Showing 15001 words to 18000 words out of 190771 words
kasa tsayuwa har saida lalube yasamu ya lalubo jikin bango ya jingina kafin ya sulale zuwa k'asa yana mai had'e jikin shi waje d'aya,
Kafin ya wani k'ara cusa fuskar shi cikin tafin hannun yana mai matse cinyoyin shi waje d'aya,kamar wani wanda yake cikin matsanan cin tsoro.
Yasan bazai taba iya kai kanshi d'aki a hakan da yake ba hakan nema yasa koda wasa baiyi gigin sauka matakalar da sunan sauka k'asa ba dan yasan wallahi yana iya missing step ya mulmula zuwa k'asan yaji ma kanshi ciwo a banza, ya dad'e zaune a wajen a kallah dai sai da yayi zama na wajen mintuna goma yana k'ok'arin ganin ya samar ma kanshi nutsuwar daya rasa a lokacin,
sai dai kuma hoton dake cikin kwalwalwar shifa sam ya kasa gogeshi dan har yanzun hoton yawo miki mishi a cikin kwayar ido kamar dai har yanzun d'in itace dai a gaban nashi a yanda ya ganta,
Tafin hannun shi daya rufe fuskar shi dashi yad'an fara warewa kad'an kad'an yana lek'o idon shi ta tsakanin yatsun dan yagani ko ta fito ne ko tana ciki sakamakon motsin da kofar dakin nata yayi,
ganin cewar ba itace ta fito ba hakan yasa ya dafa dakyar ya samu ya mik'e a dudduke ya samu ya shige d'akin da yake gefen nata wanda shine yafi kusa dashi,
"Wannan yarinyar in banyi wasa ba saita sa zuciyata ta buga na mace tun lokacin mutuwar nawa baiyi ba"
Ya samu damar furtawa a bayyane a yayinda ya samu yakai kanshi zuwa ga gadon dake cikin d'akin ya kwanta a wahalce.
Ita ko mutuniyar a gefen ta tun bayan data had'o tea dinta a kitchen a gurguje tasha tea d'in dan so take ta fita da wuri dan tama hajiya k'aryar cewa tana da lecture din safe ne alhalin su kuma kasuwa suka shirya zuwa yau d'in ita dasu Meelat dan Wallahi bata zama gida haka kawai Hajiya sai faman wani kimeta takeyi a cikin gida ita ba matar aure ba alhalin koda take da auren shi mijin ba kulle yake mata ba,
Yanzun kuma da take ganin ta samu free ta zama sakakkiyar tsuntsuwa shine kawai Hajiya zata wani k'irk'iro mata da wani zaman idan ganin ido wanda kowa yasan babu ta inda iddan ya kamata, haba ina ma dalili ai in hajiya tasan wata tofa bata san wata ba dan Wallahi babu abun da zai mata sha maki da shirin bikin da sukeyi na Meelat,
Bayan ta gama shan shayin d'akin Hajiya ta lek'a, ganin ta kwance rashe rashe a gado hakan yasa ta dawo da baya ta fad'a daki da gudu ta shek'o wanka a gurguje,
Tofa ta fito ne tana shafa mai ta farajin sallama tsakani da Allah kuma ita bata d'auki ko muryar waye bane, dalilin kin amsawarta da wuri kuma ita tayi zaton cewa ko Hajiyar ne shi yasa da farko ta shareta duk da tana jin sallamar tak'i amsawa har sai a sallamar k'arshe,
Bata tab'a zaton cewa wai idan AK ya hauro saman zai iya yunkurin shigowa d'akin ta ba dan bai tab'a kwatanta aikata mata hakan ba, domin ko zaman da tayi a gidan shekarun baya ko saman baya haurowa, hakan nema yasa koda taji motsin bud'e kofar d'akin bata wani damu da son d'ago kai dan ganin ko waye mai shigowan ba dan sau da yawa Hajiyar kan biyota d'akin su sha hirar su,
Sai gashi yau saboda rashin sa'a wani k'aton ya fad'o mata cikin d'aki a d'ai dai lokacin da take kok'arin sa riga alhalin yau ko bra bata saba,
Saboda dama ita idan tana period to bata babu bra dan nonuwan ta kan cicciko ne su kama mata ciwo na rashin dalili ko rigar da zai matseta bata sawa balle kuma bra,
Allah ma ya taimaketa ta riga ta zura dogon wandon skin tight a jikin ta aida yaci amanar ta da yawa wallahi kuma ko yanzun saita Allah kawai amma fa wallahi bata yafe ba,
Domin yafa shammace ta da yawa shigowar nashi d'akin yayi dai dai ne da sanda ta d'aga hannun ta sama da niyyar zura rigar ta, motsin shigowar ne kuma yasata juyowa a zaton ta Hajiya ce, wanda motsin juyin nata ne kuma yaba albarkatun k'irjinta daman juyawan da k'arfi suma, hakan kuma duka akan idon bawan Allah ya faru, karon farko a rayuwar shi da yaga halittar mace a waje b'aro b'aro bawai a tv ko kuma hoto ba,
Ita kuma ta juyo da zummar ganin Hajiya kawai sai tayi gamo da wani bak'on halittan yau a cikin d'akin nata wanda ya fad'o mata ba tareda gayyata ba ko neman izinin shiga ba,
Zaku sha dariya in kuka hango yanda ta buga wani uban tsalle gaba d'aya uwa wacce taga dodon da zai iya cinyeta a take, wanda tsallen nata shi kuma ya k'ara haifar mishi da wani sabon tashin hankali a cikin ruhi da jiki, dan haka babu shiri shima ya juya,
Ita kuma jikin ta ya shiga mazari kamar wata wacce ta kwana a waje a lokacin hunturu,
Da gudu ta k'arasa wajen kofar ta tura shi da k'arfi ta murza mishi key kafin ta sulale a jikin kofar itama ta zauna,
Ajiyar zuciya kawai take faman saukewa, kafin ta fara bori anan wajen daga zaune ta fara watsa k'afafuwa tana buga hannayenta a k'asa,
"Wallahi Allah sai ya saka min kawai shi kenan mutum sai ya wani shigomin d'aki babu izini duk ya gama ganina babu kaya"
Kukan tab'ara taci gaba da yi tana cigaba da fad'in,
"Allah dai ya isana wallahi shi kenan ya gama kalle min Mamaa,"
Mai da duban ta kan k'irjin nata tayi, kamar kuma wacce aka tsikara sai ta k'ara fashewa da kuka yayinda tasa hannuwan ta ta kare su dashi domin dai tuni dama tayi watsi da rigarta a can gefe,
"Nidai wallahi ban yafema ganina da babu riga da akayi ba kuma Allah ma sai ya sakamin"
Ta fad'a tana share tsilli tsillin hawayen da suka taru a idon ta,
Ta dad'e zaune a wajen kafin ta rarrafa ta d'auko rigar sai da ta kakkab'e shi tana cigaba da mitar cewa bata yafeba kafin ta zura rigar sai kuma ta nemi waje ta zauna domin dai duk saurin da take wallahi bazata tab'a yarda ta sauka k'asa ba a yanzun balle kuma tsautsayi yasa su had'u dan bata san da idon da zata kalle shiba, dan tasan yana ganin ta yanzun Maman ta kawai zai dunga hangowa koda ko daga nesa ne,
Wannan hasashen nata kad'ai ba k'aramin kunya da bak'in ciki ya k'ara mata ba, dan haka sai kawai ta koma ta kwanta ta janyo wayarta ta kira Maryam akan subar tafiyar sai zuwa anjima, domin tasan ba zaman gidan sosai yafiye yiba in yana gari, a nata nufin wai in ya fita itama sai ta fice kunga kenan bazasu had'u ba.
Shiko jikan innah can ya mak'ale a d'aki sai faman burgima yake a gado,
Pillow biyu ya rungume d'aya a tsakanin cinyoyin shi d'ayan kuma ya rungume shi a k'irji, da kyar ya samu bacci b'arawo ya silalo ya yi wuf dashi.
*CIKIN MAFARKI*
A cikin mota suke tafe shida ita sai dai kuma yanda yake tuk'in motar kamar mai shirin shiga rami ne abunda zai baka mamaki, domin kowa yasan yanda baya d'aga k'afa wajen bama mota wuta a duk sanda ya zama na shine matuk'in motar,
Da wannan tukin nashi suka samu suka k'araso cikin gidan na Hajiya har zuwa lokacin kuma tana ankare da yanda hankalin shi ya rabu biyu rabi a kanta rabi kuma akan tuk'in da yakeyi,
Can cikin lungu a wajen da ake parking motocin gidan ya k'arasa da motar duk da yanda wajen yake da d'an duhuwa saboda bishiyoyin dake wajen sab'anin ainihin wajen parking d'in da yake da haske sosai,
Koda ta yaka motar batayi yunkurin fita daga cikin motar ba, haka shima daya gyara zaman shi yana mai binta da kallo kamar ya lasheta haka yake ji a lokacin kuma ya kasa furta mata koda kalma d'aya ne,
Har sai da suka shafe a kalla tsayin mintuna 10 suna bin juna da mayen kallo, kafin ta bud'e baki tana ci gaba da kallon nashi tace,
"Me yasa kayi parking anan sab'anin bayan mu inda kowa ke ajiye nashi motar?"
"Bana son kowa ya ganin min ke shi yasa na yanke hukuncin tsayawa anan har sai kowa ya shige ciki"
Ya bata amsa.
"Saboda me to yasa hakan?"
Ta k'ara tambaya tana mai cigaba da binshi da ido, wani irin kallo take mishi mai sa mutuwar gab'ob'i,
"Saboda ina kishin abunda nike so mana bakiga wad'ancan masu gadin yanda sukayi tsai-tsaye kamar wasu masu gadin fada bane!"
Ya fad'i hakan a yayinda yake mata nuni da glass din gaban driver na cikin motar wanda ta ciki yake iya kallon abunda akeyi a cikin gidan.
Murmushi tayi tana kauda fuska gefe bayan ta rufe fuskar da tafukan hannayen ta alamun jin kunya,
"Kin san me?"
Girgiza kanta tayi alamun Ah ah ba tareda ta bashi amsa da baki ba.
"A kullum fatana shine in dauwama tare dake har zuwa karshen numfashi na" sai kuma yayi shiru,
Dan haka itama sai tayi shiru bata iya cewa bata iya cewa komai ba,
Shirun da motar yayi ga kuma sanyin ac da kamshin turaren jikin sune suka had'u suka bada wani irin daddad'an yanayi,
Wanda hakan ne kuma ya haifar da mutuwar gabb'an jikin kowannen su, ji yake ina ma zai iya daya jawota cikin jikin shi ya k'ank'ame kozai samu sa'idah akan yanda yake jin jinin jikin shi yana yamutsawa,
"Shshshshuuuu"
Taja dogon iska ta bakinta sakamakon sanyin data kejin yana huda tsigar jikinta yana ratsa tsokarta yana shiga mata cikin k'ashi,
Sai dai kuma fitar iskar bakin ta zama yayi kamar wani d'an sak'o ko kuma ince abunda akayi shi da gayya domin kuwa kai tsaye ya wuce cikin kunnen AK ya ratsa har zuwa cikin zuciyar dake bugawa a cikin k'irjin shi,
Jikin shi a mace ya jefa mata tambaya da cewa.
"Miye wannan?"
Bai jira ta amsa ba yaci gaba da cewa..
"Ko kinajin sanyi ne in kashe ac?"
Shiru tayi bata amsa ba, can kuma sai ta zura hannunta a cikin handbag dinta dake ajiye akan tsinyoyin ta,
Ta ciro jambaki sai da ta kunna hasken gaban motar ta kuma karkato da glass din dake wajen yanda zata iya ganin fuskarta da kyau ta cikin shi sannan ta goga janbakin a saman kyawawan lab'b'anta,
Chocolate ta ciro a cikin Jakar bayan ta maida janbakin, saida ta bud'e shi ta gutsira taci sannan ta mik'a mishi,
Shiko komawa yayi kamar wani sakago wajen kallon ta dan suma ne kad'ai ya rage mishi a yanda dai yake kallon bakin data bi ta shafe tass da jambaki ga kuma yanda take wani taunar chocolate din cike da jan rai,
Dan Allah inba neman fitina ba miye na wani shafa jambaki da daren nan fisabilillahi, binta yaci gaba dayi da kallo yayinda wasu miyagun miyan kwadayi suka cika mishi baki har sai da kyar yake iya had'esu,
Hasasowa kawai yake na yanda zai cinye bakin nan nata idan ya kamata.
Chocolate din ta mik'a mishi,
"Zakaci chocolate din ne kayi shiru?"
Murya a rarrabe cike da ininan daya fara a yanzun yanzun ya amsa mata da cewa.
"Ah ah ah niba chocolate nike soba"
"Mi kake so to?"
"Bakin"
Ya tsinci kanshi da furtawa cikin tuntub'en harshe,
Shiru tayi ba tareda ta kalleshi ba taci gaba dacin chocolate d'inta kamar bataji shiba,
A cikin zuciyar ta kuwa cewa take "haba malam ashe dai baka shigo hannu da kyau ba har yanzun da sauran ka to shi kenan muje zuwa"
Kallonta shima yaci gaba dayi can kuma dai ya kasa daurewa dan haka ya kira sunan ta a sanyaye yanzun din ma dai kamar d'azun muryar tashi da ininan da bata sanshi da ita ba ya kira sunan da yake kiranta dashi.
"๐ Heart"
Hummm ta amsa,
"Zan iya sumbatar ki"
"kwafal kwafal"
Wani munafukin tari ya sark'eta a bazata sakamakon shak'ewar da tayi da chocolate din bakin ta,
"Ki barni please in sumbace ki sau d'aya kawai, sau d'aya kacal"
Ya fad'a cike da rok'o yana marairaice wa,
"Tofa anzo wajen" ta fad'a a cikin zuciyar ta, a bayyane koh cewa tayi.
"Heart amma hakan fa sam sam babu kyau๐
๐ปโโ๏ธ"
Ta furta tana mai duk'ar da kanta cike da kunya,
"To shike nan tunda kin hanani"
Ya fad'a da karyayyen muryar dake nuna alamun sam baiji dad'iba,
Har yayi shiru kamar ya hak'ura sai kuma can ya juyo, "Dan Allah Heart sau d'aya kawai please ๐"
"Ka tabbata sau d'ayan kacal ne?"
"Eh na tabbata" ya fada yana mai matso da jikin shi zuwa kujerar da take sosai,
Yana binta ita kuma tana k'ara zuwa baya gashi kuma ta wani k'ankame jikinta sosai ta cure a waje d'aya,
Duk'owa yayi sosai zuwa jikin ta ba kuma wai ya had'e jikin nasu bane, a rashin sani hannun shi guda 1 daya dafe sitiyari dashi ya danna horn din motar ji kake motar ta bada sautin biiiiieeee da k'arfi.
"Waiyo waiyo waiyo wallahi Allah ni babu ruwana shine"
Meenal ta furta a firgice,
Cike da zafin nama shi kuma ya koma inda ya taso yana wani babbasarwa bayan ya lek'a dan ganin ko wani yayo tanan inda suke a cikin masu gadin gidan sai dai kuma babu wanda yake tahowa,
"Na sumbace ki!"
Ya fad'a hankali kwance,
"A yaushe?" Ta tambaya,
"D'azun mana!"
"A ina?" Ta kara tambaya.
"A kumatun ki da goshin ki"
Ya bata amsa.
"Kai ๐ณ"
Ta furta tana zare ido,
Kafin ta janyo jikinta zuwa inda yake.
"Ke miye hakan?" Ya tambaya yana makalewa a jikin kofa,
"Ki koma mazaunin ki ni wasa nike miki"
"Wasa?๐คจ ok ni kuma da gaske nikeyi in fad'a maka muahhh"
ta sake mishi sumba mai k'ara a fatar bakin shi, karar sumbar kai tsaye ya wuce cikin kunne ya cake shi a kahon zuciya, dan haka luuu yayi baya uwa wanda yake shirin somewa,
Ganin hakan yasa ita kuma ta koma kujerar ta tana fashewa da dariyar yanda taga yayi, yunkurowa yayi da niyyar cafkota sai dai kuma kafin ta ankare ita kuma ta balle murfin kofan gefen ta ta fice daga motar tana nuna shi tana kuma ci gaba da dariya a lokaci daya,
"Dawo mana kinji tsoro ne?"
"Ah tsoro halal ne"
"Dan Allah kizo please ๐"
"Kai Heart kai bakajin kunya nane? wai"
"Kunya fa naji kina magana akai bayan kinsa na rasa kunyar tawa a yanzun nan, me yayi saura kuma?"
"Aure" ta bashi amsa tana rufe fuska, kafin ta juya taci gaba da tafiya duk kiran da yake mata da cewar da yakeyi ta jira shi hakan bai sa ta tsaya ba,
"Kai Abdul!
Kai Abdul!!
Mai Jama'a fa, wai baka jina ne bazaka tashi ba kazo ka kwanta kamar wani mai shafar aljannu sai wani faman kiran sunan Heart kakeyi a'ah ba heart ba zuciya, dallah can tashi, ni anya kuwa Yaron nan ba dagaske bane kuwa da ake cewa ko aljannah ce ta aure ka shi yasa kake k'in kula yan mata ba kuwa?,
To inba haka ba miye wani na kwanciya kana mafarki da kiran sunan Heart da rana tsaka? Tashi da Allah ni bana son lalaci kana namiji kana baccin hantsi"
Duk surutan da Hajiya keyi tsaf yake jin duk abunda take cewa sai dai kuma gaba d'aya bashi da karfin dazai yunkura ya tashi, dan hatta labban shi ma ji yayi sun mishi nauyi ta yanda ya kasa bud'esu balle ya tanka mata ko sau daya ne dan tasan ya tashi.
Kuyi hakuri da guda 1 bamu da wuta ne wallahi kuma na cinye cajin wayar tun safe shi yasa.
Babu editing fa๐คจ
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[8/22, 7:00 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
*~{{MY FAMILY}}~ BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
* ~{Ummiee Zaria}~*โ๐ผ
___*Page 7*
Kuyi hak'uri jiya nayi mistake wajen rubuta number mai makon insa page 6 saina k'ara maimaita number 5,
***Kai Abdul shin wai kodai dannau d'in dake danne mutane in suna baccine ya danneka shi yasa ka kasa tashi ne ban sani ba?"
Ganin cewa babu mai bata amsa a d'akin kuma shima da take magana dashi d'in bai nuna alamun cewa yana jinta bane hakan yasa ta koma da baya ta shiga cikin bathroom din dake d'akin, wani k'aramin roba ta ciko da ruwa sannan ta fito,
Ta gefen kanshi ta koma tayi tsaye tana k'are mishi kallo, can kuma sai tasa hannun ta ta zare pillow d'in da kanshi ke kai ta zauna a wajen sai ta maida kanshi akan cinyoyin ta,
Ruwan data d'ibo ta d'auko daga kan side drawer din data ajiye shi sai da ta karanto addu'o'i ta tofa a ruwan kafin ta dunga d'iban ruwan da hannun ta na dama tana shafa mishi bakin ta kuma yana karanto ayatul kursiyyu tana tofa mishi duka a lokaci d'aya,
Shigar ta da kuma fitowar ta cikin bayin duka akan kunnuwan shi hakan ya faru sai dai kuma har zuwa lokacin yak'i bud'e idon shine a nashi zaton in taga bai tashi ba zata fice ne ta bashi waje, kenan idan ta fita shima sai ya lallab'a ya fice a Sashen salin alin ba tareda tasashi a gaba da tambayoyin data fara jera mishi tun yanzun ba,
Sai gashi mai makon yaji ta fice daga d'akin ah ah sai ma saukan sassanyan ruwan da yake da tabbacin a cikin bayin ta dibo shi yaji