Showing 36001 words to 39000 words out of 190771 words
gidan gaisuwar zaku sauka gaba d'aya ko in munyi gaisuwar zamu wuce can gida nane ku sauka a can in yaso gobe ko ban samu damar mai daku gidan gaisuwan ba ita sai in bata mota ta dunga kaiku da safe in dare yayi sai ku dawo, ina ganin kamar hakan zaifi duba da yanda gidan zai cika da mutane nasan zaku fi sakewa a gidana ko ya kuka gani?"
"Eh to kuma kaima dai ka kawo shawara amma dai bazanyi saurin yanke hukunci ba sai mun isa tukun idan naga da takura anan din ai sai mu bika d'in"
"Nidai Hajiya bazan je ko ina ba gaisuwar mutuwa fa mukazo shine kuma za'ace muje wani unguwan mu tare idan gidan nashi kuma yana da nisa fa sai dai inke ce zaki koma can gidan nashi ki tare ke kad'ai?"
"In yana da nisa baga mota ba ko dama a k'afa nace ku taka ne?"
Hajiya ce ta amshi maganar da cewa,
"Nima shi yasa kikaje nace ya bari har muje mu gani in wajen yana da yalwa ai sai muyi zaman mu, nasan dai shima dan yasan bana son takura ne shi yasa yace mu sauka a gidan nashi amma inda nisa ai sai mu hak'ura"
"Balle kuma ba wani nisa Sosai fa Hajiya ina unguwan dosa ina Malali? kedai bakauya ce kawai tunda ba wani sanin garin kikayi sosai ba kifin rijiya kawai baki san ko ina ba daga Zaria sai Zaria yaushe rabon daki k'etare zuwa wani wajen,
yarinya kizo in bud'e miki ido kiga yanda ake wayayyar rayuwa ba irin wacce kika saba gani ba"
"Eh d'in koma mai zakace"
Suna kawo wa dai dai chawai na SMC akan titin unguwan dosan, Meenal ta fara cewa,
"Stop! Stop!! Dan Allah ya'ya ka tsaya"
"Ke meye wai kuma? Me zakiyi in mun tsaya anan?kefa kin cika fitina kamar sauro wallahi "
Sai da ta karkata jikin ta tana waiga baya kafin ta amsa mishi da cewa,
"Dan allah kad'an koma baya kad'an, kaji wallahi chips din wajen nan nike mutuwar so, shuuuu "
Sai kuma taja iska tana bubbud'e kofofin hancin ta,
"Dan Allah kai bakaji yanda kamshi ya cika maka ciki ba?"
"Idan naji kamshin kuma sai mai ya faru? Naga dai yanzun yanzun kika gama ciye ciye balle kice min yunwa kikeji, in ma kin siya kafin ki samu lokacin da zaki zauna kice zakici aiya riga ya huce bazakiji dad'in cinshi ba zafiba kuma, in kina sone ki bari sai anjima ni zan dawo in siya miki harda kaza da kifi ma duka in kina so"
Yayi maganar yana ci gaba da tafiya,
"Kayi alkawari zaka siyamin d'in?"
"Aike bakuwata ce dole in siya miki duk abunda kika gani kina so akwai wani waje ma a can Unguwar Sarki inda suke saida ice cream mai shegen dad'i wallahi, nasan zaki soshi sosai da zarar kika d'and'ana"
"Waiyo Allah dan Allah Ya AK ka kaini, kasan yanda nake bala'in son ice cream kuwa balle wannan tunda naji ka yaba nasan zaiyi dad'i"
"Ai yarinya dan ma ba'a gidana zaku sauka ba dana kaiki yawo kinga yanda cikin garin kaduna take da kayan dad'in da suke dashi naci wanda babu shi a kauyen ku"
"To ai Hajiya tace in munga akwai takura can gidan naka zamu bika, kaga idan mukaje gidan gaisuwa da dare idan mun dawo sai ka Kaini yawon koh? ,
Kuma shine harda wani cema Zaria kauye koh? Allah ma yasa kaima can ka fito"
Dariya yakeyi k'asa kasa, a zuciyar shi ko dad'ine ya rufe shi dan da alama hak'ar shi zata cin ma ruwa kamar yanda yake fata,
"Dan Allah ya AK ka dunga dariya in kuma dariyar ke maka wahala ko murmushin ne ka dunga yi, Allah sosai yake maka kyau in kanayi"
"Oh shi yasa bakya gajiya da kallona kenan?"
"Nidai ai bance maka haka ba kawai dai na fad'a maka gaskiya ne cewa murmushi na maka kyau"
"To tunda kina so zan dunga miki nawa murmushin amma da sharad'i idan na miki murmushin kema zaki min naki murmushin dan naki yafi nawa kyau"
"Eh ai nima na fika kyau shi yasa nafika iya murmushi ma, Yaya kaga kana ta jana da surutu saura kad'an mu wuce layin koh! "
"Ina ne layin nasu?"
Ya tambaya ita kuma ta nuna mishi suka sulala cikin unguwan,
A wannan lokacin zan iya cewa daga shi har ita sun manta da zaman Hajiya a cikin motar barin ma dai shi ,
domin labari kawai suka ci gaba dayi yana bata labarin yanda garin na Kaduna yake da wajajen hutawan da suke cikin cikin garin da alkawarin cewa duk zai kaita wajajen d'aya bayan d'aya kafin su koma,
Su zauna a waje d'aya irin haka na tsayin awanni ace basu yi fad'a yanda suka saba ba sai ma hira mai dad'i dake gudana a tsakanin su, wannan shine na farko,
Kila kuma hakan nada nasaba da kasancewar wannan d'in shine tafiya na farko da suka tab'ayi a cikin mota d'aya a tare,
Tun bata ce mishi nan ne gidan ba ya gane gidan, saboda canopy da kujeru d'in dake kofar gidan ga kuma mutane nata d'aura alwallah dan tuni aketa ta kiran Sallah a masallatai, gefe ya nema shima ya faka nashi motar kamar yanda yaga motocin wasu a wajen,
"Alhamdulillah "Hajiya ta ambata bayan ya faka,
Kallon kallon aka fara tsakanin shi da Meenal, Meenal din ce tayi k'asa da muryar ta sosai tana d'an kwantowa ta inda yake,
"Kai Yaya ashe fa tare muke da Hajiya a cikin motar nan wallahi na manta da ita sam"
Fashewa yayi da dariya
"Aiko sai na fad'a mata"
shima ya fad'a murya can k'asa kamar yanda tayi.
"Kana fad'a mata wallahi bazanje gidan kaba"
ita kuma ta fad'a tana turo baki kafin ta janye jikin ta ta fita daga motan, shima fita yayi ya bud'ema Hajiya kofa,
Ita dai Hajiya yau take ganin ikon Allah,
Wato dai da kad'an da kad'an maganar da Yusuf ya fad'a matane yake k'ara rikediwa zuwa tantagaryar gaskiya ganin idon ta,
To aiko ido zata zuba musu taga iya gudun ruwan mutum dan uban shi ai in yasan wata bai san wata ba, wato ita ya raina zai wani ce mata yarinyar fa k'arama ce bayan gashi a gaban idon ta ba kunya balle tsoron Allah ya tsare yar mutane har tana bashi abinci a baki, daga baya kuma ya b'ige da cewa ko zasu sauka a gidan shi,
Aiko sai tayi maganin shi wallahi tunda yayi da maiyi,
Baibi su zuwa cikin gidan ba anan wajen yayi alwallah ya shige masallacin dake kofar gidan shima dan ya samu jam'i,
Su kuma cikin gidan suka wuce, tun daga harabar suke gaisawa da mutane,
"Ina ne Sashen Raheenat d'in?"
Hajiya ta tambayi Meenal ganin gidan ya kasu sashe sashe,
"Gashi can wancan na ukun mai fenti mai ruwan toka"
"To ai gara mu k'arasa koma samu mu gabatar da sallan muma akan lokaci kinga in mun idar sai mu d'aura da gaishe gaishen dan in muka tsaya gaisuwa da jama'a tofa har sai a kira ishsha'i bamu gama ba"
A kofar falon nata sukayi kicibus da Innar yara wacce ke shirin fitowa,
"Ah ah Hajiya kuna tafe ashe, barkan ku da zuwa hala takwarar kice ta matsa kuka taso da yamman nan?"
"Ah ah wallahi Ameena ai da dan tani ne da tuni ma ina garin to sanda labarin ya iskeni ita kuma tana makaranta bata kuma dawo da wuri ba, ya mukaji da k'arin hakuri ya mai jegon kuma? Tana dai lafiya koh"
"Hakuri sai mai aiki mai jego kuma Alhamdulillah suna lafiya su duka ita da Babyn ku shigo daga ciki"
Bayan ta suka bi zuwa cikin Sashen dake cike shima da matan tun daga kan yan uwan Aunty Murja Maman Raheenat d'in zuwa kan sirikan gidan Malam din su Aunty Billy matar ya Sa'eed Matar Farooq Yayan Meenal d'in dama sauran Matan yayyen Meenal din da wasu daga cikin yaran Malam mata suma,
A tsai-tsaye suka gaisa da mutanen falon hajiya bata yarda ta zauna ba sai fad'i take a nuna mata inda zatayi Sallah,
D'aya daga cikin d'akuna ukun dake falon Innar yara taja Hajiya, dan lokacin Mommy Hauwa tana Sallah itama,
D'aya bayan d'aya Meenal ta gaishe da yan uwanta mata dama matan yayyen nata suka ma juna gaisuwar rashin,
"Mai jegon tana ina?"
Meenal ke tambayar su,
Farida matar Farouq ne ta amsa mata da cewa,
"Tana cikin wancan d'akin"ta karashe da nuna mata d'akin da take nufi d'in,
Mikewa Meenal tayi zuwa d'akin babu mutane sosai a ciki daga Mommy Hauwa sai Matar malam na biyu Dije dake rik'e da jariri ita kuma Mommy Sallah takeyi,
Karasawa inda Dijen ke zaune tayi bayan tayi Sallama dijen ta amsa,sai da takai zaune a gefen gadon dijen ke tambayar ta " yanzun kuka iso", ita kuma ta amsa mata da,
"Eh" tana amsar yaron, dan kyakyawa abunshi sai saiyi yakeyi kamar zai bud'e ido sai kuma ya koma ya rufe,
Tausayin shine ya kamata har idon ta ya cika da kwalla,
Gaisawa sukayi da Dijen tayi mata gaisuwa kafin ta tambayeta uwar yaron,
"Tana cikin makewayi" cewar Dijen,
Yaron na rik'e a hannun ta har Mommy ta shafa add'o'in da takeyi bayan ta idar da Sallah,
Sabon gaisuwa sukayi itama Meenal d'in tayi mata gaisuwa,
"Ina ita Hajiyar take na ganki ke d'aya?"
Momy ta tambaya,
"Tana tareda Innan mu a wancan d'akin dake kusa da wannan"
Mik'ewa Mommy tayi ta fice daga d'akin bayan ta nad'e daddumar da tayi sallan ita kuma Meenal taci gaba da zama yaron rik'e a hannun ta tanaci gaba da kallon shi,
Jin motsin bud'e kofar toilet din da Raheenat tayi ne yasata d'ago kanta da sauri sai kuma ta mik'e da sauri ta d'aura ma Dije yaron akan cinyanta ita kuma da hanzari ta k'arasa wajen Raheenat din suka rungume juna Raheenat din kuma sai ta fashe da kuka saboda ganin Meenal din,
Mai makon Meenal din tayi aikin rarrashi ah'ah sai itama ta biye mata sukaci gaba dayin kukan,
"Amma dai kun san wannan ba abun kwarai kukeyi ba koh, ke dama Meenal zuwa kikayi dan ki sata kuka ne kome, ke kuma Raheenat tun safe fa kike kukan nan amma ace mutum ko gajiya da kukan bayayi, ai ko dad'ewar da kikayi a cikin bayin nasan zuwa kikayi kikasha kukan shi kafin kika fito, fisabilillahi in kuka na dawo da matacce ai duban nin mutane ne zasu dawo duniya bayan sun mutu suci gaba da rayuwa kuma, ki saketa tazo ta zauna taba yaron nan Mama tun bai fara kuka ba, bawan Allah dan ma ta same shi mai hakuri tunda ya fad'o sau biyu kawai fa kika bashi abincin shi"
Sababin da Dije keyi shi yasa Meenal ta sake Raheenat din bawai dan taso ba, tana share mata hawayen ta da sukak'i tsayawa, kafin ta kamo hannun ta ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna,
"ya kikeji a jikin ki akwai inda yake miki ciwo ta ciki ko ta waje?" Meenal ta tambaya,
Girgiza mata kai Raheenat din tayi alamun ah ah,
"Babu inda yake miki ciwo?"
"Babu kirjina ne kawai yake d'anyi min zafi kad'an kad'an"
"Sannu kiyi hakuri kinji, amma kinci abinci?"
"Meenal ban iyacin komai baki na ba dad'i ko yunwa ma banaji"
"Kuma dai kin san bazai yuwu ki rayu da yunwa ba, Mama Dije ki had'o mata tea da abinci taci yanzun dan Allah inta gama sai tasha magani ta kwanta"
To Dijen ta amsa dashi tana mik'ewa ta fice daga d'akin ita kuma Meenal ta zauna taci gaba daba Raheenat din baki wacce keba yaron Nono har ya koma bacci,
Bata tashi ba sai da Dijen ta dawo da abincin kamar yanda Meenal ta buk'ata sannan ta amshi yaron ta kwantar,
Sai da Raheenat ta shanye tea din ta faracin abincin kafin Meenal ta shiga toilet tayi fitsari kana kuma ta d'auro alwallah ta fito ta tada Sallah bayan ta idar bata tashi ba har saida ta gabatar da sallar ishsha'i Hajiya ma kuma ta shigo tayi ma Raheenat d'in gaisuwa,
AK ma ya shigo har cikin Sashen na Raheenat din yayi gaisuwa tareda su ya Sa'eed da Farouq da suka had'u bayan sun fito daga masallaci.
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
[8/29, 10:40 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 15*
Tunda suka shiga cikin falon yake ware ido yaga ta inda zai gano Meenal ko Hajiya sai dai dukan su babu wacce ta fito falon ya daiyi ma mutanen falon gaisuwa Mommy Hauwa ma dake d'aya d'akin da Hajiya take ta fito sun gaisa itama ya mata gaisuwa Raheenat d'in ma ta fito sun gaisa,
Bayan sun fito daga sashen na Raheenat gefe suka koma k'arkashin canopy d'in dake harabar gidan suna ci gaba da hira dan tunda aka idar da ishsha'i yan zaman gaisuwan suka watse sai ya zamana saura yan gidan kawai,
D'aya bayan d'aya matan su Ya Sa'eed suka dunga fitowa sunayin sallama da mazajen su, sai yayi yunk'uri kamar yace su taimaka su kira mishi Meenal sai kuma ya k'asa suna zaune a harabar gidan har karfe 10 na dare ya gota su Ya Sa'eed suka fara haramar komawa masaukin su, dan haka tare suka fito daga cikin gidan dasu Ya Sa'eed d'in sai dai su suna fitowa sukayi Sallama dashi suka shiga motocin su suka wuce masaukin su duk da ya musu tayin zuwa can gidan shi amma suka nuna mishi a'ah karya damu,
Bayan wucewar su shima cikin motar shi ya koma ya kwantar da kujerar motar ya kunna ac sannan ya sanya karatun qur'ani a radio din motar yana bi da sauti mara amo,
Lokaci bayan lokaci yake duba wayar shi a zaton shi wai ko hajiya zata tab'o shi suyi haramar wucewa suma tunda dare ya farayi sai dai kuma shiru,
Sai ya d'auki wayar da niyyar ya kirata kuma sai ya fasa,
Can dai daya kasa sukuni ganin ana neman k'arfe 11 sai kawai ya maze ya lalubo number d'in nata ya doka mata kira,
D'in din din wayar taci gaba da k'ara sai dai kuma harta yanke ba'a d'aga kiran ba, bai gajiya ba haka yaci gaba da danna mata kira ba k'ak'kautawa amma sai da ya mata kira 6 babu wanda ta d'auka,
Ajiyar zuciya ya sauke mai zafi,
To me ya samu Hajiya haka kardai ace hartayi bacci ne ta barshi a kofar gidan mutane ya dakon fitowar su,
Yau rana ta farko da yayi abunda bai tab'ayi ba,
Number d'in Meenal wacce ya dad'e da adanata a cikin wayar shi ya lalubo, ya dad'e yana k'arewa number d'in kallo wacce yayi saving dinta da emoji mai shape d'in ๐ heart,
Ya dad'e yana jayayya tsakanin shi da zuciyar shi, wannan tana fad'i mishi cewa ya kirata kawai dan wannan shine damar da yake dashi na samun kusanci a tsakanin su, yayin da wata zuciyar kuma take ce mishi yayi hak'uri kawai ya wuce ya tafi tunda dare dai ya riga yayi in yaso ai gobe ma rana ce, sai yasan yanda duk zaiyi goben dan yaga sun koma can gidan nashi da kwana,
Sai dai kuma a kokarin shi na fita daga kan number d'in nata kuma kawai sai yayi dialing number din ba tareda ya luraba har saida kara d'in d'in d'in da wayar take alamun cewa kiran yaje kan nata wayar ne ya ankarar dashi,
Da azama har wayar na neman kub'ucewa daga hannun shi yayi saurin yanke wayar yana sauke ajiyar zuciya kamar wani wanda ya had'u da abun tsoro, bai gama dai daita kanshi ba wayar nashi ta fara k'ara, k'ur yama wayar domin kuwa Meenal d'ince ta biyo bayan nashi kiran,
Kamar bazaiyi picking kiran ba sai kuma can dai kiran na gabda katsewa ya runtse idanuwan shi ya amsa kiran nata ba tareda yakai wayar kan kunnen shiba sai kawai ya sata a speaker,
"Assalamu Alaikum"
Tayi sallama daga gefen ta bayan ya d'auki wayar,
"Ameen Alaikum Salam, baku gama bane wai dare yana yifa kice ma Hajiya ku nike jira ina waje a inda mukayi parking d'azun"
Yana gama fada mata hakan yayi saurin yanke kiran ba tareda ya tsaya sauraren amsar da zata bashi ba, dan Allah ya sani bazaiso yaji cewar bazasu bishi zuwa nashi gidan daga bakin taba,
Ita ko ata gefen ta bayan ta idar da Sallah Maryam da Meelat ta kira a waya ta had'asu da Raheenat sukayi mata gaisuwa,
Ta dad'e zaune tare da Raheenat d'in a cikin d'akin dan ko lokacin dasu AK d'in suka shigo sashen tana jin shigowar su bata daiji fita zuwa falon bane shi yasa kawai tayi zaman ta bayan fitan su kuma cika d'akin da suken yayi da yayyin su mata nan kuma sabon hira ya b'arke akan mutuwar auren ta, da yike yawancin su tun bayan mutuwar auren nata basu had'u ba,
Kun san mu mata ba gidan mutuwa ba yasin ko cikin mak'abarta ne sai dai in hirar bata zoba amma sai anyi,
To hirar mutuwar auren Meenal d'in shi ya rage jimamin mutuwar da suke ciki aka cigaba da tattauna batun ko wacce a cikin su na tofa albarkacin bakinta daga masu ganin laifin Sarki sai masu ganin laifin Teemah,
Itafa gaba d'aya ma wallahi ta manta da batun cewa wai zasuje gidan AK dan tunda suka iso ita da Hajiyan kowa nashi sabgar kawai yakeyi,
Bata tashi tunawa ba sai da ta kira, koda ya kirata tana cikin yan uwanta suna hira ita kuma dama bata tab'a saving number din shiba shi yasa koda ya kirata bata san shi bane ganin dai cewa kiran ya katse shi yasa ta biyo bayan kiran dan taji ko waye kuma duk hirar da sukeyi ita bata san dare yayi sosai har haka ba,
Koda ya gama rattafa mata abunda zai fad'a ya yanke wayar,