa mai a motar ba!"
"Oh yanzun kuma wajena za'a amshi kud'in man kenan?"
"Ah ah nifa ba wai na rok'a bane amma dai idan ka bani bazan k'i amsa ba kasan ai nidai bana maida hannun kyauta baya"
Hannu yasa a cikin aljihun shi ya zaro wallet din shi yan dubu dubu ya zaro bai k'irga ko nawa bane ya mik'a mata,
"Gashi in kuma bazai isa ba in kun fita sai ki biya wajen Farouq ki amsa ko kuma a wajen shi sabon ustazun shima"
"Ai da ina kusa bazaka b'ata kud'in nan bama, ke Meenal ina ce d'azun nan kika amshi kud'in mai a hannun Abban ku? Anya kina da tausayi kuwa? kin san bazaki iya cacar siya ma motar mai ba kika amshi kyautar ta nifa bana son wannan d'abiar naki na titsiye mutum kisa ya miki kyautar da baiyi niyya ba, ko kuma shi kenan tunda kin san suna baki komai kike so sai ki tun karesu kai tsaye, suma fa suna da nasu iyalan a k'ark'ashin su, ke baki da wani matsala sai dai a baki kud'i ki kashe"
Cewar mommy Hauwa
"To Mommy tsakani da Allah in ban amshi kud'i a hannun suba ai ko Allah ma sai ya tambayeni gani da yayye maza da yawa yarinya yar dangi to so ake inje in rok'a a wani wajen daban bayan gasu nan reras kin haifo musu ni,
Ai hak'uri kawai zasuyi su dage da nema Allah kuma yaci gaba da bud'e musu k'ofofi na alkhairi suyi ta bani ina Tarawa a nawa asusun Allah Mommy kud'i nike son tarawa masu yawa in Siyama Babana gida yaje can gefe ya huta da hayaniyar jikokin da suka cika mishi gida.
Da sauri Meenal din ta fice daga falon tana dariya,
Tsaye a wajen motar ta ta iske Sultana,
"Me kike jira kuma da baki tada motar ba?"
Ta tambaya tana shirin zagayawa gefen mai zaman banza dan in zasu fita Sultanar ce ke jan motar dama tunda suka dawo,
"Zonan kema!"
Tajiyo muryar Sheikh yana bata umarni daga bayan ta,
"Na'am nii ina kwana!" Ta fad'i nii d'in tana nuna kanta saboda ta tantance koda ita d'in yake yi,
"Lafiya lau eh kefa ina zaku? Ina lura da yanda kullum sai kun fita daga gidan nan bakwa kuma dawowa da wuri ina kuke zuwa? "
"Gidan Sa'adatu zamuje"
Meenal ta bashi amsa,
"A hakan